Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da maman Zee uppan ba, ko kallon in da take ma bai yi ba. A ɗari maman Zainab ta sha gabansa tana faɗin. "Kada ka haɗa wannan aure, zaka yi danasani". Wani irin mari ya zabga mata wai dan ta sha gabansa, rai a ɓace ya daka mata tsawa ta bashi hanya ya wuce. Ɓacin rai iya ɓacin rai yau ranta ya ɓaci, dama ga baƙincikin tafiyar Sadiq, sannan ga bakincikin da ya ƙunsa mata da safe na sanyata ta yi girki da ya yi, ga na jiya da daddare, sai abin ya haɗu ya yi mata yawa, yanzu kuma ga marin da ya dalla mata, sannan ga future yarta da yake ƙoƙarin lalatawa ta hanyar aura mata Haidar, ta ƙuduri niyar ba zata bari hakan ya faru ba!!. Hauwa dake tsaye a bayansa kaɗan ne ta ce. "Yes honey, wlh ka kyauta da ka mareta, kai sa'arta ne da zata tare maka gaba?". A wani irin kaunace maman Zainab ta ɗauketa da wani irin wawan mari wadda sai da ta ga wani haske ya gifta a gabanta idanunta, yau ɓacin rai ya rufewa mmn Zee ido. Cakumo wuyar rigarta ta yi da nufin ta yi mata ɗan iskan duka. Baban Zainab bai bari hakan ta faru ba ya fara ƙoƙarin kwatarta, wasa wasa yaga idan bai saka karfi ba ba zai iya kwatarta ba. Cikin fushi yasa kafa ya kwashe kafafunta sai ga mmn Zee a kasa rigijib, har lokacin kuma bata saki wuyar Hauwar ba, a tare suka yi ƙasar, ta ƙanƙame wuyar tata kamar mage a saman ɗan siririn reshen bishiya da idan ta sake saza faɗo, kunga dole ta ƙanƙame da kyau. To haka maman Zainab ta ƙanƙame wuyar Hauwa!. Mari baban Zainab ɗin ya sake kai mata, daga karshe ya fara haɗa mata da duka, Hauwar ma ta fara kai mata duka domin ta kwaci kanta, ta ji shaƙa shegiya, ta ji kamshin lahira, dole ta fara kai duka dan ta samu ta tsira da ranta. Dukan da baban Zainab yake kai mata ne ya yi mata tsananin zafin da yasa ta saki Hauwar, a guje ta miƙe ta nufi kitchen, sabuwar wuƙa ta ɗauko wadda ba'a taɓa amfani da shi ba, dan komai na cikin kitchen ɗin sabbi ne. Da gudun gaske ta yi kansu da wukar faɗi take yi yau ko sama zata haɗu da ƙasa sai ta kashe Hauwa, sai dai duk abin da zai faru ya faru. Sanin halinta da balai'n bakar zuciya yasa Hauwar ta ruga a guje ta yi ɗakinta. Da mahaukacin gudu ta rufa mata ba, kamar wata mahaukaciya haka maman Zainab ta zame masu, hauka take yi masu kamar wadda take da aljanun kukar buluhi a kanta. Da gudu baban Zainab ya bi bayansu. Ihu Hauwa ta fara yi tana kewaye ɗakin dan ta ceci rayuwarta, ita kuwa maman Zainab yadda kuka san bata san menene hankali bama yau, binta take yi kawai tana faɗin. "Yau idan kinga baki mutu ba to ni ce nan na mutu, shegiya mugun iri, ina kika ce ke shaiɗaniya ce? To ki tsaya dan ubanki, yau sai dai hajiya ta haifi wata Hauwar!!" Sai kewaye ɗakin suke yi, a hau gado a sauka, duk maman Zainab sai farfashe abubuwan cikin ɗakin take yi. A haka baban Zainab ya iskosu, da gudu ya yi ƙoƙarin shiga tsakaninsu dan ya rabasu, ai kuwa maman Zainab zata cakawa Hauwa wukar sai ta caka mashi a tsakiyar cikinsa wajen cibiya. Dama da Hauwa taga ya shigo sai ta tsaya a saman gadon, dan tasan zai tare mata, shi ne maman Zainab ta nufota da wukar, zata caka mata shi kuma ya shiga tsakani. Nan take jininsa ya fara yin wani irin tartsatsi kamar wutar welder, ga wukar ta cakesa har can cikinsa, gabaɗaya kaifin wukar ta lume a cikin nasa. Kan kace me ya zube ƙasa a kan gadon, jini ne yake zuwa kamar an buɗewa ruwa hanya. Wani irin mahaukacin ihu maman Zainab ɗin ta saki tare da yin kansa tana kiran sunansa, ita kuwa Hauwa waje ta nufa a guje kamar mahaukaciya tana kurma nata ihun. Da gudu su Khadija suka fito daga ɗakinsu jin irin ihun da mamansu take kurmawa, kai daga jin wannan ihu kasan bana lafiya ba, dan ihu take kurmawa tamkar maƙoshinta zai ɓalle, sai ambatar sunansa take yi. Gwanin ban tausayi shi kuma sai shure shure yake yi kamar wadda ransa yake fita, ƙafafunsa sai kaɗawa suke yi, ko'ina na jikinsa kakkarwa yake yi, harta gashin kansa sai da suka mimmiƙe tsaye, wani irin zara zaran jijiyo ne suka fito ɓaro ɓaro a hannunsa zuwa ƙafafunsa har gaban goshinsa da kuma wajen wuyarsa, wahala ta fito da su, nan take ya yi wani irin fari kamar ba shi ba, har lokacin jini na feshi kamar wutar welder, haka zalika har lokacin yana ta shure shure, idanunsa sai juyawa sama suke yi, bakin ciki sai ƙoƙarin ɓacewa yake yi, wani irin zufa dake tsastsafo mashi yana wanke ko'ina na jikinsa sai ya baka tausayi, fuskarsa kamar an watsa mashi ruwa, ya jike sharkaf da zufa, kayan jikinsa duk sun jike da zufar azaba!!. Ai Khadija na leƙowa taga abin da yake faruwa sai ta yi waje da gudu domin ta kira mutane su zo su taimaka masu kada babansu ya mutu, ita kuwa Zainab ta yi kansa da gudu tana ihu, Hauwa kuma sai Allah kaɗai yasan in da ta nufa...... Tashin sense!!! Akwai matsala fa my people's😥💔 Shin baban Zainab zai mutu ko zai rayu? Ina Hauwa tsohuwar makira? Ya makomar maman Zainab?. Zuciyata ba zata iya jurar ganin tashin hankalin da waɗan nan ahalin suke ciki ba, bari dai na leƙa Dubai muga me yake faruwa a can, my people's yanzu littafin RAWANIN ZALINCI zai fara ɗaukar 🔥 dan yafi karfin ɗaukar zafi sai dai wuta, mun dai kusa isa ga RAWANIN ZALINCI da gaske!. Second to the last page of book 1 my people's. 💘🔥 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________52🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️🌼🕊️ ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥 A karo na biyu ma wahala Leesharh ta sha sosai wajen neman mai kai abinci, sai dai kuma bata ci nasara ba har yanzu, sake dawowa cikin ɗakinta ta yi, a bakin gado ta zauna, uban tagumi ta buga tana tunanin mafita, mahaifinta ne kawai a ranta, shi kaɗai take tunawa, ta ci burin yau ta yi magana da shi. Sallamar Sharifat a cikin room ɗin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. Da kallo ta bita, ta kasa iya amsa mata sallamar, dan hankalinta baya a jikinta, duk ta yi la'asar. Kusa da ita Sharifat ta zauna, cikin sanyin murya ta ce. "Leesharh Yah Guyson ya gaya mun kin yi kuka a kan wani abin ya shiga maki cikin ido ko?". Kai ta gyaɗa mata alamar e haka ne. "Eyya sorry, amma kuma dan wani abin ya shiga cikin idanun ki hakan doesn't mean sakacin masu aiki ne, i told Yah Guyson kada ya ce laifinsu ne, kada a hukuntasu, be cause yau rana ce ta taro, baki dayawa sun zo, a wajen shige da fice ma za'a iya samin kwari ai". Da sauri ta amsa mata da. "Yauwa Sharifat, even me abin da na gani kenan, please ki rarrasheshi kada ya ce za'a hukunta masu aikin nan, please ya yafe masu". "Leesharh tell me the truth, what's wrong with you? I already saw many problems in your eyes, so please feel free and tell me!". Tsuru tsuru ta yi da idanu, yanzu me zata ce da Sharifat? Ta tambayi kanta da kanta. "Leesharh from which country you came here?". Ta sake jefa mata tambaya, Sharifat tana zargin ko Leesharh tana kewar iyayenta ne yasa take shiga damuwa haka, kamar dai yadda Guyson ya yi hasashe ɗazun, suna ganin yarintarta sosai, suna ganin bata kai a rabata da iyayenta ba, shiyasa suke yawan tambayarta ko tana kewar iyayenta ne, basu ma san ita Leesharh ai ta jima rabonta da iyayenta ba, idan da sabo yanzu ta saba da kaɗaicinsu. "Am from Nigeria". Ta bata amsa a takaice, ta yi maganar kuma kanta na'a ƙasa tana kallon ƴatsun hannunta. "Do you mean Nigeria African?". Ta faɗa tana zaro idanu alamar mamaki. Kai ta gyaɗa mata alamar tabbatarwa daga Nigeria take. "From Nigeria you came here because of work? Kai dole ki yi missing na parents naki, dole ki shiga damuwa, but why your parents zasu yarda su barki ki zo nan aiki? Su ba zasu ji kewarki bane? And su basu ga akwai nisa bane?". Tana maganar still mamaki ne sosai a saman face ɗinta. Shiru ta ɗan yi mata, kamar zata fashe da kuka take ji, zuciyarta na yi mata zafi, Sharifat ta taɓo mata in da yake yi mata kaikayi, ta tuna mata da iyayenta, duk sai ta ji wani irin. "Sorry ko Leesharh, dole ki rinƙa kuka na kewar parents ɗinki, in saya maki waya ki rinƙa magana da su dan ki rage damuwa da kewa?". Sai a lokacin ta zaro nata idanunta da suka girmewa na Sharifat a girma, idan ta zarosu kamar ka ruga a guje. Ko me ta tuna sai kuma ta ɗan yi ƙasa da kai. "Leesharh meyasameki kuma? Is there any problem again?". Kai ta girgiza alama a'a babu komai. "Leesharh talk to me now! should I buy phone for you? Saboda ki rinƙa kiran parents ɗinki, I don't want to see you always crying and worried". A takaice Leesharh ta ce mata. "I don't have anyone in my life, I don't have a mother and i don't have a father, they're not alive, they're all dead". Ta faɗa kamar zata yi kuka, kuma ta gaya mata hakan domin Sharifat ɗin ta rabu da ita da zancen saya mata wayar nan, kada ta zo ta saya mata waya hakan ya zame wa babanta babbar baraza, dan masu nikaf basu bata damar yin amfani da wata waya ba bayan wanda suka bata, shi ma kunji sun gargaɗeta a kan kada ta kuskura ta kira kowa da shi, so hakan yasa ta ce bata da har da uba, ni da ku mun san iya mamanta ce kawai bata raye, amma ta haɗa harda babanta dan tsira daga wajen Sharifat kada ta saya mata waya. Tasan cewa duk abin da zata aikata a kan mahaifinta masu nikaf zasu ɗauki fansa, idan ta yi kuskure babanta ne zai ji a jikinsa! Hakan yasa take taka tsantsan sosai!. Wani irin mugun tausayinta ne ya kama Sharifat ɗin na jin cewa bata da iyaye, Allah sarki duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ji ta yi zata yi ƙoƙari ta ɗauketa kamar yar uwarta dan ta rage mata raɗaɗin rashin iyaye, da yake ita da Guyson akwaisu da zuciyar zinari na tausayi sosai, ga hakuri kamar damo, basu da faɗa kuma basu son hayaniya, kowa ya zauna da su sai ya ji yana tsananin kaunarsu, saboda kyawawan halayensu. Ɗan matsowa ta yi ta rungumeta tana yi mata sannu a kan rashin iyaye. "As from today i am your sister kin ji? Sorry ko?". Ta faɗa tana mai kara jin tausayinta sosai. Ita ma Leesharh ɗin duk jikinta ya yi sanyi, tana jin kaunar Sharifat ɗin tamkar ƴar uwarta na jini, saboda kauna da ta nuna ma, duk sai ta ji bai kamata ace ta yi abu komai ƙanƙantarsa dan ta cutar da bayin Allah nan ba, ita tama rasa a wani matsayi zata ajiye Sharifat da Guyson, babu ruwansu da girman kai, mahaifinsu yana da murya mai karfin faɗa aji kuma dole ayi abin da ya ce a faɗin ƙasar, ga ɗimbin dukiya da shi kansa bai san adadinsu, ga matsayi a siyasance, sannan ga matsayi a sarauce, ga tarin masu kaki kala kala a ƙarƙashinsa, duk wata kaki a faɗin ƙasar bata isa ta motsa ba ba tare da izininsa ba, karfin iko gare shi ba kaɗan ba, amma su Sharifat duk basu ɗauki hakan a bakin komai ba, abin duniya bata damesu ba, basu ɗaurawa kansu girman kai ba, Guyson kam ma ai shi ta ko'ina ma jinin mulki ne yake gudana a jikinsa, ta sama da ta ƙasa, amma babu ruwansa da girman kai ko kyamar talaka, yana son kowa da zuciya ɗaya. A can wajen walima kuwa. Tun da suka je wajen Guyson yake ta ƙoƙarin dannar twins Obaid and Omaid, shi Omaid ma ya hakura ya barwa cikinsa abin da yake tunani dan gane da Leesharh, dama shi kun san ya iya takunsa. Obaid kuwa sarkin bakar zuciya, sai cika yake yana batsewa, shi lallai lallai dole sai Guyson ya yarda Leesharh criminal ce, har da wani cewa su basa hasashen abu kuma ya zama karya. Shi kuma Guyson ya ce sam ba zai yarda a kan ita mai laifi bace kuma abin zargi, saboda shi baiga laifin da ta yi masu ba, kuma shi ba zai yarda ya zargeta ba, ya kafe masu a kan lallai ita ɗin mai gaskiya ce, sune kawai basu sonta. Tun da suka shigo wajen yayyun nasu suke yi masu kallon tuhuma except Abu Abdussalam da ya buƙaci su zo kusa da shi su zauna ya yi kewarsu, Abu Abdussalam yana bala'in kaunar Momma da King Zuhair, shiyasa yake kaunar ƴaƴan nasu. Kusa da shi suka zauna cikin manya manyan ministoci da ƴan majalisu, Guyson yana ta gefen damansa, su kuma ta gefen hagu suka zauna, basu taɓa raba wajen zama, duk in da ka gansu a tare suke, kai su basu raba komai ma ba wajen zama kawai ba, in dai ba zaka basu abu a tare ba gara ma ka barshi, dan ɗaya ba zai karɓa ya bar ɗaya ba. Abbie ne ya ce. "Guyson where's Ramish?" Ya yi maganar cikin kwararriyar laraɓcinsa, yare biyu Abu Abdussalam yake ji a duniya, daga turanci sai larabci. Cikin sanyin murya haɗe da nutsuwa ya ce. "Abbie wai kansa na yi mashi ciwo, he can't come here, dan kara mashi ciwon kai za'ayi da surutu, so ya kwanta". Kallon Bilal Abbie ya yi. "Jeka duba mun shi, Dr Raj ka kula da lafiyarsa sosai". Da okey suka amsa mashi kafin su miƙe su nufi hanyar fita. Tun da suka miƙe maza da mata kallonsu suke yi, ba dai haɗuwa ba kam, sun fito ba'a magana, kyau iya kyau. Shi kuwa Rizwan ya kafa kansa a kan waya yana chatting da Chuchu, sai zuba mata kalaman soyayya yake yi, ita kuma sai narke mashi take yi!. Bayan anci an sha, kowa yasan da cewa lallai yau Abu Abdussalam empire ya zo, biki aka yi na girma da girmamawa, rakuma har biyar ma'aikata suka gasa, nama kamar hauka, da nama na magana yau da ya yi a gidan Abu Abdussalam, drinks da ruwa suma da sai sun yi magana, abinci kala kala, a yau ba wata ma'aikaciya ko ma'aikacin masu yin girki waɗan da basu ji a jikinsu ba, yau sun sha aiki sun kuma wahala, jiki duk ya yi tsami. Rera karatun Alkur'ani mai girma manyan baki suka fara yi, kun san fa larabawa akwai iya rera ƙira'a, Abu Abdussalam ne ya buƙaci da a yi karatu sosai kafin a tashi daga taron. Duk wanda zai yi karatu saman stage yake hawa, abin ya yi tsari sosai ya kuma bada ma'ana, sannan ya ƙayatar matuƙa. Lokacin da Guyson ya fara rera kira'arsa sai da gabaɗaya jama'ar cikin hall ɗin suka bar abin da suke yi suka zuba mashi idanu, tsantsar madarar kyau suke gani, ga zakin murya kamar me, karatu yake rerawa cikin kwanciyar hankali cikin suratul Yusuf, yadda yake fitar da kowani baki, kowani gunna sala sala yake fitar da ita, baya mance wasali ko yaya, dai'dai yake zayyanosu ga nutsuwa matuƙa a tattare da shi sai ya tafi da imaninka, dama ga yaran Momma da bala'in farin jini kamar su suka bawa kansu. Wasu kyan da Allah ya yi mashi suke gani, wasu kuma kyakkyawan arab hairnsa suke gani, dan fa kunsan gwani ne wajen iya gyaran gashi, ga shi ɗan wanka, wasu daga cikinsu kuma wankarsa suke kallo, wasu zazzaƙar voice ɗinsa ne ya tafi da imaninsa, wasu kuma yadda yake rera karatun cikin nutsuwa ne ya tafi da imaninsu, yaro mai farinjini, dayawa daga cikin manyan bakin nan sun kwaɗaitu da son samu ɗa kamar sa, ji suke yi dama ace ɗansu ne. A hankali zazzaƙar muryarsa ta fara rikiɗewa daga yadda ya faro karatun cikin zaki da nutsuwa zuwa muryar mai kuka, da kaɗan da kaɗan fararen idanunsa suka fara rikiɗewa izuwa ja saboda kukan, siraran hawaye ne suka fara bin kyakkyawar farar kumarunsa, ba komai ya ja hakan ba kuma face sanin fassarar surar da yake karantawa da ya yi, zuciyarsa tana kara jinjinawa girman Allah, jikinsa har tsuma yake yi yana kerma a lokacin da yake karanta gudurorin Ubangiji da ya yi ta yi wa annabi Yusuf. Kukansa kara tsananta ya yi lokacin da ya zo in da aka raba annabi Yusuf da mahaifinsa, sanin fasarar surar tasa shi kuka sosai da yake karantota. Guyson bai kai 17 years ba a duniya, amma Allah ya bashi baiwa ta ilimi fiye da tunaninku, ba boko ba ba Arabic ba, dukka akwai tarin ilimin a kansa, shiyasa yake da saukin kai sosai, saboda ya san girman Allah sosai, yasan duniya ba'a bakin komai take ba, a wajen Allah duniya kamar wuni guda ce. A ƴan shekarun nan nasa ya san farrasarar rabi da kwana na surorin dake cikin Alqur'ani mai girma, kun san larabawa fa ba baya ba wajen iya karatu, basu wasa. A bangaren littafan addini ɗan tahaliƙin nan ba'a magana, yasan dayawa daga ciki, ya haddace dayawa, kuma har yanzu bincike yake cigaba da yi yana kara nutsawa cikin karatun addini, yana ta ƙoƙarin ya haddace fasarar Alqur'ani gabaɗaya, ɓangaren bokon ma baya wasa, yanzu kunga ya kammala secondarynsa, jam zai rubuta kai tsaye ya shiga babban makaranta da kananun shekarunsa, shiyasa ƴan uwansa dukka suke sonsa, saboda jajircewarsa wajen neman ilimi. Su Omaid kuwa, akwai tarin ilimin suma, amma sai shegen shakiyanci, iyashege, da tarin rashin ji, ga ɗan banzan shiga rai garesu kamar me, ga farin jini kamar su suka yi wa kansu, amma duk da hakan baya hanasu karatu, duk iskancin da suke yi basa wasa da karatu, dan idan suka kuskura suka yi wasa wlh zasu kwashi kashinsu a hannun idan su Ramish suka riƙe su, shiyasa kome zasu yi banda wasa da karatu kam. Kai in takaice maku labari gabaɗaya jinin King Zuhair babu jahili, sai dai ilimin wani ya fi na wani, wani ya fi wani kaifin basira, ga tafasasshen jini, dagiya da kafiya, jarumta da jajircewa, babu jahili sam sam! Suna da dagiya wajen neman ilimin boko dana addini basa wasa!. Kukan Guyson a cikin hall ɗin nan yasa dayawan mutane kuka, masu raunin zuciya sun taya shi kuka, shi kansa Abu Abdussalam sai da idanunsa suka ɗan yi ja. Kasancewar a nutse yake karatun sai ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya kammala. Yana kammalawa Abbien nasu ya miƙe ya rungumo shi tare da fara goge mashi hawaye, kabbara jama'a suka fara yi suna zuba mashi ruwan albarka sosai da sosai. Omaid ne ya miƙe ya fara rera nasa kira'ar cikin suratul ma'ida, dama kun san su sarakan shiga rai ne, ga farinjini, nan take jama'a suka fara binsa dana mujiya, sai santin kyansa da muryarsa kusan irin na Guyson suke yi. Shi kam Omaid saboda dakiya da taurin zuciya ko ɗigon hawaye babu a idonsa, sarai kuma yasan fassarar surar da yake karantawar, amma akwai taurin zuciya, ko alamar hawaye ma babu a idanunsa, idanun suna bushe karau yake rera karatunsa har ya kammala, har lokacin kuma Abu Abdussalam bai saki Guyson ba, yana bala'in kaunarsa, duk da sun koma sun zauna yana ƙanƙame da hannunsa suna sauraron kira'ar Omaid ɗin. Bayan ya kammala Obaid ma ya miƙe ya fara rero nasa cikin suratul Maryam. A wannan gaɓar ma sai da Guyson ya yi hawaye, saboda yasan fassararta, sosai kuma ya kara jin tsoron Allah matuƙa, sai goge mashi hawaye Abu Abdussalam yake yi. Shi kuwa Obaid da ya karanta surar ma idanunsa a bushe karau, Guyson sai sharar kwallah yake yi shi da ba shi yake karatun ba, mai karatun kuwa idanu a bushe karau, ga gashin idanun nasa zara zara a tsaitsaye na rashin kunya da rashin jin magana, kowa ya ga idanun Obaid da Omaid ya san akwai tarin rashin tsoro da rashin kunya game da mugunta a cikinsu, basu tsoron a mutu. Bayan Obaid ya kammala karatun ne ƴaƴan manyan baki suka fara rero nasu. A can cikin gida kuwa, Leesharh ta saki jiki sosai suna ta hira da Sharifat. "Leesharh anata gudanar da abubuwa a wajen walima ni kuma ina nan a tare da ke, ki tashi mu je can mana? Kin ga ai sai mu yi hira a can ko?". Cewar Sharifat. Make mata kafaɗa ta yi. "A'a Aunty Sharifat ni bana son zuwa, ban son shiga cikin mutane sosai, ki barni a nan kawai". Gyara zama ta yi. "To shikenan Leesharh mu zauna tare a nan ɗin kawai ko? Mu cigaba da hirarmu ni ma na fasa zuwa duk da nasan Yah Guyson zai damu idan bai ganni ba". Da sauri ta girgiza mata kai tana faɗin. "A'a Aunty Sharifat, kada ki sa ya ji babu daɗi, idan kin san zasu damu da rashinki a wajen kawai ki tafi". Gyarawa ta yi ta kwanta a saman gadon tare da miƙe kafafunta. "Kawai mu cigaba da yin hirarmu Leesharh ba zasu damu ba, ai na gayawa Yah Guyson bari na je wajen ki tun lokacin da ya gaya mun kin yi kuka". Okey ta amsa mata da shi haka suka cigaba da yin hirar duniya cikin nishaɗi abinsu. Sun shagala da hirar duniya mai daɗi Sharifat ta dubi ɗan siririn diamond watch dake manne a hannunta. "Kai Leesharh karfe 7 ta yi bamu yi sallar mangariba ba! Sannan karfe 7: 30 dai'dai zan kaiwa Yah Ramish abincinsa da cappuccino, kin san shi bai yarda da kowa ba, bai yarda da ƴan aikin gidan nan ba, abincin da zai ci ma wanda yake girka mashi na musamman ne, bai yarda wata ko wani mai aiki ya keto cikin ɗakinsa ya kawo mashi abinci ba, garama idan da rana ne yana zaune a babban parlourn haka zai iya cewa a kawo mashi, nan ma sai idan yasan na tafi school ko bana kusa ne zai yarda wata ta kawo mashi abinci, duk wata ƴar aiki da kika gani a cikin gidan nan sai da Abbie ya aminta da ita kafin ta fara aiki, amma shi ya Ramish bai aminta da kowa ba sai ni da su Yah Rizwan, ke ni ina ganin ma kamar Ummie ma bai yarda da ita ba fa, dan naga baya wani sakin jiki da ita kamar yadda su Yah Rizwan suke yi". Shiru Leesharh ta yi tana sauraron tun da ta fara maganar, wani irin sanyi ta ji yana ratsa mata zuciya, tsuntsu daga sama gasasshe! Ta sha wahala wajen neman mai kai mashi abinci cikin room ɗinsa, ashe dai tana tare da ita bata sani ba, wannan shi ne tsuntsu daga sama gasashe! Sosai abin ya yi mata mugun daɗi, har wani sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke. "Leesharh tunanin me kike yi?". Ta yi maganar tare da ɗan taɓata. Ƴar razana ta yi tare da cewa. "Babu komai, amma meyasa Yah Ramish ɗin

Chapter 73 of 75