ne ya rage a kammala ginin, amma duk da haka akwai cin kuɗi, duk basu ga hakan ba su kam, dan rashin adalci irin nasu.
A yau ne Maman Zainab da Aunty Hauwa suka shirya zuwa wajen malamin Aunty Hauwa, zasu je ne kuma da nufi ya yi masu aiki guda uku, na farko hana karin auren baban Zainab, na biyu hana auren Haidar da Khadija, na uku a saka dangin baban Zainab su sota sosai sosai kamar su haɗiyeta, wannan shi ne aikin da za'ayi masu.
Yau dai Maman Zainab ta ɗan saki fuska kaɗan, dan tana ganin kamar da sun je wajen malamin komai zai zama daidai cikin lokaci ƙaƙani kamar yadda Aunty Hauwa take ta faɗa mata, hakan yasa ta ɗan saki fuska yau.
Su Khadijah dai izuwa yanzu sun gama fahimtar komai da yake faruwa a cikin gidan nasu, da yake sun sami tarbiya mai kyan gaske, sai suka fawwalawa Allah komai nasu, suka dukufa babu dare babu rana wajen yin addu'a, kuma kawunsu Sadiq kullum idan suka kai mashi kukan halin da suke ciki yana kwantar masu da hankali tare da kara masu kwarin gwiwa a kan su miƙawa Allah al'amuransu komai zai warware.
Hakan yasa suke samun sassauci a kan halin da suke a ciki ɗin, Sadiq bawan Allah ne, ya yi ƙoƙarin nusar da Maman Zainab da ta yi hakuri ta fawwalawa Allah komai zai yi mata sakayya a lokacin da bata zata ba, amma ina kishi da takaici ya rufe mata idanu, bata ji bata gani, har saɓani suka samu da Sadiq ɗin a kan maganar, ba dan Sadiq yana da hankali ba kuma yana taimakawa baban Zainab ba da ya bar mata gidanta, dan ba ƙaramin zaginsa ta yi a kan case ɗin ba, ta ce babu ruwansa da ita, amma ya hakura saboda yana taimakawa baban Zainab, kuma ko ba komai baban Zainab ya yi mashi abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba, shi ya ɗauki nauyin karatunsa tun daga nursery har izuwa master da yake yanzu, so koda baban Zainab ya saki maman Zainab shi gaskiya ba zai iya juyawa baban Zainab baya ba, ya yi mashi abin da babu wanda ya yi mashi shi a duniya, domin ilimi shi ne mutun, ya tsaya mashi ya yi karatu kuma boko da islamiya dukka, hakan yasa ya hakura ya cigaba da zama a gidan.
Misalin karfe 9 na safe bayansu Khadija sun tafi school, baban Zainab ya fita kasuwa, Sadiq duk basu nan suna kasuwa, sai ga Aunty Hauwa ta zo domin su je wajen wannan malami na kan dutse da ta faɗa.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
https://chat.whatsapp.com/LAEmIGs3z0KBdL3NQsRixW
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 29/7/2024.....✍️📚🌹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________23🔥
Misalin karfe 9 na safe bayansu Khadija sun tafi school, baban Zainab ya fita kasuwa, Sadiq duk basu nan suna kasuwa, sai ga Aunty Hauwa ta zo domin su je wajen wannan malami na kan dutse da ta faɗa.
Maman Zainab bata gaya wa baban Zainab zata fita ba, kawai ta biyewa Aunty Hauwa ta saɓi mayafi suka fita. Ya Allah ka rabamu da makiran kawaye munafukai, rimi rimi zaka yi wa ƴarka tarbiya na tsawon lokaci, amma wata shegiya cikin ƙanƙanin lokaci zata zugata ta juyar mata da tunani, sai wadda Allah ya tsare ne kawai bata afkawa zugin ƙawaye, to a koma ina Allah ka haɗamu da mutane na Allah masu gaskiya da sommu da gaskiya!.
Haka dai suka kama hanyarsu suka tafi, sai kara zugata Aunty Hauwa take yi, abin ku da shaiɗan, sai buga mata gangan yake yi abinsa, tana ganin kamar suna zuwa shikenan matsalarta ta warware, ta manta da cewa idan Allah bai kaddara abuba to wlh idan duniya dukka gatanka ne, in zasu taru duk duniya su baka wannan abu karɓama ba zaka iya yinsa ba, saboda Allah bai rubuto maka a kaddararka ba, amma ita ina idanunta sun rufe, kishi ga kuma takaicin da Maman Haidar take kunsa mata nan, ga takaicin auren Khadija da Haidar duk sai ya haɗu ya rufe mata idanu ruf, bata ji kuma bata gani!. Allah dai ya kyauta.
To kafin su dawo daga wajen bokan nasu bari mu fara ƙutsawa cikin ainahin labarinmu, bari mu taɓo wani ɓangare kaɗan mu gani, dan ina son mu nemo in da RAWANIN ZALINCI yake, saboda har yanzu fa bamu ko alamun samo shi ba! A gefe gefe muke!.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
Bari mu leƙa UAE wato United Arab Emirates, a cikin UAE ma bari mu leƙa Dubai, a cikin Dubai ma bari mu leƙa prison na Al Aweer Juvenile AAJ, wato prison na yara under 18 years kenan.
AAJ Prison ne kamar yadda kuka san kowani prison na yara waɗan da suka aikata laifi kuma ba su kai shekarun da za'a yanke masu hukunci ba, so ana ajiye su a AAJ ɗin zuwa su kai munzalin karɓar hukunci, ba kamar prison na manya yake ba, nasu yafi na manya kyau, tsaro, kula da lafiyarsu, lafiyayyen abinci, ɗakin kwana mai kyau, masu kula da lafiyarsu suna ƙoƙari sosai, da dai sauransu, ana basu kula sosai ba kamar manya ba, domin kunga su yara ne, wasu ma kaddara ce take afka masu su yi laifi ba'a son ransu ba, amma kowa yasan da cewa dokar kasar Dubai tana da tsauri sosai, musamman ma da ya kasance a yanzu jinin modarawa wato su Akka su ne suke rike da ƙasar, shi ne yasa dokar ta kara sauri over, dan kowa yasan jininsu basu da wasa kuma basa ɗaukar wasa, bugu da ƙari komai da zasu yi dai'dai da faɗar Allah suke yi! A ko'ina da akwai ɓata gari, akwai kuma na kirki, idan suka yanke hukunci fa to ba lallai ne su sake sauraran wani excuse ɗin ba kuma, sai dai idan ta ƙarƙashin kasa za'a bi kamar dai yadda aka saba idan wani ɗan masu hali ya yi wani abin, fatan kun gane?.
Ɗaki ne na yara mai kyau, gadaje irin na sama da kasan nan har gado shidda ne a ɗakin, sama da kasa sama da kasa guda uku kenan shi ne zai kama gado shidda, mattress da suke a saman kadajen mattress ne masu kyau ga kuma laushi, harta bedsheet ɗinsu ma mai kyau ne, tiles mai kyau da tsada ne a kasar floor ɗin ɗakin, suna da Ac kamar ba prison ba, ga bargon da suke rufuwa a lokacin da sanyi ya sauko masu ma mai kyau sosai da shi, pillows ɗinsu duk masu kyau ne, dama na gaya maku su ana kula da su sosai fiye da manya, wajen cin abincinsu a cikin prison ɗin, in da kowa yake fitowa su haɗu su ci abinci ma an kawata shi da dinings tables daban daban sama da guda ashirin, kuma tables ne masu girma wanda kowanne yana da 24 to 32 chairs, da yake katafaren prison ne hakan yasa aka zuba tables ɗin dayawa a wajen cin abincinsu.
Sai hada hada yara suke yi, suna ta kai komo kamar gida, wasu suna buga kwallo a filin ball da yake a cikin prison ɗin, dan harda fillin ball ne da su. Part na maza daban na mata ma daban, kun san dama ba'a haɗasu waje guda!.
Ƴan matasan ƴan'mata da ba za su wuci 13 to 15 years bane su huɗu a cikin wannan ɗakin, da alama ƴan mata biyun cikon gadaje shiddan nan sun fita waje wasa, abinku da yara.
Waɗan nan ƴan'matan uku daga cikinsu sai kai komo suke yi tsakanin toilet da wajen gadajensu, kowacce da abin da take yi, ɗaya tana sanya da blue AAJ uniform a jikinta, ɗaya kuma tana ƙoƙarin shinfiɗa bed ɗinta, ɗayar kuma tana ƙoƙarin naɗe bargonta, da alama yanzu suka tashi daga barci, su dai babu takura babu komai, kawai za'a tsaresu ne sai sun girma sun kai munzali su girbi abin da suka shuka. Dukka waɗan nan ƴan'mata uku dake a cikin ɗakin larabawa ne saɓanin ɗaya da take zaune a saman bed ɗinta ta buga uban tagumi, da alama tana cikin mawuyacin hali ne, saboda yadda ta yi wannan uban tagumi ya nuna tana a cikin damuwa sosai, ba balarabiya bace ba, saboda yadda take bakar fata a cikinsu, sai dai kuma ta fisu kyau sosai, kyakkyawar gaske ce na kin ƙarawa, chocolate color ce dangin Africa, kalar fatarta kala ce mai tsada a duniya wanda yanzu samunsa yake wuya, tana da dogon hanci har baka, ga ɗan madaidaicin bakinta da ya yi ɗas a saman ɓul ɓul ɗin kumatunta, idanunta farare tas dara dara, kyakkyawa ce ajin farko, face nata ɗan dai'dai, bata da wani ƙiba, ƴar dai'dai da ita, ba zata wuci 15 years ba a duniya, tana sanye da kayan AAJ ɗin wadda kowasu prisoners suke sanyawa, kanta babu ɗan'kwali, tana da yelwar bakin gashi mai tsawo, gashin nata a nannaɗe yake irin kamar rubber hair ɗin nan, amma gashin nata akwai tsawo da kyau sosai, duk da ya kasance tana zaune ne hakan ba zai sanya ka kasa iya gane cewa dirarriyar mace bace, tana da dirarren jiki mai kyau wadda kamar ita ta yi wa kanta, coca cola shape ne da ita sosai, kirjin nan nata a cike suke fam kamar ba ƴar 15 years ba, kamar mai 18 years haka, ta buga uban tagumi kamar wadda aka saukowa da wahayin yinsa, her face looks she's so silent, innocent face ke gareta.
Wata yarinya wadda a kallah zata iya kai 17 years ce ta shigo cikin room ɗin, fara ce tas balarabiya, kyakkyawa ce sosai, amma bata kai wannan chocolate color ɗin yarinyar kyau ba, ita ma kanta babu ɗan'kwali, ta ɗaure gashin kanta two step, ta saki jelar gashin nata ɗaya ta bayanta, ɗaya kuma ta saman shoulder ɗinta ya yo gaba, kyakkyawa ce sosai ita ma, ga dara dara idanu farare tas, tana da sura mai kyan gaske.
A kusa da wannan chocolate color yarinya ta zo ta zauna a saman bed ɗinta kenan. Cikin harshen larabci mai nuna cewa kwararriya ce a iya larabci ta ce "أنت لم تأخذ حماما Leesharh? (Leesharh bakiyi wanka ba)?"
Ta yi maganar tana taɓa shoulder ɗin Leesharh ɗin.
Ƴar firgita ta ɗan yi alamar ta ɗan razana, dan ta afka duniyar tunani ne bata ji shigowar yarinyar ba, shi ne yasa da ta taɓata ta firgita.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa, cikin muryarta da kwata kwata baya fita, tamkar wata bebiya ko mai koyar yin magana, idan ba su da suka saba da ita ba wani daga waje ba zai iya gane me take faɗa ba, sam muryar tata bata fita kamar irin wadda mura ta shaken sosai ɗin nan, ga in'ina a cikin maganarta abin gwanin ban tausayi.
"اليوم أتذكر والدتي، ولهذا السبب مات جسدي كله، ولم أستطع الاستحمام
(Yau na tuna mahaifiyata, shiyasa duk jikina ya mutu, kuma na kasa yin wanka Jasrah)"
Ta bata amsa cikin harshen larabci ita ma.
Ɗaya daga cikin yaran nan ne da suke a cikin ɗakin before shigowar Jasrah wadda take shinfiɗa bed ɗinta ɗazun ta ce. "To ba kin kashe mahaifiyar taki ba? Menene kuma abin wani sake yin tunata?".
Ita ma cikin harshen larabci ta yi maganar, da alamu larabci kawai suke ji wata kila da turanci!.
"Aaradiya wai meyasa kuke yin haka ne?".
Cewar Jasrah dake dafe da shoulder ɗin Leesharh.
Wani kallon banza wadda aka kira da Aaradiyar ta wurga masu daga Leesharh har Jasrar, sannan ta sa kai ta fice waje abinta ba tare da ta sake yin magana ba, dan ta gama gyaran gadon nata dama.
"Leesharh ki yi hakuri, ki je ki yi wanka ki zo mu je mu ci abinci".
Cewar Jasrah.
Leesharh kenan wadda rahotonta yake a rubuce cewa ta kashe mahaifiyarta da hannunta a cikin kitchen suna tsaka da yin aikin girki ta caka mata wuƙa a ciki, nasan dai dukkanku zaku sha mamakin yadda aka yi yarinya kyakkyawa karama kamar wannan ta kashe mahaifiyarta har a kawota prison ɗin yara, na san za ku so jin ainahin labarinta da yadda aka yi ta kashe mahaifiyarta da kuma yadda aka yi ta zo gidan AAJ, meyasa zata kashe mahaifiyarta? Uwa fa? Hmmmmm mu je dai zuwa.
"Jasrah bana jin zan iya cin komai yau, ki je ki ci abincinki, ni ki barni kawai".
Ta yi maganar idanuwanta suna kawo ruwa, alamar dai da gaske yau bata cikin yanayi mai daɗi, ko dai tana nadama ko makamancin hakan.
"Amma Leesharh yau tsawon shekara guda kenan tun shigowarki gidan AAJ kullun ina baki shawara da ki cire wannan tunanin a cikin zuciyarki, ki hakura ki rungumi kaddararki, ki manta da kowa da komai ki sake ki yi rayuwa kamar mu, ni dai kina gani na barwa Allah komai, Allah ya sani ni ba da gangan na kashe Ameer ba, amma saboda bani da hujja kuma iyayena basu da karfi kinga an kawoni nan wajen an tsare, kuma ni na hakura na rungumi kaddarata, a kullum ina tunanin iyayena sosai, amma bana bari hakan ya hanani farincikina, nasan akwai ranar sakayya, kullum da tunanin ƙanwata Alveena nake kwana nake tashi, amma ya zan yi to? An rigada an rabamu, sai idan Allah ya ƙaddara muna da rabon haɗuwa a gaba, idan kuma lokacin yanke mana hukunci ya cika ba'a gane gaskiya ba aka kashemu shikenan akwai lahira ai, akwai ranar da babu wanda ya isa ya yi karya ko ya cuci wani, rana ce ta kwatarwa waɗan da aka cuta hakkinsu ba tare da zalinci ko son kai ba!".
Ta kai karshen maganar tana goge hawayen da suka fara zuba mata a saman fuskarta, gwanin ban tausayi.
Zuba mata idanu kawai Leesharh ta yi tana kallon yadda take sharar kwallah, hawaye wani na bin wani kamar famfo, abin tausayi, wlh ba da gangan ta kashe shi ba, saboda wani saɓani da aka samu ne, kaddara ce ta faɗo mata kawai, dan iyayenta talakawa ne kuma yasa ba'ayi wani shari'a sosai ba, yanzu shekarunta uku a cikin wannan prison ɗin, tun tana da 14 years aka kawota, yanzu kuma tana da 17 years, saura mata shekara ɗaya ta cika 18 years a duniya shikenan sai a yanke mata hukunci wadda dani da ku dukka munsan dai wanda ya yi kisan kai hukuncin kisa shi ma ake yanke mashi, wannan ita ce dokar kasar Dubai, a kanta kuma suke tafiya, doka ce ta addinin Musulunci, duk wanda ya kashe rai shi ma a kashe shi! Dan rai bata fi rai ba!.
Ainahin Jasrah iyayenta larabawan ƙasar Turkey ne, zama ne ya kawosu kasar Dubai, wahalar rayuwa yasa suka baro Turkey suka zo nan Dubai neman abin da za su rufawa kansu asiri, kasancewar Jasrah ita ce babba sai take zuwa gidajen masu kuɗi tana yi masu aiki suna biyanta, a lokacin ma kwata kwata bata wuci 14 years ba, tana dai yi masu ɗan aikin da karfinta zai iya, to ita yarinya ce mai hakuri sosai, ga sanyin hali da tausayi, kanwarta ɗaya Alveena, su biyu iyayensu suka haifa, basu zuwa makarantar boko saboda halin rashi da mahaifinsu yake fama da shi, amma suna karatun islamiya sosai a wajen iyayen nasu, da yake mahaifinsu babban malami ne, akwai ilimin addini, so sun sami ilimin addini sosai.
A haka dai kullun tana zuwa wani babban gida na masu kuɗi da yake a unguwar tasu tana aiki, matar gidan sam bata kaunar Jasrah ɗin, amma mijinta kuma yana son yarinyar, saboda shiga ranta, tana da hankali sosai, suna da yara maza biyu da mace ɗaya, mazan manya ne, babban zai kai 20 years, sai mai bi mashi Ameer wadda aka ce ta kashe kenan, shi kuma yana da 17 years kamar dai ita a yanzu, macen kuma tana da shekaru 7, kullum idan ta je ta yi masu aikin goge gogen ma idan babansu baya gida basu bata komai, dan maman bata kaunarta, amma idan baban yana nan zai bata abinci dayawa ta tafi da shi gida su ci da iyayenta da kanwarta Alveena, zai kuma bata kuɗi.
Wata rana idan baban ma baya nan korinta mamar take yi idan ta je yin wannan aiki, amma da yake tana samun abincin da suke ci da iyayenta da kanwarta, tana kuma samun kuɗi wajen baban sai yasa bata gajiya da zuwa gidan duk walaƙancin da suke yi mata, tana hakura ta je, damo ce sarkin hakuri.
A haka suke rayuwa a takaice kwance tashi watarana suka sami saɓani da wannan Ameer ɗin, ya so ya lalata mata rayuwa ne taki yarda, duk da tana karama amma ta samu ilimin addini daga iyayenta, ta san illar yin hakan, shi kuwa a lokacin ya doshi 18 years yana ji da tashen balaga, kansa na rawa sosai yaron, ya fi yayansa ma bushewar idanu, da alama kuma yana yawan kallon fina finan batsa, hakan yasa ya yi ƙoƙarin lalata mata rayuwa.
Da taki yarda ne ya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata, kullum idan ta zo tana aikin goge gogenta in dai zai gifta ta kusa da ita sai ya kai mata mari a mazaunanta, kamar shi ya halitta mata su, tun tana kuka har ta saba.
Wata rana ta ce ba zata sake zuwa gidan ba, dan ta gaji da azabtar da ita da Ameer ɗin yake yi, ga shegen sakata aiki da yake yi, ya yi ta dukanta kuma, wani lokaci a gaban mamarsa yake dukan nata, amma uwar bata cewa komai saboda zalinci, sai dai ta kawar da kai, dama na gaya maku uwar bata da hali mai kyau. Sai dai ko da ta ce ba zata sake zuwa gidan ba tana hakura ta sake zuwa, saboda abincin da take samo masu su ci da iyayenta, mahaifinsu ya manyanta sosai, baya iya yin aikin karfi, amma yana iyaka bakin ƙoƙarinsa!.
Wata rana mamarsa tana ƙasa ita kuma Jasrah tana sama tana goge goge, sai ya ce ta je ɗakinsa ta gyara mashi, kamar zata ce ba zata je ba, amma saboda tsoron mamar tasa yasa ta je ta fara gyara masa. A nan ya iskota tana faman gyara mashi bed ɗinsa, ai kuwa yana zuwa ya turata saman bed ɗin tare da ƙoƙarin yi mata fyaɗe ta karfin tsiya, tana ƙoƙarin yin ihu ne ya yi saurin toshe mata baki da hannunsa. Hakan yasa ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ta karfin tsiya a in da suka fara kokawa, ya sanya karfi zai yi mata fyaɗe ita kuma ta sanya karfi zata kwaci kanta.
Da yake mummunar kaddara ta gifta a tsakani sai ta sanya hannu tana laluɓar abin da zata buga mashi, cikin ikon Allah ta ɗauko kwalbar mardbe da ya yi amfani da shi ya barshi a saman bedside drawer ba'a fitar ba, ai kuwa yana danne da ita yana ƙoƙarin cire mata riga, bata yi wata wata ba ta buga mashi kwalbar a kansa, hakan yasa ya tashi daga kanta a haukace, saboda azaban zafi da ta ziyarce shi.
Abinku da yarinta, zuciyar kuruciya tana ɗebansa, cikin fusata ya kwace kwalbar daga hannunta tare da fasata a ƙasa, tana ƙoƙarin guduwa ta fita daga cikin ɗakin ya rikota da nufin ya kasheta da kwalbar, dan yana ɗaukarta a ƙasƙantacciyar ƴar aiki mara galihu, koma me ai baiwarsu ce ita ɗin, ko ya kwasheta ya kashe banza a banza.
Wage baki ta yi a in da ta zunduma ihu da karfi, a zuciye ya kai mata duka a bakin nata da ta yi ihun, ba shi ta haɗiye ihun da take ƙoƙarin kurmawa a karo na biyu, gadan gadan ya yi niyar kasheta, sai dai cikin ikon Allah ta samu ta ɗauko ɗaya daga cikin kwalaben da suka yi saura a kasan wanda ya fasa, a ƙoƙarin ta yi mashi barazanar kada ya kara matsowa kusa da ita, sai kuma mummunar kaddara ta gifta ta caka mashi wannan kwalbar a cikinsa, wannan ita ce sanadiyyar mutuwarsa kenan.
Wannan ihu da ta yi na farko yayansa ya ji ihun nata, hakan yasa ya nufo ɗakin, ya shigo kuma dai'dai lokacin da ta caki Ameer ɗin da kwalbar har ya faɗi a saman bed ɗinsa da yake yana a kusa da bed ɗin dama, hakan yasa yayan ma ya kurma ihu mai sauti wanda ya ja hankali kowa da yake gidan. A guje suka nufo ɗakin, kafin ma ayi wani yunƙuri Ameer dai ya ce ga garinku, rai ta yi halinta, wannan shi ne abin da ya faru, ko da aka kira jami'ai sai cewa mamansa ta yi ai daba Jasrah bata kaunar Ameer, kuma ta taɓa cewa sai ta kasheshi a baya lokacin da ya mareta, to shi ne yanzu ta bishi har cikin ɗakinsa yana kwance ta kashe shi.
Da jami'an suka tambayi cewa ina shaidar maman na cewa Jasrah ta taɓa yin ikirarin zata kashe Ameer, sai ta gabatar da shaida na farko yayan Ameer ɗin, da kuma sauran ƴan aikinta wanda dan dole suka amsa da anyi hakan, dan kawai basu da zaɓi da ya wuce hakan in dai suna son cigaba da rayuwa su kuma cigaba da yin aiki, haka suka bi bayan karya suka rufawa Ameer asiri na cewa shi yake neman lalata Jasrah, suka ɓoye wannan magana, kuma kowa na gidan yasan da cewa tabbas Ameer shi yake neman Jasrah da faɗa, saboda wani lokaci idan tana tsaka da yin aiki tare da sauran ma'aikatan gidan ya zo wucewa zai kai mata mari a mazaunanta a gaban kowa, kuma ya wuce ya mari banza, so sun san komai, amma basu da zaɓin da ya wuce su amsa maganar maman Ameer ɗin a matsayin gaskiya.
Wasu matan wlh munafukai ne na karshe, Maman Ameer dai da kanta ta goge ɗaukar CCTV camerar da yake parlourn wanda ya ɗauki video Ameer ɗin lokacin da yake cewa Jasrah ta je ta gyara mashi ɗaki, sai ta goge wannan ɗauka dan ta kara tabbatar wa da jami'ai cewa tabbas haka kawai Jasrah ta shiga ɗakin Ameer ta kashe shi saboda ƴar tsama da ta taɓa shiga tsakaninsu har ya mareta, ko da aka tambayeta wace tsama ce, sai ta ce ai Jasrah ɗin ce ta zubawa Ameer ɗin tea mai zafi a jiki bisa rashin sani, shi ne shi kuma ya fusata ya mareta, shikenan ta ce ba zata barshi ba. Haka dai suka shirya karya da gaskiya tare da shirya hujjojin da dole sai ka yarda da maganar tasu, wannan dalilin yasa aka kai Jasrah kotu ba tare da ɓata lokaci ba aka yanke mata hukunci kisa daga nan sai gidan AAJ za'a tsareta zuwa lokacin da zata kai munzalin karɓar hukunci kisa kamar yadda ta kashe Ameer ɗin.
Iyayenta sun yi kuka ne har mahaifinta ya kwanta jinya na tsawon lokaci, haka kanwarta Alveena, mahaifiyarsu har yau bata dai'na kuka ba, suna zuwa AAJ ɗin ziyartar Jasrah ɗin, amma ba koda yaushe ba, saboda basu son zuwa su ganta a cikin wani hali, idan suka koma gida a ranar da suka ziyarceta kwana suke yi basu yi barci ba bayin Allah. WANNAN SHI NE LABARIN SUHANA DA KUMA DALILIN ZUWANTA AAJ, BA SAI NA TSAYA YIN DOGON BAYANI BA NASAN KUN FAHIMCI IN DA AKA DOSA!.
Mu koma kan labarinmu.❤️🔥
"Shikenan Leesharh, bari na je lokacin cin abincin yana kurewa, kuma kin san komai yana da lokacinsa a cikin gidan nan, dan haka bari na je na ci nawa kada time ya kure banci ba a hanani". Cewar Jasrah. Ta kai karshen maganar tana miƙewa tsaye.
Da idanu kawai Leesharh ta bita har ta fice
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 75