Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a wani yaki da suke zuwa ba, gara commander ya taɓa jin ciwon da sai da ya kwanta jinya, saboda jikin tsufa ya sha wahala sosai, shi kuwa Hoorain sabon jini ne, jininsa a tafashe yake, lafiya lou yake jan ragamar rundunar sadaukan yaki sama da dubu biyar ya jagorancesu su je yaki su dawo, basu taɓa fita yaki basu yi nasara ba, duk girman daula in dai Hoorain da Commander suka jagoranci rundunar mayakan to fa sai sun jijjige wannan daula sun jefar da ita, basu gudu kuma basu ja da baya a fagen yaki komai tsanani kuwa. Idan ka kalli Hoorain ta wata fuska zaka gansa so silent haka, baya da magana kuma baya son hayaniya, amma fa da zaka same shi cikin abokansa mayaƙa ƴan uwansa, yana hira da su sosai, idan ka kalle shi ta fuskar assistant commander kuwa ba zaka so ka sake yin ido huɗu da shi ba, domin kuwa ganinsa a wannan siffar fa bata da kyau, wasu suka ce tamkar ganin mutuwa ne ganin Hoorain a siffar assistant commander, gara ku haɗu da shi a Hoorain ɗinsa a kan ku haɗu da shi a assistant commander. So a kullum a tseren gasar dawakai ma shi yake zuwa na ɗaya, kunsan ita fa doki tana gudu ne kusan dai'dai da bugawar zuciyar wanda yake a kanta, iya karfin da ka sanya mata iya gudun da zata yi kenan, iya yadda zuciyarka take harbawa domin muradin cin nasara, iya power da zata baka kenan, so shi Hoorain yana da zafin zuciya sosai, bugu da kari akwai karfin dantse kamar dokin, idan ya hau kanta yana bata wuta sosai da sosai ta yadda idan ya zo na ɗaya ma ratar dake tsakaninsa da wanda zai zo na biyu ba ƙaramar rata bace, yana kere masu sosai, ko kamshinsa basa jiyowa a gasar. Shi fa har wani wasa yake yi da dokinsa a hanya ma idan ya kusa iso wa, har wani irin karkatawa yake yi kamar zai faɗo kasa, amma har ya dawo cikin kingdom ɗin babu mai iya cin masa bare ma ya wucesa. Sosai Gimbiya Zunaira da kuma Gimbiya Chuchu suke jin daɗin kallon wannan gasa, saboda Zunaira ma yasa King ya kara karfafa wannan gasa ta zama kamar al'ada a masarautar, wajen da ake yin wannan gasa a cikin masarautar take, amma ba ta bangaren fada ba, ta baya ne, an ƙawata wajen sosai, babban fili ne sosai da sosai, tsawon wajen gasar har ta fita daga cikin kingdom ɗin, basa iya ganin karshen filin daga in da suke, kafin a fara gasar dama already za'a ɗaurewa wata lafiyayyar bujumar doki wani jan kyalle mai ɗauke da tambarin kingdom of power wadda kowa yasan tambarinsu shi ne kan zaki, so za'a ɗaurawa wannan lafiyayyar dokin wannan kyalle, sannan a saketa kamar da minti 20 haka, sannan su Hoorain su bi bayanta da nasu dawakan, wanda ya riga kama wannan dokin ya ciro wannan jan kyalle ya kuma ɗaure dokin dan kada ta yi wani wajen, sannan ya dawo da kyallen wajen King shi ne ya yi nasara, abin fa ba sauki ne da shi ba, ba ƙaramin abu bane, har faɗa mayaƙan suke yi a tsakaninsu, su jiwa juna ciwo, amma a haka kullum sati Hoorain ne yake yin nasarar zuwa na ɗaya, duk masu yin wannan gasa fa matasan sadaukan mayaƙa ne masu jini a jika, dukkansu basu wuce sha'anin Hoorain ɗin ba a shekaru, amma shi ya kerewa tsara, renon Commander Zafar ai dama ba za'a haɗa shi da kowa ba, ɗan commander da kansa ai dole dama ya kerewa tsara, horon da ya samu na musamman ne, tun yana ɗan ƙaramin yaro Commander yake koyar da shi dabarun yaki da sauransu. So a takaice dai saboda wannan gasa yasa labarin rashin lafiyar mama ya fita, King ya tsoke yin wannan gasa a wannan sati saboda rashin lafiyar tata, hakance yasa kowa ya sami labarin bata da lafiya, amma babu wanda ya san me ya sameta sai ƴan cikin gida. Nasan kuma kuna son jin me ya sami mama, to ku saurara, daren jiya ne aka samu wasu mayun kwari da babu wanda yasan daga ina suka fito, suka rinƙa ɗana mata harbi kamar zasu kasheta, kafin ta yi ihu a samu a kawo mata agaji duk sun yi mata ruɗu ruɗu da jiki, duk in da suka ɗana mata harbi sai wani kuraje ya bayyana a wajen tulele da shi jajir, abin ku da farar fata, duk jikinta ya yi ruɗu ruɗu, hakan ya saukar mata da mummunar kuma zazzafar zazzaɓi sosai, ga kurajen sai yi mata zogi da raɗaɗi suke yi, ga azaban kaikayi, babu kuma halin ta sosasu, idan ta ce zata sosa sai raɗaɗin azaba ya kasheta, wannan shi ne halin da take a ciki, harta face ɗinta waɗan nan shegun kuraje basu bari ba, har face kwarin suka cijeta, fuskarta ya kunbura kamar cincin puk puk. Tun a wannan dare da abin ya faru, family gabaɗaya suka taru a room ɗinta lokacin da take ihun neman taimako, ba wasu masu yawa bane fa kwarin, basu fi su goma ba amma suka yi mata wannan aika aikan, kuma baa iya gane menene ya cijeta ɗin ba, domin kuwa kwarin basu da yawa, gasu ƙanana ido baya ganinsu. Sai dai tun a daren Momman Zunaira ta fahimci tabbas wannan cizon na waɗan nan kwarin na su Obaid ne, sai dai bata nuna kamar ta gane nasu ɗin bane, domin kuwa tasan idan kowa yasan nasu ne ba ƙaramin rikici abin zai zamar masu ba, mama tana da yara ita ma, so suma za su ce ba zasu bari ba sai sun ɗauki fansa, saboda dai suma jinin Modarawa na gudu a jikinsu, akwai jinin Akka, ba sai na sake faɗa ba kun san dai Modarawa basu barin bashi, ko ya ka taɓosu sai sun rama, babu yafiya, idan baka taɓosu ba kusan za'a ce sun fi kowa iya zaman amana da adalci ga mutane, amma ka kuskura ka taɓosu fa sai sun rama, ba ɗaga kafa, idan kowa ya ce zai ramawa mamarsa to fa daga nan gida kuma ya dai'na zaman lafiya, duk da cewa dama yanzu ma ba wani zaman lafiya iyayen suke yi ba, ɗan garama yaran nasu da yake basu ne masu yin kishinba, su kansu a haɗe yake, amma iyayen dai sai a hankali, kun san da hakan. Wannan dalilin yasa momma ta ɓoye cewa kwarin nan nasu twin's ne suka ciji Mama, amma dai ta ƙuduri niyar sai ta yi masu faɗa sosai, zata tsawatar masu ta yadda ko da sunan wasa ba zasu sake yi wa wani makamancin irin hakan ba, domin wannan irin cizon kwarin ba ƙaramin azaba ne da shi ba. Amma kash bata samu damar ganawa da su ba har suka wuce Dubai, hakan kuma ya samo asali ne saboda suna a tare da mamar ita da Mummyn Gimbiya Chuchu da Mammiensu Yah Jawad, sai kuyangun da suke yi wa mamar aiki, su ne a tare da ita. Kwararrun likitoci kala kala har kala wajen biyar ne suke a kan mamar suna kula da lafiyarta, ba'a kaita hospital ba duk da a cikin kingdom ɗin asibitin yake, King ya ce likitoci su zo har cikin room ɗinta su yi treating ɗinta. Hakan kuwa aka yi, suka zo suna kula da ita, so su Momma suna a tare da ita. King ma yau bai fita fada ba, yana a tare da ita, bata iya gane wanda yake kanta ma saboda zafin zazzaɓi, tasha bakar azaba, har da suma ta yi kafin likitocin su zo, a sume suka zo suka sameta. Da kyar da taimako Allah suka bata taimakon gaggawa ta farfaɗo. King bai bar wajenta ba sai da lokacin tafiyarsa masallacinsa na jumma'a ya kusa, sannan ya nufi part ɗinsa domin ya je ya shirya. Akka ma tana cikin room ɗin, ita ma Akka ta so ta gane cewa waɗan na kwari na su twin's ne suka ciji mama, saboda ita ma Akkar ƴan biyu ce, daga wajenta aka gado twin's ɗin nan, sai dai ita ɗan uwanta namiji ne, amma kuma sai zuciyarta ya raya mata a kan me su twin's zasu yi wa mama wannan aika aikan? Ganin babu wani dalili ne yasa ta kawar da tunanin su suka yi wannan aikin. King bawan Allah yana can yana tunanin ta ina aka samu irin waɗan nan shegun kwarin masu cizon har cikin room ɗinta saman gado? Dan ya gano waɗan nan kuraje da suka feso mata a jiki cizon wasu halittune daga cikin halittun Ubangiji, sai dai bai san ya aka yi aka sami kwarin ba, bai kuma ga kwarin da idanunsa ba, yasa an cire komai na gadonta an kakkaɓe, amma basu ga komai ba! Ya ɗaura tuhumarsa a kan kuyangun da suke gyara mata ɗaki, bai san shakiyan ƴaƴansa suka yi aika aikan ba, sun koma Dubai sun barsu da jidali. Wannan rashin lafiya ta mama ai jidali ne suka ɗaurawa family, dan kowa sai jikinsa ya gaya mashi, zasu sha wahala kafin mamar ta sami lafiya. Sosai King ya yi shirinsa kamar yadda ya saba zuwa masallacin, ya haɗe a cikin farar alkyabbar wadda kwalliyar jikinta ma duwatsun gold ne, sai kyalli suke yi, haka zali takalmar sarautar da suke a kafafunsa kwalliyar jikinsu da zallar madarar gold aka yi su, ya sha naɗin na wani haɗaɗɗen farar rawanin, ya yi masifar kyau sosai, haka ya fito domin zuwa masallacin. Already an ƙawata mashi dokin da zai hau, ta sha kwalliya da kayan ado na dawakai masu bala'in kyau da tsada, kuɗin kayan kwalliyar dokinsa kawai ya isa ya sayawa mutun katafaren gida a babban birnin tarayya Abuja Nigeria. Tun ba'a buɗe kofar fada ba kilishi da sallama suka fara zuba kirarin sarki zai fito, masu busa suka hau yin busa, tun kafin a buɗe kofar fada da take fuskantar harabar kingdom ɗin mai sanarwa ya sanar da fitowar sarki ta hanyar amfani da amsakuwa. Hakan yasa kowani bawa mai rai da yake cikin masarautar sai da ya nutsu jin sarki zai fito. Nan take masu busar dake a wajen fadar suna dakon fitowarsa suka fara buga busar tasu, masu kirari ma suka fara rera kirarinsu, abin gwanin ban sha'awa, komai cikin tsari da bin ka'ida tare da ƙayatarwa, mayaka duk sun nutsu, ga wasu jiga jigan mayaƙa da a kallah zasu kai su 100 da suka jeru tun daga farkon kofar fadar har izuwa karshen stage na haurawa wajen kofar katafaren fadar, duk waɗan nan mayaka suna a ƙarƙashin kulawar Hoorain ne tare da bin umarninsa, already dama sun saba yin hakan, suna tsayawa a wajen ne domin tabbatar da sun bawa King tsaro har ya hau saman dokinsa zuwa masallaci. Commander kuwa dama shi a cikin Fada yake zama kun sani, da shi ake tattauna duk wata zance da ta shafi fada dama kingdom ɗin gabakiɗaya. Bawan Allah tsufa ta ɗan fara kama shi, yana da ƙoƙari da jajircewa ne sosai, assistant commander yana kula da mayakan sosai, shi kuma yana cikin fada, idan ma zasu je yaki to yana ciki zasu tattauna, idan King ya tsayar da zance sai ya kira Hoorain ya gaya mashi, shi kuma ya hau shirya sadaukai kawai, so haka tsarin yake. Sai da komai ta kankama sannan aka buɗe katafaren kofar fadar, su Galadima ne a gaba shi da malam liman, sannan su makama suka biyo baya, King yana a tsakiya an rufe shi, wasu jiga jigan mayaƙa biyu suna take mashi baya, Hoorain and commander kuma suna ta gabansa, su ne masu bashi tsaro ta gaba. A haka suka fito suka nufi wajen dokin da aka shirya mashi dan zuwa katafaren masallacinsa da yake a cikin kingdom ɗin, sai dai masallacin yana da nisa da family part. A haka King ya nufi masallacinsa masu busa suna ta aikin busa tare da zazzaga mashi kirari kala kala. Dakarun kwararrun mayaka ne suka yi gaba domin sharar hanya kada ko tsinke ya taɓa mai girma King. Ni kuwa na haɗa kayana zuwa DUBAI dan kwaso maku labaran can kuma, mu je muji wace wainar ake toyawa kafin mu sake dawowa mu duba jikin Mama......🥱 DUBAI🔥🤍 Sosai Leesharh ta sha mamakin ganin irin hidimar da ake yi a gidan yau, ta ga gidan nasu sai baki suke yi, jiniyar motoci ne suke ta dira a cikin gidan duk bayan ɗan lokaci, manya manyan baki suke ta yi, ministocine abokan Abu Abdussalam suke ta faman zuwa. Sai tsantsara girke girke kala kala ake yi, a koda yaushe girki kala kala ake yi a gidan kun sani, to amma yau na musamman ake yi. Wanka ta tsantsara ita ma tare da shiryawa cikin wani malesian gown mai bala'in kyau launin up pich, ta ɗauki ɗan ƙaramin please call me hijab ɗinta white color mai kwalliyar duwatsu masu haske a jikinsa ta sanya a jikinta, malesian gown ɗin ya zauna a jikinta sosai, ya bi coca cola shape ɗinta kamar dan ita aka yi sa. Sam sam Leesharh bata damu da yin make up ba, bata yin sai jefi jefi, natural beauty gareta, dan haka a yanzu ma bata yi make up ba, natural beautynta ya kata fitowa sosai saboda zama a Ac ga cima mai kyau, sannan ga sabulai masu zafi da suke kara gyara mata skin ɗinta, sai chocolate colornta ya kara fitowa sosai yana wani glowing. Sai dai fa duk da hakan tana ɗan rame, kuma tana firgice, dan a kullum cikin fargaba da zulumi take, kullum tana tsorace asirinta zai tonu, tana cikin tunanin ya zata kasance ranar da akace asirinta ya tonu, ita sam bata taɓa yin tunanin ya za'ayi ta fita daga cikin gidan ma idan ta kammala aikin ba, bata taɓa kawo wannan tunanin bama a ranta, burinta kawai ta kammala aikin ta koma kasarsu. Hmmmm ni kam na ce akwai gagarumin yaki kuwa a gabanki, dan kuwa kin shiga in da babu fita ne, ko dai my people's kun gano mata hanyar fita bayan ta gama aikin da ya kawota ɗin?. Akwai gagarumim cakwakiya, dan kuwa fita daga cikin gidan Abu Abdussalam ba duk kai ba wlh, wane mutun in ji mutuwa! Ba yadda take tunanin abin bane, ya wuci tunanin mai tunani. Tana shirin nata tana tunanin ta je wajen Sharifat ta tambayeta ko biki za'ayi a gidan ne da yasa ake ta shirye shirye haka, ga motocin ƴan'sanda da sojoji birjin da suka rinƙa rako ministoci gidan. Ta yi kyau sosai, waje ta nufo. A parlourn ta isko su Fadila suna aikin gyaran parlourn nasu. Sannu ta yi masu tare da sanya kai zata fice daga part ɗin nasu. "Leesharh ki shirya da misalin karfe huɗu zamu yi serving na baki drinks da sauran kayan cima a cikin hall ɗin Abbie na yin walima". Cewar Fadila. Kamar zata tambayeta biki za'ayi a gidan ne? Sai kuma ta fasa ta amsa mata dawo okey kawai, a cewarta gara ta je ta tambayi Sharifat zai fi mata kuma zata fi samun cikakken bayani a matsayinta na yar masu gida. Tana amsawa ta wuce izuwa waje. Da kallo su Fadila suka bita har sai da ta fice, sannan ne Radia ta ce. "Gaskiya Leesharh kyakkyawa ce ajin farko, gata kuma black beauty". "Faɗe ma ai ɓatawa ne". Cewar Fadila, ta yi maganar tana shirya pillows dake a saman sofas ɗin nasu. Ita kuwa Leesharh kai tsaye bedroom na Sharifat ta nufa, dan tasan tabbas a nan zata sameta. Sharifat yarinya ce da bata cika son hayaniya ba, dayawan lokuta idan bata a tare da Ummienta to zaka sameta a cikin room ɗinta ta haye saman katafaren king bed ɗinta tana aikin karance karance, ita ɗin macece mai ra'ayin karance karance da bincike bincike kamar yayanta Jaish, wato kamar ƴar jarida, sai iya kaƙale kaƙale. Baki a ɗauke da sallama ta tura kofar room ɗin ta shigo, yau ba ita ta gyara babbar parlourn ba, saboda yau gyara na musamman aka yi mashi, manya manyan masu aikin da suke aiki a hawa na ƙasa ne suka zo suka gyara, ya kuwa sha gyara, kusan komai na parlourn sai da aka canza, aka zuba sabbi, sai tashin fitinannen kamshi parlourn yake yi, kun san larabawa da shegen son turarukan wuta, ƙamshi mai kwantar da hankalin duk wani mai shaƙa ne yake tashi. Kwance ta isko Sharifat a saman gadonta, ta ci kwalliya kamar ba ita ba, arab dressing ta yi kamar yadda ta saba, ta yi rolling veil a kanta, kasancewarta farar fata hakan yasa bakaken kayan suka yi mata kyau sosai. Ta nutsu cikin karanta wani ɗan littafi da yake riƙe a hannunta, littafin larabci ne. Guyson na zaune a saman sofa a cikin room ɗin nata, yana latsa wayarsa, bai jima da gama magana da su Obaid ba, sun gaya mashi jirginsu ya sauka, suna gidan King Badeen, ya ce yaushe zasu zo, suka ce mashi ai ba za su zo ba sai an yi hutun school, saboda ba lokaci, za su je wajen uncle Rahab kafin su koma school, so ba zasu zo gidan Abu Abdussalam ba. Sarai Guyson yasan da cewa gudun haɗuwa da su Yah Ramish suke yi, hakan yasa basu son zuwa, amma bai wani damu ba ya ce masu shi yana nan zuwa gobe su ga juna kafin su wuce school ɗin, on Monday zasu koma school, daga haka suka yi sallama a kan shi zai je gidan King Badeen ya same su. Gaisuwa ta ɗagawa Guyson cikin girmamawa. Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mata gaisuwar tata cikin mutunci. A yanzu shi ma ya fara sabawa da ita saboda ganinta a tare da Sharifat da yake yawan yi, so ya fara sakin jiki da ita, ita kuma Sharifat already dama kunsan ita ta fara neman sabo da Leesharh ɗin ma, so a yanzu sun saba sosai, sun zama kamar wasu ƙawaye. Leesharh kuma har yau har gobe tana aiki ne bisa umarnin masu nikaf, duk abin da kuka ga ta aikata sune nan suka bata umarni, a yanzu suna yawan waiwayarta, suna turo mata saƙonni ba kamar da can baya da suka zuba mata idanu ba, da alama a yanzu sun ɗa gano wani haske dan gane da aikin da suka sanyata ɗin ne yasa suke waiwayar tata. A saman bedside drawer ta zauna tana ɗagawa Sharifat ɗin ma gaisuwa bayan Guyson ya amsa mata gaisuwar tata kenan. Rufe littafin hannunta Sharifat ɗin ta yi tare da miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin, fuska a ɗauke da ƙayatattcen murmushi ta ce. "Leesharh kin yi kyau sosai, kamar kin san yau Yah Bilal zai dawo, shi da Yah Ramish za su je ƙasar Tunisia duba jikin Queen Mama, kowa na gidan nan ya yi kwalliya sosai, kinga Yah Guyson ma ya yi kwalliya". Ta kai karshen maganar tana nuna Omar ɗin da hannu. Haƙiƙa kuwa ya sha kwalliya fiye da kullum, duk da cewa shi dama tun ainahinsa ɗan kwalliya ne, babban yaro ne ɗan kwalisa, shegen son gayunsa ma yasa suke ce mashi Guyson, amma fa gayun da ya ci yau na musamman ne, ƙananan kaya ne a jikinsa, wandon jeans and polo shirts masu bala'in kyau launin white color up and down ɗin dukka, ya gyara kyakkyawar dark black arab hairn nan nasa, abin ba'a magana, kamshi kuwa duk yadda ka kai ga sonta ina ga Guyson ya fika sonta, yana bala'in son kamshi sosai. Wani irin faɗuwar gaba Leesharh ta ji da jin sunan Yah Ramish a bakin Sharifat. "Kai Masha Allah, Allah ya dawo da shi lafiya, shiyasa naga anata hidima a gidan". Cewar Leesharh. "E ai dole kiga ana hidima, da Yah Ramish, Yah Rizwan, Yah Bilal, Yah Raj su ɗin na musamman ne a wajen Abbie, yana ji da su fiye da tunaninki, kamar shi ya haifesu, shekaru dayawa fa suna nan ya ki yarda ya bari su je ƙasar Tunisia, saboda ba ya son su yi nisa da shi, yanzu ma ba dan Queen mama bata da lafiya ba da ba zai iya barinsu su yi nisa da shi har haka ba, ko tafiyar da kika ga Yah Bilal ya yin nan dan saboda aiki ne, badan haka ba suna nan a tare da Abbie". Ta kai karshen maganar tare da zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin. Miƙewa Guyson ya yi yana faɗin. "Is time, Shareefat lokacin zuwa airport ya yi". Ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita. Da sauri ta miƙe ita ma tana faɗin. "Wait for me mana Yah Guyson, Leesharh zan bisu airport, sai na dawo, idan kuma zaki bini ki zo muje, a jerin tawagar motacin Yah Ramish zamu tafi". Da sauri ta girgiza kai tare da faɗin. "A'a ina tsoron binki, sai dai kun dawon kawai". "Me kike tsoro?". Cewar Guyson. Ya yi maganar tare da tsayawa daga tafiyar da yake yi, ya ɗan juyo gareta. "Ina tsoron waɗan nan securitys masu face mask ɗin, da kuma waɗan can masu manya manyan bindigun, fuskokinsu tsoro yake bani". Murmushi ya yi har sai da haɗaɗɗiyar dimple ɗinsa ta lotsa. "Kada ki ji tsoronsu, babu abin da za su yi maki, kawai face ɗinsu ne kullum a fusace, amma ai ba zasu yi wa mutun komai ba ba tare da ya yi masu laifi ba, dan haka ki dai'na jin tsoronsu". Da okey kawai ta amsa mashi, amma fa tsoro kam dole ta ji, waɗan nan fusatattun mutane masu kama da dodannin, ita idan aka ce mata waɗan nan securitys ɗin suna cin namar jikin mutun ɗanya ma ba zata musa ba, domin kuwa fuskokinsu babu ɗigon annuri ko sauki a kansa, waɗan nan idan suka kama mutun ya yi masu laifi Allah sarki, sai dai wani ba shi ba, sun iya ganawa bawa azaba. Wucewa Guyson ɗin ya yi ya nufi waje, da sauri Sharifat ta riƙo hannunsa tana murmushi, a haka suka fice daga ɗakin suka bar Leesharh. Ta ɗan jima a zaune tana tunanin saƙon da aka turo mata yau da safe, saƙo ne da masu nikaf suka turo mata a kan lallai ta nemi wanene or wacece take kaiwa Ramish abinci a cikin ma'aikatan dake gidan, idan ta gano wanene to lallai ta san ta yadda zata yi su ƙullah alaƙa, su sami kusanci sosai, idan suka saba shikenan akwai wani aikin da zasu bata, wannan shi ne saƙon, yanzu ya za'ayi ta nemo mai kaiwa su Ramish abinci a cikin ma'aikatan gidan nan fisabilillahi? Ma'aikata ba ɗaya ba biyu ba, kowani hawa da nasa ma'aikatan, ita da kwata kwata ma bata san a wani hawa su Ramish ɗin suke ba, ba ta taɓa ganinsu ba, yanzu ya zata yi kenan? Wannan shi ne abin da ya tsaya mata a ranta take ta aikin tunani a kansa tun safe. Daga karshe dai ta miƙe ta nufi waje domin ta koma cikin room ɗinta, sai tunanin take yi ko dai ta tambayi Sharifat wacece take yi wa su Ramish aiki ne? Ko kuma ta tambayi su Radia? Tana tsoron tambayarsu kuma kada hakan ya zamar mata matsala, kada wani abin ya zo ya faru ace ai ita ce ta taɓa neman masu yi mashi aiki ta shiga uku. Babbar parlourn ta fito tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Wani irin razana ta yi tare da zaro idanu tana kallon Ummie dake a zaune a saman sofa mai zaman mutun uku tare da wata jibgegiyar hajiya ita ma tana zaune a saman sofa mai zaman mutun uku. Sosai Leesharh ta zaro waɗan nan manya manyan idanun nata tana ganin wannan mata. "Wlh ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan ita Hajiya two seater da ta ɗauko ni daga AAJ House". Ta faɗi wannan magana a cikin zuciyarta tana mai cigaba da kallon matar. Matar bata lura da ita ba, haka zalika ita ma Ummie bata lura da ita ba, da yake parlourn yana da matuƙar girma, daga in da suke zaune da in da take akwai rata sosai da sosai, so basu san da ita a cikin parlourn ba, su suna a saman sofas da suke ta kusa da dining room ne, ita kuma kunga tana ta ɓangaren ɗakinsu Sharifat, akwai rata a tsakaninsu. Hannu ta kai ta sake goge idanuta sosai

Chapter 62 of 75