? Please just let me know tell me what is going on".?
Numfasawa tayi tace". gaskiya ne ina cikin damuwa dan ji nake zuciyata ba daɗi".
"Ayyah Dr .dama yanzu ai kina matakin da zakiji kowane irin sauyi tunda kina tare da 3brother's kinga ko nida Abdulraham ba halin mu daya ba haka Abdulmajid ma halin sa da ban dole kiji ban banci a kulum".
murmushi tayi "tace kama bani 3 nima kenan?".
yace "haka nake fata kinga kin cike gurbin shekara 7 da mukayi ko?"
Murmushi tayi ta ce" abinda yafi bani tsoro Nasir ya gaya min wai ka nuna masa PIN ɗin laptop dinka yanda zai sararrafa ta sannan kanuna masa yanda zayyi amfani da agogon ka wajen gano me dukkan company ɗinka suke ciki bayan da ko bathroom zaka shiga baka cire agogon ka amma yanzu sai naga agogon ka a ƙatsan filo shine son yake cewa wai ka koya masa anya lafiya kuwa?"
"cikin sanyi yace lafiya ina son Nasiru yasan sirrina ne ta yanda koda bani bazaku sha wahala ba ke da shi".
cikin damuwa tace "ai kaji irin abin da yake sawa nake shiga damuwa yanzu Nasiru har ya kai wannan matakin bayan ga yan uwan ka su yakamata su sani Nasiru yarone bazai iya rik'e sirri ba"?.
Numfasawa yayi yace" ki daina damuwa Fatima na ba komai NASURUDDEEN kuma nasan halinsa duk da yaro ne yasan abinda yakeyi, Sam ƙwaƙwalwar sa bana yara bane zai iya riƙe sirri sosai,
yan uwa na kuma ɗan cikina ya fisu can-canta yasan sirri na tunda inada ɗa shi ne magaji na ba su ba."
cikin sanyin murga tace "Allah ya dawo dakai lafiya."
"Ameen yarabbi my dear kar ki damu I love you".
yace daga nan sukaci gaba da fira jikin su a sanyaye musamman Dr. Fanna dan wasu daga cikin furucin sa kamar yana bar mata wasiya
ne har sukayi sallama.
daga nan ya kashe wayar ma gabaɗaya yana cewa driver yasa masa wa'azin Dr. mansur sokoto suna cikin sauraron wa'azin ne
dai dai zasu shiga kwanar Dardum motar man fetur ne a gaban su, sai wata mota da take bayansu ta danno overtaken da shirin shiga tsakanin su da motar man amma wajen bai isa ba sanadin da yasa motan ta haɗe dana man kenan atake motan man fetur ɗin yaf ashe yana fashewa man yayi wani irin tashin wuta yafara bulbulowa wanda hatta motar Alhaji Abdulsamad da ya liƙe da jikin daya motan bai tsira ba cikin second 5 wuta yayi wani irin mamaye wajen wanda har motan bayan Abdulsamad ya kama
nan da nan motoci suka dinga ja da baya wani irin tashi wutan yake wanda ba wanda ya isa ya tunkare sa ahaka mutane suka ƙone, motocin nan guda 4 sukayi ƙurmus amma motan da bodyguard ɗin Alhaji Abdulsamad suke sun tsira kasan cewar wannan wanda ya hassada Accident shiga tsakanin su yayi, lokaci daya har direban bodyguard zai fara faɗa sai kuma abin ya afku ashe de ƙaran kwana ne cikin razana su Usman suke kiran Sir amma ba daman tunkaran wutan nan
Wayyo mommy ya zataji da wannan mummunar labarin ƙaddarah kenan Hajja abdulmajid, Abdulraham
*NASURUDDEEN*
*Ku biyoni a page3*
*B JATTKO*
[4/8, 1:46 PM] Batul Adam Jattako: *FURRUCI NA NE*
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURRUCI NA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*fatan alkairi gareki HAUWAU USMAN JIDDA jiddota Allah ya sa kaffara ce*
*Page3*
Bayan mutuwar wutan dak'er Jami an tsaro suka samu nasaran fito da kawawwakin su Alhaji Abdulsamad da aka gane wanne ne shi kasan cewar akwai escorts biyu a seat din baya Alhaji shine a tsak'iya sai direba da wani escort din agaba su 5 ne a motar
ba tare da bata lokaci basu Usman suka nemi abasu gawar wakin su tare da rakiyar yan sanda su ka kama hanyar Kano
jin jiniyar ambulances a cikin gidan ba k'aramin rikita mutanen gidan yayi ba a compound din hajja a ka kantar da gawar wakin
arikice Laure tashiga tana ihu
"hajja kifito kiga k'addaran data fado gidan nan yau".
Hajja da tun da taji jiniyar ta kasa mek'ewa bakin ta yana furta Abdulraham ne ko Abdulmajid ko Abdulsamad yau me idanuwa da kunnu wana zasu jiye min Allah kar kasa naga gawan daya daga cikin su nafison su subinne ni bazan iya daukan wannan k'addaran ba!!!!!
Laure waye kar kicemin ABDULsamadu nane
Mommy da taje tsaye ajikin window kamar an dasata komai ya tsaya mata kawai kallon gawar da aka ware gefe take amma tabbar na mijinta ne ta tana kallo Hajja dasu Mama suka fito suna kuka suna fisge fisge amma ita ko d'aga lebinta ta kasa wani irin jiri dushu take gani ita bata zube ba ita bata fadi ba kanta da gan-gan jikinta ta zura ta window zata fado ta saman benin da sauri Khadijan me aikin ta ta tareta tana kwallah wa asabe me aiki Kira tare suka kama mommy da ba tama suma janta sukayi suka kantar a k'asa suma suna cigaba da kukan cikin k'an kanin lokacin babban rashin Alhaji Abdulsamad ya mamaye Kano da duniya baki daya
a islamiyar su Nasir mlm Hasan ne yashigo yace "an arufe makaranta yau sai zuwa jibi insha Allah saka makon babban rashin da akayi na wanda ya bude makarantar wato Alhaji Abdulsamad a gobe za ayi Jana'izar da misalin 8 na safen gobe Allah yaji k'ansa halayensa na gari su.....
ai Kamal da Agrif basu gama jiba suka sa ihon kuka shiko Nasir shiru yayi yana tunani wai mutuwa da yaji anacewa idan anyi ta shikenan ba a dawowa Abban sa yayi wani irin zabura yayi waje yayi da gudu bodyguard din sa suka bishi amma basu kama shiba kasancewar bawani nisa tsakalin gidan da makarantar duk girman gidan amma yacika dan k'am dak'er yake gurtsawa yana faduwa yana tashi a lokacin har anzaga da kawar baya inda za a musu wanka falon Hajja ya nufa nan ma cike yake da
mata ana ta bawa Hajja hakuri sai mai maita Allahumma gafurni wal'hamni take Mama ce tafara hangoshi kuka tasa Hajja mata d'aga kai ta kalleshi tamek'o masa hannu da gudu ya k'arasa rungume sa tayi ta saki kuka "Muhammad Nasir shikenan ka tabbata MARAYAN da yarasa uwa da uba ya Allah ka rayamin wannan yaron shikenan shikenan Nasuru har abadan muda Abdulsamad".
"Hajja wai Abba na yamutu?
"Nasuru hakuri zamuyi "
cikin kukan da kamar ba d'an shekara bakwai ba yace
" dama sai da nacewa Abba kar yatafi". kowa kukan yake an rasa me lallashin wani
Hajja ta kalli Ummu tace"Amina ina Fanna".?
cikin kuka Ummu tace"anyi anyi bata farfado ba Dr Hafsa ta wuce da ita asbiti".
aiko Nasir yasa kukan shide akaishi wajen mommyn sa kar itama ta mutu
Allah sarki Abdulmajid yarasa inda zai sa ransa iya dauriya yayi amma yakasa saide Abu yafishi shiga damuwa dan shi acikin jirgi sai suma yake ana shafa masa ruwa dan suna Lagos sai 5 jirgin London din zai tashi wannan labarin ya riskeshi
Abdulraham yana zuwa gun Hajja ya wuce ya bada cinyar ta cikin kuka yace "Hajja ya zamuyi ya zamuyi shima Abdulmajid sai a sannan yaji kuka yazo masa duk suka rungume ta suna kuka Abdulmajid yace "Yarabbi muna son d'an uwan mu amma ka dauke mana shi alokacin da bamu zata ba Allah kasaka mana dauriyar da dangana".
Abdulraham yace "Allah bazai daurawa bawan sa abinda bazai iya ba Allah yana turo dangana tun kafin mutuwar tazo Allah ka yafewa Abdulsamad".
ya mek'e tareda d'an uwan sa
K'iran sallan magari ba akayi bayan anyi sallah aka sake sanar da mutane ayi hakuri a tafi tunda Jana'izar sai gobe sai yan uwa wanda yakama aka bari
Abdulraham da Abdulmajid cikin dauriya suka wanki d'an uwan su da kansu bayan sallar ishai ba wanda yasamu daman rinsawa hatta Abbaty dan shekara 3 shiko Nasir yana asbiti wajen mommyn sa cikin dare mommy ta barka idon ta akan Nasir da ya damk'e mata hannu yana gengedi a hankali tasa hannu ta kwantar da kanshi afirgice ya bude ido yana cewa "mommy kita shi".?
murmushi tayi masa tace" my son meyasa kayi kuka haka?".
tayi maganar tana shafa masa gefen fuskar da jijiyar sukayi rudu'rudu da gani ba k'aramin kuka yasha ba
"Mommy ba Abba ne yamutu ba kema zaki mutum shikenan bani da Baba bani da Mama".
d'ago kansa tayi tana kallon sa tace "Nasir bazan mutu ba Allah bazai kasheni ba ko dan saboda kai zan rayu da kai sai na dauki y'a y'an ka awannan hannu nawa ta k'arashe maganan nata tana nuna masa hannu ta
Dr Hafsa tace "am sorry Dr Fanna kiyi kakuri kisa dan gana acikin zuciyar ki mutuwa de d'aya ce kowa zaman jiran sa yake babba ko yaro duk wanda wa'adin sa yazo kisa dangana ko dan abinda yake cikin ki duk dama yanzu ba bak'aramin barazana ya samu ba dan Allah kiyi hakuri kar ki rasa abinda yake cikin ki shine k'adai son da zaki nunawa Abdulsamad ki Haifa masa abin da yabari".
Mommy shafa cikin ta tayi tace'' Dr hafsa cikina bai zube ba".?
"Eh bai zube ba".
Mommy tace'' Alhamdulillah zan kula in sha Allah nasan Abdulsamad zayyi farin ciki dan rushin sa yatafi da farin cikin wannan abinda yake ciki na Allah ka yafewa mijina isha Allah zan Haifa maka abinda yake cikina".
Amma kuka kam ta kasa yinsa sai wani irin radadi da zuciya ta yake mata
tace'' Dr ki cire min ruwan nan zan tafi naga Abdulsamad".
numfasawa Dr tayi tace'' k'awata bawai ba nason kije bane zan so ki masa addua amma bana son hankalin ki ya tashi ne".
"hankali na zaifi kwanciya agida ba anan ba Dr".
haka Dr hafsa da Dr Farda suka dafa mommy suka shiga da ita zaunar da ita sukayi a kusa da Hajja sabon kuka mutane wajen suka sake sawa ita ko mommy masu kukan sha'awa suke bata dan ita tama kasa kukan sai wani irin ajiyar zuciya take sauk'e wa
Dr Hafsat tace Hajiya dan Allah kudena wannan kukan kwantar mata da hankali yaka mata ayi ahalin da take ciki akwai barazana da abinda yake cikin ta da sauri duk suka kalle ta Hajja tace "ciki kuma!?.
Dr Hafsat tace "eh ai tana da ciki wata 2 dan Allah abata kulawa Hajja amdala tayi har su Abdulmajid
2
Allahu akbar mutuwa me yake jin dadi me raba d'a da mahaifi me sa mata zawarcin dole a hannu mukazo ahannu zamu koma ba a kauce masa duk kudin ka duk da baran ka mutuwa bata barin ku dubi yan da Abdulsamad yayi FURRUCIN yana da matakan kariya a motar sa Wanda bazai tabayin hatsari ba kuma Koda yayi ko gwarzani ba zayyi ba saboda matakan kariya amma sai gashi motar tazama sanadin sa yau da ana sayan rai Abdulsamad yana da kudin da za a tsaya masa rai ko da dubu ne amma sai gashi a hannu an d'agashi za afita dashi
Malama Shamsiya ce take ta nasiyar kada amasa rakiyar kuka haka suna ji suna gani aka fita dashi abokan sa daga k'asashen duniya irin su Albaity Abdallah Amar da shugaban k'asashe da dama har akayi sadan kan bakwai
amma bak'i kamar k'arosu ake wasu suna tafiya wasu na shigowa tsabar amsa gaisuwa yasa mutanen gidan muryar su dashewa sai de maganan kurame Abdulraham da Abdulmajid ko sai de su rubuta idan suna sonyin magana
suko yaran har sun fara mantawa dayake dama Abba ba mazauni bane bawani shak'uwa a tsakanin su dan haka jisu ke kamar yayi tafiya ne
*bayan wata daya*
munane kam sun watse sai jifa-jifa yan gaisuwa ganin yanda mommy take cikin damuwa yasa Hajja tace mata ta taro tazo part dinta su sauna breakfast suke kowa yana cin abinci banda mommy da ruwan tea kawai take hadawa me kauri tana sha
Abdulmajid da yazuba mata ido ne yace "Doctor please tabbas kinyi hakurin juriya amma dan Allah ki sake daurewa ki rungumi k'addaran da Allah ya d'aura mana ayanzu addua kawai brother yake da buk'a awajen mu mukuma abinda yake cikin ki shine buk'a tarmu hakan bazai samu ba sai kin kwantar da hankalin ki damuwa da kuka dazai dawo dashi da ko kwana bazayyi acikin kabari ba"
Abu ma yace "hakane dukkan mu bawanda baya cikin damuwa amma mun sani bazai dawo ba mu fuskanci rayuwa tare dayi masa fatan dacewa...
shiru yayi dan shima kukan ne yake son kufce masa ganin
Mommy ta sun kuyar da kai hawaye yana ta diga akan dining table din suma su Ummu kukan sukeyi
Hajja cikin kuka tace " ai kuka nidashi har tawa tazo Abdulsamad nefa wai babu shi yayi tafiyar da ba wowa yatafin inda Haruna yatafi".
sai tasake k'ara karfin kukan nata haka de wannan ahalin suka kasance cikin damuwa cikin mommy wani irin girma da nauyi yakeyi tun yana da wata hudu tayi scanning anan tasan yara ukku ne kuma duk maza ta dage sosai da kula da cikin duk da takasa cire damuwar da yake cikin ranta wanda ko wane irin abinci kawai cinsa take kamar magani yawanci drip take sawa kanta sai kuka abu medan ruwa-ruwa
*bayan wata 4*
Mommy ta shiga watan haifuwa suna zaune ita da Hajja a compound Hajja ta na bare mata gyada tana bata Mama tana mammatse mata kafar ta dayake a kumbure Hajja ta kalleta cikin tausayawa tace"niko Fanna cikin nan naki me secangin ya nuna dan ba daya bane gaskiya a yanda yarabu gida biyun nan kuma kashi har kin kusa fita awata na goma".
shiru tayi tana tunanin bai kamata ta boye musu ba
tace'' yanuna yara ukku ne."
amma batace maza bane".
salati Hajja tayi cikin hamdala da washe bakin da tunda Abdulsamad ya mutu batayi ba tace "kuma kikayi shiru abinki wannan abin al'kairin haka Allah mun gode maka kai din abin godiya ne ako da yaushe ka kwace Abdulsamad ka musanya mana da har guda ukku Alhamdulillah yaushe ne
EDD naki?".
Mommy tace'' tun jiya yacika kuma tun ajiyan na fara alamun labor amma bawani matsala in sha Allah zuwa shida na yamma zan iya haifuwa".
azabure Hajja tace'' wai ni keko wannan Fannan wace iriyar macece wane irin zurfin ciki Allah yabaki yanzu haka nak'uda kike kike zaune haka"?.
Mommy murmushi tayi tace" ai Hajja bana jin wani ciwo kuma ai ina tashi nadan zaga abinde ina ga da sauki zai zo mun dama yawanci haifuwar yan biyu ko ukku ba ciwo kamar na daya yawanci daya yafi ciwo sabo da mutum yagama ciye ciwon a goyon cikin su bawani damuwa nakira Dr Hafsa ma nace idan ta tashi tabiyo tanan bawani damuwa dan ba sai munje hospital bama In Sha Allah".
" Hajja tace'' kuma fa hakane nima Abdulsamad banyi nak'uda ba ina jan rijiya naji marata tayi nauyi nishi yana zuwa min ina tsugunnawa Abdulsamad yana fadowa amma Abdulraham da Abdulmajid nayi nak'uda har Sai da muka je asbiti Allah de yakawo miki da sauk'i ya raba lafiya".
Mama cikin mamaki take kallon mommy ta ma kasa magana
can tace'' sannu mommy Allah yaraba lafiya ko da wani abinda zan iya temaka miki"?.
Mommy tace''a a hajiya Mama karki damu".
Mama tace'' to bari naje na sanarwa da Ummu wannan abin farin cikin yara har ukku".?
Hajja tana kula da duk motsin mommy ba jimawa Dr hafsa ta k'araso mommy har lokacin ciwon bai wani dameta sosai duk da dauriya yarta yafi yawa part din Hajja suka wuce tana tafiya dak'er da misalin k'arfe biyar darabi mommy ta haifo yaranta ukku wanda tsakanin su bawani b'ata lokaci murna awajen hajja da mutan gidan Abu da Daddy ma suna gidan bayan an waki yaran Abu da Daddy suka shiga suka dauki yaran daddy yace"sannu Fanna Allah yabaki lafiyar shayar dasu Abu ya dauki babban yamasa K'iran sallan tareda huduba ya mekawa Hajja yace "gashi sunan sa Abdulsamad yasake karban me binsa bayan yamasa yamek'awa Mama yace sunan sa Abdulraham dayan ma yace Abdulmajid Ummu tana juya Abdulmajid da yake hannuta tace "ni yaron nan kamar bashida cikekken lafiya Dr Hafsa tace'' nima abinda zance kenan daga yanayin kukan suma zaka gane duk ba suda cikekken lafiya amma bari mukira doctor Yusuf likitan yara tayi maganan tana zaro wayanta ajaka bayan doctor Yusuf yazo yaduba su yace gaskiya basuda lafiya dole za akai su hospital dan su samu kulawa ta musamman abin tausayi yaran duk wani irin kuka suke haka aka tar katasu zuwa asbiti,
Nasir suna zuwa a islamiya sukaji mommy ta haifu amma duk yan gidan suna asbitin sai Ummu kadai aka bari agida rigima suka sa mata dole tasa driver yakaisu
Nasuru sai murna suke da suka ga jarirai har ukku suka sa rigima sai da akabawa kowa d'ai d'ai Kamal yace "la ni mekama dani aka bani Agrif ma yace nima muna kama da wannan Nasir yace"dalla ai su ba bak'ake bane kamar ku kamar nida mommy na sukayi dukkan su dariya akasa na hannu Nasir yafara kuka Kamal yace "woo kaga baya sonka yana maka kuka".
Mama tace'' "to duk ku kawo su basu da lafiya idan sun warke kowa shi zai na renon nashi".
da dare yayi kowa ya watse anbar Hajja da mommy anyi anyi da Nasir ya tafi gida yak'i sai zazza gawa
"Mommy surutu yake akan murnan samun k'anne ita ko bin sa take da eh ko a a dan da abubun da suke damun ta sosai shima Nasir yarin tane
''yawwa mommy ai da safe kince yaune birthday dina na cika shekara 8 ko".?
Tace'' "Eh my sweet boy amma bazamuyi party ba saboda gaka ba ayi shekara da rasuwar Abba ba amma nex insha Allah sai amuku kai da k'annen ka ga a lokacin kai kana shekara 9 su kuma 1 Allah ya hada birthday dinku har lokacin haifuwar ba kusan dayane da mintuna kawai ka zuce su zan shirya muk......
shiru tayi gani yanda babban d'an yake ta wani irin hamma addua tafara tofa masa ahankali yake hamman har ya rufe bakin sa shafashi tayi tako ina taji baya numfashi ajiyar zuciya ta sauke taja ta rufeshi tana kokarin mayar da hawayen idon ta dan kar Nasir yagani sai karamin cikin su yasa kuka daukan sa tayi tana diga masa ruwan zam-zam amma baya iya hadiya sai dawo dashi yake da asuba shima yabi dan uwan sa sakin wani irin kukan tausayin kanta tayi tana shafa dayan da shima numfashi sa yake fita ahankali shima ba alamun zai rayu cikin kuka tace'' yarabbi na gode maka da wannan jarrabawan da kamin da safe kam su hajja sunsha kuka dan mutuwan jaririn ya sabon ta musu da rashi Abdulsamad daga su har likitaci kuma kulawar su yakoma kan Abdulmajid jaririn da yarage amma ayanmacin ranan shima yabi yan uwan sa mommy kam kowa yagan ta yasan tana cikin tashin hankali bayan watanni ukku Hajja tace'' tabara fita aiki koda campany shikafar ta ne dan tasamu sauki idan tana fita aiki zata rage wasu damuwar hakan ko akayi ta fara fita aiki sosai tafara cakewa da aikin ga company yana samun cigaba sosai har fiye da da anan fa maza suka fara mata ca har samari ba wanda take kulawa dan atunanin ta kawai dukiyar ta suke hari ba ita ba
*Bayan shekara daya*
yanzu kam komai ya dedeta kowa yayi kokarin dawo da walwalan sa saide mommy dannewa kawai take bata da abin farin ciki sai Nasir shi kadai take gani taji dadi yau ma birthday party dinsa ake har dare ana ta ciye-ciye Nasir yaro dan shekara tara amma dayake yana da tsawon kafa za azata masa fin haka
a dare ranan mommy han tayi shirin kwanciya taji ana mata knocking murmushi tayi afili tace "kai my Son tea dinka ko duk wannan ciye-ciye amma baza ka kwan ta ba sai kasha tayi maganan tana mek'ewa amma sai taga Hajja ce cikin sauri taja shijabinta ta saka tana cewa
"Hajja da kan ki ai dakin ce nazo".
Hajja ma murmushi tayi tace'' a a zuwan nawane me musihmmanci Fanna magana nake son muyi na fashimtar juna game da mazan da suka miki ca duk da nasan ba kyason maganan amma yazama dole dan kedin yarinya ce idan muka zuba ido kika zauna an shiga hakkin k'uruciyar ki Sarai ina sane da yanda maza suka takuraki har da abokan mijin ki to gaskiya a ganina yawancin sufa bake suke soba dukiyar da yake hannuki suke hari dan duniya ta gama sanin kaso 80 daga cikin dukiyar Alhaji naki ne duk da ba raba gado akayi ba ansan idan aka raba dole za acire kason yaran ki maza har ukku da suka rasu kuma ga tumilin takaban ki ma dayawa ne sai nida Nasuru Wanda baifi kaso 20 ba aci da zamu samu tabbas bazaki gane waye yake sonki da gaskiya ba to bawai bana son ki aure wani bane a a Fanna ina gudu kawo wani b'arakan ne ayanda gidan nan ya ginu da son juna da kwanciyar hankali da zumunci ba zamu so bare ya shigo ba shiyasa muka zauna muka yanke shawaran zamu nemi alfarma a wajen ki duk da muyi da yaran agobe zamu tunkare ki amma naga yana da kyau nafara jin ta bakin ki nida yaran nan mun yanke shawaran zaki auri daya daga cikin su dan gujewa wannan matsalolin da zamu iya shiga idan kika auri bare".
da sauri mommy ta d'ago kai tana kallon hajja
hajja taci gaba "amma idan hakan bai miki ba abar zancen".
cikin karyewar muryar mommy tace'' Hajja kamar yanda bani da kowa sai ku haka bani da wani zafin da zan bijirewa shawaran ki ni ina daukar kine a matsayi uwa mahaifiya umarnin kawai zaki bani ba shawara ba".
Hajja rungume mommy tayi tasa kuka tana sa mata albarka
tace'' kuma Abdulmajid ne fara nuna ra'ayin hakan cikin kwana kin nan yayi mugun takurani akan na fada miki tunda yaga alh Yahaya yazo da batun yana son ki ya gigice abinda na fuskanta Abdulmajid yana sonki sosai son da banajin ko marigayi yana miki shi
kuma Abdulraham ma da muka gaya masa yayi murna da abin sosai".
dasafe bayan an gama breakfast hajja tace'' tana sonyin magana dasu a main parlour bayan yara sun tafi makaranta Hajja ta umarci Abu da yabude taro da addua cikin shikima tayi musu bayanin abinda yake faruwa da kuma amincewar Fanna
da sauri mommy ta d'aga kai ta kalli Mama sai taga murmushi take ita tafara cewa "Alhamdulillah Hajja hakan shine dai-dai dama muma baza muji dadi ba idan a kace yau mommy ta fita acikin mu insha Allah zanci gaba da daukan mommy amatsayin tana yar uwata kamar da Allah yabamu zaman lafiya".?
Ameen sukace dukkan su suna murmushi Hajja tace'' ai Aisha dama nasan bakida matsala balle Fanna Allah yamuku albarka kuma zan kafa na tsare muku daga kuba k'ari.'
ta k'arashe maganan cikin raha
Ummu tayi saurin cewa "Yawwa hajiyarmu mun gode Allah yabar manake".
Hajja tace'' bar saurin godiya kema sai yayi biyun eshe".
tak'arashe maganan tana ged'a kai
duk murmushin sukayi banda mommy data sunkuyar da kai
bayan mazan sun fita Hajja mata tashi ta haura sama dan gabatar da walha Ummu ma tace " bara naje zanyi bak'i ta tashi takoma part din daga mommy sai Mama awajen ganin yanda mommy ta kasa sakewa ne yasa Mama ta mek'e ta koma inda take kamo hannan ta tayi cikin sanyi murya
tace'' mommy dan Allah kar kisa wani abu aranki inde tani ce ba damuwa ni tunkafi Abdulmajid ya aureni ya gaya min cewa bashi da ra ayin zama da mace daya saboda yana son yara dayawa dan dun kafin nashigo nasan ba ni daya bace
kuma dadin da dawa ma a haifuwar bari
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 40