Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne kawai ya kai ta part din su Kamal tana cewa ya Kamal sun mutu da gaske ne!!! dan Allah ya Kamal me yake faruwa Kamal da yake zaune a parlou da carbi hannu agaban sa tazube summemiya a gigice yace " suwaye suka mutu jin k'aran Kamal yasa Humairah fitowa da sauri Kamal yace " yau me zamu gani Nasrim kashe San kikayi da kugu Humairah da Kamal suka fita direct bedroom din Agrif Kamal yayi kanin halin da yake yasa ya fasa wani gigitaccen k'ara yayi waje da gudu haka Humairah ma Mai ai'kin Humairah ne suka sanar wa mutanen gidan dan Humairah wuk'a ta dauko tana ta faman sumbatun itama sai ta kashe Nasrim tunda takashe mata Dan uwa itako Nasrim asume ma take bata masan me take ba duk masu ai'kin Humairah suke rike Humairah gaba daya gida ya rikice tun ba asan mutuwar su Fayyat ba mommy ce ta gano basu awajen tashi tayi ta shiga dakin fitowa tayi tana nuna d'akin da yatsa tana cewa "ku shiga nan kuga". Khafulan sai da yaji muryar su Abbaty ya bude kofar yana cewa" wllh mamy ce mamyn muce ta kashe su kafin kace me har yan sanda sunzo Nasrim da take cikin wani hali suka dauka zasu saka amota mommy ta rik'e ta gem tana kuka "wllh ba Nasrim bace wannan wani mak'ircin ne aka kulla mana wllh Nasrim baza a iya kashe mijin ta da yaran ta ba" . Hajja tace'' idan ba ita ba waye ba gashi Khafulan ya fada ba kuma jiya agaban kowa tace sai ta kashe daya acikin ukku tace rigiman duniya dame rai akeyi ". cikin kuka me tsanani mommy tace "abin ya hau kan *FURRUCI TA NE* Khafulan yace "wllh mommy itace da wannan kayan na jikin ta ta shigo ni ina batdroom zanfito na ganta tana kashe su har na mata video kashi nan ma dama papa yace duk abin da zatayi na mata video ". yan sanda ne suka karbi wayan hannun Khafulan suka hada Nasrim suka fita da ita mommy tana kuka tace'' na sani duk mak'irci ne wallahi wallahi inde Ina raye kuma kudi suna magani a duniya Nasrim ko furzin ba zatayi ba ........ *Tofa masoya sai kunyi hakuri fa dama sunan litafin rikicin babban gida nasan pg yau zai ba k'anta ranku kamar yanda nima yau dag'er nake typing amma ya muka iya wannan shine jigon labarin* *Dan Allah kuyi hakuri rashin yawan typing dalilin wani uzzu'a nagode sosai da comment din ku Allah yabar kauna* Bj S&R kayan Mata Assalamu Alaikum shin Kuna da labarin S and R kayan mata, Kaya masu inganci da sauki daga sokoto Sai angwada akan San na kwarai, Muna da Gumba, Gumbar Aya, Gumbar nonon rakumi, Gumba aya, kwakwa da dabino, Gumbar mallaka, akwai kaska, ko kurma ne, Issasar mace, tsimin maqale mata, tsimin ridi, tsimin dabino, Dahuwar kaza, Dahuwar tantabaru 'yanshila da sauransu, Muna aika Kaya a duk inda mutum yake. Distance is not a barrier. Wallahi duk macen da bata gyara kanta tana tare da ganin bacin rai gun mijinta, Hajiya ki cire komai kike ji ki gyara kanki, gyara shine mace, gyara gaskiya ne, mudai mun gyara Kuma mun gani. Akwai da yawa matan da kullum zakaji basu da matsala Sai ta miji da ya shiga ya kawo some ko 2 minutes basayi🙈🙈hajiya wallahi hada rashin gyara na Kara haddasa wannan matsalar ki Sayi Kaya kiyi amfani dasu ke da kanki Zaki bada labari . 07014149410 S and R kayan Mata Sai na jiku. [4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE* (```Rikicin Babban Gida```) *NA* *BATUL ADAM JATTKO* ```Marubuciyar``` *DAMA TA* *AMFANIN SOYAYYA* ```NOW``` *FURUCI NA NE* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* *15* Mommy bin motan take tana rusa kukan ita akwawo mata y'arta walahi Nasrim tafi k'arfin shiga motan Police tana binsu har kusan babban get tana faduwa tana tashi Barira da mainunau masu ai'kin ta ne suka rik'eta suna ta kuka mainunau tace ''dan Allah mommy kar ki bisu a haka ki bar Adamu yakai ki a mota Allah yana ji yana gani da k'er suke rike ta Allah sarki mommy sai sunbatu take tayi tayi da hausa tayi da turanci tayi da barbarci tayi da asalin yarenta na ibo Barira ce tafito da waya ta kira Dr Hafsa ta mata baya yanda zata iya Har ambulances na asbitin yazo tafiya da gawar wakin dan ayi musu gwaji daga mutane gidan har ma'aikatan gidan bame ko bakin kuka gaba daya an hargitse suna gani aka dauki su Khafulan da Agrif aka fita dasu itako Ummu jitake ba awannan duniyar take ba gaba daya kwakwalwar ta takasa daukan abin Hajja tace'' inna'lillahi wannan wacece iriyar musifa Allah ya tsaukar a gidan nan bana zaton ko a tashin duniya zamu shiga cikin irin wannan yanayin Abdulmajid me ka haifa mana irin zuciyar kafurai ko ashe kwara da Allah yakashe yara ukku maza da wannan dangin kafuran ta Haifa ashe ba al'kairi bane da sun rayu ba gashi k'anwar su mace ma tayi haka da suna nan da duk sun kashe mu me yasa baki kashe iya yaran ki ba dan kirage mana mugun iri kika kashe Haruna da baiji ba bai gani ba nifa dama wllh ba wani gamsuwa nayi da wannan Fanna din ba kawai dan naga Abdulsamad yana sonta ne nabari ya shigo mana da ita cikin zuri'a mu........... Kamal yace " Hajja ki dena fadan haka baki da wani hujjan da zaki daurawa Nasrim al'hakin kisan nan Nasrim bazata taba iya kisan kai ba musamman yaran ta idan ta kashe Agrif saboda kishi to yaran ta fa?". "haba Baba na rashin Ima'ni mana bakasan marar Ima'ni kansa ma sai ya kashe ai irin kafurai ce ba bakaji abin da ita kafuran uwar ta tace ba wai ko duk dukiyar da ta tara zai k'are yarta Ko person bazatayi ba ni kuma na dau alk'awarin tare za a jera gawan su a kabari daya ita dasu Haruna .... jin rin wannan kalaman na Hajja yasa Barira da maimuna suka janye mommy da bata ma cikin hankalin ta zuwa compound dinta suna ta tofa mata duk adduar da tazo bakin su har dr Hafsa tazo ita dawata k'anwar ta da yarinyar ta Amira k'awar su Nasrim ce matar Aliyu abokin Nasir Allah mai iko dubi yanda cikin k'an'k'anin lokacin wannan ahalin sun koma kamar basu taba farin ciki a duniya ba tun ba afi 30 minutes da yin abin har abu yazaga duniya abun ka da gidan da dama ansan sa a duniya duk wani kafa na labaru da social Media da duk wani kafafun yada labarai ba idda zance bai jeba duk inda kashiga a Media to hotunan su da bayanan sune duk da haka wai Kamal yasa masu gadi sun hana kowane yan jarida ahigowa yan uwa ma idan ba najikin 3A full bane sosai to ba kowa ne yake samu yashigo ba *Dubai* Aliyu ne yafara gani a fece book cikin dabara yakira gida aka tabbatar masa da gaskiya ne cikin dabara ya kwace wayoyn Nasir ya kashe wayayoyin ya samesa akwance zama yayi abakin gadon yace "yade my friend yanzu ba lokacin kwanciyar ka bane yau duk na ganka wani iri very slowly kode aikin ne". juyi Nasir yayi yana yamutsa fuska yace " gabana yana faduwa kuma kasan me misani 1 pm naga kiran Khafulan ba adadi atunanin na sunyi abinda suka sabane shida Fayyat amma da na kwanta nake ta mafarkin yaran abin ba dadi kuma kasan wayan su games ne ba waya bane basu kai rike waya ba nasa anyi setting na yanda nida A A. kawai wayan zata iya k'ira da nayi mafarkin nayi da K'iran number A'A baya picking Khafulan kuma ba daman na kirashi saide shi ya kira na kira Kamal mommy da Abu da daddy duk bawanda yayi picking". Aliyu yace'' inaga basu tashi bane amma ai kaima yanzu zakaje 9j din nagama shirya mana kaya har wayoyinka na kashe nabawa P'A danmu samu mu shiryar dawuri jet na jiran mu tashi mutafi". "Nigeria kuma kasan me kake cewa Ali". Aliyu yace'' Eh zanyi surprise din Ameera ne yanzu muka gama waya da ita take cewa wai ni Inata maka bauta amma da zannemi alfarman lokaci daya baza ka iya min ba sai nace meye alfarman sai tace tana son ganina yanzu idan na isa kuma tana da matsayi shine ni kuma naci mata alwashin bani ba har kaima yau breakfast din mu yana hannun ta dan Allah sir kar ka nuna ban isa da kai ba kamin wannan alfarman mutafi yanzu". tsaki yaja yace " bani da wani lokacin b'atawa akan wata macce kude da kuka daurawa kanku kuje kuyi tayi wancen shegen ma daga zuwa aikin da baifi na 1 week ba yace dole sai 1 months zayyi kuka duk kan macce ne nasani". ajiyar zuciya Aliyu ya sak'e azuciyar sa yace inda kasan halinda yake ciki da bazaka ce haka ba Afili kuma yace" to ai rayuwar duniya sai da mata shi kansa neman dan suwa mukeyi yanzu de zan samu wannan alfarman"?. tattare fuska yayi yana mek'ewa yace " ba dole na ba inde ina son amin aiki da nusuwa bayi mata kawa". "Thanks so much my friend". ko ajirgi a zaton Aliyu Nasir zai nemi wayan sa amma ina ko tambaya bayyi ba kawai wantar da kansa yayi akan kujera tare da lumshe ido ya sauk'e numfashin a hankali Nigeria Bayan sauk'an su Nasir amamakince yake min mutanen da suke tare tun farkon layin su da kallo wanda dole su suka sauk'a dan mota bazai shoga ba amma dayake bashida kuzarin da zayi wani masifa kawai sai ya sauka tabbas agidan sune amma to meyake faruwa". yayi maganan afilli hannun sa Aliyu ya sake damkewa yace "sorry MUHAMMAD mushiga ciki ko". dak'er suke kur tsawa har suka samu nasaran k'arasawa wajen get din masu gadin suna ganin Nasara suka bude kofar ya shiga da d'ai-d'ai yake kallon mutanen gidan Wanda su Hajja ma har yanzu suna compound duk ana waje a zaune a k'asa Hajja ce kawai take kukan da bama fitowa yake ba muryar ta yagama dashewa Ummu ko tuni ta suma anyi asbiti da ita yana jefa idon sa kofar part din mommy yagan ta kwance sai faman shafa mata ruwa ake ahankali yake takawa gaban sa yana faduwa ya k'arasa wajen mommyn zuba gwaiwogin sa yayi a k'asa lips din sa narawa yace "mommy meyake faduwa"""? Mommy jin murya Nasir yasa tayi saurin mude idon ta kamo hannun Nasir ta damke cikin wahalallen murya tace'' sun tafi da ita Nasuru zasu kashe min y'ata zasu kashe ta Nasuru kaine gatan mu ka karbo min y'ata agaban Alhaji Abdulmajid aka jefa min ya a hilux police suka tafi da ita zasu kashe ta wllh Halima bazata kashe Fayyat da Khaldum da Agrif ba tana son su Dan Allah Nas........ "FAYYYYT KHALDUM cikin wani irin k'ara da amonsa ya amsa duk gidan yasake cewa "mommy ina Fayyat ina Khaldum kafin mommy tayi magana Khafulan yace " Papa mamy ta shashe su har abbanmu yan sanda sun tafi dasu ni buya yani a toilet Ina ta kiran ka bakayin picking ba papa". "ahankali Nasara yamek'a tsaye yana girgiza kai yace mutuwa "Ah Ah baza su mutu ba mommy ki min bayani ta yanda zan gane ya za ayi Khaldum da Fayyat su mutu ban nemi yafiyar suba ah ah mommy ki min bayani ya kalli Dr Hafsa yace Ummyn Ayman meya faru? ". Mommy tace'' Nasuru nima ban san meyake faruwa ba bana gane komai Fayyat ya mutu khadum ya mutu jikokina dana daura dukkan burina akan su an kashe Aiban da guba banyi magana ba naga illan shiru yanzu gashi makiya sunci galaba a kaina an kashe min jikoki an daura al'hakin kisan akan y'ata mutuwa zanyi Nasir". "Mommy da gaske yarana sun mutu abokina yamutu". Humairah ce tace'' wllh ya Nasir ta kashe su dama tun da rana tace'' sai ta kashe ya Agrif akan ya amince zai auri Izza ta kashe masa yara har biyu". cikin wani irin amon murya yace "tana ina tana Ina wllh idan rai goma Allah yaba bata to duk sai sun fita cikin a zaba wllh zatayi mutuwar wulak'ancin sai na daura ta ajikin mota na jata a kwalta sai nayi pieces pieces din naman jikinta tana ina yayi maganan yana cikumo Humairah yana wani irin gurnani kamar mahaukacin zaki". Humairah kasa magana tayi dan yanda ya cukumota ko numfashi ta kasa ja Kamal da Ayman da Aliyu da sarkin gida dak'er suka ceto Humairah sai alokacin Izza tasamu shigowa dan tana asbiti tun dukan da Nasrim ta mata kwanciya tayi a k'asa tafara wani irin birgima tana rusa ihu haka Mama ma sai yanzu tasa kuka Kamal Abbaty da sauran mutane duk suka fasa kuka daddy da Abu jisuke kamar su kashe kansu duniya ta musu k'unci da gudu daddy yayi part din sana Mama ya haura sama rarufe kansa a d'aki yayi yak'i fitowa kawai shi jira yake ace tashin duniya ne kowa ma yamutu ahuta yakeji Abu ne yabiyo bayan sa yana buga kofar yace "haba Abdul ka zama namiji mana ka daure kafito mu kwantar wa da matan nan da yaran nan hankali muje station a karbo Nasrim muyi cuku cukun karban gawar wakin mu musu sutura". cikin tashin hankali daddy yace "Ah ah Abdulrahaman bazan iya fitowa ba kawai kayi duk abin da yadace ba zan iya cigaba da kallon mutane ba y'ar da na haifa ita takashe d'an ka dan uwanta mijin ta Hajja tayi gaskiya kar kayi kuskuren bellin din Nasrim duk Wanda ya kashe ran mumuni da gan-gan shima a kashe sa". Abu yace " yanzu kafito ni kadai bazan iya duk wannan ba ga Nasir ma yazo baya cikin hayyacinsa mu yaka mata mu kwantar musu da hankali". dak'er daddy ya yarda yafito suka dan kwantarwa da matan hankali suka shiga parlou su kuma suka tafi asbiti dan karbo gawa zasu fita yan sanda suma sukazo binciken gidan aka nuna musu part din da abin yafaru sai da yan sanda suka gama nasu binciken akan gawar wakin doctors sukayi aka batu gawar wakin dan haka ba asamu daman suturan su a ranan ba Saida suka sake kwana Nasir sai binciken wane station Nasrim take yakeyi amma yarasa dan bayan magaruba mommy da aminceciyar kawarta Dr Hafsa suka tafi Nasrim tana asbiti hannuwan ta dukka biyi a daure ajikin k'arafunan gadon asbiti a d'aki na musamman yan sanda ciki da wajen d'aki Mommy girgiza kai tayi tana kallon yanda Nasrim take fitar da numfashin duk da bacci take amma ba na dad'i bane kallon ta tamaida kan Dr Hafsa tace'' Hafsa yanzu Nasrim ce ahaka y'ar dana haifa da cikina ce ahaka a daure ajikin gadon asbiti wllh Hajja ta cuceni Allah ya isa tsakani nadake Hajiya Maryam ke kika hura wannan wutan wllh ko duk abin dana mallaka zai k'are bawanda ya isa yasa a kashemin y'ata ita kadan nake da Nasir yajuya min baya ". sosai ta fad'a jikin Nasrim take kuka Hafsa tace'' wannan itace mummunan k'addaran ta amma dan Allah Fanna k'in tada hankalinki dayawa in sha Allah Nasrim zata fita cikin wannan yanayi koda biyan kudin diya zamuyi zamu dauki kwararrun lawyer da suka san aikinfu Nasrim ko ita tayi kisan in Sha Allah sai ta fita". "Mommy mommy". su kaji Nasrim tace da sauri mommy ta d'ago " My daughter gani meye how you feeling now me kike ji yanzu ajikin ki".? "Mommy ina Agrif ina Fayyat ina Khaldum". "Nasrim kin kashe su kin kashe Fayyat da Khaldum da Agrif Nasrim meyasa kika mana haka idan kin kashe Agrif saboda kishi su yaran me suka miki me jikokina suka miki gashi kinsa zan rasaki ai da kin barmin su zanji sauk'i ". "Mommy da gaske sun mutu? Mijina yarana duniya ta kuma ake zargin na k'ashe su meya ke faruwa dani da gaske ni na kashesu mommy". Mommy tace'' Nasrim kece mana duk bincike ya tabbatar kece Khafulan yaganki kina wasa wuka kuma yace kafin sannan da kuma wukan da yaga kin wasa dashi kikayi kisan duk kuma dama kinyi furucin hakan". mommy idan ni nakashe su mommy wane hukunci za ayanke min". "Kisa mana Nasrim ke ba lawyer bace kinfini sani ai". Murmushi Nasrim tayi tace'' mommy a yau ayanzu yaka mata ayanke min hukunci inason a kasheni yanzu inason naje inda Fayyat d'ana me sona yaje na tambaye shi waye ya kashesu Ina son naje naga mijina na tambaye shi waye ya kashe sa mommy a cikin daren jiyan bayan fitan ya Kamal saida Agrif yaje mukayi magana na fashimtar juna mun sasanta dashi munyi dashi zamu tafi mubar zaman Nigeria mommy meyasa to na k'ashe sa bayan mun sasanta ya yafemin yankan dana masa a hannu ya tabbatar min da mak'irci aha hada bashi ya d'aura hoton ba amma yaga Wanda yadaura hoton dan duk Wanda yayi amfani da wayan sa yana ganewa saboda wayan yana daukan hoton duk wanda ya taba amma nayi nayi ya gaya min yace" hakan bai dace ba amma yasamu munafikin ya tabbatar masa kuma ya nemi yafiyar sa yafe masa dan haka basai yagaya min ba mommy Dan Allah akai ni kotu yanzu zan amsa nina kashe su a kasheni gwara rad'adin mutuwa da kuncin yaruwar da zan fuskanta idan ba Agrif acikin yaruwa ta". Mommy tace'' Al'hamdulillah kina nufin bake kika kashe suba ". "Mommy kisa aranki ni banyi ba amma afili ki barshi anice". Mommy ta girgiza kai tace'' Nasrim bazan bari ba bazan bari akashe minke ba kokina da lefi balle baki dashi sai kin fito sai me lefin yafito da kansa". murmushi Nasrim tayi tace'' mommy wai meye acikin mutuwa ne duk gudun da zaka yiwa mutuwa zai zo duk tsawon shekarunda mutum zayyi a duniya baya wuce dubu to da mutuwar yanzu dana wata shekaran duk sunan su mutuwa kowane rai sai ya dan danni mutuwa ban damu na mutun ba mommy". Doctor din da yake kula da Nasrim ne yashigo zubewa yayi har k'asa yace ranki shi dade an wuni lfy ya mukaji da wannan abin da yafaro". mommy ta juya tana kallon sa tace "Yawwa Dr suleman kaine akanta ko dan ALLAH akula sosai idan Muhammad Nasir yazo kar abari ya ganta inde ba Daddy ta ko yayanta Kamal ba banason kowa ya shigo". "Ok ma'am amma muta ta fama da yan jarida". tace na gayawa police din kar abari su shiga ayanzu bata cikin nutsuwar ta". sai can dare Dr Hafsa da mommy suka bar asbiti har lokacin gidan tamkar nara kuma ba adena koke koken ba mommy part dinta ta yawuce direct ita kuma Dr Hafsa tace bari taje gunsu Hajja da dawo a falon sama ta samu Nasir ya daura Khafulan a cinya yana da aikin lalashin sa dan shide akawo masa su khadum kallo daya tayiwa inda suke tayi hanyar bedroom din ta Khafulan yace " Papa Allah itace ta kashe su da kayan data shiga ta mana addua da zamu kwanta dashi ajikinta ta kashe su kuma ta rofe fuskan ta har hannun tasa safan hannu dogo baki da dogon shijab ina tsoron nima kar da kasheni tunda tayi ta buga kofar naki na bude tayi da turawa da karfi kofar yaki buduwa ta nemo key tayi ta gwadawa ni kuma sakata nasa ". shiru Nasir yayi can yace sorry my son baza ta kashe kaba ina tare da kai kuma idan zan koma tare zamu tafi kaji". yaci gaba da lalashin yaron har yasamu bacci ya daukeshi ya kaishi bedroom din sa ya kwantar dashi ya fita knocking yayi a bedroom din mommy batayi magana ba yashigo samun ta yayi atsakiyar godo tazuba uban takumi hannun sa zube cikin aljuhon wadon ya karasa inda take Mommy bata d'ago ba tace'' kai ma ka yarda Nasrim zata iya kisan kai ita ta kashe su ko".? Cikin b'acin rai yace" to idan ba ita bace waye waya kashe su wayayayi FURUCIN zayyi kisan kai idan ba ita ba"' Nasir ba ita bace ba ita bace Nasrim bata kashe su ba ta fadamin gaskiya". " Eh mommy zakiyi kareta because y'arki ce amma nikuma jinin yarana bazai tafi abanza ba Ina nan Ina binciken asbitin da aka kaita wllh wllh awannan daren da zan ganta zan dinka yan kan naman jikin ta sai nayi piece piece dinta a tattara naman ta a binne danasu Fayyat". Mommy sauk'owa tayi akan gadon tazuba gwaiwoyin ta a k'asa a gaban Nasir ta hada hannayin ta cikin tsananin damu tace'' Dan Allah muhammad katema kamin Nasrim ta fita cikin wannan k'alubalin zan iya shiga matsala idan narasa ta dan Allah Nasir kadubi soyayyar da yake tsakani na da kai kamin a dalci muhada karfi da karfi mu ceci rayuwar Nasrim uban da ya haifeta ma bai koyi bayan ta ba kuma bata dalefi". "Juyawa yayi zai fita da sauri mommy ta kamo k'afafuwar sa tana kuka tace'' katema min". girgiza kai yayi a hankali ya furta "impossible". ya janye kafar sa mommy tana kuka tana k'iran sa "MUHAMMAD kai kadai ka ragemin Nasir kar kamin haka". Bai ko jiya ba yafice washe gari k'arfe 9 nasafe akayi musu sutura ansha fama da Nasir da za afita da gawar wakin dan sunbatu yadin gayi dan Allah kar kukai min abokina wllh yafi kowa sona da rufamin asiri na Agrif ko mutum na kashe zai rufa min asirin dan Allah kar ku binne min Khaldum da Fayyat kubar su surayu su girma na nemi yafiyar su wllh idan muka hadu awajen Allah bazasu yafemin ba ni me lefini awajen su nasa sunzo duniya bata hallaceciyar hanya ba inaso sugirma in nemi yafiyar su". Mutane basu wani tsaya sun fashimci abinda Nasir yake fada ba dan duk muryar sa adashe basa jinsa daddy yace a jan shi asani a d'aki ba aje mak'abarta dashi ba Abu ya hana zaman makoki na mata da maza gaba daya wanda ya kama dole ya musu gaisuwa yana zuwa idan yayi musu soke sallaman shi washi garin ranan Izza da Baban ta tace'' Baba wai dama wannan mutuwar kagani kace gidan zai hargitse wllh Baba gida ya hargitse gaba daya Hajja ta dauki lauyoyi ciki harda ni zamu gobza Shari'a kuma kasan me akotun daddy kasan shine na biyu a najeri daga shi sai high court babban kotu na k'asa dan haka Nasrim Baban ta ne zai yanke mata hukuncin kisa yanzu yau yan sanda zasuyi minciken su na k'ashe daga nan su mek'a cases din court insha Allah zamuyi wining". Baba yace "ba nagaya miki ba akwai babban rigimar da zai taso wanda yafi karfin tsafina ba yanzu ya cikin gidan yake dan naji shiru". "Uummmmm Baba cikin gidan nan bakyau Abu da Ummu de basuce komai ba har yanzu amma Daddy yana bayan Hajja Kamal Kai ma kasan ida yake gida ha hargitse yanzu yau Hajja zata sa daddy yasaki mommy ta bar gidan kai rigima fa gaba ta kama ita mommy tana Shirin daukan lauyoyi taci alwashin ba wanda ya isa ya yakewa Nasrim hukuncin kisa". da yammacin yaran yan sanda suka zo gidan gaba daya a main parlour na Hajja suka taru dakka mutanen gidan tambayar farko Kamal sukayi wa suka ce "Kamal bincike yanuna akwai tes message da Haruna marigayi ya tura maka da misalin 2 na pm ka boye baka nuna mana shiba a binciken farko da muka maga ga tes din kamar haka _kamal kazo dan Allah da gaggawa ashi Nasrim bata hakura ba gashinan zata kasheni tace ta kashe min raya_ fashewa da kuka Kamal yayi yana girgiza kai ya dafe goshi ya fara kuka Sannan dan sandan yace " kayi ne Dan ka rufawa yar uwar ka asiri ko ita ma tayi

Chapter 18 of 40