NASARA MAI WUYAR FADANCI GOSHIN JIRGI MAI WUYAR KARAU
SAI DAN GADO".
Nasir bin ma ai'katan yayi yana basu hannu suna nuƙewa amma yana sake matsawa cikin sakin fuska yake amsa gaisuwar su daga ƙarshe ya rungumo Baba Yakubu yana tsakar masa murmushi yade kasa magana har Mommy ta shige parlurn Hajja shima sakin Baba yakubu yayi ya dauru bayan Mommy
Hajja rungumo Nasir tayi ta saki kuka tace "oo ni Maryama Nasuru kaine farin cikin gidan nan me yasa ka gujemu". zamewa ajikin ta yayi yana lalashin ta
ya zube agaban Abu da Daddy yace "Daddy Abu.......
sai kuma muryar sa ta fara rawa yakasa ƙarasa maganan kawai ya kifa kansa a ciyoyin ABU yana sauƙe numfashi shafa kansa Abu yayi yace "please my son karkayi kuka kai jarumine jarumai basa saurin kuka musamman cikin yaran su"
yaƙarashe maganan cikin tsigar wasa".
"Abu kugafar tamin kaida Daddy wllh ban wulaƙan taku da son raina ba saide kawai dan banason kuce zaku tursasani zuwa gida ne wanda nasan hakan halakane a gareni dan zan sabawa umarnin Mommy na Daddy ku yafemin duk lefukana Daddy na san na ɓa ƙanta maka nayi Repping din ƴarka aranan auren ta Abu na ɓa tawa ɗan ka AGRIF dare mai mushimmanci nayi sanadiyar jefa ka cikin rashin lafiya Abu idan baku yafemin ba Allah bazai yafemin ba kunje ne mana na wulaƙanta ku na nuna ban san kuba nacuci ahali ........
da sauri Abu ya girgiza masa kai tare da sa hannun sa na dama yatoshe masa baki Daddy saukowa yayi akan kujeran ya ja Nasir jikin sa
yace" my Son mu mun yafe maka dama ba kaine mai lefin ba an hukunta masu lefin..........
"Daddy nima mai lefine na rasa me yasa nayiwa ƴan uwana da banida kamarsu NASRIM da AGRIF haka yasaki kukan da yake dannewa tun shigowar sa gidan Khaflan da Abdul ne sukazo suka faɗa jikin sa suna murnan ga papa wayyo ga papa
hannu biyu yasa ya rungumesu yana tambayar su ina su Muwadda sukaje
su kace uncle yaje daukosu a gidan gyaran gashi Izza da Humaira cikin ladabi suka zo suka gaida shi haka Fajji ƴar gidan Mala yayan Mommy na maiguguri wanda zatayi kusan sa a dasu Nasrim amma budurwa ce itama cikin ɗoki tace "my brother ga sister dinka da baka santa ba."
Nasir kallon ɗaya yamata yagane eh family su ce dan ga kamanan da Mommy har farin ta farace tas kamar Mommy amma dayake ita yar zamanice ta hada da mai tazama kamar zabiyan gyaɗa kansa Nasir yayi yana son yace ƴar wajen waye amma miskilancin sa ya hana
kawar da kansa yayi yafara magana da su Musanat da suka shigo yanzu da gudu suna rige riken faɗa fasa ya kamo hannun Musanat
yace "my daughter kin girma me kike cine murmushi yarinyar tayi tace "papa bakomai....
Ummda tace " wllh papa musanat cine da ita komai ci takeyi sunan tafa ci TARA Allah har yafi so 9 ma takeyi".
murmushi Nasir yayi yana kallon tsantsar kaman Ummda da Aiban hatta maganan su iri dayane jayo yarinyar yayi yana shafa kanta
yace " daughter ai kwara tayi ci taran bakiga tafi Muwadda ba".
ya ƙarashe maganan yana kai hannun sa wuyan Musanat
Musanat tace "Allah Papa ka hana su cemin ci tara".
yace " daughter barsu su fada ai ci lafiya ne wani a gadon asbiti yake sai de ayi ta saka masa ruwa kinga keko kina da cikekken lafiya yanzu koda Boss zaki iya karawa."
ya ƙarashe maganan yana sauƙe idon sa akan Khaflan wani kallon raini Khaflan ya watsawa Musanat amma bayyi magana ba
Hajja tace ina Aisha ina wannan wanda akayiwa rowan imani".
Nasir yace "har yanzu bai dena dukan suba Son kadena sune fa manya yayun ka ne Ummda ce kawai ƙanwarka".
Khaflan yace "ni ina ruwana dasu".
yayi maganan yana rungumo Mommy yace welcome my Mom nayi missing naki thank kinzomin da papa na,"
tureshi Mommy tayi tana meƙewa
tace "dallah ɗagani ni naje nawatsa ruwa sai yanzu ka ganni".
Hajja tace "dama ko ƴan maiduguri sunzo suna can part dinki".
cikin murna tace "har sun ƙaraso gobe sai lagos kenan".
ta ƙarashe maganan tana me ƙewa ta kwashi tarkacen ta tafice
Nasir sauƙe numfashi yayi yace "Daddy Mama Emaka fa ta mutu na kasa gayawa Mommy yanzu idan munje ya zamuyi'".
Hajja da su Abu sun jajanta mutuwar Emaka saboda Mommy ta kwallafa rai akan tanason ganin mahaifiyar ta
Hajja tace " tun yaushe tarasu ".?
Nasir yace "zatayi shekata goma da rasuwa ayanda ƴan uwanta suke gayamin".
Mommy taji daɗin ganin su Baba danginta dayawa suka zo Mala Sharif da sauran su
Humaira da gudu ta faɗa jikin Nasrim tana murmushi tace
" He loves me and I love him very much wllh bayan Khamal ban zaci zan fada soyayya haka ba Zarran yacika namiji wow wllh yafi ya Kamal iya soyayya kodan damafa Kamal haɗin gidane".
tureta Nasrim tayi tace"
Lallle Humaira ko kunyar idona baza kiji ba ki fito a hannun dan uwana ki zauna agabana kina ambaton kina son wani".
Humaira tayi murmushi tace "koke da kukayi soyayya da Agrif kamar zaku cinye juna naga yanzu kin bawa Habib dama.
"cikin sauyin yanayi Nasrim tace "ya zanyi Aisha a take taken su Abu tabbas idan ban fitar da miji ba wllh zasu min dolle da wanda ban sani ba amma wllh habib baya cikin jerin mazajen da nayiwa kaina buri kuma ma nifa soyayya da aure ahalin yanzu basune agabana ba du du du shikara daya da rabi da mutuwar mijina awani matsa sai na fitar da miji akan me".
Humaira tace "pls sis wllh ganin mu duk kan mu ukku a zaune a gidane ya janyo hakan yanzu ba ga Izza ba shekaran Aiban biyar da rasuwa ai basu matsa mata ba saida mu muka ƙaru yawan mune yakawo hakan kuma idon mutanen duniya akan mu yake saboda wannan abubuwan da ya faru especially make amma kinsan wani magana danaji ɗazu a falon Hajja wai an baida kudin auren ki dana Izza ke da izza an muku miji baza abawa Habib kema itama Izza baza a bawa Zayyat ba an fasa saboda wasu matsaloli da suka ɓullu wai abin yaban mamaki to suwaye mazajen naku kuma fa shirye shiryen biki ake daga anzo daga lagos za a daura aure".
Nasrim tace "ban gane ba anayiwa bazawara auren dole ne kuma yama za ayi a ce an bai da kudin auren mu mu ba muji ba".
Humaira tace "kude zuba ido tunda bamu san manufar hakan".
duk gidan kowa yace sai yaje lagos har Hajja da take kushe arna dayake safgar yawone tana wajen ga gaiyar yan maidukuri awani ɗan ƙaramin jiri nasu na family maicin mutum 34 suka shirya tafiyan gasu suda yaran su har ƴan maiduguri su arba'in da ɗaya ne dan haka yaran yawanci a cinyar mutane suka zauna
Nasrim itace kusan ta ƙarshen shigowa dan haka tana shigowa saura seat din mutum biyu kuma ajere dan haka adayan da zauna bayan ta Bukar ne ɗan gidan yayar mommy da matar sa sai daga gaban ta izza da Fajji
tana shirin gyara zaman ta kawai sai taga mutum yana shirin zama a gefen ta cikin ɓacin rai ta fara kalle kalle amma ina ba wani seat sai ƙwaya biyun zama tayi tana daure fuska shiko ko kallon ida take bayyi ba ya zauna cikin izzar sa
Nasrim zama tayi tacigaba da wayan da take ƙamshin turaren sa yana tariyo mata wani abu jitayi gabanta yafadi domin bazata taba banta wannan ƙamshin ba a take taji wani irin ɓacin rai ya ziyar ceta amma ta daure tacigaba da waya da Habib har jirgi yatashi Nasrim tajima tana waya tunkun taji networks ya ɗan dauke bata jinsa sauƙe wayan tayi tana murmushi Fajji da take gaban su tajuyo tace "kai sister irin wannan dogon wayan haka ba sararawa kewai baƙya gajiya dawaya ne baki da wani lokacin sai na wannan koɗaɗɗen meyasa ba kya gajiya .?'
murmushi Nasrim tayi tace "
because my souls and spirit boid with his blood".
zaro ido Fajji tayi tace "rushin ki da jinin jikin ki hade yake da nasa lalle kam ba gajiya cigaba yar uwa
Murmushi Nasir yayi ya kwantar da kansa sosai ajikin seat din yakai bakin sa setin kunnnen Nasrim idon sa alumshe ahankali yanda ba meji sai ita
yace" most of the time whats ours heart desired may not happened
So tari abinda zuciyo yin mu keso bashi yake tabbata ba
wani irin mugun kallon ta watsa masa amma ina ido sa alumshe kamar ma bashi yayi maganan ba
wayan tane yasake rin Habib dinne kuwa dauka tayi tare da gyara zaman earpieces din ta tacigaba da sauraron zaƙaƙan kalaman Habbib
a lagos Mommy tasha kuka jin Maman ta tarasu sai ƴan uwanta wanda yanzu Nasir ya gama wadata su dayawa daga cikin matasan yabasu aikin yi wasu a america wasu anan nigeria su Mommy sunga kar ramawa awajen wadan ba addinin su daya ba kwanan su ukku ƴan maiduguri suka wuce sai ƴan kano ma suka juyo
ƴan gidan malam Ladan sunkawo wa Nasir ziyara Nasir sai tambayar ina Sady yake Ummu tace da yamma zasu zo ita da Zurfa'u
da yamman ko sai gasu fir Nasir ya hanasu tafiya har dare kuma shi bawani fira yake da ita ba ana gama cin abincin dare ta kalli Mommy da Ummu cikin kunya tace "zamu tafi ".
sukace to madalla ku gaida gida Mommy tace "gashi Abbaty bai zoba yatafi Abuja yana ma hanya amma nasan kuna waya ko".?
ta ƙarashe maganan tana kallon gefin da Nasir yake wanda hankalinsa baya ma inda suke
Sadiya ta durkusa a gefin sa tace
" bro we're leavings now Zamu tafi . "
Nasir yace "wait a little while please My sister ".
taɓe baki Nasrim tayi ganin yanda yake baza idon sa akan ƴar mutane
***********************
*bayan sati biyar*
yaune yakama daurin auren su Nasrim amma ita da Izza basu san wa za'a aura musu ba abinda yake bawa Nasrim mamaki yanda Mommy ta zage tana ta yiwa Humaira da Izza gyaran jiki amma ita tace banda ita har tafara jin daɗi a tunanin ta ko banda ita za adaura auren sai kawai yanzu Garba wani mai aikin su yake gaya mata harda su har an daura
tayi tayi yafaɗa mata da wanda aka daura yace ah ah
dariya Humaira tayi tace "to ke meye damuwar ki nasan de su Daddy bazasu cuceku su baku mazajen da bazaku soba kuma nasan ba sadakan ku zukayi ba kai koda sadakan ne duk wanda aka kaiwa ku ai an masa gata musamman ke da kike da kayan aiki nide fatana Allah yasa ba kishiya dan wllh idan aka kawomin irin ki a matsayin kishiya duk son da nake mishi zan hakura na nemi daidai ni tun kafin zuciyata ta buga tunda de shi ba dangin waliyai bane balle yace zai iya kwatanta adalci".
taɓe baki Nasrim tayi tace "idan kuma tafini komai da kike gani ina dashi fa?".
Humaira tace "da wuya idan za a samu komai da komai ɗari bisa dari ummmm kede wllh ko wacece ina tausaya mata".
********************
da dare Abu da daddy suke ƙirasu bayan sun masu nasiha Daddy yace kuyi biyyaya da mazajen ku kamar yanda kukayi ada ƙaddara ta rabaku yanzu ma haka musamman ke Humaira babban gida zakije ki zauna lafiya da cowa."
sosai aka musu nasiha tare da basu sadakin su sukayi godiya suka ƙarɓa
Nasrim ganin har za atashi ba agaya mata waye mijin ba yasa ta cire kunya tace "Abu nida Izza wa aka aura bana".
Hajja tace "ungo naki rasa kunya ɓeran tan-tan Izzatu batayi magana ba sai ke".
Abu yace ku shirya gobe za akai ku keda Izza da yake ba a ƙasan nan mazajen ku suke ba ita Aisha yau za a kaita idan kunje can zakuga zabin da muka muku duk da ku kuke da ikon zabawa kanku mazaje a matsayin ku na bazawarai amma bamuyi kurkure ba dan mun nemo muku mafita kuma idan kukayi biyayya ba kuyi kuskure ba kuyi hakuri sosai watarana zaku ci riban abin musamman ke NASRIM sai kinyi hakuri saboda mijinji yana da bauɗeɗen hali amma mutumin kirrine ki masa biyayya bisa umarnin mu............
*TO MASOYA DAN JIN WA AKA AURAWA NASRIM DA IZZA KU TARENI A PG 32 NGD SOSAI DA COMMENT DINKU* 👍👍
BJ
[4/8, 1:49 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*32*
Nasrim sai juyi take tanajin hayaniyar ƴan daukan Amarya ba abinda yake mata yawa cikin brain nata sai Furucin Abu na cewa mussamman ke Nasrim sai kinyi haƙuri dan mijin ki mai bauɗeɗɗen haline to mehakan ke nufi waye mijin tsaki tayi mitss akaro na ba adadi tace nide koma waye bai isa ya boɗa ni ba wllh".
Izza de duk gabanta yana faɗuwa duk da ran ta ba daɗi amma idan tayi duba da harda Nasrim da take ƴarsu akayi wa dulen ba da sai tace dan sunga ita marainiya ce aka mata haka haka de taci gaba da shiga cikin jama'a duk da Hajja ta hana taro amma dangin mijin Humaira sun shiyar ƙayatattcen diner da zasuyi idan an tashi kuma gidan ta za awuce da ita Humairah tasha kuka wanda ko auren ta na fari batayi ba tunda na fari agida ne tamkar ba aure ba taji yanzu gashi zata rabu da gidan su gidan daɗi bayan duk an tafi wajen dinner din Mommy ta shigo ta sameta zama mommy tayi akan bed seat din tare da janye blanket din
tace "haba daughter wai meyasa taurin kanki yayi yawa ne izza da yake ba asalin ƴar gida ba ma tayi haƙuri tayi biyayya sai ke duk kinbi kin tsangomi kanki ai sarai kin san halin Abun ku zai ɓata miki rai kuma koda kinje banason wani lefi yafito ta ɓangaren ki ki zauna lafiya da mijin ki".
"Mommy ki naji fa Abu yace wai nawa mijin sai nayi hakuri dashi yana da ɓauɗeɗen hali taya zan iya rayuwa da mai ɓaudedden hali nida nayi rayuwa da miji mai saukin kai mai saurin yafiya mai kwantar da kai ko nice da lefi idan mun samu tsaɓani shi zai zo yayita bani hakuri Mommy kinsan ni bani da hakuri ina da saurin fushi da zafi taya zanyi rayuwa da shi ni wllh tun ban san saba danaji ance mai ɓauɗeɗɗen haline na tsane shi saboda tun ina yarinya nakejin Hajja tana ƙiran wanda nafi kowa tsanan sa da mai ƁAUƊEƊƊEN hali ko tace BAYAHUDE shiyasa ana amma ba tan hakan naji na ~NATSANE SHI AN DASA MIN TSANAN SA TUN KAFIN NA SAN SA~".
murmushi Mommy tayi tace "idan kuma akace shi bayahuden nefa ya zakiyi?".
da dauri
Nasrim ta zaro ido tace" Mommy dena faɗin haka bazai ma yuwu ba hakan bama zasu fara ba wllh har kinsa na sake tsanan mijin dan Allah ki bari".
Murmushi mommy ta sakeyi tace "shi kenan na bari amma abin da nake son gaya miki shi kansa mijin bai san ke matar sa bace dan haka inason idan kinje kar ki nuna ke matar sace har sai yafurta miki yana son ki ta yanda zakiyi daraja a idon sa naso ace ni na rakaki amma ance ni Izza zan raka ke kuma Umman ku zata rakaki amma na nemi alfarmar awajen su Daddyn ku na kar agayawa shi mijin naki ke matar sace zaki wanashi yanda kikeso kuma yana mutuwar sonki sonda ko Agrif baya miki rabi rabin sa amma ya kasa nunawa saboda girman kai shiyasa duk gyaran jikin da akayiwa su Izza ke ba a miki ba idan kuka dai daita kar ki yarda ki bashi kanki sai kinzo an miki gyaran jiki kinji Allah ya miki Albarka yasa kwanciyar hankali jikin rayiwar ki".
gaba daya kan Nasrim kullewa yayi
awajen dinner kama dangin miji sunyi kara sosai suka nuna suna farin ciki z
da shigowar Aisha familyn su sun shiryawa bikin sosai Humaira da ɗan mutanen ta irin su Amiran dr Hafsa Zahra da Izza basu fi goma ba sai suka renawa kan su sosai ɗangin ZARRAT suka nuna shi ɗan gatane ko ina waƙokin ango Amarya ne yake tashi daga manyan mawaƙa wani wanda ALI JITA yayi yafi tafiya da hankalin mutane mai tajen
_MUYI RAWA MU CASHIR EMMA TA GA ZARRAT ANGON ƳAR TA HABA AISHA INDON MATA MUYI RAWA MU CASHE_
ƴan mata ne masu kyau da aji suke juyi aciki dama familyn UMARU ƊAN ƘWALLI ba de kyau ba kwata kwata three brother basu zaji ɗan ƙwalli zasuyi wannan gagarumin bikin ba saboda shekara daya tak da rasuwar Matar Zarrat din da tarasu a haifuwar fari Zarrat tun Humaira tana budurwa yasota kamar ya mutu da bai sametama yace bazayyi aure ba ya tsallake ya tafi karatu har yazama professor da yadawo dole aka tursasa masa auren wata cousin sister din sa Asmau amma a haifuwar fari ta rasu
Alhaji Ɗan kwalli Babban mutum ne da yarike muƙamai da dama a nigeria ambassador a ƙasar saudia minister mai anan ƙasar gomnar a garin kano dade muƙamai mai da dama wanda har yanzu ana damawa dashi kuma yana cikin dattawan da ake ganin ƙimarsu a fannin son cigaman ƙasa
Zarrat shine ɗana biyu a wajen Ɗan ƙwalli sai ƙannen su mata ukku wanda du suyi aure biyu ma ba a ƙasan suke ba matar auren sa daya Hajiya Zainab faɗin murnan da wannan ahali sukayi na haɗa zuri'a da THREE A FULL ɓata lokacine
Event kam yayi dan center din da suka kama ma shine ƙololon mafi tsada kuma Humairah tayi kyau ba ƙarya ba me ganinta yace ita ta haifi Abdul ko da yake nawa suke ma dan de an musu auren wuri ne suna ƴan 18 zowa 19 akayi auren su sai yanzu zasu cika shekara 28 dan haka har yanzu akwai wasu ƙawayen su ƴan mata wasu dayawa yanzu ake auren su gashi daga Izza har Nasirm da Humairan Allah yabasu kyan jiki
Ummmmm wani kallon yana gidan Humairah da yake a Badawa lay out fadin haduwar gidan ɓata lokacine saide muce Allah yasa gidan tane yakuma kaɗe fitina
washe gari Ummu da Nasrim suka wuce america Mommy da Izza swizerlad
sun sauka lafiya
gidan sai masu gadi ba kowa cikin kiɗima Nasrim take bin hotunan ƴan gidan su da yake birjik a parlour da kallo musamman na Nasir wanda shi yafi yawa sai abinda yasake ruɗata kamshin turaren sa jitayi bakin ta yafurta *kode shine* da sauri tace subbahallashi Ah Ah Ah bazai yuwu ba ta dafe ƙirjinta da hannu biyu wani irin sauƙe numfashi take da sauri da sauri kamar mai asma Ummu tayi saurin ƙarasawa gunta ta kama hannun ta
jin kamar numfashin zai tafi yasa tace " please what is you,re doing Nasrim yaka mata kiyi tauwakkali fa".
damƙe hannun Ummu tayi cikin rawar murya tace "Ummu wa aka auramin dan Allah ki gaya min tunda munzo promise bazan bijire ba zanyi tauwakkali".
Ummu tace "Halima kina da wutar ciki tunda munzo ai zaki ga kowaye ko dayake kunyi ma kokari ade yaran yanzu kafin asamu masu biyayya irin naku sai an tona to inaso ki cigaba da kakurin Insha Allah bazakiyi da nasani ba a rayuwar ki duk ɗan da ya farantawa iyayen sa shima Allah zai faran ta masa daga ɓan garenki kar muji kar mugani wanda iyayen ki suka baki shine rufin asirin ki Nasrim koda ba zabin ki bane kiyi hakuri wata rana sai labari shi dama rayuwa ba duk kan abinda mutum yake so yake samu ba burin duniya baya taɓa cika saide mutum yayi juyi yajisa a cikin kabari aranan buri yake ƙarewa ba duk kan abin da ake so ake samu ba ki tashi muje mudan watsa ruwa murama sallalin mu".
sama suka waura ɗakin ƙashe suka shiga acikin jerin ɗakunan biyar na saman ɗakin da suka shiga fes a share amma ba alaman ana amfani dashi dan ba komai a kan mirror haka gadon ma ba bed shit kai tsaye bathroom Ummu ta wuce ba bajimawa tafito daure da towel daya a ƙugunta daya tarufe jikin ta cikin sauri Nasrim ta sun kuyar da kanta dan har yanzu tana jin kunyar Ummu a matsayin ta na tsohuwar surukar ta
meƙewa tayi tareda daukan kayan da zata saka idan tayi wanka ta shige bathroom din dasu anan tayi dressing din ta cikin wani riga dogon riga pich colour bajajje daga ƙasa ta sama kuma daidai jikin ta balefi yafito da matsayin boobs din ta sosai yayi mata das da ita gawani ƙamshi na musamman ajikin kayan Mommy ce tayi mata sabin ɗunkuna ta kife kayan da turarukan wuta irin nasu na maidunuri bata san da zaman jakan ba sai da zasu fito tace bada wanda ta dauko zata tafi tace ta bata ta ƙarbi nata ta bata wannan kuma yawanci ɗunkun nan kayan wanda zai kama jikinne wai wannan da ta dauko shine ma na mutumci sai english wears na gayu masu bayyana sirrin jiki a daya jakan Ummu kallon ta tayi tace "masha Allah zaki ruɗa ɗan nawa damma Mommyn ku ta kafe kar akaya masa ke matar sace amma dan Allah Nasrim duk wanda kika kani a matsayin mijin ki rumguni kaddara shi kaddara yaƙine idan yacimaka ba yanda zakayi amma ki dage da addua addu'a tana ko kuwa da kaddara kinji".
gyada kai kawai tayi ita ta gaji da wannan hakurin nan da ake bata ita yanzu so take taga waye ne."
Ummu tace "yawwa my daughter Allah yabaki ladan biyayya dana aure muje falon ko".
suna taka step 3 daga sama suka ga yana shirin shigowa palon cikin shigar sa kamar kullum maroon din suit sai farar t'shit daga ciki da Nicktile baki yasha stockng daganin yanayin sa a gajiye yake cefa jakar hannun sa yayi akan kujera ya cire suit din saman shima ya jefa yasa hannun yaɗan sassauta daurin nicktile din sa ya jefa kansa cikin kujera a mugun gajiye ya sauke numfashi tareda lumshe ido ya kwantar da kansa ko socks din kafar sa bai cire ba
Nasrim dan ƙarewa tayi a wajen ta kamo hannun Ummu ta matse kamar zata karya jikin ta ya dauki yara cikin rawan murya da in ina tace " Ummu ba shiba ne ko dan Allah kar kice shine".?
kasan cewa parlourn babban ne kuma shi yana kujeran bakin kofa bai ji maganan Nasirm ba da sauri Ummu taja hannun ta suka koma ciki
"Nasrim kar ki saki Daman ki Nasir de shine ƙaddaran naki da muke ta baki ƙakuri dashi kuma yana sonki sosai kina da daman da zaki juyashi yanda kike so Nasirm auren Nasir shine rufin asirin mu musamman Khaflan".
"Ummu na tsane shi bana son koda ganin sa yazan yi na zauna dashi".
"kin tsane shi ba zakiyi biyayyar ba kenan Nasrim meyasa kike da shegen taurin kai ne to nabaki shawara kibi a hankali sarai kinsan Nasir yafiki iya shege duk abin da kike ta ƙama yafiki idan kin bi ahankali ki samu salama idan kinbi a zafi kan ki ai dama Hajja ta fada ke zumace sai da wuta haba tun agida nake lalashin ki ko su kamal da suka kashe miji miji da yara baki ƙullacesu kamar haka ba wllh zan fita harkan ki haba mutum sai kace kin fito a kafuran farko me Nasir yayi ne haka ......
ganin yanda Ummu ta dauki zafi tana ta fada yasa ta saki kuka tace "Ummu zanyi biyayya daga ɓan garena ba za aji komai ba wllh ban zaci ƙaddara ta zata zomin da haka ba wllh da a auran min wannan bayahuden gwara ace an auramin kuturu makasho jashili wllh taya zan fara rayuwa da wanda ko sunan sa bana sonji white tayi maganan tana cigaba da kukan YA ALLAH Ummu yazanyi ? ya zanyi nayi rayuwa da wanda ya gama da rayuwata ina ma YA Allah ya dauki raina kafin yasan ni matar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 40