ai tana mana temako yanzu ga wannan shege doctor din Baban Nasuru yafita dashi kuma wai yaki fadan k'asan ma da zai kai
nifa yanzu abin duk ya dagole min".
Kamal zanyi magana yaji shigowar message cikin wayan sa
yana gani azabure ya mek'e tsaye yace'' what!!!!!!!!!?
A take wani irin gumi yafara karyo masa Karatun ma yakasa
Mama ce ta k'arba ta fara karantawa kamar haka
_slm ya abin kauna na dan Allah Ina neman izinin tafiya amatsayin ka na mijina amma fa ba zaka san inda zan jeba kasan duniya abin tsoro ne Ina gama sai ranan Wednesday zan zo da misalin 11 na safe mu hadu high court I love with all my heart by_
Mama tace'' shikenan Kamal komai ya tsaya asirin mu zai tonu".
" Ah ah Mama hakan bazai taba faruwa ba basu da wani hujjan daura mana ba agan mu Ido da Ido ba yanzu fa nabar Humairah a part din mu Ina zuwa".
Yayi magana yana shirin ficewa Mama tace'' ah ah Habubakar dawo bazaka samu Humairah ba mu samu mafita yanzu ni na yarda zan dauki duk wannan al'hakin kisan da sharrin a kaina kai karayu a hukunta ni".
"Ah ah Mama kwara mu gudu zan kwashe duk kudin mommy na account nata dana Nasir ya shihemu rayuwa zamu gudu k'asar maggep Ina da account ancan kuma da gida da takardan shedan zama a k'asar na har abadan idan muka je zamu shafa assets a fuskan mu kinga daga nan musa a canza mana fuska muyi zaman mu cikin kwanciyar hankalin shi kuma Abdul mu barwa daddy zai dinga tunowa dani".
Mama tace'' good hakan yayi ".
ka ahiya mana tafiyar kawai amma kasa duk company da yake waje akasuwa mu saida dan mu k'ara guzuri".
Nasir tun fitar sa a gida yake yawo idan yagaji ya huta idan lokacin sallah yayi yasamu masallaci yayi har dare a masallaci cin da yayi sallah isha'a anan ya kwana washe gari ma haka ya dinga yawo sa arsa daya shi bame daura hotuna bane a media bai fiye tsayawa yayi fira da yan jarida ba hakan yasa ba wanda yagane shi dan wani ne
saide mutane suna yawan kallon shi har Yana tsarguwa nan ko tsaban kyan shin da hutun suke gani dan Nasir irin farin igbo din nanne me tar kamar balerabe
sai gashi awani anguwar da kamar ba akano yake ba anguwar masu k'aramin k'arfine sosai ishir ruwa ya addabe sa yunwa kam yaji ya cinye shi yana cikin haka yaga wata yarinya tana buga tuk'a tuk'a ruwa Yana fitowa ahankali ya karasa inda take ya mata alama da zai Sha ruwan atunanin sa zaifi wannan ruwan na buta daya ke alwala
dashi wani irin rugawa da gudu yarinyar tayi tabar ruwan da bokatin awajen karasawa yayi yasa hannu biyu cikin bokatin ya ibi ruwan ya kai bakin sa ruwan ya na taba harshen sa yayi wani irin dawo da ruwan har yana zuwa masa ta hanci d'an d'anon bakin sa bai taba bashi abu marar dad'i irin wannan ba zubawa ruwan ido yayi azuciya sa yace toko magani ne wannan baruwa bane
cigaba da tafiya yafara har magaruba yayi tsayawa tsallah yayi har akayi isha'a Qu'rani ya dauka yana karatu har yafara jin garin shiru yunwa sosai ya bara addabar kwara ruwa awajen alwala ya rintse Ido yadan gurba amma shima Yana shiga cikin sa ya amo dadi kaman misalin 9 pm yaji anata hayani ya sai kuma yaji ana cewa wllh layin nan yayi nan yayi sai kuma yaji ance gawani mutum a masallaci sai suka shigo suna cewa shine shene wllh shine daga nan kawai yaji an shiga dukan sa ta ko ina tun yana fashimtar me ake har ya suma
bude idon sa yayi yasamu a gadon asbiti yan sanda akansa ahanhali yamutsa hannu sa da da yake ji kamar ba ajikin sa ba wani k'ara yasa tabbas hannu a karye yake haka k'afar sa daya doctor din ne ya k'araso yace "sorry kabar motsa hannu za ka iya samun matsala kwanan ka biyu anan duka aka maka awani anguwa dalilin kayiwa wata rayanya y'ar shekara 12 fyade kuma kafin wannan ancirewa wata yarinyar Ido daya yarinyar da a ka cirewa Ido tana nan hospital din mun kawota ta guka ta bada tabbacin Kaine ka cire mata ido San nan da yammacin randa kayi fyaden ka Kai wa wata yarinya Maryam hari abakin famfo Allah bayyi ba ta gudu ta barma bokatin itama Maryam tazo ta bada shedan Kai ka Kai Mata wannan harin dan gaka muna son jin sunan ka da inda zamu samu family ka".
"cikin dak'iya yace bani da family ayanke min duk hukuncin da yadace dani.............
*To masoya Ina Humairah taje*
*Mosoyi kuyi hakuri wllh yau ba samu daman yayin typing me yawa ba*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*21*
*NASIR*
Police din yace'' ok kama amsa lefin ka kenan".?
gyada kansa yayi alaman eh
"Ok family kafa Ina zamu same su".
ajiyar zuciya ya sauk'e ahankali yana son ya shafa idon sa da yakeji kamar ba a jikin sa yake ba baya gani dashi sake gwale daya idon yayi Yana kallon doctor din da police din yace''
I don't have any family ".
Palice din yace''please da ganin ka Kai ba k'aramin mutum bane daga yanda jikin ka ya nuna kaidin wani ne kafada mana family din ka suzo wllh ko cell baza kaje ba za akashe cese din anan iya ka Wanda kacirewa Ido su karbi diyan idon su suma na raipping masu k'aramin k'arfine dan wani abu zamu basu arufe cese din dan bakayi kala da cell ba
Kuma idan ka sake report din yaje station to tabbas oga zai turaku court kuma kasan abin da zai biyo baya".
cikin k'osawa da maganan ya ya mutsa fuska tare da cizon lips yaja daya idon ya rude daya kuma a kumbure sosai
police ganin de Nasir bashida niyar magana yayi shiru
*Prison*
ayau Barrister Zahra ta samu daman ganin Nasrim
Nasrim tace
"Zahra nace miki bana buk'atan komai hukuncin kisa shi nake jira idan aka barni a duniyar amfanin me zanyi d'adin mai zanji zan rayu cikin bak'i cikin da k'unci bugu da gari cikin zargi tunda tabbas wasu idan sun yarda banyi ba wasu bazasu yarda ba so mutuwa tafiye min sauki".
Zahra tace'' please Nasy tare muka tashi dake nasan abinda zaki aikata da Wanda bazakiyi ba Nasrim baki kashe Agrif dasu Khaldum ba amma kinason daukawa kanki al'hakin kisan yanzu kinyiwa Agrif adalci kenan duk wani son da kike i'kirarin kina yiwa Haruna wllh ya tashi a banza inde baki tsaya kin gano waya kashe shi ba kinci amanan shi'
jajircewa wajen gano waye yayi wannan aikin shine zai sa Agrif yaji dad'i yayi alfari dake Nasrim ki bamu dama mu gano waye yayi aikinnan
nima sai jiya na tsaya na k'arewa video din kallon a tsinake ba ke bace Wanda yayi kisan bai kai ki tsawon ba yafiki jiki muna da huja da dalilai da zaki kubuta ki bamu dama bawai dan ki cigaba da rayuwa kadai ba a a dan ki gano waye mak'iyin ki ko kinsan Mommy tana cikin matsala Sosai gidan fa kowa yana zargin dan uwan sa kinga kece zaki warware ta hanyan bamu labarin abin da yafaru ko kinsan Mommy da Nasir sun rabu kaca kace ba shiri ya ajiye komai ya tafi"
daganan ha kwashe komai ta fad'a mata amma Banda na yaran na Nasir ne
da daura da kinga kece zaki temaki gidan nan Nasrim bani da dangan taka daku amma acikin gidan three brother na tashi naga kaina Allah yagani bani da wasu dangin da yawuceku kowa yana cikin damuwa Nasrim kece kadai zaki fitar mu aduhun da muke ciki please Halima".
numfashi Nasrim tayi tace'' amma mommy da bata zargi d'an taba Nasir yana son Agrif musamman su Fayyat bazai kashe su ba duk da bamu so da shak'uwa tsakani na dashi bazan iya zargin sa da haka ba sai idan ko a ma'aikatan gidan wani yake son ganin bayan mu".
Zahra tace'' yauwa to Nasrim hadin kan ki shi zai fitar mu cikin wannan ko kadan ki bamu wani haske".
ajiyar zuciya Nasrim ta sauk'e tace'' Zahra ko banyi ba nayi ne FURUCINA NE tabbas nayi FURUCIN sai na kashe shi amma wllh adare Haruna ya sameni da wuk'an da na masa barazana a hannun sa yace Halima gani ki kasheni inde zaki iya to ki kasheni na kasa bacci barazanan ki yabani tsoro da mamaki wai Halima yau kece da wuk'a ahannu kina i'kirarin zaki kasheni bayan ni kece nafison kirayu fiye da komai
atake na fad'a jikin sa na fara kuka Ina neman yafiyar sa tureni yayi ya jefanin wuk'an wai dole sai na kashe sa daga k'ashe de muka sasanta ya yafemin nima na yafe masa har zan bishi d'aki mu kwanta yace Ah Ah nabari nayi kwanciya ta tunda nayi masifa ina buk'atan hutu idan ina kusa dashi bazai barni ba amma da asuba yana jirana ganin nima tabbas ina buk'atan hutun na barshe ya tafi kawai sai da asuba na tashi da wani irin faduwar gaba kamar a mafarki nake jin kuka a d'akin su Fayyat ina shiga naga an musu yankan rago sai kuma Khafulan yace' nice shikenan iya abinda zan iya tunowa kenan kuma nasan Khafulan baya k'arya ban san ya akayi na k'ashe su ta yaya da yaushe akan me zan kashe yarana zahra duk duniya waye zaji ciwon rashin su kamar yanda nake ji yanzu zahra shikenan ba khadum ba Fayyat da gaske tafiyar kenan Agrif ma babu ".
ta k'arashe maganan tana sakin wani irin kuka
Zahra ta share hawayen ta tace'' Nasrim waye ya ganki da dress din ki na karshe".?
"Zahra wannan kuma wane irin tambaya ne".
Zahra ta zaro wayan ta a cikin jaka ta kunnwa Nasrim video din ta mek'a mata sai ayau ma Nasrim ta san da wannan lalle kowaye yayi wannan aikin dan ya jefa rayuwar ta cikin wannan halin dama yayi kuma gashi Allah yabashi sa'a...
"Ah ah Nasrim ki dena cewa Allah yabashi sa'a Allah baya barin hakkin wani akan wani musamman hakkin rai ran ma na yara k'anana da basu jiba basu gani ba Insha Allah Allah zai tona asirin su".
"Zahra kinga fa mutumin yayi amfani da kayana yayi amfani da FURUCINA yamin kyakkyawan kamu ya zanyi na fita kiga fa yanda akayi abin kamar nice ya za ayi na fita".?
"please Nasy zaki fita kirayu kamar kowa zakiga mak'iyin ki
ni zan wuce nasan ma zan sake zuwa kafin lokaci amma barrister Fu'at Jiji da Barrister shashid sune lawyer din ki nida Humairah da Nusaiba kuma zamu temaka musu".
ta k'arashe maganan tana shafa kan lil Agrif da yake bacci a cinyar Nasrim
*Izza da Baban ta*
cikin wani irin tsawa Baban Izza yace'' Izza lafiyar ki ni zan saki aiki kice ke bazakiyi ba ni".?
"Eh Baba bazan iya kisan kai ba Baba Al'hamdulillah meyeAllah bai min ba zanyi butulci Baba narayu cikin ni'imar cikin wadacecen illimi Allah yamun baiwa da mafi kirman baiwar ya bani Al Qu'ranin sa mai girma wan bakowa yakeyiwa baiwar hakan ba amma na butulce na kashe rai Allah yafi kowa son ran bawan sa taya zanyiwa Allah butulci wajen dauke wannan ran Baba abinda yasa na biye maka nun farko saboda son Agrif ne Allah bayyi auren na dashi ba na auri k'anin sa badan Allah yaciremin son Agrif ba "Ah Ah dashi nake yayuwa sai gashi dare daya Allah ya dauk'e mijina atunani na dan burina yacika na auri Agrif ne yasa Aiban ya mutu na biyeka kake duk wannan kulla kullan amma bawai zuciyata tayi bushewar da zan iya kashe rai ba
mek'ewa tsaye tayi tana kallon Baban ta tace'' Baba kasan abinda yasa na biye muku bayan rasuwar Agrif dan na gano waye ya kwashe Agrif ne nasan Nasrim bazata taba iya kashe shiba kuma Al'hamdulillah na gano ayanzu aikina zai fara sai na bayyana wa duk duniya waya kashe Agrif sai na d'auka masa fansa ko shine karshe abin da zanyi a duniya ne sai na cika burina Agrif salishin bawane jinin sa bazai tafi a banza ba".
ta k'arashe maganan tana juyawa zata fita
cafkota yayi ya wurgar da ita yace'' kikace kin gano waye kina nufin bazaki mai da hankali ki auri Kamal ba kenan?".
cikin tsoron yanda idon Baban nata yakoma Wanda zai iyayin komai ma tace'' ah ah Baba zan aureshi".
"to waye ya kashe Agrif".?
cikin in Ina tace'' ban gama binciken ba zan gaya ma idan nagama".
komawa yayi ya zauna yace'' Izzatu nasan kinsan Kamal ne yayi duk wannan kisan to Wllh karkiyi gigin tona masa asiri ki bari ayankewa Nasrim hukuncin a kashe ta bayan an kashe ta sai ki fito da duk hujjojin da zai nuna Kamal ne yayi kisan shida uwar sa kinga shima Kamal za akashe shi dukiyar zai koma wajen Abbaty kanin mijin ki anan zanyi aikin da dole sai Abbaty ya aure ki kinga komai zai dawo hannun mu ankusa ki daure akwai nasara rayuwar ki fari ne tas Ina hangowa haske acikin rayuwar ki".
Izza wani kallon baka da ilimi tayiwa Baban tace''to Baba amma yanzu bazan iya kashe Mommy ba abari sai bayan Shari'a zanyi duk yanda ka keso".
da haka Izza ta lallaba Baban ta ta fota
*Kamal da Mama*
"Mama na gama kwashe duk kudin nan na cikin account din mommy amma na Nasir ne ban gano ba kinsan shege ne Mommy kuma nayi duk da bara tace ba yanzu ba na bari asamu nutsuwa sata gayamin password din daya account din shima akwai manyan ajiya aciki ".
Mama tace'' duk ba wannan ba ko kasan munyi waya da K'aura yace kar mu tafi idan mun sake mun tafi kwai matsala amma yanzu yace muyi zaman mu zai haukatar da Humairah kuma bata gayawa kowa ba kayan yana hannu ta yanzu abin da nake so dakai kaje wajen uwar ta kasata agaba kace kund'an samu tsabani da Humairah ta dugu dan Allah tagaya maka inda take kaje ka sameta sokuwar fada maka Inda take zatayi sai musan abinyi".
*************
Kamal da Ummu
Ummu tace
"ikon Allah wai dama tsabani kuma samu kai da ita ai ban sani ba nide ta cemin zata je Kaduna gidan Balaraba dama nayi mamaki da tace min zata kaduna dan ita ma Balaraban yau zata bar k'asan zuwa saudia duba Abun ku
Humairah kenan shiyasa ta barmin wayoyin ta anan dan karma kane meta to tana gidan Balaraba". ta k'arashe maganan tana murmushi
jumm Kamal yayi yace'' amm Ummu ina wayoyin nata to?".
zuciya daya Ummu tace'' yana d'aki ta mek'e ta dauko masa
Murmushi Kamal yayi yace'' thanks Ummu amma dan Allah kar ki gaya mata gani nan zuwa dan zata iya canza waje yanzu zan wuce Kaduna gidan Aunty BB".
Kamal direct wajen Mama yasake komawa yace'' Mama komai yazo mana da sauk'i tana gidan wannan ma tsiyaciyar k'anwar uwar ta ta Balaraba kuma wai Balaraban sun tafi dubo Abu ita da mijin ta kin sa ba masu gadine da su ba agidan ba ma tsiyata
zansa yanzu amin kidnappers dinta kafin naje idan naje nakira uwar ta nace banga Humairah ba kinga zamu b'atar da ita cikin sauk'i ga kuma wayan acikin na dauki wasu tsirrika dayawa har".
"Shikenan Kamal Allah yasa bata gayawa kowa ba".
murmushi yayi yace "ai Mama aikin K'aura yana tafiya yanda yakamata amma.....
jin sallaman mommy ne ya katse masa maganan
Mommy cikin tashin hankali tace'' Kamal ya akayi kudin general account din
na duka babu kuma meyake faruwa?".
da sauri Kamal ya mek'e tsaye a zabure ya zaro ido yace'
"babu kuma mommy kamar yaya da sa hannu wa aka cire kuma?"
Mommy Zama tayi a kujera twositer tace'' da sing dina wai amma transfer akayi zuwa account na company nan Nigeria".
hannun Kamal ya d'aura akai yace "ai Mommy d'a zunnan naga an kwashe kudin company gaba daya dan haka kudin ko rabin ma'ai katan da suke iya cikin gidan nan ba bazai biya ba balle na company kuma ba Wanda zayyi wannan aikin idan ba Nasir ba".
Mommy tace'' Nasir! Nasir ! Nasir!".
"Mommy please kiyi hakuri mu bar shi da Allah mufuskanci yanda Shari'ar Nasrim zata kasance dan shine a gaban mu akwai kwararun lawyer da nasamu insha Allah za adace".
Mommy tace'' kai Kamal Allah de yabar zumunci ko bayan Raina Nasrim ta b'ata maka ban yafe mata ba".
"Ameen mommy zanje Kaduna dauko Humairah wai rigima take min Sosai akan sai na goyi bayan su a Shari'a nace ah ah shine ta nace sai na saketa wllh badan Abu da daddy ba da zanyi yanda takeso nagaji zan iya rabuwa da ita akan Nasrim kwata kwata kwanakin nan ta hanani kwanciyar hankalin".
girgiza kai mommy tayi tace
"Ah Ah Kamal kayi hakuri duk rashin fashinta ne itama tana da gaskiya rashin dan uwa tayi abin akwai ciwo fatan mu de gaskiya ta bayyana kowa ya gane Nasir ne ya aikata wannan aikin a kamoshi aduk inda yake a hukunta shi akan kudi ban zaci Nasir zanyi haba yayi surprise dina inda tun farko kudi yake so dana bashi mun tsira da lafiyar mu da mutumcin mu ni duk nafi tunanin makomar Zainab da Khafulan ko d'azu saida Hajiya Amina ta korosu wai su tafi dangin shegu wllh nafi jin su
su kam su Fayyat da suka tafi ai sun huta".
ta k'arashe maganan tana sakin kuka kamar kullum
hakuri Kamal da Mama suka shiga bata
**************
Dr Hafsa da Mommy
Dr Hafsa tace'' Dr Fanna kinyi gan gancin me yasa zaki dauki duniya ki dan kawa Kamal shi Kamal ba dan Adam bane wanda zai iya can zawa asanda yaga dama nifa zargina bancire kowaba a cikin gidan nan ina guje maki nadama yanzu har idan Nasir zai kwashe miki kudi zai barmiki nashi yatafi nifa nake gani kamar wannan abinda yafaru ya taba kwakwanki".
cikin b'acin rai Mommy tace
"Dr Hafsa idan ba temakona zakiyi ba kidena rabanin hankali Sam banga wani abin da kikayi Wanda zai temaka min ba sai Aisha da Kamal su
suke fafutukar akan Nasrim tunda wannan Abu yafaru dan haka ki bari naji da abinda yake damuna ni na gamsu da son da Kamal yakeyiwa Nasrim kinga fa yanzu har sun tsamu matsala da matar sa akan cese din".
girgiza kai Dr Hafsa tayi tace'' banga lefin kiba dan ayanzu dake da wanda ruwa yacisa daya kuke ko huta akace ki kama kamawa zaki amma.....
dakatar da ita mommy tayi tace'' stop Dr".
Kamal
cikin karayan murya Kamal yace'' please Ummu dan Allah ki tambayi min Aunty BB mana kode tare suka tafi da Humairah bata gidan nasu bokowa ba agidan".
Ummu tace'' Ah ah yanzun nan muka gama waya da Balaraba sun sauk'a basa tare amma Kamal ka kwantar da hankalin ka tasan zan gaya maka ne yasa ta canza waje amma de a gidan suka bar ta duk inda take bazata wuce kwanaki 5 ba zata zo kodan wannan Shari'ar da ta kwallafawa rai zata zo dan shi yahana taje duba Baban ku ma kayi hakuri kwanakin nan tana cikin damuwa kayi hakuri kafin nan ma zata dan samu sauk'i insha Allah Allah de ubangiji ya kawo mana sauk'i wannan Abu".
ajiyar zuciya ya sauk'e kamar gaske abin yana damun cikin
sanyin murya yace" Amin Ummu".
Yana kashe wayan yace Madam keda y'arki sai a *darussalam*
Al'hamdulillah komai yana zuwa min cikin sauk'i alokacin da nake so yanzu ba batun guduwa
yayi magana yana daddana wayan sa
ana dauka yace "Gagare cika'aiki tafadad'i Wanda tagayawa ne".
"Allah ya temaki oga tace ita kadai take aikin ta kuma kaya ta k'onasu baya wajen ta''.
murmushi yayi yace"k'arya take ku bata azaba ku sata a bencin sama har sai ta fadi gaskiya".
ya kashe wayan yana kiran lawyer din Nasrim yana dauka yace'' barrister Fu'at Jiji nine Habubakar Abdulmajid wanda da cese din k'anwa ta yake hannun ka ina son zan dan ganka kafin lokacin".
Barrister haryayi shiru de yace'' ok Ina zamu hadu".
Kamal yace yanzu ina kd amma zuwa dare kafadi inda zan sameka".
*Kotu zama na farko*
tacika makil
bayan maga takadda yayi bayani kotu ta buk'aci lawyer su gabatar da kansu da shedun su
aka mukaci lawyer mai k'ara yafito idan yana da tabaya
Lawyer ya kalli Nasrim
yace'' muna son ki fad'a mana sunanki".
"sunana Halima Abdulmajid Haruna".
"Ok Halima adaren ranan 8 ga watan 3 da misalin 12 pm kina ina".
"Ina gida".
"Mijin ki fa?.
"shima haka".
"Ok da yaushe yazo gida tunda ranan yakama ranan Monday ne ranan aiki".
"da misalin karfe 12 ya shigo".
"Halima ayanda CCTV ya nuna mana Yana shigowa kiyayi inkurin kashe sa hakane".?
"Eh anyi haka".
juyowa Brr Zayyat yayi Yana kallon Mai Shari'a yace'' ok my load Halima ta amsa lefinta na yunk'urin kashe mijin ta Haruna Ina son a saka wannan memory din na cc din gidan ne shine babban sheda na Halima Abdulmajid Haruna ita ta kashe mijin ta Haruna Abdulrahaman Haruna".
take aka saka memory amma daga inda Humairah take zuwa ta gaya mata Izza ta daura hoton Agrif zuwa inda take barazana sai ta kashesa video yake tsayawa
Sai sheda na biyu wayan Khafulan da
sheda na ukku
sak'on tes message da Agrif ya turawa Kamal
Lawyer me k'ara yace " bisa watan nan kwararun shidu da muka gabatan a gaban wannan kotu Mai albarka muna neman kotu ta yankewa Halima Abdulmajid Haruna hukuncin kamar yanda Shari'a musulumci t...........
Azabure
Zahra tace'' objection my load Barrister Zayyat yana daurawa wanda muke karewa lefi kai tsaye batare da kwararun shedu ba idan Halima zata kashe CCVT daga 1 na dare zuwa assuba bazata furta barazana agaban Humairah wanda k'anwar shi marigayin ne ba kuma bazata furta agaban Habubakar Abdulmajid ba sannan da wajen da zata kashe mijin ba ta buk'atar kashe CCVT kuma har idan tana da
da baran kashe CCVT ai zata iya deleted din inda tayi barazanan my load mu
mukeda kwararun shedu da yake nuni da Halima ba ita takashe mijinta Haruna Abdulrahaman da yaran Abdulmajid da Abdulrahaman ba".
Alk'ali ya d'ago kai yace kotu tana buk'atar shedun Halima Abdulmajid Haruna".
da sauri Barrister shashid ya mek'e yace'' my load muna neman k'arin lokaci dan samun isowar shedar mu Aisha Abdulrahaman Haruna bata samu isowa ba".
Alk'ali yace "Kotu ta bada dama kafin ta dawo a hutun rabin awa".
Zahra hankali tashe tace'' Kamal wai Ina Humairah idan Humairah bata zoba za a iya samun matsala fa dukan shedan mu yana wajen ta akwan kyawawan hujjojin da shedu a hannun ta".
shima Kamal cikin tashin hankali yace'' Zahra wllh shiru ba labarin ta".
Mommy tace'' wai kun barni aduhu Humairah ce zata bada sheda akan Nasrim batayi kisan ba".
Zahra tace'' Eh mommy Tasha wahala akan aikin kuma mu bata gaya mana komai ba tade ce sai ranan Shari'ar ta tabbatar min da wannan shedan hannu ta kad'ai ne zai fidda Nasrim".
hankali lawyers din Nasrim idan yayi dubu yatashi alokacin
da aka buk'aci a koma d'aki Shari'a
kai tsaye alk'ali ya nemi shedan Halima akace bata k'araso ba
gyaran murya alk'ali yayi yace'' adalili rashin sheda na Wanda ake zargi da kuma duba da kwararun shedu da masu Kara suka bada kotu ta...............
*Muje zuwa ina Humairah Ina Nasir ina Izza mu hade a page 22*
*ngd sosai da comment naku*
*Bj*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
( _rikicin babban gida_ )
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
*22*
"Objection my load sunana Barrister Aisha Abdulrahaman Haruna ni k'anwace ga marigayi Haruna Abdulrahaman Haruna
wacce ake zargi da kashe d'an uwana Haruna da yaran sa biyu ba ita tayi kisan ba Ina son kotu ta bani daman ga batar da sheduna ina
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 40