Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
```waishi me yake damunsa``` "Nan kece. ya furta cikin sanyi da tausasa murya "ni kuma Nan kinki barin yayuwata ta huta kalma daya tak nake son naji ki faɗa min nasamu salama duk da kin taba fada min batare da kinsan ni bane amma yanzu inason ki furta min a matsayin Nasir ne agaban ki". ganin yanda shirmene kawai acikin zantukansa kuma idan ta cigaba da tsayawa zai iya jefata wani hali ganin yanda yake shirin hade jikin su ya jefata halin jiya sai kawaai ta fincike hannun ta Allah ya temake ta bai reke da karfi ba tasamu ta kubuce cikin sauri ta taka step din shiko zubewa yayi dafe da maran sa anan Hamza da Umar yaran Ladan sukazo suka same shi sunyi mugun tsorata da ganinsa kwance yana faman birgima rasa yanda zasuyi sukayi ganin yana cikin ma wuyacin hali yasa da sauri suka kira number doctor din sa dayake kwanki Aliyu yayi rashin lafiya dr dinne ya dubashi suna da number sa suna masa bayani yace gashinan zuwa Umar ya taba jikin nashi yace "Ya Hamza jikin bro kamar wuta wani irin nishi Nasir yake fitarwa cikin ƙanƙanin lokaci yafita daga hayyacin sa kuka kawai suka fashe dashi alokacin da suka ga Nasir ya suma daidai lokacin kuma Dr ya iso dr bai sha wahalan gano matsalan Nasir ba ganin yanda manhood din sa ya kandare temakon gaggawa ya bashi bajimawa bacci ya daukeshi anan free parluor din suka kwana sai gabannin asuba yatashi sai asannan yasan su Aliyu sunzo tashi su yayi a firgice Hamza ya tashi yace "yaya ka samu lafiya Alhamdulilah". Nasir yanuna su Umar da suke bacci yace "tashesu ku wuce masallaci nima ganinan zuwa kuyi amfani da bathroom din palon nan dakin ku akwai baki ciki yayi maganan cikin karfin hali tareda juyawa yana taka stepdin ahankali har yashige ciki lif yayi cikin bathtub yarasa me yake damun ƙwaƙwalwar sa gaskiya abanza iyayensa bazasu kawo masa Nasrim gida haka kawai wai dan tayi karatu ba kuma ma har yanzu ba suce ga makarantar da zatayi ba numfashi ya sauke yana cigaba da tasbishi a zuciyar sa badan ance idan ka roki Allah bai amsa maka ba ka saurari abinda zai baka wanda sai yafi abinda ka roka awajen sa ba zai iya hakura da Nasrim ba amma ba agajiyawa da rokon Allah halin da yake ciki ko makiyin sa bayason da fada ciki jin ana shirin tada kikamane yasa yayi saurin karasa wankan Nasrim itama de tasha wahala kafin bacci ya dauketa Allah ya isa ta jawowa Nasir yafi cikin kondo maganan sa na jiya ne yake gilma mata cikin kunne _daga ni harke mabukatane duk Maccen da yatsun kafarda suke aware zaki sameta da ni'ima mai gamsar da namiji amma zaki samu bata da matsi sosai nikuma hakan nafiso nafison na sake sosai yanda bazan wahala ba_ hakan yana nufin ita jarabebiya ce akuma bude take shiyasa yawanci Agrif yake sayo mata maganin b Matsi kenan sake kallon yatsun kafar ta tayi numfashi ta sauke afili tace dan adam tara yake nasha gayawa su Zahra idan sukace min ban rasa komai ba gashi yanzu Nasir yamin bayanin da yake nuni da zan iya rasa babban abu bata san sanda ta fashe da kuka ba inama kyan fuska na rasa da kanta tashiga kitchen akaron farko dan abincin saya kawai sukeci tunda tazo batayi gigin shiga kitchen din ba komai fes saide bawani isheshen kayan abinci musamman abin zata mukata babu saide taren kayan hadin coffee kala kala fitowa tayi tazauna a palon tana tunanin yanda zatayi ta samu abinda zata dafa kodan yaran ajere suka shigo dasu Umar kallo daya yayiwa gefen da take ya haye sama cikin takun isa su Umar suna ganin Nasrim suka gane yar uwar Nasir ce dan sunsan fuskan ta alokacin da ake zarginta da lefin kisan kai bawanda bai san fukan taba kuma sun san ita aka aurawa Nasir sunji Baban su yaba faɗa cikin ladami suka durkusa har kasa suka gaisheta har Hamza ta idan bai girmeta ba zasu iya zuwa sa'anni itama tanaganin fuskan Aliyu tagane dan uwan Sadiya ne cikin sakin fuska irin nata ta amsa tana tambayar yaushe sukazo anan suke shedamata ai anan suke weekends kawai suke zuwa gidan tace "balefi Allah ya temaka dan Allah ko zaku dan sayo mana kayan abinci". da sauri sukace me za asayo rubuta musu abinda zata buƙata tayi tabasu amma tayi tayi sukace bazasu karbi kuɗi ba da ATM din Nasir a hannun su bajimawa sai gasu Hamza ne kawai bai bita kitchen din ba Aliyu da Umar tare suke aikin sun ko temaka mata sosai anan suke gaya mata yayan nasu bashida lafiya saida suka gama jere komai a kan dining table Abdul ne ya fara fitowa da wankan sa fes da sauri ya karaso yayi hugging din ta yace "good morning my Ammi "morning my son ina Khaflan".? "yana sallah waro ido tayi tace " baku tashi da asuba ba". "bacci mukeyi bamuji asuba ba ina papa?". shima ya jewo mata tambaya". yana sama bari nadubo su Muwwada". tace tare da wucewa ɗakin da su Muwaddan suke shima Abdul ya koma saman dan dubo Papan nasu Khaflan yana fitowa ya hango kowa a dining har su Umar amma babu papa yasa yace" ina papan"?. wani uban harara Nasrim ta zuba masa tace "yana gidan Salamatu". daure fuska yayi ya yakoma saman dakin papan ya same shi ƙudundune cikin blanket barkon yaja Nasir ya dago yazuba masa jajayen idon sa yace "son ban tasheku da asuba bako na barku ku huta ne kunyi sallah". Khaflan bai bashi amsa ba sai hannun sa da yakai goshin papan nasa a tsorace yace" papa jikin ka zafi ba kada lafiya ko,". yakarashe maganan yana kara laluman jikin nasa kamar zai saki kuka murmushin karfin hali yayi yace "ina lafiya khaf bari nasaka a kawo muku abinci dauko waya ta ka rubuta abinda kowa yake so". Papa Mami tayi breakfast kafito muje" nacin yaron yasa ya tashi suka fita Nasir yaji dadin abinci musamman irish da pepper chicken Khaflan ya kurbi Hollandia yace "thanks Mami abincin ki yayi dadi papa Mami ta iya abinci ko". Nasir bai dago ba yace "yes good nan danan yaran sukayi sabo dasu Umar dan sun jasu jiki sosai daga karshe ma suka kwashesu suka fita gida yarage daga Nasir sai Nasrim dan Rukkaya ma tare aka tafi da ita saboda ta kula dasu Musanat Mommy da dr ya kirata ya gaya mata abinda yake damun Nasri tsorata tayi gashi ta kira wayan sa baya picking daga karshe ma yakashe bai taba mata haka ba dan tasan Ringing din ta ma daban yake acikin wayan sa Nasrim ta kira Ringing biyu da tauka tana cewa "ran Mommyn Khaflan ya dade mommy wai ni ina auta dan Allah mommy ko awaya ku hadani dashi mana ko gwaranci yamin ko video call zamuyi ". "ba dan wannan nakira ba ina Nasir".? tabe baki Nasrim tayi tace "Mommy inaga yana dakin sa tun safe de ya fito yayi brea kfast amma bai sake fitowa ba su Khaflan ma da zasu fita sun shiga wai bacci yake". "Nasrim kina jina Eh Mommy kingade Nasir mijin kine kuma ɗan uwan da baki da kamar sa dan gidan yan biyu na Nasir ya kafe idan bake ba macce da yake so dama ina son ya kwantar da kaine awajen ki to hakan bazai samu ba dan haka ina umartar ki da kije ki temaki mijin ki saboda dr yakirani ya gayamin magun gunan da yake sha na rage karfin sha'awa yana son kawo masa illa abin ka da bature a yau din yasamo masa mata sunfi 20 ƙi yake daga karshe ma koran dr din yayi shine ya kirani yake kayamin na kira Nasir amma baya dauka kinga auren sane akan ki aure ba abin wasa bane Allah zai iya kamaki da lefin hakkin sa ki kai masa wayan zamuyi magana dashi". ahankali Nasrim ta tura kofar ta fara takawa har gaban bed din baya kai sai wasu hotuna masu yawa da aka baza akan gadon dauka tayi daya bayan daya tana kallo hotuan tane tana jaririya da kuma wanda ta fara tasowa har zuwa girman ta wasu ita dashi wasu ita daya amma wanda take a babban ta yawanci tana bacci aka dauke ta hotunan sun cika gadon gasu abaje wani litafi wanda aka rubuta ( HISTORY N'N) tagani zama tayi a bakin gadon ta dauki litafin page farko sunan sa tagani tarishin rayuwar sace har zuwa pages 5 a gurguje ta dinka tsalaken karatu ta wuce shi page na 6 (*MY HALIMATUS SADIYA HASKEN YARUWA TA*) tagani da manyan baƙi bin rubutun ta dingayi tarishi yaruwar tane tun daga inda Mommy take fada masa zata haifa masa brother yace "no Mommy nafison sister irin Humaira ni sister nakeso har inda mommy take cemasa to tayi scanning burin sa yacika baby girl ce hugging din momny yayi yadinga salle yace mommy sunan ta Halima sunan mommy na da tarasu za amaida kuma zamu kirata _Nasrin minallah_ nasrin minalla wata itaciya agidan aljanah wanda Allah ya albarkace ta da kamshi da ni'iman babu mai shigar sa sai wanda yadace da aiki mai kyu Mommy sunan ta Nasrin harzuwa inda ake haifarta da kwanakin watan da abinda yayi na bayason ganin ta afili amma a boye yana mata zafaffen son da ko mommy bata mata inda yacire mata dan yatsa saida shima yayi yunkurin cire nasa da kalaman nadama da yarubuta har zuwa inda yazo mata da sunan yana sonta da suna Na'im tare da zafafan kalamai duk wani kyauta da yake bata dasunan shine Na'im da zoben NN da yabata Na'im Nasrim tayi soyayya da Na'im a boye tayi tayi ya bayya na mata kansa koya yake zata yarda dashi amma yaki daga karshe tace ba mutum bane aljani ne ta hakura tashi ta karbi Agrif din ta kawai alokacin auren su da Agrif yasha mata wanning amma take sharewa saboda aganin ta ba mutum ba ne saboda komai na rayuwar ta kamar atafin hannun sa yake idan yana zayyano mata abu game da kanta ko ita bazata iya rikewa ba daɗin daɗawan ƙara tsoron sa kenan komai yasani game da ita kuka taji ya kuf ce mata inda taga halinda ya shiga adalilin auren ta da Agrif amma akasan ranan aure ya rubuta kalamai kamar haka _banyin nadaman karban vaginity din kiba Allah yagani na wahalu kuma zanji sauki idan natuna ni nafara sanin ki ina miki fatan gamawa lafiya Agrif baya daukan wanning da bai aure min ke ba duk wanda yarasa masoyi yayi babban rashi_ sai inda cikin su Khaflan ya bayyana yarubuta MY BLOOD IS PASS YOUR OWN I HAVE SUCCEED ON YOU _ayanzu zaka barmin ita tunda gashi Allah yabani raboda ita_ sai randa aka haifi yaran da yarubuta _Allah mezan cewa yara ukku idan ka gurfanar mu agaban ka suna neman hakkin su na samosu danayi ta kazantaccen hanya nasan de aduniya asirina bazai taba tonuwa ba saboda nasan halin dan uwana bazai taba tona asirina ba lashira nakeji_ bari tayi tasha kukan ta afili ta furta dole hausawa suce girman kai rawanin tsiya da kafurta kana sona tun farko hakan bai faru ba ashe kai ne Na'im bazata taba manta irin kalaman sa da yake rikita mata kwakwalwa ba kullum ta kwanta sai tayi mafarikin kalaman Na'im kamar yanzu yake rubuto mata rufe litafin tayi ta fara tariyo kalaman nasa _Nan ta yayama zanfara define dinki ne Bri fleey yar gayu ce mai aji hankali nutsuwa gata da golden voice idan na canka daidai kina da manyan idanuwa da dogon hanci kina da dimple na ban sha'awa kina da iko da isa ga dan karen son kwanin da son asan sani Na'im yana zama raggo agaban ki kwarjinin ki ya janye nawa my Nan_ _honey you re beautifull nothing less nothing more_ _duk dama nafiki kyau amma kema naki kyaun daban ne idan zan fadi gaskiya you are beauty kina da kirki very friendly baki da matsala ko kadan gakiya ni muhammad idan na sameki zan iya cewa karshen burina kenan_ amsan da take mashi take tunowa _a ragwaye bansan wane matsayi zan baka ba gaskiya jaruntan ka akwai rauni ka bayyana kan ka_ _suffarka ko idan zan iya hasasowa zan iya cewa kai farine kyakkyawa dogo ina hasaso voice dinka zayyi zaki kamar yanda yake kyau a rubutu bazan iya cewa ina son ka da soyayya ta aure ba sabo na riga na bawa marar tsoro amma zan iya cewa ina son ganin ga koda so daya ne ahalaye nasan zaka iya zama mai isgilanci idan akayi duba ga kalaman ka zakayi iko da nuna isa son a girmamaka_ amsar da take bashi kenan shiru tayi tare da furta *NA'IM*......... Na'im tayi ta maimaitawa razananun idanuwan sa ya watsa mata cikin firgici yace "NA'IM dafa kansa yayi yana maida kansa ƙasa alokacin da yafito a bathroom yaga littafin sa a kan cinyarta meƙewa tayi ta ƙaraso gareshi har ta karkata kai zata masa magana ya hade rai tare da fige litafin sa ahannun ta "waya baki izinin shigo min ɗaki da kika dauka min litafina". ya tambaye ta da muryar da yasan zata razana "da farko de mommy ce ta turoni littafi kuma suna na nagani na bude kuma ina tuhumar ka da yin wasa da hankalina Nasir ko nace Na'im". nuna mata hanya yayi batare da yayi magana ba yace "get out from my room ya furta furucin ne ba alaman wasa a face din sa a Nasaran sa sak cikin dauriya itama ta daure fuska tace "Mommy tace na kawo maka waya".. ta karashe maganan tareda ajiye masa wayan a bed seat din sa ta juya cikin takunta na isa ta yanda zata fita da duk kan imanin sa yana kallon ta kamar ya bita ya hadiyeta yahuta sai da tafice yaji towel din da yake daure a kugun sa yana shirin kuncewa ya kallin yanayin sa ya girgiza kai yace ".Allah ya isa insha Allah zanyi aure sai kinyi mamaki sai nayi sex da matata agaban idon ki sai na tada miki hankalin da ko baza goma kikayi sex dasu bazaki gamsu ba sai kinsan a maza akwai mazaje sai kinzo ki fasa kuka a gabana akan nayi sex dake bana yafiya sai na rama kuma dole na aure ki sai kinji abinda naji sai kinji kishin da naji asanda kika kaiwa Haruna kan ki da sunan matar sa,'. sosai yaran sukaji dadin yawo dasu Hamza sunje market yamusu sayayya duk abinda yara zasu bukata irin su ball keke camera games da sauran su matan kuma teddy duna masu kyau sai dare suka zo haka masu aikin gidan suka dinga shigowa da kayan dai-dai lokacin da Nasrim ta fito dan ta shiga kichin dan daura musu abinda zasu ci amma ta gansu da takeaway niƙi_niƴi da gudu Musanat tazo ta faɗa jikin Nasrim tace "Mami munyi yawo sosai uncle Hamza ya mana sayya". murmushi Nasrim tayi tace "kun bawa su uncle din naku wahala ko my daughter balle su Zeenat masu bakin shan zaƴi " . turo maki Zeenat tayi Khaflan yace "Mami Papa ya tashi kin bashi abinci yayi maganan batare da wani jiran amsan taba ya haye sama cikin sauri dagani ya wuni da son yaga papa din na sane Nasrim ta kalli su Hamza tace "yau kunyi wunin rikici ga Musatat ga Khaflan da Zeenat basaji nasan de Abdul da Muwadda da Ummda lafiya lafiya". Umar yace "ai ko Khaflan duk yafisu daɗin zama ga hankali da saurin sabo fada ai idan basu bashi girman sa bane yakeyi ni wllh yaron ya burgeni yana da takun girma sosai". murmushi Nasrim tayi tace" wane girma zasu bashi bayan Abdul da Musanat da Muwadda duk sun girmesa dade ya tsayar da ikon sa akan kannesa Ummda da Zeenat yafi". cikin mamaki su Umar sukace wai dama sun fishi". Nasrim tace " Eh Musanat da Muwadda twins ne sun fishi Abdul ma yafishi". Hamza yace "dan Allah Aunty kar a dinga fadan hakan a gaban su wllh yana controlling din su sosai kuma idan an fashimceshi akan gaskiya yake ban taba ganin yaro da halin manya kamar saba komai nasa da banne". tabe baki Nasrim tayi tace "duk wanda zai ce halin khaflan yayi to bayyi dogon zama dashi bane yan zude dinner far dan abinci rana ma ina gani nayi asaran sa kunyi nisan kiyo gaskiya". Aliyu yace "gaskiya is okay Hajiya Aunty kema gashi keda yaya munsayo muku a binda kukafi so zabin Khaflan ne". Nasir kam bayan ya gama juye juyen sa tukun ya dauki wayan Nasrim tabe baki yayi ganin hotunan Agrif ne kala kala yana gilmawa ajikin screen akwai password a wayan sunan ta yasaka amma bai bude ba yasake saka number wayan ta yaki bude wa yasaka sunan Khaflan Zeenat Lil Agrif bai bude ba kawai sai ya daura a compute din sa atake ya nuna masa password din 4 Decembae 2018 yagani shiru yayi yana tunowa wane rana ne kode haifuwar lil Agrif ne no yace tunowa yayi ashe ranan muruwar Agrif ne numfashi ya sauke yace shine ranan da bazaki manta dashi ba kenan number Mommy yasa yayi kira kawai sai yaga tayi saving da Mommyn bayahude, murmushi yayi yana gyada kai har sanda yaji Mommy tana cewa "Nasrim yaki karba ko". "Mommy inba keba ba wanda ya isa ya damen da kira 12 miss call haba". ajiyar zuciya Mommy ta sauke na jin dadin muryar sa tace "to my dear da har zanyi ta kiran wayan ka kana cut call dina bayan Dr ya kirani yamin duk bayani amatsayin kana doctor bai kamata kayi ta shan abinda kasan zai maka illaba kasan illolin shan maganin amma kake afawa to ni ina bukatar jikoki masu yawa agaba". "dakata Mommy nafa gaya miki matsala ta kuma kina da karfi da ikon mallaka min abinda nake son kinki ya kike son nayi kinsan halinda nake ciki ne ko kuzo ku fitar min da tsohuwar bazawaran nan ko wllh komai ma yafaru wllh Mommy Khaflan ma yana son hadin mu kodan jinina ne jikin sa yabashi ina bukarar Mamin sa inaga har amafarki yayi wai an aura min Nasrim". "Nasir nakasa gane kai wane irine ita fa macce mulkin ka izzar ka duk baya ɗaɗata ita de kawai ka kula da ita amma kakasa ganewa". "Mommy har kuka nayiwa Nasrim na durkusa mata amma danaga tana neman raina min hankali kawai sai nace acikin maye nayi wllh Mommy tanada taurin kai so nikam so ya zame min guba". Mommy tace "duk taurin kan nata batayi kama ai da kabari a hakurin daka bata da yanzu tazama matar ka". "wllh Mommy bazan kwantar da kaina ba nifa duk duniya bayan ke bawanda na taba bawa hakuri amma ita nabata take raina min hankali ina rokon ta tayarda adaura mana aure tana raina ni nifa bawanda nataba roka yaban abu idan ba Allah ba bana rokon kowa sai Allah amma na roki shegiyar yarinyar nan take raina ni wllh bazan kara bata hakuri ba aurene sai na aureta dole kuma wllh sai ta gane kuren ta'". "shikenan Nasir naga ta inda za ayi auren bazawara a dole amma na haneka da kar kasake shan maganin da zai maka illah na gaya maka wllh zanyi mugun bata maka.......... da sauri ya kashe wayan tun kafin zuciya ta ingizo sa ya gaya mata maganan da zai zo yayi danasani Mommy itama ranta yayi mugun baci da halin sa awannan karan amma de abin da tasani tasan bazai sake shan maganin ba tunda ta hanashi Hamza ya ƙira Khaflan suka fita compounds ya kallin yaron yace my big boys kasan me da kaje dakin papa meyakeyi".? Khaflan yace "uncle yana waya da Mommy ne wai Mami bata son sa nifa yanzu haushin Mamin nan nakeji dama ta tafi". Hamza yace "Ah Ah kadena haka ba acewa Uwa haka Allah zai kona ka kasan abinda yasa na kiraka nasan zaka iya kaje wajen Mami kace papa yana kiranta tana shiga dakin nasa kaja komar ka kulle ta ga key din nan naciro Mami ta kwana awajen sa kaga zata kula dashi bashida lafiya jiyama mu muka kula dashi yanzu mukuma tafiya zamuyi kaga ba dadi barin marar lafiya shi daya kamata dabara kaji". Khaflan ya tafa da Hamza yace "good idea my uncle zan rufeta a ciki". Nasrim tagama shirin ta na kwanciya cikin sleeping dressa din ta mararar nauyi wanda tsayon sa ya tsaya mata iya cinya daya ke pick color ne sai ya haska skin din ta sosai tana shirin jan blacken taji anan murda handle din "Mami papa yace kizo". "yana ina"? "yana dakin sa". ya bata amsa a ta kaice tare da juyawa ya fice". "Khaflan Khaflan". tafara kiran sa amma yanuna kamar baiji ba yayi gaba dogon tsaki taja tace "ƊAN GODO". dogon shijab dinta da tayi sallah ta dauka ta daura akan sleeping dress dinta ta saka flet din takalmi da take amfani dashi a daki ta fita takun da mai wuce shida bane yake saka ka da dakin nasa daga nata Khaflan dayake leken ta a dan lungun daya dakin yana ganin shigan ta yazo yayiwa kofar key tareda barin key din ajiki ya ɗanyi karan cin na sara yafita da kudu wayen uncle Hamza yamasa bayani tafawa sukayi tare yace ''to good night su bro suna jirana a mota je ka kwanta kar ka manta da adduar". "oky thanks my uncle kaima kar ka manta da karan ta li'ilafi bayan gama Addua yana kuɓutar da bawa daga aikata shirka". Hamza girgiza kai yayi yana matukar mamakin hankali da wayon yaron ya wuce duk tubanin mai tunani Nasir yana zaune yana duba wani aiki da yazame masa dole acikin laptop din sa yana kan gado yarake wutan daki sai na bacci dayake a gefen gado yaji an murda handle an shigo kafin ya dago yaji sanyeyen kamshin ta yabigi hancin sa bai dago ba yaci gaba da aikin sa itama batayi magana ba tunda ai yaji shigowar ta kawai sai ta tsaya kallon sa adan hanken da yake gaban sa yana aikin sa kamar bai san an shigo ba azuciyarta tace Allah sarkin halitta ka halici wannan bawan naka da kyau na daukan hankali wani irin kwantaccen gashin da yake kirjin sa wanda yahade da farin fatan sa yabada wani kala na daban yanda yake baza kyawawan idon sa akan laptop din dole yatafi da imanin kowa shagala sosai tayi da kallon sa neman masu irin kyan sa take takasa tuno wanda ya kaishi gaskiya bataga lefin shiba dan yaji da kansa Allah ya masa baiwar kyau Nasir ganin sai fara shirme yake saboda kamshin turaren ta da ya gama rikita shi ya rufe laptop din ya daura akan bed seat ya dauki cup din coffee sa ya masa ya jinginu da fuskar gadon ya fara kurban coffee din sa cikin nutsuwa fuskar daure tamau Nasrim a zuciyar tace wai shi bayajin kunyar zama daga shi sai boxer ne batasan afili ta fada ba kawai sai ji tayi yace "ke kuma gaki jarababbiya ko to kwalelen ki wllh ko ciwon kai nayi ke zan kama dan dama ai maita basai ka gadaba " . ya karashe maganan yana ajiye cup din tare da jan blanket sa". "kana da daman da zaka kirani ka gaya min duk abin da kaga dama gidan kane ikon kane ina waya na idan baka da abin cewa".? wayan nata dayake kan seat ya nuna mata tana zauka ta danna screen din kawai sai taga ya canza hotunan Agrif dayake fuskan wayan ya daura na Khaflan bude wayan tayi tana shirin shi yaki buduwa an canza password din kamar zata tambaye shi amma ta fasa tayi hanyar fita tayi tayi kofa t yaƙi buduwa juyowa tayi tana gallan sa shima ita yake kallon azuciyar sa yana cewa lalle wannan tacika yar rainin hankali ta tabbara jarababbiyar ce kenan harda rufesu a ɗaki "zo ka budin min". tace a ta kaice "ni nashigo dake ko ni narufe". yace cikin zafin sa dan yafara kosawa da ganin ta a gaban sa dan yasan ba zai iya control din kansa ba". cikin sanyi murya tace

Chapter 36 of 40