Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tayi wankan tukun zan shirya natafi makaranta haka da yamma ranan da tsausayin zai fadamin danaje da safe sai nace wa aunty dan Allah zan kaiwa Umma Mubashir ta gansa sai tayi dariya tace'' to Halima da yammma sai ki kai shi kinga yanzu Abban Rashid bai fita ba bazai bari ba nace to da yamma kuma Musa saurayina ya nace sai naje na duba yayar sa gidan ta kuma danisa idan nagaya Umma baza ta barni ba shine nayi shirin islamiya naje gidan yayar Musa ban ma same taba haka nadawo a k'afana sai da magaru ba nazo sai na tsaya a gidan anuty amarya dan nasamu nacewa Ummu anan na tsaya rike mata mubashir nasamu aunty tana wanka sai kishiyar ta tana sallah yaran kishiyar ta kuma duk maza ne suna masallaci na samu yaron akwance acikin katifar a baranda sai kishiyar ita ma tana sallah a kofar barandan ganin lokaci yakure yasa na wallah nace Aunty amarya nazo kuma kina bandaki ni natafi na fice da saurina naje nacire kayan islamiya nayi sallan magaru ba bayan Isha Zakar dan gidan kishiyar aunty Amarya yazo wai Halima inji aunty ki kawo Mubashir Abba yakusa zuwa sai nace ai banzo dashi ba wasa wasa shikenan sama da k'asa aka nemi Mubashir aka rasa gowa sai yace nice karshe fita kuma shijab ne ajikina sai jakata ta leda da yasinke na runguma to nan fa kowa sai yace ai yaganni rungume da rayo itama aunty Amarya tace'' aidama ni nace da yamma zan kaishi wajen Umma haka kishiyar aunty ta bada shida a kotu na taga lokacin da na dauki yaro kinji dalilinn da yasa aka yanke min hukunci zama gidan yari Ta k'arashe maganan tana fashewa dakuka Nasrim tace shikenan kiyi hakuri ni sunana Barrister Halima Abdulmajid insha Allah zan temaka miki saura na Maryama da Lawisa bayan magaruba Nasrim ta samu lawisa ta mata tambaya cikin shikima tasu ta lawyer kuka Lawisa ta fashe dashi tace'' tabbas nayi kisan kai amma wllh ban zata zai mutu ba Sunana Lawisa Hasan iyayena cikakkun yan shi'a ne wata rana muka kaiwa wani abokin Babana ziyara jigawa state a wani k'aramar hukumar malummadori kwanan mu biyu amma ban gamsu da yanayin kallon da abokin baban nan nawa yakemin ba bayan sati biyu kawai sai abokin Babana ya kawo mana ziyara shima da dare yayi kawai sai yacewa Baban mu shi bazai iya kwana ba macce ba dama da matar sa yake tafiya yanzu kuma tana da tsohon ciki bazata iya bulaguro ba kawai sai Baban mu yace sai kayi auren mutu'A da Lawisa ko da Baba yagayawa mamar mu yarda tayi tace Allah yabada lada malam ai bak'on ka annabin ka Baba yasame ni wai naje d'aki bak'i nace mezanyi yace yamin auren mutu'A da abokin sa dan haka natashi muje Baba ya sokoni agaba har d'aki ya barni kulle koba abokin Babana yayi zai kwace min budurci da k'arfin dan naki amincewa dan ni bana ra ayin shi'a inada akidata aboye akwai wani saurayina dan izzala ne na gani kasheni kullum yana gargadina da auren mutu'A shine muke ta fafatawa har yakusa cin galaba a kaina Allah ya temake ni naga wani Reza ak'asan kujera shikuma yariga ya shagala da abin da yake bai san ma na dauki Reza ba dana kama gaban sa yazaci na bada kaine yafara sakamin albarka Yana cewa yawwa shafamin kawai ni kuma tun k'arfina na gusza Reza a gaban sa wanda najimasa ciwo Sosai yafara ihu nan take jini yafara zuba su Baba jin ihun ba iyaka yasa sukazo bakin kofar suna tambaya lafiya kasa bada amsa nayi har Baba ya tura kofan yashiga kafin akai abokin Babana asbiti har rai yayi halin sa wlllh banyi da niyar kashesa ba nayi ne da niyar na kare kaina Allah ya k'addara hakan dan ni nariga nayiwa kaina alk'awarin Habu zan bawa kaina kinji dalilin". shiru Nasrim tayi tana girgiza kai can tace ''Lawisa insha Allah zaki fita ai kinyi ne dan ki kare kanki bawai niyar kiyi kisan kai bane kuma ko a Constitution na k'asa ba ayarda namiji yace zai nemi macce da k'arfin yaji ba inde ba matar saba ko abinda yafaru dashi shi yaja kuma auren mutu'A sahabban anbabi sunyi da sukazo Annabin duk da bai ce meyasa sukayi ba amma ya hanesu dasu kiyaye gaba dan haka auren mutu'A Annabi bayyi ba ba sunna bane Isha Allah zaki kubuta iyakar ki kiyi azumi kaffara". Nasrim da tunanin wannan ta kwanda dasafe tasamu Maryama tana tambayar tabata tarishin ta Maryama tace'' wai me zakiyi da tarishina tarishina bashida kyau Nasrim tayi ta naci amma taki rabuwa tayi da ita Nasrim wajen sister Safeeyya taje ta lallabata ta bata wayan ta ta kira daddy sai da sister Safeeyya ta duba sosai taga bakowa ta bata tace " to minti 1 cikin sauri hannu na rawa Nasrim tasa number daddy wanda private ne bajimawa ya dauka "hello hello yace shiru Nasrim tayi tana sauk'e ajiyar zuciya yace "waye akan layi kuka Nasrim ta fashe dashi Daddy da yake zaune tashi yayi tsaye Yana cewa NASRIN'' cikin kuka tace'' nice daddy " Nasrim meyasa zaki min haka meyasa duk lawyer da yaje miki sai ki k'i bashi hadin kai kode da gasken kin aikata ne". "Daddy bani da amsan badawa ne nide nasan ban kashe suba amma daddy Dan Allah ga wata alfarma nasamu wasu yaran da aka yanke musu hukuncin irin nawa amma bataren da bincike ba daddy inason kasamu tsayayyun lawyer su fitar dasu wllh yarane kanane basu Kai nima duk yan mata ne". Daddy yace ok idan akayi nadu zaki yarda ayi naki kema cikin sauri tace'' Eh daddy". "Ok zan tura Barrister shashid ya binciki ka filet din su afara aikin akansu amma yakike my daughter " kina cin abinci Sosai naki shariyar ma sai kin haifu mun nemi alfarma an d'aga". "Ok daddy kadinga turawa Aunty safiyya kudi ita zata dinka siyamin abinda nake so daddy Ina son naganka naga mommy naga Zainab da Khaldum". "Ok my daughter ni ba halin na ganki mommy ki ta tafi ummara dan ta gayawa Allah kema ki dage da addua kinji". ********************** ako kaman wasa aka fara Shari'ar su Lawisa kuma Al'hamdulillah anyi Na sara na Halima kishiyar aunty Amarya ce ta dauke yaron tsabar kishi amma de bata kashe Shiba wata kawar ta bawa kyauta a Bauchi an yanke wa kishiyar anuty amarya zaman gidan yari na shekara daya bisa adalci tunda aunty Amarya tace ta yafe To fa wannan abin yasake jayo hankalin mutane kan Nasrim kowa sai tofa al'barkacin bakin sa yake wasu suce duk neman sunane wasu suce tana da tausayi Umma Halima zubewa tayi agaban Nasrim sai fatan alkairi take mata tana cewa insha Allah kema sai kin fita Nasrim ta maida hankalin ta akan addua da kuma kula da cikin ta ajefi tana bibiyar Maryama dan tana mugun son jin labarin ta ko meye ********************** *bayan kwana biyu* Kamal da daddy Kamal yace " daddy me yasa gidan nan daga wannan sai wannan ya za ayi ace wai anje anyi belling din mommy kuma batare da sa hannun kowa a gidan nan ba sannan ba asan inda take ba daddy hakkkin kane ka neme ta amma kayi shiru". Daddy yace to Kamal ya kake son nayi Ina zan same ta nasani ". "Daddy ni na bincika ance Nasir ne ya dauke da a police officer din amma tsabar ana tsoron sa ankasa tuntubar sa Ina yakai ta aiko ba komai har yanzu mommy bata gama idda ba amatsayin matar ka take". girgiza kai daddy yayi yace" Kamal kana damuwa da abinda bawani abin damuwa ba Fanna ba karamar yarinyar bace nasan Nasir bazai cutar da ita ba in ma shi din ne ya dauketa kuma kayi lisafi mana ta gama idda furuwan abin wata ukku ne cuf yanzu so ban sani ba ko ta canza wajen zamane ". "Daddy Nasir shi ya dauketa an tabbas min da haka amma da na tambaye shi cewa fa yayi shi bai dauki mommy ba sannan ana gani yafita da su Khafulan da Zainab sati biyu an rasa inda suke ni wllh duk motsin Nasir tsoro yake bani Ina zargin abubuwa dayawa". Daddy yace'' me yake maka tsoron"?. numfasawa Kamal yayi yace gani nake dukiyar mommy yake so kar ya hallakata ga yaran Nasrim ba asan inda yayi dasu ba". gyaran murya daddy yayi yace'' Kamal ka dena irin wanna magan ganun ai idan cutar dasu zayyi bazai fita dasu a idon jama'a ba bana zargin Nasir na komai saboda bai kasance cikin masu boye abu ba komai nashi afili ya keyi ". haka de Kamal ya tashi shi yarasa inda zai bulowa wannan lamarin k gaba daya kansa ya gama kullewa Mommy tayi shiru awani tafkeken parlou da dake ciki ta gasa gane wane garine amma de nasan ba Kano bane tunda anyi tafiya me nisan gaske da ita idon ta arufe juyowa tayi tana shafa kan Zainab da take bacci sai Khafulan daya dameta da jikinsa yana masa ciwo tanemo basa Ball Jin an murd'a handle yasa da sauri Mommy ta juyo mek'ewa tayi atsaye tace " Nasir dama Kai kasa aka kawomu nan". Murmushi yayi Yana k'arasowa yace" mommy Eh wllh ya zauna yana ajiye file din da yake hannun sa a gefin sa yafito da bindiga acikin al'jihun wandon shima ya ajiye yace "mommy ayau nake son komai ya zo k'arshe dan nagaji da wannan b'oye b'oyen zaki saka hannu a wadan nan takaddun da sunan kin barmin dukiyar ki gaba daya sai komai ya zo k'arshe kamar yanda na karboki haka zan karbo y'arki ma nide dukiyar da ubana ya Tara wata ba zata zauna tana ciba kum.......... Bai k'arasa ba mommy ta tashi tana nunashi bakin ta Yana rawa tace'' Nasir wllh k'arya". shima mek'ewa tsaye yayi yace mommy idan ni zanyi k'arya ai wannan bazayyi ba ya k'arashe maganan yana dauko bindigan tare da seta mata a k'ey". *To masoya muje zuwa wai waye sta din FURRUCNA NE nikam meje zuwa ranan Monday insha Allah da misalin 9 pm* *masu yawantambaya na sunayin da suke cikin littafin *FURUCI NA NE* *ai nake ga duk ka sunayi ne na hakikka sai kawai dan alkunya da akayiwa* *Halima nasrin wata itaciya ce *me k'amshi da fan sha'awa a* *gidan aljannan* *NASRIN MINALLASHIH* *Haruna Aarif ana nufin kaman babban mutum ko jaroran* *Khaldum basarake* *Aiban kalman godiya* *Khafulan jajircece* *Fayyat mai alfarma shima de kalman sarautan* Bj [4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE* ( _rikicin babban gida_ ) *NA* *BATUL ADAM JATTKO* *18* "wllh k'arya shima bindigan da bullet din su keyi k'arya suke su fasa kan mommyn Nasir tace'' tana ture bindigan a k'eyar ta dariya yayi yana jefawa Khafulan bindigan wasan yace'' wai mommy kina nufin ban iya Acting bane baki tsorata ba".? murmushi tayi tace'' ai ba aikin ka bane shiyasa ko kyau bai yima ba". Khafulan yace'' Papa nifa Ball nake so jikina ciwo yake min so nake nayi Execise.' dafa kansa Nasir yayi yace''ooo my God son rigima dare ne kaje sama ka kwanta zamuyi magana da mommy good night ". yaron zai sake maganan Nasir ya d'aga kai yamasa kallo na gaske Wanda idan Zainab ko su khadum yayi wa har fisari suke amma da yake Khafulan shima Theron kan sane jifa yayi da bindigan hannu sa yana turo baki da gun guni yayi gaba mommy dariya tayi tace'' oho de ai kwara da yazo inda ni da karena ne ai baza kaje ba". Bai juyo ba amma yanda yake yarfa hannun da gani masifa yake Nasir ya sauk'e a jiyan zuciya yace'' Mommy yaro nan bashida kunya ko kadan fa". Mommy tace'' duk waya batashi ai idan ana original copy to Khafulan naka yayi ba ma photon copy ba." zama yayi Yana dauko Files din da yashigo dashi ya mek'a mata yace'' zaki sa ka hannu anan mommy mommy k'arba tayi takaddun ne na company daya bayan daya tasa hannun shedan ta mallaka masa batare data tambaya meye dalilin sa nayin hakan ba ita de tasan bazai cuce ta ba jiki a sanyaye yake kallon ta shi yarasa wane irin so da kauna mommy take masa ai ko dan da ka haifa yazo da wannan batun babba za ka iya tsayawa kace meye dalili musamman idan akayi duba da wasan da yamata na yanzu da kuma abin da Dr Hafsa ta kaya mata bai san da afili ya furta" mommy idan ina dake a duniya narasa komai ma zanyi godiya". d'ago kanta tayi tana cigaba da kallon sa tace'' ina ai bazaka rasani ba banayi maka alk'awarin sai naga jikojin ka ba dan Allah Muhammad ya isa haka kayi aure kai baka ga duniya yana k'erewa bane ga Abbaty nan kanin bayan ku zaiyi aure badan wannan abinda ya faru ba da wata kila matar sa tana da k'aramin ciki amma kai shiru yanzu da mutuwan Agrif da Aiban kaine shikenan watara za amanta ka gaba daya yanzu kaga ko su khadum da Fayyat ba za a manta suba tunda ga Khafulan nan duk Wanda ya gan shi zaice ai su ukku aka Haifa jikoji da tattaba kunne ma sai sunce ai kakan musu ukku aka Haifa amma kai kam b'ata zakayi bat". a take yanayin sa ya canza cikin b'acin rai yace" towai mommy banji zan iya son yarinyar mutane ba zanyi aure ne bayan nasan bazan iya mata adalci ba ai Annabi yace aure sai kaji zakayi adalci kayi hudu ma amma idan kaji ko dayan ma baza ka iyayewa adalci ba ka hakuri dama sunna ne ba farirla bane". "haba Nasir buri nane fa kayi kodan ni". tsaki yaja yakoma Nasuru sa sak yace'' saboda ke zaki zauna da ita ina gaya miki gaskiya kina sake wahalar da kanki." Cikin b'acin rain itama tace "to Nasir ai naga kana da Wanda zaka iya zama da ita mutane sunfara surutun inda ni na haife ka bazan bari ka kai kusan 36yrs ba aure ba kana shiga 40 fa ka fara zama dattijo kuma naga kana da Wanda zaka iya zama da ita Ina Zuhura yar maiduguri nan tana da kirki zata dace dakai daganin hakurin ta zata iya zama da baud'adde irin ka.... katseta yayi dacewa "mommy bakina da naki na cemiki Ina son ta zan iya zaman aure da ita nifa kawai na ganta da irin zanen kine fa kuma yar maiduguri shine nake dan mutumci da ita shine so".? "To shikenan my son kar ran ka yab'aci ina maka addua wata rana zakayi". d'aga kafada yayi yana mek'ewa tsaye yace'' shi ke nan mommy ki kula da kanki da yaran". Mommy tace'' kai Ina zaka"?. "Kano". Yabata amsa a tak'aice cikin mamaki tace'' nan din ina ne". cikin wasa yace'' gidan kaso ne". girgiza kai tayi tace'' my Son". har yaje tsakiyar parlourn mommy ta mek'e ta kamo hannun sa tabaya tace'' dan Allah Nasir kafitar dani a duhu kagano wani abu ne waye yasawa Hajja guba ina Barira waye yayi belling din ta kana ganin idan aka kama Barira ai asiri zai tonu". "Mommi komai yazo k'arshe fa kiyi hakuri ko kin koma gidan kar kicewa Barira komai nasan yanda zanyi bana son kisake cewa komai". "shikenan Nasir nabar komai a hannun ka har cese din k'anwar dan Allah Nasir ka temaki rayuwar k'anwa....... dakata Mommy wai meye naki na damuwa da wacce y'ar ne ni kadai ma na isheki rayuwa balle ga Zainab ga Khafulan daga yanzu ki lissafata cikin gawar waki dan cikin da yake jikin tane ya hana bamu daukaka k'ara ba dan al amarin yafara bani mamaki har wasu makasan k'awayen ta ta fitar acikin gidan prison din da take..... ajiyar zuciya mommy ta sauk'e ta katse shi da cewa shikenan Nasir yanzu yaushe zamu koma gida dan kwara ina daga can yafi". "akwai gyare gyare da akeyi a part din ki ne saboda k'ara matakan tsaro zuwa tomorrow ma Ina ga saudia zaki wuce idan kin dawo sai ki sauk'a a can nan inda kike Kaduna ne akwai komai a gidan Sai anjima adamu zai kawo miki girls house akwai masu gadi sosai a gidan". har juya zai fita kuma yajuyo yace'' amm yawwa Mommy zakiga na kulle general account din ki idan kina buk'atan man yan kudi ki tambaye ni". gyad'a masa kai kawai nayi takoma tana zama gaba daya tunanin ta ajagule yake meyasa Nasir ya tsani Nasrim haka wane zuciya yace duk lefin ki ne tun yana k'arami zuciyar sa ta ginu da kiyayar ta amma baki kwabe saba gashi yanzu anzo inda shi kad'ai ne zai iya mata maganin abin amma ba zayyi ba saboda yana daukan ta amasayin mak'iya yanzu yazanyi Ina Dr Hafsa tabani shawara ko tana zuwa duba Nasrim nide tun ranan farko bata sake zuwa ba da sauri ta mek'e har an bude masa mota zai shiga back seat yaga fitowar Mommy tsayawa yayi yana sake hade fuska a tunanin sa maganan Nasrim zata masa cikin sauri ta k'araso tace'' waya ta fa ?." a tak'aice yace'' suna gida". "to Nasir haka zanyi ta zama inason yin magana da Dr Hafsa". bai sake ko juyowa ba ya shige mota Mommy dafa kai tayi afili tace'' Allah ya shiryamin kai ya kareka daga dukkan Sharri yabaka sa'a da Nasaran rayuwa". Komawa tayi ciki ******************* *Three brother* Nasir numfashi yasak'e idon sa akan Hajja yace "ammm Hajja Mommy ta mallaka min komai nata hatta company dinta na shikama nikuma na mallakawa Zainab yar gidan Agrif company sarrrafa Madara nawa na Legos sai yaran Aiban mata guda 3 tun gafin ya karasa gaban Izza yayi wani irin bugawa !!!!! yacigaba yaran Aiban Muwadda da umdatu da Musanat na mallaka musu k'aramin company k'arfe da yake Chaina babban company karfe kuma Khafulan San nan dama Khafulan da Khaldum da Fayyat suna da kaso 1 bisa 3 acikin nawa hakan yabawa Khafulan daman mallakan rijiyar Mai fetur na Istanbul ma ana na hade masa waje daya kenan nashi da na yan uwan sa da yagada ina fatan kowa yagane". ya k'arashe maganan yana mek'awa Abu takardun kyautan da yayi kowa yace Kai Masha Allah ka kyauta Allah yakara bude Hajja tace'' amma Nasuru banji na Abdulsamad dan wajen Kamal ba". Nasir juyowa yayi yana kallon Mai sunan Abban sa dayake zaune a kusa da Mama dan shara 7 yajuyo yasake kallon Hajja yace ai shi yana da uba ni kuma marayu na yiwa". yana gama fadan haka yamek'a yafita Hajja sai data tabbatar yafice tace'' lalle wannan kyauta na renin hankali ne yoo banda renin hankalin ya zauna Yana mana kyauta na iko wai Fanna ta mallaka masa komai cikin dukiyar ta kuma ya dauka yabawa Khafulan jikanta kaso mafiyawa yo anyi ba ayi ba abude a gindin su ya k'are yo banda ma mutuwa har a dukiya Abdulsamad mutum zai zauna yana min iko Abdulsamad wanda naga dama yake wa kyauta Kuma alokacin sa ba nuna ban banci amma shi yaraba bai bawa dan Babana Kamal ba yo banda ma bayahuden banza da bai san darajan mai sunan uba ba ai shi ya kamata ma yafara bawa kyautan yaci darajan sunan uban sa ma mana zonan Abdul ni Ina da gidan gona na baka kaji". ta k'arashe maganan tana jawo yaron jikin ta a wani irin fusace Kamal ya fita a fili yafur ta yau za ayi fallasa acikin gidan nan Nasir yana shirin shiga bathroom har yakama handle yajuyo jin an banko Kamal ya k'araso inda yake yace'' Nasir me yasa ka renawa mutane hankali ne kana Abu kamar kai ka haifi gidan gaba daya to wllh kayi hankali a tafin hannu na kake ina ka kai Mommy nasan duk inda Mommy take tursasa ta kayi ta samaka hannun a dukiyar ta". ahankali Nasara ya saki handle din ya tako gaban kamal dafa kafadan sa yayi cikin jan murya da isa da k'ajinin sa yace'' kamar ne ma ai ni ne babban wa acikin gidan nan shi kuma babban wa ubane sannan ai uwar da ta haifi iyayen gidan ma a gaban ta nayi komai banji tace wani abu ba sai kai Mommy kuma da dukiyar kuma iko nane sai yanda ni nayi". Kamal cikin bacin rai yace'' ba ikon ka bace ikon mijin tane kuma shi yake da ikon duk wani shawaran ba kai ba". Nasir Karan hancinsa ya shafa yace "to yanzu yakake son ayi maidawa mommyn zanyi ko baka zanyi ka maida mata mijin ta kuma da kake magana akai ya saketa har tagama idda baka da labari ne". "naji daddy yasake ta amma ai suna ta y'ar atsakanin su Wanda dukiyar mommyn hakkin Nasrim ne ita kuma Nasrim daddy yana da gadon ta nima dan uwan ta Ina da gadon ta". Murmushi Nasir yayi yace'' anzusa zuwa wajen Kamaluddeen Baban Hajja Kamal da wayo ba hankali inji Baba yakubu ko ba kirarin ka kenan ba *Kamal da wayo ba hankalin* To inba rashin hankalin ba taya dukiyar Nasrim zai zama naka bayan tana da yara". murmushi shima Kamal yayi yace'' tana da y'a daya de Zainab amma Khafulan ai shege ne bashida gado ba dan sunna bane........... !!!!!!wani irin bugawa gaban Nasir yayi faduwar gaban da tunda yake a rayuwa bai taba jiba amma cikin jarumta yace'' Khafulan ne shegen ya akayi yazama shegen!??". wani irin Dariya Kamal ya kece dashi yajuya zai fice yana cigaba da dariya sai daya bude k'ofan yafitar da k'afarsa daya waje yajuyo yace'' muje suwa Nasir k'aryar ta kusa k'arewa babban shukan da kukayi Kai da Haruna kunyi a idon mak'orwa sai nayi abinda Mommy da kanta zata ce ka maida mata dukiyar ta sai nayi abinda Mommy zata ce ba ita bakai zai ta daure ka da hannun ta saboda kai din ba mosoyin gudan jinin ta bane Kai kasha cewa zaka cusa rayuwar su cikin matsala ita da Haruna kasha cewa k'addaran Nasrim ba mekyau bane Ina da kyawawan hujjojin da idan naga dama wllh a yau baza ka k'ara kwana a duniya ba duk kudin ka da ikon ka amma na bari saboda wasu dalilai ko ba FURUCIN KA BANE a kullum sai ka jefa rayuwar yar uwata cikin matsala to tabbas gidan nan akwai RIKICI d'ana kuma da kaware ba kayiwa kyauta ba Alhamdulillah nima na tara Wanda na tara ma ya isheni nida shi." ya k'arashe maganan yana ficewa Inna'lillahi dama Kamal yasan da wannan maganan waye ya gaya masa daga ni sai Agrif ne fa muka sani no no Agrif yanda yake tausayin rayuwar yaran nan yake hana nima intona asiri bazai tona ba to ya akayi Kamal yasani wannan rana inda Agrif yana raye sai nafi kowa farin ciki kodan Khafulan yazama d'ana a idon kowa amma yanzu zafi kowa bak'in ciki idan ya tuna girman alk'awarin da yayiwa Agrif da sauri ya bi bayan Kamal Kamal yana sauk"a step Nasir ya cin mashi ya janyo shi har cikin d'akin yarufo ya sauk'e numfashin yace'' meye shidan ka na sheganta Khafulan". dariya Kamal yayi yace" ba wani sheda hasashe ne fa musamman idan mutum ya kafawa Khafulan Ido to zai sheda uban sa yana raye ba maraya bane kai ni Zeenat din ma ban yarda y'ar halak bace Aiban ne kawai dan Agrif kuma ya rasu amma sauran sai ahankali". ajiyar zuciya Nasir ya sauk'e jin Kamal bai San komai ba zargine kawai ya d'aure fuska Sosai yace'' idan abinda na bawa yaran Haruna yasa ka zargi wani Abu to zunubi kake kwasarwa kan ka dan sanin kan ka ne Aiban da Haruna sunfi karfin komai a wajena Especially Haruna yayi aiki tukuru a three brother zuciya daya kuma ba abinda ya tsira dashi dan haka dole yaran sa su mori wahala da uban su yayi idan kasa ke ai bata yaran Agrif abin bazayyi maka kyau ba a kan k'anrwa ka kuma kayi komai ma Shari'a ba fashi wawa kawai". ya sakeshi Yana shegewa batdroom dariya Kamal yayi yace'' zaka ga aikin wawanci idan na kafa k'iyayyar ka azuciyar wanda kake takama uwar kace *Prison* cikin mamaki Nasrim take kallon masifaffiyar matar mai

Chapter 21 of 40