dai ce kawai ta buɗe drawers ta kawo mashi magungunan.
Tana buɗe drawers ɗinsa na wajen bed ɗin ta ci karo da uban tulin hotuna sosai, kala kala, wanda yake a saman kawai ta kurawa idanu ne, hotonsa ne shi da twins Obaid and Omaid ƴan albarka jikokin hajiya Akka tamu......😅
Da yake su twin's ɗin suna da tsawo sosai sai yasa da kaɗan Omar ɗin ya fisu tsawo a hoton, sun yi matuƙar kyau sosai da sosai, a gidan kakansu King Badeen suka ɗauki hoton, dukkansu suna cikin arab alkyabba bakake, while daga ta ciki suna sanye da farar arab jallabiya, sun naɗa rawani irin na sarauta fari tas, Omaid yana rike da sandar sarauta mai matuƙar kyau mai kuma tambarin kan zaki, Obaid da Omar fuskokinsu ɗauke da cool murmushi, shi kuwa Omaid fuska a ɗaure sosai, dama idan baku manta ba shi bai cika dariya ba sai sun shirya mugunta sosai. One thing about this twin's da baku sani ba shi ne, su fa ba normal makaranta suke yi ba, tun suna yara they're very very stubborn, hakan yasa Ramish ya sanya su special swat academy, a tunaninsa idan suka shiga nan zasu nutsu in sun ci kwakwa, bai san cewa kuskure ya tabka ba, domin kuwa ƙaro rashin ji over tare da taurin zuciya da rashin imani suka yi, sun zama basu da tausayi, ga ɗan banza rashin ji! Mugunta kuwa ba'a magana kuma shaida ne, kun ganewa idanunku, da alama duk wasu kayan muguntar da suke amfani da shi daga school suke tahowa da shi, domin dai in ba daga school ba babu in da zasu samo shi. (Yah Ramish ne ya kaisu special swat academy, wato makarantar koyar irin aikinsa kenan, ya kai su ne dan ya samu su nutsu, amma kun dai ji yanzu ga shi mahaifiyar Yah Ramish ɗin wato maman Gimbiya Aneesa ita suke shiryawa mugunta da zasu yi mata idan zasu dawo Dubai😅 hmmm ba zan yi magana ba, amma wlh idan Ramish ya kamasu ko King Zuhair sai ya yi da gaske zai iya gane su, saboda irin ragargazar da Ramish ɗin zai yi masu😅 Allah dai ya kwacesu, mu dai ana yi muna shan Maltina ko my people's?.🥱)
Kasancewar tasan halin da yake a ciki ne yasa bata tsaya gulmar ganin hotunan ba, amma dai ta so duba hotunan ko zata kalli hoton Ramish ko dai na wani daga cikin ƴan gidan, amma haka ta hakura ta rufe drawer ta miƙe.
Kusa da shi ta dawo, a nutsu ta ce. "Guyson ban ga drugs ɗin naka ba".
Ciza lips ɗinsa ya yi da karfi, alamar azaban zafi yake ji, juyi ya yi ya sake kifawa a kan cikin nasa, idanuwansa a lumshe ya sanya ɗayan hannunsa yana laluɓar saman bed ɗin kamar mai neman wani abin.
Cike da tsoro tab a ranta ta ce. "Wani abin kake nema ne?".
Ƙasa ƙasa ya amsa mata da. "My phone".
Ɗan juye juye ta fara yi tana neman mashi phone ɗin, hannu ta kai ta kara janye duv ɗin nasa ƙasa. Can wajen kyawawan fararen ƙafafunsa ta hango haɗaɗiyar wayar tasa. Cikin hanzari ta ɗauko mashi, hannunta sai kerma yake yi.
Miƙa mashi ta yi tare da ce mashi "This is the phone".
In a low voice sosai ya ce. "Check my contacts, ki duba Yah Ramish or Yah Raj ki kira mun ɗaya daga ciki".
Wani irin muguwar faɗuwar gaba ta ji jin sunan Ramish, har wani irin haɗiyar wahalallen yawu ta yi, a duk lokacin da kunnuwanta suka ji sautin sunan Ramish har cikin ranta take jin kanta a matsayin gawa, ji take yi kamar shi ne ajalinta, ita da bata ma san wanene bane, amma a yadda ta kalli yanayin gidan da kuma yanayin yadda take tsintar maganarsa time to time a bakin su Radia yana mugun sakawa ta ji cewa in dai asirinta ya tonu to tabbas Ramish shi ne ajalinta!.
Tana shiga contacts ɗinsa da sunan My baby (Gimbiya Zunaira) kenan ta fara cin karo, ƙasan numberta kuwa number Dr Raj ne da ya yi saving da Yah Raj. Dialling na number ta yi, gabanta sai dukan uku uku yake yi. Ringing wayar ta fara yi har ta kusa katsewa, sannan ne aka yi picking call ɗin.
A hanzarce ta miƙa mashi wayar. Sam ya kasa iya kai hannunsa ya karɓa. Ganin hakan yasa ta matso mashi da wayar a kusa da ɗan bakinsa tare da sanya wayar a speaker.
Daga ɗayan ɓangaren wani irin cool voice ya fara magana da. "Assalamu alaikum Guyson".
Sautin kukansa ya kara tare da cewa. "Yah Raj come and help me........ My". Sai kuma ya yi shiru yana goggoga kansa a jikin pillown da ya kwantar da kansa.
Sosai Leesharh ta tsorata lokacin da Dr Raj ya yi magana a karo na biyu. "Omar where are you?!".
Ya yi maganar ne cikin ɗaga murya, hakan ne ya tsoratata, tamkar bashi ne ya yi magana cikin sanyin murya da farko ba.
"Yah Raj am in my room". Da kyar ya furta hakan.
Diff aka kashe kiran ba tare da an sake yin magana ba. Ajiye mashi wayar tasa ta yi a kusa da shi, a hankali ta lallaɓa ta nufi kofar fita daga cikin room ɗin.
Tana sanya kai zata fita suka yi karo da mutu, baya baya ta yi ta faɗi ƙasa. Shi kuwa shigowa ciki ya yi bai bi ta kanta ba, da alama ma bai san ya buge mutun ba, dan hankalinsa kacukam yana a saman bed ɗin guyson, tun da ya shigo waɗan nan eyes ɗin nasa irin na King Zuhair suna a saman bed ɗin kawai, sanye yake da wando three cuter milk color, sai t-shirt sky blue mai haske sosai, ƴaƴa King sun gado tsawo kam, dogaye da su, so shi ma Dr Raj yana da tsawo sosai, ga cikar halittar sai ka rantse da Allah renon commander ZAFAR ne shi ɗin, tsayayye ne sosai mai ji da lafiya, kyakkyawar gaske ne sosai, duk dai Akka suka ɗauko. Da alama yau bai je hospital ba, domin kayan shan iska ce ma a jikinsa, arab hairnsa ba dai kyau ba kam, ya sha gyara sai kyalli yake yi.
Bin shi da kallo Leesharh ta yi gabanta na dukan uku uku, tunani take yi kenan dama suna cikin gidan? Amma kuma shi ne ba'a taɓa ganinsu? To a ina suke zama kenan? Ita a tunaninta ai basa nan ne yasa ba'a ganinsu, bata san dukkansu wani lokaci ma a gidan suke wuni basa fita ba, kawai ganin nasu ne sai wane da wane, daga Abu Abdussalam sai Ummie, ita ma Ummie ba kullum ba, gara ma Sharifat tana zuwa ɓangarensu jefi jefi, musamman ma wajen Rizwan suna shiri da shi sosai, so tana yawan zuwa room ɗinsa, ita bata jimawa sosai bata gansu ba.
Kai tsaye wajen bed ɗin ya nufa. Yana zuwa ya janye duv ɗin da guyson yake lulluɓe, gabaɗaya ya cire duv ɗin. Hannu yasa ya tallabo kan Guyson ɗin.
Ƙanƙame shi guyson ɗin ya yi, hawaye suna bin kyakkyawar kumatunsa. "Omar did you take your drugs?". Ya tambaye shi cikin sanyin murya, yana magana yana goge mashi hawayen nasa da kyawawan fararen tafukan hannunsa.
Girgiza mashi kai ya yi, cikin raɗaɗin ciwo ya ce. "No Yah Raj".
"Why?". Ya jefa mashi tambayar tare da miƙewa tsaye ya saɓe shi a saman shoulder ɗinsa, ya wani saɓesa kamar baby, kamar ba shi ne mai kanne har uku ba, wato da twin's da auta Zunaira, dukka fa kannensa ne, amma da alama duk sun fi shi jarumta, dan dai shi kam ga shi yana ruwan hawaye abinsa, abin da kunsa Obaid and Omaid kam ba zasu aikata hakan ba, waɗan nan yara ma ai sai addu'a, dan abin da zai saka su yi kuka ba ƙaramin abu bane gaskiya............😅
Leesharh tana zube a kasa ta kasa motsawa daga in da ta faɗi ɗin har Dr Raj ya fice waje da guyson a saman shoulder ɗinsa, sai binsu da kallo take yi, sun yi matuƙar burgeta over, sai ta ji tana sha'awar da ace tana da ɗan uwa ita ma. Nan take kuma mood nata ya sauya, jiki ba kwari ta miƙe ta dawo cikin room ɗin ta fara aikin gyaranta kamar yadda ta saba, tana yi tunanin yadda ta kalli Dr Raj wanda yake a matsayin kanin Ramish, abubuwa da dama a tattare da shi sun rikitata, tunani take yi to shi kuma Ramish ya zai kasance kenan? Ace Dr Raj kaninsa ne haka ga shi kyakkyawa, to shi ya zan kasance kenan? Tunanuka sosai ne a cikin kanta har ta kammala aikinta ta fito ta nufi wajensu Radia.
Yau gabaɗaya sukuku ta wuni, sai tunanin ya jikin Omar take yi, idan ta rufe idanu sai ta rinƙa kallon fuskarsa a yayin da yake ruwan hawaye, tausayinsa ne sosai a ranta, da shi ta wuni, tsabar ƙoƙari irin tata har da yi mashi addu'a da ta yi sallah, ta yi mashi fatan Allah ya bashi lafiya.
Da daddare misalin karfe 9 na dare, ta fito daga room ɗinta ta nufi kitchen, dan ta ɗan sha wani abin, yunwa take ji, sam ta kasa iya cin abincin dare ne, saboda tunani da ya taru ya yi mata yawa, na farko tana tunanin in dai Dr Raj haka yake to ya Ramish kuma yake? Na biyu kuma tunani a kan me yake damun Omar? Yanayin yadda yake cikin ciwo ya tsaya mata a rai, waɗan nan tunane tunane ne suka hanata cin abinci, so shi kuwa yunwa ai bai da sabo, ta fara jin ana yaki a cikinta, haka yasa ta yi maza ta fito nemanwa kanta mafita.
Elevator ta hau zuwa ƙasa, ta sanya ɗan hijabinta a kanta, riga da wando na barci ne a jikinta, farare tas masu laushi sosai.
Kai tsaye kitchen ta nufa, tana tafiya tamkar wadda kwai ya fashewa a cikin ciki, kamar wadda aka zarewa laka. Ko da ta shiga cikin kitchen ɗin pina colada kawai ta ɗauko daga cikin fridge, sannan ta ɗauki glass cup guda ɗaya ta fito. Sama ta koma, kamar zata wuce part ɗinsu, sai kuma ta ce bari ta leƙa living room ta gani ko Sharifat tana ciki su ɗan gaisa, yau throughout basu haɗu ba.
A hankali ta nufi parlourn, da alama ma a tsorace take. Ƙasa ƙasa ta yi sallama. Shiru ba'a amsa ba, parlourn tsit, da alama babu kowa, sai daddaɗar kamshin da yake tashi ga sanyin Ac. Shigowa ciki kaɗan ta yi, ganin babu kowa yasa ta juya da nufin ta koma, kamar daga sama ta ji ance. "Hey come here".
Da sauri ta juyo da kallonta izuwa in da ta ji sautin muryar, tun bata juyo ba tasan wanene, saboda duk da yana cikin ciwo ya yi mata magana a ɗazun to ta rike voice ɗin nasa.
Zaune yake a saman ɗaya daga cikin wasu haɗaɗɗun sofa set kanana marasa girma da suke ta can gefe guda, sai ka yi zaton ma ba'a parlourn suke ba, saboda girman parlourn kuma su suna ta can gefe ne, set ɗin suna da kyau, kanana haka aka yi su gwanin birgewa, ga decoration na flowers masu kyau da ɗaukar hankali da aka ƙawata wajen da su.
Zaune yake, daga shi sai wata ƴar riga mai karamar hannu ƴar shara shara fara tas da ita, daga kasa wando ce three cuter ita ma fara tas, kafafunsa suna cikin wasu kyawawan slippers sky blue masu laushi sosai, arab hairn nan nasa dai tana nan kamar wadda aka kifawa hula, bakinkirin da shi har gaban goshinsa, sai kyalle yake yi. Ƴar ƙaramar haɗaɗɗiyar cup ce mai ɗauke da capacino a hannunsa, a hankali yake sha ga laptop a gabansa yana yin video call da auta, a duniyarsa bayan iyayensa babu wanda yake so biyun gimbiya Zunaira, sai Sharifat kawarsa ɗaya tilo........😅
Ita ma auta kun san tana son shi sosai ai.
Gabansa Leesharh ta ƙariso tare da yunƙurawa zata tsugunna, da hannu ya nuna mata saman sofa dake fuskantar tasa a kan ta zauna ba tare da ya yi magana ba. Ba musu ta zauna a in da ya nuna mata, domin Fadila ta gaya mata cewa su ƴan gidan nan basa son ayi masu musu, komai suka ce kawai ace masu to, idan ka yi masu musu yanzun nan zasu hau su fara faɗa kamar wasu mayunwatan zakuna dake jiran a taɓosu dama, amma idan baka yi masu musu ba lafiya lou zaku zauna.
Daga cikin laptop ɗin auta ta ce mashi. "Yah Omar kai da waye kuma a daren nan? Ko dai Aunty Sharif ce?".
Girgiza mata kai ya yi tare da juya mata laptop ɗin izuwa saman fuskar Leesharh. "I don't know her kawai she is the one who helped me in the morning, that's why I called her now domin in tambayeta ya sunanta".
Sai satar kallonsa Leesharh take yi, kamar shi ya yi kansa, yana da kyau sosai, sai ma idan yana magana, lips ɗinsa suna da kyau sosai, ga yadda gashin gerarsa suka zauna sosai a face nasa, bakinkirin da su a kan farar fata kamar madara.
Ɗan zaro idanu auta ta yi tana kallon Leesharh ɗin, kwance take a saman gadon mommanta, da alama mommar bata nan. "Sannunki". Auta ta faɗa tana sakar mata murmushi, har ta ji tana son Leesharh ɗin tun da ta taimaki yayanta, kun san halin auta dama da son mutane, ita bata da walaƙanci ko kaɗan.
Juyo da laptop ɗin ya yi ta saitinsa yana tambayar Leesharh menene sunanta kuma wacece ita?. Sake maimaita mashi wacece ita ta yi kamar yadda ta gaya mashi ɗazun da yake a halin ciwo.
Guntun murmushi ya sakar mata kafin ya ce mata shi kuma sunansa Omar kuma ya gode da taimakon da ta yi mashi ɗazun, ta gaya mashi me take son ya bata a matsayin gift na taimakon da ta yi mashi.
Girgiza mashi kai ta yi tare da ce mashi ita bata son komai, dan Allah ta yi. Kara ɗan sakin murmushi kaɗan ya yi kafin ya miƙa mata cup ɗin da yake a hannunsa. "To karɓi wannan ki sha, good night zaki iya tafiya".
Bata yi mashi musu ba, dan tasan dokansu, dan haka sai ta karɓi cup ɗin ta miƙe tare da yi mashi godiya ta nufi hanyar fita. Cigaba da yin hiransa da auta ya yi suna ta sakin murmushi, duk auta ta ƙosa ya dawo, Abu Abdussalam kuma ya hana shi komawa, sai fakewa da ciwonsa Abu Abdussalam ɗin yake yi yana kara rike shi, baya son rabuwa da shi ne, shi ma kuma King Zuhair yaki hakura ya bar mashi guyson ɗin, dan bayan auta ba wanda yafi so biyun Omar, yana kaunarsa, amma ya zai yi? Dole ya hakura ya cigaba da lallaɓa yayan nasa har ya yarda ya barshi ya dawo, shi kuma King Zuhair ɗin yaki barinsu twin's su dawo, ga shi yanzu an buɗe school nasu this week, so ya zama dole su dawo, shiyasa King Zuhair duk ya bi ya damu sosai, Abu Abdussalam kuma yaki kula shi.
Har Leesharh ta kai tsakiyar parlourn sai kuma ta juyo, cike da tsoro ta ce. "Yah Omar me yake damunka ne?".
Kansa na'a duke kan laptop ɗin ya ɗago da dara daran idanun nan nasa. "Ciwon ciki nake fama da shi since ina da two years a duniya, amma ina taking drugs yanzu da sauki, and Yah Raj yana treating ɗina very very well". Ya bata amsa fuska ba yabo ba fallasa.
Addu'a sosai ta yi mashi na Allah ya bashi lafiya, sannan ta wuce zuciyarta a cike tab da tunani, Allah sarki ciwon ciki tun yana ƙarami, Allah yasa dai ba da shi ma aka haifesa ba, ashe dole ya yi kuka, ciwon ciki waje ƴa mace ma mugun muni garesa bare kuma namiji, ciwon cikin ɗa namiji ai babban haɗari ne ba kaɗan ba, suna shan bakar azaba sosai, wani ma nan take yake kashe shi, amma Alhdulillah shi Omar nasa tana jimawa bata tashi ba, sai ya kai wata shidda bai ji ciwon ba, sai dai idan ta tashin mashi kuma kamar ba zai rayu ba, Dr Raj ne likitansa, shi yake kula da shi sosai da sosai, shiyasa basu yarda su yi nisa da shi sosai, dan a kowani lokaci ciwon tana tashi, shiyasa suke lallaɓa shi suna kula da shi sosai, komai yake so suna yi mashi ba ɓata lokaci, shi kuma yana da kirki sosai, kusan halinsa ɗaya da Zunaira, sai dai shi baya taɓa yarda ace mashi bai iya abu ba, idan kana son ka yi faɗa da shi to ka ce ka fishi iya abu, yanzu zaku ɓata, shi dai gani yake jarumi ne shi ya iya komai ato.
Sosai ya ji matuƙar daɗin addu'oin da ta zuba mashi, harta auta da ta kasan kunne tana sauraronsu ta ji daɗin addu'ar, sai ta ji ta kara son Leesharh ɗin sosai, ita dai tana kaunar mai son ƴan uwanta.
Tas Leesharh ta shanye cappucinon da ya bata, sai ta ajiye nata pina colada da ta ɗauko, ta ji nasa yana da wani irin shegen daɗi sosai, kamar a kara mata ta ji, sai tunani take yi ko waye ya haɗa mashi wannan gaɗaɗɗen haɗin haka? Bata san shi guyson in dai ba Ummie ce ta girma mashi abu ba to ba zai ci ba, sannan shi abincinsa ba kamar na sauran ƴan gidan yake ba, dan shi yana kan tsarin magani, so abincinsa ya banbanta da nasu, Ummie da kanta take haɗa mashi komai da zai buƙata.
Sai tanɗe baki take yi, da haka ta kwanta zuciyarta cike da tunanin kirki irin na Guyson, ga shi fuskarsa ba yabo ba fallasa, ga shi kuma ya iya murmushi mai kara mashi kyau sosai, ta wani ɓangaren kuma idan ta tuna yadda taga Dr Raj sai ta ji gabanta ya yi wani irin bugawa, tsoro ya kamata, da haka dai barci ɓarawo ya saceta.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
KINGDOM OF POWER 💪🔥
Mammien Yah Jawad.
Zaune take a saman wani irin shinfiɗa ta alfarma irin na gidan sarauta mai kwalliya da gashin jimmina, shinfiɗar ta haɗu sosai da sosai, tana cikin alkyabbarta, ta zuba gwala-gwalai ɗin nan a hannu da wuya dam kamar ba za'a mutu ba, daga samanta har kasa dukiya ne aka narka. A in da take zaunen nan cikin minti ɗaya idan ta buƙaci kuɗi sama da 100 million a take za'a bata, kada ku manta Rizwan ɗan farinta ne, ga Yah Jawad shima yana da nasa company's ɗin, uncle Abbas ba'a magana, kuɗi ta ko'ina, amma ita fa duk basu a cikin plan ɗinta, sai ka rasa me take nema a duniyar nan to.
Ta ɗaura kafa ɗaya biya ɗaya, ta baza alkyabbar nan tata a wajen gabaɗaya, ta wani dake sai ɗage hanci sama take yi, tana zaune ne a wajen shan iskan uncle Abbas da yake a cikin part ɗinsu, uncle Abbas ɗin kuma baya nan, ga wasu ƴan matan kuyangu biyu a kusa da ita, ɗaya tana zaune ta gefenta na dama, ɗayar kuma tana zaune a gefenta na hagu, ga wasu uban tulin kayan marmari dake a cikin wani kyakkywar kwando da suka jibgemata a gabanta, very fresh kayan marmari ne, sai wani fadanci take yi kamar ita ce Queen of the Kingdom ɗin na ainahi, ko mummyn Gimbiya Chuchu uwar gidan King Zuhair bata irin wannan fadanci sai ita.
A hankali iskar bishiyoyin dake wajen suke kaɗata, ga kuyanga ɗaya tana yi mata fifita da maficin gashin jimina, an kawata in da take zaune ɗin da luntsuma luntsumar throw pillows masu girma.
Wata Kuyanga ce ta shigo cikin wajen, sai sauri take zubawa kamar zata kife kasa, da alama an ɗebo gulma fal ciki, shiyasa ake sauri kada ciki ya fashe gulmar ta zube a hanya.
A gaban wannan shunfuɗa ta zo ta zube gwiwowinta tare da fara zuba kirari na girma ga Mammie ɗin. Kara dakewa ta yi cikin alkyabbar nan tata. Sai da ta ɗauki a kallah minti biyar tana sauraran wannan kirarin kafin ta ɗagawa kuyangar hannu alamar ya isa haka ta dakata, sannan cikin nuna isa ta yi wa kuyangun dake wajen nata umarni da su bata waje zata yi magana da wannan kuyanga da ta shigo a yanzu.
Cikin hanzari suka miƙe suka fice daga wajen. Akwai sadaukan yaki biyu dake gadin kofar shigowa wajen shan iskan, dan tsaro.
Ko da suka fita sai da ta sake ɗaukar good two mins kafin ta ce. "Bintu meyafaru kika shigo da sauri haka?".
Ƙasa ta ɗan yi da kai kafin ta ce. "Allah ya kara maki tsawon rai, farar mace mai farar zuciya, Allah ya ja da ranki wlh yanzu ne ma Yah Jawad yake ƙara kula Gimbiya Chuchu sosai, daga majiya mai karfi na jiyo cewa har yanzu bai dai'na kulata kamar yadda kika hana shi ba, yanzu ma sai abin da ya cigaba sosai". Cikin girmamawa ta yi maganar.
Shiru Mammie ta ɗan yi kafin ta ce. "Shikenan je ki ki cigaba da yin aikinki, ki saka ido sosai, sannan kada ki kuskura ki kawo mun maganar da ba haka ba, ki tabbatar da ingancin magana kafin ki kawo mun".
"In Sha Allah ranki shi dade, Allah yaka maki girma da ɗaukaka". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye ta nufi waje.
Da kallo Mammie ta bita har ta fita, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Bintu tana fita sai ga kuyangu biyun can sun dawo ciki. Wajen zamansu suka koma suka zauna, suna zama wayarta dake saman throw pillow dake kusa da hannunta ne ta fara ruri alamar shigowar kira.
A hanzarce ɗayar kuyangar dake ta wannan bangaren ta yi sauri ta ɗauko wayar ta miƙa mata. Sai da ta sha kamshi kafin ta karɓi wayar.
My son, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar, ajiyar zuciya ta sake saukewa kafin ta ɗauki kiran.
Sallama ta yi cikakke. Daga ɗayan ɓangaren Rizwan ya amsa mata cikin girmamawa tare da ɗaga mata gaisuwa.
"Lafiya lou Alhdulillah my son, ya aiki?".
Da Alhdulillah ya amsa mata kafin shi ma ya jefa mata tambayar ya gida ya kowa da kowa.
"Kowa yana nan lafiya, amma ka tambayeni kowa baka tambayeni ya matarka ba?".
Cikin nuna halin ko in kula ya ce. "Wacece kuma matata?".
"Wai kai Rizwan kullum sai ma na tuna maka wacece matar taka ko? Ya yi maka kyau, ka cigaba da yi mun kamar ni kakarka ce".
"Kai Mammie bafa haka bane, duk lokacin da zaki gaya mun wacece hankalina yana kan wani abin ne, but yanzu gaya mun zan rike ba zan manta ba".
Shiru ta ɗan yi kafin ta amasa masa. "Jannat mana ko in ce Chuchu tun da da shi kuka fi saninta, tana ta kara girma, yakamata fa ka kawo mana ziyara, ni kam yanzu fa kun kai almost 12 to 14 years haka rabonku da masarautar nan fa ko? To yakamata ku zo gaskiya, matarta ta girma kuzo ku yi aure sai ku koma".
Chuchu kuma?! Tashin hankali to me Mammie take nufi? ta dai san Yah Jawad yana son Chuchu, kenan dama da gangan take hana shi kulata dan Rizwan take sonwa? To amma menene banbancin Rizwan ɗin da Jawad ɗin da zata hana kanin ta yi wa yayansa sha'awarta? Akwai matsala babban kuwa in dai haka ne, domin kuwa in dai tasa Rizwan ya fara son Chuchu shi kuma Jawad fa? Wai ni kam me Mammie take so ne a duniyar nan? Ita sam bata son zaman lafiya! Ba'a taɓa gane ina ta dosa sam sam! Mata kamar wata aljana ko shaiɗaniya! Sai iya haɗa makirci da faɗa! So take ta kashe Jawad ne ko me? Bawan Allah shekara kusan 11 yana dakon soyayyar Chuchu? Anya wannan abin ba zata tarwatsa mashi zuciya ba? Yayansa uwa ɗaya uba ɗaya, tashin hankali akwai rikici kam ba kaɗan ba, Mammie da alama zata kashe ɗanta da hannunta, ko me dalilinta na yin hakan kuma? Mu dai je zuwa, sannu a hankali komai zai warware. Hmmm ga shi shi kuma Jawad bai sani ba, yana ta wahalar da Chuchu har yasa ta fara tsanarsa, akwai rikita rikita ba kaɗan ba kuwa a nan gaba! Da alama nan gaba kaɗan kingdom of power zata kama da wutar bala'i, kai tabɗijam!!!.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Kai Mammie yanzu waye yake da lokacin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 54 Chapter of 75