Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Chaina da sunan zaki wada wani chemist ashe mutane zaki bawa wata daya da yawuce kin karbi biyu sai jiya kika karbi daya kin cuceni nikam". Mommy tace'' wai ni me nayiwa mutane."?!!!!!!??? Abu yace "me kikayiwa kanki de haba Fanna me kike so nan duniya baki samo ba idan dukiya ne keda talauci har abadan amma kika jefa kanki cikin wannan halin gashi yanzu idan ba a yanke miki hukuncin kisa ba to zaki k'are rayuwar ki a pirson ". Murmushi me ciwo mommy tayi tace'' shi kenan na daukawa kaina asaki Nasrim tunda nice me lefi duk abin da ake zargina dashi nayi Nasrim kuma a sake ta". Nasir yace "hakan bazai yuwu ba ita Nasrim rai har ukku ta kashe ke kuma ansame ki da safaran kwayoyin poison sannan kin sawa yara jikokin ki daya yamutu daya ta tahi yanzu kuma yau kin sawa uwar mijin ki wanda ta na nan rai ahannun Allah ke lefinki da ban lefin y'ar daban". cikin mamaki mommy ta daka har inda Nasir yake tace'' kai ma ka yarda nice nayi duk wannan kulleleniyar ko Nasir". Mommy ai ance ke kika cewa Hajja zata ga aikin tubebbiya so FURUCIN ki ne." girgiza kai mommy tayi tace'' TABBAS NASURUDDEEN WANNAN *FURUCINA NE* amma ka yarda zan aikata hakan". tabe baki yayi ya d'aga kafadun sa yace" me zai hana na yarda nasan abinda yake jikin zuciyar ki ne ai *ZUCIYAR MUTUM BIRNIN SA* ". ya k'arashe maganan yana juyawa ita kuma mommy police suka kamata suka shiga da ita cikin motan cikin kuka maimunatu me aikin mommy ta dauki waya ta kira Dr Hafsa tana gaya masa wannan sabon labarin Mommy acikin cell ta kalli Barira tace'' Barira dan Allah ki dubi zaman da mukayi dake tun baki kai budurwa ba har Allah yayi na hadaki da drive na kukayi aure na dauki duk wani d'awai niyar ku da dangin ku da mijin ki da ranan ku na zauna daku bisa Amana ki dubi da rajan wannan ki gayamin Wanda yasaki wannan aikin ni wllh zan sa afitar dake kuma bazan gayawa kowa bani kawai rayuwar nasrim nake son kubutarwa kinga Nasrim y'ar kice kema". dariya Barira tayi tace'' mommy dawayo zaki min to dan kin min aure ina zauna a k'ar k'ashin ki sai me ba wahala nake miki ba wahalan da nakeyi dake kin isa kiyiwa kan kine ko kudin ki zai miki to Wanda yasani aikin kudin da zai bani yanke talaucine nima yanzu gashin kaina zanje naci na dauki ma aikata masu yimin shidima duk iko da isan da kikayi min da wahalan da na sha akansu zan sauke maganan zaki sa asake ni malama kiyi ta kanki ni yanzu za azo ayi belling dina". tana rufe bakin ta kafin mommy tashi magana akace Barira Adamu tazo aka bude mata har zata fita tajuya tace " ammm Mommy zandan bude akwain gol din ki zan Dan zab'i wanda suka min kinsan na zama Hajjjaju." ta k'arashe maganan tana d'agawa mommy kafada tare da canza tafiya irin kita tama zama Hajiyar tafice police din yaja kofar yasake kullewa dafe kanta mommy tayi tace BARIRA aminceciya ta ke duniya bajimawa aka zo akace Mommy tazo ahankali tamek'e tabi yar sanda Dr Hafsa tagani a zaune a falon station din tazuba uban takumi mommy dafa Dr Hafsa tayi firgir ta juyo mek'ewa tayi tsaye tace'' Fanna kece acikin wannan halin waini meyake faruwa ne meyasa duk wannan abubuwan suke faruwa dake Dr Fanna ke macece me son ibada me yawan kyauta mewancan tausayi me yasa why why Fanna"?. zama mommy tayi tace'' Hafsa sai yanzu na gane duk akan me duk wannan abubuwan suke furuwa dani Dr Hafsa nayi kuskure babban duk wannan abunda yake samuna na gama nazarin hakkin mama Emaka ne mama ta tana Sona tasha wahala akaina Mama har faskaren itace dayi tayi tuyan kosai tayi dako akai na duk dan tabani ingan taccen rayuwa duk wanda ya batamin rai Ina yarinya Mama sai inda k'arfin ta ya k'are tasha fada da mutane a kaina ta nuna min gata da son da ban taba ganin wata uwar ta nunawa y'arta ba amma lokacin daya na gudu na barta akan soyayya da kuma ra ayin zama musulma burina duk ka yacika narayu cikin in'ima wanda harda masu aiki na ma motar da suka ga dama suke hawa a duniya gaba daya ahalin yanzu idan banzo na 8 a masu kudi ba to bazan haura na 10 ba amma nabar mahaifiyata da danginta cikin talauci yanzu idan mama emeka taji nice Dr Fanna 3brother zata yafemin nayi kuskure babban a da tsoron masifan mama emeka ne ya hanali zuwa amma yanzu ai ba abinda zata iyamin meyasa banje na sauk'e hakkin ta dayake kaina amatsayin y'a ba duk da airniyace tana da hakkin akaina Allah bazai barni ba Ina son ganin Mama na duniya ta shagalar dani na manta uwar ta haifeni sai yau na tuna da ita ina buk'atan adduar Mama Dr Hafsa mama ta kawai nake son gani tabbas hakkinta ne yafara bibiyata nasan ta rayu cikin kunci adalilin rashina ". Dr Hafsa ta numfasa tace'' hakane amma yanzu mu fuskanci halinda kike cikin idan kika fita zamuje wajen Mama zata yafe mana maimunatu tamin bayani a rar rabe naje nasamu nasir amma yana gaya min wasu magan ganu da ban gansu dasu ba meyake faruwa". Mommy cikin kuka tayiwa Dr Hafsa bayani Numfasawa Dr Hafsa tayi tace'' kinsan wanake zargi yanzu kuma NASIR nake zargi doctor". girgiza kai mommy tayi tace'' Nasir bazai taba min haka ba duk da bai goyi bayana ba nasan mutumne da yake bayan gaskiya akoda yaushi azaton sa Ina da lefine shiyasa bai shiga cikin lamarina ba amma nasan watarana zai kuka da kansa idan abin yabiyo ta kansa". cikin b'acin rai Dr Hafsa tace'' Fanna ki ajiye duk wani yarda da ki kayiwa Nasir ki bude Idon ki idan ba haka ba wllh haka zai gama dake dama so dayawa abinda kake son tashi Allah zai jarrabeka ni danaji FURUCIN Nasir akan ki tabbas na zar geshi". Mommy hannun Dr Hafsa takama tace'' Dr kidena zaigin Nasir akan me Nasir zai min haka". Dr Hafsa tace'' akan dukiya mana ba kin dauki dukiyar ki gaba daya kin dank'a masa ma yayi nutso aciki yaji dad'i yana tunanin yazama nasa saboda baki da yaro namiji sai kuma ga Nasrim ta haifi maza kinga dukiya wata rana zai zama na Nasrim ne da yaran ta shiyasa ya kashe mijin ta da yaran ta kuma ya d'aura al'hakin kisan akan ita Nasrim yanzu haka kimga wannan *sammaci* ne na daukaka k'ara wai bai yarda da hukuncin da aka yankewa Nasrim na zama agidan yari ba sai de a yanke mata hukuncin kisa kuma gashi kema ance kotu za aturaki kinga dukiya yazama nasa yanda yahau kan dukiyar nan ba Wanda ya isa ya k'owace". Girgiza kai mommy tayi tace'' Ah Ah Ah Hafsa Kar ki rabamin hankali karki da samin wani abu azuciya akan Nasir Nasir Amana ne awajena kuma Nasir bazai taba min haka ba duk Wanda ya shirya wannan to da niyar yarabamu da Nasir yayi dama kuma wllh kowaye ba zanyi nasara Allah yana ji yana gani". tsaki dr Hafsa tayi ta tashi zata tafi mommy ta rik'ota tace'' Hafsa ya Nasrim kin je wajen ta kuwa".? cikin b'acin rai Dr Hafsa tace'' eh anji ma zan koma akwai lawyer da yace na rakashi Nasrim akwai taurin kai irin naki har yanzu taki bada hadin Kai tayi bayani yanda lawyer zasuyi aiki akan sa saboda cese babban ne a high court anan za ayi Shari'a amma yanzu kafin nan zanyi cuku cukun beliln din ki dan idan kina nan aikin bazai tafi yanda yakamata ba duk dama Ayman da Ramadan da Kamal suna bakin k'okarin su k..... Police din da yake tsaye akan sune ya ce Hajiya lokaci yayi haka de mommy ta dashi Dr Hafsa kuma tawuce office din D P O Difio yace Hajiya cese din doctor Fanna babban ne bazamu iya bada belling din ta ba yanzu haka ma cuku cukun turata kotu muke idan kotu ta bada beliln to Al'hamdulillah". haka Dr Hafsa ta hakura ta karasa gida tana zuwa gida abakin get ta tadda motan yan sanda da kuma wasu motancin 3 A FULL har anbude mata get zata shiga wani police ya dakadar da ita dacewa ita suke jira sunyi arrested dinta cikin mamaki tace'' menayi motan da yake tsakiyan motocin 3Afull ya nuna mata fitowa tayi ta karasa wajen motan ahankali Nasir ya bude kofar yafito da k'afar sa daya wajen Ido cikin ido ya kalli Dr Hafsa yace "Mom yakike"?. "Lafiya Nasir meyake faruwa ne". Numfasawa yayi tareda kunna mata recorder din muryar ta acikin wayan sa inda take cewa Nasir take zargi ya mek'a mata sai da tagama ji ta mek'a masa tace "kenan a yan sandan ne aka samu wani muna fikin ya tura maka tattaunawar mu ko." murmushi yayi yace " ba munafiki bane akan aikin sa yake". "Dr Hafsa tace'' shikenan yanzu yakake son ayi"? "Mom baki ji police yace za atafi dake ba Ina neman hakkin na ne akan kazafi da kika min dan k'azafin kisan kai ba k'aramin cese bane". Dr Hafsa tace'' Nasir kai ba mutum bane butulu azzalumin maci Amana ban taba ganin azzalumin irin kaba Dr Fanna kayiwa haka matar da har yanzu bata yarda kaine kake kulla mata duk wannan abun ba yanzu gashi ni da nake k'ok'arin akan naga tafidda ta nima kajefani cikin wani hali to wa zai tsayewa Fanna bata da kowa". cikin sauri ya k'atse ta "Ah Ah Ah Mom kika jefa kanki de Sharri na miki baki fada ba to Nasara baya yafiya kuma ba a sabawa umarnin sa." ya k'arashe maganan zai ja kofar motan yarufe Amira da take cikin gida tafito da gudu tace'' haba Ya Nasir Mom cefa idan bakaji nauyin ta haifi irinka ba ai zakaji nauyin ya Ayman ko Ya Aliyu". wani kallon kekuma awa Nasir ya mata yace "ta shiga cese din kidan mune cese din gidan mu kuma hatta mommy ban ragawa ba balle ita cese din gidan mu family issue ne idan bare ya shiga bazai masa dad'i ba dan haka cikin ku duk Wanda yace zai shiga to zai gama rayuwar sa agidan prison bayan haka Ina kuma Wornig din ku duk Wanda yayi gan gancin zuwa acikin ku da sunan zanyi belling din Dr Hafsa to shima zai gama rayuwar, sa a prison Yana gama fadan haka yaja kofar yarufe direba yaja Kuka Amira ta fashe dashi tana gani akayi cusa momn ta amota aka tafi *Ummmm wannan rikicin na gidan manya ne Dr Hafsa kin kain ki sai Allah yafiddaki* *Tofa masoya muje zuwa ko ya Izza da Humaira zasu kasance ko ya ya Nasrim take a* furzin BATUL *ban taba kuka acikin labarin na iran na yauba idon har dishi dishi yake dak'er nayi typing wllh pg yau yaman tausayi Sosai mommy tana cikin wani halin mutanen duniya akan dukiyar ba abinda bazasu iya ba wani lokacin kai talakan kafime kudin kwanciyar hankalin* *BJ* *08062383027* [4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE* _rikicin babban gida_ *NA* *BATUL ADAM JATTKO* *masoya Ina godiya sosai da comment din ku Allah yabar kauna* 🤝 17 *Prison* "kai kai kai ke dan uban ki haka ake surfen marara kiga ko dusa bai faraba shine kika bari kika zauna dan uban ki bayin kine zasu miki surfen da za a dafa abincin abaki". ta k'arashe maganan tana d'aga kulkin hannun ta zata dokawa Nasrim da sauri Nasrim ta mek'e tace'' ma'am dan Allah kiyi hakuri wllh hannuna ciwo yakeyi tayi maganan tana nuna mata tafukan hannun ta da yaduru ruwa sabar rike Tab'arya ". "ke ki fa kiyayeni baki sanni bako ina miki sassauci nefa akan ke bak'uwa ce amma naga ke zumace sai da wuto dan haka kiyi surfennan tas yafita gacan wankin barguna na mokofta na na nazo dashi kezaki wanke tsaf Nasrim sake zubewa tayi a gaban shrgegiyar matan da tasha stocking cikin uniform na ma'aikatan gidan prison "Dan Allah dan Allah ma'am bani da lafiya Wllh". kallon ta matar tayi tace'' rashin lafiya kike ke ba rain ma gaba daya kika dauka ba dan Allah ya d'aura miki dan rashin lafiya zaki damu mutane ke ko ba kece Halima 3Afull ba wanda labarin ki yacike duniya oganniyar marassa Ima'ni ashe gado kikayi gashe can uwar ki ma taso kashe kakar ku uwar mijin ta ta hanya saka mata poisonin acikin abinci wai dan bata goyi bayan ku ba kai ni da zuma naji a cikin a daidata a nacewa ma tsohuwar ta mutu kinga gada kikayi awajen uwarki kisa saboda kuna da kudi". "Paison mommy Hajja ta mutu to ina mommy me aka mata ita kulleta akai .? tana magana cikin sauri kamar zata janyo amsan abakin matar tabe baki matar tayi tace'' ai an kulle shegiya ashe anguluce da kan zabo kullum ita kenan a gidajen radio rerere da baki tana tallata aikin al'kairin da takeyi kowa kaji Dr Fanna three brother kamar ita dayace me kudi a duniya ashe de wai kudin nata bata hanyan halak ta Tara ba haba ai dama wannan dukiya da ayar tambaya akansa shi kansa Abdulsamad din fa cikin dama cikin shekaru kadan yayi kudin da duk duniya aka Sansa dukiya kullu zakaji anyi kaza an gina ismiya agu kaza an ankaiwa marayun jaha kaza tallafin gashi daga k'arshe hau ai ya gama fadawa kan ki da uwar taki yanz.......... katse ta Nasrim tayi dacewa "Dan Allah yanzu ina mommy tana ina". tana can cell mana tana ta kanta daga k'arshe nan za a kawota ku hade ku cigaba da girban abinda kuka shuka". wani irin azabeben Kara Nasrim tasaka ta zube a wajen summemiya asbitin cikin prison din aka kaita doctor din ita ma ma'aikaciyar gidan prison din ce tace'' haba madam Timona nafa gaya miki yarinyar nan ki bita a sannu tana da k'aramin ciki sannan bata ma cikin nutsuwar ta gaba daya ni wllh duk da tana da lefi tausayin Haliman nan take bani badan komai ba sai yanda magan ganun ta ya baza duniya ko Ina ita kamar ita tafara kisa kowa da abinda yake fada bayan kisan nan ko yau anyishi amma dayake ba sanannu bane shiru kakeji kai shahara da kudi masifa ne Allah mun gode maka da kamar a haka". Madam Timona tace'' ke Safiyya ni wllh baruwana dawani kudin ta ko cikin ta duk abinda sauran sukeyi itama shi zatayi uban ta ma ya yanke mata hukuncin balle mu kuma ya rubuta horo me tsanani ajiki da bai rubuta ba da bazamu saka taba". ta k'arashe maganan tana ficewa can Nasrim ta bude Ido arazane ta mek'e ta zauna zata cire dripe dinda yake hannuta sister Safeeyya ta rik'eta tace'' please Halima kar ki cire". "Doctor dan Allah da gaskene mommy na ma ankama ta dan Allah meyasa rayuwa ta juya mana baya meyasa hakan take faruwa damu wllh mommy tama shirri aka mata kamar yanda aka min nasani mommy bazata kashe Hajja ba". "Please Halima saurara waye yace miki mommyn ki tayi kisan kai karya ne mommy ki ko dazu tazo to abinda yasa bata ganki ba duk Wanda aka yanke masa hukuncin irin naki ana jimawa ba azo masa visiting ba kinga ke yayanki Kamal jiya yazo kuma Dr Hafsa tazo shine aka hana mommy ganin ki amma tazo". Nasrim tace "wllh wancan maam din ce take gayamin yanzu". sister Safeeyya tace'' auke dama wancen mahaukaciyar ce ta gaya miki kuma kika yarda kinga alamun hankali a tattare da ita ai mahaukaciya ce". shiru Nasrim tayi tabbas da alaman hauka ajikin matar kam ko dan ba sabawa tayi da ganin irin wannan mutanen ba ita hatta masu aikin gidan su sunfi wannan fasali wai ahakan ita ma aikaciyar gomnati ajiyar zuciya ta sauke tace'' shikenan Allah yakere mommy da Khafulan da Zainab". Sister Safeeyya tace'' Amin harda abinda yake jikin ki ko"? da sauri Nasrim ta shafa cikin ta tabbas tayi wata biyu bata ga period din ta ba wannan hargitsin ne ya hana ta gane ahankali ta shafa cikin na ta koma ta kanta tana ambaton Agrif haka zakamin katafi ka barni awannan duniya Allah kadau Raina ka kai inda ka kai na mijina towai ni mema ya faru har yamutu ah ah na tuna Izza ce tace zata shigo rayuwar mu amma ban kashe shiba fa mijina nefa yanka kane fa kawai kawai dan kaji tsoro kace kafasa ai da zan kashe da tun lokacin dana yan kekan zan kashe ka amma hannu ka fa kawai na yanka kuma ai kaya femin zamu gudu fa kace ni dakai mun saba yafewa junan mu fa ..... Sister Safeeyya tace'' dan Allah Halima kiyi hakuri ki bawa Brain dinki huto kinga fa har yanzu arikice kike ai da tun farko kin bawa lawyer ki hadin Kai da tun azaman farko baza akayo ki nan ba dan bawani hujja sashishi da yatabbatar da cewa kece ki kayi kisan in kece a video din da yaron ki yamiki ai bakiyi magana anji muryar ki ba kuma fuska arufe ida kece meyasa zaki rufe fuska tunda da faro fuska abude kikayi barazanan kuma meyasa akayi deleted din CC TV na gidan daga karfe daya na dare zuwa k'arfe biyu inda kece meysa bazaki yi delete din daga inda kika wasa wuka harzuwa inda kike masa farazana ba kai wannan abinma ba na dauka bane kibawa Brain naka hutu insha Allah za adauka k'ara gaskiya zai fito akama melefi a dauwa mijin ki da yaran ki fansa kiyi kodan yarinyar ki macce idan kika bar abin ahaka zai shafi yaruwar y'arki idan ta girma me auran tama sai ta rasa za ace ai uwar ta ita takashe uban ta akan kishi kinga zaki jefa rayuwar ta cikin matsala ki daure ki zama jaruma ko dan yaruwar y'arki shi namiji bashi da matsala Sosai kamar maccen". girgiza kai Nasrim tayi tace "a a akasheni ni dan Allah bana son na kashe kaina na tashi kafura bayan Agrif musulmine kinga bazamu haduba nafison akasheni dan Allah Ina son na mutu". hannu ta sister Safeeyya ta sake kamawa tace" kinsan wani abu Halima idan kika kuskura aka daukaka k'ara kika amsa ke kika kashe su bayan kina da daman da zaki kubutar da kan ki wllh da keda Wanda ta rataya kanta ta kashe kanta daya bazaki taba ko hada hanya da Haruna ba amma idan kika fadi gaskiya wllh akwai hujjojin k'arfafa da zaki fita cikin sauk'i a zaman farko ma dan haka ki daure ni kuma idan lawyer ki yazo nace masa yanemi k'arin lokaci dan ki sake samun nutsuwa dan saura kwana ashirin da ukku ayi zaman amma zance yanemin k'arin lokaci baki da lafiya zan bashi katin ki yakai dan asan kina da ciki kafin lokacin kin gama shiga hankalinki Agrif da yaran ki yanzu sunfiki samun nutsuwa nuna gidan aljannan ki kwantar da hankalin ki kinji wata rana zaku hadu tunda dole kowane rai sai ya d'an d'ani mutuwa". Nasrim tace" aunty Agrif dan aljannan ne duk halinsa irin na yan aljannan ne hakuri saurin yafiya sauk'in Kai tsoron Allah biyayya ka iyaye tausayi Kai wayo gidan marayun sa na Zaria ko wa zai na kula dasu yanzu bayan haka akwai kuragu da makafi da sauran nakasassu da yake biyan su albashi duk wata dubu talatin wa zaici gaba da biyan su dama ni yake sakawa ko baya k'asan nake vocher duk wata sai ansamu k'arin mutane yanzu waye zanyi duk wannan". Sister Safeeyya tace'' ke Nasrim amma sai kin yarda kin rayu ke zaki cikaba da yimasa sadakatun jariya duk abinda mutum yafara amma Allah bai bashi ikon gamashi ba ya mutu akai to duk wanda yazo ya daura daga inda yatsaya Allah zai bawa wancan ma ladan sa shima Wanda yafara yai bashi batare da yaragewa kowa ba wannan Yana daga cikin adalcin Allah da rahaman sa yanzu ko shekara nawa kikayi kinayi shi Yana da lada kema haka idan kika koma ga Allah duk Wanda yazo yasake farawa kina da Lada shiwanda yafaran Yana dashi shima Haruna Yana da shi dan sada katunl'jariya ba karamin abu bane Allah kamamu ikon yin sa ko da kadan ne". numfasawa tayi tace'' insha Allah Aunty inde da Raina sai sai na k'ara daga inda ya tsaya yanzu haka inda za aduba account din Agrif wllh baza asamu kyakkyawar Million talatin ba duk yayi kyau dasu kullum bayar wa yake su ya Kamal har company ne dasu Abbaty ma k'anin sa amma shi kullum idan nace meyasa ba zayyi tatali ba tunda dukiyar ba dashi bace dukiyar mutum ba abin dogaro bane sai yace'' shima rai ba abin dogaro mane Wanda kabayar shine naka acan inda ran zaije ashe da gaske tanadin yakeyiwa kansa Allah yasa halayen sa masu kyau subishi wayoo Haruna meyake faruwa". b'ata rai sister Safeeyya tayi tace''zaki fara ko bari ma na miki alluran bacci kada wancan azzalumin tazo taga idon ki biyu ta ce kikoma ciki". ********************** *Three brother house* da alama meeting akayi Hajja an salamota tana zaune Nasir cikin b'acin rai yace " to idan ba atsakanin mu abin ya fito ba waye yafito da magana bayan nace abar abin a hannu na ni zan dauki mataki nasa anzo an kama mommy amma kuka fitoda maganan nan a duniya kowa yaji duk inda kalek'a a duniya hoton mommy ne koma wane danshegiyar ne ya fitar to zan bincika na tabbatar a cikin gidan nan abin yafito wllh ko waye idan nasamu dasa hannun sa wllh abin bazayyi dad'i ba kuma a kansa zan dasa binciken abin da yake faruwa". Abbaty yace'' yes boss wllh nima abinda nake son aduba kenan wllh boss Ina tausayin Nasrim". haka de kowa ya tashi gida kam kowa yanzu jikin sa lak'os Hajja ma tunda abin yafaru da ita shiru kake ji tayi k'im tana tsoron ran Izza ma samun Baban tayi tayi masa tatas da cewa idan ma shine yake kashe kashe to wllh itan yakashe Hajja burin na auren Kamal bazai cika ba Dariya yayi yace tasu ma ta ishe su Dan har yanzu rikici gaba daka ma zata b'are musu *Bayan sati 2* *rayuwar Nasrim a gidan yari* balefi ta dan sake har tana shiga cikin abokai sannan aikin wahalan ma yanzu an dan rage mata saboda ciki ta bata wankin barguna bata faskaren itacce sai surfe shara guga da dan k'ananun abubuwa kallon Halima da take dinke uniform nata na firsunoni tayi yarinyar k'arama Sosai cikin tausayawa tace'' niko takwara dan Allah me ki kayi aka yanke miki hukuncin rai da rai ina sausaya muku keda Lawisa da Maryama bazaku wuce shekara ashirin ba kuma gaku makarantan Al'kurani kuna son ibada sai nake ga kamar akasi aka samu balefin ku bane kwata kwata bakuyi suffan masu kisa ba". tashi shiru tana jiran taji daga Haliman Halima ajiye alluran hannun ta tayi ta fuskanci Nasrim Sosai tace'' Aunty Halima wllh bani da lefi kullum Ina gayawa Allah yafito dani kodan mahaifiya ta ni kadaice macce Allah ya daura mata Sona yanzu haka hawan jini ya kamata kullum ana jigila asbiti da ita wllh inason na rayu kodan ita amma gashi har na shekara anan". gyad'a kai Nasrim tayi tace" to wakika kashe". cikin kuka tace'' kamar yanda kika gani arubuce ajikin rigana sunana Halima Ibrahim ni haifefeyar cikin garin nan Kano ce ni daya ce mace acikin yan uwa na maza goma nice ta hudu wato Ina da yayu ukku ina da kanne bakwai maza a cikin anguwar dawanau Ina da uwar d'aki aunty amarya Wanda tana da uwar gidan ta me yara Tara ita kuma uwar dakin tawa amarya ce dan haifuwar fari ma tayi in zata shiga wanka dasafe ni take K'ira na rike mata jaririn ta idan

Chapter 20 of 40