Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fito a babban mutun mai kima da mutunci, yanzu yana da 28 years, sai ya fito a cikakken matashi mai cike da nutsuwa da kamala. "Kawu Sadiq ina zaka je?". Cewar Zainab ɗin. "Babu gaisuwa sai tambayar ina zan je ko?". Ƴar murmushi kaɗan ta yi, Zainab baka taɓa ganin fara'arta sai idan da Sadiq ko iyayenta or Khadijah suke tare, nan ne zaka ga tana murmushi. "Ai mantawa na yi, naga kayi kyau sosai ne yau shiyasa na manta da gaisuwar, to ina kwana". Ta kai karshen maganar tare da ƙarisowa gabansa. Hannu yasa ya karɓi kayan abincin yana amsa mata gaisuwar kafin ya ce mata. "Ina da class 7:30 dai'dai ne, yau ba kasuwa zan wuce kai tsaye ba, shiyasa na yi kyau haka, ko baki son na yi kyau ne?". Girgiza mashi kai ta yi tana faɗin. "Kawu Sadiq ai dama kai kana da kyau, ranar ba na gaya maka kafi mamanmu kyau ba? Baba ya ce mama dan ita fara ce kawai, da ita baka ce mummuna ce, wai ka fita kyau baba ma ya ce, so ko baka yi kwalliya ba dama kana da kyau sosai, yau ɗin ne naga kyanka ya karu sosai". Cool murmushi ya sakar mata kafin ya ce. "Bari maman ta jiki kin ce na fita kyau, idan ta rikeki ba mai karɓarki a gidan nan, kin san ko lokacin da muke gida kafin ta yi aure bata taɓa yarda ace na fita kyau, Allah ki bari ta jiki zaki yi bayani ne ba ruwana, yadda take jin ita kyakkyawa ce ɗin nan". Dariya sosai ta yi har sai da wishiryar dake tsakanin fararen hakwarantan ya bayyana. "Allah kawu Sadiq ka fi mama kyau sosai, amma na san mama da Oumma take kama shiyasa, kai kuma da Abba kake kama" Abba shi ne mahaifinsu Sadiq ɗin, kakansu namiji kenan, Abba suke ce mashi, kakansu mace kuma Oumma. "Kai, kai, kai, lallai Zainab yanzu kam ni ne zan zaneki, Oummar tamu ce kenan mummuna ko? Shiyasa da mamarki ta yi kama da ita ita ma ta yi muni ko? To baki isa ba wannan kuma, Allah duka zaki sha, ni Oummarta kyakkyawar gaske ce da babu biyunta a duniya, mamarki dai sai Allah kaɗai yasan da waye take kama". Ya kai karshen maganar yana fitar da wallet nasa daga aljihunsa. Sai dariya take yi tana kara gaya mashi Allah kakarsu mace mummuna ce, shiyasa mamarsu bata da kyau sosai sai hasken fata. Kuɗi 1k ya ciro ya bata, sannan ya juya ya nufi cikin ɗakinsu yana faɗa mata su yi breakfast da 1k ɗin idan sun je makaranta, dan yasan ƴan makaranta ba'a rabasu da saye saye na kwalama. Sosai ta yi mashi godiya sannan ta wuce izuwa cikin parlourn ita ma. A gaggauce suka karya, dan lokaci karfe 7 ta yi, kuma 7:30 dai'dai suke shiga cikin school kullum, babansu baya yarda su yi latti, yana kula da karatun nan nasu fiye da tunaninku. Bayan sun kammala sai suka fito harabar gidan da nufin tafiya, su Zainab kowacce ta goyo jakarta a baya, Mamansu ta rakosu harabar gida kamar yadda suka saba. Jin fitowarsu harabar gidan yasa Sadiq ya fito domin ya fitarwa da Baban Zainab ɗin mashin ɗinsa daga cikin kitchen ya kai mashi waje, haka suke yi kullum, shi kuma Haidar sarkin son girma yana ciki. Kun san jahilci tana tare da girman kai, girman kai kuma yana tare da shegen son girma kamar me, mutun mai ilimi wanda yasan abin da yake yi ba zai yi girman kai ba wlh, wannan sai jahili, to dai haka Haidar yake da bala'in son girma kamar menene, ga shegen girman kai rawanin tsiya. Ya fito da mashin ɗin harabar gidan kenan da nufin ya fitar waje, shi kuma Haidar yana ciki yana aikin zuba barci, dan shi kasuwar ma sai sanda ya tashi barcinsa yake zuwa, wani lokaci sai 11 na rana yake zuwa, shegen barcin safe ke gare shi. Murmushi ne a saman fuskar kowannensu, musamman baban Zainab, sai tsokanar Sadiq yake yi a kan ya yi kyau sosai yau dan ba Kasuwa zai je ba, wato zai je school akwai ƴan'mata a can shi ne ya tsara kwalliya ko?. Sai murmushi Sadiq ɗin ma yake yi yana cewa da ai shi babu ruwansa da mata. Maman Zainab kuwa ta ce ba wani nan idan ba dan ƴan'mata ba ai ba zai yi irin wannan shiga a kullum idan zai tafi makarantar ba, meyasa baya yi irin shigar idan zai je kasuwa? Sai dai ya ɗauki wasu tsofaffin kaya ya sa ya tafi kasuwar, makaranta kuma a tsantsara kwalliya. Zainab sai dariya take yi mashi tana faɗin Allah ya kama kawu Sadiq, yau asirinsa ya tonu. Khadija kam fuska kamar ko yaushe, sam bata a cikin walwala baiwar Allah. Sadiq bai kai ga fitar da mashin ɗin ba suka ga an banko kofar gidan an faɗo masu cikin gida. Zainab sarkin tsoro har ta juya zata zunduma cikin ɗaki da gudu, ita kuma Khadija da yake dama hankalinta baya a tattare da ita, sai bata wani tsorata sosai ba, Maman Zainab ma saura kaɗan ta zunduma da gudu izuwa cikin parlourn. Baban Zainab da Sadiq ne kawai basu tsorata ba, suna tsaye a yadda suke. Tun daga kofar gida ake surfa uban masifa, ba kowa bace face Maman Haidar, kakansu da kuma ɗayar ƴar babansu Zainab ɗin mai suna Zainab. Tun daga bakin kofar gida suke surfa uban masifa tamkar zasu tashi garin. Da sauri Mamansu Zainab ta juya da nufin ta wuce cikin parlourn abinta, dan ba zata iya masu ba. Sirikar tata ce ta daka mata tsawa a kan ta zo nan munafuka, ai wajenta suka zo, zata wani sa kai kamar wata tsohuwar munafuka zata wuce. Cikin girmamawa ta ɗagawa surukar tata gaisuwa da "Ina kwana". Cikin faɗa surukar tata ta ce. "Da ban kwana ba zaki ganni ne? Wato dama baki so na kwana a duniya ko? To na kwana na tashi, kuma ni dai nan gani nan bari, baku isa ku mallakeni ba, nafi karfinku". Shiru Khadija ta yi tana sauraron kakar tata, idan kakan nan nasu tana magana sai ka rasa ina ma ta dosa, sam maganarta babu kan gado, idan ba rashin kan gado ba yanzu me ya kawo wani zancen mallaka da kuma zancen wai Mamansu bata son kakar tasu ta kwana a duniya, daga cewa ina kwana? Abin ma abin dariya, ko me haɗin ina kwana da kuma ba'a son mutun ya kwana a duniya? Kawai jaraba ce da dole sai anyi faɗa. "Mama wai me yake faruw ne?". Cewar baban Zainab ɗin, ya yi maganar a nutse. "Rufe mun baki hai, ai yau wlh kome wannan matar taka ta yi maka ta mallakeka sai ta karya shi". "Sadiq ku je ka kai su Khadija makaranta daga nan ka ajiye mun mashin ɗin a kasuwa zan hau mashin ɗin kasuwa na je kasuwar". Cewar baban Zainab ɗin. A hanzarce Sadiq ya amsa tare da jan mashin ɗin ya fitar da ita waje, su Zainab suka rufa mashi baya da sauri. Ran Zainab kamar bakar leda saboda bakin ciki, zuciyarta sai tafasa take yi, kamar ta tsinke kakan nata da mari take ji, mata ce sai jarabar bala'i, sai ka rasa me matar nan take so a duniyar nan, kamar wadda ake sakawa battery, idan ta fara zuba bala'i ita da kanta bata sanin me take faɗa. "Mama mu je cikin parlourn koma menene sai mu tattauna a cikin nutsuwa ko?". Cewar baban Zainab ɗin dai. Ita dai maman Zainab bata da bakin magana. Cikin faɗa mamar tasa ta ce. "Kai har kana da ɗakin da zan shiga in zauna ne? Babu in da zan shiga sai wannan bakar munafukar matar taka ta gaya mun uban me ta yi maka ka lalace ka dawo mata soko sai abin da ta ce kake yi". Shi dai baban Zainab har yanzu bai gane a kan me mamar tasa take surfa wannan bala'in ba. "Maman Haidar wai me yake faruwa ne? Waye ya taɓo mama yau kuma?". Cewar baban Zainab, ya yi maganar kuma yana kallon Maman Haidar dake tsaye tana wani cika tana batsewa. "Ba gaka ga mamar ba, ai ita zaka tambaya, ni ka rai'na zaka tambaya ko?". Maman Haidar ɗin ta bashi amsa tana wani watsa mashi harara. Nisawa ya yi kafin ya mai do da kallonsa a kan ɗayar yayar tasa dake tsaye shiru tana binsu da ido. "Maman Hanif ke ki gaya mun wai meyake faruwa ne? Me aka yi wa mama? Ko me aka ce nayi?". Nisawa ita ma ta yi tare da fara magana a nutse. "Wata ce nan ta je ta gaya masu cewa wai jiya ka sayawa matarka tsadaddun lace da shaddoji da sauran kaya namu na mata, ta dai ce makwabciyarku ce ita, wai maman Zainab ta mayar da kai wani soko, kai ne kake yin sharar gida da komai da komai, maganganu dai dayawa ta gayawa mama, ni ina waje sama sama najiyosu suna tattaunawa da mama......". Katseta mamar tasu ta yi da cewa. "To karya aka yi mashi ne? Ai idan da baya yi makotansu ma ba zasu sani ba, abin da kika ga har makota sun sani ai kinsan ba karamar abu bace ba, abin ya yi yawa kenan". Dafe kansa ya yi, dan shi yasan ba wata matar da ta gaya masu, karya ne, Haidar ne ya kai masu wannan magana, dan shi ne mai kwasan duk abin da yake faruwa a cikin gidan yana gaya masu, kuma duk abin da Haidar yake yi mamarsa ta koya mashi, dan ita ce tun yana ƙaramin yaro idan ya je wajenta sai ta rinƙa tambayarsa me aka yi a gidansu Zainab ɗin, me yake faruwa a gidan, shiyasa babban kuskure ne idan yaronka ya je waje ya dawo ka rinƙa tambayarsa me aka yi a wannan gidan, ko me suka dafa da ya je, hakan ba ƙaramin mummunar dabi'a bace kake koyawa yaro. Ni kuma PRINCESS TEEMA shawarar da zan bawa mata a nan shi ne, kuskure ne ki bari wani daga cikin familyn mijinki da kike rikonsa ya rinƙa sanin halin da kuke ciki ke da mijinki, ke ko ɗan miji kike riko, kada ki yarda ki bari su rinƙa sanin me yake faruwa a gidan, ko kuma ya tukunyarki take, ace komai mijinki zai saya maki sai sun sani, ko cefenen gida sai sun san komai da yadda aka yi. Kun dai san abin da yake faruwa a gidansu Zainab ɗin nan kaf abu ne da yake faruwa sosai a cikin al'umma, amma dayawa daga cikin mata basu san daga ina matsalar take samo asali ba, na tabbata mata dayawan zasu gyara wasu abubuwa nasu a dalilin karanta labarin gidansu Zainab, dan labari ne mai cike da darusa sosai, ko ya kike da mutu kada ki bari ya san abin da mijinki yake yi maki na kyautatawa, kome zai saya maki ya zama sirrin ke da shi, kada ki nunawa kowa sai iyayenki da kannenki idan kina da su, domin duniyar yanzu wlh ta wuce tunaninki, ke zaki gayawa mutun abin alkhari da mijin yake yi maki dan ya tayaki murna da farinciki kin yi dace, baki san shi haushin ki yake ji kin sami abin da shi bai samu ba, hakan zai sa ya yi duk yadda zai yi ya shirya maki mugunta, dan tsabar bakin ciki da hasada, dan haka mata sai ku kula, maman Zainab tun farko ita ta yi kuskure, ita ta yi ganganci da ta sakewa Haidar fuska, ta kyale shi yana shigo masu har cikin ɗaki, duk abin da Baban Zainab zai yi ma matarsa da ƴaƴansa sai ya sani, kome suke ciki yana sane, a lokacin maman Zainab tana ɗaukarsa yaro, a duniyar yau wlh yara sunfi manya iya gulma da munafurci, ta yi sake ga shi yanzu abin ya kwaɓe mata ba yadda ta iya, abu ya fi karfinta, Allah dai ya kyauta ya kawo mata mafita. "Maman Hanif zaki iya gane fuskar matar?". Cewar baban Zainab ɗin, duk da zuciyarsa tana gaya mashi Haidar ne ya je ya kai masu rahoton ko ya kirasu a waya ya gaya masu cewa babansu Zainab ɗin ya dawo dasu laces and atamfofi a leda, sai dai bai isa ya nuna cewa yasan Haidar ɗin bane, dan idan ya ce shi ne to ba makawa wata ruwan bala'in ce zata sauko mashi, dan yanzu Maman Haidar ɗin zata yi tsalle ta dire ta ce ai ya zagan mata yaro, ita ma kakan ta hau kai ta zauna. Amsa maman Hanif ta bashi da cewa. "Matar sanye take da nikaf a fuskarta, ban ga face nata ba". Shiru ya sake yi yana tunanin irin wannan rayuwa, tabbas bai yarda da zancen Maman Hanif ɗin bama, ba wani bata gane wacece bace, gaya mashi gaskiyar cewa Haidar ne ya yi hakan ne ba zata yi ba, domin Haidar ɗin ne ya san cewa ya ɗauko atamfofi daga kasuwa, shi ne kuma yasan cewa ya sayo masu abubuwa na mata daga kasuwa, so dole shi ne ya kai rahoto. Kakar tasu ce ta katse mashi tunanin da yake yi cikin faɗa da cewa wlh dukka kayan nan da ya kawo ya yi maza ya kwasosu ya kawo mata dukka. Da yake zaman lafiya yake nema, sai ya ce da maman Zainab ta je ta ɗauko masu kayan, ya kudurci niyar zai kawo masu wani ba tare da sanin kowa ba, ko Sadiq ba zai bari ya sani ba bare Haidar. Da sauri Maman Zainab ta wuce cikin parlourn, sai kuka take yi hawaye bibbiyu, wannan jarabar bala'i dame ta yi kama? Kamar yadda ya kawo masu kayan a leda haka ta ɗauko ta fito masu da shi, dama can bata wani cire kayan daga ledojinsu ba, dama sun bari sai da safe ne su buɗe suga irin kayan da ya kawo masu. Tana zuwa ta duka ƙasa ta miƙawa sirikar tata. Cikin faɗa tasa hannu ta karɓa tare da cewa su Maman Haidar su wuce su tafi, sannan ta dubi baban Zainab ɗin cikin fushi ta ce maza ya sameta a gida, daga haka suka wuce fuuuu kamar wasu kumfaye suka nufi waje. Suna fita Maman Zainab ta saki wani marayar kuka tare da juyawa da sauri ta koma cikin parlourn. Bayanta baban Zainab ɗin ya bi, hakuri ya je ya rinƙa bata tare da yi mata alkawarin anjuma da rana zai kawo mata wasu kayan waɗan da suka fi wannan kyau. Cikin kuka ta ce ita ba kayan ne ya dameta ba, meyasa zasu rinƙa zaginta haka? Su zageta su zage iyayenta, laifin me ta yi masu?. Hakuri dai ya cigaba da bata, ba shi ya tafi kasuwa ba har sai da ya san ya sanyata murmushi ta cire damuwar a ranta, sannan ya fito ya nufi kasuwa, shi kuma Haidar sai zuba barci yake kamar wani gawa, duk wannan rigima da aka yi a cikin gidan sam bai sani ba, nauyin barci ke gare shi, idan ya yi barci kamar wanda ya mutu. Baban Zainab na tafiya ta rufe kofar parlourn da key ta wuce cikin bedroom nata ta haye gado domin ta ɗan yi barci, dama haka take yi, zata tashi tun asuba ta yi aiki, idan ta sallamesu suka fita sai ta kwanta ta yi barci zuwa 11, sannan ta tashi ta hau aikin girkin rana, dan karfe 2 dai'dai Sadiq zai zo ya ɗaukawa baban Zainab abinci rana zuwa kasuwa, su Khadijah kuma karfe 3 suke tashi makaranta. To bari mu waiwaya bangaren su KAMRAN, wato daji kuma muga me ake ciki tun da Maman Zainab ta yi barci. 🏞️FOREST🏞️ Tafiya Kamran yake yi cikin wannan shiga tasa dai da kuka sani, ya ratayo kwari da baka a bayansa, da alama farautar nama zai je yi, yanzu ya zama matashi, kyau da cikar haiba tare da kamala sun kara bayyana a tattare da shi, yanzu yana da 25 years, dan rabonsa da su twins yanzu shekaru 10 kenan, kirarsa na jaruman maza ya kara bayyana, Mamma ta iya reno sosai kam, cikakken jarumi ne mara tsoro, haka yake kutsa cikin wannan ƙungurmin dajin babu ko ɗar ɗar a tattare da shi. Sai tafiya yake yi Rocky yana gefensa, yanzu Rocky ma ya tsufa, ya zama wani bujumi da shi, ya kara girma sosai............. Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI. 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/7/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________10🔥 Sai tafiya yake yi Rocky yana gefensa, yanzu Rocky ma ya tsufa, ya zama wani bujumi da shi, ya kara girma sosai. Sai kutsawa cikin dajin sosai suke yi, da yake basu saba zuwa wannan yankin ba a cikin dajin, sai Rocky ya fara yi mashi alamar sun wuce dai'dai in da suke tsayawa fa, sun fara shiga wani yanki na daban, sai alama yake yi mashi ta hanyar tsayawa yaki tafiya. Sarai Kamran ɗin yasan me Rockyn yake nufi da shi, amma sai yaki kula shi, domin yau yana da burin ya tsalleke yankinsu ya shiga wani, dan shi ma dai ya kalli wannan dajin da kyau da kyau. Da dai Rocky yaga da gangan Kamran ɗin yaki kula shi, sai ya sha gabansa tare da ɗaga kai sama zai zuba wannan kukan nasu mai rikita dabbobin dake yankin. Hannu Kamran ɗin ya ɗaura mashi a saman kansa, still da wannan yare nasa dai ya yi mashi magana a kan cewa ya bari suje wasu yankuna koda guda biyu ne a cikin dajin dan suga abubuwa, wata kila akwai abin da akwai a sauran yankunan babu a nasu part ɗin, sai su ɗebo su kawowa Mamma. Girgiza jiki Rocky ya yi kafin ya wuce gaba, da sauri Kamran ɗin ya ce lallai ya dawo baya ko kuma ya dawo su jera a tare kamar yadda suka saba tafiya. Kin dawowa ya yi, sai ma cigaba da tafiya da ya yi. Shi kuwa Kamran kamar ya kifa mashi mari dan haushi, sai dai koya mare shi ma shi ne zai ji zafin hannunsa, Rocky kam babu abin da zai ji. Kamran yana matuƙar jin haushi idan suna tafiya Rocky ya wuce gaba, abin yana baƙanta mashi rai sosai, ya fi son shi ya yi gaba, a cewarsa idan Rocky ya yi gaba kenan tsaro Rockyn yake yi, shi kuma wai baya son ace ga wani yana bashi tsaro, yana ji da jarumta sosai, ya fiso ace shi ne a gaba shi ne jarumi. Cak suka tsaya a wani wani mai cike da dogayen itatuwa masu yelwar cikar ganyayyaki korayen shar, kasancewar itatuwar suna da tsawo sosai, sai cikar ganyayyakin jikinsu bai sa wajen ta yi duhu ba, sai ma hasken rana da ya bayyana ta tsakiyarsu, abin ya kawatar da mai kallo matuka, kasan wajen ya kasance farin yashi ne tamkar yashin bakin manya manyan tekuna na ruwa. Bin wajen da kallo Kamran ya fara yi, hakiƙa wajen ya yi matuƙar burgesa sosai, ga yanayin weather wajen is very very so nice, akwai yelwar ɗumi a wajen, tamkar ba a cikin dajin wajen yake ba, da yake dama dajin Allah mai girma haka ai sai abin da ka gani kawai, Allah ya yi ikonsa kala kala a ciki, duk abin da ka gani kawai ka gara jinjinawa iko da kudura ta Ubangiji. Shi kansa Rocky da yake yawace yawacensa son ransa, babu inda baya shi ga, tabbas wannan waje ta bashi mamaki kuma ta yi matuƙar burgesa. Shi dai Kamran yana zuwa bakin teku ya ɗebi wasu abubuwa daga cikin albarkatun cikin ruwa, amma bai taɓa ganin farin yashi (ƙasa) tas irin na wannan waje ba, dan wannan ya fi ƙasar bakin teku haske sosai, idan hasken rana ta haska yashin ma har wani kyalli sosai yake yi. Gabaɗaya ma yanayin tsarin wajen idan ka gani sai ka ji imaninka ya karu, domin babu ɗan adam da ya isa ya yi wannan halitta, yadda kasan a manyan wajajen buɗe idanu na duniya suke, tamkar ba'a cikin dajin ba. Duk da cewa Kamran bai san Allah ba, bai ma taɓa jin sunan Allah ba, bai san a akwai Allah ba, bai san akwai wanda yake halittar abubuwa ba, amma da ya zo wannan waje ya ji a jikinsa yana son sanin wadda yake halittar waɗan nan itatuwa da sauransu, saboda itatuwa ne irin masu bala'in tsawon nan, bai taɓa ganin irinsu a cikin wannan dajin ba, dan suna da tsawo sosai gaskiya, shi ne yasa ya ji cewa gaskiya yana son yaga waye ne yake gyara itatuwar nan haka? Waye mamallakin wannan dajin? Ya kuma kudurci niyar idan ya koma gida sai ya tambayi mamarsa, sai ya tambayeta ta gaya mashi wanene mamallakin wannan dajin? Dan a ilimin da yake da shi dai yasan abu bata kyara kanta, dole duk abin da ka gani akwai makerinta, musamman idan ya waiwaya ya dubi yadda Mammansa take kyara tukanen dafa abinci da taɓon da yake ɗebo mata, sannan ta kyara kwanikan cin abinci da katakon itatuwa da yake saro mata, hakan ce ta kara tabbatar mashi da cewa lallai komai da ka gani akwai wanda ya yi shi......... Toh fa, Kamran ya ɗauko babbar magana, kuma ya fara tunanin ta gaskiya, domin komai da ka gani a duniyar nan baya taɓa kyara kansa, masu cewa babu Allah kowaye ya halicce su?🤔 A barka da iya dutse ma kawai ka gaya mana waye ya yi ta?🤔 Ko kuma ka kawo wani ya yi ta mu gani, an dai ba zata kyara kanta ba kam, idan ka kai dubanka izuwa kan motoci da abubuwan hawa, dukkansu akwai waɗan da suka kyarasu, to sai halittun Ubangiji ne za'a ce babu wanda ya haliccesu dan kin gaskiya da son dole sai an shiga wutar jahannama?.🤔 To Allah ya kyauta ya kuma yafe mana zunubanmu ya kara ɗauramu bisa tafarkin koyarwan fiyayyen halitta. A hankali hankali kunnuwansa suka fara tsinkayo mashi sautin zubar ruwa sha tamkar ruwan sama. Dawo da kallonsa ya yi daga kallon wajen izuwa kan Rocky. Kasa kunne shiru suka yi dan su ji menene yake wannan shahhhh kamar zubar ruwan?. Karar tana ɗan nesa daga in da suke, hakan yasa Kamran ɗin ya kara gaba domin ya ga menene? Kai tsaye babu tsoro ko shakka ya nufi ta hanyar da yake jiyo wannan kara. Da sauri Rocky ya rufa mashi baya, haka suka cigaba da tafiya, sai dai a wannan karon tafiyarsu ta sauya daga ta jarumta izuwa ta mutumin daji, wato tafiyar sanɗo kenan, tamkar wadda yaga wata nama zai farauceta, saboda basu san me yake wannan kara ba, gada ya zamana sun dimfari abin gadan gadan kuma ya fi karfinsu, gara koma menene su yi mashi tafiyar mage mai kwanciyar ɗaukar rai, idan yaso in sun ga menene, sai su san abin yi. Kara matsowarsu ta in da wannan kara yake tashi ne ya bawa Kamran ɗin damar fahimtar cewa lallai ruwa ne yake zuwa daga ƙoramar dutse, duk da cewa babu irin wannan ƙoramar dutse dake zubar da ruwa a yankinsu, amma Kamran ɗin yasan da akwaita a cikin wannan dajin sosai, dan idan ya tsaya a saman ɗaya daga cikin tsaunikan dake ta kusa da su yana iya hango koraman dake kusa da yankinsu, waɗan da suke zubar da ruwa, sai dai kanana ne waɗan da suke kusa da su, ba katafare tamkar wannan da yake karan bane, su waɗan can ma ba zaka ji karar ruwan sosai ba, amma shi wannan karar ruwan tun daga nesa kunga suka fara jiyo shi, alamu sun nuna katafaren ƙorama ne sosai. Jin

Chapter 12 of 75