da misalai masu k'arfi har ta yarda zata shigar da Nasir *k'ara* idan an gama cese din Nasrim ya sake kafa fadan sa Sosai a zuciyar mommyn sosai taji ta yarda dashi tashi yafita da dukkan file din company three brother
d'akin sa ya shiga ya baza dukan documents din akan gado yana ihun murna cikin farin cikin yace " woow Nasir wow Nasir Nasara ko gani kafi mutum NASARA me wuyar badanci goshin jirgi me wuyar karau ".
Mama ce tashigo "lafiyan ka kai kuma meke damun ka haka".
"Mama wannan shine dukiyar three brother gaba daya yazo hannu na ni zan juya yanda naga dama".
ya k'arashe maganan yana nuna mata documents din
murmushi Mama tayi tace'' da kyu d'a daya tamkar dubu nayar dakai tunda har kasamu na saran dasa k'iyayya Nasir a zuciyar Fanna".
Dariya yasake kecewa dashi yace my Mom
this is nothing yet until I close his chapter The way Dr Fanna will look into fece again Wllh".
dogon ajiyar zuciya Mama ta sauk'e tace'' and now what's our next plan".?
Mama akwai big problem muda muke ta murnan mukadai ne da mommyn wai sai yanzu take cemin wancen tsohon mahaukacin da yafi shekara 40 a haukace wai uban tane kinga murna yakoma ciki kenan mommyn tana da family".
dariya Mama tayi tace'' da kai sai yanzu kasani ok ashe ranan da Malan k'aura ya gayamin baka k'asan ai najima da sani kuma yamin aiki akai bazai taba iya tuno inda dangin sa suke ba kuma Fanna bazata iya zuwa wajen mahaifiyar taba amma tunda ta kano uban tane abu yafara warewa kuma kasan yanda mukayi da K'aura na baka umarnin ayau yau ka kashe tsohon mahaukacin nan kisa bata hanya wuka ko paison ba kisa ta hanyar ba za a gano wani ne ya kashe Shiba kisa ta hanyar toshe masa numfashi sannan kafin wannan kaje kasamu Fanna kace tazo tabawa daddyn hakurin amaida auren su kace mata idan tana amatsayin matar sa zata san yanda zatayi ta shawo kansa ya tsaya mata akan Shari'a Nasrim kace mata kuna buk'atan Daddy Sosai a cikin cese din idan fa ba amaida auren nan ba baza a samu duk yanda akeso ba koda an kashe Fanna kasan ana yankewa Nasrim hukuncin kisa aranan zan San wa Fanna maganin da K'aura yabani wanda zai fasa zuciyar Dr Fanna tafara aman jini idan aka kaita hospital Doctor yace zuciyar ta ce tasamu matsala kaga kuma K'aura ya tabbatar min muddin aka samu mutum yaci maganin nan to bazayyi ko kwana 2 a duniya ba kaga muta ne zasuce ciwon zuciya ne ya kashe ta sai Zainab kuma yace mota ce zata k'adeta ta mutu wannan Theron Khafulan din ne ankasa gano meye k'arshen sa idan yakagara shima de mai sauk'i ne inde muka samu duk wannan abin amma yau bana son mahaukacin nan ya waye da rai".
"No problem Mama".
"amma Kamal ka tabbatar ba wannan shagen CC TV din agidan nan ko".
"ai Mama dama nine me kula da cc din gidan kuma na lalatashi bayan da za ayi ya gyaru yanzu tunda me naci akan CC TV din ya bar gidan".
dariya Mama tayi tace "ai wannan gida saide ya hangesa daga nesa bakaji abinda K'aura yace ba Nasir sai yayi *dako* akansa Nasir saiya zama* boyi boyin*
gidan mutane".
Kamal ya kece da dariya yace'' ai aikin K'aura Yana tafiya yanda ya kamata duk abinda yace mana sai ya faru kai wayaga NASARA da aikin gidan mutane wayaga NASARA da dako wayaga NASARA cikin rana yana bara *GOSHIN JIRGI ME WUYAR KARAU NASARA KO GONI KAFI MUTU*
THANKS MY ALLAH ka bani DAMA dukiyar three brother a hannu na
yanzu abin da yarage na tunzura Humairah itama ta kashe Izza kinsan kishin ta yafi na Nasrim zata kashe min Izza itama Humairah a kashe ta shikenan tunda ga Abu yakamu da paralysis zai mutu shikenan ba mesamin Ido Abbaty yana tafin hannu shi wannan".
Mama tace'' yakamu da paralysis ko K'aura yayi aiki ai ba Abdulrahaman ba taka doron k'asa sai de bayan k'asa zai tadda Abdulsamad acan su k'araci soyayyar su can".
Mommyn bayan fitan Kamal mommy tana shirin kiran Dr Hafsa kafin ma ta danna Kiran taji sallaman Dr Hafsa
asanyaye Mommy ta amsa
zama Dr Hafsa tayi
mommy tace'' da yanzu fa kezan kira naji sallaman ki".
Dr Hafsa tace
"ni bam ma kunna wayan ba yanzu shigowata k'asan ko 30 minutes banyi da sauk'a ba"
Mommy tace'' Dr Kamal yace min Nasir yasa an kamaki da gaske ne".?
ajiyar zuciya Dr Hafsa ta sauk'e tace'' da gaske ne amma kwana 2 nayi a cell aka fitar ni a k'asan ma baki daya dafari Istanbul aka kai ni wata na biyu acan ana bani kulawa ta musamman saide bana amfani da waya daga nan aka kaini saudia acan nayi wata 4 yau Ina zaune yaron da yake kula dani yazo yace wai idan Ina sha'awar komawa gida daga yanzu zuwa san da naga dama atake nace masa yau shine fa muka zu bakiga mayyan kudin da aka ban ba wai nayi sayya niko ban ma samu nutsuwar da zanyi wani taayya ba kawai inason naga nazo yaran na su gani naga halin da kuke ciki ina sauk'a Amira tace wai kema bak'ya gidan sannan saura 1 week ayi zaman Shari'a Nasrim hankali na yatashi yanzu meye abinyi".
Mommyn fad'awa jikin Dr Hafsa tayi tafara kuka tace'' nashiga ukku Dr narai ni makashina na rai ni mak'iyina ashe Nasir shine yake duk wannan abubuwan ".
da sauri Dr Hafsa ta cire Mommy ajikin tace'' wait impossible ba shi bane ba Nasir bane nima dashi nake zargi amma tunda yasa aka daukeni nadena zargin sa da shine me yi da bazai daukeni a idon mutane ba dan duk ikon sa ai yasan hukuma ta fishi da Nasir ne me kulawa bazai dauke ni a bayyane ba kuma da aka dauke ni bazai bani kulawa ba kawai de inaga yabamu kariya ne kema bari dayayi aka tafi dake dan ki samu kariyane sai da nayi dogon tunanin na gane hakan kuma ai sh......
tace
"da kata Dr Hafsa wllh wllh shine daganan ta kwashe komai ta fad'a mata har bayyana Babatan".
"Inna'lillahi
Yasalam wannan wane irin musifa ne meyake faruwa su Khafulan shegu...
shigowar Zeenat da tsananin kuka ne ya k'atse Dr Hafsa cikin sauri suka tambaye ta me yafaru
cikin kuka tace'' Ummu da naje neman uncle Abbaty zai kani wajen wasa shine tace bazai jeba wai shi ba uncle dina bane ni shegiya ce bani da Baba shine Abdulsamad yake min dariya wai gobe sai ya fada a class dimu nima za ayi ta tsokana ta irin na Muddam za acemun shegiya".
Mommy tace'' yanzu Ina uncle din naku ".?
"yana can suna fada da Ummu yana ta kuka".
ajiyar zuciya mommy ta sauk'e ta sun kuyar da kanta
Dr Hafsa tace'' Zeenat zonan Zeenat tazo hannun ta Dr Hafsa ta kama tace ina Khafulan yake".
"tace Yana cikin gedin yana Exercise".
"Ok kije ki kiramin shi".
bajimawa sai gashi sun shigo tare
Dr Hafsa kama hannun Khafulan tayi tace'' Khafulan kasan wani Muddam a school din ku".
"Eh meye friend dinane"
yafada cikin iko irin nasa
Dr tace to me yan class suke ce masa".
"cemasa suke shege bashida Baba amma yanzu duk na musu duka suna tsoro na basa fada yanzu".
Dr Hafsa tace'' good to gashi can Abdulsamad yace wai tomorrow idan yaje zai gaya yan class Kai da Zeenat shegune kaje kamasa Wornning Sosai kar yaje yafada".
da gudu Khafulan yafice Yana huci kamar zaki
Mommy tace'' Dr Hafsa da bakiyi
haka ba Khafulan fa bashida dad'i zai jiwa dan mutane ciwo gashi dama Humairah yanda take acike kiris take jira wllh zai iya zama matsala".
Dr Hafsa tace'' ai hakan shine dai-dai Fanna idan yaje yafada a makaran matsala zayyi yawa kwara tun agida ayi maganin abin".
Dr Hafsa bata rufe baki baki ba Hajja shigo tana cewa'' gata nan annoban kungan ta".
ta k'arashe maganan tana nuna mommy
dan aiken Alk'ali ne ya mek'a sammaci wa mommy mommy k'arba tayi ta duba wai ana tuhumar ta da janza jariri shekaru 37 baya za ayi zaman kotu ranan Wednesday me zuwa sati daya kenan kuma aranan za ayi zaman kotun Nasrim mommy ajiye takar tayi tace'' Allah yakai mu".
Hajja tace'' ehhhe za a ne monin jinin Abdulsamad dina dan ban karbi wancan ba kuma ba a kotun mijin naki za ayin Shari'a ba dan naga ba alamun damuwa a fuskar ki ehee na kai inda za a share min kuka shi Abdulmajid danace zan Kai kotun sa ai haka yace wannan maganan shirme ne ba to zasuga gaskiya zata fito dashi oyo duniya yanzu meye ba ayi mak'irci da zalici yayi yawa dan kina son auren me kudi sai kin bi ta wannan hanyar".
ta k'arashe maganan tana kallon Baba Nasuru cikin mamaki tace'' to shikum Nasuru me yake anan nifa nafara gajiya da tsuntattun maguna kowa ya kama gaban sa wllh".
Dr Hafsa tace "ba tsintaccen mage bane shine asalin Baban Dr Fanna atake Dr Hafsa tayiwa Hajja bayani
Hajja tace'' allahu Akbar kabila wassubbahanakal lahu kasiran walhamdu lilashi bukuratin a asila
o ni haka shiyasa Fanna da Nasir sukayi kama Kai itama Haliman ai muryar ta da kafar ta da kwayar idon iri daya da Halima duk Halima an can za mata fuska ai jini baya b'ata wayyo Abdulsamad dina
Kai maimunatu kiramin yaron kotun tan nafasa karan sace min jikana na dena tan tama shine yanzu zan shigar da k'ara Fanna ta koremin jika ta nemo shi duk inda takore sa yaro da kidan uban sa".
yaron kotu Yana zuwa Hajja tace'' yauwa yaron kotu ka juya Karan zuwa ga Dr Fanna ta koremin jika tanemo min duk inda yaje tana gani yafita anemomin NASURUDDEEN dina eyee".
yaron alk'ali girgiza ai yayi yace'' hajiya wannan ba aikina bane ki koma office kiyi bayani".
aiko Hajja ta fara kutum tuma masa zagi tana cewa yo kajini da matsiyacin wllh kaine matsiyaci yo Allah na tuba ni Alk'alin sukutum na haifa duk Nigerian nan shine na biyu ka kayan min haka ko baka san nan ne gidan su alk'ali Abdulmajid Haruna bane d'an uwan three brother Abdulsamad kai wata k'ila ma d'ana Abdulrahaman ne ya koyar da Kai a B U K furofesa Abdulrahaman shima d'ana ne ni zaka gaya hanya kode bakin ku daya da Dr Fanna din nasan matakin d'auka".
ta k'arashe maganan tana dungurin k'eyar sa
sumsum yaron yafice zata bisa waje Humairah tashigo da masifan ta tace'' ke mommy ke kika aika Khafulan yayiwa Abdulsamad duk wllh zai shigo zai na tabbatar masa shi hakori yacirewa Abdul ni kuma wllh kafa zan cirewa yaro".
Hajja tace'' Amma Amma Aisha dama kedin tsiyace ban sani ba Dr Fanna kike cewa ke mommy yo kice Mata Fannan ta ma mana shi Abdul din naki naga yafi Khafulan da wata har 3 in ba dai ragon banza akayi ba har yana tsaye zai zudda ma hakora".
Humairah kallon Hajja tayi Sosai tace'' ke kuma Hajja yanzu waya ke take ai asbitin mahaukata zamu turaki nide ba abinda zai hana ni illata d'a wllh zan kamashi".
Kururuwa Hajja tasa tace''
to Dr Hafsa Fanna Yawwa Kamal kama kashigo kune sheda ga Humairah tayi FURUCIN sai ta illatamin dan jika duk abinda yasame sa itace yo dan yafito a ta silan Zina ai ba kansa farau ba nide inason kaya na ai jinin Abdulsamad ne dan gidan Nasir ne fa"
tsaki Humairah tayi tace'' kinga dangin ma kasa nan".
tafice tana rantsuwar ba abinda zai hana bata illata Khafulan ba
Kamal da Mama yace " Mama ki kira K'aura yanzu ki sanar masa ga Humairah tayi FURUCIN akan Khafulan inda yuwar abinda zanyi yayi kinga munjefi tsusu biyu da tarko daya kenan idan Humairah ta kashe Khafulan itama aka kasheta kinga na futa daga binciken ta wllh Mama Humairah shegiyace bincike take sosai zata iya bamu masala fa".
cikin dare mommy take jin ihu a d'akin da abawa Baba Nasuru a part din ta
cikin sauri take sauk'owa a steps din tana tambayan laf..........
*Masoya mu kasance a 20 pg 20* *zai zo miki da abin mamaki *
*taku bj*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*_Assalamu'alaikum_*
*_dan Allah duk wanda_* *_na b'atawa akan auren mutu'A suyi hakuri banyi dan wata manufa ba bana son ana min fassara na daban wan ba shine manufata ba da banyi niyar magana ba amma cecekuce yayi yawa dan Allah ayi hakuri ba ak'ida na zaga ba ko kushe a cikin kowacce ak'ida akwai masu son zuciya nawane acikin izzala zasu kirawani babban malami suce ai wane meci da addini ne kuma D'an ak'idar sace me fadan hakan nawane acikin d'arik'a zasu ce malam wane meson zuciya ne so ba akida na zaga ko na kushe ba masu son zuciya na fad'a dan acikin labarin Lawisa ai nace babata kudin abokin ya bashi yaci ya dauke ta ya kaita so ban zagi ko wacce a k'ida ba amma kusani akowacce ak'ida akwai masu son zuciya kai ba ma ak'ida ba ko uwa daya uba daya kuke da mutum zakiga Fatima tafi Zainab son zuciya ko kiga Ali yafi Haruna son zuciya balle ak'ida to sorry sorry sorry sorry sorry sorry sorry sorry dan Allah kada akara min magana akan wani ak'ida ilimina bai kai inda zan tabo wannan ba son zuciya nayi magana akai kuma awanan zamani dan uba yaci kudi ya d'auki y'ar yakai ayi zina da ita wllh ba abin mamaki bane nawa Yana faruwa ba adaki so amin afuwa Dan ALLAH_* 🤲🏼
*20*
cikin sauri ta tura kofar Baba Nasuru ta gani ya danne Kamal yana ta duka cikin sauri ta k'arasa gadon tace'' ya haka Baba Kamal ne kadena dukan sa bar shi dan Allah kaga duk kaji masa ciwo ".
ko gizan Baba Nasuru bayyi ba kuma bilhak yake jingar Kamal abin ka da d'an hutu jikin har yasake ganin komai zai iya faruwa ga kuma tana ta kururuwa ba meji yasa tafita da dudu part din Mama taje cikin kuka ta haura sama cikin kuka tunkafin tayi knocking daddy da Mama sukaji muryar ta da sauri suka fito ta musu bayani cikin sauri suka k'arasa Hajja ma har taji tafito Humairah ma da yake dama ba bacci take ba tana saman baran dan saman taga shigan Kamal part din mommy har zuwa fitowan mommy dan dama tafito ne saboda nayi taget ko Kamal gun Izza zaije sai kuma taga yayi part Mommy shine ta tsaya taga fitowar sa
dak'er daddy da masu gadi suka kwaci Kamal ko hannu baya iya d'agawa dan yadoku Sosai
Baba Nasuru cikin huci yafara cewa " kubani shi wllh kashe sa zanyi kashe sa zanyi marara amfani wawa mugu makashi zai kasheni yazo ya kasheni filo ya dan namin zai kasheni ni zai k'ashe ni zai k'ashe kubari na k'ashe sa nace mugune amma soko ko k'arfi bashida shi kubani shi".
Hajja tace'' to kisa kuma Kamal me Baba Nasuru yama kabiyo shi har d'akin da yake zaka kashesa kakan Nasuru nefa Amanan Abdulsamad nefa ikon Allah ni mariya Haruna ya tafi yabarni awani irin duniya..
sai ta fashe da kuma
Kamal cikin shak'iwar muryar yace'' ah ah nashigo ne fa zanyi masa mu kwan lafiya tunda mommy tace Baban tane naji ina son girmamashi shine nasamu yayi bacci kuma naga ya sauk'a akan fito zan gyara masa shine kawai ya hau kaina me wannan tsohon zai min da har zan nemi kashe sa".
aiko Hajja ta dena kukan tana Jan majina tace'' Babana ban da abinka ana irin wannan ganganci da mahaukacin ne yanzu fa da yakashe ka yakashe banza ba a Shari'a da mahaukacin
to tsaya tsaya ma meyaha naka kwanciya har karfe daya darabi kana yawo gidan mutane yo idan ba munafiki wayake yawon dare ko de gadin mu kake saboda tsaro ganin kashe kashen da ake agidan ran mutum ba abakin komai yake ba agidan yan ukku".
Mommy tamatsa kusa da Kamal sosai tace'' sorry my son amma de ba abin da yake damun ka ko".
"Eh mommy Ina lafiya".
"Ok dan Allah kayi hakuri Allah yakiyaye gaba
dama yanzu doctor din sa yakirani yake cemin wai gobe za afita dashi abin yaban mamaki dazu mukayi waya yace ba komai amma yanzu wai za afita dashi nace zan nemi me kai shi yace ah ah shi zai kula dashi jirgin asuba zasubi".
Mama tace'' mommy amma bai dace abawa doctor kawa yatafi da Shiba sai kace marar gata wacce k'asane za akai shi ma ".?
Mommy tace'' wllh ban sani ba".
Hajja tace'' to de Allah yabashi lafiya ya fada mana inda danginsa suke musan asalin Halima ita wancan k'edarar ta Lagos kuma yau she zakuje mata ai ni wannan abin kunyar har Ina ni Maryama ce da hada jini da k'edaraye Haruna ka hadani da aiki".
Ta k'arashe maganan tana ficewa tare ta toshe baki tana rufe hamman da takeyi
Daddy yace'' Dr Fanna muma a goben zamu wuce da Abdulrahaman JIDDA zamu tafi da Aisha da Abbaty yayi magana yanayin gaba Mama tace'' gaskiya alk'ali ba inda zani y'artawa tana cikin wannan hali ankusa zaman kotu na bari na tafi Ina ai bazai yuwu ba".
Daddy zuyowa yayi Yana kallon ta yace'' ba jimawa zamuyi ba bai fi 2 days ba zamu zo saboda cese din".
Mama da daddy suka fita ita ma
Humairah ta kama hannun Kamal tana cewa " kai me yakawo ka ai da kashe kan yayi da ya kashe banza za afake da mahaukaci dangin makasa kawai Allah sai ya isar mana jinin ya Haruna bazai tafi abanza ba sai an kashe Nasrim ko ajikin gol aka sassak'o ta".
Kamal yace"Humairah na gaya miki gaskiya zamu iya samun matsala idan kika cigaba da fadin wannan kalaman naki shifa Shari'a sabanin hankaline wai Nasrim da kikafi kowa sanin ta kike gayawa irin wannan Magan ganun".
Har suka fita mommy ta sauk'e ajiyar zuciya ta kama hannun Baba Nasuru ta kwantar da shi taja blanket ta rufesa ta tofa addua a kowacce kusurruwa na d'aki tafita Taja masa kofan
A parlou ta zauna tayi tagumi tana tuno irin matsin rayuwar da suke cikin duk tunanin da tayi yana tsayawa ne akan Nasir ya aikata duk wannan ta asan dan ya tsani Nasrim tunda har zai iya mata fyade ranan auren ta a daren tana farko kuma ya hana mijin sake kusan tar ta to meye ma bazai yi ba tunda dukiyar ta yake hari
girgiza kai tayi afili tace'' why why Muhammad Nasir me zakayi da abin duniya kaidin d'anane jinina d'aya nake daukar ka da Nasrim meyasa kayi kisan kai me nayi maka".
cikin kuka da yazame mata abinci da sha duk Wanda yasan mommy ada a yanzu idan yagan ta dole ya tausaya mata gaba daya a birkice take tama rasa meyake damun ta dafe k'irjin ta dayake mata matsanancin ciwo tayi tana fadin inna'lillahi
atare suka fito daga wankan nasa kayan tafara daukowa ta bashi yafara sawa ita kuma ta juya tana kallon cikin wodrop din da alaman akwai abinda take dubawa har yagama saka kayan ya k'arasa mirror Yana shafa Mai har ya gama yajuya yace "ai kin kasa zaban wanda zaki sane kome dare yayi bacci nakeji".
juyowa Humairah tayi tace'' kasan me my money wllh sleeping dress dina wanda ya Agrif ya kawo mana nida Izza da Nasrim a zuwan sa na k'arshe shi nake ta nema ban gani ba Wanda de Nasrim ta kashe su ajikin ta".
cikin basarwa Kamal yace'' ok kina da irin sa kenan kema ".
"wane irin tambaya ne wanna Kamal da akwai wani kaya da Nasrim take dashi ni banida shi naga idan kaine katashi sayo mana tare kake sayowa haka ya Agrif tun muna yara kata ba ganin an ban ban tamu da wani Abu ne? ".
"haka amma ai kaman sleeping dress in naga wanda yamin ai ina iya sayo miki musamman idan na kunya ne sosai ko".
Humairah tace'' Eh amma ina dashi nawan naraa shi".
kai my heart kisa wani mana dolene sai shi
ko kuma ya b'ata awayen wanki ne dan nima Ina neman wasu kayan Ina rasawa".
ajiyar zuciya Humairah ta sauk'e tace'' ah ah bana tunanin haka dan gaskiya ni ban taba sa shiba ma Kai ban fitar shi a ledan saba ma gaskiya balle yashiga kayan wanki
sannan akwai wani shijabi na marroon color wanda shima de irin me nikaf din wanda shima dashi Nasrim tayi kisan gaskiya ina son sa mommy ce takawo mana a saudia bana ganin sa shima kuma nasa sade amma ban ma sa acikin kayan wanki ba bazan manta randa na sakashi ba zamu Kai kayan sa rana na ya Abbaty na fara sa shi ina zuwa anan na rataya kuma kasan washe garin ranan Wednesday abin ya faru sai takalmin da yake k'afan Nasrim a video din da tayi kisan bazan manta ba Nasrim tayi kyauta da nata ko sakawa batayi ba tabawa Nabila ina na Izza kuma bak'i ne namu yellow to abin yana daure min kai".
Kamal k'an k'an ta Ido yayi yana kallon Humairah yace" to me hakan yake nufi kenan".?
Humairah ta sake jefa idon ta cikin nasa tace'' meko kawai de neman kayan nake daga shijab din har takalmin da rigan ban ganshi ba".
tsaki yaja yace "yanzu Humairah har kedin ce kike neman kayan da yayi kusan shekara kituna ko kin bawa wani de dan mutur su Agrif mafa wata shida kin manta ne dare yayi bacci nake ji idan kuma baki da niyar kwanciya sai da safe yayi magana yana hayewa kan bed din yaja wutan gefin sa ya kashe yaja blanket yana sake jan tsaki
gyad'a kai Hummee tayi ta dauki wani rigan bacci tasa ta haye gadon
Da asuba doctor yazo yatafi da Baba Nasuru shima daddy shida Abbaty suka tafi asbiti dan wucewa da Abu India
" Kamal kana nufin kayan sun bata kuma da jinin ajikin sa ya akayi hakan ta faru dama tun ranan ba nace kafita da kayan a gidan ba wannan abin fa ba karamin abu bane idan kayi wasa wllh zamu iya kwana ciki fa yanzu dama daga takalmin har rigan da shijab din da safan hannu da nabaka ka fita dasu aranan a cikin daki kaje ka ajiyesu inna'lillahi Kamal ka b'ata komai".
Kamal dafa kan sa yayi yana feso da iska me hucin zafi ta cikin bakin sa yace'' wllh Mama ban samu dama ba aranan kinsan yanda gidan nan ya hargitse shine naje na daga katifa nasaka a k'asan bed shine na manta gaba daya yanzu kuma na duba ban gan shiba".
Zama Mama tayi ta dafe kanta tace'' shikenan dama binciken da Humairah take yawan yi maka akan sane tasani Humairah tasan komai amatsayin ta na cikekkiyar lawyer wannan kayan kadai ya isa hujji awajenta Kamal yanzu ya za ayi gashi saura 6 days ayi zaman kotun ".
azabure ya tashi yace'' Mama yau Humairah zata mutu baza ta kwana da rai ba".
zai fita Mama ta kamo hannun sa
cikin tashin hankali tace'' Kamal kar kaje ka sake tafka kuskure bamu sani ba ko Humairah ta sanar wa wani kaga idan ka kasheta kamar ka kashe macijine ba ayanke kan ba dan haka yanzu abin yi dauke Humairah za musa ayi akaita wani gu abata azaba ta fadi wanda ta fad'awa sai musan abin yi amma bayan ta fad'a mana sai mukashe ta
ga mata dayawa agari kazabi zabin ranka ba wanan matar cushe ba".
shiru yayi ya gamsu da abin Mama tace'' masa
Mama tace'' Kamal har yanzu ka kasa gane inda Barira take ko wllh bamu kadai bane muke ai ki acikin gidan nan tunda kaga bamu muka saka abawa Hajja paison ba mahaukaciyar tsohuwar nan bata gabana yanzu abar ta tun da tana mana aiki ai ita take k'ara hura wutan Shari'a Nasrim kaga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 40