kafin ta sa kai ta wuce ɗakinsu.
"Maman Zainab wai menene yake damun Khadijah ne? Yau na ganta wata iriya da ita, sam bata da walwala". Cewar Aunty Hauwar, ta yi maganar kuma tana zuba ruwan da Zainab ta kawo mata a cikin cup dan ta sha.
"Hauwa kenan ke da kin san komai, maganar nan ne dai na aurenta da Haidar, wai ina kika baro su Khalid ne Hauwa?".
Sai da ta sha ruwan da ta zuba a cup ɗin, sannan ta amsa mata da cewa. "Su Khalid suna gidan kakarsu, amma kema maman Zainab wlh da laifinki, yaushe zaki tsaya suna yi maki irin wannan cin kashin? Sai na yi maki magana sai ki ce ai yayyunsa ne ba kannensa ba, to su yayyun nasa idan suka yi ba dai'dai ba ba'a gyara masu zama ne? A ina kika taɓa jin irin wannan? Ki zauna ki yi shiru kina ji kina gani za'a lalata maki rayuwar yarinya, kefa haka kike, tun muna makaranta ma ni nake tare maki faɗa, sai ki yi shiru ki bari kowani kare da doki yana takaki son ransa, ni wlh ba zan ɗauki wannan iskanci ba, shiyasa ma nake kara godewa Allah da ya bani yara dukka maza babu mace a ciki, dan na huta da waɗan na rigingimun". Ta kai karshen maganar alamar ranta ya ɓaci.
"Hauwa ke ba zaki gane bane, wlh ni ba zan iya fito na fito da mahaifiyarsa ba, saboda kinga babban Zainab bai cancanci na yi koda musu ne da mahaifiyarsa ba, shi zaki duba, yana yi mana komai dan ya sanya mu cikin farinciki, a gaskiya ko ba dan ma haka ba ni ba zan iya tsayawa ina fito na fito da mahaifiyarsa ba ko na yi mata rashin kunya, ba zan iya ba, dan uwa uwace ko mai lalacewarta".
Girgiza kai Aunty Hauwar ta yi. "Ai nima ban ce ki yi fito na fito da mahaifiyarsa ba, ita wannan Maman Haidar ɗin zaki gyarawa zama, ita zaki takawa birki, cin kashi ya yi yawa, suna zaginki a kan kin tara masu ƴaƴa mata a goda, ga shi har Yanzu shiru baki sake haihuwa ba sai dai ki ci ki kwanta sai kiɓa kike yi, sannan kuma saboda basu da kunya sai su dawo suna neman auren ƴar taki da kika tara masu a gida wa ɗansu? Kuma duk da suna neman auren ƴar taki ma basu dai'na ci maki mutunci ba? A haka kuma kike tunanin zaki zuba masu ido? Ai wlh basu isa ba, bari zaki yi rana ɗaya idan Maman Haidar ɗin ta zo ta nemi kawo maki rai'nin wayo, a nan ne zaki taka mata birki, ki karta mata jar warning mai zaman kanta, hakan zai sanya ki ɗan huta, haba abin ya yi yawa mana".
Tana magana tana wani kara ɓata rai.
"Hauwa ba zaki gane bane, misali yanzu idan na yi wa maman Haidar magana cikin ɗaga murya ma, wlh to ki jirayi zuwan kakansu, dan sai ta je ta kwashi karya da gaskiya ta gayawa mahaifiyar tasu, ita kuma zata sako hijabi ta zo nan ta ci mutunci na fes, kullum sai ta ce zata sanya baban Zainab ya sake ni, ni kuma a yadda su Zainab suka taso yanzu suke ƙoƙarin zama ƴan'matan nan zamana dasu shi ne mafi a'ala a gareni, a yanzu nisa da su babbar haɗari ne a gareni, kinga yanzu suke tashen girma, yanzu ne suke buƙatar kulawata sosai, dan haka gara na jure na cigaba da hakuri na zauna da babansu har izuwa lokacin da zan kaisu ɗakin mazajensu lafiya, daga nan sai na san abin yi".
Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka, idanuwanta sun ciko tab da kwallah, abin gwanin ban tausayi, takura sam bashi da daɗi a rayuwar nan.
Aunty Hauwa na ƙoƙarin yin magana suka tsinkayo sallamar baban Zainab ɗin a bakin kofar shigowa parlourn, sun dawo ne daga masallacin sallar issha.
Jin sallamarsa yasa Aunty Hauwar ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Zamu karisa maganar idan kin zo gida ko kuma idan na sake zuwa, yanzu dai bari na wuce dare ya yi, kuma kinga unguwar nan taku sai a hankali, kada wani ya bugeni ya kwashe mun kaya".
Tana magana tana tattare kayan nata, haka ta jidesu ta nufi waje. Dai'dai lokacin kuma Baban Zainab ya shigo cikin parlourn.
Kamar yadda kuka sani ne, ko sannu bai ce wa Aunty Hauwar ba, yasa kai zai wuce, dan haka yake.
Cikin sauri ta ɗaga mashi gaisuwa, ya sha dakakkiyar shaddarsa ɗinkin mutunci, yanzu kuɗi sun fara zama mashi zamzam, wani katafaren gini ma yake ta faman gina masu, hawa ɗaya ce gidan, idan ya kammala zasu koma can abinsu, sai dai kash dangi sun sako shi a gaba a kan ya kara aure tun da Maman Zainab taki ta sake haihuwa, Maman Haidar har da wani cewa sun gaji suna son sake ganin yara ƴan dogwai dogwai a gidan. Ɗan adam kenan, ba'a iya mashi.
A takaice ya amsa mata gaisuwar tata tare da sanya kai ya wuce ciki abinsa.
Har bakin kofar gida Maman Zainab ɗin ta rako Aunty Hauwar, yau ma kamar kullum sai da ta bata dubu ɗaya wai ta hau mashi.
Karɓa ta yi tare da zuba mata godiya. Daga haka suka yi sallama, Maman Zainab ta wuce ciki, ita kuma Aunty Hauwar ta nufi waje.
Tana fita Sadiq bawan Allah ya fito daga cikin ɗakinsu ya zo ya rufe kofar gidan tare da kalewa da sakata, sannan ya koma cikin ɗakin nasu.
Haidar sai faman sanya kaya yake yi shi a dole zai fito tsakar gida su yi hira da Khadijah, ita kuma sam bata son yin hira da shi da daddare, dan kullum sai ya rinƙa ƙoƙarin taɓa jikinta, tsabar jahilci sai ya ce ai ita ƙanwarsa ce kuma aurensu ya kusa.
A kule take ce mashi ya bari sai anyi auren tukun nan, haka dai take fama da shi, baiwar Allah, ga shi ta kasa iya gayawa babanta abin da yake yi mata su ɗauki mataki, ta rasa ina zata saka kanta, mamanta ta yi so silent over. Shiyasa wani lokaci shiru shiru ma bashi da daɗi sam.
Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 8/7/2024.....✍️📚🌹
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________9🔥
A saman sofa baban Zainab ya zauna yana jiran shigowar maman daga rakiyar Aunty Hauwa da ta yi. Bawan Allah tunaninsa duk yana wajen yadda zai yi da mahaifiyarsa, ga jikin tsufa, idan ka fara yi mata magana duk sai ta bi ta rikice ta ce wai an zageta, haka take yi, ta tsufa sosai, dan a ƴaƴanta Baban Zainab shi ne wajen na shidda, and dukka mata ne ƴaƴan nata shi ne kawai namiji, uku daga ciki sun rasu sun bar mata jikoki tana tare da su, wani lokaci ƴaƴan suna wajen kakarsu ta wajen ubansu kenan, wani lokaci kuma suna wajenta, yanzu daga maman Haidar, sai wata mai bin Maman Haidar ɗin takwarar Zainab, sai babansu Zainab, sune manyan da suka rage, sai kanana mata guda biyu da duk suma sun yi aure suna ɗakin mazajensu, so a takaice dai tsohuwa ce sosai kakar tasu, shi ne yasa take a birkice sosai.
Baki a ɗauke da sallama Maman Zainab ta dawo cikin ɗakin, kusa da shi ta zo ta zauna tana yi mashi sannu da dawowa daga masallaci.
Ƙaƙalo murmushin dole ya yi kafin ya ce. "Ina su Khadijah? And ina kayan da na dawo da shi daga kasuwa?".
"Suna ciki, kayan ma na kai ɗaki".
Ta bashi amsa tana miƙewa tsaye, ɗakinsu Khadijah ɗin ta nufa domin ta kirasu su zo su ci abincin dare.
Da fitowarsu kallo ɗaya baban ya yi wa Khadijah ɗin ya kawar da kallonsa, har ƴar rama ta yi.
A in da suka saba zama a nan suka zauna.
"Khadijah ɗauki abincin su kawu Sadiq ki kai masu". Cewar mamanta, da yake bata san abin da yake faruwa ba, bata san cewa Haidar ɗin yana son keɓewa da Khadijar dan ya rinƙa taɓa mata jiki ba.
Cikin sanyin murya a takaice ta ce. "Zainab ta kai masu pls Mama".
Babansu ne ya amsa da cewa. "Yeah nima abin da zance kenan, Khadija ba zata sake kai masu abinci ba, ita ma Zainab ɗin daga yau idan ta kai masu shikenan, su zo su rinƙa ɗauka da kansu!".
Ya yi maganar ne cikin umarni, babu wasa a tattare da shi, hakan yasa Maman Zainab ɗin ta amsa mashi da to In Sha Allah hakan za'ayi.
Turo baki Zainab ta yi kamar zata sa ihu, dan ita fa a duniya ta tsani zuwa koda kofar ɗakinsu ne, bare ma idan kawu Sadiq baya nan, sai ta ji kamar ta yi ta zunduma ihu idan aka aiketa koda ɗaukar abu ne a cikin ɗakin, bata son ganin Haidar, amma ya zata yi? Dole ta miƙe ta zuro hijabi kafin ta ɗauki ƙatuwar kular abincin tare da plates ta nufi waje da shi.
A bakin kofar ta tsaya ta kaiwa kofar ɗakin kauri da kafa kamar shi ne ya yi mata laifi, yadda kuka san kofar ne ya sakata dole ta kawo abinci.
Daga ta cikin ɗaki Sadiq bawan Allah ya ce. "Zainab ba? Ai nasan sai ke ce zaki buga mana kofa irin haka, to sannu da ƙoƙari ƴar neman rigima......"
Bai gama rufe baki ba Haidar da yake tsaye wajen mirror ya karɓi zancen cikin faɗa da cewa.
"Ai wlh Zainab sai na koya maki hankali a gidan nan, ba ke baki da hankali ba? Yanzu mu sa'anninki ne da zaki zo ba sallama ki hau dukan mana kofa? Bari na same ki a waje sai na sharara maki Marika". On a serious note ya yi maganar.
Murguɗa mashi baki ta yi dan tasan baya ganinta, sannan ta ce. "Kawu Sadiq ga abincinku nan in ji mama".
Har suna haɗa baki shi da Haidar wajen magana, shi Sadiq ya ce ta ajiye a waje bari ya zo ya ɗauka, shi kuma Haidar ya ce to uban waye take so ya zo ya karɓa? Waye sa'anta? Ta kawo ciki ta ajiye.
Banza ta yi da Haidar ɗin kamar bata ji me ya ce ba, dan dama ita Zainab haka take, yadda kuka san me za'a ce ne, ta iya mannin hauka ta mayar da mutane ƴan iska, idan ka yi mata maganar da bai yi mata daɗi ba kuma kana da matsayin da ba zata iya ramawa ba kamar dai yayan nasu, sai ta mayar da kai ɗan iska, ta yi kamar ma bata ji me ka ce ba, kamar ma bata san kana yi ba, idan kuma tasan tana da halin ramawa, to wlh bata barin kota kwana, tsab zata solleka soso da sabulu. Yanzu ma abin da ta yi kenan, ta ajiye abincin a kofar ɗakin tare da murguɗa baki kamar Haidar ɗin yana ganinta, sannan ta watsa masu daƙuwa da yatsunta biyar yadda kuka san suna ganinta, kofar ɗakin ma fa a rufe yake, amma haka ta tsaya tana huce haushinta a waje, abin gwanin ban dariya.
Bayan ta watsa masu dakuwar ma bai yi mata ba, sai da ta dunƙule hannu ta yi alamar zata kai haushi tana wani watso harara da waɗan nan fararen idanuwan nata kamar na mage.
Muryar Haidar ne ya katseta da cewa. "Ke ba zaki kawo mana abincin bane kina tsaye a waje?".
Kara murguɗa baki ta yi kasa kasa ta ce.
"Mahaukacin banza ba za'a kawo ɗin ba".
Ta yi maganar ta yadda ita kanta bata wani ji sautin muryarta ta fita sosai ba, sannan tsabar faɗa irin nata da rigimar tsiya har da murguɗa mazaunanta kafin ta sa kai ta wuce parlournsu ba tare da ta sake kula Haidar ɗin ko ta ce masu ga abincin a kofar ɗaki ba, ta mayar da Haidar ɗan iska, ta barshi yana ta zuba masifa a kan ta kawo abinci cikin ɗaki, irin shi yaya babban nan, Zainab kam dai'dai take da shi yarinyar nan, ita ce nan tasan maganinsa, idan yana mata magana ma wata sain wlh sai ta toshe kunne, ko kuma ta kara gaba ta bar shi a gantale.
Shiru shiru Haidar ya ji Zainab dai bata amsa ba kuma bata shigo da abincin ba, a kule ya nufo kofar ɗakin da nufin yana buɗewa sai ya zabga mata mari.
Sai dai kash, yana buɗewa bai ga ko mai kama da ita ba, tuni ta ajiye masu abincin a bakin kofa ta yi gaba abinta. Ransa idan ya yi dubu ya ƙara ɓaci sosai, amma ba yadda zai yi, dan babansu yana nan, bai isa ya je ya kamata ya daka ba, hakan tasa ya hakura ya koma cikin ɗakin kawai, tsabar shegen son girma sai bai ɗauki kular abincin ba, ya koma cikin ɗakin ya ce Sadiq ya je ya shigo da abinci.
Sadiq kuwa bawan Allah ɗan ba ruwana, miƙewa ya yi ya ɗauko abincin ya shigo masu da shi ciki, sai wani cika Haidar yake yi yana batsewa, shi a dole an ɓata mashi rai.
A can cikin parlourn kuwa, Khadija cikin hanzari ta ci abincin darenta, a daddafe ma ta tura abincin, ba wani ɗanɗano da take ji, ci kawai take yi.
Suna kammalawa ta miƙe sauri sauri ta wuce cikin bedroom nasu, da kallo iyayen nata suka bita da shi, dukkansu ba karamin tausaya mata suke yi ba, babanta ya so ya tsayar da ita dan taga kayayyakin da ya sayo masu daga kasuwa, ya so su buɗe kayan a daren nan ya bawa kowa nasa, amma ganin bata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yasa ya kyaleta zuwa da safe.
Ita kuwa Zainab sai da ta ɗan jima a parlourn tana hira da babanta bayan sun gama cin abincin kenan, sai ƙarfe 9 dai'dai ta miƙe tare da yi masu sallama ta wuce ciki.
Kwance ta isko Khadijah a saman bed, sai dai da alama bata yi barci ba. Wanka Zainab ɗin ta yi tare da fitowa ta yi shirin kwanciya, sannan ta haye saman bed ɗin tana kallon ƴar uwar tata.
"Baki kashe wutar ɗakin ba ai Malama". Cewar Khadijah.
"Aunty khadina ki bar wutar a kunne mana tun da dukka labulayenmu a sake".
Shiru Khadija ɗin ta yi mata, bata sake yin magana ba. Zainab bata shiri da duhu ne, bata barci cikin duhu, idan kunga sun kashe wutar ɗakin nan nasu to sai dai idan Zainab ta yi barci ne, sai Khadijan ta kashe, wani lokaci dukkansu suna yin barci su barshi a kunne, sai iyayensu sun shigo yi masu addu'a, sannan ne suke kashe masu wutar ɗakin.
Kwanciya Zainab ɗin ta yi tana tunani rayuwar yayar tata.
A hankali Khadijar ta ambaci sunanta Zainab.
Juyawa gareta Zainab ɗin ta yi suna fuskantar juna.
"Lafiya Aunty Khadina?".
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Babu komai, amma anjuma idan kin tashi yin sallar dare ki sakani a cikin addu'a sosai, dan ni yanzu na shiga lokacin rashin sallah tun bayan sallar issha da na yi, dan haka kada ki tasheni yau".
Shiru ta ɗan yi kafin ta bata amsa da cewa. "Aunty khadina ai kinsan kullum ina yi maki addu'a, da izinin Allah ba zaki auri Yah Haidar ɗin nan ba, Allah ni kakan nan ma wani lokaci idan tana masifar nan tata kamar na kifeta da mari nake ji".
Harara Khadija ɗin ta wurga mata kafin ta ce. "Ki mareta ta mutu ki shiga uku, wannan tsohuwa baki mareta ba ma tana rangaji ita kaɗai a saman iska, ai kina yin kuskure ko kaɗan ne kika bugeta wlh ranga ranga za'a kwasheta, kin ga daga nan ke kuma sai koma".
Guntun tsaki Zee ɗin ta ja tare da juyawa ta bawa Khadijahr baya tana wani ƙara haɗe rai. Da alama fa da Zainab aka ce za'ayi wa wannan aure to ba shakka zata yi fito na fito da su, sam lamarinta babu sauki, da wuya su Maman Haidar su sha a hannunta, dan da alama zasu gasu sosai, yanzu ma dan mamanta na taka mata birki ne, ba dan haka ba, da ba abin da zai hanata yi wa Maman Haidar ɗin tas idan ta zo gidan tana zuba masifa, amma Mamansu da yake macece mai tarbiya tana tsawatar masu sosai, tana gaya masu maman Haidar dai ɗaya take da babansu, so idan har Zainab zata yi mata rashin kunya, to kenan zata iya yi wa babanta, dan haka babu ruwansu, idan ma sun ga Maman Haidar ɗin ta zo maza su wuce cikin ɗaki, kada ma su kawo kunnuwansu a kan abubuwan da zata yi ta faɗa, su kyaleta watarana sai labari.
A can parlourn kuwa, Haidar ya zo da nufin su yi hira da Khadijah, babanta ya ce mashi ta yi barci, tsabar bashi da kunya wai a tasan mashi ita akwai abin da zai gaya mata ne.
Da farko Maman Zainab zata je ta tasheta, sai baban ya ce a'a a barta ta yi barci sai da safe ko idan sun dawo daga makaranta sai ya gaya mata koma me zai gaya mata, yanzu dai tun da ta rigada ta yi barci ya kyaleta.
Da farko kamar ba zai tafi ba, dan ba hakan ya so ba, ransa ta ɓaci, ya so ne su yi hira da ita, amma da yake kawun nasa ne ya yi magana dole ya hakura, da ace Maman Zainab ita kaɗai ce a gidan da ba abin da zai hana shi shiga cikin ɗakinsu ya tasheta ta fito ayi hiran dole, dan ba kunya ne ke gare shi ba, ga rashin hankali cikakke, kuma kun san ba ganin mutuncin Mamansu yake yi ba, tsab zai iya cewa zai shiga ya tasota da ace baban baya nan.
Amma fa duk rashin kunyar Haidar yana tsoron kawun nasa, dan fa baban Zainab shi ma mutun ne mai zafi sosai, kawai sai anyi mashi ba dai'dai ba ɗayar halin nasa ta zafin rai take bayyana, Haidar ɗin ya ci duka a hannunsa lokacin da yake kin zuwa makaranta, ya sha punishment, sai da kakansu wato maman baban Zainab ɗin ta ce bata so kada ya sake dukan Haidar, ya kyale shi mana tun da ba za'a ci karatu ba, har da cewa wai shi ma baban Zainab ɗin da ya yi karatun ai ga shi nan result ɗin bata amfane shi ba, ya ajiyeta a cikin akwati kawai yana kallo, to dan haka ya rabu da Haidar ɗin, kun san kaka dama yawanci haka suke, sai su hana a ladabtar da jikokinsu.
Haidar dai kamar zai yi kuka ya wuce ya koma cikin ɗakinsu, a lokacin shi kuma Sadiq yana zaune ya zuba abinci a cikin plate dan ya ci abinsa, shi ko zancen auren ma baya yi, yanzu haka master nasa yake haɗawa a ɓangaren computer engineering, ya gama degree nasa bawan Allah, akwai shi da ƙoƙari sosai, so baya batun aure ma, mata ma yanzu ba su ne a gabansa ba, ilimi da kuɗi kawai yake nema, mamansa ta ce ya nemi kuɗi da ilimi mata zasu biyo shi har in da yake ba sai ya wahalar da kansa ba wajen bin matan ba, ya bi kuɗi da ilimi a guje su kuma mata zasu biyo shi a guje, uwa ta gari kenan, saɓanin uwar Haidar da take cewa ilimi bashi da wata amfani.
Washegari da safe kamar yadda suka saba, tun karfe biyar na asuba bayan sun yi sallar asuba Maman Zainab ta wuce cikin kitchen, abinci mai rai da lafiya ta girka masu a matsayin breakfast, a tare da Khadijah suka yi aikin komai, ita kuma Zainab ta gyare masu gidan ko'ina tsab, ta zuba turaren wuta mai rai da lafiya kamar dai yadda suka saba, yanzu Maman Zainab ƴan'matanta sun girma, aiki ya ragun mata sosai, idan Khadija tana kitchen, ita kuma Zainab zata hau gyaran gida, komai a tare suke yi su ukun kamar wasu kawaye, haihuwan ƴaƴa mata akwai daɗi kuma akwai falala da rahama sosai, ƴa macece kawai Allah ya ce a ranar gobe kiyama zata kai iyayenta aljanna, manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce duk iyaye da suka haifi ƴaƴa mata guda uku, suka tarbiyantaddasu har suka aurar da su ba tare da waɗan nan ƴaƴa sun taɓa yin zina ba, to ba shakka sanadiyar haka Allah ya bawa waɗan nan iyaye aljanna, ƴan macece kawai take da wannan falala, amma a duniyarmu ta yau dayawan iyaye maza basu son a haifa masu ƴaƴa mata, ɗa namiji baya kai iyayensa aljanna kai tsaye, mace kawai Allah ya bawa wannan falala, ai ko dan kwaɗayin aljanna dole muso ƴa ƴa mata, idan ka duba sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, irin shekarun da suka shafe suna aikata aikin Allah ba dare ba rana kafin su sami aljanna, wasu daga cikinsu ma kashesu aka yi, wasu daga cikinsu kafurai sun azabtar dasu azaba mafi muni, idan ka dube su ka dubi ɗan aikin da kake yi, sai ka ji aljanna fa ba abar wasa bace, ba'a samunta a sauki, Allah dai ya bamu ita ba dan halayenmu ba, sai dai mu roki cin albarkacin fiyayyen halitta.
Karfe 6 dai'dai suka kammala girki, ita kuma Zainab ta kammala gyaran gida har ta yi wanka ta shiryo cikin white uniform ɗinta, kal kal da shi, ya sha guga malam, ta fito fes, Zainab sarkin farin jini, kowa ya ganta sai ya ce yana sonta, sai dai akwai ta da mugun hali in ji matasa da suke biyota bata kulasu, suka ce mugun hali ke gareta......... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce tsare mutunci da tsare kai dai, ba wani mugun hali munafukai, dan basu sami abin da suke so ba, bata kula kowa, ga shegen kyau jajir da ita, nan gani nan bari munafukai kawai.........😂😅
A parlourn suka zauna dan yin breakfast kamar yadda suka saba, Khadija ta wuce cikin bedroom nasu dan ta yi wanka ta shirya cikin uniform nata, ita kuma Maman Zainab ta wuce nasu bedroom ɗin dan ta taso baban Zainab ya yi wanka ya zo su yi breakfast, sai ya ɗauki su Zainab a kan mashin nasa zuwa makaranta, dama shi yake kaisu, lokacin tashi kuma sai ya bawa Sadiq key ɗin mashin ɗin daga kasuwa ya zo ya ɗauko su ya mayar da su gida sai ya dawo, islamiya kuma a kusa da gidansu yake, ba nisa sosai, so da kafa suke zuwa.
After some minutes
Gabaɗayansu sun haɗu a parlourn, baban Zainab ma ya yi wanka ya yi shirin zuwa kasuwa.
"Zainab ɗauki abincin su Sadiq ki kai masu". Cewar mamansu.
Babansu ne ya ce. "Ba na ce su zo su rinƙa ɗauka da kansu ba?".
"Yi hakuri na manta ne ban sanar da su su zo su rinƙa ɗauka ba, amma idan sun fito zan gaya masu, yanzu dai ta ɗauka ta kai masu".
Shiru ya yi bai sake magana ba.
Ita kuwa Zainab tamkar zata zunduma ihu dan bakin ciki, ga shi jiya ta yi wa Haidar rashin kunya ta gudu, yanzu in ta je idan ta yi knocking na kofar, in dai Haidar ɗin ne ya fito tasan confirm sai ya rankwasheta a kai ko kuma ya mareta, da dai Sadiq ne ya fito lafiya lou zai karɓi abincin ya koma ciki.
Rai a matuƙar ɓace tana hura hanci ta ɗauki kular abincin tare da plates ɗin ta fito.
Ta kuwa yi sa'a tana fitowa ta ci karo da Sadiq wanda ya fito a lokacin shi ma, ya fito zai fitarwa da babansu mashin nasa ne, yana shirye cikin white shaddarsa mai shegen kyau, ɗinki half jompa, ya sha hularsa, sai ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 75