Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sama ta kurma wani irin gurnanin azaba sakamakon wani irin kaifaffen wuƙa da Mamma ta caka mata a ciki. Wani irin gurnani ta saki take da girgiza jikinta. Mamma dake tsaye a dake kamar wata commander mayaka ta fara kalla. Ko alamar tsoro babu a fuskar Mamma, tana tsaye cikin jarumta, ko shakkar damisar bata ji ba, zuciyarta tafasa yake yi, wani irin bakinciki ta ji na jiwa ɗanta ciwo da damisar ta yi, burinta kawai ta zo su gwabza ta kashe banza, dan ita ba yau ta fara faɗa da damisun dake cikin wannan dajin ba, kafin Kamran ya girma ta sha gwagwar maya kafin su shafa mata lafiya, so Mamma ta wuce tunaninku, ita kaɗai tasan wacece ita kuma me yake ranta. Kanta damisar ta yi cikin zafin nama. Ai kuwa bata yi wata wata ba ta sunkuya ƙasa tare da daba mata wata kaifaffiyar wukar a wuya wajen maƙogwaranta. Kun san damisa da zaki taurin rai ne da su, basu mutuwa ta daɗi, dan haka suka fara kokawa da Mamma babu kakkautawa. Ganin haka yasa Kamran ya lallaɓa da kyar da makyarkyata ya miƙe, yana ta layi ya fara nufar hanyar da take ta kudu domin neman Pretty, bawan Allah shi bama ta rayuwarsa yake yi ba, Pretty ce kawai a ransa. Ita kuma Pretty gabas ta yi, Mamma kuma na faɗa da damisa tana ƙoƙarin ƙarisa kashe ta, yau Rocky baya nan, su suke kwatar kansu da kansu, Allah sarki ga Sweetie dai an tafi da ita, ko su wanene?............ Wai yau ina wannan jarumin mai irin idon su Pretty wanda yake kawo masu ɗauki kullum ne?😥💔 To wannan shi ne sanadiyar rabuwar waɗan nan bayin Allah da suka shafi tsawon lokaci a tare, Sweetie, Pretty, Kamran, shin zasu sake haɗuwa? Ya Kamran zai yi idan aka ce yau babu Pretty? Anya zai iya cigaba da rayuwa? Kun san kaunar da take a tsakaninsu fa! Shin Kamran zai je neman babansa? Wanenen ma shi? Wacece Mamma? Ina mum twins ta tafi ta barsu a cikin wannan dajin? Su waye su Pretty? Suwaye suke neman rayuwarsu? Su waye suka biyo mamansu time da take da cikinsu? Meyasa su kaɗai ake da buƙata ban da mamarsu? Meyasa lokacin da aka biyota waɗan da suka biyota cikin nata kawai suke da buƙata? Ina babansu? Ina baban Kamran? Waye wannan jarumi mai irin idon Prettyn? DUBAI. Menene makomar Leesharh? Shin asirinta zai tonu? Maganin me Ramish ya sha? Shin zai cutu da gaske?. Idan Allah yasa Leesharh ta gama aiki shin masu nikaf zasu cika alkawarin da suka ɗaukar mata na haɗata da babanta kuma su mayar da ita kasarsu? Shin da gaske Leesharh ita ta kashe mahaifiyarta? Idan ita ce menene dalili? Wacece ita ma? Ya makomar tsakaninta da Obaid a yanzu? GIDANSU KHADIJAH. Menene makomar maman Zainab? Baban Zainab ya mutu? Ina Hauwa? Idan baban Zainab ya mutu ya maman Zainab zata yi? Zata tsira kuwa? Kisan kai ta yi kenan? Hukuma zasu barta?. KINGDOM OF POWER. Nan ba sai na yi magana ba, cakwakiyar dake ciki ya wuce tunaninku, abin ya wuce zatonku. Shin da gaske Sweetie ce zata kaimu ga RAWANIN ZALINCI? Suwanene waɗan da suka ɗauketa? Ina kuma zasu kaita?. Amsoshinku yana step two, yanzu zamu afka cikin labarinmu, kada ki bari a baki labari, labari ne da yazo da salo na daban, zalinci, cin amana, hainci, cutarwa, zanba cikin aminci, tauye yarda, tauye hakki, cin hakki, cin zarafi, mugunta, keta, da kuma zazzafar soyayya mai cike da kaddarori haɗi da nasarori da kuma fafutukan cikar buri. 500 Naira kacal kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI from step one to end, da 500 naki zaki cigaba da karatunsa cikin aminci da kwanciyar hankali, trust me ba zaki taɓa yin danasanin karanta littafin RAWANIN ZALINCI ba, zaki ilmantu matuƙa, zaki nishaɗantu matuka, zaki wa'azantu matuƙa, ku kunsan yadda alƙalamina yake, akwai tarin abubuwa a tattare da shi, ba sai na ɓata bakina wajen sake gaya maku ba. Duk wadda ta shirya biyan kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI zata tura kuɗinta ta wannan account ɗin 1882812910 Musa Fatima Zahra access bank. Sai ta tura mun shaidar biya ta nan. 08161390581, kina biya zaki afka cikin tafiyar nan, ayita dake, kada ki yarda a baki labari!!. TAƁA KA LASHE STEP TWO🔥💔😥 KAMRAN AND MAMMA. "Kamran idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu, mutuwa kuma mafi muni a rayuwa, kamar yadda ka taso baka san kowa ba, sai ni, to haka zaka riƙe ka manta da duk wasu tunanin banza". "But Mamma why? I want to know my father ko da kuwa hakan ce zata zama sanadiyar numfashina na karshe, just tell me where's he? Ni zan je in da yake koda kuwa ya fi wuta zafi dole na tunkaresa!! Na kusancesa!!". Tsawa ta daka mashi mai sauti, cikin fusata, idanunta sun kaɗa sun yi jajir, jijiyon kanta har wani mimmikewa suka yi, da alama ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci take yi kamar zakanya. "Kamran ina gaya ma zaka yi mutuwar walaƙanci in dai ka sake yin magana a kan babanka! Kai ba mutun ne kamar kowa ba! Kai ba kamar sauran mutane kake ba! Kai na daban ne, farautarka ake yi kamar yadda ake karautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana! Zaka mutu idan ka fita! Zaka mutu kamar dabba! Dan haka ka tsaya a in da na tsayar da kai!!". "Mamma i can't! I can't gaskiya! Idan kuma kina son na bi maganarki so tell me who I am?! Where's my father and my family?! Why are you hiding our life anytime?! Am tired! Am tired Mamma! I want to see my father and my family, cos I can't stay with you again! Tafiya zan yi na nemo babana and Prettyta even wannan shi ne ganina dake ta karshe!". Tashin hankali kenan, ɗan tsokaci a tsakanin Mamma da Kamran kenan, menene dalilin Mamma na hana shi sanin tarihin babansa bayan ya buƙaci sani? Waye shi? Ina mahaifin nasa yake? Meyasa take cewa zai mutu idan ya sake yin magana a kan babansa? Meyasa?!!. SWEETIE.🔥 "Ɗago idanunki da kyau ki kalleni, sannan kuma ki yi mun shiru, a nan ba'a son hayaniya, kada ki bari a jiyo ki". Shiru dole ta yi ba dan ta so ba, sai dan tsoron irin muryar da ta ji anyi mata magana da shi, tabbas wannan murya da ta ji ba muryar wasa bace, kuma da alama babu imani a tattare da mai wannan murya ko ɗigo. "Ina Spender yake? Shi kawai muke da buƙatar ki bamu, kina bamu zamu sakeki, mu bamu da bukatarki a nan wajen!". Wannan murya ce ta sake katseta da faɗin hakan. Su waye su? Meyasa suka ɗauketa? Menene Spender? Ina kuma yake? Me zasu yi da shi?. Murya a dashe saboda kukan da ta rinƙa sha tun safe, murya ya dashe, da kyar ta iya furta. "Menene Spender?". A fusace Delisha ta ɗaga wannan katakon hannu nata zata zabga mata mari, dan a ganinta Sweetien ta raina masu wayo ne, ta isa tace bata san Spender ba? Ba zai yiwu ba dole ta basu yau, abin da suke haukace suke nema, nemansa suke yi kamar hauka, kuma sun san yana wajenta, sama da shekaru biyar suna nemanta, da kyar suka ganota, sun sha bakar wahala a nemanta, amma ta nuna masu bata ma san shi ba? Tama isa?!!. Tana ƙoƙarin sauke mata wannan katakon hannun nata a saman lallausan kumatunta kwatsam ta ji hannun nata ya sage a saman iska bai ƙarisa kai saman kumatun Sweetien ba. Yar karar azaba ta saki kafin ta furta............. Kai kai kai taɓa ka lashen ya isa haka my people's, sai dai mun haɗu a step two kawai, akwai cakwakiya over. Hanzarta ki biya kuɗin karatu dan ki morewa ganin wannan cakwakiyar!.🤸💃💃 Ƴan Niger kuma ban barku a baya ba, ku mun magana ta wannan numberta ɗin dan na gaya maku ta yadda zaku yi naku payment ɗin. 08161390581 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 75 of 75