bude ruwan tayi ya fita ta tara na dauraye jiki ta dauraye jikinta ta ɗaura towel ta bude kofar, tsaye ta samesa daga shi sai boxer yana tsaye.Suna haɗa ido ya kama kunnen sa alaman ya tuba".
murmushi tayi tace"kayi wani laifin ne ai kai baka laifi in makayi abisa kuskure to tun kafin kayi laifin an yafe my heart hubby".
Murmushi yayi ya kamo hannan ta suka ƙarasa wajen mirror ya zaunar da ita akan seat ɗin gaban mirror yana kallota ta cikin mirror yana murmushi yace "dan me akayi mudubi".
murmushi tayi tace dan ya haska kyau ko muni".
Murmushi yayi yana shafa fuskanta sannan yana kallonta
ta cikin mudubin yace "amma gaskiya nasan shikansa budubi yafi tsoron masu hasken fata irinku saboda kinga ke kika haskaka mudubin nan ba shi ya haska ki ba. Ni Abdulsamad inason wannan fuska me cike da Kamala da annuri damuwa ko ɓacin rai da fushi bai isa yasa annurin sa gushewa ba. A yanzu fa nasan kina cikin fushin dukar miki ɗa amma gashi fuskar bai nuna ba nagane ne kawai a aikace mun saba wanka tare shine da kina fushi kin barni kin shiga kinyi".
Ita ma murmushi tayi tare da daura hannuta akan nasa dayake shafa mata fuska cikin salonta na jan hankali tace''
nagaya maka bana fushi amma kai ma kasan dukan yayi yawa ko".
kujera ya jawo yazauna yana kallon idonta
'"idan akayi duba da laifinsa baiyi yawa ba Dr inda ya ƙona Aiban fa".?
"ai laifin Aiban ne shi ina ruwanshi ko uwar shi batayi magana ba Kamal da akayi gabansa baiyi magana ba sai shi yaron ya rena Son sosai shiyasa ma Son yace sun dena tafiya tare yanzu ko boko Aiban motar sa daban kullum shari'a. Shi ne nagaji na raba su duk da basa taren ma bazai daina haɗin faɗan ba waye baisan tsakanin Nasir da Agrif ba ko sunyi faɗa basa 10minutes sun shirya. Yanzu da Agrif ya fito dining da sun shirya bawanda ya sani ba...
Ya ce" to shikenan doctor shidama me ɗa fa baya ganin laifin ɗansa. Koni da nake dukan sa ji nake kamar jikina nake duka balle keda aka baki amanan sa".
Murmushi tayi tace '
"ai kaima amanan aka bar maka shi".
Ya ce"ba kamar ke ba, ni wllh Halima bata cemin Nasir amana ba kullum sai nayi tunanin meyasa tayi hakan amma inaji a jiki na kamar nima bazanyi rayuwa me tsawo tare dashi ba shiyasa batace min amana ba. Dan Allah FATIMA ki riƙe min amanan Nasir kamar yanda kika saba sannan naji duk kalaman da Hajja ta jefeki dashi, Hajja ta manta da rashin haifuwa da yawa ko a haifi daya ko biyu a zuri armu ne ba laifin ki bane. Babana shi kadai iyayen sa suka haifa sannan shima Baban sa wato kakan mu su biyu ne. Kakan mu da Kawu Haruna me sunan Baban haka muma daga kanmu ba kari kinga daga mu ne...."
"A a my hubby daina cewa haka yanzu haka ina ɗauke da jinin ka na watanni 2 da sati biyu naso nayi surprise dinka ne." Dr
Are you sure?"
"Very sure my heart".
"Dr Dan Allah ki cire maganan wasa"
Murmushi tayi tace shekara bakwai ka taɓa jin irin wannan wasan a baki na duk yanda kake nuna son kaga mun samu ka manta nakai maka ziyara a China, wata biyu kawuce paris ni nazo gida idan kayi lisafi dai_dai da lokacin cikin zai nuna maka wllh tun a chana na gane amma nayi shiru dan nayi surprise ɗin ku gabaɗaya".
A hankali ya sunkuyo ya manne ta a jikin sa yace" fatima batul kin bani farin ciki tabbas ke ɗin haske ce a rayuwata dole nayiwa Allah godiya. a gobe dayawan ma buƙatan da suke cikin garin kano zasu kwana da farin cikin Alhamdulillah! Allah yamin komai Allah yabani matar da nafi so a rayuwata wanda tun ina yaro nake kwatanta irinta a Raina, yabani dukiyar da ban san iyakar taba yanzu kuma yara Alhamdulillah! ni kam ba dan kar nayi sabo ba da sai nace ina ma ba a wajif ta mutuwa ba dan nikam Allah ya shimfidamin rayuwa a duniya kamar bazan mutu ba amma nasan hakan saɓo ne yarabbi ka Gina min lakhirata fiye da duniya ta. Ya rabbi ka dora ni kan hanya madai daiciya, dukiyar da na tara kasa yazama silar ciyo na zuwa aljana ba ya kai ni ga wuta ba. Allah yasa yara na da zan bari su tafiyar dashi ta hanya madaidaiciya."
"Ameen tace tare da ɗaura hannuta kan nasa da yake yawo a cikin ta
ta ce "my Son yana wajen Hajja nasan kuma bazai yarda ya kwana a can ba duk hankali na yana can".
Murmushi yayi yana shafa cikinta
yace"niko hankalina yana nan."
da sauri ta ɗago kai tana kallon sa da alaman ɓaccin rai, harshin sa ya kai kunneta yana lasa yace "kina yaudaran kanki fuskan ki fa baya nuna ɓacin rai ko damuwa a kullum cikin annurin take".
In dai zaka taɓa my Son to sai na fasa kawo maka ɗan adawar namu".
dariya yayi ya ce" faɗan Allah ne ai ba ikon ku bane ai kwara a kawo masa ɗan a dawar ko ya daina taɓara. Wllh taɓaran Nasir dan ganin shi ɗaya ne yanzu Agrif dayake da ƙannai Aiban da Abbaty ai bayayi ga Aisha ma data ɗauko ƴar riko Zahra ai Kamal bayayi, shi ko kullum abin jarirai yakeyi har shekara bakwai sai dai kimasa wanka da kanki kuma baya yarda yan aiki su masa ko wando bai iya sawa ba nasan idan ya samu ƙane zai san ya girma".
A ɓangare hajja kuwa daƙyar ta lallaɓa mutumin ya yarda yayi bacci. Bacci yayi rigimar a kaishi wajen Mommyn sa.
Da safe duk an haɗu a dining za ayi breakfast, su Mommy da Abba sun makara har anfara ci suka karaso cikin raha. Abdulmajid yace" kai Abba amma ko dai jiyan nan....
sai kuma yayi shiru yana dariya.
Abba ma darinyan yayi yana gyarawa mommy kujeran ta yace ƙarasa mana karamin marar kunya."
Duk akayi dariya, mommy ko idonta akan kowa ganin bata ga ɗan taba har tabuɗe baki zatayi magana taji Agrif yace" mommy Abba Ina kwana Ina my bro?".
Mommy amsa gaisuwan tayi tare da kallon Hajja da alaman tambaya kafin Hajja tayi magana sukaji Nasir yana cewa "to ni ina ruwana da kai naga Mama ce tace kar musake shigowa arabe shine dan na tsaya na gaida baba Yakubu yayi gaba, dan zan maga magan kawai ka saki fitsari shi ne Aiban yacewa Abba wai nayi faɗa dakai ya min duka".
Agrif yace " to bakai kayimin tsawa ba fisarin yafito ban sani."
dariya duk sukayi ban da Nasir da yaci kunu Ummu tace "Allah sarki NASARA ai dama nasan ba laifinka bane shima Abba dan ba ma zauni bane baisan halinka ba baka fadan rashin gaskiya haka ne kam kamar yanda Mama tace kudun ga shigowa tare ku haɗa kan ku kar a ganku a rarrabe mugayen mutane zasu iya samun nasara akan ku kuji ƴan albarka".
Yes! suka ce
Shi kuma Nasir durƙusawa yayi har ƙasa kamar yanda suka saba yace "Daddy Abu Ina kwanan ku".?
Lafiya suka amsa suna tambayar ya jikinsa bayyi magana ba yaci kunu
yana cewa "Mama ummu ina kwana?
Mama tace "Nasara ko gani kafi mutum NASARA me wuyar ɓatanci ya jikin naka?"
ya sake yamusa fuska yayi bai yi magana ba,
Mommy ganin Nasir ko inda take bai kalla ba yasa cikin sanyi murya tace
"my Son".
ɗagowa yayi ya zuba mata dara-daran idon sa da suka gama cikowa da kwallah yayi
yana juya idon alaman yana son mai da kwallan, bai amsa ba har ya maida kansa ƙasa
ta sake cewa "my Son fushi kake damu".?
girgiza mata kai yayi
tace" to me yasa baka gaida mu ba nida Abba".
miƙewa yayi ya ƙarasa inda take yayi saurin faɗawa jikinta ya saki kukan da yake dannewa tun jiya ya ƙwace masa cikin kuka yace "mommy ba ke bace kika barni kika tafi na kasa bacci, baki min wanka ba, baki min addu'a ba, baki bani tea ba, banyi bacci ba, nayi ta mafarkin ki
Ga ciwon da Abba yajimin sai zafi yakemin kin gani".ya ƙarashe maganan yana ɗaga rigan uniform din sa abinka da farin fata duk birdi yayi jajir wani ma ya fashe".
Alhaji Abdulsamad da sauri ya ɗauke idon sa akan ɗan nasa wani irin tausayin ɗan nasa ne ya ziyarci zuciyar sa amma ya dake mai kawaici ne, sai kawai ya ɗauki pork yafara caccankan dankali.
Mommy itama idon tane ya cicciko tace "sorry my love. Soon zaka warke nima nayi missing naka banyi bacci ba zo kayi breakfast karku makara idan kazo zan shafa maka magani kaji".
Agrif yace" Abba ba muyi fada bafa kalli jikin bro". yayi maganan yana fito da ƙwallan da suka taru a idon sa yana shafa dantsen hannu Nasir cikin tausayi da ƙyar Nasir ya yarda ya dan sha tea Maimunatu me aiki ta haɗo musu wanda zasu tafi dashi suka fita
bayan fitan yaran Alhaji yayi gyaran murya yace " Hajja dama nayiwa Fatima wani kyauta ne nake son sheda muku ke da yan uwa na,
a daren jiya na mallakawa Dr Fanna *Three brothers Rice*
dan haka ina son kusa mata albarka.
Sai Ƴan uwa na kuma
Abdulraham da Abdulmajid na mallaka musu kamfanin *Ashana* ta tanan Kano dan zasu fi jin daɗin aiki dashi kuma naga akwai cigaba a harkan ashanan nan wllh zakuyi mamakin kuɗin da kamfanin ashana take fitar wa a kullum. Hajja sai ke me kike so?".
Numfasawa tayi tace umh! nikam ba abinda nake so illa Allah yahaɗamin kan ku sai de nake ga kamar yautar ƴan uwan ka baiyi yawan na matar ka ba tunda baza'a haɗa shinkafa da ashana ba".
yace "a a hajja shima ashanan ana samu dai-dai gwar gwado kuma ita Fatima bafa babban kamfanin nin rice na Lagos na bata ba, na nan Kano ne su kuma yan uwa na kome suke so acikin dukiyata zan mallaka musu ai kayana nasu ne bani da wanda yafisu. A nan Kano dai a yanzu ba companyn da yawuce na ashanan samu kuma na basu shine saboda su agida suke shi ɗin zaifi musu sauƙin aiki amma ni banƙi ace kowa cikin su ya zabi companyn da yake soba nasha gaya musu ga sunan sai suce ai da ya zauna a guna wai basu da ra'ayin business ne. Idan suna so duk wanda suke so ikon sune ko wani zasu iya bawa kayana ".
Abdulraham yace "hakane Hajja ba abinda Abdulsamad yaragemu dashi kowane mataki muka taka silar sace"
shima Abdulmajid haka yace sukayi godiya itako mommy wani banbarakwai taji kyautar duk da tun a ɗaki yasanar mata tukuicin surprise ɗin da ta masa sai a gaban hajja amma batayi zaton har tukuicin yakai haka ba.
Tana cikin wannan tunanin taji Abdulmajid yace "Dr congratulations!"
Itama cikin maida masa martanin murmushin sa tace "thanks my love!" Abdulraham ma yace "Dr Allah yasa albarka a ciki, Mama da ummu ma suka mata murmushi tayi cikin jin nauyin ita dai bata so Abdulsamad yayi mata haka ba.
Abdulsamad ya kalli Mama da Ummu yace" Aisha ke kuma daga yau gidan Mai na hanyan kondila naki ne ke ma Amina na yan awaki nakine.
Sannan duk a tara min ma'aikatan gidan nan duk mai buƙata in dai na kuɗine to a masa zan sa MD HOD Accountant su fito da kuɗin da za'a bawa mabuƙata mutum dubu goma a kano da kuma dubu goma a duk jahohin arewa sannan a bawa kwamitin marayu na kowacce jaha kuɗin adadin yanda aka saba badawa a zakka amma ba zakka bane kyauta ce. Dan nuna godiya ta da kyutar da Allah yabani".
Hajja tace"Abdul abin bai yi yawa ba wannan ai sai kasa dukiyar ka ya girgiza".
murmushi yayi yana matsowa kusa da ita ya juyo mata da agogon hannun sa yana nuna mata yace "Hajja kin gani a yanzu da muke maganan nan kuɗin da suka shigo min ya kusa rabin kyautar da nayi kuma gobe ma haka. Kyauta ko sadaka Hajja bazai girgiza dukiyar Three brothers ba sai dai ma yaƙara masa ambaliya".
murmushi tayi tana kallon agogon nasa tace "ina zan gane wannan lissafin Allah yasa albarka cikin dukiyar ka su kuma wanɗan da ka bawa Allah yasa silar arzikin su kenan ".
Amin! suka ce dukkan su Mama da Ummu har ƙasa suka durƙusa suna masa godiya a ranan dai kowa yaga 3brothers yasan yana cikin farin ciki duk wanda Allah yatsaga da rabonsa dai yayi arziƙi duk da bai fito ya faɗa ba yan uwa sa da Hajja sun san yana cikin gagarumin farin ciki.
Miƙewa yayi Abdulmajid ya kalleshi yace
"to yanzu sai ina ?
"Alƙali zanje zamfara Alhaji Yahaya yasan Hajiya Hauwa ba son kishiya take ba ya tashi ya ɗankara mata yanzu gashi matsalolin suna ta kunnowa ga business yasha gaban sa".
Mommy tace"a a fa my heart ba a yanke hukunci da bangare daya sai an hadu dukkan su ai nima ta gaya min yanzu haka ya sauke igiyar aurensa biyu a kanta saura ɗaya ai ko me ta masa bai kamata ya furta saki ba"
Ya ce "ai shine zanje nayiwa tufkar hanci yanzu haka tana Abuja nace ta biyo jirgi yanzu mu hadu a family house nasu."
Ummu da Hajja atare suka ce "Allah ya tsare."
Mommy ɗan sunkuyawa tayi dai-dai kunne sa yanda ba wanda zaiji tace
" Halimatus Sadiya tana adawo lafiya".
ta ƙarashe maganan tana nuna cikin ta da ido
shima cikin basarwa ya
shafa cikinta yayi ƙasa da murya yace"har kinsa mata Halima kenan ni kuma dana fison asa Hajja a farko amma Halima ma yayi. Yawwa wai ina my Son fushi dai yake ko".?
Murmushi tayi tace"kasan sa da zuciya kuma baka yi lalashi ba".
Tayi magana tana bin bayan sa dan yayi gaba suna fitowa suka hango mutane gidan a compound din Hajja da alaman Abu suka rako dan shima zaiyi tafiya seminar zuwa Egypt kowa yana masa fatan a sauka lafiya
hannu ya bawa Abba sukayi musabaha, Abu yace "sai nan da wata biyu kenan ko, Bro?"
Murmushi Abba yayi yace " a a kai kam zamu hadu a Englan ai ba dan issue ɗin gidan Yahaya ba da tare zamu wuce yanzu kaga Hajja tana ta faɗan na jima banje dardum ba shine na shirya tafiyan a mota zan shiga dardum nayi ziyara
sai na wuce zamfaran insha Allah zuwa Wednesday ina England".
Abu yace "kasan yanda hanyar zamfaran nan take kake cewa zaka tafi a mota"?
Murmushi yayi yace "ba komai bro in ma yan kidnapping ka ke tsoron mota ta bayajin bullet
in kuma accident ne mota na bazai fadi ba koya faɗi akwai matakan kariya wanda ko ƙwarzani ba zai yi ba".
shiru Abdulraham yayi duk da yasan akwai kuskure a *FURUCIN* Ɗan uwan nasa amma yamasa fatan alkairi da cewa
"to Ɗan uwa saduwar alkairi sai mun hadu acan din dan ina ga seminar ɗin zai ɗaukemu kusan few weeks sai kuma idan mungama ina da hutu na 2weeks zamu kasance tare."
Abba yayi murmushi shikuma har zai shiga mota da gudu Nasir ya rungumoshi ta baya yana cewa"Abu na zamuyi missing naka."
Juyowa Abu yayi yace "haka ne my Son amma me kuke son na kawo muku Nasir yace "computer". Abu yajuya yana kallon Agrif da Kamal
yace kuma kun yarda computer kuke so ko?"
ya ƙare maganan yana kallon Kamal da Agrif da Aiban".
Suka ce yes! Abu
''Ok"
Yace yana shafa kan Abbaty da yake hannu ummu yace kai fa cikin gwarancin sa yafadi wani maganan da duk basu gane me yake cewa ba ɗan shikara 3 amma yayi nauyin baki ba agane maganan sa driver sa yabuɗe masa front seat yashiga suma bodyguard dinsa suka shiga yaja drive.
Motan Abu suna fita Nasir ya juya da niyar komawa duk da yasan Abba ma tafiyar zayyi amma yak'i ya tsaya yaga tafiyar sa
Mommy tace "son baka san Abban ku ma tafiyar zaiyi ba"?.
Ko juyowa baiyi ba yashige part ɗin Hajja
Abba har an mude masa kofa zai shiga yajuyo yana kallon hanyar part ɗin Hajja ɗin ji yayi bazai iya tafiya ba sai yanemi sulhu da ɗan nasa yace "sorry ina zuwa".
dariya Hajja tayi tace"ka ce baka ji, wa ya gaya maka karo da nasara akwai riba? ai Nasara goshin girji ne me wuyar karo".
bai juyo ba yana cigaba da tafiya yace"ai Hajja ku kuke ɗaure masa yake abinda yaga dama".
yana shiga yasamu Nasir akan two seat ya daura ɗaya kan ɗaya yasa Laminu mai aiki yana tsiyaya masa ruwa a cup
ya nuna kamar ma bai ga Abban ba Abba ya zauna a gefin sa ya numfasa yace "kana jina NASURUDDEEN?
Turo baki yayi baiyi magana ba Abba yace "me yasa kake haka ne laifi fa kamin amatsayina na mahaifinka na tambayeka me ya haɗa ku da ɗan uwan ka? kamin shiru dan Aiban ƙanin ka ya faɗamin shi ne ka tura masa tea ajiki da yana da zafi da ka konashi. shi ya sana dake ka kai fa yaro ne har yanzu shekarun ka 7 kawai a duniya Nasuru amma ba wanda ya isa dakai meyasa kake haka bana son wannan halin naka kana da zuciya,Saurin fusata,iko,isa gadara ka daina, da Agrif ne yakeyi ko Kamal baza a sama sa ido kamar kai ba. Kai a ido kake duk abinda kayi za ace dan kana ɗanane duk da nasan baka kai matakin da za ace hakan ba amma in ka tashi da wannan ɗabi'ar za ace hakan wataran".
Nasir yace". To Abba me yasa idan Agrif ne ko Kamal baza aga laifin sun ba".?
dafa kafaɗan sa yayi yace"duk da ƙwaƙwalwar ka tayi wa amsa ta nauyi amma
zan baka ya zama dole kasani Nasir kai kana idon mutane ba daya kake da yan uwan ka ba duk abin da kayi za ace dan kana ɗana ne kana taƙama da arziƙi na ne, shi yasa nake son ka gujewa laifi komai ƙanƙantar sa kazama mai biyya ga iyayenka Abdulmajid, Abdulraham da mommy ka sannan inaso kayiwa Mamar ka Halima addu'a kullum idan kayi sallah har nima."
Mommy da ta jima a wajen tayi gyaran murya tace haba Abba wadan nan kalaman sunyi wa son nauyi".
Abba ya furzar da iska yace "ni ma nasan sunyi masa nauyi ban san mesaya nake wasu abubuwan ba Dr dan Allah kamar yanda Halima ta bar miki amana nima na bar miki amanar Nasir da abinda ke cikin ki.....
Nasir ne ya katse shi dacewa "Abba wacece Halima"? Abba da mommy da sauri suka kalli juna tana masa alaman kaga irinta ko kallon agogon hannusa yayi ya miƙe tsaye tare da rike hannu Nasir cikin sanyin murya yace"fatima kawo hannu ki miƙo masa tayi ya haɗa da hannun Nasir yace a karo na biyu amana dan Allah ki bashi duk wata kariya a rayuwa bawai ina gaya miki maganan nan bane da wata manufa ko dan ki tada hankalin ki ina fada ne saboda niba mazauni bane shine dalilin da yasa Halima tace ke tabawa Nasir yarda ce tasa na barmiki amana. Nasir nima
kuma ni nasan yan uwa na basu da matsala ba zasu tada muku hankali akan abinda yazama rabon kuba amma ki musu adalci yanda ya kamata.........
Mommy
cikin ɓacin rai tace "please ya isa".
murmushi yayi yafara tafiya hannusa na saƙale da nasu har inda ake jiran su parking sp ɗin
har an ɗude mota yashiga yafito yana kallon Hajja da daddy yace " Hajja Alƙali a yita haƙuri da halin Nasir insha Allah zai dena Dan Allah ka bashi tarbiyya bisa amana kamar yanda zaka bawa Kamal.....
Hajja tace "kai Abdulsamad nidai zan koma ciki Allah ya tsare ka gaida mutanen daldum sosai. Allah yamaka albarka" tayi ciki
shi ma ya shige mota yana ɗaga musu hannu amma kafin direba ya rufe Nasir yayi wuf yafada jikin sa haka kawai ya saki kuka yana cewa
"Abba kar ka tafi".
murmushi Abba yayi yace" my Son ba dan school ba tare zamu yi tafiyar gobe nefa zan zo jirgin asuba zanbi gobe iyanzu ma muna tare ɗan al'barka".
Ya juya ya kalli Kamal da Agrif da Aiban da Abbaty ya sake fitowa duk sai da ya rungume su shida ba bawa ni damuwa yayi da safgan yaran ba amma yau jiyayi kamar kar ya tafi gani yake idan ya tafi wani abun zai iya samun iyalin nasa musamman da Nasir yace ABBA KAR KA TAFI ɗaya bayan ɗaya yajuya yana kallon su duk sai yaga jikin su yayi sanyi a hankali yashiga motar direba yaja suka fice a harabar gidan idon sa yana kan Fanna da Nasir
duk a sanyaye suka koma gida
Abba har sun kusa fita daga Kano sarkin kasuwa ya kirashi.
ɗaukan wayar yayi yana cewa "Allah yaja zamanin shugaban yan kasuwar duniya".
daga can ban garen Alhaji Nuhu yace "au ranka shi ɗade kama bani na duniyar baki ɗaya kenan".
dariya Abba yayi yace '"eh! mana kano ai duniyace yanzu haka gashi munfi awa mun kasa fita a garin ashe haka fita amota yake da wahala acikin Kano ".
Alh Nuhu yayi saurin cewa
" Sir fita kuma duk fa anshirya kai akejira".
Abba
yace "kai Alhaji Nuhu na wakilta Adamu zai halarci meeting ɗin nan ni bazan samu dama ba".
cikin damuwa Nuhu yace "Adamun yazo amma yallabai dole sunce sai dakai duk akan rage farashin kayan da kayi ne sauran kamfunnnan sunce basu yarda ba kuma suna da gaskiya ragin yayi yawa kaga harda president har ya ƙaraso kai kawai ake jira".
tsaki Abba yayi yace "toh wai ya suke son wadannan mutane nayi ne nifa ba dan zasu ce ina takama da abinda Allah yaban ba dasai nace kowa yaji da kansa wllh duk abin daza ayi sai dai ayi bazan rage ba, musamman shinkafa da taliya da fulawa ni yanzu shikafa ma ba nawa bane madam ita keda iko".
Alhaji Nuhu yace" shikenan yallaɓai amma dan Allah ko a gurguje ne kazo dan idan kana nan zakafi yimusu gwarjini".
dole Abba yasa driver yakoma baya anyi meeting an tashi lafiya amma Abba bai samu fita daga Kano ba sai wajen 2 na rana.
Ajiyar zuciya ya sauke sanda yaji sun fita acikin gari yana jawo wayar sa na family ya kunna saƙon nin ne suka fara shigowa amma na Fanna ya fara ɓudewa
_barka da wannan lokacin hubby idan ka samu waje mai network ka kirani na kira ban sameka ba_
Murmushi yayi ya kirata jin yanayin muryar ta yace
"dama dan naji ya hanya nakira ka amma kun kusa ko?"
"A'a my wife ai yanzu muka bar kanon ma na halarci wani meeting ne wanda ke ma ya shafe ki Dr. Idan kina da ra ayin yin aikin kiyi da kanki bazan hanaki ba tunda ba irin na da bane, wannan kina da ƴancin da wanda kika ga dama in dai kina da ra'ayi idan kin haifu zaki fara fita kafin nan kibar komai a hannun Ahmed kamar yanda yake ayanzu yana da amana".
cikin sanyin murya tace "a'a a yanda hutu ya gama ratsani gaskiya ba zan iya wani aiki ba balle ma irin wannan aikin ya man nauyi".
dariya yayi yace "hakane gaskiyar ki madam kisha hutun ki mijin ki a wahale, ke a wahale ai ki huta rayuwar duniya dai baku da matsalan sa ko da za ace rabin al ummar Kano yara na ne da jikokina wllh kuda talauci *ruwa tasha* inji yara....
Mommy cikin sanyin murya ta dakatar dashi dacewa "Niko Abban Nasir wani lokacin kalaman ka suna bani mamaki, kamar ma kana mantawa da ƙaddarah ne ko FURRUCIN ka na ɗazu na cewa kai motar ka baza ta fadi ba kuma Koda ta faɗi da matakan kariya anya ba kuskure cikin FURRUCIN ka".
shiru can yace "ni ba wani kuskure cikin FURRUCI NA please my wife jikina yana bani kamar kina cikin damuwa please what's happening
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 40