atake yaba
suna komawa anguwar mai anguwa yatara mutane shedu gida yazama na mlm Ladan
murna awajen mlm Ladan da iyalen gidan sa ba acewa komai abin da basu taɓa tsammani ba
Nasir yafito da dan kayansa cikin jakan keda
yazube agaban malam da matan sa da yaran sa da suke ta murna
yace " malam nagode sosai da karamcin ku bazan taba mantawa da kuba nakoyi abubuwa dayawa daga gidan nan wanda kuɗi bazai tsayesu ba Baba ga ragowar kuɗin kaja *jari*
ni yau zanyi gaba Allah yasaka muku da alkairi".
cikin sauri Umma da Mama sukace kamar yaya Ahamed ina zaka."?
" Umma bazan iya rayuwa a gidan da akasaya akuɗin wannan zoɓen bane daganan ya kwashe tarishin rayuwar sa yagaya musu amma bai ce shi daga 3Afull ya fito ba
da zaifita daga yaran har iyayen kuka suke sosai
matsawa yayi kusa da sadiya cikin sanyin murya yace " my HALIMA yau de shi'shigi zai tafi amma kisa aranki zan zo".
cikin kuka yaran suke cewa dan Allah yaya ka dawo mu bamason gidan kai mukeso dan Allah kar ka tafi shima Malam yameƙe yace " inde gidane mun hakura Ahamed daw..........
*******************
cikin murmushi Nasrim da tayi parking tace " au kana nan kenan ranka shi dade
".
ta ƙarahe maganan tana dauko jakar t abayan mota tareda juyowa tana kallon kyakkyawan saurayin da yake azaune
a saman motan durƙowa yayi yana murmushi
yace " ke kuma baki so hakan bako tunda naga alaman guduna kike ko".
ba haka bane
Habib kawai de ban zaci zan zon dawuri ba sorry".
"bawani sorry da zaki cemin Halima tun yaushe nake bin bayanki kike wani wulaƙantani to koke ƴar golce na hakura dake ki auri tsohon korton naki da kije jira yazo banda ba so makaho me zanyi dake ina dan gidan shugaban ƙasa banyi auren fariba na tsaya ina kulaki banza karuwa dake to dama i..........
"Habib ni kake kira da karuwa".
" au har dan nace miki karuwa kike jin haushi dan ban kiraki da asalin sunan naki ba kefa galefin zina gana cin amanan aure gana haifuwan yara shegu gana kisan kai soboda kada yaran su girma susan gaskiya kika kashe su saboda kina nason ko mawa wajen kortonki kika kashe mijin ki da hadin bakin ki kortona ki shi ya gudu da asiri yatonu k............
"da kata Habib wllh ni ban taba aikata *zina* ba asali ma ba abin dana tsana irin aikata zina amma kaine mutum na hudu da sukamin wannan gorin bazan dauka ba yanzu zan nemi hakkina na ƙazafin zina a wajen ka ba ɗan hugaban ƙasa ba ko ɗan majalisan ɗinkin duniya ne kai b".
cikin tsawa shima Habib yace "dalla malama ki rufawa mutane baki waye bai san da wannan ba afadin ƙasan nan ."
daganan yafara bata rabarin tiryan tiryan kamar a
gaban sa akayi harda video din jayayyar da Nasir da Agrif sukayi dayake Kamal alokacin ya watsa duniya aɓoye saide an dakatar da abin dawuri
amma shi Habib da yake amin nin Kamal ne har video din ranan da aka haifi Zainab yana dashi da amsan da Nasir ya bawa Agrif nacewa Zainab ma tashi ce da kuma tambayar da shi Agrif din yamata duk an gajerun videos
abin kamar shirin film take gani har
murmushi yayi yace
"to akolacin da Kamal ya turomin wannan wllh jinayi kamar ni kike aure dan haushi har nayiwa Kamal faɗan meyasa yafito dashi saboda son da nake miki tun kina prison nayiwa kai na alƙawarin kina fitowa zan aureki ashe ke daduron ki kikeso shi kike jira ayanzu da kaina zan sake ya ɗa wannnan video tunda anyi delete din wancan wannan nawan zaifi jan hankalin mutane ma idan baki yamiki cah naga ta jirar kwarto".
Nasrim wani irin duhu ta fara gani jin zata fadi yasa tayi saurin dafa mota tana gani Habib ya shiga mota jami'an tsaron sa suka taka masa baya suka fice a gidan da motocin su
NASRIM cikin wani irin murya tace" me yake faruwa? !!!!!!!!..................
*tofa masoya anzo kusa zuwa wajen fa 👯👯 comments dunku yafara sanyi nima typing dina yafara sanyi yawan comments yawan typing*
*SORRY SIS NAYI TYPING network ya hana bansamu nayi posting ba ni ina ganin duk messages din ku nawa baya tafiya jiya har 12 ina online naga ko grp daya yaje amma bai samu ba sorry*
*B JATTKO*
08062383072
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
( *rikincin babban gida*)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
*26*
*GIDAN*
*MALAM LADAN*
Malam Ladan yace "Ahamed shikenan mubar gidan mukoma wani gidan ina da wani babban gona da nagada tun iyaye da kakanni yanzu yakusa shiga gari har anfari gine gine awajen zan saida goban sai mubar ko fuloti shida ne na dauki fuloti daya na gina suran kuma kai da ƙannen ka idan kuntashi kowa yayi nasa ginin".
nisawa Nasir yayi yace "Malam abinda baka gane ba shine daga yau idan ban bar gidan nan ba za azo nemana dalilin wannan zoben dana saida bakajiba mutumin yayi waya da company three brother nan zai kai zoben kuma yana kaiwa ansan nawane akwai yan uwana suna nemana dole su matsawa Alhajin da yakai musu yafada musu inda nake kuma gasan wanda yasayi zoben da sanayya sosai tsakaninsa da Alhaji mai gidan nan kaga dole asan inda nake nikuma bana buƙatan hakan yanzu saboda Mommy ta tace bata son ganina bata ƙaunan sake ganina arayuwa nikuma duk abinda bataso na barshi kenan banason ta sake ganina saide inason ƴan uwana ina musu adduar fadan alkairi MALAM tafiya ta baya nufin nun rabu har abadan zan dinga ziyaran ku insha Allah kuma ku daukeni a matsayin ɗa bani da wanda yafiku a yanzu".
ajiyar zuciya Malam Ladan ya sauƙe
yace " shikenan AHAMED Allah yamaka albarka ya kare gabanka da bayanka ALKAIRIN ALLAH ya sauka aduk inda zakaje ya rabbi kamar yanda akayi tuggu aka rabaka da masoyan ka da dukiyar da mahaifin ka ya tara ya Allah yabaka fiyeda abinda ABDULSAMAD yatara
Allah kuma yasa kwanciyar hankali cikin rayuwar ka".
Amin Amin matan da duk yaran suka hada baki suka faɗa
Malam yace "ina zuwa..
yashiga ɗakin sa yafito
da kudi ahannun sa zaikai kimanin dubu ashirin da biyar
yace " gawannan kayi guzuri dashi nasan bakason ruwa haka kar ka galabaita kafin kasamu wani sana'ar natara wannan kudinne saboda na biya Alhaji kuɗin hayan sa dubu tabanin ne ba yawa bai haduma kuma gashi gida yazama nawa ka karɓa".
Nasir hawayeni ya taru a idon sa wai yau shine akeyiwa yauta da dubu 25 da sauri ya maida hawayen yasa hannu biyu ya jarɓa yayi godiya
Mama da take ta kuka itama tayi saurin shiga ɗaki tafito da kudi ahannun da batama san yawan suba zasu kai ƙimanin dubu arbain tace nima ga wannan Ahamed kanemi sana"a haka Umma duk yaran gidan saida suka dinga fasa asusun su na cewa Yaya gashi yaya gashi zuciyar Nasir yagama karaya kanin yanda yaran da iyayen suke kuka suna meƙa masa kuɗi bai san sanda yazu ɓe gwuwowin sa a ƙasa ya rungune autan Malam ɗan da bafi shekara 7 ba sa'an Khafulan da yake ta faman meƙa masa kuɗin yan biyar biyar shima ya fasa asusun sa rungume yaron yayi sosai yana kuka inama familyn sa ma suna sonsa kamar haka meyasa su sanda yace zai tafi bazasu sake ganin saba ko ajikin su har farin ciki ma yagani a fuskokin wasu daga cikin ƴan uwansa,
amma su wadan nan yace musu zai zoma suka shiga wannan tashin hankalin kamar anmusu mutuwa wani irin so suke masa inama zai iya zama dasu amma hakan bazai yuwu ba dole ya tsaya da ƙafafuwan sa kada lokaci yamasa nisa a hankali yaraba jikin sa dana auta Amir yayi kiss din yaro yana meƙewa ya karfi kuɗin duk wanda suke meƙa masa ya zuba acikin jakan sa ya bi duk yaran maza yana haɗa hannu su,
matan yadinga musu murmushi yana kama sunan su
yace "ku cigaba da yimin addua zan zo insha Allah".
har yasa ƙafa zai fita Hamza yace Yaya ga waya dan mudinga jin lafiyar ka dan Allah".
ganin idan bai karɓa ba zasu shiga damuwa yasa hannu yaƙarbi wayan Hamza Cecno k9
yace "thank my brother".
yajuya yafita kuka sosai suka fashe dashi duk su bawanda yayi yunƙurin rakashi sai zubewa da sukayi a wajen
*to sis bay gidan malam ladan zamuyi missing gaskiya ni de har araina naji ina son gida ina ma akan su na kafa jigon labarin ba 3A ba*
********************
*Three brother*
dafe ƙirjinta tayi sosai tana sake mannuwa ajikin motan Usman wani ma aikacin sune yazo da sauri yace " subbahanallahi ranki shidade lafiya".
ya ƙarashe maganan yana tattara mata wayan ta da sauran tarkacen ta daya zube awajen
cikin ladabi yasake cewa "ranki ya dade mushiga ciki k...........
cikin wani irin tsawa ta katseshi da cewa
"bazan daɗe ba nace maka bazan daɗe ba mutuwa zanyi shi Agrif da yamutu baya shuta ba nima mutuwa zanyi menayiwa mutane ake tamin bita da ƙulli haka duk wannan shirin film din yanzu akaina aka shiryashi akan a tozar tani
bazan iya ba yara na ake shegan tawa".
a zabure ta meƙe shima Usman a zabure ya jada baya yana bata haƙuri dan a tunanin sa kansa zatayi da duka
direct part din Mommy wanda yanzu ita da Humaira nan suka koma ta nufa Mommy ma dawowar ta kenan a wajen aiki ta zube a parlur tana maida numfashi da Sauri Barira tayi kanta tana cewa " innalillashi rai ahidade meye haka"?.
cikin in ina Nasrim tace "Mommy Mommy ina Mommy Barira me nayi komai yake sauka akaina wai yanzu zargina ake da lefin aikata zina ni wllh ƙazafin zinan bai dameni kamar shegan tamin yara ba
ba mutum daya ba biyu ba kowa gori abin yafara isata duk wanda yazo yace yana sona idan ban amince ba sai yace kwartona nake jira waye kwarton nawa ......
Mommy da take sauƙowa a steps wani irin faduwan gaba taji kamar ta juya
"tofa ranan da ake gudu yazo" tace afuli
Nasrim meƙewa tayi idon ta yakoma ja sosai ta tako gaban Mommy ta kwashe komai ta gaya mata duk wanda suka mata wannan gorin ya d
taura da
cewa "amma nasan zargine gawai da sharri video haɗa wa akayi ai yanzu ba abinda mutum bazayyi dan yaga ya tozarta dan uwan saba wllh Mommy ƙaran Habib Usman Argugun zanyi inyaso duk abinda zai faru yafaru".
dafa kafaɗan ta Mommy tayi tace "pls my daughter ki nutsu bawa baya kaucewa ƙaddaransa kinji dan Allah kidena ɗaga hankalinki akan wannan yanzu anjima Abun ku yace zayyi meeting zakiji komai meye awajen kiyi hakuri".
"Mommy nayi hakuri fa kike maimaitawa kamar baki fashimci meyake faruwa ba ahegan tamin yara fa akeyi kawai saboda sunyi kama da Nasir harda hada video na ƙarya".
kama hanun ta Mommy tayi suka haura sama
Barira ce taje ɗakin Humaira ta gaya mata alokacin suna tare da Izza
girgiza kai Humaira tayi tace yanzu ya zamuyi sister".
nisawa Izza tayi
tace "gaskiya sis ni shiryawa zanyi na tafi gidan Zahra idan abin yalafa nadawo wllh bazan iya cigaba da ganin Nasrim ahalin da zata shiga idan wannan abu yafito ba kuma dama ko hakan bai faru ba Abu yace yau zai gayawa Nacy komai so bazan iya zama ba".
Humaira ta sauke ajiyar zuciya tace "banso taji awani gun ba dama ɗazu take cemin sunyi da Habib yau zanzo ita kuma gaskiya ta gaji dayi masa ƙarya tunda yanace sai yaturo zata gudu gidan Ameera to bayan yazo ance batanan sai yafita kamar wanda yatafi gaba daya shine fa nace tazo yatafi ashe bai tafi gaba ɗaya ba sai gashi yazo kafin na ƙirata na sanar da ita sai gata na hangosu ta window amma banzaci Habib zayyi haka ba kinsan mutum ne me zuciya kuma tun Nasrim tana budurwa yagama naci bai samu ba sai da nacewa Nasrim idan tasan ba auran sa zatayi ba ta lallaba su rabu lafiya nasan halin Habib sosai ko kamal hakuri yake dashi".
Izza tabe baki tayi tace " me ma zatayi dashi ai bai cika masoyi ba da yacika mosoyi ɓoye mata sirrin ta zayyi ba tona mata asiri agaban ƴan aikin gidan su ba
ai AGRIF shine cikekken masoyi abin so mai ɓoye sirrin masoyi."
murmushi Humee tayi tace " to ta Agrif zaki fara ko".
Izza tace "ba batun zan fara bane kema kinsan halinsa yayi arayuwa nifa ban taba ganin mutum mai hali irin nasa ba nifa ko acikin aljanna na bude idona na ganni da Agrif to nasan aduniya nayi abin kirki ni ko haka ma abani shi ba sai an masa wankan da akace anayi ba".
Humaira tayi murmushi tace" balle ma zaki samu wanda yafishi shegiya kuma ya Aiban ɗin gauro zaki barshi a la'hiran ".
shiru Izza tayi tana sauƙe ajiyar zuciya
Abu yabude taro da addua yace " Halima wannan zaman nakine danke muka taru anan Halima dan Allah ina son duk abin da zakiji ki daukeshi amatsayin ƙaddara wanda bawa bai isa guje masa ba Nasrim duk yanda zakiji abin inason kisa hamdala domin nawani ko wata abin yafi haka ƙazanta ke lawye ce duk da baki daɗe da fara aiki ba nasan kinci karo da cese sosai
dan haka
abin zai zo mana cikin sauƙi idan akayi la'akari da ke ɗin malamar addine ce inason kiyi amfani da illinmin ki da nusuwar ki kisani wani baya haihuwar ɗan wani watama uban da ya haifetane zai mata ciki kuma a haifi abin
wata yayan ta muharramin ta wata ƙanin Baban ta muharramin ta wani ƙani ko wan uwar da ta haifeta wannan abin tun munajin sa a nesa yanzu yazo ƙasar mu munji kuma mungani namu mai sauƙine Nasir ba muharramin ki bane ƙidaure kicigaba da karanta innalillashi abin kam da ciwo wanda ni kaina saida nashiga halin da kwana ne kawai ya tashi ni ciwon abin da zafin sa shiya hana mugaya miki tuntuni amma cigaba da ɓoye miki ba abin da zai haifar sai da nasani mumga misali aɗazu Halima ina me baki hakuri ki daure ba kanki farau ba kiyi hakuri ki daure ba Allah yana ƙinki bane ya dauramiki ina son ...........
shiru yayi yana tsunkuyar da kai
Humairah sarkin kuka har tafara Izza kam dama tagudu
cikin rawan murya Nasrim
tace "Abu meyake faruwa koma meye nasan yana da girma tunda har kayimin wannan jawabin nifa musulmace zan dauki dukkan ƙaddara kamar yanda kace RABBI BAYA DAURAWA BAWANSA ABINDA BAZAI IYA BA dan Allah kugayamin".
Daddy share hawayen sa yayi haka Abbaty ma Hajja ma harda jan majina ita Ummu ko tashi tayi cikin sauri ta fita
Abu yafara tundaga yaran da Nasir yayi mata rapping har zuwa haifuwar yaran ya daura dacewa
amma duk ba lefin NASURU bane AIsha ce tayi bokan tane wai yabata wannan sa'an sukasawa Nasir maganin sha'awa tunda sunyi bincike son gano Nasir ba wanda yakeso arayuwar sa *saike* ta gaya mana wannan ne aranan da tace musameta a prison kuma agaban ki tafara faɗa amma da akazo daidai nan Fanna tace Abbaty yafita dake
daganan yacigaba da bata abinda Mamar tagaya musu wanda ba abari Nasrim tajiba harzuwa ƙarshe
shiru tayi tana kallon kowa har sunfara jin daɗi Nasrim ta dauki abin da sauki
sai kawai sukaga ta meƙe tana murmushi tace " kun yarda asiri ne ko toni ban yarda ba a video da
Habib yanuna min jiya akwai inda yace ƙaddarata ba mai ƙyau bane har yana warning din Agrig da yarabu dani duk wanda yaraɓeni to shima tasa ƙaddaran ba zatayi yau ba
gashi nan ya ɓata min rayuwa ta yaci zarafi na ya ɓata rayuwar yara na yanzu shikenan Zeenat da lil Agrif ma mutane ba zasu yanda yaran sunna bane suma duk sunbi rububun shegu tabbas yaci na saran ɓata min rayuwa da yayiwa kansa Alƙawari zayyi wannan *FURUCIN SANE*
ko Mama da kamal da suka kashemin miji da yara basu ci zarafina kamar shi ba ai su mutuwa sukayi shi kuma mutuwa yana kan kowa amma tabon haifan yaran shegu har mutuwa ta me nayi me nayi hakan ta faru akaina
a wani irin zabure tayi bakin kofa zata fita da sauri Abbaty ya kamota kokuwar fisgewa ta farayi tana cewa Adamu kabarni bade yana duniya ba wllh sai narama sai na samo shi duk inda yake nice ajarinsa sai na masa tabo mai muni arayuwa
Abu yace "kenan baki yarda da duk abinda na faɗa miki ba ko Halima
ina Nasrim taƙi lallasuwa daga ƙarshi ma suma tayi a hannun Daddy da Abbaty
sai da ta kwana washe gari ta bude ido ta ganta a gadon asbiti dafa kanta tayi tana wani irin sauƙe numfashi
"Mommy". tace cikin murya ta wanda daƙer yake fitowa
Daddy yace" my daughter sannu yanzu meyake damun ki ahankali ta kama hannun Daddy ta daura a ƙerjin ta
tace Daddy wani abune a ƙerjina kaciremin nauyi yake min sosai".
gigiza kai Daddy yayi yace "Halima kin daurawa kanki damuwa dayawa ne zuciyar ki yana barazanan kamuwa da ciwo ki daure mana ki samu sauƙi tanan zaki samu ƙarfin guwiwar Samun Nasir din kirama abinda yamiki amma idan kin daurawa kanki damuwa wani abun yasameki ai Nasir yaci bulus".
ahaka Daddy ya lalla ba Nasrim kamar yanda doctor yafaɗa har ta dinga sauƙe ajiyar zuciya
cikin muryan jin jiki sosai tace "Daddy idona idon BAYAHUDE wllh sai narama wannan *FURUCINA NE* " .
Daddy yace " Eh mana my daughter ai dole ki rama har nafara miki binciken inda yake".
Nasrim abin saida yazame mata kamar hauka hauka daƙer da adduar da lallashi tafara shiga haiyacin ta sai kuma takoma shiru shiru ko tasaka Khaflan agaba tayi ta kuka tana tsinewa Nasir yau ma kamar kullum khaflan yana zaune taje bakin gadon ta
zauna tace " my son zane kakeyi mugani home work ne".
azabure yajanye kayan sa yana turo baki yace " wai mamy banace ki dena kulani ba tunda kina zagin papa na shima kina son ki kashe sa kamar yanda kika kashe min brother na da Abba na yanzu gashi kullum ba ganin su sai Abdul ni wllh nafison Fayyat da Khaldum amma bazan ƙara ganin suba gashi papa ma bayanan kuma shima kina cewa sai kin kashe sa".
girgiza masa kai tayi tace "haba khaflan nifa mamyn kuce ban kashe maka brother din kaba kuma bazan ƙara FURUCUN ZAN KASHE WANI BA ni bance zan kashe papan kaba amma papan ka mugu ne shine kard......
da sauri ya katse ta da cewa "sai de kece muguwa NASRIM pa......
wani irin mari Nasrim ta eibi khaflan dashi tasake yin ball dashi ɗagoshi tayi ta sake zuba masa mari bakin sa hancinsa duk jini yake amma ko kusa ko alaman kuka yaron bayayi sai ma idon sa da yake jefawa cikin nata yana hura hanci itako dukan sa tashi ga yi kamar an aikota ya galabaita sosai amma ba alaman sayyi kuka Allah yatemaka mommy ta shigo
"SUBBAHALALLASHI Nasrim meye haka kashe sa zakiyi shime yasani meye lefin sa".
Mommy lefinsa shine yafiyo halin bayahude mommy ahaka shima wancen bayahuden ya ɓaci yanzu ya haɗamu da gurbataccen jinin sa".
Mommy bata sake tsayawa biyewa Nasrim ba ta ɗaga Khaflan tayi waje dashi dan bashi temakon gaggawa
Nasrim zubewa tayi awajen afili tace "sharri sharri yanzu har yanzu Khaflan yana daukana a wanda tayi kisan kai innalillashi Kamal Nasir Mama wayafi cutata ne ɗana yana zargina da na kashe masa ƴan uwa mutane suna gani na a mazinaciya duk ɓangaren binyun sun min illa ya zanyi Khaflan ya yarda ba lefina bane da wannan aƙidar zai girma zuciyar ɗana zai kinu da ƙiyayata fiye da yanda zuciya NASIR ya ginu akan nice sanadin mutuwar uwar da uban sa khaflan zai min tsanan da ko Nasir bai min shi ba KAMAL MAMA NASIR duk kun cuceni wa yafi cutana cikin ku kun ɓata min duniya ta ya rabbi ka dauki raina ".
Humaira da take shigowa tace " Kamal da uwar sa sunfi cutar dake rai yawuce gaban wasa duk wanda hassadar sa yakai har yakashe rai to yakai ƙololuwar rashin imani ko a wajen ALLAH".
cikin kuka tace
" haba Humairah shima ƙazafin zina bakin san har jikoki na ba."
Humaira tace "za adau matakin rufe bakin mutane inji Hajja".
Hajja ganin yanda NASRIM take cikin damuwa tace a shiya musu tafiya har na sati biyu zuwa island of greece duk wani abinda zai sata nishadi ana mata
*bayan sati ukku*
NASRIM ka tarame sosai tayi mugun yin duhu amma a matakan da aka dauka an ajiye masu gadin a ƙofar babban get duk wanda yace gun Nasrim yazo ta ba abarin sa yashigo macce ko namiji
ayau de tayi shirin fita aiki saboda akwai wani cese da wata sohuwa ta dage sai ta ganta koda ta saurari sohuwar cese din bai kai yakawo ba wai wata yarinya ce ta maƙalewa jikan ta kuma ana zargin mayune ta kwashe masa kuruwa yanace sai ita shine ta shigar da ƙara
Nasrim abin dariya yabata yanda sohuwar ta rikice kamar Hajja takeji shine dalilin fitan ta
har gida taje tasamu matar kuma ta shawo kan jikan nata da lallami da hikima irin nasu na lawyoyi yaron ya abince zai auri cousin dinsa kamar yanda kakar ta buƙata to Nasrim kawai matar nishadi take sakata har tafi Hajja rikicewa da fariyan ɗanta mai kuɗi ne bata magana biyu bata sako Alhaji Isya nawa komai Isya HAJJA TA SORO kenan
*NASIR*
da farko kaduna yaje yakama yawo yana kwana a masallaci har tsowon sati 5 yaude yasake dawowa kano
yawo yake acikin wani anguwa da ganin anguwar anguwar masu kuɗi ne sosai ake zafga rana da yagaji yazauna a ƙarƙashin wani bishiya kusa da wani mutum da yake kan binci yana bacci da alaman mai gadin gidan da suke jikin sane jinginuwa yayi ajikin bishiya kawai sai bacci ya kwaheshi
yana cikin bacci yaji ana tashin sa yana bude idon yaga wannan mutumin ne yace masa
"malam naga da ɗigon sallah agoshin ka kai musuline to lolacin sallah yayi aje ayi sai azo a ci ga ba da jiyar Alhajin ko".
Nasir binsa yayi yayi alwalla a fanfon masallaci bayan an idar da sallah atare suka fito da maigadin wannan gidan
suna zuwa aka fito da abincin mai gadi tayi mai gadin yayiwa Nasir har yace ba zaicima amma mai gadin yamatsa masa dole sukaci tare serious yaji dadin abincin yayi daidai da tes din bakin sa
bayan sun dawo daga sallan la'asar ne mai gadin yake cemasa
"yaro kasan Alhaji bazai zo yanzu ba dare ko da safe yagama rabon kuɗi idan yazo da daddaren ma baya tsayawa shigewa yake ciki dan haka sai da safe ake samun sa guarantee".
nisawa Nasir yayi yace Baba nifa ba maula nazo ba wucewa ma zanyi neman aiki nake ko na ƙarfi ne."
mutumin yace "ayya wllh ka kyauta ai ka ci da gumin ka yafi cida gumin wani
amma idan zaka iya da halin wata sohuwa me masifa da izza tana neman megadi dama tacemin batason baƙin mutum fari tas take so tana mugun son farin fata idan kayi hakuri da irin halinta zaka samu alkairi sosai ga ɗanta duk abinda take so shima yanaso".
Nasir sai da yayi murmushi yace ita kuma amma zanso na ganta zan iya da halita nima kakata haka take".
Maigadin yace "kai ba kamar HAJJA TA SORO ba Izza a cikin ta tsohuwar mai gadin gidan sarkice ALLAH ya ɗaga ɗanta yayi kuɗi kaga gidan da ya konkwatsa mata ita daya sai idan jikokin ta sunzo".
ya ƙarashe maganan yana nuna masa gidan da yakai gida alayin baye shi
yace" ka gani ko wani kallon ma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 40