Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma Gimbiya Chuchu tana kwance ta shige cikin bargo tana waya da Yah Rizwan, Autar tana kwance tana fuskantar kofar shigowa tana latsa wayar Yah Jawad da ya bari a wajensu. Lafiya lou ya amsa mata da shi kafin ya buɗe mata hannu a kan ta zo. Da sauri ta diro ƙasa daga saman gadon ta tafi ta faɗa jikinsa tana murmushi, duk wannan bidiri da ake yi Chuchun bata da labari, hira ya yi daɗi ga shi tana ƙule a cikin bargo ne yasa sam bata jiyo komai sai kalman yayan nata da yake zazzaga mata tana kara macewa haɗe da narke mashi. Sosai ya rungumi Autar a jikinsa yana jin tsantsar kaunar ƴar uwar nan tasa, ita kaɗai suke da shi mace a ɗakinsu, suna ji da ita kamar me, da kyar ya iya raba jikinsa da nata sannan ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba. Ta ɗan yi mamakin ganin hakan da ya yi, amma bata kawo komai a ranta ba ta koma cikin ɗakin tare da hayewa gado ta kwanta. A wannan rana dai Jaish ya bar kasar ba tare da sanin kowa ba sai Jawad ɗin da yake tamkar jinin jikinsa, kun san shakuwar da take a tsakaninsu tun suna yara. Ko airport ma Jawad ɗin ne ya kaisa a sirrance, sun jima sosai a lokacin da suka yi hugged na juna kafin jirgin ya ɗaga, ba yau bane farau na su yi tafiya ba tare da sanin kowa ba, su je su dawo, amma su kansu yau ji suke yi kamar waɗan da zasu yi rabuwa ta har abada. Jiki ba kwari Jawad ya juya ya dawo gida, duk sai ya ji wani iri, yana tukin mota yana tunanin Jaish ɗin kamar yau suka saba rabuwa. Yana dawowa gida room ɗinsa ya shige ya yi kwanciyarsa dan ya ɗan huta. Da misalin karfe 8 na dare gabaɗayansu sun haɗu a saman table a dining room domin cin abinci, Mama dai tana can room nata ta sha allurar barci, saboda azaban da take ji a jikinta na raɗaɗɗin cizon kwarin nan da kuma tsakanin kaikayi da wajen yake yi mata, ga shi babu halin sosawa, hakan yasa da kanta ta buƙaci ayi mata alluran barci ko zata huta da azaban!. Kasancewar yau Jaish baya nan sai Jawad ya halarci dining room ɗin, ba zai iya cin abinci shi kaɗai ba, dama kun san a tare da Jaish ake kai masu nasu part ɗin ɗaya daga cikinsu, so yau baya nan sai ya ji gara mashi ya fito su haɗu a dining room ɗin ko ya rage kewar ɗan uwan nasa. Sosai King ya yi mamakin ganinsa a room ɗin, bai yi nauyin bakin tambayarsa yau kuma a nan ya ga damar cin abincin ne? Da e kawai ya amsa mashi. Sosai King ya lura da yadda jikinsa yake a mace, ya yi wani sukuku da shi, nan ma bai yi nauyin bakin tambayarsa ko bashi da lafiya bane yake yi kamar wani mai jin barci?. Sam basu kawo a ransu cewa Jaish baya gidan ba, dan kowa yana da ra'ayin zuwa in da yake so ya ci abinci, sun yi zaton Jaish ɗin yana ɗakinsa. A'a lafiyarsa lou ya amsa da shi. Shiru King ya kyalesa da nufin idan sun gama cin abinci sai ya tasashi gaba ya gaya mashi me yake damunsa? Dan dai ga damuwa kam nan karara a saman fuskarsa. Kowa ya hallara a room ɗin ban da Gimbiya Chuchu dake cikin room ɗinta tana ta aikin zuba soyayya da Yah Rizwan, waya suke ta yi ba kakkautawa, ya gaya mata gobe zai biyo su Ramish domin kawai ya zo ya ganta, sai daɗi take ji. Da alama Rizwan ya iya soyayya sosai, sai zuba uban murmushi take yi fuska cike fal da annuri. Allah sarki shi kuma Yah Jawad yana can daning room yana tura abinci kamar dole yana fama da kewarta da kuma tunanin Jaish. Da dai ya gaji sai ya ce da Auta. "Auta ina Jannat ne?". Ya tambayi in da take ne kuma domin yana da buƙatar ta zo nan ko zai rage kewa da tsananin tunanin ɗan uwan nasa da ya tsaya mashi a rai sosai, bai san meyasa ya damu har haka ba. "Aunty Chuchu tana ɗakinta". Auta ta bashi amsa. King ne ya ce. "Meyasa bata fito cin abinci ba?". Still dai Autar ce ta bashi amsa, domin babu wanda zai iya ce maka yasan halin da Chuchu take ciki a gidan biyun Autar. "Daddy nima ban sani ba, ina ganin kamar bata jin yunwa ne ko kila sai ta yi shirin kwanciya zata sha wani abin mara nauyi kamar shekaran jiya da jiya". Jawad ne ya ce. "Go and call her for me". Ya yi maganar ba zato ba tsammani yana kawar da kallonsa daga kan Autar suka haɗa ido da King. Wani irin kallo King ɗin ya jefa mashi wanda ya ɗan sanya shi sakin siririn murmushi. Hannunsa ɗaya ya kai ya ɗan shafa sumar kansa yana cigaba da ɗan murmushi. Hararar wasa King ya wurga mashi yana mai cigaba da kai abinci bakinsa. Sai kallonsu a sace momma take yi, ta fahimci akwai wani abin dai da King bai gaya mata ba dan gane da Jawad, dan yadda yake binsa da irin wannan kallo akwai wata a ƙasa. Shi kuma Yah Jawad sai ya kawar da kallonsa daga kan King ɗin ya cigaba da cusa abincinsa cikin baki wanda yake jinsa kamar magani saboda rashin daɗi. Miƙewa Auta ta yi ta nufi fita daga room ɗin. Ko da ta je manne da waya ta isko Chuchu, sai zuba hira suke yi, tana ta kashe Yah Rizwan da shagwaɓa, soyayya ta yi daɗi tama mance da abinci. Kiranta Autar ta yi sannan ta juya bata tsaya ta jirata ba, dan yunwa take ji Allah ya gani. "Yah Rizwan daddy na kirana in je in ci abinci, ka bari sai na dawo ko?". Daga other side ɗin ya amsa mata da. "Bari na zo to na baki a baki ko? Dan bana son ki sha wahala, da akwai yadda zan yi in tauna maki ma sai na tauna maki". Wani irin sihirtatcen murmushi ta saki kafin ta bashi amsa da. "Kai Yah Rizwan, ai zan ji kunyar su daddy idan ka ce zaka bani abinci a baki, ba zan iya ci ba, har da Akka fa da su Mummy dukka a wajen, kuma sai ka iya bani a baki ba zaka ji kunyarsu ba?". Nisawa ya ɗan yi. "Wacece kuma Akka? Ina ruwana da ita? Zan dai ɗan ji kunyar Mummy, amma banda daddy". (Da alama Akka fa dukka jikokinta ne basu kaunarta 😅 kun ji Rizwan da walaƙanci wai wacece kuma Akka😅 ko da yake wannan tsohuwa zama da ita sai irinsu Guyson ne za su iya, wato masu mugu mugun hakuri sosai kenan 😅 babu ruwana dai ni kam kada ace na ce, to ban ce ba.🌝) Ɗan zaro idanu ta yi na jin ya ce wacece kuma Akka da kuma ba zai ji kunyar daddy ba sai Mummynta. "Yah Rizwan ni kuma na fi jin kunyar daddy a kan Mummy fa". Ta faɗa tana sauƙowa ƙasa daga saman gadon. "To bana son gimbiyata ta zauna da yunwa, jeki ki ci abinci ki ƙoshi sosai, hirarmu ba zata kare ba, idan kin dawo zan baki wani labari kin ji ko?". Da okey ta amsa mashi tana ƙoƙarin katse kirar ta tsinkayo muryar can ƙasa ƙasa yana faɗin. "I love u my sister, ki kula mun da kanki, i will going to miss this your sweet voice wadda idan kina magana yana sanya na rinƙa jin mamar barci zai ɗaukeni, bana........" Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon shigowar Ramish da Bilal cikin room ɗin nasa. Ita kuwa jin ya dagata yasa ta mayar mashi da kalmar i love u too tare da katse kiran ta nufi waje. Kai tsaye dining room ta nufa. A saman kujera kusa da Auta ta zauna, ya zama suna fuskantar juna ita da Yah Jawad ɗin, shi kuma daddy da kujerarsa take a gaba yana iya ganin fuskar kowa, a side ɗin kujerarsa ce kawai a wajen. "Meya hanaki fitowa ki ci abinci?". Jawad ya tareta da wannan tambayar. Gaisuwa ta fara ɗagawa daddyn nasu, bayan ya amsa ta gaishe Akka sannan su Momma haɗe da Akka, sannan ta bawa Jawad ɗin amsa da tana waya ne, da yake bata iya karya ba, amma bata gaya mashi da waye take yin wayar ba. Bayan ta bashi amsarsa ne ta ɗagawa su Sarina gaisuwa a matsayinsu na sister ɗinta. Cikin nutsuwa suke cin abinci. Kuyanga Zubaida ta zubawa Chuchun abin da take buƙata. Room ɗin ya yi tsit kamar ba mutane, sai sautin spoon ɗai ɗai zaka ji yana tashi. A hankali Chuchun ta ɗauki cup mai shake da pina colada zata kai ɗan bakinta, tana jin ra'ayin shansa kaɗan ba dayawa ba. Bata ƙarisa kai shi bakin nata ba ta ɗan yi ƴar ƙara tare da sakin kofin ya faɗi a saman table ɗin. A hanzarce gabaɗaya kowa dake saman dining ɗin ya ɗago da kansa tare da kai kallonsa kanta. Auta ta riga kowa tambayarta lafiya me ya sameta?. Autar bata rufe baki ba King ya jefo nashi tambayar. Nan take kowa ya fara jefo nasa tambayar, sun tsura mata idanu suna jiran amsa. A hankali ta ɗan ɗago idanunta ta saci kallon Jawad da suke fuskantar juna, ya yi wani yin ƙasa da kai kamar babu shi a room ɗin. Bin in da take kallo da kallo King ya yi, ganin Jawad take kallo yasa ya cigaba da cin abincinsa ya fita shirginsu, dan yasan in ya biye masu ma shi zai ji kunya a banza. Su Momma sai tambayarta suke yi ta ƙasa yin magana, kowa ya ruɗe yana ta cewa lafiya kuwa? Amma ina ta ƙasa magana. King ne ya ce. "Wai ku ku rabu da ita mana, Zubaida ki sake zuba mata wani pina colada domin ta sha dan naga shi take ra'ayi". A hanzarce kuyanga Zubaida ta zo ta fara kwashe wanda ya zube ta gyara wajen, sannan ta zuba mata wani ta turo mata shi gabanta. Ɗauka ta yi tana ta kallon fuskar yayan nata. Shi kuwa kamar babu shi a wajen. Tana ƙoƙarin kai cup ɗin bakinta a karo na biyu ya sake yi mata abin da ya yi mata ɗazun yasa ta zubar da wancan pina ɗin, ba tare da ya ɗago ya kalleta ba. Ba komai yake yi mata ba face babbar yatsar kafarsa yake zurowa ta ƙasar table ɗin yana ɗan yi mata kamar tafiyar tsutsa a kafafunta, da yake doguwar riga ce a jikinta, ta ƙasar rigar yake zura kafar tasa yana taɓa mata tata. To da ya yi mata na farko tsoratata ya yi, dan bata yi expect na jin hakan ba, ta tsorata. Yanzu ma a hankali ya sake zuro kafar tasa ya fara yi mata kamar ɗazun. Still yanzu ma ta tsorita, sai dai bai kai tsoron da ta ji ɗazun ba, ɗan lumshe idanunta ta yi tare da kai cup ɗin ɗan bakinta. Bata cire cup ɗin daga bakin nata ba ta waro idanun nata a saman fuskarsa, a lokacin shi ma ya zuba mata idanu yana kallonta, wani irin kyau ta yi mashi lokacin da ta lumshe idanun nata, sai ya ji ta gama tafiya da shi mai gabaɗaya, da babu kowa a room ɗin ba abin da zai hana shi rungumota. Cigaba da yi mata tafiyar tsutsa a kafar tata ya yi yana mai cigaba da kallonta, ita ma tana shan pina ɗinta tana kallonsa tana ɗan murmushi. A hankali ya gangaro da kafar tasa izuwa dai'dai sai tin tata, sannan ya sanya ƴatsun kafafun nasa ya riƙo nata babbar yatsar kafar yana wasa da shi. Duk abin da suke yi King yana kallonsu, amma ya cigaba da cin abincinsa tamkar bai ga komai ba, tunanin abin da zai yi kawai yake yi a ransa, tunanin kalar hukuncin da zai yanke masu yake yi. Matse mata babbar yatsar kafar tata ya yi a cikin tsakiyar nashi yatsun. Har sai da ta ɗan yamutse fuska alamar zafi, ɗan turo mashi baki ta yi tare da ajiye cup ɗin pinan nata, kamar zata sanya mashi kukan shagwaɓa. Ganin hakan yasa ya ɗan sakar mata ƴatsun nata, yana saki ita ma tasa nata wai zata kamo nashin ta matse ya ji idan da daɗi. Amma ina ƴan yatsunta ba za su iya kama na shi ba, ya yi mata girma. Kamar zata yi kuka take binsa da kallo tare da turo baki. Wani siririn cool murmushi ya sakar mata wanda ya sanyata sauke ajiyar zuciya, sannan ya kashe mata ido ɗaya. Plate ɗin abinci da kuyanga Zubaida ta zuba mata ta jawo ta fara ci tana sakin murmushi, tana jin daɗin kasancewa da Yah Jawad a yanzu, saboda yana sakar mata fuska kuma yana mata wasa sosai, so tana jin daɗin kasancewa a tare da shi sosai da sosai. Bayan sun kammala cin abincin ne ya janye kafarsa daga kusa da tata, a hankali ya miƙe tsaye. "Jannat ki kawo mun wayata da na baki room ɗina". Yana maganar unexpect again kallonsa ta sauka a kan King, tun ma daddyn nasu bai yi wani yunƙurin ba ya sakar mashi murmushi tare da sa kai da sauri ya wuce. Sai dai kafin ya fita muryar King ɗin ta daki dodon kunnuwansa da cewa. "Ka sameni a room ɗina yanzu Jawad". Da okey kawai ya amsa sannan ya fice. Da ɗaiɗai da ɗaiɗai kowa ya watse a room ɗin. Akka tana shigowa cikin room ɗinta wayarta dake saman bed ya fara ruri. A hanzarce ta ƙarisa ta kai mashi agaji. Picking ta yi tare da hayewa saman gadon mai gabaɗaya. Daga can ɓangaren Rizwan ya fara tsantsara mata sallama tare da ɗaga mata gaisuwa. Sai da ta zage shi kafin ta amsa, wai yau kuma wani munafurcin yasa ya kirata? Dan rabon shi da kiranta tun last year sallah da ya kirata ya yi mata happy sallah, to yanzu kuma gulmar me yasa ya kirata?. Hakurin ya fara bata tare da rarrashi yana gaya mata aiki ne ya yi mashi yawa. Tatas ta zage shi daga shi har su Ramish ɗin gabaɗaya kafin ta saurare shi, Akka akwai dirama tsohuwar nan. Cikin zumuɗi ya sanar da ita dalilin kirata, ya kira ne ya sanar da ita ya samu mata kuma ba kowa bace face Chuchu, dan haka ta taya shi kafin ya zo. Wani irin matuƙa fari tas ɗin farinciki ne ya mamaye mata cikin zuciya. Haƙiƙa ta ji daɗi kuma ta yi murna, amma sai ta ɓoye murnar tata, ta fara zazzaga mashi masifa a kan ai dama tasan yanzu ma buƙatar kansa ne yasa ya kirata, to dan haka ya sani ba zata bashi Chuchu ba, kuma dai yasan ita ce mai zartar da hukuncin a kan komai. Lallaɓata ya fara yi yana magiya tare da marairace murya, yasan Akka ita ce nan take da iko da su da iyayensu, yasan idan ta bashi Chuchun to fa babu uban da ya isa ya hana, haka zalika idan ta hana shi, wannan dalilin ma yasa ya biyo ta wajenta kai tsaye bai je wajen daddy ba, dan ko ya je ga daddyn ma zai ce mashi sai abin da Akka ta zartar ne, so shiyasa ya fara bi ta wajenta, kuma Mammaiensu ce ta bashi wannan shawara, ta ce kai tsaye ya tunkari Akka, kuma kada ya wani ɓata lokaci wajen jira, ya yi saurin tunkararta ya gaya mata, hakan yasa ya gaya mata ɗin......... Lallai da gaske Mammie ta shirya raba Jawad da soyayyar Chuchu karfi da ya ji, domin kuwa hanyar da ta biyo mai karfi ne wanda ya fi na Jawad karfi, tun da Rizwan ya gayawa Akka shikenan kuma, Akkar zata tambayi Chuchun tana son yayan nata ne ko bata sonsa, idan har ta amsa da tana son shi fa shikenan babu wanda ya isa ya sa a fasa wannan aure sai mutuwa sai kuma wani ikon na Allah. Ku ma dai kun san Chuchu dai tana son yayan nata, dan haka da e tana son shi zata amsa. Akwai cakwakiya ba kaɗan ba, akwai tashin hankali. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥 Nutsuwa sosai Leesharh ta yi tana sauraron abin da yake faɗa. Daga yadda yake fitar da word's ɗinsa kai kasan nutsatsen mutun ne mai ji da izza haɗe da class, ba karya jinin King Zuhair yana gudana a jikinsa. Magana yake yi a kan lallai a cikin daren nan dole zasu yi wannan meeting ɗin, domin gobe da safe za su wuce ƙasar Tunisia, so ya zama dole a daren nan su haɗu, umarni ya baiwa wanda suke yin wayar da shi a kan lallai karfe takwas ya samesu a wani katafaren luxurious guests house ɗinsa. Ba taro ne da zasu yi a ma'aikatarsu, taro ne na team guda ba na gabaɗaya special weapons and tactics ba, manya manyan zakarun gurayen mazan dake cikin Team na Ramish ɗin su sha biyu ne dai'dai, kowanne daga cikinsu kuma yana da yaran aikinsa a karkashinsa, hakan yasa waɗan da suke a ƙarƙashin Ramish ɗin sun fi mutun 200, waɗan nan maza sha biyun sune jiga jigai masu kula da kannar dake cikin team ɗin, su suke karɓar umarni daga wajen Ramish ɗin su zartar wa da na kasa da su ɗin, so haka suke, team, team, suke, sai dai team na Ramish ya fi na kowa shahara a cikin special weapons and tactics, saboda bashi da wasa, duk kuma wanda za su kasance a cikin team ɗinsa to ba karamar horar wa yake sakawa a basu ba, domin kuwa shi baya ɗaukar faɗuwa, burinsa a kullum cin ma nasara, baya wasa da aikinsa, waɗan nan gurayen maza guda sha biyu na cikin team ɗin nasa ba karamar horar da su ya yi ba kafin su kai matsayin da suke kai a yanzu, ba shi da aboki daga waje sai cikin gida, su ne kuma Bilal, Rizwan and Dr Raj, haka zalika bashi da wani kusanci da wani a wajen aiki, duk da ya kasance cewa ƴan team ɗin nasa horonsa ne, amma baya yarda da kowa, dan yasan farautar rayuwarsa ake yi kamar yadda ake farautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana, yasan komai hakan yasa bashi da wani makusanci biyun Bilal, Rizwan and Dr Raj, a waje baya yarda da kowa, kallo da ido kawai ta raba shi da kai. A ko da yaushe yana yawan zaman meeting da waɗan nan gurayen mazan ƴan cikin team ɗin nan nasa domin kara karfafa team ɗin nasu ya cigaba da kasancewa shi ne na ɗaya a cikin hukumar special weapons and tactics, yana son ya kasance a sahun gaba kullum....... Yo dama jinin King Zuhair jinin Akka ai dole ya zama haka, su fa basu ɗaukar wasa a lamuransu, wai kun manta me Akka ta ce ne a kan jarumta?..........😅 Sosai Leesharh ta tsumaya da sauraron zazzaƙar muryarsa, tana naɗar duk abin da yake faɗa tana kuma jin daɗin yadda yake yin maganar one by one. Bata bar wajen ba har sai da ta dai'na jin maganarsa alamar ya bar wajen kenan. Cikin hanzari ta fito daga in da ta laɓe ɗin ta nufi room nata, jikinta sai kerma yake yi kamar wadda ta aikata wani abin rashin gaskiya....... Ko da yake rashin gaskiyar ai ta aikata tun da ta yi wa wani laɓe ta ji abin da yake faɗa. Tana shiga ta haye saman gadonta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, kirjinta sai bugawa da sauri sauri yake yi. Zuciyarta sai harbawa pat, pat, pat, yake. Wani irin razana ta yi jin vibrate na wayar dake ƙarƙashin pillownta, dama can a razane take tsabar rashin gaskiya, da wayar ta fara vuuu kuma sai ta kusa rugawa a guje. Dafe kirjinta ya yi tana furta Hasbunallahu wani'imal wakil cikin rawar murya. A hankali ta kai kallonta kan pillown, jiki a sanyayye ta janyo pillows tare da ɗauko wayar. Da farko kamar ma ba zata ɗauki wayar ba, amma tuna cewa number ɗaya ce take kirarta a wayar kuma wannan number babban barazanace ga rayuwar mahaifinta yasa ta hakura ta janyo wayar. Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye lokacin da idanunta suka sauka a kan wannan number, ji take yi kamar ta maka wayar da ƙasa ko ta haɗiyi zuciya da mutu kawai huta, ta fara gajiya da fargaba da faɗuwar gabar da suke jefata a ciki, idan ta cigaba a haka wlh faduwar gaba ne zai zama sanadiyar rayuwarta. Picking ta yi tare da kara wayar a kunnanta jiki kamar wadda aka zarewa laka. Daga other side ɗin aka fara magana cikin sanyin murya. "A'isha na manta ne ban sanar dake wani abin ba, idan kin je wajen walimar nan ki mayar da hankalinki sosai a kan mutane, babu ruwanki da yin magana da kowa, sannan kada ki manta wajen a cike yake tab da camera's sosai". A tunanin matar yanzu ne Leesharh zata tafi wajen walimar, bata san ita kam har ta je ta dawo ba abinta, zama ya gagareta a wajen walimar saboda rashin gaskiya. Da kyar ta ɗan iya saita nutsuwarta tare da fara gayawa matar duk abin da ya faru tun daga zuwan ta wajen walimar har izuwa yanzu da take zaune a bakin bed dinta. One thing about Leesharh yarinyar nan bata karya, kome zaka yi mata in dai zata buɗi baki ta yi magana to gaskiya zata faɗa, sai dai idan tasan gaskiyar bashi da amfani a wajen ko kuma tana tsoron faɗarsa kada ya zame mata illa to a nan kuma shiru zata yi sai dai a kashe ta, amma ba zata taɓa yin karya ba!!. Wani irin sautin dariya ne ya fito daga ta cikin wayar, a hankali sautin yake tashi, da alama sun ji matuƙar daɗin news da Leesharh ɗin ta basu. Shiru baiwar Allah ta yi tana sauraron dariyar matar har na tsawon minti ɗaya. Ɗan taɓe baki ta yi tana mamakin ko me ya sanya matar yin dariya? Ta tambayi kanta. Ta shagala da tunane tunane ta tsinkayo muryar matar tana faɗin. "A'isha Allah ya yi maki albarka, ashe da rabon kin kusa komawa wajen babanki, yau kin gaya mun labari mai daɗi, amma kin tabbatar a guests house ɗinsa ya ce zasu yi zaman?". Gyaɗa mata kai Leesharh ta yi tamkar tana a gabanta kafin ta ce e ta tabbatar. "Good! Kenan Ramish zai fita gida kafin karfe takwas na dare, dan shi baya wasa da lokaci, hakan ma dai'dai ne, yanzu dai abin da nake so da ke shi ne, akwai wata magani da zan sanya a kawo maki, ko in ce ki fita ki je ki nemo wacece zata kai wa Ramish abincin dare? Idan kin dawo zan kiraki karfe 6 dai'dai dan na gaya maki a in da zaki ga wannan maganin, abin da nake so da ke lallai lallai ki shammaci mai kai mashi abincin nan ki zuba mashi wannan maganin a cikin cappuccinonsa, dan na san ko bai ci abinci ba tabbas ba zai fita daga gida ba tare da ya sha cappuccino ba, dan haka zai sha maganin kafin ya halarci wannan taron, idan kika yi komai cikin nuna taka tsantsan da kulawa tabbas gobe zan haɗaki da babanki a waya ku gaisa, idan komai ya tafi yadda muka tsara kam ma a cikin daren nan zaki bar gidan, kina barin gidan kuma sai ƙasarku zaki koma....." Zubur ta miƙe tsaye tare da zaro idanu tana faɗin. "Aunty da gaske zaki haɗani da babana a waya? Kuma da gaske zan koma ƙasarmu?". Tabbatar mata da hakan matar ta yi kafin ta katse kiran kit. Wani irin farinciki Leesharh ta ji ya rufeta, nan take ta ji kwarin gwiwa, tabbas in dai zata gaisa da mahaifinta a waya to ba shakka yanzu ba sai anjuma ba zata nemo waye zai kai wa Ramish abincin dare. Lallai ba shakka matan nan sun san lagon Leesharh, sun san da cewa idan suka ce zasu haɗata da babanta to fa zata yi masu abin da suke so cikin sauri, basu zaɓota a kan wannan aiki haka kawai ba sai da suka tabbatar da lallai tana da jajircewa akan abu idan ta sanya kanta, in dai ta ce zata yi abu fa to wlh sai ta

Chapter 68 of 75