Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fara gani dishi dishi, yunƙurin miƙewa ya fara yi domin ya lura abin tana so ta fi karfinsa, sai dai ina, bai iya ko motsin kirki ba, tamkar an sanya igiya ne aka ɗaure shi ɗaurin goro, ƙoƙarin buɗe bakinsa ya yi domin ya kira Mamma, nan ma ina ya kasa, dan kuwa ji ya yi tamkar an ɗaure harshen nasa ne kam, ya kasa. Sanya dukka ilahirin karfinsa ya yi da nufin ya miƙe da karfin gaske, duk da haka a banza man kare, ko motsawa bai iya yi ba, ya juyar da idanuwansa ya kalli gefe guda ma ya kasa, iya saman ɗakin nasa kawai yake iya kallah, duk wata jijiya a jikinsa sai da ta tsaya sak da aiki! Jinin jikinsa duk ya dai'na gudu, nan take idanuwansa suka kara firfitowa waje sosai tamkar zasu faɗi ƙasa, tamkar wadda aka matse sosai, sai ƙoƙarin ya yi magana yake yi, yana son ya kira Mamma ta kawo mashi agaji, amma ina ya kasa, harshensa ma a ɗaure take gam. Dai'dai lokacin Mammar ta faɗo cikin ɗakin tana faɗin. "Tun jiya barci yaki karewa kamar ba lafiya ba, maza ka tashi lokacin motsa jiki ya yi, ka kama ka tafi yawonka ba dole ka gaji ka yi ta barci ba, kafa baya zama waje ɗaya, baka bawa jikinka hakkinsa na hutawa!". Jin motsin shigowar Mamma tana waɗan nan surutan ne yasa gabaɗaya ya ji jikin nasa ta sake, nan take ya ji ya koma normal kamar ba shi ba, abin da ɗaure kai da kuma mamaki. Waro idanuwnsa da suke jajir saboda barci ya yi a kan Maman tasa dake tsaye a kusa da bed ɗin nasa tana faɗin ya tashi su tafi, ya zo sai wani zuba barci yake yi tun jiya da yamma, da daddare ta tashe shi har ta godewa Allah yaki ya tashi, har ruwa ta shafa mashi a fuska, amma yaki tashi, sai dai ya ɗan motsa kaɗan ya sake cigaba da barcin abinsa, da farko abin har ya fara bata tsoro, sai daga baya kuma ta kyale shi kawai ta je ta ci abincinta ta kwanta, to shi ne fa bai iya farkawa ba sai yanzu, e gaskiya kam abin da abin mamaki sosai Wlh, akwai kuma ɗaure kai!. Kada ku manta daga cikin littafin RAWANIN ZALINCI wanda alkalamina ni PRINCESS TEEMA ya rubuta maku kuke karanta wannan daddaɗar labari mai cike da ruɗu da ɗaure kai, to yanzu muka fara, bamu ma fara kutsawa cikin labarin ba tukun nan, bamu ma yi komai ba, ku dai ku kasance dani, na tabbata In Sha Allah ba zaku taɓa yin danasanin karatan wannan littafin ba!. Har yanzu lokacin harshensa ta yi mashi nauyi wajen magana, da kyar ya iya furta. "Mamma ya naji kina cewa tun jiya nake barci sai yau na tashi? Kina nufin kwana ɗaya ta wuce kenan?". "E mana Kamran, kwana ɗaya ta wuce, wai me kasha jiya ne? Ka je ka sha ƴaƴan wata itaciyar mai bugar da mutun ko? Ina ta tashinka daga barci kaki ka tashi" . Zaro idanuwansa ya yi tare da furta what?! Da ɗan karfin, kwana ɗaya ta wuce kuma? Ya sake tambayar kansa. Ganin haka yasa Maman ta ce. "Kamran anya are you okey kuwa? Menene kuma ya faru?". Ɗago dara daran idanuwan nan nasa ya yi a in da ya sauke su a saman fuskarta, shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Mamma yau ba zan motsa jiki ba, ina zuwa, bari na je nan baya yanzun nan na dawo, sai na zo na yi wanka......." Wani irin kallo da ta wurga mashi da waɗan nan sexy eyes ɗin nata ne yasa bai san lokacin da ya haɗiye sauran maganar tasa bai ƙarisar ba. "Wuce muje ka fara aikin motsa jiki, idan ka gama ka yi wanka ka ci abinci sai ka tafi in da zaka je, dama zaka je kawo mana nama ai, babu abin da zai hanaka yin training, wai shin ni ina ma ka je jiya da ka dawo mun kamar a buge ne?". Da kyar ya iya miƙewa zaune yana turɓune fuska tare da ɓata rai. "Mamma ni ina kuma zanje da ya wuce in da muka saba ni da Rocky, wai Mamma please yau ki kyaleni da zancen motsa jikin nan mana". Shiru ta yi mashi bata sake ce mashi ko uppan ba. Yasan fassarar shirunta, hakan yana nufin dole sai ya motsa jikin nan ko yana so ko baya so, ga kuma ciwo a yatsarsa. Dole tasa ya miƙe jiki duk ciwo take mashi, gaɓɓansa duk suna yi mashi zafi, haka ya wuce gaba yana kara turɓu ne fuska. Rufa mashi baya ta yi, a saman tsaunin ta bayan kogon nasu suka tsaya, ga wasu manya da kananan duwatsu a wajen, a nan suka tsaya ya fara aikin training da waɗan nan duwatsu, ita kuma Mamma ta wani tsaya kamar jarumar sadaukiyar yaki, yacce kuka san wata commender masu bawa mayaka horo, haka ta wani tsaya tana aikin kirga sau nawa ya ɗaga wata katuwar dutse. Sai da ya ɗaga sau hamsin cif tana kirgawa, sannan ta ce ya fara press up, haka ya fara yi kamar zai yi kuka, yau duk jikinsa ciwo take yi mashi, ga shi Mamma ta zo tana kara mashi azaba a kan azaba, haka dai ba yadda ya iya, dole ne ya yi idan yana son zaman lafiya. Da Mamma ta lura fa baya yi da sauri zai ɓata mata lokaci, sai ta koma cikin ƙogon nasu. Tana tafiya ya yi zamansa yana tunanin maman twins, sai wani mai da numfashi yake yi da sauri da sauri, irin ya sha aiki ya ƙoshin nan. A hanzarce ya tashi ya cigaba da yi jin alamar takun dawowar Mamma wajen, ba shiri ya ɗaura daga in da ya tsaya. Kusa da shi ta zo ta tsugunna hannunta na rike da wata iriyar doguwar takobi na mayaƙa, sai dai takobin tana a cikin gidanta, bata fito da ita ba, da ƙotar gabaɗaya ta ɗauko. Ɗaga takobin ta yi ta fara kai mashi wajajen hannunsa, hakan yasa ya fara yi da sauri, dan idan ya bari takobin ta taɓa hannunsa zata ji mashi ciwo, dama ga ciwo a yatsar hannunsa tana yi mashi zogi, dan ma dai da diddigen tafin hannu ya dafa ƙasan ne, bai isa ya tsunsa sun taɓa kasa ba, saboda ciwon yatsar nan. Mamma ta wata fuska idan ka gani sai kaga kamar bata son ɗan nata, amma kuma ita ce ainahin mai sonsa da gaske, yanzu duk in da ya shiga zai iya kare kansa ba sai ya jira wani ya zo ya kare shi ba, sai dai ni PRINCESS TEEMA ina ganin akwai wani dalilin da yasa Mamma ta zaɓi Kamran ya zama jarumi sosai har take bashi irin horo haka mai haɗari, hannunsa yana ciwo ma ba zata kyale shi ba, sai ta sanya shi yin wannan abin, haba mana Mamma..........💔😭 Yau sai da ya kusa saka mata kuka, sannan ne ta rabu da shi tare da kama ƴatsar tasa dan ta cire wannan bandejin nasa ta kara yi mashi dressing na wajen. Shi dai burinsa ɗaya kawai, shi ne ta barshi ya je ya ga maman twins, ko yunwa ma baya ji, yana son ya koma ya sake ganin yaran ne, amma bai isa ya tirjewa Mamma ba, dole ya bita a yadda take so dan kada ta yi zargin yana aikata wani abin a ɓoye, dan haka sai ya hakura ta sake yi mashi dressing na wajen ciwon nasa, ta gasa wajen sosai da ruwan ɗumi, sannan ta ce ya je ya yi wanka ya zo su yi breakfast. Ba musu ya je ya aiwatar da duk abin da ta ce cikin zafin nama, dan ya yi sauri ya gama ya laƙa mum twins. Zama suka yi suka ci abincinsu kamar yadda suka saba, sannan Mamma ta ce mashi ya je gonarsu ya kawo masu masara ɗanya, ya duba ƙosassu ya ciro, sai ya haɗo masu da nama, daga karshe ta yi mashi kashedi a kan ya kula da yatsar nan tasa sosai, dan yatsar kamar tana son samun matsala. Okey kawai ya amsa mata da shi kafin ya miƙe ya koma cikin ɗakinsa, kwari da bakarsa masu lafiya ya ɗauko domin farautar nama, sai wata ƴar wuka mai kaifin gaske da ya ɗauka dan tsaro, a kugunsa ya sanya ƴar wukar, ita kuma kwari da bakar ya ratayota a bayansa, sannan ya sanya takalmarsa mai kama da waterproof shoe, a hanzarce yake yin komai, duk dan ya yi sauri ya fita. A wajen madafa ya isko Mamma, kwandon da suke ciro tomatoes a ciki ya ɗauka dan zubo mata masarar da ta ce ya ciro masu a gonarsu, sannan ya ɗauki wata karamar kwando ma wanda zai zubo masu fruits, dukka kwandunar da itace aka saƙasu, sai dai sun saƙu da kyau. Sallama ya yi wa Mamma tare da nufo kofar fita. Sosai ta sake yi mashi kashedi a kan kada ya yi wasa da hannun nan nasa fa, ya kula sosai. Okey ya amsa mata da shi tare da ficewa, yau ya fito sak maharbi. Wajen wata bishiyar lemu ya tsaya ya fara ciro lemun da suka nuna, yana cirowa cikin nutsuwa. Ɗan dai'dai ya ciro kafin ya je wajen bishiyar gwaiva, ita ma ba dayawa ya cire ba, sai mangoro da ita ma bata fi biyar ya tsinko ba, dukka nunannu yake bi yana cirowa, haka ya tara fruits ɗin dayawa, sannan ya nufi hanyar wajen mum twins dan ya je ya kai mata fruits ɗin, ita ya cirowa wannan, na Mammansa sai yana dawowa zai ciro mata, yaron kirki...........😅 Tafiya yake yi cike da jarumta, yana wani bubbuɗe kirji kamar wani mayunwacin zaki, ko alamar tsoron wannan daji babu a idanunsa, tsuntsaye sai shawagi suke yi abinsu, shi ma sai tafiya yake yi abinsa. Wani irin mahaukacin birki ya ja lokacin da ya isa wajen da mum twins ɗin take, sam bai san lokacin da ya saki kwandon fruits na hannunsa ta faɗi ƙasa ta tarwatse ba, fruits ɗin duk suka watse a wajen. Wani irin kara zaro idanuwansa waje ya yi, nan take fuskarsa ta bayyanar da alamar zallar madarar mamaki, cikin hanzari da zafin nama ya kara matsowa wajen dan ya tabbatar da gaske ne abin da yake gani. Tabbas gaskiya ce, babu mum twins kuma babu twins, ɗakin bukkar da aka yi masu ma duk an kakkarya shi, an karya itatuwar gabaɗaya, tamkar waɗan da suka yi faɗa da Damusa ko kuma Damusa ya faraucesu, duk komai a kakkarye, ga kwaryar magangunanta a wajen duk a farfashe, an fasasu, ga kuma towel ɗin da aka rufe baby's ɗin duk suna nan, babu abin da aka ɗauka a wajen face baby's ɗin da Mamansu. Tamkar a mafarki haka Kamran yake ganin wannan al'amari, tambayar kansa yake yi to ko Damusa ce ta shigo wannan yankin ta cinyesu? Kasancewar shi bai san da cewa biyo maman nasu aka yi daga masarauta za'a kwacewa mata baby's ba, sai bai yi tunanin ko mutanen masarautar tasu ne suka zo suka ɗauketa ba, shi dai tunaninsa wata dabbace a cikin wannan daji ta hallakasu ta kuma ɗaukesu suka tafi cikin dabbobi ƴan uwanta suka cinyesu. To waye ya ɗauki mum twins? Shin da gaske wata dabbace ta cinyesu ko kuma dai waɗan nan warriors na masarautar tasu ne suka dawo suka ɗauketa? Allah mai iko, Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana❤️ Wani irin bakin ɓacin rai ne ya bayyana a saman fuskar Kamran, tamkar ya saba da su, tamkar ƴan uwansa haka yake jin mum twins ɗin nan, kawai daga jiya da la'asar zuwa yau ace bata nan? Ina take?. Idanuwansa ne suka kaɗa suka yi ja sosai saboda tsananin ɓacin rai, har wani huci ya fara fitarwa. Cikin matsananciyar damuwa ya fara kewaye wajen yana nemansu, a cewarsa idan ma damusa ce ta faraucesu zai ga ragowar kasusuwansu, shi ne ya bazama ya fara nema, duk wasu lunguna da saƙuna, bayan bishiyoyi da bayan duwatsun, ƙoguna da ramukan itace dake arear wajen, ko'ina shiga yake yi yana leƙawa, nemansu a haukace kawai yake yi, duk yana kiɗi me, baya damuwa da in da yake shiga, ba ya damuwa ko akwai maciji ko wata muguwar dabba da zata cutar da shi, shi dai kutsa kai a ko'ina kawai yake yi yana nemansu, har cikin ramuƙan dake arear wajen irin ramin da ta faɗa ciki ta haifi twins ɗin, har ciki duk sai da ya bi ya rinƙa leƙawa, amma ko alamarsu babu a wannan arear, tamkar ma ba'a taɓa yin wasu halittu irinsu a wajen ba. To fa babbar magana, tashin hankali da ba'a saka mashi rana, my people ina mum twins?. *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 4/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ *My people's duk abin da kuka ga na rubuta a cikin wannan littafi na RAWANIN ZALINCI ba sai kun tambayeni a kan meyasa aka yi kaza ba, idan kuka nutsu za'a warware maku komai, ita labari ai ba lokaci guda ake warware komai ba, ku da kanku ba zaku so labarin da komai nata yake a wangale ba, duk abin da marubuciya zata rubuta maku a cikin storynta, ku sani tana sane da wannan abin da ta rubuta, kuma idan kuka yi hakuri zata zo da kanta ta warware maku komai a nutse ba sai kun yi ta tambaya ba, fatan kun gane?. And lastly littafin RAWANIN ZALINCI babu complete nasa, masu tambayata complete babu, yanzu nake rubuta shi!!* E____________7🔥 Sosai Kamran ya bazama ciki dajin nan yana nemansu, duk ya shiga damuwa bawan Allah. A takaice dai ya kwashe shekaru yana neman mum twins, kullum da su yake kwana yake kuma yashi a ransa, sun zo lokaci guda sun shiga mashi cikin tunaninsa da kuma rayuwarsa, lokaci guda kuma sun tafi sun bar shi, kamar ba'a taɓa yinsu a wannan daji ba, a cikin waɗan nan shekaru da suka suɗe babu wata rana da zata zo ta wuce Kamran bai yi tunaninsu ba, duk idan suka fita farautar nama shi da Rocky, to sai sun yi ta kewaye a cikin dajin ta arearsu ko Allah zai sa ya ga koda tsinke ne daga cikin kayansu ko wani abin nasu. Amma ina, bai ga komai ba sam, kuma tsabar ƙoƙari irin nasa bai taɓa cire tsammani tare da sa ran ganinsu ba, yana ji tamkar ko ba jima ko ba daɗe zai gansu, dan yana ji a jikinsa basu mutu ba suna raye, to Allah dai shi ne masa. And One think about KAMRAN and MAMMA, both of them are not Muslim, ba musulmai bane ba su ɗin, basu da addini dukkansu biyu, Mamma bata yarda da kowace addini ba a rayuwarta, a kan haka ta reni Kamran, sai dai Allah da ikonsa shi Kamran zuciyar musulunci ke gare shi, dan tsantsar son taimakawa na ƙasa da shi yake da, ga son ganin mutane cikin farinciki, wasu abubuwan nasa idan yana yi kamar cikakken musulmi. Kullum ya zauna sai ya bawa Mamma labarin mum twins, tun Mamma bata kula shi har kunnunwanta suka saba da jin labarin, sai dai bata taɓa bashi goyan baya a kan ya shiga sauram yankunar dake a cikin dajin ya dubasu ba, hasalima ɓacin ranta ne yake bayyana a duk lokacin da Kamran ɗin ya yi zancen wasu bama mum twins kawai ba, sam bata son jin yana magana na ko da maharba ne, amma ba yadda ta iya, mum twins ta riga da ta shiga cikin tunanin ɗan nata, ya rigada ya sanyasu a ransa, ko Mamma bata so dole dole sai ya bata labari, dan dole take saurara. Mum twins dai shiru, ba ita babu labarinta, babu wanda yasan in da ta yi tsawon shekaru, ko ina suke? Allah masani. To bari dai mu ɗan kutsa ta wani ɓangare na cikin wannan littafi na RAWANIN ZALINCI ko zamu sami wani ɗan haske a kan abubuwan da suka faru a baya, ko kuma dai har yanzu lokaci bai bamu dama ba, bari dai mu gani. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ KINGDOM OF POWER💪👊🔥 Masarauta ce da babu biyunta a tarihi, ku daga jin sunan POWER kun san me sunan yake nufi, kalmar POWER ta tattara karfi! Isa! Izza, taƙama dukka!. Masarauta ce mai cike da karfin da jin sunansu kawai ya kan sanya duk girman Daula ta girgiza, suna da horarrun jaruman sadaukai yaki sama da dubu uku, mayakansu mayaka ne da ba su sarewa a pagen yaki, matuƙar sun fara yaki, to fa komai wuya komai daɗi ba su juya baya har sai sun cimma abin da suka je nema, mayakansu ne ake yi wa lakabi da Dangerous warriors, wato mayaka masu haɗarin gaske, jin sunan mayaƙansu kawai ya kan sanya hantar manya manyan masarautu su kaɗa, basu da tausayi ko kaɗan, aiki ziryan suka iya. Commander ZAFAR shi ne commander na mayaƙansu bakiɗaya, dattijo ne wadda a kallah zai kai shekaru 50 zuwa 55 a duniya, amma da yake dakakken horarran mayaki ne, ya sha training ya ƙoshi, jikinsa duk ta murɗe sosai, idan ka gan shi, sai ka rantse da Allah ba zai wuce ɗan 35 years ba, saboda kyan jikinsa, ya murɗe sosai, damatsan hannun nan nasa tamkar za su fashe, yau sama da shekara 30 yana training tare da bawa mayaƙa horo da dabarun yaki, ai kunga dole jikinsa ya murɗe sosai. Commander ZAFAR yana da wani dakakken horarran jarumin yaro ɗaya tamkar da dubu mai suna HOORAIN, HOORAIN dakakken namiji ne, tsayyayye, kuma shi ne mataimakin mahaifin nasa, wato assistant commander na mayaƙan KINGDOM OF POWER a yanzu, matashi ne mai jini a jika, shekarunsa 28 a duniya, tun yana ɗan yaro Commander ZAFAR yake koyar da shi yaki, shiyasa ya taso a sadauki kuma cikakken jarumin namiji da KINGDOM OF POWER take alfahari da shi, bashi da mahaifiya, kuma bashi da kani or kanwa, shi kaɗai Commander ZAFAR ya haifa. KINGDOM OF POWER dai Shinfiɗaɗɗiyar masarauta ce wanda ta kasance na cikakkun jarumai da suka tsaya tsayin daka wajen ganin sun tsayar da masarautarsu ta yarda babu wani mahaluƙi a duniyar nan da ya isa ya nuna su da hannu, koda gate na farko na shiga wannan masarauta ka nuna da hannu, to wannan hannun naka sai ta tashi a aiki, dan sai an sareta daga diddiginta. A bakin gate na farko na shigowa cikin wannan katafaren Masarauta dai gumakan zakuna ne guda biyu waɗan da aka sassaƙasu, suna daga zaune sun buɗe baki ga waɗan nan gabza gabzan hakwaran nasu, an yi fentinsu da fenti launin gold color, daga bayan zakunan kuwa gunkin mutun mutumin wata jarumar macece wadda aka sassaƙata tana a zaune saman dokinta rike da takobi cikin shiga ta doguwar riga. A takaice KINGDOM OF POWER katafaren masarauta ne wanda yake da gate ɗin shiga ɗai, ɗai, ɗai har guda 5, girman masarautar ta wuci tunanin mai tunani, fadoji har guda uku ne a cikin wannan katafaren masarauta, ko wani fada ya haɗu haɗuwa ta wuce misali, ya kawatu da kayan kwalliya na alfatma irin na sarakuna, masarautu manya manyan guda goma ne a karkashin KINGDOM OF POWER, ga su da tarin uban dukiya na wuce misali tare da maadanan cikin ƙasa. Babbar fada wanda sarki ya fi yawan zama a cikinta, girmanta ya wuci misali, an zuba kayan iya kayan more rayuwa wadda suka amsa sunansu, komai na cikinta Golden color ne, hakan tasa suke wani irin kyalli tamkar gold, suna ɗaukar ido, akwai wasu kwalliya na jikin kujerar sarki waɗan da aka yi su ne da zallar madarar gold, shinfiɗun alfarma dake a tsakiyar fadar nan kuwa kawai abin kallo ne, bare azo kan irin kwalliyar da aka kawata gabaɗaya cikin fadar har izuwa jikin bangon, abin sai dai baki ya furta masha Allah kawai, su kansu luntsuma luntsumar sofa sets dake a cikin wannan fada kyansu ya sha gaban tunani, komai na cikin wannan fadan daga ƙasar Dubai yake. BARDE KING ZUHAIR ABDUL MALIK, shi ne sarkin KINGDOM OF POWER daya karɓi mulki daga hannun marigayi King ABDUL MALIK BADEEN, wato mahaifinsa kenan. KING ZUHAIR ABDUL MALIK jarumin ubane jajirtatcen sarki ne wanda ya tsaya tsayin daka akan ƴaƴansa da kuma al'ummar kasarsa bakiɗaya, yana da adalci fiye da tunanin mai tunani, shi ma kafin ya karɓi mulki wajen mahaifinsa, jarumin sadaukin yaƙi ne, ya taɓa zama commander warriors nasu a lokacin da babansa ABDUL MALIK BADEEN yake a kan karagar mulki, yana matashi lokacin, sai dai bai ruke muƙamin commander sosai ba, kasancewarsa ɗan sarki ne, dama kuma su ƴaƴan sarakuna suna karɓar horon yaki ne domin kawai su kare kansu ba dan su yi mu'amala da mayakan dake a cikin masarauta ba, sai dai idan suna ra'ayi, za su iya shiga yaki idan za'a je, wannan ra'ayin kansu ne, amma banda haka sunfi karfin wani mayaki ma ya kalli in da suke, to dai shi ma King ZUHAIR ABDUL MALIK jarumin sadaukin yaƙi ne, hakan kuma yasa ma ake ce mashi BARDEN namiji, domin kuwa BARDEN ne da gaske, ba wasa, jininsa a tafashe yake, bugu da ƙari KING ZUHAIR ABDUL MALIK bamodare ne, nasan dayawanku baku san su waye modarawa ba, modarawa larabawa ne wanda tun zamanin kakanni sun yi suna wajen jarumta da ba'a barin ko ta kwana, da ka taɓa bamodaren balarabe gwara maka ka kwana da yunwa, tun zamanin da can kowa yasan modarawa basu yafe laifi idan aka yi masu, komai ƙanƙantar laifi idan ka yi masu sai sun rama, ga zuciyar bala'i, jininsu a tafashe yake, ga su da shegen haɗin kan bala'i, idan ka taɓa bamodaren balarabe guda ɗaya wlh sai goma sun hayayyaƙo maka, to haka suke, jarumai ne da suka shiga kundin tarihin duniya. So haka BARDE KING yake, tsayayyen namiji ne mai cikar zarra da halitta. Ƴarsa ta farko shararriyar sadaukiyar yaki ce kafin ta yi aure, jaruma ce a cikin jarumai, ta iya takobi fiye da tunaninku, jininta a tafashe yake tamkar na mahaifinta, bata da wasa kuma bata ɗaukar wasa, har gunkin mutun mutuminta aka gina a bakin gate na farko na shigowa cikin KINGDOM OF POWER, an ginata tana a zaune saman dokinta rike da takobi, ta fi iya takobi sama da komai, tsayawa zayyana maku jaruntar gimbiya Miemie ma ɓata lokaci ne, dan baki ba zai iya faɗen shi ba, duk da ta yi aure, amma tana a cikin KINGDOM OF POWER da mijinta har yanzu, saboda ɗa ga abokin mahaifinta ta aura, wanda shi ma a cikin KINGDOM ɗin yake, jarumine na gaske, kuma su a al'adarsu ce hakan, su zauna inuwa ɗaya, wato family su haɗu su cure waje guda, har gobe Gimbiya Miemie tana wasa da tokobi tamkar mai wasa da ƴar baby, shekarunta 37 kacal a duniya, saboda auren da yake a kanta ne yasa ta dai'na duk wani abin da ya shafi yaki da sauransu, sai dai ta koyar da kananan yara mata masu tasowa ruke tokobi da kuma amfani da ita, wato ta bawa mata horan yaki, amma fa duk wani yaki da za'a tafi, sai mahaifinta ya nemi jin ta bakinta, dan ita ɗin mace ce mai kaifin fikira da basira tare da sanin dabarun yaki, to haka dukka ƴaƴansa suke, jarumai ne na kin karawa, a tsarin KINGDOM OF POWER basu tunkarar waje da yaki kuma su juya, basu ja da baya a yaki, idan fa suka dumfari waje, to komai girman Daular sai sun jijjigeta sun jefar da ita, idan suka ja wa masarauta kunne taki ji, to sai sun rugujeta sun

Chapter 8 of 75