Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kula dasu wanda lokaci daya ta canja mata bawani abu na more rayuwa Wanda bata bawa Nasrim tasa an kai ta special d'aki ita daya mekyau komai na more rayuwa akwai daga kan firiji tv lafiyeyyen gado amma da alama musamman dan ita aka gina d'akin san nan yanzu tazo mata dawani batu tace'' ma'am serious dan Allah waye yake gaya miki sirrin gidan mu taya ki kasan yaune birthday din Agrif nasan de dama kinsa mutuwar sa wata hudu ne cif kuma waye ya dauk'o miki waya ta?". Murmushi bayerabiyar matar tayi tace'' Madam Halima ai sirrin gidan ku bawani boyayye bane kawai inason na baki wayan ki zaki hau duk wani kafafen social Media zaki daura pic din Haruna ki masa happy birthday kinga mutane zasu tuna dashi su masa addua kuma amma daurawa kawai zakiyi cikin 10 minutes ki bani wayan naje na boye". karban wayan tayi tabbas natane wayan amma a Ina Timona n ta samu wayan da sauri tashiga cikin wayan pic din Haruna ta fara cin karo dashi sosai take kuka kasa cigaba da duba wayan tayi Maam tace'' ok ni zan daura miki wak'ar da pic din nasa kawo". tayi maganan tana karban wayan ahannun Nasrim Nasrim zama tayi tana cigaba da kuka tace''dan Allah ma'am kifita da wayan nan ni bazan iya cigaba da rayuwa irin wannan ba kuma dan Allah basai kin daura hoton mijina a media ba hakan zai janyo mutane suyi min wani fassaran na daban kuma a gidan yari nake fa". Murmushi matar tayi tana dashi da wayan tace'' duk abinda zasu fada mutanen duniya ai ni shi na bid'a akan aikina nake Nasrim nasan me make inason hankalin mutane yasake dawowa kanki yanzu an fara manta abinda ki kayi kinga hakan zai janyo mutane suyi cece kuce akai". ta k'arashe maganan tana ficewa *Three brother* Humairah ce ta fara gani dama ita yar media ce na gani gasheni Wani uban asher ta maka tace Nasrim kina gidan prison kina daura wak'a mutuwar dan uwana ko shekara banyi ba waka ma har biyu na farko cikin sanyin sauci na kayaran murya mawak'iya take rera wakan me tsuma jiki _Allahu sarki ka kafurtawa mijina wayyo Allah na nayi kukan rashin ka abokin rayuwa ta wayo Allah na wai ni nakashe miji na ya zanyi na kashe mijina ni Sadiya anyi min k'azafi arayuwa ta bazan yafe_ sai daya wanda hotunan tane da kayan prison aka tana kuka wan ita mata masan sanda akayi ba _idan na tuna da mosoyi sai inji kwallah nata kwarara idan na nuna da mosoyi sai inji tamkar infasa k'ara nayi kewa nayi k'ewar Mai mini fira_ jiki asanyaye Humairah ta tafi part din Ummu samun Ummu tayi tasa waya agaba tana ta rusa kuka itama Humairah rungume Ummu tayi ta fara Kuka Ummu tace'' Humairah bazan iya ba bazan iya ba ankaini bango ya isa daga yanzu zan nuna nima uwace kuma Haruna yana da gata kamar kowane da agun uwa da baifi da ba mutuwar Agrif ko shekara bayyi ba har Nasrim da take gidan kaso ta ware tana daura hotunan su da waka ba shakka wata ranan sakin ta za ayi ta zo ta zauna to ko yanzu meye yayi saura tana gidan prison amma tana da duk wani Freedoms na rayuwa da ganin Nasrim acikin walwalan ta take tunda har tasamu danan daura hotuna". Humairah tace "Ummu kiyi hakuri ai ya Nasir yana bayan mu shiyayi duk wani ciku cikun daukaka k'ara kuma wannan abinda tayi ta sake tabo kowa ma duk wani wanda baya koyon bayan ta to zai fito yayi magana muna tare da ya Nasir Kamal ne yake tare dasu ni wllh sai na bar masa gidan sama akan fansan dan uwana kuma ni har shi Kamal din zan shigar k'ara duk wani bayanan da yan sanda suka nema duk yasani kin fada yayi dan kar a kashe masa k'anwar sa tes din da ya Agrif ya turamasa na yazo yaceceshi Nasrim zata kashesa ai gogewa yayi sai a wayan ya Agrif din aka gani". "Humairah Abu kune yake cewa nayi hakuri shima Abbaty bawani abinda yakeyi Yana bayan Dr Fanna gaskiya yanzu bazan iya ba Nasrim ta cutar dani ta kashe min d'an da yafi yimin biyayya me farin jini ta kashe yaran sa amma anbarta nata rayuwa kamar kowa". Humairah tace'' Ummu dama hukuncin da aka yankewa Nasrim bayyi dai dai da lefinta ba hukuncin rataya yakamata ayanke mata kawai shima daddy kanin y'ar sa ce bayyi adalci ba wllh wllh sai an kashe Nasrim idan ta haifu". Nasir ya shiryawa Mommy zuwa umara yayi Wanda zatayi wata ukku acan kuma idan tazo agida zata sauk'a ranan da mommyn tazo aranan Nasrim ta cika sati da haifuwar dan ta namiji me kama da Agrif sak amma shi farine Abu yazo duba yaron an masa hud'uba da Haruna a ranan sunan aranan Madam Timona ta shirya wani Dan party akayi sa'a kuma aranan ne birthday din Nasrim ita Nasrim duk wannan bai da meta ba bata ma tuno yau ne birthday din taba tana tsaka da kuka su Maryama suka zowai sai tafito waje haka firsunoni yan uwanda suka jata ta fito abin mamaki Mp takani suna ta raye raye girgiza kai tayi ta dafe kai zata koma wata ta jata tsakiyar filin alallai wai sai tayi rawa murmushin da yafi kuka ciwo tayi tad'an ged'a kai a laman tayi rawa murmushi tayi tafice acikin filin d'akin ta koma direct tana rusa uban ihu kuka ko zataji sanyi suko sai rawan su suke suna na nata Haruna happy birthday Halima happy birthday tana jin iface ifacen su da raye raye da suke ashe duk wannan party da Timona ta shirya dan ta sake daurawa a media ne murnan haifuwa dakuma birthday party Nasrim takeyi a cikin gidan prison abu yasake jakulewa masu zagin Nasrim suka Kara azama tsine mata Ko Ina kale k'a a media bayanan Nasrim zakaji k'arya da gaskiya aranan Mommy ta dawo Nasir bai koma ba komai na three brother ya tsaya cak hatta aiki Mommy jikin a hanyaye ta sake kallon Nasir tace'' to wai ya akayi ta samu wayan ta kuma meya hada gidan prison da kayan kid'a meyasa Nasrim batayi tunanin abinda zai biyo baya ba take haka ko mutuwar Allah mijin ta yayi ai bazatayi haka ba mutuwar sa ko shekara bayyi ba Nasrim ta janyo mana hau da abin fad'a duniya da a gidan nan ." Nasir yace'' Mommy wannan shi ya tabbatar da Nasrim me lefice kamar yanda kowa yake fada dan haka karma kiji wani abu idan an yakke mata kukuncin kisa". kuka mommy ta fashe dashi Nasir fe cewa yayi mommy taci gaba da rera kukan ta Kamal ne yashigo yana yadin ga zuga Mommy akan Nasir baya kaunan Nasrim tare da hujjoji masu k'arfi numfasawa tayi tace'' nasani Kamal baya sonta nun tana yarinya amma meyasa har yanzu bazai can zaba". "Mommy saboda yayi alk'awarin bazai taba barin Nasrim taji dadi a duniya ba ko kinsan Nasir ya kulle Dr Hafsa saboda tana zuwa visiting wajen Nasrim watan Dr Hafsa hudu a kule kamar yanda ke kike a kulle bakiga kina can ba mezuwa ba haka Nasrim ma da nake zuwa wllh yahana zuwan kuma idan lawyer bai samu daman ganin Nasrim ba lalle muyi Na sara ba zamu iya samun babban matsala Mommy ki ajiye son Nasir a gefe ki k'waci yaruwar y'arki wllh Nasir baya son Nasrim kema kudin ki yake so daga zaran ya samu zai gujeki duk take taken sa wllh dukiyar yake yiwa k...... Mommy mek'ewa tsaye tayi cikin sauri tace'' Kamal koma baya me kake cewa Nasir yasa an kulle Dr Hafsa saboda mu shiyasa yaki yakawo min wayata tunjiya da nazo nake bin bayan sa ya bani waya ta na kirata yaki kuma ya hanani fita ashe shi Sherri da ya kulla kenan me Dr Hafsa ta masa".? Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Kamal ya d'aura da cewa "Mommy abinda nake son kigane kenan duk akan kudi yake yi". "kudi fa kace Kamal iya na kudin yake komai yana gunsa harrta company shikafa yanzu Yana wajen Nasir". Murmushi cin nasara yayi a fakaice yasake cewa mommy wllh kinyi kuskure mommyn akwai wani abu da na nake son na bayyana amma sai anje gaban Hajja an Kira family meeting anan zaki gane Nasir k'in gaskiya yake miki keda y'arki". "Kamal ka kayamin tun anan meye ne dan Allah ". "Mommy zai iya daga miki hankali sai mun hadu a main parlour Sai da safe Kamal yasa aka tara kowa Nasara ne Yanuna bazai iya zuwa ba mommy da kanta tazo ta sameshi tace taron nawane sai katashi kazo". tana gama fadan haka tafice cikin mamaki yake bin bayan ta da kallo to meyasa mu Mommy a haka ya tashi ya bita daga shi sai riyan bacci yana tsaki ya yi sallama daddy ne ya amsa yasamu gu a twositer ya zauna Kamal tashi yayi tsaye yayi addua bude taro ya fara bayani kamar haka Daddy kai da Abu nasan abin da zan bayyana ayanzu zai muku ciwo tunda ya shafe ku shine ma dalilin da yasa nayi shekaru 7 Ina boye abin saide cigaba da boyeshin zai iya zama matsala zuwa gaba musamman yanzu da ake neman mafi akan wannan abubuwan da suke faruwa amma dan Allah kuyi hakuri". ya k'arashe maganan yana zuwa gaban tv memory ya fitar yasaka acikin DVD ya kunna tv take Nasir da Agrif suka bayyana danna stop yayi yasake yace wa "daddy wannan video ne na daukeshi aranan da Hajja tak'ira Agrif akan yazo Nasrim tana da ciki ai su biyu suka zo idan baku manta ba suna zuwa direct a gerdeng suka tsaya nima Ina cikin akusa dasu bayan bishiyar kwaiba daganan ya danna pl duk tattaunawar da Agrif da Nasir sukayi wanda yanuna k'arara yara na Nasir ne gashi a filli ya bayyana har gargadin da Nasir yakeyi wa Agrif na idan bai saki Nasrim ba rayuwar baza ta tabayin musu kyu ba kowai gashi ashi a bayyane wannan shiya tabbatar wa iyayen yara na Nasir ne Hajja ce tabara kwallah Kara tana ihun kuka suma su daddy kukan suka fara haka Humairah Mama Ummu hatatta Izza yau abin ya girgiza ta sai kuka tayi ita duk masifan da take tsammanin zai balle batayi zaton zayin haka ba daddy da Abu suma kukan suke suna maimai allahuma gafurni'walhamni gaba daya dasu da yaran kuka suke ba me lallashin wani cikin kuka Ummu tace'' Nasir Allah ya isa tsakani na dakai da Nasrim da ita uwar munafukan Dr Fanna ashe kwara da gaskiya ta bayyana na dena yiwa shegun yara kuka haba dama da alaman tabbaya yanda sukayi kaman nan kaman ma har ya b'aci ni nasa wannan araina tun randa FAYYT ba shida lafiya jinin kowa bai masa ba sai na Nasir za a saya a saka yace kar a sawa d'an sa jinin saidawa gashinan zuwa aranan yazo kuma nasa jinin ne yayi mun dauka duk a zumunci yakeyiwa ashe yaran sane Allah yajin k'an Haruna ya mutu da bak'in ciki mafi girma wllh ita ma Zainab din tashi ce banzan karbeta amasayin jika ba harshi wannan jaririn duk da ban ganshi fili ba a hoto fari ne bazan k'ar ba ba bajinin Haruna acikin su balle Zainab da itama kama daya sukeyi sak ai shegiyar ce.... Mommy cikin Wani irin zafi ta dashi ta shak'e Nasir iya k'arfin ta dace da gaske ne nace da gaske ne Nasir Allah yagani ni da al'kairi na soka nace da gaskene ban yarda da wannan video ba gayamin gaskiya duniya abin tsorone za a iya hadashi amma ka fadamin da bakin ka..... ta k'arashe maganan tana sakin sa zubewa Nasir yayi agaban iyayen nasa yace'' Mommy sharrin shedan ne da k'addaran ALLAH ya rubuta dama rayuwar su Khafulan a haka zai zo amma Aiban Zainab da wannan jaririn wllh yaran Haruna ne ni sodaya tak habin yafaru ku yada dani kumin duk hukuncin da yayi dai-dai dani". "girgiza kai mommy tayi tace'' Nasuru kafi shedan iya hada tuggu kuma Nasir Allah ya isa ba wani hukuncin da zamu yanke nida kai sai agaban Allah". Hajja tace''towai Abdulmajid Abdulrahaman ku ba abinda zakuce ne bazaku dauki madoki ku fasa kan shege ba wannan ba jinin Abdulsamad bane tabbas an can zasa Dr Fanna sai muyi Shari'a dake wannan wani shegen d'anki kika Haifa yazo dai-dai lokacin da Halima zata haifu kika dauke namu kika sako naki kuma kika samu nasaran shiga cikin gidan kika reneshi ni dama najima ina tunanin ya akayi yaron nan yake kama dake ashe dan ki ne ban yarda ba sai kin nemo min jikana na asali wannan ba jikana bane wllh Shari'a zamuyi da gan_gan kika kashe Halima bawani wasiya da tabada na ki auri mijinta yama za ayi hakan ta faru kawai dan kin karbi haifuwar ta dan yayi kama dake sosai ni dama Ina zargin wani abun yau ayanda kuke kama dashi wllh ban karbi Nasir ba kamar yanda Amina tace bata karbi Zainab da wannan jaririn da akasawa sunan Haruna ba cikin kuka ta k'arashe maganan zan iya cewa tun da family nan suke basu taba shiga cikin tashin hankali irin wannan ba dan atake Abu ya yanke jiki ya fadi daddy da Abbaty sukayi kansa amma Ina da alaman ya gamu da paralysis cikin sauri daddy da Abbaty ne suka dauke sa zuwa asbiti mommy taci gaba da newa nazama makafuwa dama Dr Hafsa ta gayamin kaine kaine naki yarda yanzu Kashi kayi abinda hankali bazai taba kawoshi ba Nasir na tsaneka ina son ka dawo min da dukiya ta ko sadaka nayi dashi yanzu nake son kadawo min da komai nawa Nasir yanzu zan bar gidan nan bana son ganin ka tsakani na da kai sai alashira..... da sauri Nasir yace'' Mommy kuskure daya nayi zan nemi yafiyar Nasrim Agrif ya yafenin mommy kibabi dama na gyara kuskure na dan Allah Mommy ki dena FURUCIN na bazaki yafemin ba yayi tsanani akaina mommy cewa fa kikayi KIN TSANE ni mommy ke nasani bane da kowa ke kar kimin haka ki naji Hajja tace'' bata karb'eni a jikan ta ba dan gidan Abdulmajid ba ke bai kamata kimin haka ba ki yarda kedin kece uwata kamar yanda ta fad'a ke nasami mommy mommy ke nasani mommy". cikin wani irin tashin hankali Mommy tace'' ban taba tsanan wani Abu aduni sama dakai ba Nasir bana son ganin ka zan karbi kakkina ko agaban Shari'a ne". da sauri Nasir ya fice duk wani file da yasan Yana hannun sa yakwaso da sauri harda woyoyin sa da laptop din sa ya dire agaban momny yace'' Mommy inde abin duniya ne ni na barmiki su halak dinki ne mommyn ban taba tsammanin makiyan mu zasuyi nasara akan mu ba nayi zaton mune zamuyi nasara mommy makiya sunyi Nasara akan mu mommyn akwai abinda ake kullawa acikin gidan nan kar ki zauna acikin dan ba aikin mutum daya bane mak'ircin gidan nan mommyn kuma nasan keda NASRIM!!!!!! ne zaku fi fad'awa ciki amma Isha Allah daga wannan bazasu cutar daku ba zan dauki mataki mommy zan tafi kamar yanda kika buk'ata amma nasan zaki nemeni Mommy kwana kusa zaki ne meni zan tafi hatta takadduna na makaranta ba zan dauka saboda agidan nan na samesu zan nemi komai da gumina Mommy Allah wadaran abin duniya da zai shiga tsakanin mu Mommy iya kayan jiki na zan fita dashi Naira biyar din gidan nan bazan dauka ba haka ga komai na bar muku zan nemi halak dina yasa hannu acikin ajihun wandon sa yafitar da dukka al'jihun waje alaman bazai fita da komai ba ya juya sai da yakusa fita yajuya yace Mommy dan Allah kije wajen Baba Nasuru kice masa zaki he Lagos kiji abinda zai ce miki yana gama fadan haka yafice da sauri mommy tana kwallah masa K'iran kazo ka zauki shegen yaron ka wazaka barwa su". juyowa yayi ya mata murmushi ya fice masu gadi da ma'aikatan gidan suna mamakin ganin yanda Nasir yafita a k'afa suna daga masa hannu sai da yaje fita daga babban get yajuyo yayiwa gidan kallon k'arshe ya fara takawa cikin sauri Mommy da sauri ta k'arasa part din Baba Nasuru cikin sauri tace'' Baba Nasuru ni zanje Lagos". azabure ya tashi yace'' Lagos Lagos ki kaini zoki ki kai ni wajen Emaka zan karbo y'ata ZANNA FANNA Emaka muguwa ce a a Sherri akamin ta yarda zata sa y'ata ZANNA FANNA ta tashi arniya dan Allah ki kaini ai kece Halima ko FANNA yan biyun HALIMA ce zan je Lagos na karbo yarinyata maiduguri zamuje FANNA EMAKA FANNA EMAKA wani irin runguma Mommy tayiwa Baba Nasuru cikin kuka tace'' BABANA............. *wai ya batun su Abu a hospital ne* *To masoya muje zuwa rikicin babban gida yanzu aka fara fa da gaske ne Hajja bata yarda Nasir jikanta bane ya Ummu za ta dauki Zainab da jaririn Nasrim mu hade cikin pg 19 insha Allah* *Bj* [4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE* _rikicin babban gida_ *NA* *BATUL ADAM JATTKO* *SOSAI NAKE YABAWA DA* *COMMENT NAKU* *JATTKO GROUP 1* *JATTKO GROUP 2* *BATUL BATUL JATTKO GROUP* *FURUCINA NE 1 2 3 4* *KANUWA 1 2 3* *SOSAI KUKE SANI FARIN CIKI ALLAH YABAR KAUNA MASOYA BAZAKU LISSAFU BA* *SAI NACE KOMAI WUYA DAKU BALLE NO WUYA INSHA ALLAH MUNA TARE OVER AND OVER* *Allah ya albarkaci rayuwar nawa three brother din* *BABAITU* *KURU* *MUNNA* *19* " sake d'agowa tayi tana janyewa a jikin sa ta kama hannunwan sa duk biyu tace idan na kai ka Lagos kasan inda Emaka take zaka iya kai ni gidan ta?. cikin rashin fashinta yace'' sai gobe zamuje gidan Emaka Lagos ah ah zanje zanje". cin son tasake tabbatarwa tace'' a Pasta yake gidan Emaka din ko". "Eh eh a layi na ukku ne gidan me number 43 d'akin mu number 6 ne eh eh anan take y'ata Fanna zan karbo". kuka mommy tacika dayi tace'' BABANA nice Fanna nice Baba". "to to Fanna ce to Halima zamu karbo". sai yazubawa Mommy Ido tare da girgiza ai yace " ai Halima bak'ace kece Fanna Halima dani take maka Fanna tabiyu dogon hancina sai tabiyu b farin Emaka ai Fanna kece kinsan Halima ansace ta ahanyan Lagos muje mu karbota Fanna ce to to kina sallah ko Emaka bata saki kafirci ba ko"?. girgiza kai mommy tayi tace'' insha Allah Baba zaka warke zaka dawo tunanin ka gaba daya kama hannun sa mommy tayi suka fita zuwa part din ta bayan tashigar dashi d'aki na musamman ta samu adamu tace" dan Allah Adamu asake kulamin da Baba Nasuru". Adamu yace'' ai ranki shi dade jikin sa yafara samun sauk'i ada yanda nasan Babban Nasuru bashi da yawan magana amma yanzu gashi yana magana sosai kuma yana cewa shi dan maiduguri ne". Mommy neman wayan ta ta shigayi dak'er ta samu hannun ta na rawa take neman number doctor din da yake kula da Baba Nasuru suna gaisuwa ta daura da tambayar sa "ammm doctor dama jikin Baba Nasuru ne yanzu yafara magana saide yana yawan suraitar barkatai kuma gashi bai zama normal ba har yanzu". Doctor yace "Madam ai sauk'in kenan kin san da baya iya maganan sosai yanzu kuma ya samu daman magan sai yazama kamar irin yaron da yafara koyon magana kinsan yadinga surutai kenan amma shawaran da zan bada kudin ga yawan tuna masa abubuwan da ya sani ada da rayuwar da yayi a baya musamman abinda yafi so da Wanda yafi k'i sosai hakan zai dinga motsa brain din shi ko adinga gaishi guraren da yake yawan zuwa da shima zai temaka wajen dawo da tunanin sa adinga yawan yi masa abin yake so da Wanda bayaso hakan zaisa brain din motsawa". Ok Dr nagode amma idan kasamu lokaci dan Allah kasamu lokaci kazo kasake dubashi sosai". "Ok madam". tana gashe wayan Kamal yana shigowa da dukkan file din da Nasir ya ajiye a main parlour na Hajja yace'' Mommy ga wannan ki adana ai ba abinda zakiyi wasa dashi bane wannan fa shine shedan mallakan duk company na 3AFUL". Mommy zama tayi tana cewa " Kamal ina maccen ya zan ajiye abu irin wannan kai ya kamata karik'e awajen ka tunda dama ai na Nasrim ne kai kuma kai ne shak'ik'in Nasrim ka rik'e a wajen ka kafin muga abinda Allah zanyi amma shi wancan azzalumin da yabar mana nashi yatafi ka d'auki nashin ka bawa Abu ko daddy su suka san yanda zasuyi dashi nide nawa na Nasrim ne da yaran ta kuma kaine mafi can canta yarik'e mata kafin yaran su girma". ta k'arashe maganan ranta ba dad'i cikin wani irin ya nayi Kamal ya zube k'asa yace'' Mommy Allah yabar kauna Insha Allah y'ar uwa ta zata kubuta wannan daukaka k'ara da Nasir yake fa futuka insha Allah zai zame mana al'kairi mommy Nasir yayi abubuwa da dama akan Nasrim ai kinji irin Furucin sa akan bazai taba barin rayuwar Nasrim taji dad'i ba ko".? cikin kuka mommy tace'' ai kaima Kamal da nefinka tun wuri meyasa baka fada mana ba tun Agrif yana raye yanzu gashi abu duk ka ya dagule yanzu waye zai yarda da cewa sauran yaran ma yaran Agrif ne musamman Zainab da take kama da Nasir din ko Qu'rani aka hadiya bame yarda da kasani baka tona wannan asirin ba Kamal kajefa rayuwar y'ar uwar ka wani hali bakayi tunani ba nida kace muje meeting ban taba tsammanin haka bane Kamal koni kasaka min tantama azuciya ta balle wasu Allah sarki Zeenat itace abin tausayi ya rayuwar zata kasan ce idan ta girma gashi anyiwa mahaifiyar ta k'azafin kisan kai Kashi anshegan ta ta kanajin abinda Hajiya Amina tace ai ko da kasani bakayi ba Kamal na tabbata saboda kare mutumcin Nasrim da yaran Agrif yafufe wannan kasan Agrif akwai tunani baya taba yanke shawaran cikin fushi tun yana yaro Allah yabashi baiwar hakuri da ka kayamin baka tona abin ba yanzu idan Nasrim taji ya zatayi abin yayi min tsanani ya Nasrim zata dauki wannan al'amarin ni ai kwara mutuwar ta yafiye mata dan haka ni ko an daukaka k'ara bazan dauki lawyer ba gwara kawai akasheta Allah yasa can yafite mata.....…... "subbahanallah Mommy kidena fad'an haka adduan nasara kawai zaki mana". Mommy tace'' Kamal Allah ya zaba mata abinda yafi al'kairi amma Kamal ka yarda kayi gan gancin tona acirin nan dan Nasrim zatafi Nasir fad'awa cikin matsalan rayuwa amma Ina mata fatan alkairi". "Ameen yarabbi mommy me kuma wannan mahaukacin yakeyi anan?". Ya k'arashe maganan yana nuna Baba Nasuru Mommy tace'' haba Kamal Baba Nasurun ne mahaukacin kasan shidin waye kuwa mahaifina nefa". cikin sauri Kamal ya d'ago yace'' Mommy mahaifin ki kuma a a mommy wannan wani tuggun Nasir ne saboda ya cimma wani nufin sa karki yarda dashi Mommy shiyasa yace miki kije ki gayawa baba Nasuru zakije Lagos".? "ah ah dakata Kamal shiden Babana ne da gaske har numbar gidan mu da d'akin mu dai dai ya fada amma batun yarda da Nasir nidashi har abada insha Allah ba d'an yar uwa ta ba ko a cikina yafito na hakura dashi Allah yagani Halima tun bansan ita din wacece a guna bana rike mata Amana d'an ta ya butulcemin". "Mommyn kiyi hakuri kina dani ba abinda zai sameku Zainab kuma insha Allah Ummu zata hakuri ta karbeta a matsayin jika kai idan taki sai mu shigar da k'ara ai shariyar musulumci tabawa Agrif yaran duka ma balle Zainab". "to Kamal Allah yabar zumunci shiyasa akace d'a da dukiya ba a musu mugunta baka san Wanda zai amfane kaba yanzu gashi kamin gatan da Wanda na daukaka fiyeda komai a duniya bai min ba ko aurebna ban rike kamar yanda na rik'i Nasir ba Allah yanaji yana gani insha Allah zai ga sharrin abinda yamin akan sa sai Allah yaciremin hakkin na". haka de Kamal yayi ta zuga Mommy

Chapter 22 of 40