An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
COMPILED
BY
AYSHA GALADIMA
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURRUCINA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*Page 1*
" Please Madam kar ki damu in sha Allah za ki shiga lfy ki fito lfy mu wannan asbitin aikinmu ba ya samun matsala kin ji? Ki kwantar da hankalinki don kwanciyar hankalinki shi zai ba wa aikinmu karfin gwiwa kin ga a yau ma mata 2 na yi wa Theater nan da sati za ki ji kamar ba ke aka yiwa ba sai de ki sa d'anki a gaba kina kallon sa ki ci kaji ki ci ragon suna".
Dr Fanna ta k'are maganan tana mata murmushi
Hajiya Halima ta yi murmushi cikin azaban ciwo ta ce "Dr ba wani Dan Adam da ya isa guje wa kaddararsa a jikina nake jin ba zan rayu da abin da zan haifa ba, amma don Allah Dr Fanna ina neman alfarma a wajenki dan Allah idan Allah Ya sa ban tashi ba ki rike min d'ana amana kar ya yi maraici yanda ni na yi kuma ina son ki auri Addulsamad mijina ni ban san asalina ba an ce wai hatsari mota muka yi da Babana shi ya yi loosing memory wanda har yanzu bai dawo hayyacinsa ba iya sunansa kaɗai ya sani yake iya fada kullum idan na ce masa Baba ina ne gidanmu su waye danginmu ba ya magana sai de ya ce *Nasuru* ni kuma fuskata ta b'aci aka canza min wata dan da banma san asalin fuskata ta da ba
a gidan su Abdulsamad na samu kaina kuma shi ya zama mijina. Ba wahalar da ban yi ba wajen neman dangina ga shi har ina shirin barin duniya ban san ni wacece ba, ban san dangina ba. Babana bai dawo hayyacinsa ba kuma motan da muka yi accident da shi ance ya kone ba asamu wani bayanai a ciki ba. Ina tausaya wa abin da yake cikina don shi ma na san zai yi rayuwa cikin rashin uwa duk da yana da nagatarcen uba kamar Abdulsamad. Ki ceci rayiwan d'ana ta hanyar auren ubansa dan idan na san a hannunki na bar shi ba ni da sauran damuwa, Dr Fanna kina da tausayi da amana duk da ban san halinki ba, amma ki min alk'awarin za ki auri Addulsamad yana da kirki haka danginsa ma suna da kirki amma hankalina ya fi kwanciya dake"
Juyawa ta yi ta kalli inda mijin nata yake da ganin yanda ya hade fuska ka san ba ya son maganganun da take yi.
Murmushi ta yi ta sake damk'e hannusa ta ce " Ya Abdul na san ba ka son wannan maganganun nawa amma na rasa me ya sa nake yin su nima. Kuma na san ka amince za ka auri Fanna ko da ina raye ne ina son ka dauki Fanna a matsayin Halima ka ga kai ma ka sha cewa muna yanayi da ita. Abdulsamad ka yafemin idan da gaske ne scanning din da akamin namiji ne abinda zan Haifa kasa masa sunan Babana *NASURUDDEEN* idan macece Halima dan Allah ka ce wa dukkan danginka su yafenin, idan Babana ya warke ka ce masa ya yafe min. Ina son sa haka ina son mahaifiyata idan ka ganta ka ce na rayu da son ganinta Abdul Ina SON KA INA SON KA , INA SON KA AURI FANNA SHI NE FANSAR SOYYYAR DA NA MAKA YA ABDULSAMAD ka yafemin"
Cikin rikicewar murya da tsorata da al'amuran nata ya ce
" Halima amma mun gama duk wannan maganganun tun a gida ko? Da kin bari an fara aikin nan da yanzu an gama ma."
Dr Fanna fita ta yi dan wani irin kuka ta ji yana shirin kwace mata da sauri wata Nurse ta bi bayanta
ta ce
"Dr idan ta k'ara wasu minutes za a iya samun matsala fa".
Ficewa ta yi a Theaterroom gabadaya ta yi office dinta nurse Zainab na bin bayanta. Daukan wayanta ta yi akan Table amma ya kubce zai fadi da sauri Zainab ta tare ta ce" Dr wa za a kira miki".
Cikin kuka ta ce "Dr Husaina ko Dr Hafsa".
Zainab ta yi saurin danna K'iran Dr Husaina yana fara ringing ba jimawa ta dauka tana jin an dauka ta karawa kunne Fanna. Dr Fanna cikin kuka tace "Dr ki yi saurin zuwa ceton rai Dan Allah ki hanzarta".
Daga can bangari ta ce "subbahanallah Dr Fanna ya aka yi?".
"Dr Husaina ba lokaci kawai ki kamo hanya na shiga cs amma na kasa na fito".
"Ok gani nan ma ina B Ward na zo duba wani patient ɗina.
Ta kashe wayan ko minta daya ba a yi ba ta fado office din da saurinta.
Fanna ta ce "ga Zainab ku tafi sauran nursing din suna ciki. Husaina ba ta tsaya b'ata lokacin ba ta fita Zainab ta bi bayanta, Dr Fanna ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take a cikin office daga karshe ma bakin Theaterroom din ta je inda yan'uwan Alhaji Abdulsamad suke amma duk ta fisu fita hayyaci shiko Alhaji Abdulsamad tunda ya tsugunna ya maida kansa k'asa bai sake d'agowa ba.
Ba a fi mintuna 30 ba wata nursin ta bito da yaron a hannu da sauri Aisha ta mek'e tana k'arasowa inda take tana mek'a hannu girgiza mata kai nurse din tayi tace "Uwar yaron tun kafin a fara mata aiki ta ce idan muka ciro mu ba wa Dr Fanna."
Duk suka bita da kallon mamaki nursing ta yi inda Dr Fanna take a tsaye kamar an dasa ta ta mek'a mata yaron tayi Dr Fanna jiki na rawa ta karbi yaron tana cewa
"Ita uwar yaron fa yatake?"
Shiru nursing din tayi tana sa hannu cikin aljihunta taciro wani takaddu
"tace gashi tace a baki wannan, a ba wa mijinta wannan"
Fanna ba ta karbi takardun ba tace "Na ce miki ya ita uwar yaron?"
Ajiyar zuciya nursing ta yi cikin harshe turanci ta ce
"ba zan iya cemiki lafiya ba dan gaskiya tayi bleeding sosai..."
Abdulsamad Bai bari ta k'arasa ba ya meke da sauri yana cewa "what!!!" Haɗe da yi hanyan theates room din a zabure, da sauri Alhaji Abdulraham da Abdulmajid suka kama shi cikin wani irin sanyin murya ya ce
"brother ku bar ni na shiga na ga halin da Halima take ciki idan na rasa ta za ku rasa ni bro Dan Allah ku barni kar su fito da ita su ce ta mutu idan nashiga zance kar tamin haka na san tana Sona ba za ta tafi ta bar ni ba. Dan Allah ku bar ni. Da k'er suka ja shi suka fita da shi a falon wata babbar mace wanda da gani ita ce mahaifiyar su Alhaji Abdulsamad Hajja ta meke tana cewa
"Ke bani jikana na gan shi shi ne jikan fari magajin gida wannan nawa ne ko duka ne an ce ka dauki na fari" .
Ba ta sa hannu ta karbi yaron a hannu Dr Fanna da ba ta san ma tanayi ba ciki wani iri gudu ta fad'a d'akin theater din har sun gama dinkin amma suna tsaye a kanta nauran gwajin numfashi suke gyara mata amma ba alaman zai yi aiki a hankali Fanna ta karasa inda Halima take a kwance ta sa hannunta a bayan wuyanta tana laluman jijiyar bayan wuyan nata ta tsanya yatsunta biyu a daidai inda ta san za ta samu jijiyar wanda ko da mutum suma ya yi to za a samu wannan jijiyar tana harbawa idan ya daina to tabbas rai ya tafi ciki wani irin zafi ta cakumi Dr Husaina tana cewa "Why she didn't breathing?
Na ce me ya sa ba ta nunfashi? Halima kar ki min haka me yasa za ki mutu ba tare da kin gayamin dalilin da yasa muka kamu da soyayyar juna lokaci k'ank'ani? Cikin watanni tara na san ki amma ina jin ki kamar wata ɓangare na rayuwata"
Sauran nursing din ne suka kama ta suka fita da ita tana tirjewa.
Sosai family 3brothers suka ji rashin Halima dan yariyar kirki ce har hajja da ba wani damuwa tayi da ita ba ta ji rashi musamman ma oga Abdulsamad ba karamin wahala a kasha ba kafin a samo kansa ya fara magana shi ma da kyar ake jin maganan nasa wanda yawanci ma idan ya ga Nasir jaririnsa yake yi. Dr Fanna kam kullum tana hanyar gidan idan za ta tafi wajen aiki sai ta biya ta gan shi, idan ta tashi sai ta biya kullum da kuka take fita tana so ta ce a ba ta yaron amma tasan bata isa ta fara ba saboda Hajja ta kasa ta tsare.
Gobe ne za a yi sadakar arba'in din Halima duk suna zaune a babban falo akan dining table ana breakfast idon Hajja ne ya yi wani irin cikiwa da kwalla da ta d'aga kai ta kalli yaran nata Abdulmajid Abdulraham matan su zaune agefinsu sai Abdulsamad ne kawai shi kadai ba matarsa tana tausaya masa musamman idan ta tuna a rana daya ta haifesu sunyi karatu lokaci daya sunyi aure lokaci daya amma shi ga shi tasa matar ta mutu, ta goge kwallan idonta ta sauke idonta akan Amina matar Abdulraham wanda ita ma ko yau ko gobe tasake kallon Aisha matar Abdulmajid ita ma da cikin wata biyar da dan kwanaki ahankali ta ce "Allah Ya raba ku lafiya shi ne fatana Allah Ya raya min NASURUDDEEN".
Cikin sanyin murya suka ce Amin shiko Abdulsamad bai yi magana ba sai kawai ya kai hannu kan kujeran gefinsa wanda wajen zaman Halima ne
Hajja ta ce" kar ka damu Abdulsamad za a samu wacce za ta zauna a kai cikin kwanan nan".
Abdulmajid ya ce
"Hajja ai ansamu ma ya kamata ya cika wa matarsa alk'awarin ya auri zabin da ta masa Dr Fanna tana da kirki sosai".
Hajja ta ce" sosai na yaba da hankalinta ganin har yanzu bai samu nusuwa ba ne ya sa ban matsa masa a kan maganarta ba, kyanta a ce an haɗa daurin auren da arba'in din Halima amma Abdulsamad don Allah a yau nake son idan Dr Fanna ta zo kamata magana ya dace ta fada mana garinsu da inda iyayenta suke mu je neman aurenta nide iya bincikena an tabbatar min da cewa aikine ya kawota ba a nan take ba na san de ba zai wuce a ce yar maiduguri bace tunda ga zanen barebari a fuskarta kuma sunanta ma na barebari ne za ta kasance yar maiduguri ko yobe ".
Cikin sanyin murya Abdulsamad ya ce "Hajja da wuri haka ni fa ko maganan ban mata ba a dan ba ni lokaci".
Hajja ta ce
"Ba lokacin da zan ba ka inason ka samu wacce za ta rage maka damuwa kuma na san Dr Fanna wayayyiyar mace ce za ta yi saurin mantar da kai ko m...... "
Ba ta karashe maganar tata ba gani wani irin gumin da Amina matar Abdulraham take tsatssaɓowa, ganin yadda ta tsorata ta tsaya da maganan ya sa duk suka kalli inda take kallo da sauri Abdulraham ya ce "ya de Amina a hankali ta da fashi tare da sauka akan jujeran ta sunkuya k'asa tana ta faman yarfa hannu daidai lokacin Dr Fanna ta shigo tun kafin ta k'arasa ta san halin da ake ciki da sauri ta koma mota ta sako safan hannu tana tafe tana sanya ta har ta karaso tana duba ta ta ga ai kan d'a ne ma yake kokarin fasowa ta kalli mazan da duk sukayi wani cirko-cirko ta ce "Don Allah ku ba mu waje" ko suna ba su ma kai ga ficewa gabadaya ba suka ji kukan yaron a tare suka juyo suka yi murmushi tare da dafa kafadun juna suka fice haifuwa ya zowa Amina da sauki sosai duk da tun dare take abunta amma dayake macce ce mai dauriya da jaruta Koda Abdulraham ya gane cewa ta yi ba wani abu dama ance ana jin haka idan ciki ya tsufa cikin k'ank'ani lokacin Dr Fanna ta gyara Amina da zankadeden jaririnta. Zo ka ga murna a wajen Hajja da yaranta, Nasir ya samu aboki ranan suna yaro ya ci sunan Baban su Abdulsamad Muhammad amma Hajja tace amasa al'kunya da Araf washe garin sunan Araf Hajja ta sake bawa Abdulsamad umarni da babban murya akan yayi wa Dr Fanna magana. Bai yi musu ba bayan zuwanta sai da ta zo fita ya tashi ya bi bayanta Sai da tashiga mota yace "Dr idan ba damuwa in shigo ina son magana dake".
Kallon sa ta yi cikin tausayinsa za ta fito ta ga ya shiga shi ma rufo kofar bangarensa ya yi ita ma ta rufo nata sai da ya ja wasu dak'iku yaja numfashi yace "kin samu daman karanta wasik'ar Halima".
ta ce"E. Duk a kan jaddada alk'awarinta ne da kuma in rik'e mata kai da Nasir da mahaifinta amana".
Yace "ni ma nawa akan hakan ne to ya kiga".
Ta numfasa cikin sanyin murya ta ce "Gaskiya daga b'angarena akwai matsala ina tsoron yanayin mahaifiyarku gani nake kamar ba za ta yarda ka auri y'ar gidan christian ba ".
A firgice ya kalleta yace what Christin kuma ke din dama a kanuri akwai arna".
girgiza masa kai tayi ta ce
"Ni ba kanuri ba ce kamar yanda mutane suke dauka bace nagaji da bawa mutane amsa a a a ne yasa nabari a ni kanuri ce har naje nayi University dina a garin maiduguri dan na koyi irin yaren dan ance a can suke na gaji da jayayya da mutane akwai sanda ina yar secondary a logos wani malaminmu dan kanuri har marina yayi wai ina boye yarena tun daga ranan na bincika ina ne wannan k'abilan ta kanuri suka fi yawa zan je na iya yarensu dan tun ina yarinya na gaji da wannan tambaya da mutane suke min".
Dakatar da ita ya yi yana cewa " kin gane duk wannan bayanan naki bana ganesu sai kin bani labarinki ko zan tsinci wani abu ina cikin firgice Fanna jin ke ba kanuri ba ce".
Wacece Fanna?
" sunana Fanna emeka ni y'ar k'abila ibo ce a cikin garin Legos a anguwar pester na samu kaina sunan mahaifiya ta emeka dalilin zuwana nan arewa bayan gama secondary naga wani da irin zanena shi ne nayi ta nace masa har na san masaukinsa ashe irin ciranin nan ya zo shi dan maiduguri ne wasa-wasa muka kulla soyayya da Sharif ba tare da sanin momyna ba ina kokarin boye mata ne saboda ta tsani musulmai kuma tun ban gama sanin kaina ba momy take koyamin ak'idan k'in musulumci kullum gargadinta da nasihartta akan na guji musulmai duk inda suke momy duk inda taga musulmi sai ta zage shi ta ce mana amma sai ga shi nayi saurayi musulmai a dare daya muka yanke shawaran mu gudu da Sharif zuwa garin su maiduguri iya takardun secondary da primary dinna kawai na dauka muka kamo hanya Sharif shi ma yaji tsoron nuna ni ga mahaifansa, dan haka ya nemi gidan haya ya sani ya kuma nema min makaranta kasancewar takadduna sunyi kyau sosai ba a sha wahaln sama min gurbin karatu a jami'ar ta maiduguri ba shekara bakwai na zama cikekkiyar likita duk da kananun shekaruna a lokacin muka shirya aure da Sharif dan yasamu rufin asiri sosai ya bude shagon kansa a Lagos shi ya gina min wannan gidan da kaga Ina ciki a anguwar sardauna crystal muyi dashi zamu yi auren a boye har mutara yara lokacinda iyayensa ba za su iya cewa ba sa sona ba shi ne dalilinsa na nema min aiki anan zuwan mu kano dan ya tsara a nan zai ajiyeni yas ha fama sosai kafin yasama min aki anan malam aminu kano Iya abinda nasani kenan a tarishina ban taba sanin ina mahaifina ko danginsa ba dan duk sanda nayi gigin tambayar momy emeka Ina Babana to zanci na jaki kuma za ta yi sati bata ba ni abinci ba da kudin makaranta kwata-kwata ba ta bani daman in san waye ubana ba sai de kuma ina wayo Ina gane duk yanda akayi ubana musulmine kuma dan yaren kanuri shi ne yamin wannan zanen da kuma sunan kanuri duk yanda aka yi akwai wani abu me girma da shiga tsakanin su shi ne ta tsane sa."
Abdulsamad yace "baki gayamin ya matsayin ki a adini ba ko kin karbi musulumci".
Ta yi murmushi ta ce "Ai tun a Lagos Sharif ya sa na karbi musulumci ka san duk wani tarbiyar da iyaye zasu bawa yarinya idan ba ayi sa a ba cikin second k'adan soyayya yake rushe shi muna zuwa maiduguri yasani islamiya ta matan aure".
Abdulsamad yace to yanzu ina shi Sharif din".
ta sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu ta gode hawayen da yadade yana kwaranya a fuskan ta
tace" Sharif yayi hasarin mota alokacin da muke tsaka da shirye shiyen auren mu saura kwana biyar a hanyar sa ta dawowa daga Lagos".
ta k'arashe maganan cikin fashewa da kuka sai da ya bari ta yi iya yinta dan shi ma kukan zucin yake na rashin matar sa sai da suka dauki tsawon lokaci cikin sanyin murya yace sorry Dr Fanna namiki alk'awarin za ki same ni fiye da Sharif a rayuwa ke din zabin Halima ce zan iya sadaukar da komai a kan zabinta musamman tunda kika nuna min kina son Nasir kin gama min komai a rayuwa ni sunana Abdulsamad kamar yanda kika gan mu, mu yan ukku ne yan'uwana Abdulmajid Abdulraham.
Asalinmu iyayena duk 'yan nan kano ne a sani yan kofar na'isa amma Hajja wato mahaifiyata tana da dangin mahaifiya a Dardum wani k'wauye a jahar zamfara iya mu ukku nan suka haifa shakara daya da auren su Allah basu mu yara ukku maza a lokaci daya daga kanmu kuma ba ta Kara ba ni Abdulsamad, Abdulraham, Abdulmajid.
Mahaifinmu malam Haruna baza a kira shi me kudi ba sai rufin asiri dan sana ar dinkin maza kawai yakeyi ni Allah yamin nasibin tun ina shekara 9 nake bin Hamza wani abokina shagon Babansa muna taya shi auna kayan masarufi alokacin muna primary ne Allah yayi wa Baban Hamza rasuwa kasancewan suna da yan uba suka raba gado daga nan kasuwa ta rushe adan kudin da nake Tarawa awajen Hajja na ce tabani na sari kayan aleyoyin na yara idan nazo daga makaranta zan dinga kasawa a kofar gida hakan ko akayi Allah Ya sawa abin da na fara kamar wasa albarka har kofar gidanmu ya zama matattaran tara yara saboda ina da fara'a da saurin sabo tun ina bazawa a barantin Hajja har Baba yasa aka bugamin yar benci ina bazawa tun a lokacin ko ina a jikin bencin na rubuta
3brothers ajiki wanda yanzu haka shine 3brothers company a fadin duniya ni kasuwancin bai barni nayi karatu me zurfi ba amma kinga yan uwa na sunyi Abdulraham Lecturer a B. U. K.
Abdulmajid kuma alk'ali abin da yasa zan gaya miki dukiyar gidan mu nawa ne saboda shi sha'anin aure ba a boye-boye na san zama ya yi zama zaki gane to ina son na sheda miki yan'uwana suna da mahimmanci a wajenana kuma sun fiye min komai a rayuwa ba na son ki dauki kanki amatsayi kin fi matansu ki dauka duk kanku ɗaya idan Allah Ya yi aurenmu da ke."
Ta ce "in Sha Allah amma ba ka karasamin ba ya akayi kayi kudi me yawa a cikin k'ananun shekarun naka Wanda har yanzu bazaka wuce shekara talatin ba amma duk Nigeria ba wanda bai san 3.brothers ba".
Murmushi ya yi ya ce "Akwai wani lokaci a lokacin ba zamu wuce shekaru sha bakwai ba, na raka Hamza abokina garin su innarsa kauyen zamfara mun dan fita bayan kari guraren tarihi na ji nayi tuntube da wani abu kamar dusi haka ya dan dulloko da nakalli dutsin sai naga yana shek'i kuma shi ba fari ba shi ba ja ba na tsugunna na bara tonoshi ina mamakin yanda yake shek'i kuma gashi da girma amma a cikin k'asa yake har Hamza da Yakubu suka zo suka karaso Hamza yace 'yade A.3full kake tonan k'asa haka".?
nace ''wllh Hamza wani dutse ne abin sha'awa kunga shi".
Yahaya dayake dan garin ne wani irin zabura yayi yace " kunsan meye wannan kuwa gol nefa ance yanzu sama da shekara 20 ba wanda ya tsinta nima a hoto nagani tabbas wannan shine kuma wllh gomnati ne za su kwace".
Na ce wllh ba zai yuwu ba ni zan tona kayana kuma naje na saida ba wani gomnati da zan bawa ni Allah Ya bawa.
Yahaya ya ce ta yaya? Ina ka san ana sayar da shi wllh kwacewa za suyi su dan baka wani abu ai harmu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 40