Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
DADDY yace " kinga dama three brother sun fara aiki akwai sabbin motoci ba kalan da babu sai ki zaɓa masa wanda kikaga zai masa". wani irin tsalle tayi ta rungume dad din nata tana cigaba da murna "amma Dad kai zaka kirashi kagaya masa zamuje shorping "ok " ok daughter bari ayi breakfast sai mu zauna". "Ok daddy bari naje na sake showers na sake masa sabon makeup ". taƙarashe maganan ta ficewa da sauri kamar yanda ta fada kam tasha makeup ba ƙarya HANI ƙyakƙyawa ce ajin farko kuma yar gata tasamu iyayen nata zaune a parlour har sun gama breakfast Nasir zaune a kujera ya gama damƙe fuska Dad yayi gyaran murya yace " to ranka yadade Ahamed kaga ƴar shagwaban taka tafito kuwuce ko". Nasir wani irin ɗagowa yayi ya wurga musu kallon ku shiga tai tayin ku daga uban har ƴar sannan ya tsayar da idon sa ƙem akan UBAN yace "ni nace maka ina buƙatar fita". yana yin yanda yayi magan kadai idan kaji kasan ishe she ne Dad din Hanifa yace " A malam Ahame ai fitan nakane kai zata sayawa mota da kayan gayu ai wanda kakeso zaka zaɓa ahine shikiman fita da kai din". cikin isa yace " bana bukatar su" . cikin mamaki Alhaji yace ". ikon Allah kai ɗin waye a ƙasan nan ɗan waye kai wanda ni ALHAJI MUDANSIR GUGA zanyi magana kaja dani kasan ni kowaye". cikin mamaki Nasir ya maimaita MUDDANSIRI GUGA acikin ransa cikin mamaki ya daga yana kallon sa tabbas shine shine me *WANKI* da *GUGA* a gidan su kafin rasuwan Abban sa to ya akayi yayi wannan kuɗin duk da yasan tsofin ma ai 'katan gidan su duk masu kuɗi ne cikin ahekaru kaɗan duk wani ma aikaci a Three brother yakeyin kuɗi amma wannan ai nashi yayi over tun dadewa Mommy take cewa Muddansir Guga yana son ya kanshi amma Allah bayyi zai ganshin ba tasha kiran sa tace ga Guga a Dubai zaije su gaisa sai kuma wani uzzurin ya shigo masa Mommy tasha cewa yana yawan tambayar sa dama shine Guga mai company *roba* Alhaji ne ya katsar masa da tunanin da cewa "nace kai ɗin waye ne da kaƙe mayarda hannun ƙyauta baya ni kaina da kake gani ƴauta ne ɗalilin arzikina ni sunana Mudansir ni bafulatanin Gombe ne almajiran ta neya kawoni nan kano sai nasamu wata uwar ɗaki ma aikaciyar asbiti ina mata wanki da guga dr Fanna bata da kowa sai ƙawar ta dr Hafsa saboda yanda na iya wanki da guga har dr tasamu miji mai kuɗi miji na nunawa a duniya da tayi auren dani da tare gidan ta lokacin bazan guce shekara 14 ba naci gaba dayi mata wanki har uwar masu gidan HAJJA ta yarda da nagartan aikina daganan na samu cigaba sosai dan duk wanda Hajja take so to zai zana ɗan gatan Alhaji ABDULSAMAD bayan shakaru bakwai da tarewar mu gidan wata rana Alhaji zaiyi tafiya yamana wani irin ƙyau wanda shine tsilan wannan arzikin nawa amma babban abin baƙin cikin kuma a ranan da yamana wannan ƙyau tan aranan yarasu ɗan sa daya Mahammed Nasir yarasu yabar uwar ɗakina da ciki amma Allah bai sa abinda ta haifa sun rayu ba wannan hospital da ka kwanda *GUGA ClLNIC* dan Alhaji Abdulsamad nayi saddakatul jarin sannan uwar ɗaki na Hajiya fanna tamkar uwa take aguna kaga matata ma ita tazaɓa min kanwar ƙawar ta dr Hafsa shakaran mu asirin da aure Hanifa itace babba kuma sunan HAJIYA FANNA ne da ita sai ƙannen ta 5 duk maza ne suna US suna karatu a wajen ƙanina wanda yake kulamin da harkoki na nacan so temako ya kaini duk matakin da nake yanzu nima na temaki mutane dayawa amma meya sa kaida Hanifa tace tanaso zakaƙi karɓan tayin ta bayan zan iya mallaka maka rabin abinda nake dashi". Nasir ajiyar zuciya ya sauƙe ya dan gago ya kalli momyn Hanifa tabbar suna yanayi da MAMY HAFSA kuma sai yanzu ya sake ganeta ta zauna a gidan su kuma itama Hanifa sai yau ya tsaya ya kalleta sosai suke kama da Amiran dr hafsat lalle rashin daukan hoto da bayayi rahamane a wajen sa da yanzu ko da ƙarfin an baida shi Three brother asanyaye ya meƙe tsaye yace "Alhaji nagode da temakon da kayi min nima ina yuwa Uban gidan ka Alhaji Abdulsamad addua amma ni dama nazo na maka sallama ne zan wuce". cikin sauri Alhaji ya meƴe yace "ban gane sallama ba kai da kace bakada family?". "bani da family yana nufin ba inda nake rayuwa kenan". ya ƙarashe magana yana matsawa kusa da hanifa yace am so soory my Fatima". ya kama ɗaya hannu ta ya hada danashi idon sa cikin nata yasake cewa sorry sis". ahankali yasaki hannu yajuya zai fita da sauri tabi bayan sa tace " zaka *aure ni*? bai juyo ba ya girgiza mata hannu alaman no ya fita cikin takun isa wani irin ƙara Hanifa tasaka ta fadi awajen sumammiya da sauri dad da mom dinta sukayi kanta dad yaleƙa yace SAidu kada kabar wannan gaye ya fita wllh idan na rasa ƴata kai ma sai karasa ranka Sa'idu tsaremin shi Sa'idu yayi kan Nasir gadan kadan amma nasir yana watsa masa wani irin kallo ya tsaya cak yana ganin sa yafice Nasir sai da yafita a get din gidan ya tsaya yayi murmushi afili yace " duniya kenan ni Nasir wata kucaka zata gani a araha ta shige min lalle Fatima kinci darajan sunan Mommy hmmm wai yarinya harda taba min jikina me daraja ALLAH sarki Alhaji baka can canci namaka haka ba amma nayiwa kaina al’ƙawarin bazan sake rayuwa a inuwar Three brother ba da gumina zan rayu dukiyar gado masifa ne..... juyawa yayi yafara takawa cikin sauri dan jun an fara kiciniyar bude get *Three brother house* Daddy ya kalli Nasrim yace " daughter kina kaiwa dan uwan naki ziyara kuwa?". gaba daya yanayin Nasrim ya canza cikin damuwa ta girgiza masa kai gyara zama Daddy yayi yace Halima ko baki yafewa ɗan uwan naki bane yajima yana cewa yana son ganinki kije mana ya ganki akwai abinda yake son gaya miki". cikin kuka Nasrim tace "daddy bazan iya ba bazan iya zuwa naga Ya Kamal a prison ba lefin sa bai kai wanda za ayanke masa wannan hukuncin ba Mama ce mai lefi kuma an kasheta Dadd dama inason gaya maka ina shirin shigar da ƘARA akan a sassauta masa". girgiza kai Daddy yayi yace" impossible Nasrim hakan zai iya ragemin daraja a idon duniya bayan kowa yana yabon da sha'awar abin da nayi na yankewa ƴar cikina hukunci da kaina kuma anyankewa ɗana hukunci ina da ikon fitar dashi amma na bari saboda iya adalcin kena sannan anyakewa matata hukunci banja ba har aka kasheta wannan abin ya ɗaga darajata a idon duniya hakan yaja an bani wakilancin alƙalan ƙasan nan baki ɗaya yanzu nine hugabansu idan kika sake tada wannan zaki sa aga rashin girmana". "Daddy saboda mutane zaka bar ɗan ka kada kasa baki ni zan fitar da ya Kamal bazai shikara a gidan prison ba". taƙarashe maganan tana ficewa hajja da mommy "Hajja dan Allah kiyiwa Baba magana wai shi ya nace bazamu je maiduguri da lagos ba sai anga Nasir Hajja yanzu tsawon wata 5 ba nasir ba alaman sa gaskiya ni inason ganin uwata". murmushi Hajja tayi tana kallon momy tace "Fatima Zahra damo sarkin hakuri ki ƙara haƙuri Insha Allah Nasir zaizo na yarda da uzurin Babanki na cewa yafi son idan Nasir ya bayyana sai ya dauke ku yakaiwa danginsa yace halima ta rasu amma ga ɗanta gakuma ke Fatima kinga yabada uzurin lefi yayiwa ƴan uwan sa ya gudu amma idan suka ganku gaba daya zasu yafe masa suce rabon kune ya fitar dashi kin manta yace yana da mata da yara acan maidugurin dan haka ki ƙwantar da hankalinki kinga ke yar dangice ma". Mommy tace " shikenan Hajja". Hajja tace "yanzu Fanna abinda nake so dake ya kamata a tara family meeting a sanar wa Nasrim gaskiyar lamari kin ga yanzu taware tafara harka da jama'a kinsan abin duniya baya buya zataji a gefe da taji awani waje kwara taji awajen mu". Mommy tace "dan Allah Hajja abari idan shi Nasir din yazo sai sabar da ita amma har yanzu Nasrim bata gama gomawa normal ba". Nasrim akan gado ta zube tana kuka sosai taji wayan ta yana ta ƙara share hawayen ta tayi taga baƙon numbar ne amma a tunanin ta wata mata da cese dinta yake hannunta ce dan batayi saving no din nata ba cikin tsarƙewar murya na alaman ta gaji da kuka ta dauka tayi sallama daga daya bangare aka amsa sallaman matar tace "Halima 3AFULL ko ". "yes". Nasrim tace badan ta gane me maganan ba "ok Halima ni kuma Rafi'at Yakubu mrs barrister Fu'at Jiji dan Allah zan iya ganin ki a yanzu dan Allah ." cikin sakin murmushi kamar agaban ta tace ayya ba damuwa sister ina kikeson mu hadu zaki zo gidan mu ko ni kikeson nazo". ajiyar zuciya Rafi'at ta sauƙe tace " kinsan mu matan aure ba kasafe mukafiye samun daman fita ba zamu iya haduwa a gidana". murmushi Nasrim tayi bata dauki maganan ta dawata manufa ba dan ita bata da saurin farssara abu tace Ok zanzo ai nasan gida naje rannan akan wani cese da nake son sako barrister aciki sai Allah banyi samu haduba baƙanan amma insha Allah gani dan zuwa". fitowa tayi sanye da doguwar riga dankwalin rigan ne akata iya kafadun ta kawai yarufe kasan cewar rigan bubu ne maroon colour yazauna sosai a fatar ta key din motan tane da wayan ta sai jakan hannu sauri take zata shiga mota ta hango Izza da Humaira suna ɗaga mata gannu shiga motan tayi ta zauna tana jiran isowar su suma zuna zuwa izza ta shoga front seat Humaira ta zauna a back seat murmushi Nasrim tayi tace kun tuna baya kenan dan Allah mudawo da moment dinmu irin na da". Izza tace har kin tunomin da wayyo Allah ƙuruciyar mu daɗi muyi wanka tare muyi komai tare". wani irin dariya Haumaira tasaka tace " wanka tare wai ashe da wata idan ta zage wllh sai mutum yafita da gudu". Izza ma dariya tayi tace "wllh kuwa su kwaila an bada mamaki". daure fuska Nasrim tayi tace "i dade yanzu ba shegiyar data fini wani abu ai mahaƙurci mawataci da kuke cemin kwailan yanzu ai nayi shidan ku wllh". dariya Humaira ta sakeyi tace "mai rakacaniya kenan". itama Nasrim dariya tayi tace "har kin tunomin Zahra zanda Zahar ta fara fito da nono Izza ce ta fara gani ta gaya min na fasa ihu ina cewa mundena wanka da ita tunda tazama karuwa". dariya sukayi suna turo ƙuruciyar su har Nasrim tayi parking a cikin gidan barrister jijjji a babban parloun suka tadda matar gidan da bazata wuce sa'ar suba cikin mutumci ta Ƙarɓe su can ta nisa tace "kada na shagalar daku dalilin kirana fa shine HALIMA meye tsakanin ki da mijina jiya yake gayamin wasu magan ganu a kanki wanda banajin zan yarda dashi". shiru Nasrim tayi batace komai ba Izza tace " Halima da mijin ki wa yafi can canta kiyiwa wannan tambayar". cikin wani irin tsawa Rafi'at tace dakata malama bada ke nake ba da MAGE nake mai kwanciyar daukan rai ko nace macijiya wanda bata da ramin kanta tun farko Agrif ma ai saurayin ƙawar tane tayi ƙwanta ƙwanta da tagaji dashi saboda tana son auren kwarton ta wanda suka saba harka ta kashe Agrif din waye baisan irin ƙazamin rayuwar da ake agidan ba da auren ki kika hanawa mijin auren ki kanki kike bawa ƙwarto har kuka haifi yara 3 wanda ba ko tantama NASIR ne uban su bayan asirin yatonu ya gudu ya barki shine ni za lik........ HUMAIRA tayi wani irin tsalle ta cafo wuyan RAFI'AT *MU KASANCE A 25 DAN ALLAH NAGODE SOSAI* *BJ* *FURUCINA NE* ( _rikicin babban gida_ ) *NA* *BATUL ADAM JATTKO* *25* da sauri Nasrim tashiga tsakanin su tana jan Humaira daƙer tarabasu tace izza kaita mota Izza gaban Rafi,'at tazo tana murmushi tace " mrs Fu'ad kinyi kokari kuma acikin gidan ki keke mu munsan doko dan mu muke kafata ba afada da mutum acikin gidan sa duk abinda yameka kai katako amma idan a wani wajen ne baki isa ki daga ido ki kallemu bama ke idan a three brother ne wllh saide ki tsinci brain din ki a wajen kanki ai duk maccen da tayarda da kanta bata fada akan namiji" "kut ni Rafi'ta Yakubu ƴar sarki jikar sarki wata take gaya magana haka garin nawaye dan uban mutum kuɗin ku din banza me da kuɗin naku inba rigima da rikici ba waye bai san har kisa kukeyi akan kuɗin ba ". Nasrim jan Izza tayi tana dafa kafaɗan Rafi'at idon ta cin nata tace " my sis kiyi hakuri dan Nasir ya haifi ɗan Agrif duk daya ne kede kiji da kan ki kuma ki gargaɗi mijinki muddin yaci gaba da ruɗani da kalaman sa masu rikitarwa to ina gaf da shiga rayuwar ku kuma idan kika sake nashiga cikin rayuwar ku to sunan ki sorry". ta ƙaraahen maganan tareda jan hannun izza da humairah suka fice har auka ƙarasa ficewa a parlour suna jin zage zagen Rafi'at Nasrim tana cikin tuƙi ganin yanda duk moment din izza da humaira ya janza ahankali ta gangara gefen titi tayi parking ta juya ta kalli Humaira sannan ta sauƙe idon ta akan Izza tace meye haka sister dan Allah karku bari abinda Rafi'a tayi ya dameku dama yanda su khafulan sukayi kama da Nasir dole nawaje wanda baisan cikeken halaƙar muba ya zargi wani abu ko kunsan nima ada ina mugun mamakin yanda suka dauko komai nasa amma yanzu da aka gano momy da mahaifiyar Nasir ciki daya suka fito sai na dena mamaki kinga yarana mommy suka biyo dan de suma mazane shine ake ganin kamar tasu da nasir din kuma nima ai farine kawai ban dauko na mommy ba amma ai hancinmu da idon mu iri daya ne so meye abin damuwa zargine kuma Allah yasani". tacikin mirror Humairah da Izza suka hada ido suka sauƙe atare izza tace "badamuwa tayi mugun cin zarafin mune taƙiraki har gida". Nasrim tace "ba damuwa ta tada motan dan ta kauda nunanin su tace ". gobe thursday za ayi fulani's day na Rashida ku zaɓa mana ɗaya wanda zamuje a cikin Pattyn din tun bazamu iya zuwa duka ba" . da sauri Humaira tace ".bride bath". Izza tace " shegiya ƴar bidi'a to sister day zamuje ko Allah zaisa musamu ana walima". Nasrim ta gyaɗa kai tafarayin rawa tana cewa "sai bidi'a sai bidi'a". harsuka ƙarasa gida Nasrim tana cikin nishaɗi su Izza suna biyeta amma awani ɓangaren suba matuƙar tausaya mata ranan da gaskya zatayi halinta Nasir awani anguwa da akayi sallan isha'i yaci gaba da zama acikin masallacin kama da misalin 11 wani mutum yashigo yace " ah waye kuma a masallaci har iyanzu lokacin rufe masallaci yayi kuma sai 4 na asuba idan ALLAH yakai ranmu". Nasir ya ɗaga kai yana kallon mutumin da shi ba tsoho ba shiba yaro ba babba de haka ƙaton kwaɗo a hannu sa yace "Babba karufeni ni baƙone bani da wajen kwana". mutumin cikin nazartan yanayin Nasir can yace "ayya ai bazai yuwu ba ƙa idane rufe masallaci amma kai baƙo daga ina".? ahiru Nasir yayi yanayin saya canza mutumin yace "shikenan ko zaka iya bina akwai shagon da yarana samari suke kwana a jikin gidana dan daganin ka bakayi kama da wanda zaka cutar da wani ba zaka iya bina". ba musu Nasir ya maƙe yabi bayan mutumin har yakashi fanka da ƙwan suka fita yarufe, gidan nasa bani sa da masallacin suna ƙarasawa bakin shagon mutumin yace " Hamza Ali Ibrashim Umar... atare matasan samarin guda hudu suka fito cikin ladabi suka zube suna cewa gamu Baba "yawwa ga baƙo nan kumasa shinfida kunga yafiku ku girmamashi". daganan ya dafa ƙafadan Nasir yace "sai da safe ko". gyada kawai yayi yabi samarin cikin shagon da taciki babba ne harda bathroom aciki washe gari da safe aka kawowa nasir breakfast kokko da danwake da ruwa fure water 2 yaji dadin yanda yaran suke girmanashi bude kwanon samiran yayi yaga danwake duk da bai san ma meye bane cokali ya dauka yana juyawa dan yasa aransa zai koyawa kansa cin kowane irin abinci yana son ya manta da rayuwar da yayi abaya bayan ya gama juyawa ya yakai bacin sa yana rintse ido yafara tauna ai baisan sanda yayi saurin dawowa dashi ba atake yafara wani irin shaƙuwa yana shaƙuwa yana firfita bakin sa dayake ji kamar an hura masa wuta aciki fito da harshen sa yayi yana girgiza kai Umar yace " subbahanallashi Yaya ya haka yaji ne? yayi maganan ya ɓula masa ruwan da sauri ya karɓa ya kafa kai yafara sha duk ya kwankwaɗe amma ko second ruwan bayyi acikin saba yadawo dashi cikin gigicewa su Hamza suke tambayan sa bashida lafiya ne saida yadan samu nutsuwa ya kalli jikin sa duk yaɓaci da aman ruwa yace "dan Allah ko zan samu nayi wanka.." da sauri Ali yace " bari na ebo maka ruwa". ya ƙarashe mafanan yana lekawa banɗakin ya dauko bokatin yafita Nasir ko dayayi wankan kayan mai gidan aka bashi yasa dan na yaran bazai masa ba darana shinkafa da wake akayi iya magi aha saka masa yadan ci balefi bayan wata 2 Nasir kam sosai yasaba da mutanen gidan har cikin gida yake ahiga malam Ladan yayi mugun yarda dashi sosai, Nasir kam zai iya cewa yana rayuwa cikin farin ciki amma yana tausayi yanayin talaucin rayuwar da sukeyi sosai Malam ladan yana da mata biyu da yara 17 maza da mata malam ladan bashida wani sana'a sai na facin mashin a kofar gidan sa yaran sa wasu suna tayashi irin sana'ar sa wasu kuma suna zuwa kasuwa dan koyon wasu sana'o in, sosai nasir yake jin daɗin rayuwar gidan musamman yaran yanda suke girmamashi yaya yaya abu ɗaya ne Nasir yakasa sabawa dashi shan ruwa ko fure water ba ya iya sha yayi yayi ya koyawa kansa saboda yana ganin wahalan da malam yake sha wajen saya masa ruwan roba na roban ma ba kowanne yake iya sha ba Hamza yace "Umma wllh wannan Ya AHAMED ɗinnan tausayi sa kawai nakeji gashi shiru shiru". Umma da take tuƙin tuwo tace haka Umar ma yace amma sadiya tace tsoron sa takeji ko jiya da kuna kasuwa nace ta kai masa abincin sa wllh sai waje tafita tasamo yara suka kai masa". Sadiya da take gefi tace " Allah Umma yafiye kallon mutane ga shegen tambaya ranan fa wai yake tambaya na wanne makaranta nake zuwa ina da saurayi ko ina ruwansa ni wllh kaman ninsa ma tsoro yake bani ga shegen shishigi". ta karaahe maganan tana shigewa ɗakin su anan ta tarar Mamar ta Mamar ta kalleta tace "wai ke meyasa bakida kunya ne wai Ahamed ba yayanki bane". turo baki tayi tana cire shijabin islamiyar ta da sauri ni kaina jattko naja da baya wow yarinya tacika maccen da dole Nasir ya shige ma dan duk wani abinda Nasrim takeji dashi to yariyar tana dashi saide muce masha Allah dan tsaya tsara kyan Sadiya ɓata lokacine malam da Nasir suna zaune malam yana facin wani babur wani mutum yayi musu sallama malam yana ganin sa cikin rawan jiki yace "Alhaji da kanka sannu da zuwa mushiga daga zaure ko". ya karashe maganan yana meƙewa tsaye mutumin wanda malam yaƙira da Alhaji yawani haɗe Fuska yace "Ladan ba wannan ne yakawoni ba zaure kuma ai ko bakace na ahiga ba idan ina da ra ayi zan ahiga nida gidana Ladan ina maka uzuri ne saboda kanada ƙima a idon mutanen anguwa amma duk bakaga haka ba to nace maka nasa gidana akasuwa kuma dillalai sunce baza su shiga gidan matan aure ba nabaka nan da awa 2 ku kwashe duk abinda kukasan nakune kufita idan ƴan anguwan su matsu dakai saka wani yabaka nasa gidan nide gidana na sai dawane". atake moment din Ladan ya canza cikin roƙo yace "Ahaji kasan ina da iyali dan Allah ka ƙaramin lokaci koda zuwa satine dan Allah". "wllh bawani lokaci da zan iya badawa". Nasir da yake tsaye cikin ɓacin rai yace " haka ake tada mutum agida ba wani bada notice kuma haka ake saka gida akasuwa ba tare da anyiwa wanda yake ciki magaba ba ko yanada ikon tsaya, aƙa ida idan mutum ya tashi saida gida sai yayiwa maƙota magana ida da mai so mai s kuma maƙoci bawai najiki kaɗai ba a a sai ka irga gida 40 a dukan gefe hudu na jikin gidan sannan kafita a hakkin maƙoci ANNABI da yazauna yana karantawa sahabban sa hakkin maƙoci akan maƙocin sai da sahabbai sukaji kamar daga karshe Annabi zaice idan ka mutu maƙocin kane zai gajeka sabo kakkin maƙoci, balle wanda yake cikin gidan baka masa magana ba kasa gida akasuwa kana ga baka shiga hakkin saba". mutumin yace "ba hadisi nazo jiba gidana nazo na kwata awajen wanda yake ganin kamar gidan yasama nasa sama da shekara 30 tun auren fari kuma da kake maganan nayiwa makota magana akwai wanda zai iya sayan gidan nan ne cikin su kasan nawa nake son ayiwa gidan kuɗi ne". numfawa Nasir yayi yace "maganan hakki nake gaya maka ba batun zasu iya ko baza su iyaba kuma nawane gidan naka" ? Alhaji yace miliye 2 nakeso amin kudin sa lakasan". Nasir ya kalli zoben hannnu sa nadana wanda aka zana (NN) jiki girgiza kai yayi afili yace bashiba yaciro na hannnun sa na hadu yace "gashi ka saida ka dauki kuɗin ka kakawo wa Baba ragowar kuɗin". mutumin dariya ya kece dashi yace " nizaka renawa hankali zobe nanne zai biya kudin gidana". nasir yace "muje kasuwar da ake saida gol idan ansaya abaka " ko da sukaje mesayan gol gigicewa yayi da yaga farin gol irin wanda ake musu tallan su samo ko waya daya ne gram za atsaya miliyoyin kudi saida ya dauki hoton sa yatura a companyn three brother na Dubai sukace konawa ne yasaya su zasu bashi kudin ya kalli nasir yace na saya 3 million". kallon sa nasir yayi ido cikin ido yace " idan baka bukatan saya ka bamu muyi gaba kawai". da sauri mutumin yace "shikenan zan saya 5 million". Nasir kallon sayi yana girgiza kai wai zoben sa ake yiwa wannan tayin wulaƙancin zoɓen da yayi 50 million ake tayawa 5 tota yaya Nigeria zatayi albarka, amma kawai dan bayason jayayya yace "shikenan kawo". godiya mutumin yayi tayi

Chapter 27 of 40