bangaren ku dan kaida idon mutane kunsan ba iya mu bane agidan nan ma'aikatan gidan nan wani lokacin sa Ido ne dasu tun kafin su gane shigar ciki kafin hawa doki kuwuce ku k'araci rashin kunyar ku acan".
Mommy ce ta fara tashi tana hamma tace Hajja sai da safe bacci nake jin ta kalli Abu tace " Abu Allah yabamu al'kairi tayiwa Mama da Ummu ma dama daddy ya ba itace dashi ba dutyn Mama ne yaran ma suka mata mu kwan lafiya sai
Abu ma yana tashi a dining room bayyi zaman fira ba dan haka Ummu ma tabi bayan sa Daddy ma ya kalli Hajja yace"Hajja nima de zan dan fita zamu hadu da Alhaji Gambo".
tace'' adawo lafiya Allah ya tsare Abdulmajid".
Hajja tashi tayi tana kallon Agrif tace'' marar kunyar k'arya me yahana agaban iyayenka baka maimaita abin da kace d'adu ba ni kutashi kubani waje zan hau sama nayi shirin kwanciya kar nabar ku anan amin abin da bai dace ba eshe".
Agrif yace"to wai ni Hajja cemi ki nayi na k'oshi ne da zaki bi ki takuramin".
tana k'ananun maganganu ta wuce parlour tabe baki tayi da ta kalli Nasir tana cewa "ummm nide bani tsare gida da ciccin maganin mutum duk baya d'ad'ani sai naga mutum da mata ta fara tsirce-tsirce".
Kamal yace" lalle zaki jima ide Nasara".
ajiye laptop din sa yayi ya mek'e tsaye yace "Hajja ai kar kiji komai zan baki mamaki".
washe baki Hajja tayi tana neman wajen zama jin Nasir ya bata amsa ba k'aramin dad'i taji ba dan ita ba abinda take so irin fira da Nasir ko taga yana walwala shiko bai fiye mata magana ba ko zata wuni tanayi saide ma ya bale ta da masifa wani irin mugun so take Nasir Wanda duk b'acin rain da take ciki ta ganshi yawuce
Kamal ma zama yayi dan haka Humairah ta zauna akusa dashi Agrif kam jin zuciyar sa ba zata juri zama awajen ma yasa yace Hajja sai da safe ......
tsaye katafi da ita bana son munafirci ."
"dariya yayi yace" kajini da Hajja da cewa nayi zan bar miki ita ya zanyi na far miki rushina matar aure na halak dina".
ya k'arashe maganan yana kama hannu Nasrim data bishi ba musu wani irin kallo Nasir yabisu dashi tare dayin murmushi su yana gyad'a kai ahi k'adai yasan me yake ayyanawa acikin zuciyar sa amma afili sai kace yana cikin farin ciki
ita ma Hajja da kallo ta bisu ta mayar da kallon ta akan Nasir tace'' sun baka sha'awa ko? ban ga lefin su ba suna cin riban k'uruciyar su ne Agrif yana burgeni ya iya tsayan zuciyar macce kaga duk girman lefin da yayiwa yarinyar nan amma lokaci guda ya mantar da ita koma ina kula dasu ta ito yake aika bata sok'on ban hakuri har ya shawo kan ta Allah yasa kayi dace da macce kamar yanda Agrif yayi ya dace yasamu matar da take son sa son kowa......
cikin wani irin tsawa ya dakatar da Hajja da cewa " ke wai ni meke damun kine bakin ki anyi shine dan surutu kanki baya miki ciwo kisan irin magan ganun da zaki din ga fada agabana musamman zance wannan yarinya ko da wasa bana son k'ara jin sunan ta a bakin ki Agrif ya dade to kisani farkon dacen sa kika gani baki gana k'arshen ba".
sosai yake mata masifa kulus Hajja yayi kamar ba Hajja Lamin Haruna mai bushun iko ba
tas yamata ya ya d'auki laptop da wayan sa yafice
Kamal da Humairah tsimi tsimi suka fice kafin ta huce akan su
"Nasrim ban san da wane irin kalaman zan baki hakuri ba wannan shi ya hana ni neman ki ko a waya amma a yanzu gani a gaban ki duk hukuncin da kikaga ya dace kimin".
murtuke fuska tayi tayi kansa gadan gadan kamar tana filin dan be harda dunk'ule hannu
shiko ya lumshe ido yana murmushi yana jiran yaji bugu amma sai yaji fado jikin sa tafara masa cakul kuli jin zata zauta shi ya tsaba umarnin Nasir yasa ya kama hannun ta duk ka
biyun yana kallon cikin idon ta wani irin kyau da kwarjinin yaga tana masa take yaji muguwar sha'war ta ya taso masa ita ma shi take kallo cikin cikin sanyi murya yace
"Halimatus Sadiya sai yanzu na yarda Allah yawada tani da babban ni'imar sa da ya bani ke a rayuwata samun ki amatsayin mata shine Nasara ta fa yanzu har na can zanci ki yafemin dawuri haka".
murmushi yayi ta kwantar da kanta ajikin k'irji sa tace''ai Ya Agrif kai tun kafin kayi lefi an yafe balle wannan da bawani lefi bane lefin ka daya fitar dani a hayyacina da kayi kaga yazama tamkar ne amma ko acikin hankali na idan yaza ma dole ai zanyi kodan sauk'e nayin da yake kaina ba sai ka batar min da han kali bani halaliyar kace nariga nazama matar ka a lokacin kana da ikon yin duk yanda kaso dadi ".
jawota jikin sa yayi ya hugging din ta yana sakin wani irin ajiyar zuciya da ace Nasir bai bata masa komai ba da ba abinda zai hanashi kasan cewa da matar sa a yau wani irin kuna zuciyar sa yake masa kamar ana furama sa wuta sai cije lip din sa yake yana shafa kadon bayan ta
ahankali ta d'ago kai tana bin ko ina najikin sada kallo
tace'' ya Agrif meya ke damun ka karame sosai kayi duhu yana yinka duk ya canza kaman ba Haruna me kyau da walwala ba wllh kasa ni kaina Ina zargin kaina tun kafin wani ya zargi aure nane ya canza ka".
ahankali ya rabata da jikin sa yam dafe kafadan ta cikin sanyin muryan yace "ba auren ki bane ya canza ni kawai tunayin kamar na zaga da kula dake ne kawai damuwa ta namiki babban lefi wanda sakaci na ne ya janyo mana na tafi na barki
alokacin da kike buk'ata na akusa dake ya zanyi na wake wannan lefin Dan Allah Halima ki fadi burin ki da duk buk'atun ki insha Allah ko meye zan miki."
murmushi tayi tasa hannun ta tana shafa kwanceccen sajen sa cikin salon jan hankali tace'' burin Halima rayuwa da Haruna buk'atun Halima kuma nasan kasan su".
shima murmushi yayi yana maida mata da kashin data ya zubo goshin ta yace " nasani buk'atun Halima zama da Haruna ita kad'ai ba tare da Koda tar aiki ceba balle kishiya kisa aranki wannan buk'atun ya biya DAKA KE BA K'ARI
dake zan zauna ko acikin aljannan kin isheni I love you with all my heart my darling wife".
"I love you too my dear promise idan kayi kishiya zaka kawo k'arshe rayuwar daya daga cikin mu wannan FURUCI NA NE".
"haba my wife nafa hanaki irin kalaman nan FURUCIN ba mekyau bane nide na yarda da kaina ke daya na rike ayarna komai wuya balle inda ke aduniya ta no wahala ".
fad'awa jikin sa tayi tana sauk'e numfashi tace'' Yaya dan Allah wannan turaren da kayi amfani dashi ranan da katafi shi nake so wllh har yanzu ban sa an wanke kayan ba dan kar k'amshi ya fita kullum da kayan nake kwana amma wannan na yau ta damin zuciya yake dan Allah ka cire kayan kasamin wancan turaren.........
wani irin bugawa gaban Agrif yayi bai san sanda ya farta "bani nayi amfani dashi ba.........
da sauri ta d'aga tana kallon sa da sauri ya gyara zancen sa yace ina nufin ba dashi yau nayi amfani ba gashi kuma na barsa a Dubai amma zansa akawo kinji zan cire wannan din da bakya so".
ajiyar zuciya ta sauk'e ta kama hannun sa biyu ta daura a cikin ta cikin sanyin murya tace amma Yaya sai naka kamar baka farin ciki da cikin nan ko kana cikin maza masu ra'ayin sai andan sha'na kafin afara laulayi".
ahankali ya sauk'a akan gadon ya mek'ewa yayi tsaye sai da yayi taku ukku ba tare da yajuro ba yace' ba zaki gane me nake ji akan cikin nan bane amma kisa aranki murna ne".
yayi maganan yana k'arawa wajen wardrobe yana cire rigan t shit din sa agaban ta yacire har wandon jens dinsa ya daga shi sai boxers yayi hanyar bathroom
sai da taga yarufe k'ofar ta sauk'e numfashi tare da shafa cikin ta tana murmushi afili tace yau zaka kasan ce dare da daddy ko dan sosai take son kasan cewa tare da mijin ta gaba daya magunnunan gyaran jiki da aka mata amfani dashi ya addabeta yawanci ma pat take sawa dan pant din ta baya mintuna 20 ba tare da ta canza pant ba lumshe idon tayi tana shafa maranta tace'' kema yau zaki huta da ciwo da sauri ta tayi tafita daya dakin dan ta shiryo ita ma
Agrif yana fitowa daga wanka daure da towel wayan sa yagani yana ta hasske alaman message yana shigowa k'arasa yayi wajen yana goge ruwan jikin sa da tawel din da yake hannu sa
duk message dinna Nasir
na FARKO ga abinda yake fada
_agrif ina jadda da maka ban yarda ko hannun Nasrim ka taba ba amma kaine har da rungume ta meyasa kake da taurin kaine kasani yanzu Nasrim tamkar matata take Dan da iddana akanta shiyasa ma nayi kokarin jona C TV adukkan bedroom din gidan Ina kallon duk abinda kukeyi na yanzu na maka uzuri saboda baka sani ba amma wllh Agrif ba barazana nake ba abin fa bazayi kyau ba idan ka matsa wllh zan balla sa sirri abani cikina ku kasan zan iya ABI umarnin Nasir_
Sai daya
_ka zauna kana karantawa yarinyar k'arama kalamai kamar zaka mata sujjada_
ajiye wayan yayi ahankali akan bed sent ya zauna abakin gadon hannu sa duka biyu yasa acikin sumar kansa yana yamutsasu yana cije lip din cikin cikin karayeyyen murya yace Nasir Nasir me na maka da zafi har kaka da har kake tsabawa ubangijin ka saboda kawai kalalata rayuwata".
wayan sane yayi Rig yayi saurin dauka dan yasan shine
dariya yaji yana yi cikin dariyan yace "Alhamdulillah ashe nashika cikin rayuwar taka ina lalalawa kai da kasan bazaka iya dauka ba kayi taurin kai duk Warning din dana maka kazata barazana nane to wai tilin fin wannan agaban ka amma baka makara ba har yanzu idan ka saki Nasrim komai zai iya wuce maka.....
cikin tsawa Agrif ya dakatar dashi da cewa
"Nasir idan kai mahaukacine ni da kankali na idan idon ka arufe yake ni nawa abude yake ba batun sakin Nasrim na yarda zan dauki sharadin ka duk dan Allah kada ka fallasa wannan na yarda ko yatsan ta bazan sake tab......
shuru yayi jin k'amshin turaren
Nasrim d'ago kansa yayi idon sa cikin nata ta jeho masa tambayar daya hargiza hanjin cikin sa gaba daya
tace'' ya Agrif saki na yake umartan kayi dama wannan bayahuden shi yamin.............
*Wai masoya mu hadu a pg 9 insha Allah Ina jin dadin comment din ku*
*Kuci gaba da yimin share da comment zanci gaba da faranta muku in Sha Allah*
*Taku B JATTKO*
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*__________________________________*
*Pages 7*
Cikin gida kam Hajja tun daren take ta neman Nasrim dan zata bata wani magani wanda take son ta sha a deren asabat wayewar lahadi din amma tayi kiran tazo da kanta har part din Mama
Mama tarasa me zatace dole ta gaya mata tana wajen Agrif Hajja tafa hannu tayi tayi tana salati "nashiga ukku ni lami wannan din wani irin rahin kunya ne daga daura aure ko kaita ba ayi ba ta Kai kanta gareshi anya dama ba sun saba matse juna ba nide Allah na gode maka da muka rabu dasu lafiya lafiya sai suje su k'arata dama maganin kariya zan bata tayiwa kanta shegiya jarababbiya".
itade Mama duk kunya ya isheta ko kanta ta kasa d'agawa har tagama ta fice
Ko da aka taru a dining room Dan ayi breakfast Hajja fad'an da tayi ta mai_maitawa kenan
Kamal da yashigo yanzu yace " ai Hajja Agrif kam ba yanan muna fitowa a masalacin bai shigo gidan ba".
Ummu tace " Eh munyi sallama wai zai je Switzerland wani aiki ne ya taso masa na gaggawa wanda dole sai yaje".
Abu yace "kai yaran gidan nan akwai zafin nema sun gaji Abban su Abdulsamad in ba haka ba wane ango ne zai bar matar sa adaren farko yayi tafiya wani k'asan".
Aiban yace " muda mukazo bikin ma bamu koma ba shi har ya tafi ni abinda yafi bani mamaki ma wai Switzerland gaskiya bana jin awai wani aikin da zai sa har sai anje can tacan fa nazo kuma komai normal".
Mama tace'' zai iya yuwuwa tasowa yayi".
Aiban de yasan ba haka bane yasan idan aiki ya toso ma ta hannun sa ne amma yayi shiru
Kamal yace "ai Aiban ne me kula da komai bawani aikin da zai taso inde a waje ne batare da sanin Aiban ba yana riga Nasara ma sani kaman nine a nan Nigeria kinga ina riga kowa sanin".
Ummu tace " to wai ni yanzu ina ita Nasrim din?".
Hajja tace'' ke Amina ta ina kike jin zancen ne wai tana can bangaren su da mijin acan ya kwana da ita shine dasafe ya tsiri tafiyan munafurci ai shi yasa tun safe nazo na sallami yan biki dan wannan abin kunyar ba dani ba shine nata da burina sai da naga kowa ya tafi sai iyamu wannan abin kunya har ina dama yarinyar nan idon ta abude yake".
Mommy Abu daddy Ummu da sauran mutane sai yanzu suka gane kan fad'an Hajja
Ummu ta juya tana kallon Izza da Humairah tace "kuje ku kiramin Nasrim din".
To sukace suna dariya k'asa k'asa har zahra suka fita dan gulma
Itako Nasrim ko yatsan ta takasa d'agawa duk jikin ta yayi tsami kuka kam har tayi ta gaji tun tana sa ran ganin Agrif har tacire tsammani to me Agrif yake nufi da ita yamata irin wannan illar amma ba temako yafice yabarta haka
Zahra tace'' kuyi sauri ni wllh sonake naga idon Nasrim ko ya zata kalli idon mutane dariya Izza tayi tace'' yako zatayi kina gani tama kasa shigowa break
kasan cewar basu ka kowa a parlourn ba yasa kai tsaye suka haura steps direct bedroom din Nasrim din suka shiga amma ba alaman an sake shiga tun ranan da sukayi jere suka fito suka nufi na Agrif "Humairah tace'' what meye haka Nasrim da sauri ta haura bed din a dai-dai lokacin Nasrim tabude idon tare da fashewa da kuka me cin rai
Humairah tace'' Nasrim meye haka?
Nasrim cikin kuka tace'' Humairah ku d'agani na gaji da kwanciyar bayana ciwo duk jikina ciwo yake min".
ahankali suka d'agata tareda jinginar da ita cikin murya ta dayake fitowa d'aker tace" dan Allah kudu ba min meye a k'asana Zahra tayi saurin yaye blanket din da take rufe dashi da sauri ta sake tana fashewa da kuka Izza ma da Humairah da sauri ka bude ganin jini meyawa
" inna'lilashi wah inna'ilai'hi rajuun" suka fada a tare Humairah ta fashe da kuka Izza " tace " me ya Agrif yayi haka Nasrim kinga yanda jini ya bata ki da bed shit din kuwa".
Nasrim cikin dauriya da dashewar murya tace" Izza ku temakamin banyi sallah ba kuma fitsari nake ji".
ahankali izza da Zahra suka sa hannun su cikin kafadun ta biyu suna d'a gata tasa wani irin ihu ta zube suma kukan suka saka sake yun k'ura tayi cikin dauriya amma sai ta kasa takoma da gudu humairah ta fita
a inda tabar iyayen anan ta samesu cikin kuka tace'' Mama Nasrim ce Nasrim ce sai nuna kofar waje take atare suka mek'e dukkan su suna tambayar meyafaru ina take'?
" Mama bata da lafiya ko iya tashi batayi".
agigice Kamal yace " tana ina".?
"Part din su".
da sauri sukayi hanyar fita Mama Abu Hajja Aiban da Abbaty Kamal ne akan gaba
Mommy da daddy kawai aka bari suma de sun zauna ne saboda kara
girgiza kai Kamal yayi yafita a bedroom din yana cewa "Humairah ku kintsa ta ku daukota mota muje asbitin".
Hajja fada sosai takeyi dan da ita aka gasa Nasrim sai de Abu ya hana akaita hospital sai da mommy tazo tagani tace "ai justice dole sai ankai ta asbitin dan za amata dinki".
Kamal ne ya dauke ta suka tafi asbitin mommy da kanta tashiga theaterroom ta mata dinki mekyu ta tausayawa y'arta ta dan ba k'aramin ai ka ai ka aka mata ba afili ta shafi fuskan Nasrim da take bacci tace'' lalle namiji wazaiga Agrif yace shi zayyi wannan aika-akan'.
Wanda badan ta samu kulawa ba zai iya janyo mata matsalan yoyon fitsari
***************
kwana biyu aka sallameta suka dawo gida
Abu yace "Hajja dade kin bari ko a part din Aishan ta zauna kafin mijin nata yazo bai kamata a kaita batare da mijin yazo ba".
Hajja ta b'ata rai tace''
"Abdulrahaman kafa ficemin a ido kaine me ja da umarni na yanzu bawani bangaren Aishan da Nasrim zata zauna a tar katata can inda ta kai kanta aka mata yugu_yugu ko tajira an kai tane ba da kafan taje ba hakan ko akayi adole aka kai Nasrim part din ta aranan sai mommy tana warning din ta da takula da shan magun gunanta akan lokaci
Agrif kuma har yanzu wayan sa baya shiga ba a kuma samu labarin inda yake ba har yanzu
Humairah da Izza ne suka rakota
suna shiga Izza tace " ummmm dan Allah Hummee wannan parlourn k'amshin wa yakeyi".?
Humairah tace'' ai ni tun ranan da mukazo muka sami nasy akwance naji turaren Nasara amma ganin yanda nasy take yasa banyi magana ba ya Agrif ya canza turare baki ji ita kanta har yanzu tana k'amshin sa ba nina rasa wane irin turare yake amfani dashi".
ta k'arashe maganan tana d'aga hanci alaman tana son shak'an k'amshin
Nasrim tabe baki tayi tana zubewa a kujera
*bayan sati biyu*
amare suna murmurewa suyi kyau amma banda Nasrim ta rasa awane matsayi zata ajiye kanta tun tana fushi da Agrif bata neman sa kamar yanda bai ne meta ba amma yanzu ta dawo neman sa babban abin da yake bata mamaki bata samun sa awaya ashe bai jeda wayoyin sa ba jiya taji mommy tana fada wai laptop din sa da wayoyin sa suna bedroom dinsa na part dinta
suna tattaunawa akan Agrif ba aiki yaje ba
tana cikin wannan tunanin taji an dafa kafadun ta juyowa tayi taga Humairah ce murmushi tayi mata tareda kama hannu ta
mek'ewa tayi
Saida suka fita a parlourn Hajja din Humairah tace'' haba nasy duk kinsa my heart ya tada hankalin sa ko bacci bayayi yanzu ma cewa yayi na kiraki".
Ita de batayi magana ba binta kawai take a baya har zuwa part dinsu
a main parlour suka samu Kamal a zaune akan kujera one'siter kafan sa daya kan daya yana girgiza na saman dama zaman sa kenan Kamal kaman wani sarki haka yake ko yaushe
cikin sanyin murya tace " Yaya Kamal barka da hutawa".
tace tare da zama a kujeran two seater wanda yake facing din sa
kallon ta yayi na tsayon second 8
ya sauk'e numfashi tareda ajiye wayan hannun sa a hannu kujera yajuya ya kalli Humairah yace"
My one ki dan bamu waje ko zamuyi tsirri".
Humairah tace'' to abin hakane y'ar wariya ce".?
dariya yayi cikin son matar sa k'anwar sa yace "haba my wife dear ai kinsan ba abin da nake boye miki kawai dai naga ku ya kamata ku shawo kanta amma kun kasa shi yasa ni zan gwada amma ai kece k'arshe sirri my sweet love".
ya k'arashe maganan yana kashe mata ido daya cikin so mezafi Nasrim sun kuyar da kanta tayi hawaye yana shirin zubo mata gashi de Kamal da Humairah ba suyi wani dogon soyayya ba asali ma hadasu akayi amma gashi suna zaune cikin zazzafan soyayyar juna ita kuma Agrif yanuna mata so me zafi tun kafin suyi aure amma yanzu yasamu abin da yake so ya gudu ya barta tana cikin wannan tunanin taji tafin hannun sa cikin nata d'ago da kanta tayi tana kallon sa a tsugunne yake a kusa da ita yazuba mata manyan idon sa yana girgiza mata kai alaman kar ta bari hawayen ta yazubo amma ina yayi yawan da bazata iya maidashi ba sirtowa sukayi hannu biyu yasa ya shafe su cikin sannin murya yace" Kai cona mi Kamal y'ar uwata kwaya daya tak a duniya amma na barta take hawaye kuma a gabana kuma bani da matakin d'auka ban taba zatawa Agrif haka ba da bazan bari ya auri only one sisters dina ba amma nasan halin Agrif bazai tabayin hakan batare da wani hujjja ko dalili ba shiyasa nake neman alfarman ki gaya min akwai wani abu da ya faru tsakanin ku ne".?
girgiza kai tayi ta kasa magana
Humairah tace'' haba my dear wane lefi cikekkiyar amarya Wanda ta kawo cikekken budurci zatayiwa ango ai irin su nasy ko me sukayiwa ango dai_dai ne irin su ake Kira da amarya ba kya lefi".
d'agowa yayi yana kallon ta cikin murmushi yace " bana ce kibar nan ba".
natsaya ne because batun ya shafeni kasan nida my best sister bama moyewa juna komai".?
cikin kuka Nasrim tace "Yaya nima bani da wani wanda yafika Kai ne Dan uwa na wanda muke ciki daya dan Allah kasamo min inda mijina yake ina tsananin son ganin sa naji dalilin tafiyar sa nasan ya Agrif bazai tafi yabarni haka nen ba......
da k'er Kamal da Humairah suka samu nasaran lalashin ta har tayi shiru
****************
bayan wata 1
Nasrim kance take a bedroom din Agrif wanda ta maida shi nata yanzu juyi tayi ta tunanin tun fa last week ya kamata taga period dinta amma taji shiru gashi d'an d'anon bakin ta taji ya sauya ba abinda take so kamar kunun gyada alalan wanke
Knocking taji anayi
"Waye ."? tace
"Nice ranki shi dade."
taji muryar Barira me aikin Hajja
"shigo".
dan rissinawa tayi tace'' ranki shi dade ke ake Kira Breakfast."
shafa goshin ta tayi tare da mai da gashin ta da yarufe mata rabin fuskan ta tadan yamutsa fuska tace'' kai Aunty Barira bar breakfast din nan dan Allah idan ba damuwa ina son idan kika gama sallaman kowa ki dan had'amin min kunun madara".
"ba damuwa ranki shi dade yanzu zan hada miki na gama komai sai de hajiya babba tace lalle lalle kizo wajen break din sai na kai miki can ko"?.
tsaki tayi tace'' Hajja matsala".
Hajja tana kallon Nasrim tace'' wai ke meke damun ki kike wani tottoshe mana hanci".?
daya hannun tasake sawa akan haccin nata cikin in ina tace''
" Hajja warin tafarnuwa sai turaren daddy d.....
ai kafin ta k'arasa sai ga aman yayi yink'urin kwace mata da sauri ta mek'e ta k'arasa kan fanfon wanke hannun da yake gefen dirning din tana kwara aman cikin dan tangaran din cikin fanfon
Hajja sai gyada kai take tana kallon ta har tagama suma su ummu sun kuyar da kai kawai su kayi kowa da abin da yake sak'awa a zuciyar sa
Kamal ne ya tashi ya rike kafadun ta yana cewa sorry my best sister ko muje hospital ne".?
"a a Yaya Kamal hutawa kawai nake son yi".
tayi maganan tana Shirin sauk'a a dining room din
Mama tace'' amma baki ci komai ba daughter jiya ma baki zo wajen cin abincin dare ba".
"Mama zan sha kunnun Madara nasa Barira zata min".
Daddy yace "daughter how are you feelings now?
"Al'hamdulillah daddy tace tareda sauk'a dining room din zuwa cikin parlourn cikin kujera 2 sitar tazube tana cigaba da sauke numfashi
Humairah ce taje ta anso mata kunnu a cup tazuba ta bata tana dan kurba kamar dole cikin sanyin murya Humairah tace'' na rasa me ma zance miki Nasrim ina jin kunyar abin da dan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 40