Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
aka ciremin mahaifa dan haka kullum cikin baza idon wacece abokiyar zamana nake ta ina zata fito ya halinta yake kullum sai nayi addua Allah yakawomin wanda zamu hada kai kuma gashi Allah ya amsamin nasan ki nasan wacece ke insha Allah zaman mu zai burgr kowa ki Allah yasa nan da shekara ki kawowa Kamal k'anne ukku". shiru mommy tayi dan bata san me zata ce mata ba ita gaba daya kunyar ta takeji Dr Hafsat da mommy ne cikin office din mommy Dr Hafsa tace'' wllh ni hjy Fanna banga wani abin damuwa ba Hajja tayi gaskiya dan duk wanda zaice zai aureki dukiyar ki kawai yakeso kiga de cikin mene manki Alhaji Lawan dan uwa na ne uwa daya uba daya amma bisa amana Abdulmajid shi yafi can canta gashi alk'ali malami masani bazai cuceki ba kuma kinsan halinsa". Numfasawa mommy tayi tace'' ummm ni kawai abin yana dauremin kai mutuwar mijina ko shakara 2 ba ayi ba amma awani damu sai nayi aure kuma wllh ina mutukar jin nauyin hjy Aisha duk data nuna abin bai dameta ba amma ai kishi kishi... da gatar da ita Dr tayi dacewa ''a a Maman Nasir karki sa wannan aranki kisa aranki bautan Allah zakijeyi ba jin nauyin wata ba". cikin sati biyu aka daura auren Dr Fanna da Abdulmajid namiji ba kunya aranan a part dinta ya kwana da safe tana zaune gaban mirror tana gyara durin d'an kwalinta ya fito daga wanka towel daure a k'ugunsa yana jifan ta da murmushi tacikin mudubin gaban tane taji ya fadi da ake cewa Abdulmajid da Abdulsamad suna kama ba tagani ba sai yau ta sake tabbatarwa komai nasu irin daya hatta yanayin yanda yake tafiyar da mace kamar a makaranta daya suka koyo ban banci kawai Abdulsamad yafi Abdulmajid haske k'adan tana cikin wannan tunanin taji ya dafa kafadunta da hannayen sa ya daura kansa awuyar ta ruwan jikin sa yana diga jikinta yana cigaba da yimata murmushi yace " dan me akayi mudubi?." bata bashi amsa ba saboda wani irin mamaki da tambayar ya bata idan marigayi ne amsa take bashi da dan ya hasaka sirri fukka shikuma sai yace amma yafi kyau ga masu hasken fata irin ku saboda kinga kekika haska mudubi bashi ya haska kiba,, jinya ciji gefin kunne ta ne ya dawo da ita daga cikin dogon tunanin ta yace Doctor mubudi ma yafi son masu hasken fata irinku kiga kekika haska mirrorn bashi ya haska kiba ". ya k'arashe maganan yana kashe mata ido murmushi tayi tace'' ummmm abin yana bani mamaki ne yawancin kalaman ku irin daya". mek'er da ita yayi tsaye yakai hancinsa dai-dai nata ahankali yake tifo da kalaman acikin mak'ok'oron sa yace my heart ai ba kalamai ba hatta zuciyar mu iri daya dan munyi tarayya da juna dashi azuciya akan abu daya aranan da nafara ganin ki aranan nakamu da soyyyar ki ina shirin gaya miki naci karo da wasiyar Halima naki auri dan uwa na aranan ba k'aramin tashin hankali na shiga ba dak'er da temakon Allah na jure na daukeki amatsayin matar dan uwa na Fatima ban dauki son ki dawasa ba dan Allah ki bani matsugun ni ko ya yake na miki alk'awarin zan shafe Abdulsamad acikin zuciyar ki nin kinga kin tunoshi to wajen addua ne amma bawani abu na rayuwa ba, Fatima I love you all my heart very very gashi kin bani farin cikin a dare daya kin kaini duniyar da ban san ana zuwa ba Fatima Ina miki sonda ban san iyakan saba". zaunar dashi tayi tana masa murmushi tace'' nagode sosai". ta dauko Mai tafara shafa masa aranan de ba dasu akayi breakfast ba har angama watsewa a falon Hajja suka shiga ba itaba shima yaji kunya musamman na uwar gidan sa Aisha Nasir kam sai akwana na biyu yasan gidan nasu ya sauya tsaye yake abakin kofar mommy knocking yake sosai dan amma shiru Agrif yashawo saman yace Nasara zamuyi letty fa Nasir da gaba daya ransa yagama baci yace "dalla jeka ni sai na gaida mommy jiya mafa ban gaidata ba... bude kofar akayi mommy ce daga ita sai rigan bacci zai shiga ciki ta fito ta kama hannusa suka fito ta rufe kofar kallon tuhuma yamata yace "mommy bazamu shiga d'akin ba gaidaki fa zanyi". murmushi tayi tace'' son mu gaisa anan karkuyi letty'. Yasake cewa "mommy da asuba naga daddy yashiga d'akin ki kuma jiya ma da naje gaida daddy kamal yacemin daddy a part dinmu ya kwana me daddy yakeyi a d'akin ki?". tambayar ya daure mata kai dama shi take gujewa rasa mezata ce masa tayi ta sauk'e ajiyar zuciya tace'' kasan tunda muka dena kwana tare nake jin tsoron d'aki na kaga kaima Agrif ya dowo d'akin ka shine nima daddy ya dawo d'ak ina kuma ma ba kullum zaina kwana anan ba wataran part din su wataran nan". kallon ban gamsu ba yake mata yawani hade fuska amma baice komai ba yajuya zaibi bayan Agri Mommy tace'' my dear ko ba kason kwanan daddy din anan ne". juyawa yayi yana kallonta kai tsaye cikin maganan sa na isa tace " eh mommy ai shi namiji ne me yasa zai zo d'aki ki ai malamin islamiyar mu yace ba kyau namiji da mace suna kwana a dadi daya inba mijin gidan bane". wani irin faduwa gaban mommy yayi tana mamakin malaman yanzu yanda suke fayya cewa yara komai tun basu kai matakin hakan ba yanzu d'an shekara tara har ya isa sanin komai amma afili kuma tace'' kai my Son daddy ma ai mijin gidan nan neko". shima cikin mamaki ya kalleta yace" a a shi daddy mijin Mama ne kemuma Abba na ne mijin ki nide gaskiya Daddy ya dena shigowa d'akin ki". dafa kan sa mommy tayi tace'' oooo Nasir zaka ku makara idan kadawo sai muyi zancen kaji". cikin fushi yafice ko gaisuwar bai mata ba to haka mommy tayi ta shan tambaya a wajen Nasir cikin ikon Allah auren daddy da mommy bai cike wata 3 ba ciki ya bayyana ajikin ta alokacin Ummu ma tana daciki zaikai watani 4 tare sukayi goyon ciki har Allah ya sauk'i Ummu lafiya awannan karon macce ta haifa ayanzu yaran Ummu sun cike 4 Agrif Aiban Abbati sai wannan jaririyar me sunan Mama akasa wato kishiyar mommy Aisha anaki kiranta Humairah Hajja da kowa na gidan yanzu sai Humairah awajen takwaran ta Mama take wuni sai idan zata sha nono akawota wajen Ummu bayan wata 2 itama mommy Allah yasauk'e ta lafiya kyakkyawar yarinya mekama dasu daddy su Agrif bak'a bata biyo mommy da Nasir ba Nasir yana dawowa a makaranta zai wuce sama sai Dr Hafsa tace'' Nasara kogani kafi mutum Nasara me wuyar badan ci baka ga jaririya ba kayi k'anwa "Mami nagani". atunanin sa Humairah ce dan haka ya yamutsa fuska yace "nagan ta mezan mata".? Dr Hafsat tayi dariya tace'' shikenan zan tafi da ita gida zan bawa Ayman dama matar sace namasa kamu".? bai sake magana ba ya hakura sama sai Agrif ne yagane mommy ce ta haifu dan haka jefar da school bag din sa yayi yatafi da gudu ai yana arba da yarinyar yasa wani irin ihu yana cewa "woow mommy haifa mata ita kikayi mommy kiga tafi Humairah kyau sosai kyakkyawa ce mamin Ayman bani ita". ya k'arashe maganan yana zama akan kujeran yana washe baki Nasara da bai k'arasa hayewa ba yaji yakasa tafiya yajuyo yana kallon inda suke ahankali ya sauko yasa hannu yaja tawel din da aka nade yarinya sai da yamata kallon kamar na second 9 ya yamutsa fuska ya koma baya yana kallon mommy da take kurban tea itama shi take kallo yace mommy meyasa baki haifi fara kamar mu ba kika hafi wannan bak'ar ai wannan k'azama ce nide wllh bana son ta kuma kar a haura da ita saman mu". ya k'arashe maganan yana yarfa hannun sa daya taba tawel din alanman yana tsantsanin hannu sa Hajja ta meka masa zagi da hannu tace'' kai ungo naka". kallon raini ya mata yace " a a rik'e abin ki." cikin matsifa Hajja tace'' kai har ka isa kace kana k'amar bak'i uwar ka Halima bak'a uban ka Abdulsamad baki kaimu kaf dan ginmu ma bak'ak'e ne waye kaga fari kaima wayasani ko a hasbitin aka canjo ka da kanin b'akin halin ka baka gado mu ba idan an haura da ita saman ka kasheta". shima cikin matsifar da dama sun saba shida Hajja yanuna mommy da yatsa yace kinga uwata farace tas niban san wata Halima ba... mommy ta ajiye cup din hannu ta tace'' my Son jeka ka cire uniform din ka''. wani dogon tsaki Nasir yaja yafara hayewa Hajja tace'' Fanna kinga irinta ko ke kika b'ata yaronnan gashi yanzu y'ar da kika Haifa ma yace ba yaso kuma kinsan tunda ya furta baya so baya sonne nifa halin yaron nan tsoron yake bani bak'in halinsa fa k'aruwa yake" . Mommy tace Hajja Nasir yarone zai dena". Hajja tace''d'an shekara goman ne yaro"?. shiru mommy tayi Dr Hafsat tace'' gaskiya Dr Fanna ki duba al amarin yaron nan ki ajiye son da kike masa ki fara fashim tar dashi abu mekyau da barar kyau dai-dai da ba dai'dai ba ya kamata da rashinsa ba wata uwa wanda bata son d'anta saide hakan take dannewa da nusar dashi hanya...... Nasir da har yakusa hayewa yaji kalaman mamin Ayman sun gama bak'anta masa rai afusace ya juyo cikin rashin kunya yace "ke kije kinunawa Ayman dai-dai mana aishima jakin ajine kuma kullma sai yayi Letty kiji da kanki malama." ya k'are maganan tareda jan uban tsak'i ya haye cikin sauri Hajja tace'' kunji ko yaron nan wata rana dukan mu zayyi harke me daure masa gindin tunda gashi yafara da zagin aminiyar ki". mommy tace'' Hajja zagi kuma ai amagana Nasir ba kalman zagi martani kawai ya mayarwa Mamin Ayman'' Mommy ta kalli Dr Hafsa tace'' amma dan Allah Dr Hafsat kiyi hakuri haka Nasir yake bayason a shiga harkan sa kuma inda Nasir zai shekara da mutum wllh baya shiga har kansa sai yashiga nasa". cikin mamaki Dr hafsa take kallon mommy tarasa wacce iri yace ita itade tasan wannan ba tarbiyya bace mekyu amma afili tace '' to Allah ya shiryeshi Amin mommy tace'' tana mek'ewa tayi sama Hajja tana nunata da baki tace'' ta tafi lallashi Mommy kai tsaye d'aki Nasir ta wuce a tsaye a tsakiyar d'aki ya dafa kai ahankali ta k'arasa inda yake ta zaga tasa hannu tacire hannusa akan ta girgiza ai tace'' am sorry kan ka ko ciwo amma meyasa kake da daukar zafi da wuri ka din ga hakuri kuma zakabawa Mami ku hakuri". "me nayi mata zan bata hakuri ai ita ta zageni har tana cewa a dai'dai tani". "kayi mana cewa fa kayi bakason k'anwar ka saboda bak'ace kuma mummuna". "mommy nide ba k'anwata bace kuma wllh bazan taba sonta ba na tsaneta". cikin damuwa tace'' ''Meyasa katsaneta naga kai kake ta cewa kafison na Haifa maka y'amace kasa mata suna *NASRIM*". cikin fusata yace "Eh amma yanzu bana sonta Mommy kinsan fa duk yanda nake son abu idan wani ya rigani ina hakura meyasa Agrif zai rigani daukan ta har yana cewa tana da kyau ni yakamata na riga kowa ganin ta".? numfarawa tayi tace'' amma kaima kasan farin jini irin na jarirai nida na haifeta ma har yanzu ban dauketa agaban mutane zakace bakason k'anwar ka".? cikin k'osawa da maganan yace "Mommy ki dena cewa k'anwata niba k'anwata bace k'anwar Kamal ce tunda y'ar gidan daddy ce ni kannena sun rasu yaran Abba na ". wani irin nauyi maganan nasa ya mata lalle Nasir yazuce duk yanda take tunani gashi da azabeben kishi ta jima da sanin yana kishi da Daddy". Murmushi tayi afili tace " ok ni ina son ta kuma sunan maman ka Halima ce zamu kirata NASRIM kamar yanda kace da farko". "Wllh mommy ko da sunana Nasuru aka k'irata ba zan sota ba tunda aka rigani cewa tana da kyau". "Ok am sorry my Son kayi wanka kaci abinci ka kwanta kan zai dena ciwon". gyada mata kai kawai yayi har tajuya zata fita yace" mommy anjima zanje aski kuma zanje gidan su Ma'aruf abokina". "Ok amma kar kace zakaje kai daya Ya'u drive yakai ka yadawo dakai kuma ban yarda kace basa yabar ka acan ba". "Ok thanks my mommy." a parlour ta samu Dr Hafsa Hajja ta fita su Mama ma sun fita dr tace'' mommy Nasir zan tafi sai tomorrow insha Allah". mommy tace'' ok nagode sosai Allah yabar zumunci Dr kuma ina k'ara baki hakuri akan lefin Nasir ". murmushi Dr tayi tace''ba komai Dr Fanna kece ma za abawa hakuri dama yawanci marayu haka suke shiyasa rik'on su yake da Lada amma dan Allah ki dage ki kula da tarbiyar sa kisani amana ne ahannun ki". nisawa mommy tayi tace''hakane zan kula amma kisan me wllh bani kad'ai na batashi ba har da Hajja dan yanzu dani nafara masa magana yafusata shi haka fashewa da kuka zatayi tana cewa ai maraya ne ko tanemi cewa bana son sa wllh Hajja wata iriyace da ba agane ina ta dosa kuma Wllh ayanzu aduniya ba Wanda Hajja take so kamar Nasuru ko yaran nata bata so Kai ko shi marigayi bata masa sonda takeyiwa Nasir duk wannan fad'an da tayi na burgane wllh inda zakiyi awa daya agidan nan da zakiga yanda zata shigo tana basa hakuri kamar zata masa sujjada shiko bawani wanda ya rena kamar ita'.. Dr Hafsat tace''gaskiya naga alama bata mintuna 30 ba ta ambace shima keda ita bansan Wanda yafi wani son Nasir ba". Haka aka sha sunan Nasrim duk da bawani shagani akayi ba dan Hajja ta hana wai acewar ta rabon tane ya kashe mata d'a dama ance rabon y'amace kisa yake dan haka ko daukar ta batason yi kamar sauran jikokinta haka Nasir da gaskensa yake nunawa Nasrim k'iyayya musamman dayaji FURRUCIN Hajja na cewa ai adalili ta Abban sa yamutu ko ganin ta bayasan yi ko shiga yayi yaganta a hannu mommy to sai de yafita idan taga haka ita zata ajiye Nasrim ta fito wajen sa tun mommy tana daukan abin a k'uruciyar har abin yafara bata tsoron da akwai randa ta samesa..... *To masoya mu hadu a page 4 insha Allah nagode* *Taku BJ* [4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE* *NA* *BATUL ADAM JATTKO* ```Marubuciyar``` *DAMA TA* *AMFANIN SOYAYYA* ```NOW``` *FURUCINA NE* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* *Page 4* NASIR ta samu ya toshe mata hanci sai famar wutsilniya take a k'afa da hannu cikin sauri mommy ta k'arasa gurin ta ce "ya haka? Son kashe k'anwar taka za ka yi?". mik'ewa ya yi ba alaman tsoro ko firgici idonsa cikin nata ya ce ''Mommy so nake na kashe ta kowa ya huta tunda dalilinta Abbana ya rasu". Mommy ƙarasowa ta yi inda yake ta kama hannunsa ta zaunar da shi bakin gadon, ai ko da sauri ya mik'e yana yamusa fuska ya ce "Mommy ba na son ki sake zaunar da ni a kan bed din nan tunda kika kwatar da yarinyar a kai". Mommy ba ta ce komai ba ta zaunar da shi a kan jujeran 2setter ta kira Harira me aikinta ta ce tafita da Nasrim bayan ta dauketa sun fita, da kusan mintuna 3 tana kallon sa ta nisa ta ce ''Nasir ka yarda da ƙaddara ba Nasrim ba ce ta kashe Abba, Allahn da ya halicce shi shi ya dauk'e shi dan bawai dan zuwan Nasrim kaɗai ba ne ka ga kafin Nasrim akwai k'addaran aure da ya shiga tsakanina da daddynku ba dan Allah ya sauk'e Abbanku ba da babu yanda za a yi hakan ta faru Nasrim yarinya ce ita, ba ta ma san kanta ba yanzu dan Allah ko ba ka dauki Nasrim a masayin k'anwa ba kar ka cutar da ita sabo da". "Mommy meyasa ba kyason na cuceta".? tace''saboda ina sonta". "Mommy ni kindena sona". "haba my Son ya zan dena sonka wallahi ko da irin Nasrim goma na haifa ba su isa na musu rabin son da nake maka ba". "To mommy ba na son ki sake furta kina son ta ni kawai za ki ci gaba da so". Dariya ta yi ta kai masa kiss a kumatu ta san abin nasa har da kishi da kuma ƙuruciya "In sha Allah ba zan sake cewa ina son ta ba, kai zan ci gaba da cewa I love you my beautiful son." murmushi yayi wanda ya lotsa duk kumatunsa Ya ce" I love you too my sweet mom". "Thanks my dear Son kayi alk'awarin ba za ka cutar da Nasrim ba ko". Ya ce "E, amma ni ma ina da sharuɗɗa: Na farko ya zamana duk lokacin da zan shigo gaida ki kar na gan ta, kin san lokacin tashina tun kafin na zo ki kira masu aiki ki basu kar na shiko na ganta, Na biyu idan an san ina gidan a daina barin ta a main parlour ko hanyan da zan gan ta in dai ban ganta ba ba zan cuce ta ba, ba na son ganinta". Shiru mommy ta yi ganin da ta yi kamar kalamansa sun yi tsauri, amma dai farincikinsa shi ne kwanciyar hankalita dan ba ta son ganin sa cikin damuwa. Sai ta fara magana cikin sanyi murya tana cewa "In sha Allah zan kiyaye in dai hakan zai sanya ka farinciki dan alk'awarin da na daukarwa mahaifiyarka kenan za ka rayu cikin farinciki in sha Allah". "Mafaifiya ta kuma? Mommy ta ce'' Eh Nasir". Daga nan ta kwashe komai ta fada masa ba ita ta haife shi ba, ta cigaba da cewa "Ka k'addaran aure na da Abdulsamad shi yakashe ma haifiyar ka Halima saboda rabon yara uku da suka rasu kamar yanda k'addaran auren daddy ya kashe Abba duk da dama ina da niyar gaya maka ba ni na haife ka ba, ko dan ka yi wa mahaifiyarka Halima addu'a saboda ba ta da kowa sai kai ɗin nan, amma ba yanzu na yi niyar gaya maka ba sai ka kai ko da shekara 20 ne kafin ka sani yau de na gaya maka ko wacece Haliman da kullum nake cewa ka mata addua amma yanayin halinka ya sa na gaya maka yanzu daga yau ka yi wa Halima addua a matsayin mahaifiyarka ita da Abban ka". Cikin mamaki yake binta da kallon sai da ta gama ya ce "Mommy idan ke ba mommy na ba ce me ya sa muke kama sosai dake? ko shi ya sa Hajja kullum take cewa ban gado halin Halima da Abba ba, ita ce hotonta a main parlourn mu da na Hajja ko?" Ya jero mata duk waɗannan tambayoyin a jere "Nasir ni kaina ina mamakin kaminmu da kai sai dai ina tunanin tabbas ba za mu rasa dangantaka da Halima ba, shiyasa kullum addua ta Allah Ya ba wa Baban Halima Baba Nasuru lafiya shi zai warware mana komai dan nima ka ga ban san dangin ubana ba, ba zayyi yuwu a ce komai namu iri daya da kai ba musamman idan anyi duba da zanen barebari da yake fuskana irin sane a fuskan Baba Nasuru". "Mommy Allah yaji kan Mama kuma na ji ina son Baba Nasuru". "Ameen my Son nima na so Halima ita ma ta soni kuma ban san me yasa nake son Baba Nasuru ba duk da har yanzu ba wani magana yake sosai ba". Haka dai suka cigaba da hira kamar ta samu wani babba. Daddy da yake tsaye ta window tun fakon shigowar Nasir yana kallon duk abin da yafaru ya jij-jiga kai ya bar wajen mommy ta ce "Son zan shiga wanka ka san yau zan fara fita wajen aikitun haifuwar Nasrim". "Ok Mom zan je wajen Hajja kuma zan yi hadda anjima". "Allah ya timaki d'ana". Mommy ta gama shirinta tsaf daddy ya shigo kallon sa tayi tace''Ranka ya dade yau ba shari'a ne ban ga kana shiri ba"? "Ai week ɗin nan ma gabadaya ba ni da wani aiki amma an jima zan fita office". k'arasowa ta yi inda yake ta ce "Amma kamar kana cikin damuwa ko". " E, amma damuwar tawa ba ta da wani amfani a wajenki". Cikin mamaki ta ce '' Because of what"? kallon ta ya yi tare da juya fuskarsa wani gefen yana cewa "Saboda ba damuwar Nasir ba ne Dr! Na ga duk abin da kuka yi da shi yanzu har Nasir abin ya kai ya yi yinkurin kashe min yarinya baki dauki abun a bakin komai ba". Cikin k'osawa mommy ta ce "Amma alk'ali ai ka ga na yi masa magana ko". Cikin b'acin rai ya ce "wane magana kika masa idan ke idonki ya rufe da son Nasir ni nawa a bude yake, ko baki fashimci akwai barazana a FURRUCINsa ba? Cewa fa ya yi duk sanda zai ganki kar ya ganki da ita kuma kar ya ganta a babban falo ko hanyar da zai wuce kar a bi da ita wai hakan ne k'adai zai sa ya kasa cutar da ita, ya kafa miki sharud'a kika amsa kin karba kin yi daidai kenan? ko wannan ba damuwa ba ce a gabana fa aka furta 'yar'uwar y'ata tana cikin wani hali Dr har ga Allah ina son NASURUDDEEN din amma FURRUCINSA ya yi ts'auri a kan Nasrim, ba zan iya kwatanta miki yanda nake jin NASRIM a zuciyata ba, ko Kamal shi ne babba ba na jin sa kamar ita ba zan iya jurewa ba idan wani abu ya same ta". "To dan Allah alk'ali ka yi hakuri ai yaro ne zai dena". Shiru ya yi yana sauk'e a jiyar zuciya yace" Allah Ya sa, Ya shirya shi. A dawo lafiya". Cikin shagwaba ta ce "Haba Abban Nasrim yau ba rakiya"? Jinjina kai ya yi yana jan bargo yace I love you my wife sai kin dawo". taku ta fara a hankali da niyar ta k'arasa inda yake ta yi masa kissing Cikin wata irin murya ya ce "Allah kika kuskure kika k'araso nan bake ba tafiyar nan dan zan b'ata shiri". Cak ta tsaya tana masa shagwaba yinkurin tashi ya yi da gudu tayi hanyar fita si ya ce "Da ki tsaya mana ki ga illar tsokana". Sai da ta kai kofa ha hura masa kiss din a hannu ta yi saurin fita dan tasan in ya kamata bakyau. ******** Bayan kwana biyu haka mommy ta zaunar da Maimunatu da Harira tana ce da su "kuna ji na ko? Nasir ba ya son ganin k'ananan yara jarirai dan haka nake son ku dinga boye Nasrim idan kun gan shi kar ku yarda ya ganta a tak'aice dai ni ma ba na son ku bari ya gan ta, sannan ina neman alfarmarku wannan ya zama sirri tsakanina da ku ka da ku bari wasu su gane ko da Hajja ce". Maimunatu tace'' in sha Allah ba mai ji wannan maganar" Ita ma Harira haka ta faɗa wa mommy. Mommy ta ce "Yawwa na gode da yanda kuke kiyaye dukkan dokokina ina jin dadin zama da ku sannan ke Maimunatu iyayen Garba sunje garin ku an gama komai sai saka ranan aure kuma na ji dadin yanda suka ce ba sai kin je ba sun bar komai a hannuna su za su zo nan ayi shiyasa na sa a muku gini a nan kusa da part dina ta baya in sha Allah kafin lokacin za a gama ginin". Cikin kunya myaimunatu ta yi godiya haka maaikatan nan sukaci gaba da ɓoye Nasrim duk ko yaran da aka samu akasi Agrif ya nace ya dauketa ya ganta to duka da minsini de sai ta sha su a wajen Nasir, Agrif ko ya ce bai yarda ba dan batuwa da Agrif a kanta dan shi duk abin da Nasir yake masa ba ya damunsa amma muddin ya taba masa Nasrim to za suyi fada a ranan ko abinci ba za su ci tare ba, zai ce yayi jagolgolo ta k'azamar yarinya sosai Agrif yake son Nasrim

Chapter 5 of 40