kokarin haka dan ta CC TV yakamata muga komai amma an goge abinda yafuru daga 1 na dare zuwa karfe ukku darabi amma daga abinda muka gani na k'arfin hudu na yamma zuwa 12 na dare ya gamsar damu ita tayi kisan dan cc tv yanuna tun 12 taso ta kashe sa bata samu da ba ta kashe CC TV kafin taje tayi kisan saide marigayi Haruna yayi mata video a wayar sa alokacin da zata kashe sa tana sanye da likaf sai
Lokacin da zata Kashi yaran akwai yaron da yasamu ya tsira shima yayi video din a sanda ta kewa yan uwansa yan kan rogo amma abinda bamu gane ba shine meyasa ta kashe CC TV bayan da farko ta nuna bawani boye boye acikin aikin ta meyasa ta bari Haruna ya mata video meyasa ta sanya likaf bayan ita a bayyane take cewa sai ta kashe sa kuma yanzu ma duk tambayar daza amata cewa take ita ta kashe su dan haka gobe za a turaku kotu gomnati ta dauki nata lauyoyin sannan daga yan uwan mamatan ma sun dauka".
bayan tafiyar yan sanda Hajja tace " insha Allah gobe iwarhaka itama tazama gawa wllh sai de idan Legos din naki zaki kaita ayi jana'izar ta amma ba d'ana daya da zai mata sallah ban yafe ba".
Mommy tace'' in Allah ya yarda baza ma ta mutu ba nan da 50yrs Nasrim tana nan".
"Hajja tace'' ke tubebbiya ni zaki gayawa magana to abinki ya isheni ina gama da hadin bakin ki y'ar ta ki tayi aika Kai kan na
Abdulmajid idan na amsa sunan uwa a gurin ka ayanzu ba sai an jima ba kasaki wannan tobebbbiya taje can ta k'arata yanzu nake son ka saketa".
A tare Humairah Mama Ummu Abu suka mek'e har Kamal suna cewa subbahanalla Hajja abin har yakai haka
" yafi ma zaka sake ko sai na tsin.....
da sauri daddy yace "ni Abdulmajid Haruna nasaki matata Fanna emake saki daya".
"to kinji kifita kibar mana gidan mu ni idan kina ciki gidan hankalina bazai taba kwanciya ba".
dariya mommy tayi tace'' nafita fa kikace ai sai de nafitar daku kin manta gida nawa ne
Hajiya Maryam kinyi kuskure da kin bar auren d'an ki akai na dalilin auren d'an naki Ina iya raga miki amma yanzu nida ke ba komai a tsakanin mu yanzu zaki ga aikin tubebbiya kum.......
wani irin mari daddy ya zuba mata yace "ashe baki da mutumcin".
Mommy tace'' dani daku zaman shekara 32 bakusan bani da mutumcin ba sai yau akan y'ata ba abinda bazan iya ba".
Abu yace" au Dr Fanna duk kawai cinda nake miki agabana kikace haka to wllh za a hukunta Nasrim kamar kowa tunda duk bayanai sun nuna ita tayi kisan".
Mommy tace'' hakane mu hadu a court kawai ta
fice da sauri Kamal ne yabi bayan ta Saida suka k'arasa har parlour yace
"Mommy kinga Shari'a nan fa gobe ne kuma lauyoyi kusan ukku gomnati ya suba sannan ga shi acikin gidan nan an dauki kwararrun lawyer har 5".
shiru mommy tayi can tace'' to Kamal yanzu kana ga ya zamuyi?.
"mommy dama ai dazu na miki magana Barrister Lawan Zakar
da kuma Barrister Ishak Hamza suna da kwarewa insha Allah zamuyi nasara" .
Kuka mommy tasaka tace'' na gode Kamal Kai da mahaifiyar ka kun zame min garkuwa arayuwa".
"Mommy saide Barr Ishak ya gayamin Nasrim zata iya basu matsala dan jiya kusan wuni yayi awajen ta duk tambayar da yamata kawai cemasa take ita fa ita takashe mijinta da yaranta biyu akashe ta wannan shi zai iya sawa muyi rashin nasara".
Kutu
Court tacika makil har waje yan jarida ko ba amagan iyalan three brother sun hadu awajen makil bayan maga takarta ya gabatar da Wanda suke kara da wanda ake k'ra
wanda take k'ayar itace Hajiya Maryam Habubar Dardum
tana Karan Halima Abdulmajid wanda ta kashe mata jika da yaran sa 2
mommy kuka tayi alokacin da aka wuce da Nasrim da handcuffs a hannu yar sanda macce ta rike hannun ta taja mayafin ta rufe fuskan ta dashi Dr Hafsa tace "please Dr
My Mai shara'a ya nemi lawyer me kara ya gabatar da kansa
"sunana Brr Zayyat Inuwa atare dani akwai Barr Izzatu Mustapha sai Brr Alfa Ibrahim da kuma Barrister farida moddibi duk baris tocin sikayi gaisuwa ga court
sai lawyern wanda ake k'ara "sunana Barrister Ishak Hamza atare dani akwai Barr Hawwa Adamu sai Brr Lawan Zakar mune lawyer Wanda ake K'ara bayan suma sunyi gaisuwa aka buk'aci lawyer me kara
Izza ce tafara fitowa
tana gyara riganta na lauyoyi ta k'arasa gaban Nasrim ta dafe dan d'an gajeren d'akin katakon da Nasrim take ciki ta cefa idon ta cikin nata tace'' HALIMA ABDULMAJID HARUNA ko ?
gyad'a kai Nasrim tayi
Izza tace'' baki zaki bude kiyi magana".
Nasrim tace" Eh nice".
"Ok yanan 7 ga watan 3 da misalin karfe hudu na yamma kin bude status din mijin ki Haruna Abdulrahaman kin kaga ya d'aura hoton wanda zai aura da kallama kamar haka
_ko rana da wata zasu dena haske gimbiya ta sai ke soyayyar ki har har abada_
kin bude status din da misalin
karfe duhu da rabi
Kika masa Ripley da
_lalle kam zaka dena ganin hasken ayau_
sannan kika dauki hoton sa dana wanda zai aura kikayi kansil kika saka R I P
yana komawa gida kin gaba wasa wukar ki kamar yanda danki ya bada shida kika fara masa barazana bayan yabaki hakuri ya kwanda kika je kika kashe yaran sa shima kikaje kika kashe sa ta hanyar luma masa kuka har sau ukk...
cikin zafin rai Brr Ishak Hamza ya tashi yace objection my load
Lawyer me kara nata son daurawa Wanda nake karewa lefi bayan zargin ta ake fuskan ta arufe yake a sanda ake zargin tayi kisan dan haka ba kai tsaye ba me cewa ita tayi kisan".
Alk'ali yace
"Brr ki canza salon tambayar ki".
agurguje de anyi gobza Shari'a kamar lauyoyi zasu dambatu daga k"ashe de lawyer me kara sukayi nasa ra
Kotu tayankewa Halima Nasrim hukuncin..............
*kuyi hakurin jina shishur jiya sorry*
*Batul jattko*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
_rikicin babban gida_
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*Masoya ba abinda zan ce daku akan yanda kuka dauki wannan littafin na FURUCINA NE Ina godiya sosai da comment din ku Allah yabar kauna masu Kira da musu yimin tes message ngd BJ takuce* 🤝
*Masu yimin fatan Al'kairi har a bayan ido na nagode da adduar ku Allah yabar kauna* 🤲
16
anyan ke mata hukuncin zaman rai da rai a gidan yari tare da huro me tsanani Alk'ali Abdulmajid ya mek'e tsaye duk mek'ewa akayi ana court yafice ta k'ofar sa
mommy mek'ewa tayi tsaye tasa kuka tana maimai inna'lillahi'wa'ain'na'ilaishirajju
Allahumma ajirni fii musibati'wa 'aklifna khairan minha".
Kamal da Ayman ne suka rik'eta ita ma Dr Hafsa kukan tasa tana ta maimaita addua
haka Mama Ummu bata nuna komai ba haka Abu ma sunkuyar da kansa yayi sai Hajja da tace'' Al'hamdulillah horo me tsanani kuwa ciki harda fasa dutse da ginin suminti da duk wani aikin wahalarwa".
Izzatu murmushi suke ita da sauran lauyoyi da sukayi nasara cikin fara'a ta mek'awa Barrister Hawwa Adamu hannu shima Barrister Ishak Hamza ya mek'awa Barrister Zayyat hannu
Mommy kuka take sosai nata mek'a hannu har aka kama Nasrim aka fita da ita
Nasir wani irin k'ara yasa yace" no no impossible bazai yuwu ba wannan hukuncin bayyi dai dai ba ya za ayiwa Wanda ta kashe rai ukku za ayankewa hukuncin rai da rai wllh sai mun daukaka k'ara an yanke mata hukuncin rataya shine dai-dai da lefin ta wannan yayi sassauci ba a mana adalcin ba".
Hajja tace'' oho nima de haka naga amma da babu ai kwara ba dadi da anbiyewa lauyoyin ta baso sukayi su nuna bata da lefi ba amma namu lauyoyi suka fi karfin su ai babban shiri akayi dan abar shegiya tana yawo Allah yaga zuciyar mu".
Khafulan ma kuka yasaka yace "Papa dan Allah kace su kawomin mamy ni yanzu naji tausayin ta kaga ko fuskan ta ba agani tarufe kuka take ko Ina za akaita Dan Allah papa kasa a kawo ta baza ta k'ara kashe kowa ba wayyo sukawo min mamy ta mamy tarame mamy na Papp".
ya fisge daga hannun Nasir yafiya da gudu za asata a mota yayi saurin rik'e mayafin ta juyowa tayi ahankali ta sunkuya dai-dai tsayin sa hannu yasa ya janje mayafin a fuskan ta cikin kuka yace "mamy kiga idon ki ya kumbura mamy kizo muje gida na dena fada dakowa bazaki kasheni ba ko mamy gidan ba dad'i ba Fayyat ba khadum kema bak'e nan"?
zuba gwaiwoyin ta tayi a k'asa ta dafe kafadun sa cikin rawan murya tace " Abdulsamad dan Allah kayar da bani na k'ashe mahaifika da yan uwan ka ba".
"Mamy kece mana".
cikin hawaye tace "shikenan Abdulsamad ka yafemin kaji idan kayi sallah kayi tamin addua".
"Mamy ai Papa dina ma yace na miki addua".
shiru Nasrim tayi can tace'' ok Ina Zainab".
yace "Zeenat an kaita gidan mom Hafsa tunda bakyanan ". dafa kan sa tayi
"Allah ubangiji ya maka albarka Abdulsamad Khafulan Allah yakaren min kai da k'anwar da kuka ragenin ya Rabbi Allah na gode maka da ka tsiratar min da Zainab da ABDULSAMAD ya Allah kacigaba da karemin su ba dan wayo ko da baran bu ba sai dan yaruwa a hannun ka take ya Allah duk me shirin cutar da su kar ka bashi sa a k.....janye ta police din tayi tana kuka suka danna da amota dai-dai lokacin da akafito da mommy motan su Nasrim din yaja mommy sake fashewa da kuka tayi tace'' NASRIM".
Nasrim leko da kanta tayi ta window tana girgizawa mommy kai har suka fice Dr Hafsa ta kama mommy aka shiga da ita mota".
Three brother kam kan kowa ararrabe yake kowa da abinda yake fada dakuma abinda yake tunani wasu suna bayan mommy wasu suna bayan su Hajja itade Ummu bazan ce ga inda take ba Amma de duk yawanci cewa ake Nasrim ita tayi kisan Mama da Kamal ne kawai suke bayan mommy
Knocking din da aka matsa dayi ne yasa mommy tace shigo a tunanin ta Nasir ne cikin mamaki take kallon sa
tashi tayi zaune tana gyara sleeping dress dinta cikin b'acin rai tace'' meya kawo ka part dina bayan sakin da kamin".
ahankali daddy yake takawa zai k'araso inda take da sauri mommy ta sauko daga kan gagon tace'' wai meye haka Abdulmajid".?
"doctor ina son muyi magana na fashimtar juna nidake".
"Abdul bawani magana da zamuyi a tsakanin mu kafin ayi zaman kotu har kuka namaka akan katsaya ka saurareni Nasrim bata da lefi bak'i kayi ba sai yanzu da aka gama Shari'a meyayi saura ba kayan ke mata hukuncin rai darai ba dama aure da Nasrim ne a tsakanin mu yanzu Nasrim ta zama tamkar babu auren mu ma babu to meye yayi saura".
"doctor kina tunanin kinfini shiga tashin hankali ne ko kinfini son Nasrim duk da ina da Kamal Allah yasani kema shedace Nasrim daban ce a guna shak'uwar da nayi da ita ke bakiyi ba ninasan wacece Nasrim ba yanda za ayi ta iya kashe rai kema kinsan wannan wata kulleleniya ce me wuyar kunce wa amma iya adalcin da zan iya yiwa Nasrim hukuncin rai darai idan Allah yayi asiri zai tonu kuma ina bincike a hankali a hankali insha Allah za a dace dan gaskiya bata k'arewa kuma ba ataba ganin bayan me gaskiya nawa zanyi shara'a irin wannan daga baya asiri ya tonu azo asake sabon zama mai gaskiya yayi Nasara
ganin ki kuma da banyi kafin lokacin anyi mugun sa Ido ne akan mu idan na ganki za'a iya zargin wani abu madam ina cikin damuwa fa over maganan saki kuma ni na maidaki amma banason kowa ya gane".
bata fuska tayi tace
"gakiya nide ban maidu ba".
"Ok haka ma kikace to bari kiga".sure
yayi maganan yana jawota jikin sa a wajen de ya maida auren su amma da alk'awarin ba wanda zasu gayawa sai komai yalafa
bayan komai ya lafa daddy ya kalli mommy yace dan Allah doctor duk abinda Hajja zata gaya miki karki sake tanka mata kinga yau ma sai da tasake maimaita min kalman da kika fada wai _yanzu zata ga aikin tubebbiya_
kinga sai mai Mai tawa take wai duk abin da yasake samun wani a gidan nan to kece ki dena irin wannan FURUCIN kinga shi ya jefa rayuwar y'ar mu cikin wani hali sannan shadadu da mugayen mutane suna amfanin da harshen MUTUM su cutar da mutum kin gani akan Nasrim
san nan wani sahabbi yacewa Annabi kamin nasiha sai yace ka kiyaye hashen ka har so ukku suna haka da annabi kinga *SHARSHE* musifa ce".
Ido mommy ta zaru tace
"au haka tace ni gaskiya ban san me nayiwa matar nan ba ta tsane ni kawai dan na kasance yar k'abilan Igbo Allah yana ji yana gani duk Wanda yanufeni da shari insha Allah kansa nasa kullum ana ciyar da almajirai dubu kuma ana yanka shanu 3 da raguna 10 ana rabawa mabuk'ata Allah yakare min y'ata da jikokina da ni kaina kuma insha Allah inde Nasrim tana da gaskiya baza ta shekara a pirson ba".
Daddy yace insha Allahu".
**********************
washe garin ranan
Kamal ya samu daddy a parlou sa yana duba filet din wani cese me zafi da zayyi shima na lefin kisan kai ne Kamal yashigo ya zube a k'asa ya gaida shi yayi shiru daddy ture littafin gaban sa yayi yace Habubakar sadik Baban Hajja Abban Abdulsamad d'an Aisha mijin Aisha me yake damun kane duk karame ka k'ara duhu".
Kamal kamar yanajira ya fad'a jikin daddy yafashe da kuka yace "haba daddy yanzu y'ar ka zaka yankewa wannan hukuncin daddy Nasrim ba ita tayi wannan kisan ba dan Allah daddy ka ceci rayuwar y'ar uwa ta ita daya gareni".
shiru daddy yayi can yacire farin gilas din idon sa ya janye Kamal daga jikin sa ya dafa kafadun sa biyu yace Kamal nake yanke hukunci akan y'ay'an wasu ma balle y'ata da tayi abin agida nasan komai ai alkalanci agida ake farashi ba kana hawa Media ba ai kana ganin abinda mutane suke fad'a ko inda nabawa Nasrim gaskiya me duniya zata cemin wannan abin fa duk duniya yanzu zancen da ake kenan kasani".
cikin kuka Kamal yace'' to Daddy akan wasu mutanen duniya za kayiwa y'ar haka a koreka a aikin mana saime da de ace k'arasa y'ar ka".
"to Kamaluddeen Allah yawuce mana gaba amma idan ba Nasrim bace tayi kisan waye yayi ? Kai ne makotan su ko dawani Wanda kake zargi ".
"ni daddy bana zargin kowa amma dan Allah asake bincika wa kuma daddy dan Allah Ina neman alfarman amaida auren ka da mommy".
Daddy ya kalli Kamal yace "ikon Allah wai Kamal meye damuwar ka da auren nan neka kafa matsa da yawa".
"Daddy dole na damu ganin halinda mommy take ciki yaka mata ace an sassauta mata tawani fannin bawai a gujeta ba".
"Ok Kamal ba agaban ga mahaifiya ta tabani umarnin na sake ta ba kuma kaga tace na maida tane itama Fanna ai bata kyauta ba bakaji FURUCIN da tayiwa Hajja ba wai Hajja zataga aikin tubebbiya".
"
Kamal yace amma Daddy dan Allah kayi hakuri ka maida ta".
cikin k'osawa da maganan daddy yace Kamal bazan maida Fanna ba bani ba ita har abadan....
cikin wani irin razana Kamal yace "inna'lillahi daddy komai ya tashi kenan......
shiru yayi bai k'arasa ba".
cikin mamaki daddy yace meye ya tashi".?
cikin in Ina Kamal yace "ammm ummm Daddy sa santon da nake son nayi".
"Ok bahali bazan iya bai da taba".
Kamal gaban Hajja yaje yazube yana kukan a maida auren daddy da mommy
Hajja tace'' niko yaron nan ko uwar ka Aisha aka saka bakin abinda zakayi kenan nake ganin kamar duk damuwar gidan nan bai dameka kamar mutuwar auren kishiyar uwar ka ba kajini da yaro da jaraba kode kwadayin dukiyar ta kake saboda idan ta mutu uban kane mijin ta shi zai gajeta kai kuma magajin uban ka ko shiyasa ka damu a maida auren ko".?
"Subbahanallah Hajja wannan din wane irin magana ne Allah ya sauwake mommy tafi haka a guna ita ma uwace ke sai ana maganan arzik'i ki ballo topic na wargaza kwakwalwa".
ya k'arasa maganan yana mek'ewa tsaye
Hajja ta harari bayan sa tace'' ka kawo min wani maganan banza wata tubebbiya ai ni ce dai dai da ita har ta zauna tana FURUCIN zanga aikin tubebbiya ai saide naga al'kairi ni dinnan Ina nan har sai naga jikojin NASURUDDEEN nawa ikon Allah Nasara me wuyan fadanci ".
ta k'arashe maganan tana cewa wai Zaliha ina abincin nawa ki kawo min nan tunda gida de a hargitse yake kowa gaban sa kawo min nan duk dama abincin ba shiga yake ba."
Izza cikin takunta na isa take takawa zata wuce ta compound din Humairah
Humairah tana zaune nata chat ta d'ago kanta ta kalli Izza tace'' ke Izza zo nan".
murmushi Izza tayi tana maimaita zonan "wannan Kira haka Hajiya Humairah sai kace a secondary kin samu Junior's ko irin kin samu girls house din nan to gani".
Humairah ajire wayan ta tayi a akan kujeran da ta tashi ta jefa idonta cikin na Izza tace'' Izza me tsakanin ki da Ya kamal jiya da yau na ganku atare".?
murmushi Izza tayi tace'' idan macce ta cika macce bata damuwa dan an rab'i mijin ta
Dariya tayi taciga da cewa'' Ko da yake da gaskiyar ki macce kamar ni dole ko wacce maccen taji tsoron na rab'i mijin ta".
Humairah tace'' ke jaka akuya karya dabba annoba aike anno bace ba wanda zai so ki rabeshi kin wari Yayana ya mutu anyi maganan auren ki da Yayana shima ya mutu yanzu na ganki da mijina dole nayi magana saboda ke guba ce".
murmushi Izza ta sakeyi tana juya Ido tace'' wata kila ba rabon a jikin su saide ai maza ba k'arewa sukayi ba a gidan nan kuma ba mijin yarinya ba ko uban yarinya badan na auri d'an sa ba aure tsanani na dashi ba da nayi wuf dashi dan ni bana sake kuma bana wasa da DAMA TA .......
Wani irin uban asher Humairah ta lalo ta maka tace'' kutuma lalle yarinya a wanan Karan zaki taffa kurkure wllh abinda Nasrim tayi kadan ne akan abinda ni zanyi surprise wllh wllh abin ba zayyi kyau ba".
"Ok Humairah kema kisan zakiyi nikuma na miki alk'awarin insha Allah nice zanyi surprise dinki".
Humairah tace '' haka ki kace to wllh zaki gani".
"Al'kairin zan gani dangin ma kisa wllh saide kuyi ta kashe kan ku wahalalu
ba abinda ya shafeni ni de Wanda yace Yana sona to tilas aganmu tilar abarmu Koda za ace ransa fansa ne inji masoya
tayi maganan tana juyawa tayi
hanyar part din Baban ta
"Ai Baba nasake danno wani born din fa ga Humairah can na barta tana hauka akan wai ta gan ni da Kamal"..
dariya sosai Baban yayi yace " me nagaya miki ai nace duk mutuwa zasuyi mu ka dai ne zamu rayu sai yaranki Muwadda da umdatu da Musanat su zasu gaji tulin dukiyar 3AFULL".
Izza tace Baba wllh naga alama kaga fa Humairah yanzu tayi FURUCIN zatayi abin yafi na
Nasrim gashima nayi mata Recorder a waya ta dan zan dinga tun zurata har sai ta fusata tayi FURUCIN da zai mata illah a rayuwa nikuma ina tara bayanan cikin wayata
haka mommy tayiwa Hajja Furucin zataga aikin tubebbiya da Hajja bata daukin abinda mushimmanci ba ni na zugata nace wannan FURUCIN NA mommy bashida kyau aiko ta dauka ta hau kai ta zauna daram yanzu tace ko ciwon Kai tayi mommy ce".
dariya Baban Izza yasake yi yace aikin ki yana tafiya dai-dai ya'r Cuna anan kuma wai Mustapha ni ban ma San inda na samo wani Mustapha ba yanzu abinda nake so dake kije ki min binciken ya Dr Fanna take ciki shiru banajin labarin ta".
Izza tace Baba ai wllh wannan Fannan bata da lafiya ni ko duba ba banje ba rabona da ita tun a kotu Ina jin kunyar hada Ido da ita ayanda na dage sai da mukayi nasaran nan kasan fa duk nafi sauran lauyoyi dagewa."
b'ata rai Baban Izza yayi yace kina y'ar Cuna kike jin kunya wuce ki tafi kizo ki bani labari Koda zuwa dare ne".
Izza zubewa tayi agaban "mommy anwuni lafiya dazu naji Barira dace bakida lafiya yajikin".
cikin dauriya da kawar da komai bayabo ba fallasa mommy tace'' lafiya Al'hamdulillah Umman Muwadda yasu Musanat yau basu zo mun gaisa ba".
"Wllh mommy nima yau ban gansu ba da safe ance Ya Abbaty yafita dasu yanzu kuma inaga sun wuce islamiya ne".
gyad'a kai mommy tayi tare da cewa
"Ok madallah."
shiru mommy tayi ita ma Izza haka can Izza tace "mommy dan Allah kiyi hakuri akan abin da yafaru wllh naso ni nazama lawyer me kare Nasrim y'ar uwa ta wanda tamin dukkan halaci arayuwa to abinne wllh yafi karfina anbiyo ta inda a kafi k'arfina ne bayan da zanyi amma dan Allah mom......
"Please Izza wacece y'ar uwar ta ki ai Nasrim ban santa da wata y'ar uwa mafi kusa ba sai Humairah kuma Al'hamdulillah Humairah ma lawyer ce amma bata ce zatayi ba wanda ya dauke ki yasan zaki iyane kare Nasrim kuma dan bakiyi me yene Nasrim uban da ya haifeta ne ya yanke mata hukuncin balle ke da bama kece babban lawyer ba temakawa kikayi so bana son k'ananun magan ganu mu barwa Allah ikon sa zaki iya tafiya nagod........
Mommy bata k'arasa zancen ba Zaliha me aikin Hajja ta shigo arikice cikin in nina tace'' mommy mommy Hajja zata mutu".
Mommy tace'' meya sameta tana cin abinci kawai sai tace cikin yana ciwo bakin ta kumfa yafara fitowa yanzu ma asbiti za akai ta".
Izza tace" wayyo Hajja gatana nashiga ukku....
tayi maganan tana ficewa da gudu
Mommy ma tabi bayan ta kafin su k'arasa har Kamal da Ummu sun shiga motar mommy taja
Izza ta hau nata motan ko mayafi babu ta fita a guje arikice mommy da Mama Adamu driven mommy ya dauke su
Asbiti
duk suyin cuku cuku a kan Hajja har Nasir da Abu da daddy
Daddy ya numfasa yace " kamar yanda Dr yamana bayani Hajja guba taci to a gida an bincika wanda yasa a bata a bincin kuma an gani ta hanyar CV tv muje gidan munafiki ya bayyana ita kuma Hajja Allah yabata lafiya Al'hamdulillah Allah ya yafiyar mu cikin wannan duhu da muka shiga asiri ya tonu mujede gidan tukun".
Mommy zubewa tayi a k'asa tana sujjidan shuran cikin kuka tace'' Alhamdulillah Allah na gode maka da kafitar mu a duhu Nasrim zata yiwa mijin takaba a gida".
suna zuwa gida motocin yan sanda ne har guda 2 mommy tana fitowa daga mota Abu ya nuna ta inspector ya nunawa mommy I'd card yace Hajiya arrest
Mommy juyowa tayi cikin mamaki tace''me nayi ".
Abu tace'' kece kika saka me aikin ki Barira ta sawa Hajja guba".
ya k'arashe maganan yana nuna Barira da take bayan Hilux din yan sanda kuka Barira ta saka tace'' mommy dan Allah kizo ki ce su barni wllh ba lefina bane kece kika sani dama sai da nace Ina tsoro kikace zaki koreni idan banyi ba gashin an gamani kar akaini Police station Ina tsoro mommy".
wani irin kullewa kan mommy yayi ta taka a hankali har bakin motan inda Barira take tace'' Barira ni nabaki guba kika zubawa Hajja ni".
Barira tana jan majina tace'' eh jiya da muka je chemist anan kika karbo shima me chemist din gashi nan acikin motan".
ta k'arashe maganan tana nuna mata Friday Wanda yake aiki a pharmacy din mommy
Mommy sai alokacin ta kula da Friday yace "madam dama poison din da kika saka na miki order su a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 40