tsawon shekara ɗaya na zaman da ta yi a gidan AAJ wlh sai dai suga hakwaranta idan tana magana ko tana yin brush, amma ba dai dariya ba, sam walwala da farinciki baya a saman fuskar yarinyar na, kullum cikin kuncin zuciya take, daga tagumi sai kwanciyar rigingine, abinci ma wani lokaci sau ɗaya take ci a rana, na safe kawai, bata wani damuwa da cin abinci, sai yawan tunani kamar me.
Ita kuwa Jasrah ta ce tun da nan da shekara guda za'a kasheta kamar yadda doka ta yanke mata, gara mata ta ci abincinta ta yi duk abinda tasan zata yi, dan tasan dokar nan ba zai kau daga kanta ba, sai dai wani ikon Allah, amma babu wanda ya isa ya sanya a fasa kasheta, kisa ba fashi, so dan haka gara mata ma ta saki ranta ta samu ta yi bankwana da duniya da kyau da kyau.
Ita kam Leesharh saura mata shekaru uku ta kai munzalin ɗaukar hukuncin da aka yanke mata........ Hmmmmm ni ko na ce hmmmmm.
"Ni kam a duniya waye nake da shi da zan yi tunaninsa da ya wuce mamata?". Leesharh ta bata amsa tana mai dawo da kallonta a kanta su fuskanci juna kenan.
"To amma Leesharh where's your father? And you Said you're from Africa, so what brought you here Dubai?". Jasrah ta jefa mata tambaya.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin yin magana Aaradiya dake kwance a saman bed ɗinta ta rigata da cewa. "Shima baban naki kashe shi kika yi ko? Dan naga ke horuwa ce, tun da kika zo gidan nan ko hakwaranki ba'a gani a waje, ke anya ma ba mayya ba ce Leesharh? Dan naga duk gidan kin fi kowa manya manyan idanu kamar ball".
Cike da shakiyanci da isgilanci sosai Aaradiya ta yi maganar.
Ɗayar yarinyar da take kasan bed ɗin Aaradiyar ce mai suna Sarah ta ce. "Kuma fa Aaradiya kina da gaskiya, kila mayya ce, ta kashe babanta, yanzu kuma ta kashe mamanta, muma fa kada ta kashe mu".
Ta kai karshen maganar tana zaro idanu.
A ɗan fusace Jasrah ta ce. "Ko ta kashe ku ko bata kashe ku ba nan da lokaci ƙalilan kasheku za'ayi, kuma idan ma ta kashe ku a yanzu ai saukaka maku zata yi".
Jasrah damo sarkin hakuri, bata magana a kan kome za'ayi mata, amma bata son taga irin cin fuskar da suke yi wa Leesharh a gidan, dan ita ce kawai aka kawo wadda ta kashe mahaifiyarta da hannunta, hakan yasa yaran da kansu suke tsangwamanta, yara ma kenan sun san daɗin uwa bare kuma manya, shiyasa sam sam Leesharh bata fita waje, dan idan ta fita kowace yarinya da kalar zagin da take yi mata, ƴan manyan cikinsu ma sai ku ji suna cewa Allah ya tsine maki la'ananniya, la'ananniya ce kawai zata kashe uwar da ta yi silar zuwanta duniya.
Wannan dalilin yasa bata fita, ta gwammaci ta yi ta ƙunsuwa a cikin ɗaki kamar daddawa, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa kullum take cikin ƙuncin zuciya da ɓacin rai tare da tunani. Ga shi kuma taki buɗe baki ta gayawa kowa ya aka yi ta kashe mahaifiyarta da kanta, ko da jami'ai suka tambayeta ma iya e kawai ta amsa masu da shi, anyi anyi ta yi magana ta bada labarin yadda aka yi, amma ina taki yarda ta buɗe baki.
"Ai munsan zaku iya kashe mu ba sai kin gaya mana ba, ke da kika kashe Ameer bai yi maki komai ba".
Cewar Sarah kenan.
Shiru Jasrah ta yi bata sake bi ta kansu ba, dan in ta biye masu faɗa zasu yi sosai, kuma dukkansu zata girme masu da shekara guda, amma saboda su basu da kirki sun rainata, sun mayar da ita kamar wata kanwarsu suna yi mata cin kashi.
"Leesharh amsa me where's your dad?". Cewar Jasrah.
Nisawa Leesharh ta yi tare da ƙoƙarin fara yin magana kenan wata ganduroba mace ta shigo cikin ɗakin nasu bakinta a ɗauke da siririn sallama, tana sanye cikin uniform ɗinsu na aiki.
"Who's Leesharh?".
Shi ne abin da ta faɗa tana mai binsu da kallo.
Miƙewa tsaye Leesharh ɗin ta yi tana faɗin gata nan.
Wucewa matar ta yi ta fita tare da cewa. "Follow me".
Da sauri Jasrah ta miƙe tana faɗin. "Ina zaku kaita?".
Abin da kun rigada kun sani ne ba amsa mata zasu yi ba, dan ba sha'aninta bane su ɗin, dan haka sai ta yi wucewarta ba tare da ta sake juyowa ta kallesu bama. Leesharh kuwa bata da zaɓin da ya wuce ta bi bayan matar.
Komawa Jasrah ta yi ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin to me zasu yi wa Leesharh da suka wani zo suka kirata? Ko dai wani nata ne ya kawo mata ziraya? Ko kuma wani aikin zasu sakata? Ka dai za'a canza mata ɗaki a rabasu ne?. Tunani dai kala kala take ta yi a wajen.
Da kallon banza Sahra and Aaradiya suka bita da shi tare da binsu da addu'ar Allah yasa a kashe Leesharh ɗin ma a yau kowa ya huta, yadda kuka san a kansu Leesharh ɗin nan take zaune, sam basu kaunarta.
Kai tsaye office na shugaban gandurobobi wannan mata ta wuce da Leesharh dake ta faman jan kafa kamar zata faɗi a ƙasa, sam babu kuzari a jikinta, da alama bata ci abincin rana ba yau ma, dik a galabaice take baiwar Allah. Da alama a baya Leesharh tana da ɗan ƙiba kaɗan, saboda yanayin shape ɗin jikinta ya nuna rama ta yi, da ta fi hakan cikar bom bom and hips.
Shugaban gandurobobin tana a zaune a saman kujararta, ta yi crossing na leg's ɗinta, sanyin Ac na dukanta, office ɗin nata ya kawatu iya ƙawatuwa, tana sanye cikin haɗaɗen jallabiyarta launin sky blue a jikinta, yau bata sanya uniform ba, ta sanya wani ɗan ƙaramin please call me hijab da bai wuce kirjinta ba, ƴar siririya da ita, bata da ƙiba ko kaɗan, amma akwai kyau sosai da sosai, balarabiya ce ta usli, ga manya manyan idanu farare tas. Sai uban tulin takardu a gabanta kamar wata mai MD na Company, idanunta sanye suke da wani haɗaɗɗen farin glass mai ɗan girma, sai kamshi take zubawa ita kanta, ga kuma kamshin da office ɗin yake zubawa shi ma.
Wata macece zaune a zaman kujerar zaman baki idan suka zo a cikin office ɗin, daga sama har ƙasa idan ka cire nikaf da yake a fuskarta sanye wannan mata take da fararen kaya, nikaf ɗinta ne kawai baki, amma komai da ta sanya a jikinta fari ne tas, harta luxury hand fashion bag ɗinta ma fari ne, ta yi rolling na veil a kanta, ƴar dai'dai da ita, ba zaka kirata da mai ƙiba ba, haka zalika ba zaka kirata da siririya ba, ta dai ci ta ƙoshi, babu yunwa a tattare da ita, da alama kuma daloli bama nerori ba daloli sun yi mata mugun jiƙo, dan babu alamar gurbin talauci a tattare da ita, diamond ring da yake ɗan ƙaramin yatsan hannunta ma kawai ya haura 10 million, idanunta suna a sanye da black glass kamar wata mara gaskiya, ga nikaf ga kuma glass.
A ƙasa saman carpet Leesharh ta zo ta zauna a gaban ogar tasu, ita kuma wancan gandurobar da ta je ta zo da ita juyawa ta yi ta fita bayan ta isar da saƙon ga Leesharh nan ta kawota.
Cikin girmamawa da muryarta da sam kwata kwata bata fita sosai kamar wata mai koyon magana Leesharh ta ce. "Ganin nan".
Cikin harshen larabci ta yi maganar.
Kallon wannan mata dake zaune a saman kujara ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya shugaban gandurobobin ta yi, da hannu ta nunawa Leesharh wannan mata tana faɗin. "Bani ne nake kiranki ba, ga mai buƙatarki nan".
A hanzarce Leesharh ta juyo da waɗan nan dara daran idanun nata a kan matar, tun shigowarta bata kalli matar ba sai yanzu da aka nuna mata ita, hankalinta na'a kan shugaban gandurobobin ne kawai baiwar Allah.
Cikin girmamawa ta sake ce da wannan mata gani nan Aunty.
Kallon shugaban gandurobobin wannan matar ta yi, ɗan guntun numfashi ta ja tare da saukewa a hankali kafin ta ɗan ja ƴan mintoci da a kallah zasu kai biyu ba tare da ta ce komai ba, sannan calmly ta fara magana cikin kwararriyar laraɓcinta da zazzaƙar muryarta mai daɗin sauraro.
"Bismillah Abida kina iya bamu waje a yanzu".
Ta faɗa cikin sanyin murya, sai dai da alama akwai isa sosai da ji da kai a tattare da muryar tata.
Miƙewa shugaban gandurobobin ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba, ta nufi out door, sai dai da alama ranta bai so fitar ba, kawai an fi karfin ta ne.
Bayan fitarta da kamar minti biyar haka, suna zaune shiru, wannan mata sai karewa Leesharh kallo take yi ta cikin black glass ɗinta, ita kuma Leesharh ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da hannunta. Tana son ta ɗago kai ta saci kallon wannan mata, amma kuma tana tsoron su haɗa ido ko kuma ta ganta, hakan yasa ta sunkuyar da kan nata shiru kawai.
"Shin kina son fita daga cikin wannan bakin gida da zuwansa ba alkhari bane Leesharh?".
Ta tambayeta cike da fargabar amsar da zata bata, tana tsoron Leesharh ɗin ta ce bata sha'awar fita daga gidan, hakan zai sa buƙatarta ba zai biya ba......... Ko wani buƙata take da shi a kan Leesharh? Muje dai zuwa.🤔😥
Tamkar saukar aradu haka Leesharh ta ji sautin zazzaƙar voice ɗin wannan mata ya daki dodon kunnuwanta.
A wani irin hanzarce ta fara gyaɗa mata kai in doubling. Baiwar Allah da alama bata da wani burin da ya wuce ta fita daga cikin wannan gida na AAJ........ Ba dolema ta so fita ba ko dan yadda sauran yaran suke tsangwamanta suka takura mata.
Wani irin cool ajiyar zuciya wannan mata ta sauke, ta cikin nikaf ɗinta ta saki wani irin shu'umin murmushi wadda fassara shi zai yi matukar wahala, da alama haƙarta zai cinma ruwa.
"Very good Leesharh, na ji matuƙar daɗi da ya kasance kina son fita daga cikin wannan gida".
Ta faɗa muryarta cike da tsantsar farinciki saɓanin ɗazun da magana kawai take yi babu walwala a tattare da ita.
"Aunty ina son na fita daga nan sosai, ko dan saboda tsangwamanta da suke yi suna kyarata, ga zagina da suke yi, kuma bana son a kasheni a nan, ina son na koma kasarmu, ina son na je wajen kabarin mamata na ganta".
Ta yi maganar idanunta suna cikowa tab da kwallah, muryar Leesharh sam baya fita sosai idan zata yi magana, yadda kuka san harshenta a naɗe yake, kamar mai koyan magana, gata kyakkyawa ajin farko, amma sam bata iya yin magana ya fita, a wani daddame maganar tata yake fita, idan ba ka nutsar da hankalinka sosai ba ba zaka taɓa iya gane me take son cewa ba ko me ta ce ba.
Shiru wannan mata ta ɗan yi tana ƙoƙarin iya fahimtar me Leesharh ta faɗa, dan bata wani gane me ta ce ba bayan cewa da ta yi mamanta, iya kalmar maman kawai ta iya ji a cikin maganar nata. Da kyar ta iya fahimtar wasu daga cikin abin da Leesharh ɗin ta ce, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.
"Idan kina so yau ba sai gobe ba zan fitar dake daga cikin wannan gidan, kuma zan kai ki asibiti a gyara maki voice ɗinki, zan ƴantaki ki zama mai gata, zaki zama ƴa kamar kowa, zaki samu farinciki da jin daɗi fiye da ƴaƴan shugaban ƙasa, zaki samu rayuwa mai cike da jin daɗi, zaki ci abinci mai rai da lafiya a kullum da ko yaushe kike da buƙata, zaki kwanta a ɗaki mai Ac, zaki kwanta a katafaren bed ɗin da nasan da idanunki ma baki taɓa ganin gado irinsa ba, zaki saka suturuna na alfarma wadda ƴaƴan manya suke sakawa, ke har da gida da mota zan iya saya maki mai kyau da tsada, idan kina son yin karatu ma zaki yi, kome kike so zan yi maki amma da sharaɗi, kin amince?".
A wannan karon a hanzarce Leesharh ta ɗago da kanta, jiki na kerma ta fara gyaɗa mata kai alamar ta yarda ta amince tun ma bata ji wani irin sharaɗi bane, ita dai burinta ma kawai ta bar wannan gida, ko bara zata yi a bakin titi in dai zata bar wannan gida to zata amince da koma wani irin sharaɗi za'a sanya mata, bata damu da sai wannan mata ta bata dukka wannan daula da ta lissafa mata ba, ita dai ta fita daga gidan nan kawai.
"Good girl, wani aiki zaki yi mun, ba aiki bane mai wahala, kuma ba jimawa zaki yi kina yin aikin ba, da zarar kin yi mun shi dai'dai shikenan angama zaki sami duk waɗan nan abubuwa dana kirga, kina amincewa ko yanzu ne zaki bar wannan gida ba tare da kin kara one mins ba, amincewarki ne kawai yanzu zai fitar dake a yau ɗin nan". With full confidence matar ta yi maganar.
Shiru Leesharh ta ɗan yi, kamar zata ce wani abin, sai kuma bata yi wani tunani ba ba kuma ta ji wani irin aiki bane, idanunta ya rufe da son fita daga AAJ, hakan yasa ta gyaɗa kai alamar ta amince zata yi wannan aiki da bata san menene bane.
"Kin amince zaki yi mun wannan aiki?". Matar ta tambaya muryarta cike tab da tsantsar farinciki mai nuna alamun ta jima bata shiga farinciki irin haka ba, ga tsantsar ƙaguwa a voice ɗin nata.
Ƙara gyaɗa mata kai Leesharh ta yi alamar yes ta yarda ta amin zata yi wannan aiki da bata ji ko menene ba.
"Kin san wani irin aiki zaki yi mun ne? Bashi da wata wahala fa".
Matar ta sake faɗa cike da murna da farinciki.
Girgiza kai Leesharh ta yi alamar bata san wani aiki bane.
"Ba wani aiki mai wahala bane, so nake.............
Ko masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu, amma ku wani aiki kuke ganin wannan mata zata sanya Leesharh da har ta yi mata alƙawarin maƙudan dunbin dukiya har haka?🤔 Anya wannan mata akwai alkhari a tattare da ita kuwa?🤔 Ga shi dai ta rufe ko'ina nata ba'a iya ganin wacece!🤔 To dai shikenan su kuma nasu wasan yanzu zai fara kenan, 🥱 na yi ta nan.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/8/2024.....✍️📚🌹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________26🔥
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼
"Ba wani aiki mai wahala bane, so nake kawai ki shiga jikin wani, ina son ki shiga jikinsa ta yadda duk wani abin da yake yi zan samu labari, na sha wahala sosai kafin na samu yarinya irinki wadda take da duk wasu qualities da nake da buƙata wanda kuma nake ganin zai iya jefa Ramish a cikin tarkonmu".
Ɗan dakatawa da yin magana ta yi cike da fargabar kada Leesharh ɗin ta ce ba zata iya yin wannan aiki ba, ta kafeta da idanu ta cikin glass ɗinta tana karewa fuskarta kallo tare da karantar yanayin ta, bata san ya zata yi ba idan Leesharh ɗin ta ce ba zata iya yin wannan aiki ba.
Cike da kirsa tare da ƙoƙarin yin amfani da ƙarancin shekarun na Leesharh ɗin ta cigaba da yin magana kamar haka.
"Na san da cewa baki jin daɗin zaman wannan gida, na san da cewa kina cikin kunci da takura, na san da cewa kina cikin wahala, na san da cewa baki da burin da ya wuce ki fita daga cikin wannan gida, to dukka wannan zai faru ne kawai idan kika amince da tayi na, bafa cutar da kowa zaki yi ba"
Sake dakatawa da yin maganar ta yi tana jan numfashi tare da kara kurawa face ɗin Leesharh idanu.
Ni kuwa nace babu rami me ya kawo maganar rami? Me ya kawo zance ba cutar da kowa zata yi ba?......🤔 Anya wannan mata ta kulla gaskiya kuwa? Anya ba so take ta kai Leesharh ta barota ba? To wai waye ma shi Ramish ɗin? Kuma meyasa take son a yi mata leƙen asiri a kansa? Me suke nema daga garesa?.
"Leesharh zaki samu jin daɗin rayuwa sosai da sosai, zaki samu farinciki fiye da tunaninki, zaki sami kuɗi ki taimaki duk wanda kike so, just kawai amsa me with your full confidence that zaki iya, nasan cewa zaki iya shiyasa na zo wajenki, ban zo nan ba sai da na binciki tarihin rayuwarki, and ke ƙaramar yarinya ce, babu wanda zai yi tunanin ga abin da kika je yi a gidan, taimako fa zaki yi, wasu ne suke son cutar da shi mu kuma zamu bashi kariya ta hanyar sanin duk wani motsinsa, ta hakance kawai zamu taimakesa, kinga kema kin taimaka mashi kenan".
Cike da kwarewa a iya juyar da tunanin mutun ta yi maganar, sai dai fa tana magana ne tana fargabar amsar da Leesharh zata bata, domin ta gama saka duk wani hope ɗinta tun kafin ta zo a kan cewa lallai Leesharh zata yi mata abin da take so, amfani zata yi da karantar shekarun Leesharh, dan tasan ƙaramar yarinya kamar Leesharh babu wanda zai yi tunanin leƙen asiri ta je yi, da alama wutar ɗaukar fansa ne yake ruruwa a cikin zuciyarta, shi ne kuma take son ta yi amfani da Leesharh domin cikar burinta. Hmmmm akwai babban yaki da cakwakiya kuwa a gaba, ga shi ko face nata bata bari an sani ba, wato idan ma an kama Leesharh ita kaɗai ayi mata duk hukuncin da za'ayi mata, wannan mata bata kullah gaskiya ba, akwai babban wasa a wannan waje.
"Leesharh say something now, shin kin amince?".
Shiru ta ɗan yi kafin ta ɗago da idanunta da suke cike taf da kwallah, muryarta na rawa, da alamar tsoro sosai a saman face ɗinta, hannayenta dukka kerma suke yi, hakan zai kara tabbatar maka da tana tsorace. Magana ta fara yi cikin rawar murya ga shi dama ba fita sosai voice ɗin nata yake yi ba, sai abin ya kara kwaɓewa.
"Ni Aunty duk wata dukiya bata dameni ba, ni bana da buƙatar komai a duniyar nan da ya wuce na je naga kabarin mamata daga nan na koma ƙasarmu, ƙasarmu nake da burin na koma naje na nemo ƴan uwana da kuma mahaifina, please Aunty ki taimaka mun na koma ƙasarmu zan yi duk abin da kika ce".
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya wannan mata ta sauke da jin amsar da Leesharh ɗin ta bata, ranta ya yi haske da jin cewa Leesharh zata iya yin komai domin ta bar wannan gida ta koma kasarsu, har wani walwala ne ya bayyana a face nata, da yake tana sanye da nikaf hakan yasa ba za'a gane ba, hankalinta ya kwanta yanzu, ta samu damar da zata cinma burinta da abin da take hari a nata tunanin kenan, ko da yake bata zo wannan gidan yarin wajen Leesharh ba sai da ta shirya ta kuma san labarin Leesharh ta san da cewa zata iya aikata komai idan aka bita ta yadda ya dace, idan aka yi wasa da tunaninta, dan yarinya ce mai jajircewa a kan burinta da aikinta.
"Good Leesharh, haka ake son mutun mai zuciyar jajircewa juriya da hazaƙa, naji matuƙar daɗi da ya kasance zaki yi komai domin mahaifinki, kada ki damu kina gama aiki zan mayar dake ƙasarku ba tare da ɓata lokaci ba, ai uba ya wuce wasa Leesharh, ke ɗin yar baiwa ce Allah ya yi maki albarka".
Ɗan dakatawa da kalaman yaudarar tata ta yi tana kara kallon face ɗin Leesharhr, dan kowa yasan dai waɗan nan kalaman nata na yaudara ne, so take yi ta yi amfani da ƙarantar shekarun Leesharhr haƙanta ya cinma ruwa, daga gani bata ƙullo gaskiya ba.
Da Amin kawai Leesharh ta amsa mata ba tare da ta ɗago da kallonta ba, tunanin a ina zata yi wannan aikin kawai take yi.
"Kina jin yadda aikin zai kasance, zaki je gidan ne a matsayin ƴar aikinsu, suna da masu aiki da a kallah zasu kai mutun 50, amma dukka wannan ba damuwa bane, ni nasan ta yadda zan shigar dake gidan a matsayin mai yi masu aiki, zan saya maki sabuwar waya, ba kin iya amfani da ita ba?".
Ta dakata tana jiran amsa.
Girgiza mata kai Leesharh ta yi alamar a'a bata iya amfani da wayar ba.
"Okey wannan dukka ba matsala bane, ni zan sanya a koya maki komai, dama ba'a haka zaki je masu ba, dan su masu yi masu aiki ma sai wanda yake da degree or diploma, ba kananan kai bane suke yi masu aiki, sai na sanya an koya maki abubuwa na a kallah wata guda, kafin nan na shirya ta yadda zaki yi ki shiga gidan, babu ruwanki da kowa a cikin gidan, ko sauran ma'aikatan gidan ban yarda ki rinƙa yi masu magana ba, kada ki yarda ki sake da kowa, muna da ma'aikata a gidan da zasu kula da ke, dukkansu manyan mutane ne da ba zasu iya shiga jikin Ramish ba, shiyasa na zaɓoki, Ramish kawai zaki saka mun ido a kansa, ban ce ki kira kowa da wayar da zan baki ba, haka zalika ban ce ki bawa kowa number wayar ba, nima kuma ba zan kiraki ba, idan ina da buƙatar yin magana dake ni nasan ta in da samu haɗu mu gana, wayar da zan baki zan baki ita ce kawai dan abu biyu, na farko domin akwai abin da zan sanya a cikin wayar dan ya tayaki aikin da zaki yi domin mu kammala da wuri, na biyu kuma wani lokaci ki rinƙa ɗauka mun Ramish ɗin a video idan suna irin tattaunawa mai mahimmancin nan, kuma da zarar kin turo mun video ki goge shi a wayar, ko da yake ma time to time zan rinƙa canza maki wayar, wannan ba abin damuwa bane na san ta yadda zan shirya komai".
Ɗan dagatawa da maganar ta yi tana jiran ta ji me Leesharh ɗin zata ce.
"Aunty to ni da nake matsayin ƴar aiki ya za'ayi na iya sanin lokacin da suke tattaunawa mai mahimmancin? Kuma ai idan zasu yi tattaunawa ba'a ko'ina zasu yi ba ko? In dai haka ne ya za'ayi na san in da zasu yi tattaunawar?".
Ɗan ƙaramin tsaki ta ja kafin ta cigaba da cewa. "Aikin da zan samo maki ba kamar sauran ƴan aikin gidan bane, an gaya maki a banza na zaɓeki ne? Akwai dalilan da yasa na zaɓeki wadda ban gaya maki ba, kina da kyau, kina da diri da sai an tara mata 100 ba'a sami goma masu irin dirinki ba, da wannan zamu yi amfani mu sanya shi ya saki jiki da ke ko kuma ku sami kusanci sosai har haƙanmu ya cinma ruwa".
Shiru Leesharh ta ɗanyi, abinku da kananan shekaru, sai bata kawo komai a ranta ba, bata ma san waye zata yi wa wannan shisshigin da leƙen asirin ba, ita dai tun da ance mata taimako zata yi ai shikenan, bata san me za'ayi mashi da ake buƙatar sanin duk wani halin da yake a ciki ba, ita dai burinta na son komawa ƙasarsu ya rufe mata idanu da har take jin cewa tabbas zata iya yin komai a kan hakan.... Babbar magana, in kuwa haka ne akwai kura ba kaɗan ba.
"Tunanin me kike yi Leesharh?".
Ta faɗa a ɗan tsorace, tana tsoron kada Leesharh ta ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 75