كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________11🔥
🔥✨KINGDOM OF POWER💪👊
Zaune Gimbiya Zunaira take a saman wani haɗaɗen shinfiɗi na alfarma, tana zaune ne a wani irin waje da aka kawata shi da kyawawan kwalliya na gidan sarauta, da alama wajen hutawa ne, wajen hutawar ma da alama na wani babba daga cikin ƴan gidan ne, babba kuma wanda ake ji da shi, domin yanayin wajen sam bai yi kama da na ƙananan kwari ba, na manyan kai ne.
Tulin tuffa ne a cike a cikin gwando a gabanta, kuyanga ce ta kawo mata tuffar, yau dai Hoorain baya a tare da ita, da alama yana ta wani wajen, tana nan dai cikin wannan shiga tasu ta ƴaƴan manyan sarakuna da ake ji da su, shigar yana yi mata mugun kyau sosai, kowa dai yasan kayan yara ya fi na manya kyau, to haka idan ta sa kaya sai ya fi kyau a jikinta sama da su Gimbiya Chuchu.
Har wa yau dai bata sanya hular alkyabbar a kanta ba, sai dai a yau ta sanya wani kyakkyawar hula mai matukar kyan gaske a kan nata, ta rufe gashinta, ba kasafai ta cika yawan sanya ɗankwali ba, dayawan lokuta zaka ganta babu ɗankwali a kai, ta fi son shan iska ta ko'ina.
A nutse ta kai hannu ta ɗauki apple guda ɗaya daga cikin kwandon Apple dake a gabanta, ta kai saitin ɗan bakinta zata gutsira. Bata ji motsin mutun ba, bata ji komai ba sai gani ta yi an kwace apple ɗin daga hannunta, bata ƙarisa kai shi bakin taba.
Cikin sauri ta ɗago kanta tare da ɗago da idanunwanta sama, dan taga wanene da wannan ɗanyen aikin?.
Tsaye yake a gabanta, cikin kayansu na jarumai kuma jajirtattun mayaka, kamar kullum wannan hula tasu mai kan zaki tana a kansa, tsayuwar jaruman mazan nan nasa masu jini a jikan nan dai ita yake yi a kullum, kai daga ganinsa ma bakaga wajen wasa ba, baya ɗaukar wargi.
Zuba mashi ido ta yi bata ce da shi ko uppan ba, yau karo na farko da ta ji tana son kallon fuskar wannan dakaren nata.
Ɗan dukar da kansa ƙasa ya yi, cikin girmamawa ya ce.
"Afuwa ranki shi daɗe, ina neman izinin yin magana".
Yau ya yi maganar da ɗan sauti, sau da dama idan ya yi magana na kusa da shi ma basu jin me ya faɗa, saboda a hankali yake magana, baya fitar da sauti, baya ɗaga murya.
Gera ɗaya ta ɗaga mashi alamar go ahead ya yi maganarsa ba tare da ta yi magana ba.
Sake ɗan risinar da kansa ƙasa ya yi alamar ya karɓi umarnin kuma ya gode. Cikin natsuwa ya fara magana words ɗinsa na fita ɗaya bayan ɗaya babu hayaniya.
"Afuwa ranki shi daɗe, ban binciki tuffar bace shiyasa ban bari kin kaita bakin ki ba, Gimbiya Sarina ce ta aike ni, shiyasa ban samu damar bincikar tuffa ɗin ba har aka kawo maki".
Tun da ya fara magana ta zuba mashi wayan nan dara daran idanun nata, ta kasa koda kyaftawa, yau shine rana ta farko da ta fara jin muryarsa da sauti, idan yana magana kasa kasa sosai yake yi, kullum tana tare da shi, amma bata taɓa ganin ya yi magana da kowa ba, sannan bata taɓa ganin fuskarsa ba, sakamakon wannan hular tasu ta mayaka dake rufe musu ko'ina a fuskarsu, baka ganin komai sai ido da tsagen ɗan baki, sai kofofin hanci, suma kaɗan kaɗan ne, bayan haka baka samun damar ganin komai na fuskarsu, ga kayan yakin nasu kuma da karfe aka yi shi, kunsan dai yadda kayan shahrarrun mayaka suke ai?, Amma duk cikin dakarun dake Masarautar ya fi su natsuwa, yana da hankali sosai, yana bata kulawa, gabaɗaya masu kula da su shi yafi bata kariya yadda ya dace, ko motsi ta yi sai ya matso kusa da ita dan ya ga menene, tana da tabbacin ko barci dare baya samun dama ya yi sosai, saboda ita, baya taɓa rabuwa da bakin kofar shiga arear part na King Zuhair.
Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce mashi. "Ai babu komai a cikin Apple ɗin, daga ɓangaren Momma aka ɗauko mun fa, kuma Aunty Chuchu da kanta ita ta haɗa mun su a kwando, amma nagode da kulawarka a gareni".
Ita ma cikin nutsuwa take magana, da alama yarinya ce mai hankalin manya.
Jinjina mata kai ya yi tare da risinar da kai ya sake ɗagowa, sannan ya tsugunna a gaban kwandon Apple ɗin, dan ya duba ya tabbatar da ingancinsu, saboda ya tabbatar da aikinsa, ya tabbatar ya bata tsaro yadda ya dace.
Da ido kawai ta bishi da kallo, bata ce da shi komai ba, shi ma bai sake yin magana ba har ya kammala bincikensa a kansu, sannan ya miƙe tsaye tare da komawa ɗan gefenta kaɗan ya tsaya. Ƙasa ƙasa kamar dai kullum ya ce mata zata iya cin Apple ɗin yanzu, babu wata matsala.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da dawo da kallonta a kan gwadon Apple ɗin, a kullum idan zata ci abu in dai a waje ne ba'a cikin ɗakinsu ba, to sai Hoorain ya binciki wannan abin tsab, sai ya tabbatar da ingancin wannan abin, sannan yake barinta ta ci, hakan yasa take jin daɗin kasancewa a tare da shi, yana da kula sosai, ga shi babu ruwansa da kowa da komai, in da ya sa kansa kawai yake kallah, baya ɗaga kai ya kalli wasu ma abinsa, ga namijin jarumta da kuma nutsuwa.......... Ɗa ɗaya tilo ga commander ZAFAR kenan.💪
Baki a ɗauke da sallama wata kuyanga ta shigo cikin wajen, hannunta na rike da wani kyakkyawar kuma tsadadden Apple laptop, sabuwa gal da ita.
A gaban Gimbiya Zunaira ta zo ta tsugunna, cikin girmamawa ta nemi izinin yin magana.
Yadda kuka san mutun mutumi haka Hoorain yake tsaye, ko kallon in da suke bai yi ba, yana tsaye kamar saƙago yana fuskantar kofar shigowa abinsa.
"Mama Haulat menene yake tafe dake?". Cewar Gimbiya Zunaira ɗin.
Kuyangar ta kasance babbar macece, dan zata iya kai 35 to 40 years a duniya, hakan yasa Gimbiya Zunaira take girmamata take ce mata Mama, duk cikin ƴaƴan KING ZUHAIR babu wanda yake girmamata yake ce mata mama sai Zunaira, dama na gaya maku ita tana da saukin kai da kuma girmama na gaba da ita, sam bata ɗauki duniya da zafi ba, kuma ita wannan Mama Haulat ɗin ita ce kuyanga mafi matsayi a cikin kuyangun dake yi wa Momma wato mahaifiyar Zunaira ɗin hidima, so a part ɗin su Zunaira ɗin take.
"Dama ranki ya daɗe Gimbiya Momma ce ta ce na kawo maki wannan abin Yah Omar yana son ya yi magana dake".
Ta kai karshen maganar tana miƙo mata laptop ɗin.
Kyawawan hannayenta dukka biyu tasa ta karɓi laptop ɗin, sannan ta juyo da screen ɗinta a dai'dai saitin fuskarta.
Wani kyakkyawan matashi ne yake a zaune a saman ɗaya daga cikin wasu shegun luntsuma luntsumar sofas masu bala'in kyau, zaune yake a cikin wata katafaren parlourn mafi haɗuwa da ƙawatuwa, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kyawawan fararen halayensa ɗaya na rike da cup mai bala'in kyau, ɗayan hannun kuma yana rike da pen, sai tiriri ne yake tashi daga cikin cup ɗin, da alama abu mai zafi yake sha.
Kyakkyawa ne sosai, da ka gansa babu tambaya kasan yayan Zunairar ce, dan suna kama duk da ba sosai can can ba, fari tas da shi shi ma, gashin kansa baki siɗif, ga gashin nasa ya sauko mashi har gaban goshi, da alama kuma shi yake yanke baki bakin gashin yana dai'dai tasu, shiyasa suka yi mashi kamar wadda ya kifa hula a kan nasa, yana da dara daran idanuwa kamar na King Zuhair, farin idanun nasa ya yi tas da shi, kwayar idanun nasa kuma bai yi baki sosai ba, idan ka gansa ma zata zaci brown ne ba baki ba. A shekaru ba zai wuce 15 to 16 years ba, sanye yake da puma rigar da wandon dukka farare tas, bai sanya hular kayar a kansa ba.
"Yah Omar me kake yi ne?".
Ta faɗa tana kallon pen ɗin hannunsa, ta yi maganar kuma cikin Dubai Arabic nata.
"Koyar da gaisuwa nake yi".
Ya baya amsa calmly, kamar mai ciwon baki, voice nasa yana kama da nata, ance blood is thicker than water!.
"Kash na manta ne ina wuni tom?".
Ta yi maganar a shagwaɓe.
Cup dake hannunsa ya kai saitin bakinsa ya ɗan kurɓi abin da yake ciki kafin ya amsa mata gaisuwar tata, sannan ya ce mata. "Ina Akka?".
"Tana part nata".
Ta bashi amsa tana mai cigaba da kallonsa.
"Ai na ɗauka kina wajenta ne".
"A'a tun ɗazun na baro wajenta, amma zan je anjuma kaɗan, yawwa Yah Omar kada ka dawo fa ka jirani sai na zo mu taho a tare".
Shiru ya ɗan yi mata kafin ya ce. "Kin gayawa daddy aikar da na yi maki ne?".
"Laaaa wlh na manta, amma zan je na gaya mashi".
Guntun hararar wasa ya wurga mata kafin ya ce.
"Tun jiya fa na aikeki, Ina Omaid da Obaid?".
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Kila suna part ɗin Mommy, kasan yanzu basu cika zuwa part ɗin Mama ba ai".
Kasancewar yasan matsalar gidan nasu sai bai tambayeta dalilin da yasa su Obaid basu zuwa part na Mama ba, sai ma ya kawar da zancen da cewa.
"Yah Jawad ya tafi office ne?".
"Ni ban sani ba, rabona da shi tun da safe".
"Tom ki je ki gayawa daddy saƙona kin ji ko?".
"To amma Yah Omar gaskiya sai anjuma zan je, yanzu fada tana da baki sosai, dan na kalli motocin dayawa sun zo".
Ta yi maganar tana ɗago da kallonta izuwa kan Hoorain dake tsaye tamkar saƙago.
"Ba wasu baki, uncle Abbas ne ya zo wajen daddy, ai Momma ta gaya mun, dan haka ki je ki gayawa daddy abin da na ce".
Miƙewa ta yi tsaye, cikin murna tare da bayyanar ƙayatattcen murmushi a saman fuskarta ta ce.
"Yah Omar da gaske uncle Abbas ne ya zo?".
Jinjina mata kai ya yi alamar e.
"Wayyo daɗi, yau su Aunty Sarina zasu ga daddynsu, ni ma bari na je na gansa".
"Bafa ganinsa na ce ki je ki yi ba, ki je kawai ki gayawa daddy saƙona, idan kin faɗa in ya so sai ki tsaya a wajen uncle Abbas ɗin".
Da okey ta amsa mashi tare da miƙewa wannan kuyangar wato mama Haulat laptop ɗin, cikin hanzari ta nufi hanyar fita daga wajen.
Cikin zafin nama da taku irin na jaruman maza Hoorain ya rufa mata baya, sai murna take yi a kan zata je ta ga uncle Abbas wanda ya kasance kani ne ga mahaifinta, shi ne yake bin King Zuhair a wajen haihuwa, cikakken ɗan siyasa ne mai faɗa aji a faɗin ƙasar, yana da aure, matarsa ɗaya da ƴaƴansa huɗu, maza biyu mata biyu, familynsa suna cikin KINGDOM ɗin, shi ne dai ba mazauni ba, time to time yake zuwa, mutun ne mai kirki da son ƴan uwansa, yana matuƙar kaunar King Zuhair da ƴaƴansa, sai dai ita kuma matarsa tana so ne yazama shi ne sarki ba King Zuhair ba, shi kuma sarauta ba ita ce a gabansa ba, siyasa yake da ra'ayi, ita kuma a haukarta cewa take yi kujerar siyasa ba'a gadarta, idan ya gama wa'adin mulkinsa sauka zai yi wani ya hau, amma ta sarauta kuma fa? Ba zai sauka ba sai lokacin da ya tsufa, sannan kuma ɗansa ne zai gaji kujerar idan ya sauƙa, wannan shi ne dalilin dayasa tafi son ya mulki KINGDOM OF POWER ba wai siyasa ba. Akwai case fa my people.
A can cikin gida kuwa, labari ya gama shiga ko'ina cewa uncle Abbas ya zo, sai murna kowa yake yi, dan har ga Allah gabaɗaya ƴaƴan KING ZUHAIR suna matuƙar kaunar uncle ɗin nasu, kun san kowace zuciya tana son mai kyautata mata, to shi gaskiya mutun ne mai faram faram ga jan ƴaƴan nasa a jiki, hakan yasa idan ya kawo masu ziyara sai ka ɗauka wani hamshakin biki ake yi, su yi ta murna suna farinciki.
Sai shirin zuwa wajensa gabaɗaya ƴaƴan king Zuhair suke yi, Gimbiya Chuchu da ta fi kowa zaƙuwa ta gansa sai ƙoƙarin shiri take yi, yanzu ta fito daga wanka, ɗaure take da ɗankaramin towel da bai gana rufe mata cinyoyinta ba, tana rike da haɗaɗɗiyar wayarta kirar iphone 15 pro max, sai ɗaukar hoton face nata take yi.
A duniya Chuchu tana kaunar hoto, ko barci ta tashi sai ta ɗauki kanta a hoto, ita bata da wata matsala a rayuwarta, bata bi da kan kowa, gata da shegen son gayu, ga bala'in son jiki, kamar mage haka take, komai da kuka sani kuyankunta suke yi mata, wanka da saka kaya ne take yi da kanta, sai sallah da cin abinci, banda haka tsabar son jikinta bata son ɗaga koda tsinke, sai dai ta cancaɗa kwalliya ta haye saman bed abinta, gimbiya Chuchu ƴa ce ga Mummy, wato uwar gida kenan, kanwar Jaruma Gimbiya Raseesa ce, sai dai ita Chuchu bata da jarumtar, sai lalaci da son jiki, bata gado ƴaƴarta da mahaifinta king Zuhair ba, raguwa ce mayyar son jiki.
Sai kashewa kanta hoto take yi abinta, a ɓangaren Akka take, dan ta fi yawan zama a wajen, part na mamanta ma idan kun ganta a wajen to wani abin ta je ɗauka, kullum tana part na kakarta abinta. Hakan yasa kayayyakinta da sauran abubuwanta suka yawaita a part na kakar tata.
Sai da ta ɗauki hotunanta kala kala wajen kala goma, a haka ma wai tana sauri zata je wajen uncle Abbas ne, badan haka ba da dani da ku ba zamu iya kirga hoton da ƴar tahaliƙarnan zata ɗauka ba, dan mayyar hoto ce.
Wasu irin shegun tsadaddun lotions ta shafa a jikinta, tana shafawa tamkar bata son taɓa skin ɗin nata, saboda shegen son jiki, bata son wahala yarinyar nan sam, bata son abin da zai taɓa wannan kyakkyawar jikin nata.
Wasu tsala tsala kaya ta ɗauko, doguwar riga ce wadda ta sha kwalliya na wuce misali, kasancewar ba wata babba bace sai bata sa breaziya ba, dan bata wuce 14 years ba a yanzu, bata saka bra, haka take tsara kwalliyarta abinta, sai dai fa da yake akwai ta da halittar jiki mai kyau, idan ka kalleta sai ka yi tsammanin 16 years take da shi, tula tulanta suna cike fam da su, ga shape sosai tana da shi.
Tana ƙoƙarin zura rigar a jikinta bayan ta zuge zip ɗin kasa ne karfen bayan wuyar rigar ya maƙale mata a gashin kanta, da yake babu ɗankwali a kan nata, ta tara wannan gashin nasu na larabawar ta ɗaure a tsakiya, ta zuba jelar a bayanta, hakan yasa karfen rigar ta iya kama gashin nata.
Ƙoƙarin cirewa ta fara yi, amma ina ta kasa, ga rigar ta rufe mata fuska. Sunan Gimbiya Zunaira ta fara kira, dan tasan ita ce kawai za'a samu a part na Akkar by this time around.
Tana ta ƙoƙarin cire karfen tana kuma kiran sunan Zunaira. Shiru Auta bata amsa mata ba, bata ma san cewa auta kam tana fada a halin yanzu ba, tana can ta haye jikin uncle Abbas tana zuba shagwaɓa abinta.
Ƙoƙarin jan rigar ta yi ta cire shi daga saka shi da ta fara yi, a tunaninta idan ta cire rigar zata iya cire karfen daga gashin kanta.
Bata kai ga cire rigar ba ta ji an sanya hannu ana ƙoƙarin cire mata karfen da ya kama gashin nata, rigar ta rufe mata idanu, bata iya ganin wanene?.
"Auta tun ɗazun ina ta kiran sunanki sai yanzu zaki zo ba? Da na faɗi fa? Kina ganin sai da na fara zura rigar a jikina karfen ta saƙalomin gashina, rigar ta ki wucewa ta karisa shiga jikina, ta tsaya ni baga saka riga ba ba kuma ga iya cireta ba, idan nace zan tafi izuwa wajen Akka kuma faɗuwa zan yi".
Tana maganar ne ba tare da ta san wanene a wajen ba, a duk tunainta auta ce.
Cire mata karfen rigar ya yi tare da karisa saukar mata da rigar a jikinta, sannan ya sanya kyawawan hannayensa yana mai ja mata zip ɗin rigar sama kafin ya kama wannan ɗan karfen da ya saƙalo mata gashin kan nata ya haɗa shi da ɗan uwansa ya mannesu, dama kamar botir suke.
Da sauri ta juyo dan jin kamshin perfume nasa bai yi kama dana auta ba, bugu da kari kuma ba a amsa mata maganar da ta yi ba, da auta ce to tabbas zata amsa mata maganar tata.
Tana juyowa suka yi ido huɗu da Jawad, tsayayyen namiji mai jini a jika, matashi mai 25 years a duniya, ɗa ne ga uncle Abbas, shi ne second born nasa, kyakkyawa ne sosai, ba sai na sake gaya maku ba, gabaɗaya ƴaƴan Akka wato mahaifiyar king Zuhair, ƴaƴanta kyawawane, haka zalika ma jikokinta, cikakkun larabawane jinin Modarawa, hakan yasa suke da kyau sosai kamar su suka yi kansu, sai dai wannan yafi wannan kyau, wannan kuma ya fi wannan haske, haka suke!.
Ɗan kasa kaɗan ta yi da kanta tana ƴan kame kame, dan duk a tunaninta auta ce, da ta san shi ne ba zata yarda ya saka mata kayan ba, wani tunani ne ya faɗo mata cikin ranta, yanzu shikenan Yah Jawad ya kalleta daga ita sai towel? Waye ma yasan tun yaushe yake wajen? Kila tun da karfen ya riƙe mata gashi yake kalleta.
Shiru ya tsaya yana kallonta ba tare da ya yi magana ba, sai ma zura hannayensa da ya yi a cikin aljihun wandon suit dake a jikinsa, da alama daga office ya fito, dan shigar zuwa wajen aiki ne a jikinsa, white suit ce mai bala'in kyau, sai white cover shoe masu bala'in tsada a kafafunsa, daga ta ciki kuma safa ce baka, kyakkyawar bakin gashin kansan nan a kwance luf, ta gaba har gaban goshinsa, ta baya kuma har bayan wuyarsa, sai sheki gashin yake yi, ha sha gyara, ga wani daddaɗar kamshin da yake zubawa.
Daga Akka har marigayi King ABDUL MALIK duk suna da tsawo sosai, hakan yasa daga ƴaƴansu har jikokinsu suke da tsawo sosai, so haka shi ma Jawad yake da tsawo, ga cikar kirar karfi na lafiyayyun maza.
"Yah Jawad ina wuni?".
Ta faɗa murya na kerma, dan ita tsoronsa ma take ji, saboda bashi da wasa da yara, kuma bashi da yawan magana, haka zalika sam bashi da fara'a ko kaɗan, wannan dalilin yasa suke jin tsoronsa.
Nisawa ya yi ba tare da ya amsa mata gaisuwar tata ba, sai cewa ya ya yi.
"Meyasa baki rufe kofar ɗakin ba?". Kasa kasa ya yi maganar.
Cigaba da muzurai ta yi tana wani ƴan kame kame, sam bata san lokacin da ta fara murza ƴan yatsun hannunta ba, dan bata da abin yin da ya wuce haka.
"Am.... In... Dama na manta ne.... Kuma dama muna tare da auta ce, ta ce mun tana zuwa ne ta fita, shiyasa ban rufe kofar ba, dan ina tunanin zata dawo".
Yadda take magana muryarta na rawa, words ɗinta suna rarrabewa, hakan zai kara tabbatar maka da ba ƙaramin tsoronsa suke ji ba, dan fa da gaske ne bashi da wasa kuma baya ɗaukar wasa.
"Lafiyarki kam ko?". Ya tambaya yana mai cigaba da kallonta, ya ji ne sai famar in'ina take yi mashi a magana, sai ka ce ya ce zai zaneta ko wani abin, duk ta bi ta ruɗe mashi.
"Lafiya lou".
Ta bashi amsa still voice nata na kerma.
"Ina zaki je haka? And ina Akka? Dan na shiga ɗakinta bata nan?".
Sai a lokacin ta ɗan ɗago da dara daran idanuwanta a hankali dan ta saci kallonsa, jin bai yi mata tsawa ba, ya yi magana cikin sanyi murya, kuma bai ce ta yi laifi ba, sai hakan yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya.
Ajiyar zuciyar da ta sauke sai da yasa shi ya ɗan kara kwanto da kansa kaɗan yana kallon face nata, ya fita tsawo sosai, so a yadda ya tsaya a gabanta ɗin baya samun damar ganin face nata da kyau, sai dai tsakiyar kyakkyawar bakin gashinta yake kallo.
"Akka ni ban san in da ta yi ba, ɗazun dai na barta a cikin bedroom nata".
Ta bashi amsa tana lallaɓawa a hankali tana ɗago idanunta dan ta saci kallonsa, tana son ganin yanayin face nasa.
"Ke kuma nace ina zaki je haka?". Ya yi maganar yana ɗan ja baya daga kusa da ita, saboda ya sami damar ganin face nata da kyau.
"Part na Mammie zan je, uncle Abbas zan je gani".
Ta bashi amsa dai'dai lokacin da take ɗago idanu zata saci kallonsa. Kash bata san cewa kallon face nata shi ma yake yi ba, hakan yasa tana ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, karaf suka kalli juna cikin ido.
Da sauri ita ta yi ƙasa da nata idanun, shi kuma still dai yana kallonta bai cire idonsa ba, ga idanun nasa kamar na Akka, manya manya kamar ball.
"Bani wayarki". Ya faɗa tare da ciro hannunsa guda ɗaya daga cikin aljihun wandon nasa.
A hanzarce ta miƙo mashi wayar, dama tana rike da wayar idan baku manta ba.
A hankali ya dawo da kallonsa a kan wayar da ta miƙo mashi. Ganin yadda hannun nata yake kerma ne yasa ya mayar da kallonsa a saman fuskarta.
"Lafiya kike kuwa?". Da mamaki ɗauke a saman fuskarsa ya wurga mata wannan tambayar, dan yaga yadda hannun nata yake ta famar kerma.
"Lafiya lou nake wlh Yah Jawad".
Shiru bai sake magana ba, ya kai hannu ya karɓi wayar tata tare da juyawa cikin nutsuwa ya nufi waje da wayar.
Yana fita ta faɗa saman katafaren bed ɗin dake a ɗakin tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, hannunta dukka biyu tasa ta dafe kirjinta dake ta faman harba mata fat, fat, fat, saboda tsoro, sai ajiyar zuciya take saukewa, tamkar wadda ta sha gudu ta ƙoshi.
Ta ɗan jima a haka kafin ta furta. "Ko me kuma zaka yi da wayata Yah Jawad?".
Auta ce ta shigo cikin ɗakin bakinta a ɗauke da sallama. Da sauri ta kariso ciki tare da hayewa saman bed ɗin tana faɗin.
"Aunty Chuchu tashi kiji me daddy da uncle Abbas suka ce".
Miƙewa zaune ta yi tana faɗin. "Rabu dani auta, kada ma ki gaya mun abin da suka ce, dan yanzu ma zuciyata a kusa take, kina gaya mun wani abin na tsoro suma zan yi, yanzun nan Yah Jawad ya fita daga cikin ɗakin nan, ba jiya Aunty Sarina ta ce ya kwace mata waya ba? To nima yau ya kwace mun tawa, sai dai ni bai mun faɗa ba, ita kuma Aunty Sarina kin ji ta ce ya yi mata faɗa sosai a kan wayar".
Cikin halin nuna ko in kula Autar ta bata amsa da cewa.
"To shi Yah Jawad me zai yi da wayoyinku da ya kwace?".
"To ko zaki je ki tambayo mana shi ne me zai yi dasu?". Ta faɗa tana zuro kyawawan kafafunta kasan gadon, dan ta miƙe ta karisa shirinta na zuwa wajen uncle Abbas.
"Kai Aunty Chuchu rufa mun asiri, ni na isa in je in ce mashi me zai yi da wayarku ne? Dama dai uncle Taheer ne ko kuma su Yah Obaid".
"Saboda kin rai'na su Obaid ɗin ba?".
Ƴar murmushi ta yi kafin ta ce. "Yah Obaid fa Momma ta ce shekaru biyun da suka bani ma bai cika biyu dai'dai ba, shekara ɗaya ne da wata takwas suka bani, yanzu su basu cika 13 years ba ai, ni kuma na cika 11 years".
Cigaba da yin shirinta ta yi tana faɗin. "E lallai auta kin girma, wato ji kike yi kusan ɗaya kike da su ko? Wlh bari Omaid ya jiki, kin san halinsa da shegen son girma, ranar har da cewa ya yi wai ya girme ni".
Dariya sosai autar ta yi, Obaid and Omaid akwai shegen son girma kamar me, sai dai kuma kash sun yi rashin sa'a sune kanana, auta kawai suka fi shekaru a gidan, amma sai su dage su ce sun fi su Chuchu shekaru.
Ƙarisa shirinta tsab ta yi, sai ta fito a cikakkiyar jinin sarauta, ta ɗauko wani dankareran alkyabbarta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 75