Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaciro fari me yankekken hannun yasaka ya dauk'o wandon Marrom iya gwaiwa yasake yana brush din kansa ya sake kallon Agrif ta cikin mirrorn yace" kana lafiya kuwa".? Agrif cikin muryar sa da yake wani irin k'amewa wanda duk wanda yaji sai ya tausaya masa yace" Muhammad meyasa y'ata tayi kama da kai".? ajiye brush din yayi yana d'agowa inda Agrif yake yana jifan sa da murmushi ya dafa kafadan sa yace " wannan wacce iri tambaya ne meye abun damuwa dan y'a tayi kama da uban ta". "Nasir meyasa baza ka dauki makami ka k'ashe ni ba ka huta bana tunanin zanji dacin mutuwa fiyeda da abinda nake ji yanzu ni musulumi ne ubangijina bai yarjemin na k'ashe kaina bazan iya ba amma dan Allah Nasir ko sawa kayi akasheni banga amfanin rayuwata ba kab'ata min duniya ta yanda bazan taba jin dadi ba". murmushi Nasir yayi yace' tun daga yanzu ai nazaci zaka jure ko kazaci barazana ne ai kai shirya d'aukan wanda yafi haka ma tunda kasan ni me fad'a ne nacika bana taba fad'an abu bayyi ba ina amfanin da DAMA TA akan lokaci nafada maka k'addaran Nasrim ba me kyau bane ka gauraya da ita to ni ba da bakami san kashe ku ba da azaban bak'in ciki rayuwa zaku mutu ina son kajira ranan sunan wannan jaririn kaga abinda zai faru amma kafin wannan ga zabi idan kana son lafiya to baka makara ba zaka iya sakin Nasrim kafin satin sunan inba haka ba akwai gagarumin matsala wllh wllh wllh akwai babban rikicin a three brother?". shiru yayi yana sauraron Agrif kozai fadi wani abun amma Agrif yakasa magana can Nasir yayi murmushi yace'idan ba kada abin cewa ni zanje nayiwa y'ata hud'uba sunan ta Zainab wato Mama jummai k'anwar Hajja ta Dardum". Yana gama fadan haka yajuya yafita Agrif jiyayi ko harshen sa bazai iya d'agawa ba kamar yanda Agrif ya barsu ahaka ya samesu dan yau breakfast ma anan bangaren Maman Hajja tace ashiya musu cikin takunsa na Izza da nutsuwa yashigo "daddy Abu Mama Ummu kuntashi lafiya".? a tare su kace morning my Son daddy yace sannu zumunci Nasir ya kakejin jikin naka jiya an ibi jinin ka". "ba komai Dad ni lafiya ma yak'ara min inaga ma yanzu duk wata zanje a din ga iba wllh jina nake lafiya sosai". ya k'arashe maganan idon sa akan jaririn da take hannun Hajja numfasawa yayi yace' Mama amma y'ar ki fa ta iya haifuwa wannan baby girls din itace ontop a kaf three A full". ya k'arashe maganan yana mek'a hannun alaman a basa Hajja mek'a masa tayi tana tura bakin bai gaida taba amma bata isa ta furta ba bayan yamata K'iran sallah da salatin annabin ya mata hud'uba yana mek'ewa mommy ita yace sunan ta Zainab Maman Dardum a mamakin ce Hajja ta juyo tace'' da gaske zainabu Abu tawa mai takwayen suna nasamu cikin umma tace wai Abu cikin umma ta ina sonki Allah yarabani dake ke kenan guda banida wata y'ar uwa maccen Allahu akkar yau ga dan gidan Abdulsamad yace bai gaji da jin sunan kiba tashi tayi ta fara rawa tana cewa Zanabu abu gadon kudi Zainabu Abu gadon kudi". kowa dariya yafara har Nasrim da ranta yake amugun b'ace akan meye Nasir zai din kaga juya su Hajja ta zauna kusada Nasir sai washe baki take tace'' Nasuru ya akayi kayi wannan tunanin kai madallah dakai ai dama nasan kai din na musamman ne jinin Abdulsamad ne fa yake yawo ajikin ka". kowa haka yadinga fara'a ganin Hajja da Nasara cikin fara'a ahaka akayi breakfast ba a ma nemi Ina Agrif yake ma sai de Nasrim tayi mamaki rashin ganin sa ********************** IZZA da Baban ta "Baba baza ka gane bane wllh kowa yafi son yaran Nasrim da nazaci dan anga maza ne sai yanzu data haifi macce nagane ba komai bane nuna ban banci ne shi kansa Aiban fa yafi son yaran Nasrim akan namu komai yace 3 brother idan kaduba Media duk inda ake daura picture to hoton su zakaga ya d'aura yanzu haka ko password din wayan sa dana computer din sa sunan Khafulan ne ga Nasara bai taba ko kallon inda yara na sukeba amma yaran Nasrim tamkar shine uban su nagaji". cikin daure fuska Baban nata yace "Izza saurareni duk wata na sara yana tare da hakuri nace kiyi hakuri akwai wani guba da zai fashe acikin gidan nan wanda Ina sa ran mu zayyiwa dad'i kece da riba amma sai kinyi hakuri matakin na sara hakuri ne". "amma baba ka duba ida yanda za ayi dan Allah". "nace miki akwai abinda yake shirin faruwa wanda yafi guguwar tsafina ma k'arfi kede kiyi fadan Allah yasa yafaru mune da nasara tasu ma ya ishe su basai nayi wani abu akan su ba". "shikenan Baba bari na koma ciki dan na san ko Musanat zata fashe da kuka sai de suce ma ai'katan gidan su goyasu amma bade Ummu ko Mama ko mommy su d'auke ta ba". tayi maganan tana tashi murmushi Baban Izza yayi yana shafa gemunsa afili yace yacika taf rikicin babban gida zayyi fashewa da kowa sai ya hadiyi zuciya yamutu daga ni sai izza da yaran ta zamu rage". Nasrim tun tana sa ran ganin Agrif har dare shiru ga wanya sa bata shiga haka washe gari ma da dare yayi ta kasa jurewa sai da ta dai-dai ci kowa ya tafi part din Hajja ta saka dogon shijab ta fito ahankali take takawa har zuwa bangaren nasu shiru har tafara tunanin ko bayanan sai kuma ta tuno Zakar ya tabbatar mata da yana ciki sama ta haura bata koyi knocking ba ta murda handle din tashiga ganban ta ne yafadi asan da tagan sa a kugunnune cikin barko da sauri ta k'arasa tana cewa "Abban Fayyat kana lafiya kuwa". ta k'arashe maganan tana Jan blanket din hannu ta daura goshin sa zuwa wuyan sa zafi taji rau cikin gigicewa tace'' kai Agrif me yake damun ka kaji jikin ka kuwa".? a hankali ya sauk'e hannun ta ajikin sa yace Halima bana son haramtaccen hannun ki ya K'ara tab'a min jiki abu daya nake buk'ata awajen ki meyasa jaririn nan tayi kama da muhammad".? Nasrim tace"muhammad waye"? ku.............. *Rikicin babban gida* *jiya kunji ni shiru wani uzuri yahana nayi typing ina neman afuwan jira da b'atamuku lokacin da nayi Wanda suka kirani dan jin lafiya nagode da kulawar ku nima inayin ku over* *sannu ku da kogari karatu masoya Ina jin dadin comments naku ina kuma jin dad'i sosai shi yake k'aramin k'arfin gwaiwa muje zuwa rikicin babban gida zanzu za afara* *B JATTKO* [4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE* -rikicin babban gida- NA *BATUL ADAM JATTKO* *13* " waye MUHAMMAD? Haramtattce kuma hannun nawa ?. shiru Agrif yayi yana tunanin anya idan ya zargi Nasrim yamata adalci gaskiya zargi haramun ne kuma ayan da Nasrim ta tsani Nasir bawani abu da zai faru tsakani su wannan wani Shirin Nasir ne dan yasake dulmiya rayuwan su cikin matsala yanzu idan yabari suka samu matsala da Nasrim to Nasir yayi Nasara kenan ko kawai sai yafara wani irin karkarwa alaman zazzabin ne yake damun sa daganan yafara sururu " ammmm ke wacece dan Allah ki kiramin matata Halima ah ah ana kiranta nasssrirm wayyo kaina ne kwarkwata ne a kaina zata ciremin kwarkwata ki kiramin matata kar ki tabani da hannun ki Haramtacce........ kuka Nasrim ta fara Sosai tana jijjigashi "ya Agrif me yake damunka jikin ka kamar wuta nashiga ukku.." tayi maganan tana sakin sa tare da fita da sauri abakin get din part din taci garo da Zakar bodyguard din Agrif din "lafiya Madam".? cikin in nina tace'' Agrif Agrif " tana nuna masa cikin gidan atsorace Zakar yace Sir!.? Yayi saurin shiga cikin ita kuma da gudu tayi part din Hajja cikin kidima take musu bayani a kidime kowa yatashi akayi part din Agrif bai dena sururun ba har Saida mommy ta masa allurai har dana bacci Hajja tace'' ooo ni Lami ina jan ina murnan zamun Zainabu ashe Haruna Yana cikin wani hali haba nifa tunjiya ban ganshi ba Allah sarki me gida Allah ya baka lafiya". Mommy tace'' abarshi yadan huta Abbaty Kai zaka kwana dashi idan dawani matsala sai ka sanar dani". Hajja tace'' to Adamu ka kula da shi Sosai nima badan ban iya bacci sai a gadona na Abdulsamad ba da anan zan kwana yo idan na kwana nan ai sai na manta a shima nida duk juyi sai na masa addua Allah sarki Abdulsamad dan al'jannan Nasrim ba a son ranta ba ta tafi ko cikin dare takira Abbaty yafi so 3 Sai bayan sallan asuba Nasir yabi su daddy gaida Agrif bayan fitan su daddy Nasir yacewa Abbaty "bro kaje kadan samu bacci ina nan". Abbaty Yana fita Nasir ya rufo k'ofan har da murd'a key yazo ya zauma kan bedside yace "wllh A'A ina tausaya maka bansan yaushe kazama me taurin kai ba". tashi Agrif yayi zaune ya kamo hannun Nasir yace " ai nadena na barmaka komai ahannun ka kayi yanda ka keso na baka nan da ahikara dubu 1000 ko zaka gaji amma abu dayane bazan saki matata Halima ba yara kuma da kake tara mana wllh ba ragata kayi da komai ba sai ma k'aruwa dana ke samu ko yanzu na mutu yaran nan amatsayin nawa suke ni zanfi samun adduar su fiye da kowa ake zuwa gidan marayu ma ake daukan yara arena balle ni yaran Dan uwana makusan cina Wanda suka fito ajikin Nasrim yarinyar da bani da kamar ta wllh godiya ma yakama na maka musamman yaran da suke fitowa da kalan kyu na daukan hankali shiyasa kowa yake son su saboda albarkacin wannan kyan da suka gado". shiru Nasir yayi da alama yarasa abincewa wayan Agrif ne yayi ring hannu yamek'a yajawo akan bedside murmushi yayi ganin Nasrim ce yana d'agawa yafara mata waka " _TILAS GANIN MU TILAS BARIN MU KAUNAR KI TUN DA NAYYI NISAN SO BA BATUN NA FASA KO ZA'A CE MINI IN BADA RAI FANSA_". wani nannauye numfashi ta sauke cikin sanyi murya tace "Al'hamdulillah Abban Fayyat wllh na tsorata jiya ya jikin naka yanzu".? cikin tattausan murya yace" naki din sai kin rama min wak'ar da namiki". Murmushi tayi tafara _ME KAKE SO YAZA MA ALAMA DAN AKWAI SABO INKO YARDA KAKE BUK'ATA TO GASAN YA RABO DAN KAI GUDA NE DA BA KAMAR_ shi kenan ". "Eh ya 3brother ya baby".? tace "ga baby ai su brother suna wajen mommyn kasan wai wancen bayahuden yace agun ta zasu zau nima har yazu banga Fayyat ba tunda aka masa k'arin jini". yace' kar ki damu ai Mama tana da sauran yaran rik'o awajen ta mommyn dama ya dace abawa jikin Fayyat kuma da sauk'i jiya ai ni na dauk'o su bayan munzo ne zazzabin yazu ba min". "to kai ya naka jinkin.? "Al'hamdulillah ba abinda nakeji yanzu sai son ganin ki". hakade suka k'araci firansu Nasir yana kwance agefen sa kamar baya ji har ya kashe wayan ya maida kan bedside yayi rigin gine yana kallon sama yafara wak'an _zama na aure yana da dad'i yana da dad'i ma'arata ashe soyayya da dad'i_ sai kuma ya mek'e tsaye yana taku ahankali zai shiga bathroom har ya murd'a handle ya juyo yace " na fad'a na k'ara wanda yaso ka kaso shi wanda ya k'ika ka kleshi hassada babban ciwo a zuciyar me k'ullaahi kuma duk mai halin muciji bakin sa bayi kyan hali ba wani bai yadda JALLA keyi ba Bai yadda da k'addara ba to naga tuni yayi gaba". ya k'arashe maganan yana shegewa tare da rufo k'ofan Nasir kwantar da kansa yayi yana karanto inna'lillahi dan haka kawai yaji gaban sa yana mugun faduwan da bai san dalili ba wayan sane yayi Rig a sanyayi ya jayo acikin a'ljushun a kasalance yace "Shateema ya akayi". cikin kuka shatima yace "Yallabai Aiban Aiban ya mu tu..... azabure Nasir ya tashi "me what kace me". "Sir saide muyi hakuri wllh duk wani kwaje kwaje anyi har yanzu bamu gano meye mussababin mutuwar tasa ba ni ya ai'kani airport ina masa cuku cukun tafiya kawai sai Akkram ya kirani yana kuka wai yallabai Aiban ya mutu wllh klau muka rabu dashi.... "k'arya kake shatima Aiban dinmu ba yanzu zai mutum ba... Agrif jin sunbatun Nasir yasa shi fitowa da sauri Nasir sakin wayan yayi ya zube a bak'in gagon tare da mek'e kafafuwa Yana cewa "! Allahuma gafurni'walhamni". Agrif yace" Nasir da gaske ne inna'lillahi'wa'ain'na'ilaishirajju Ummu Ummu Ummu ya Ummu zatayi yau me kunnuwa ki zasu ji...... Humairah ce tashigo da gudu ya Agrif Dan Allah kazo dan Allah kazo ka hana ya Kamal wai kuka yake ance masa ya Aiban ya rasu Dan Allah ai bazai rasu yanzu ba ko? Dan Allah kazo ka hanashi kar Ummu taji". ta k'arashe maganan tana fad'awa jikin Agrif din cikin k'an'k'anin lokacin mutuwar Aiban yagama ras'a iyalan three brother kowa kaga abin tausayi ba me lallashin wani Allah sarki Izza masoyi ya tafi sai cikin dare aka samu daman isowa da gawan Aiban dan haka tsutura sai washe garin Nasir komai nashi ya tsaya cak yazama kalan tausayi dan Aiban yana da babban mushin manci a cigaban duk company sa shi Aiban mutum mai Amana da aiki da zuciya daya duk yafisu horuwa a aiki aran da akayi sadaka bakwai aranan Nasir yasamu Agrif har cikin d'akin sa ahankali yake takawa hannun sa zube cikin aljuhon wadon sa fuskan sa tattare da damuwa ya k'araso kujera yaja ya zauna suna facing juna da Agrif da ya zuba uban tagumi Yana tunanin dan uwan sa Aiban me damuwa da damuwar kowa Sarai yasan Izza ba zabin sa bane amma yana cewa ya aure ta dan yasamu shi ya auri Nasrim ya karbi abin da hannu bibbiyu goge guntun hawayen da yazubo masa yayi ya dago yana kallon Nasir da yazuba masa Ido Nasir numfashi ya sauke yace am sorry my brother munyi rashi muyi rashi ashe dama haka mutum yake lalle lokacin da Abban yarasu bamuda wayo bamu San meye rashi ba sai akan dan uwan mu yanzu shikenan yaran sa Muwadda da umdatu da Musanat duk sun zama marayu Allah kamamu ikon rik'e su da amana insha Allah inde Ina raye yaran Aiban bazasuyi maraici ba Aiban ya bautu a gidan nan". ya k'arashe maganan yana dauke guntun hawayen da yazubo masa Agrif yace" mutane masu yawa ne suka mutu a wannan yammacin mu ma da Allah ya jin k'ir ta mana Allah yasa muyi abubun da zai zama fujjan da zai sa daman mu zai rinjayi hagun mu duk Wanda akace daman sa tarinjayi hagun sa to shine mafi girman dacewa Allah ka gafurta mana". gyad'a kai Nasir yayi yace "Agrif mutuwan nan yagama sanyaya min jiki Agrif yanzu Agrif yazamuyi dasu Fayyat da k'addaran su yazo da haka Agrif na tsani abin dana aikata tun randa naji labarin cikin Nasrim na tsani ZINA yanzu idan da NI NE na mutu mezan gayawa ubangijina dan Allah Agrif kayarda musanar da iyayen mu 3 brother yarana ne nasan duniya zata zageni zagin da za'a min shi zai rage min wani zububin sannan ko bakomai yaran idan sukasan nine uban su zasu yafenin tunkafin mubud'i Ido mugan mu agaban ubangiji". Agrif yace" hakan bazai yuwu ba saboda kare mutuci gidan mu da rayuwan Nasrim idan Nasrim taji wannan abun ni kaina sai ta tsane ne sannan idan mukace su Khafulan mazane zasu iya jurewa rayuwa duk ta inda yazo musu ita Zainab macce ce ito abin zaifi damu kuma zai shafi rayuwar ta sosai". Ido Nasir ya zaro cikin sanyi murya yace" wai kana nufin ka yarda Zainab ma y'ata ce wllh ni rabona da nasa Nasrim a idona tun washe garin haifuwar 3bro Zainab yar kace halaliyar ka abin da yasa da ka tambayeni na amsa maga da eh wllh saboda ina son kaje kayi ta kuntatawa Nasrim ne amma wllh Zainab ba y'ata bace na gayama natsani Zina tun ran da na san Ina da d'an shege". Murmushi Agrif yayi yace' kadena kiransu y'ay'an shegu sud'in y'ay'an k'addaran ne Allah yariga ya k'addara rabon ka ne a farkon nawa da Allah bai k'addaran ba baza ka samu daman hakan ba kuma Al'hamdulillah Allah ya rufa asiri". "Agrif kana nufin ka yafemin duk abinda namaka ". shiru Agrif yayi can yace "na yafe dan nima ina son Allah ya yafemin amma sai ka dage wajen neman yafiyar ubangiji "Agrif Ina neman yafiyar ubangiji amma bazan iya hakura da yara na ba kome zai faru nide na maka alk'awarin na rabu da matar ka amma yara dole koma me zai faru za a ban su". Agrif yace" hakan ma bazai faru ba ai kai baka gudun abin kunya ne". mek'ewa Nasir yayi tsaye cikin b'acin rai yace" Haruna bana gudun duk wani abinda mutum zaice ai nafi son ma a zageni". Agrif yace "to ni Ina gudun abin kunya dan haka yara anan duniya de yarana ne alashira su tashi da sunan ka". "Agrif baka isaba wllh ka kwace min dama biyu lokaci daya mata da yara". Dariya Agrif yayi yace "anzu wajen dama ai najima da sanin son Nasrim ka ke wawanci ya hana da mallakan ta a lokacin da na baka dama kak'i AMFANIN dashi da ka aure". Kallon sama da k'asa Nasir ya masa yace " Haruna inda Ina ra ayin hakan tun farko baka same taba amma kasani a kwai gagarunin rikici akan yaran na ka ba yanzu ba". shima Agrif cikin b'acin rai yace"saide duk rikicin da za ayi ayi ni ma ina son yaran bazan bada ba". Nasir yace "Ok shikenan". tare da juyawa yafice Agrif zubewa k'asa yana furta Al'hamdullah Allah ka fitar ni a duhun da nake son fita Zainab y'ata ce ******************* " Izza cikin kuka tace "Baba dama abinda kace kana hangowa mune zamu fad'a ciki Baba bokan cinka bayyi min amfanin komai ba gashi nice na tashi amatsayin bazawara yanzu shikenan idan nagama tagaba maza zasu dinga fito min ace nayi aure nabar gidan 3 brother". "Ke dakata IZZA kina abu kamar ba jini na ba tabbas banyi aikin bokanci akan kowa agidan nan ba saboda na hanko abinda yafi karfin tsafina amma awai rigima Sosai kozuwa gaba ne dan daren jiya ma sai da nayi duba kin tuna tun gafin kuyi aure da Aiban nace miki Ina mamakin gani akwai aure tsakanin ki da Aiban sannan akai a tsakan ki da Agrif amma na Aiban yafi al'kairi to jiya ma duban da nayi tabbas akwai maganan aure tsakanin ki da Agrif amma gaban abin kuma rikici ne amma bansan dalilin rikin ba zanci gaba da dubawa na tabbatar bai shafemu ba mutanen gidan ne fa masu shegen sadaka da kyauta duk wani masifa yana zuwa musu da sauki". dariya Izza tayi tace'' Baba kace akwai maganan aure tsakanin na da Agrif amma idan hakan ta faru zanfi kowa jin dad'i wallashi Agrif yafi Aiban iya soyayya kaga yanda yake yiwa Nasrim ne wllh dama Nasrim haushi take bani iko da gadaranta yayi yawa komai fa itace kan gaba agidan nan daga Mama har Ummu komai saide suce Nasrim atambayi Nasrim ni Baba inaso kasa tsanan Nasrim azuciyar kowa agidan nan fiye da yanda Nasara ya tsaneta". dariya Baban yayi yace "kai Izza lalle ke jina nace yanzu Nasrim din da itace silan zuwan mu gidan ta kanta zaki fara". "Eh baba bari nakoma kar wannan kini bebbiyar shohuwar can ta fara nemana dan tana takuramin wai macce me tagaba bata yawa nagade takaba kwana 40 ne sauran watannin idda ne a Ina akace me idda bazatayi yawo ba tana abu kamar jashila". ta k'arashe maganan tana mek'awa tayi gaba akofar shiga part din Hajja suka hadu da Nasrim tana Shirin fitowa tana ganin Izza tace ''yauwa dama ke nafita nema mutumiyar tun dazu take fadan ina ki kaje". murmushi Izza tayi tace'' wllh naje wajen Baba ne kinsan jiya yadan yi zazzabi". "Ok ankai shi asbiti kuwa". Izza tace "Ina bai je ba". Nasrim wayan ta da zaro tayi K'iran Bala sarkin gida yana dauka yace " ran madam ya dade". "Sarkin gidan dan Allah akira dr yaduba jikin baba Mustapha kuma dama Ina son dan Allah a dauke shi a cikin ma'aikatan gidan tunda shima yana cikin ahalin gidan nan a gyara Koda bedroom da parlou ne a part din Baba Nasuru amma yagirmi zaman cikin ma'aikata". "Ok ranki yadade baki da damuwa". tana kashe wayan Izza ta fad'a jikin ta tasa kuka tace'' Nasrim kin gama mana komai a duniya bamuda bakin gode miki". ******************* *Agurguje* *bayan shekara biyar* Nasrim tasake haifuwa d'an ta me kaman Agrif an mai da sunan Aiban shekaran sa 3 a yanzu a kan ALLAH wllh a wannan karan sai kafito kanuna Kai mafa kana da iko akan yaran ka haba ya komai sai yanda wani yace akan yaran mu makarantan k'asan nan duk bai isa ba sai ya d'auke min yaran da ba sufi sheka bakwai ba a duniya yakai su wani k'asan dama yanzu ma kana ganin yanda muke fama da Khafulan duk kokarin tarbiyar mu yaro kamar ba mayi baya jin magana bawan da ya isa ya hanashi ga daurin kai da iko da isa baya tsoron kowa ace afita dashi k'asashe turawa ya sake lalacewa wllh idan kaga an fitamin da yara to wllh mutuwa nayi ko zasu fita abari sai sun mallaki hankalin kansu kum...... "Ummy Papan mu ne fa yafada ke meye naki da zaki hana wllh nide ba Wanda ya isa yahana ni zuwa London makarantan mekyu ne ai Papa ya furon videon makarantan ke dama bakya sona muta.... marin da yaron ya sha awajen Nasrim shi ya dakatar dashi maganan defe k'unci yayi yana kallon ta ido cikin ido yace "kika mareni wllh sai na fadawa papa kuma agaban Abban kika dakeni bai ce komai ba". ya k'arashe maganan tare da taka steps da sauri ya haye da alaman de waya zaije yayi". ba afi mintuna 3 wayan agrf yayi ring Nasir ne dauka yayi yana murmushi yace "a a papa ankai k'aran ummy kenan". "dakata Agrif ba wannan ne damuwar ba ina ga lokacin da nabaka kafito ka gayawa matar matsayi na awajen yarana yayi wllh ba barazana nake ba Kai kasani". dariya Agrif yayi yace"kayi yanda kaga yadace". ya kashe wayan yana kallon Fayyat da yake masa magana Fayyat yace " Abban wai kaje inji Hajja kai da ummy". Hajja tace'' to dalilin ta raku anan shine Ina son hada aure tsakanin Izza da Haruna Wanda ina fatan yazama alkairi ". Abu yace" Hajja aure kuma ".? "Eh wllh kuma duk Wanda yayi yunk'urin hana auren nan to mut zai mutu ayi bashi saboda ni naga ishara akan auren Abdulmajid da Fanna rabo ya kashe Abdulsamad yanzu inda nayi kishin d'ana na hana ayi auren da rabon Nasrim mut zai kashe ni ashi bani". shiru daddy yayi amma gaban sa yana faduwan dan shima yasan kishin y'ar sa Abu yace " gaskiya Hajja wannan bame yu" "Kai gafara can rufemin baki meyasa sanda Abdulmajid zai aure Fanna baka ce bazai yuwu ba saboda ita Aisha ba y'ar gida bace ba sai yanzu da abin yazo takan y'ar ku wato bakaso ayiwa Nasrim kishiya ko t....... tashi Nasrim tayi tsaye tanawani girgiza kai tace'' wllh awannan karan ikon ki da isar ki bai samu gurin zama ba kuma gigin tsufanki bai gaya miki gaskiya ba wll...... marin da daddy ya wanke ta dashine ya k'atsar da ita wani irin ihun murna Khafulan ya saka yace "yeeeeee daddy yarama min marin da tamin bari naje na gayawa Papa........... *Mu hadu a 14 Insha Allah* *ina sake baku hakurin rashin jina a akan lokaci wllh Ina da uzuri sosai ne* *08062383027* [4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE* ( _rikicin babban gida_ ) NA *BATUL ADAM JATTKO* *14* Agrif ne ya mek'e tsaye yace "daddy maza ne suka k'are a duniya zan auri suruka ta matar k'ani na dade ace nine na rasu sai Aiban ya auri matata amma ni babba ai da

Chapter 16 of 40