kamar ba wajen bane ba.
Mamaki ya lulluɓe shi ya ƙasa gaba ya ƙasa baya, while shi kuma Rocky ya yi gaba abinsa yana son wucewa ya je ya shiga cikin bukkar.
Ganin Rockyn zai shiga ciki ne yasa shi ya ɗan farfaɗo daga sumar mamakin da ya afka.
Da sauri ya ƙarisa ciki dan ya kara tabbatarwa da kansa abin da yake gani. Tabbas ba gizo bane, kamar yadda mum twins ta sha madarar mamakin ganin an taimaka masu an gyara masu komai, haka shi ma ya sha wannan madarar mamakin.
Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanuwansa suka sauka a kan mum twins da babynta, da farko ya ɗauka basu nan ne, ganin suna nan yasa ya ji wani sanyi ta ratsa shi.
Da sauri ya ƙarisa kusa da mum twins ɗin yana mai gayawa Rocky kada ya ce zai shigo cikin ɗakin nan ya ɓallah masu abubuwa, dan kofar shiga ma ta yi mashi kaɗan, idan ya ce zai shiga kaf zai karya itatuwan da aka kafa a bakin kofar, dan haka ya tsaya a waje.
Wani irin gurnani ya yi alamar bai ji daɗi ba, Kamran ya hana shi shigowa yaga ne a ciki.
(Ga ji mun Rocky da gulma😒 wato suma sun san gulma fa😅)
Jin motsin mutun a kanta ne yasa ta yi saurin waro fararen idanuwanta waje, dan taga wanene.
Duk da cewa ɗazun da ya taimaka mata ita da baby's nata suka fita daga cikin ramin nan bata a cikin hayyacinta, amma hakan bai sa ta ji tsoron ganinsa ko makamancin haka ba, sam bata iya gane face nasa a ɗazun ba, tana cikin wani hali, bata san wanene a kanta ba lokacin.
Ganin shi cikin nutsuwa da kamala sosai a tattare da shi ne yasa ta kura mashi idanu tana mai binsa da kallo.
Tsugunnawa a gabanta ya yi, cikin sanyin murya ya tambayeta wanene ya yi mata dukka wannan abin? Ko dai ita da kanta ne ta yi?.
Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba ita ce ta yi ba, amma bata iya buɗe baki ta yi mashi magana ba.
Sake shiga cikin kogin madarar mamaki ya yi, amma sai ya daure ya kawar da mamakin nasa tare da ce mata.
"Zaki iya tashi zaune?".
Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar.
"In ɗaga ki?".
Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a bata buƙatar ya ɗaga ta.
Zai sake yin magana ɗaya daga cikin baby's ɗin nan ya fara motsi haɗe da kuka kaɗan kaɗan.
Kusan a tare ita da shi ɗin suka kai kallonsu a kan yaran.
Wannan mai black cuiry hairn ne dai yake motsi tare da kukan.
Da sauri Kamran ɗin ya kai hannunsa ya ɗan ja towel da aka lulluɓesu zuwa kasa kaɗan, ɗan girgiza babyn ya fara yi.
Ai kuwa yana taɓa babyn kamar ya ce ya kara ihu, wage baki ya yi ya fara zunduma ihun da gasken gaske, dama already kun ga da kuka ya zo, sarki ne wajen zuba kuka, dan haka kuwa sai ya cika masu kunne da ihu.
Runtse idanuwanta gam maman nasu ta yi, har can cikin ranta take jin wannan kukan nasa, wani irin zafi zuciyarta take yi mata.
Hannu biyu Kamran yasa zai ɗauki babyn, ai kuwa bai kai ga ɗauka ba ɗayan baby mai golden white hair ya fara ihu shi ma.
Kasancewar daga Kamran har maman tasu basu san cewa tun da aka haife shi bai yi kuka ba, sai kukan nasa bai basu mamaki ba, sai ma rikita Kamran ɗin da suka yi, ya rasa me zai yi masu, ya kuma rasa wanne zai ɗauka daga cikinsu.
Allah sarki uwa da ƴaƴan, jin kukansu su dukkansu biyu yasa ta ji ba zata iya jurewa ba, ciza laɓɓanta da karfi ta yi tare da yunƙurawa dan ta miƙe zaune.
Da sauri Kamran ya juyo da kallonsa a kanta.
Wani irin wahalallen kara ta saki tare da dafa kasa da iya karfinta tana son tashi, nan take har wani irin zufar wahala ya fara tsastsafo mata, daga gani kasan tana jin azaba ba kaɗan ba, dama kuma ai dole ta ji azaba, suka da kifiya a ciki ai ba wasa ba, dan ma ta auna arziki ne ba kaɗan ba, ba dan haka ba ai da ta jima da mutuwa, kuma kunga wanda ya harbeta da kifiyar bai harbeta a in da zata cutu sosai ba, ya mata da sauki.
Kamran sarkin tausayi, duk zafin zuciyarsa akwai tausayi sosai, har cikinsa yake jin wani irin matuƙar tausayinta ya lulluɓe shi, ji yake yi kamar yasa hannu ya ɗagata, amma sam bata son ya taɓata, sanin tana gudun ya taɓata ne yasa ya hakura ya jure yana ganinta cikin wannan hali bai yi yunƙurin taimaka mata ba, ya bita da kallon cike da tausayawa fal a face nasa.
Bai kuma hanata miƙewa ɗin ba, duk da yasan tana da ciwo a cikinta, kasancewar yaga anyi mata aiki sosai a kan ciwon ne yasa sai bai hanata ba, amma kuma duk da wannan magani sosai da aka zuba mata, yana da kyau ta sami kamar kwana uku bata motsawa sosai, dan wajen ya ciko da wuri, sai dai ina, hakan sam ba zai yiwu ba, saboda yaran nan nata, da alama rigimammune number ɗaya, dan sarakan kuka ne, ita kuma ba zata iya jure jin kukan nasu ba, hakan yasa zata miƙe zaune dan ta san ta yadda za'ayi ta basu nono.
To ya Ubangiji ka sakawa iyayenmu da gidan Aljanna, ya Allah kamar yadda suke sadaukar da abubuwansu da dama masu matuƙar mahimmanci wani lokaci ma har da rayukansu a kanmu, ya Allah kasa su zamana daga cikin al'ummar da annabi zai fara ceta a ranar gobe kiyama, ka bamu ikon yi masu biyayya sau da kafa a kan dai'dai.
Da kyar da suɗin goshi ta iya tashi zaune, ta jingina bayanta da jikin itatuwan da aka haɗa masu ɗakin, tsabar azaba har wani irin jajir idanuwanta suka yi, tamkar wadda ta sha kuka na tsawon lokaci ta ƙoshi, zufa cigaba da tsastsafo mata yake yi a gefe da gefen face nata, fuskar nan tata tamkar wadda aka watsawa ruwa.
Ta datse lausasan laɓɓan bakinta gam da hakwaranta, ta kuma datse idanuwanta gam tana girgiza kai alamar azaba take ji sosai.
A hankali take sauke numfashin da yake fito mata tamkar wadda ta sha uban gudu ta ƙoshi, sai a lokacin kuma ta ji nauyin kayan jikinta ya ragu, alamar an rage mata kayan jikin nata. Tana son buɗe idanuwanta ta bi jikin nata da kallo, amma ta kasa iya buɗesu, saboda azaba, ji take yi kamar idan ta buɗe kara karuwa raɗaɗin ciwon zai yi mata.
Sosai Kamran ya yi matuƙar jinjina mata, dan kuwa ta yi namijin ƙoƙarin na wuce misali, ba kowa ne irin abu haka zai faru da shi kuma ya iya miƙe zaune a yau ba, sai wanda yake da matuƙar jarumta, da alama jaruma ce sosai ita ma, dama idan baku manta ba a baya na gaya maku da alama jarumace, da alama an sha fama da ita sosai kafin a iya kaita ƙasa.
Duk jarumta irin na Mammansa yau dai Kamran ya jinjinawa maman twins ma, bai taɓa tunanin aduniya za'a sami jaruma mai tafasasshen jini irin Mammansa ba, sai ga shi yau ya ganta duk da bata kai Mamma ba, dan ita Mamma karshe ce, jarumtarta tamkar wani sadaukin yaki haka take, macen da zata yi faɗa da Damusa ai kunga ba ta wasa bace ba!.
Su dai baby's da yake basu san halin da ake ciki ba, sai tsallara ihu suke yi abinsu, ko a jikinsu, duk sun sa Kamran ya shiga ɗimuwa, ya rasa waye za rarrasa, sun rikita bawan Allah, duk da dama can ba iya rarrashin ya yi ba, yana dai kwatantawa ne, kunga shi kaɗai ne a wajen Mamma, bai da kani ko kanwa bare ace yana ganin yadda Mamma take renonsu shi ma ya koya.
Da hannunta ɗaya ta dafe wajen ciwon nata, ɗayar hannun nata kuma idanuwanta a datse gam ta fara yi wa Kamran ɗin nuni da ya bata baby's ɗin, ba halin yin magana, baki na datse gam.
A hanzarce ya ɗauko wannan mai bakin curly hair ya miƙa mata, dan yafi tsala ihu, babyn nan tamkar maƙoshinsa zai fashe, saboda iya kuka.
A karkace Kamran ya ɗauko shi ya ɗaura mata a saman cinyarta. Jin babyn a jikinta yasa ta sauke wani irin wahalallen nauyayyar ajiyar zuciya, alamar ta ji sanyi ya ratsa cikin zuciyarta.
Da kyar ta iya tallabo babyn ta fara kiciniyar bashi nono duk da bata da tabbacin tsabtar jikinta, ita dai burinta kawai ta shayar da su su daina wannan ihu, dan a tunaninta yunwa suke ji sosai ne yasa suke irin wannan uban ihu haka.
Shi dai Kamran yana son taimaka mata, sai dai babu hali, dan kuwa bazata taɓa yarda ya taɓa jikinta ba, sanin hakan yasa ya kawar da kansa daga kallonta ya cigaba da girgiza ɗayan babyn dan su sami saukin wannan ihun da yaran suke rera masu.
Shi kuwa Rocky ya yi kwanciyarsa a bakin kofar shigowa, sam ba haka ya so ba, ba yadda ya iya ne kawai, yana jin maganar Kamran sosai.
(Hmmm Damusa dai ki sabo ne! Duk da akwai masu amana kamar yanda yake a ko'ina akwai masu amana dana banza, Allah dai ya tsare mana su Kamran, kada wata rana Rocky ya rasa abinci ya yi ram da su😅.)
Da kyar ta iya fitar da nonon ta sakawa babyn abaki. Ai kuwa kamar jira yake yi ya fara sha babu kakkautawa, Allah sarki ashe da gaskiyarta, ashe tasan me suke yi wa kuka, uwa kenan! Babu biyunta a duniya!.
Mamaki ne ya kama Kamran sosai na ganin yadda wannan babyn ya yi shiru yana shan nono, sai a lokacin ya lura da babu wannan alkyabba ta jikin Maman twins ɗin wanda kuma yasan dai ya fitar da ita daga cikin ramin nan da wannan alkyabbar a jikinta, to ko waye ya cire mata shi?.
Ya tambayi kansa da kansa. Ƴar waige waige ya fara yi ko zai ga ta in da aka ajiye mata alkyabbar tata, sai dai ina, bata babu labarinta.
Shiru ya nutsa cikin tunaninsa yana tunano a ina alkyabbar to? Waye kuma ya ɗauketa?. Sai a lokacin ya tuna da cewa ba iya alkyabbar bace kawai, akwai sarka, abin hannu, da kuma ɗankunnenta na zallar madarar gold, suma ina suke? Dukka babu ko zobbe a wajen, bayan kuma shi yasan da hannunsa ya kwaso mata su daga bakin ramin ya biyota da su zuwa wannan wajen time ɗin da take ja a kasa da zasu zo wajen.
Da hannunsa ya ajiye mata su a kusa da ita a lokacin yana yi mata sannu, to ina suke yanzu kuma? Abin da ban mamaki sosai gaskiya, kuma ga dukkan alamu ba wai satarsu aka yi ba, babu ma ɓarawo a wannan daji, tsawon shekaru 15 ɗin nan daga shi sai Mammansa ya sani suke rayuwa a cikin wannan dajin, sai baƙin maharba idan sun zo wucewa, sai kuma idan hanya ta kubcewa mutun ya faɗo cikin dajin, ko su maharba ba kasafai suka cika shigowa cikin wannan dajin ba, dan akwai manyan namun dawa a cikinta, idan suka yi wasa su da suka zo farauta to za'a faraucesu kamar kuda da bujumin sa, hakan yasa sam basu gigin zuwa dajin farauta, sai time to time.
Wannan dalilin yasa abin ya ɗaurewa Kamran kai ya kuma bashi mamaki, to wani ɗan albarkan ne kuma ya kwashi kayan maman twins? Allah masanin gaibu.
Sai da ta ji alamar barcin babyn dake a hannunta ne ta kara sauke nauyayyar ajiyar zuciya, ya sha ya ƙoshi sai barci.
A hankali ta waro idanuwanta waje, sun yi jajir da su kamar wuta, baiwar Allah fuskarta duk a kumbure kamar ba ita ba.
Zubawa babyn idanu ta yi tana mai karewa ɗan kyakkyawar face nasa kallo, ga dukkan alamu wannan baby mai golden white hair yana da matuƙar hakuri sosai, domin kuwa wannan jijjiga shi da Kamran yake yi yana ɗan bubbuga shi a hankali hankali yasa ya hakura ya yi shiru kamar babu shi a wajen, saɓanin mai black hair nan, ai shi ko jijjigawar ma baya jin ana yi, ihu kawai abinsa, da alama acici ne, sarkin cin abinci ne ba wasa!.
Hannu ta kai ta ɗan buɗe towel ɗin jikin babyn da kyar da makyarkyata, domin ta duba shin wai me ta haifa ne?.
Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta kalli cewa macece wannan babyn dake a hannunta, wani irin daɗi da sanyi ta ji yana ratsata, wanda ita kaɗai ta san dalilin.
Ni kuma dai na saka mata ayar tambaya? domin kuwa dole akwai wata a kasa da yasa zata ji daɗi tare da murnar haifar mace da ta yi, ita da take son su ɗauka mata fansa? Mata dai ba iya ɗaukar fansa zasu yi ba, to ko me dalilinta na murnar samu ɗiya mace? Ina da tambaya, amma lokaci ne zai amsa mana waɗan nan tambayoyin.
Ganin tana murna da samun ɗiya macece yasa shi ma Kamran ɗin ya ce bari ya duba babyn dake a wajensa ya gani.
Yana dubawa sai yaga ita ɗin ma macen ce, ajiyar zuciya ya sauke tare da dawo da kallonsa a kan mamar tasu yana mamakin irin uban annuri da farinciki da ya bayyana a saman fuskartar daga ganin ta haifi mace ko ace mata, duk sai kansa ta kulle bawa Allah.
A dai'dai wannan gaɓar ni PRINCESS TEEMA nasan na jijjige teburin dayawa daga cikin makaranta wannan littafin mai albarka, some that are sayin this twin's it's all boy's how far?. And also some that are saying it's boy and girl greeting from this side..........🥳😅🥱
Dawo da kallonta a kan Kamran ɗin ta yi, tana son ta ce mashi ya ɗauke mata wannan babyn tun da ta yi barci ya bata ɗayar ta shayar da ita, amma ta kasa iya yi mashi magana, domin juriya ce kawai irin tata yasa ta iya miƙewa ma.
Ganin tana ta kallon shi babu ko kyafta idanu ne yasa ya fahimci lallai da akwai abin da take son gaya mashi, kada ku manta yana da kaifin ƙwaƙwalwa kamar Mammansa.
Ɗan zuba mata idanu shi ma ya yi, a nan ne ya fahimci ga abin da take da buƙata wadda ta kasa gaya mashi ya yi mata. Hakan yasa ya kai hannu cikin nutsuwa ya ɗauki babyn yana bin fuskar yarinyar da kallo, kyakkyawar gaske ce kamar ita ta yi kanta.
A in da ya ɗaukota da farko ya mayar da ita ya kwantar kafin ya ɗauko baiwar Allah sarkin hakurin nan ya ɗaurawa maman ita a saman cinyarta, sai kallon fuskar yaran yake yi, dukkansu idanuwansu a rufe, ita ma mai black hair har ta gama zuba ihunta bata buɗe idanu ba, suna a rufe take wannan zunduma ihun, har ta sha nono ta ƙoshi ta yi barci da haka.
Bawan Allah Kamran, shi ma sai zogi hannunsa da ya ji ciwon nan yake yi mashi, amma haka ya daure ya jure.
Ita ma wannan baby ana bata nonon ta yi maza ta capke ta fara sha kamar ba gobe, bayin Allah yunwa ce ta yi masu yawa.
Ɗago kai maman twins ɗin ta yi tare da dawo da kallonta a kan Kamran ɗin, tana son ta tambaye shi waye shi? Me yakawo shi nan?, amma ba halin iya buɗe baki ta yi magana, dan wani irin azababben nauyi ma harshenta ya yi mata, ko motsa shi bata iya yi bare ta yi magana.
Shi ma Kamran ɗin a nasa bangaren yana son ya tambayeta wacece ita? Me kuma ya kawota wannan bakin daji mai haɗarin? Amma ina, shima sai ya ji harshensa ta yi mashi nauyin da ya kasa iya tambayarta, sai dai ya bisu da kallo kawai.
Kukan da Rocky ya yi mai ɗan sauti ne yasa dukkansu suka mayar da kallonsu izuwa bakin kofar shigowa.
A takaice Kamran ya ce da Rocky ka gama kukanka dai ba zanzo ba, yau ba wani yawon da zamu je, muna tashi daga nan gida zan koma.
Ya yi maganar ne da wannan yaren nasa, da alama yafi yawan magana da wannan yaren, domin tafi zama sosai a bakinsa.
Sam Maman twins bata ji me ya faɗawa Damusar ba, dan bata jin wannan yaren, sai dai jin ya yi magana da wannan yaren ne yasa tunanin abin da ya faru ɗazun a baya ya faɗo mata.
Shiru ta yi tana tunanin tabbas ta ji irin wannan yaren ɗazun ya daki dodan kunnenta, amma bata iya tuna wanenen ya yi magana da yaren kuma a ina aka yi maganar ba, ta dai san ta ji wannan yaren ɗazun.
Ganin yadda ta lula duniyar tunani ne yasa Kamran ya fara bubbuɗe kwaryayyakin da suke a rufe a gefenta, dan yaga menene a ciki, da farko duk a zatonsa abinci ne a ciki, sai da ya buɗe yaga ashe magungunar gargajiya ne a cike a ciki.
Mamaki ne ya kama shi, wanene ya kawo waɗan nan magunguna? Ya dai san wannan ba na Mammansa bace, domin haɗin maganin Mammansa ba irin wannan bane, kuma yasan ita Mamma wlh ba zata zo nan ba, ita fa a gaban idanunta bakar Damusa ta hallaka wani bawan Allah da hanya ta kwace mashi ya shigo cikin dajin, Kamran ɗin yana kuka yana su taimaki mutumin, amma Mamma taki yarda su taimaka mashi, a gaban idanunta ya mutu ko a jikinta, so ita ba zata taɓa yin taimako ba a cewarta, sam ba ita ta kawo waɗan nan abubuwa ba, bama su yi kama da nata ba, to waye ya kawosu?.
Dole Kamran ya tambayi kansa dan dai yasan su kaɗai ne a cikin wannan daji.
Ni ma dai dole na shiga ruɗani kuma na tambayi kai'na, waye ya yi wannan aikin dukkan?. To koma wani ɗan albarka ne ko wace ƴar albarka ce lokaci zai nuna mana ita ko shi.
Ganin lodin magunguna ne a ciki yasa Kamran ɗin ya miƙe tsaye dan ya je ya samowa maman twins ɗin abin da zata ci, saboda ko ba'a gaya mashi ba yasan tana jin yunwa sosai.
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/7/2024.....✍️📚🌹
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
*Labarin RAWANIN ZALINCI labari ne a kan sarauta dake tafe da Zalinci, cin amana, tauye hakki, walaƙanci, zanba cikin aminci, ku dama daga jin sunan RAWANIN ZALINCI kun san batu ake a kan sarauta mai tsuma zuciya da gabaɗaya ilahirin gangan jiki, soyayya mai cike da bahagon kuma makauniyar kalubale tattare da kaddarori, fata na dai kada ku yi sauri, ku daure ku bi komai sannu a hankali har mu kai in da kuke da buƙata, duk wanda yake da wata tambaya ko wata magana dangane da littafina RAWANIN ZALINCI, to kai tsaye ya mun magana, 08161390581 my contact, ni ce mai littafi, a wajena zaku sami duk wasu amsoshinku da kuke da buƙata. And lastly duk wanda labarin RAWANIN ZALINCI ta taɓo yarensu, al'adarsu, da sauransu, to ya mun afuwa, akasi ne*
E____________5🔥
Ganin lodin magunguna ne a ciki yasa Kamran ɗin ya miƙe tsaye dan ya je ya samowa maman twins ɗin abin da zata ci, saboda ko ba'a gaya mashi ba yasan tana jin yunwa sosai.
Waje ya nufa. Da kallo ta bishi, tana son ta yi mashi magana, amma ba hali, dan bata da bakin iya yin magana, sai kawai ta bishi da idanu har ya kurewa ganinta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin nan ta dawo da kallonta a kan baby's ɗin nata, har cikin ranta take jin tsananin kaunar yaran nan, tana kuma godewa Allah dayasa ƴaƴa mata ta haifa, da alama ta fi buƙatar mata sosai.
Shi kuwa Kamran, yana fita gida ya koma, ya yi sa'a Mamma tana wanka, a hankali ya lallaɓa ya shiga cikin wajen da take girki, shi kuma Rocky yana tsaye a waje yana jiransa, dan ba zai iya shiga cikin ƙogon ba, kofar ta yi mashi kaɗan, idan baku manta ba dama na gaya maku kofar karama ce sosai, bazaku haɗa jikin mutun da Damusa ba, shi Kamran zai iya shiga, amma Rocky ba zai iya ba.
Kayan cima da mamma ta girma lodi ya ɗebo a cikin kwaninan cin abincin nasu, ya haɗa duk abin da yake ganin ya dace mashi, cikin sauri ya ɗauka ya nufi waje.
Kai tsaye wajen maman twins ya koma. Mamma kuwa, tana fitowa daga wanka ta fahimci ya shigo cikin ƙogon, sahun kafarsa ta gani, kada ku manta gari ne na damina.
Shiru ta yi tana mamakin yadda aka yi yau Kamran ya shigo cikin sanɗa ya kuma sake fita, abin ya bata mamaki, tunani take yi a kan anya kuwa ba zata bi bayansa dan taga me yake yi ba?.
Tunawa da abin da ya faru a tsakaninsu ɗazun na ya ce mata ta taimaki wata mata ta ce ahir ba zata taimaka ba, tuna hakan yasa ta girgiza kai tana mai ciza laɓɓanta, alamar abin bai yi mata daɗi ba. Hakiƙa Mamma tana da wata ɓoyayyiyar baiwa, domin rashin tsoron nan nata da wannan uban jarumtar tata dole akwai ayar tambaya, tabbas ana samun mata marasa tsoro, amma kamar Mamma haka dole a dasa mata ayar tambaya, ita ɗin ba mace bace kamar sauran mata, akwai dai wata a ƙasa, lokaci shi ne alkalin komai.
Cikin ɗakin maman twins ya sake komawa, a kusa da ita ya zauna tare da ajiye mata kayan abincin. Buɗe kwano ɗaya ya yi, wani irin gasasshen nama ne mai matukar kyau a ido, ga kamshi da yake tashi, namar shaniyar daji ce, da alama Mamma bata jima da gama kasawa ba, dan akwai ɗumi a jikinta sosai, ta sha kayan kamshi irinsu curry leaf da sauransu, duk wanda ya ga namar nan sai yawunsa ta tsinke.
Ita kanta maman twins sai da ta ji yawunta ya tsinke da ganin namar, sai dai bata jin kamar zata iya cin wani abin, bakin ta babu ɗanɗano ko kaɗan.
Cikin harshen turanci ya sanar da ita cewa ga abinci ya kawo mata ta ci mana.
Da kallo kawai ta bishi shi da abincin nasa ba tare da ta motsa koda laɓɓan bakinta ba.
Ganin sai kallonsa take yi taki ta yi magana ne yasa ya miƙe tsaye yana gaya mata zai tafi, amma zai dawo anjuma da yamma can.
Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar to ta ji.
Daga haka bai sake yin magana ba yasa kai ya fice abinsa.
Yana fita Rocky ya rufa mashi baya, gida suka nufa, dan ya san in dai Mamma ta fito daga wanka sai ta fahimci ya shigo cikin wannan ƙogon, zata gane sarai, hakan yasa ya yi saurin komawa, saboda kada ta biyo bayansa, ƙarami ne daga cikin aikinta ta biyo shi ta ce bari ta je taga me yake yi, ba yau bane farau wajen biyo bayansa da take yi idan ya fita, in kuma ta zo ta tarar da ga abin da yake yi na taimako, to wlh suna ina samun gagarumin matsala a tsakaninsu, kamar yadda ta tsani ranar mutuwarta, haka ta tsani ta ga Kamran ya raɓi wasu, ko kuma wasu sun raɓesu, shiyasa bata son ya fita, bata kauna ko kaɗan, ita ko maharban da suke wucewa time to time ma sam bata son Kamran ɗin ya ce masu ko sannu. To fah, Mamman akwai matsala babba in kuwa haka ne, da alama dai akwai wani gagarumin al'amari dan gane dake a ƙasa.
Ni kam ina da tambaya sosai a kan Mamma gaskiya, lamarinta akwai ban mamaki, nasan kuma my people kuna da tambayoyi a kanta dayawa, to ku adana tambayoyinku, lokaci zai bamu amsoshinmu.
Yana komawa ya wuce cikin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 75