Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da Mammie ɗin ba sai ga wata kuyanga ta doso katafaren parking space ɗin hannunta na rike da leda. Ƙasa ƙasa ya ce da driver ya fita ya karɓo mashi hijabin. A hanzarce ya amsa da okey sir tare da ɓalle marfin motar ya fito da sauri. Kuyangar bata ƙariso wajen ba ya yi saurin isa in da take ya karɓo hijabin a cikin ledarsa, da alama sabo ne gal. Tun daga yanayin nauyin hijabin a cikin leda zaka fahimci babba ne sosai, hakan ne kuma, ko da driver ya kawo hijabin Yah Jawad ya karɓa ya miƙa mata a kan ta sanya a jikinta, tana ciro shi sai taga ya fi karfinta wannan hijabi, zai ja mata har ƙasa sosai. Ɗago idanu ta yi ta kalle shi, sam kallonsa baya a kanta, hasali ma idanuwansa a lumshe suke, bata da zaɓin da ya wuce ta sanya wannan zunbulelen hijabin haka a jikin nata. Kamar zata yi kuka ta ware ta sanya, ya yi mata yawa over, harta wuyar hijab ɗin yafi karfinta, sai zamewa yake yi yana sulluɓewa ƙasa, ga gashin kanta dama da masifar tsantsi. Haka dai ta kai hannu ta rike wuyar dan kada ya zame, sai satar kallonsa take yi ko zai ce a canzo mata wani, amma ina idanunsa a lumshen nan yaki buɗesu kawai ya bawa driver umarnin ya wuce da su hospital. Ba ɓata lokaci ya karɓi umarnin tare da kunna motar suka nufi asibitin nasu. Yah Jawad bai sake bi ya kanta ba har suka isa. Katafaren hospital ne na gani na faɗa, kusan za'a ce ma da wuya a sami hospital mai girmansa a ƙasar, manya manyan masu faɗa aji a ƙasar ne suke kwanciya jinya a cikinta. Abin mamaki dai baya karewa, da Yah Jawad suka shiga cikin hospital ɗin kuma sai yaki yarda likita namiji ya duba mashi kanwar tasa, wai sai dai mace ta dubata, ita dai tana fama da zunbulelen hijabin wadda ko matar limamin masallacin jumma'ar ƙasar saudiya bata saka kamarsa, ko kula shi shi da Drs ɗin ma bata yi ba, bama ta fahimtar me suke faɗa ba, ta dai kwantar da kanta shiru a saman gefen shoulder ɗinsa tana sauke numfashi a hankali hankali, duk gudun kada shessheƙar kukan da take yi ne ya bayyana, ya ja mata yanzun nan ya sauketa ya ce ta tafi da kafafunta, dan ƙaramin aikinsa ne ya sauketa ƙasa ya ce ta taka kafafun, hakan yasa ta kwantar da kanta shiru tana jin bakin ciki kamar ta shake shi, ya iya mugunta. Shi kuwa sai da ya zaɓi nurse ɗin da ta yi mashi, sannan ya buƙaci ɗaki domin ya kwantar da ita wannan nurse da ya zaɓa ta duba ta. Gabaɗaya ɗakunan da suke a cikin wannan katafaren hospital ɗin ba ɗakuna ne kamar ɗakunan sauran hospitals da kuka sani ba, waɗan nan ɗakuna sai ka rantse da Allah ɗakunan gidan wani ministar or governor ka shiga, saboda manyan kai ne suke kwanciya jinya a cikin hospital ɗin, kowane ɗaki ka shiga ɗauke yake da katafaren bed 6/7 wanda ya sha shinfiɗu na alfarma, sai ka rantse da Allah ba hospital bane, dan wasu shegun bed sheets dake saman beds ɗin ma kawai abin kallo ne, ga lafiyayyun freezers, Ac, kai harta shi kansa tiles na cikin wannan hospital ɗin na musamman ne, curtains da sauran kayan alatu na more rayuwa duk na musamman ne, kamar ba wajen yin jinya ba. Ka kwararrun likitoci da kuma kayan aiki masu inganci wanda ake kawosu daga kasar China, idan aka kwantar da kai jinya a wannan hospital ɗin kuma kaga baka sami sauki ba to sai in ciwon ajali ne wanda shi kuma bashi da magani ko kuma wani ikon na Allah, likitocin wannan asibitin kamar mayu haka suke, sun kware wajen iya aiki ne babu wasa. Hospital ɗin hawa har biyar ne, so da haɗaɗɗe kuma tsadadden elevator suke amfani. A hawa na biyu aka bawa Chuchu ɗaki, can Yah Jawad ya nufa da ita. Yana kwantar da ita a saman katafaren bed ɗin da za'a dubata wayarsa ta fara kara alamar shigowar kira. Zama ya yi a gefen bed ɗin tare da ciro wayar tasa. Jaish ne yake kiransa a kan ya zo su wuce office. Shiru ya ɗan yi yana kallon call ɗin har sai da ta katse, sannan ya ɗan saci kallon Chuchu ta wutsiyar idanunsa kafin ya fara rubutawa Jaish ɗin sako kamar haka. Daddy and Akka sun sakani aiki, just go kawai sai mun haɗu da yamma. Yana gama rubutawa ya tura mashi, sannan ya kashe wayar tasa ma mai gabaɗaya ya zura a aljihunsa, sai ya ciro ɗayar wayar kuma ya fara latsawa. Nurse manyan mata biyu ne suka zo suka fara duba Gimbiya Chuchu, yana zaune a in da yake bai motsa ba, duk abin da suke yi yana kallonsu, sam hankalinsa baya a kan wayar da yake katsawa, ya dai rike wayar ne kawai, amma a zahirin gaskiya hankalinsa yana a kansu. Gimbiya Chuchu tana son ta yi kuka saboda zafin da kafar tata take yi mata, amma kuma tana tsoron yin kukan, dan kada Yah Jawad ya kara nata wani punishment ɗin, idan baku manta ba ya ce idan ya sake kamata tana kuka sai ya hukun tata, hakan yasa ta nutsu tsit baiwar Allah, tana jin yadda waɗan nan nurse ɗin suke mammatsa mata kafafun nata, har zogi yake yi mata, sai aikin tsuke fuska da ɗan bakin nan nata take yi, amma babu halin yin kuka. Duk kuma abin da take yi a kan idanun Yah Jawad ɗin take yi, yana kallonta sarai, amma sai ya yi kamar bai san tana yi ba, dan mugunta, ko irin ya ce mata sorryn nan babu. A ɓangaren Gimbiya Sarina kuwa, shiryawa ta yi cikin shiga na alfarma, ta fito a ainahin jinin sarautarta, kyau iya kyau, kayan jikinta wasu shegun tsadaddun kaya ne masu bala'in kyau Dubai make, goduwar riga ce ta ƴaƴan sarakuna, sai haɗaɗɗen alkyabbarta launin pink color, ta fito ras da ita, wlh ko baka so in dai ka kalli Gimbiya Sarina ta ci kwalliya to fa sai ka fola, shegiyar kaya ce, ta san kan duniya, idanunta a buɗe suke, wannan idan namiji ya shiga hannunta sai ta Allah, ko mata ƴan uwanta idan ta fito sai sun kalleta sun sake waigawa bare kuma maza, bata cika yin dressing da ya yi dai'dai da addinin musulunci ba, yawancin shigarta na turawa ne, sai dai idan a cikin masarauta take takan ɗaura alkyabbar a kan shigar tata gudun kada ta haɗu da su Jawad su saɓa mata kamanni, amma idan ta bar masarautar ko ziyara ta je wajen yan uwan mamanta ko kuma school ɗinsu, to fa ta soke sanya alkyabba, shegiyar kaya ce ta gasken gaske, ta wuce yadda kuke tunani, bata tarayya ko abota da mutun sai mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira kamar twins Obaid and Omaid, kuma ita ɗin zata iya amfani da kai ta cinma burinta ba tare da ka sani ba, wayo gareta kamar dila, shiyasa da uncle Abbas ya lura da wayewarta ya fi shekarunta yasa yake son aurar da ita, bata bin maza, kai bama ta kula namiji duk haɗuwarsa da iliminsa ko kuɗinsa, ko ɗaga idanu bata yi ta kalli namiji, dan tana da wani abin da take shiryawa ranta za'a ce ne ko mamarta take shirya mata ne oho masu. A ɓangaren mahaifiyarta kuma burinta kawai shi ne da Sarinar da Fanan ɗin duk su auri ƴaƴan King Zuhair, saboda idan baku manta ba ita mamansu mayinwaciyar mulki ce, tana son taga ƴaƴanta a kan kujera mai matsayi, shiyasa take ƙoƙarin taga yayanta sun auri koda ɗaya daga cikin Prince na masarautar ne tunda uncle Abbas dai ya ce siyasa yake da ra'ayi. Kamar yadda ake tarban baki a gidan sarauta haka aka tarbi Yusuf Abdulaziz Takur wanda ya zo da abokinsa guda ɗaya mai suna AL Amin Muhammad Zayyad. A katafaren masaukin baki da yake ta ɓangaren King Zuhair aka sauke su, an kawata parlourn ya sha kyau, sai tashin kamshin yake yi, ga kayan cima kala kala wadda a kallah zasu kai kala 10 da aka shirge masu a sama katafaren dining table dake a cikin parlourn. Yusuf dai ya sami tarba ta musamman, dan uncle Abbas da kansa yasa aka shirya mashi abubuwa da dama, sai dai lokacin da ya zo uncle Abbas ɗin yana tare da King a fada, so kai tsaye masaukin da aka tanada masu aka wuce da su. Wlh babu laifi, Yusuf haɗaɗɗen matashi ne kuma lafiyayye mai jini a jika, kyakkyawa ne ga shi dogo da shi, duk in da ake neman cikakken namiji mai kamala da riƙo da addini to Yusuf ya kai nan, bashi da makusa, haka zalika abokin nasa ma, basu da makusa, ga naira ta zauna masu, wasu fresh da su kamar suma jinin larabawan ne. Tun da ya shigo cikin parlourn yake ta faman raba idanu ta ina zai ga tauraruwar tasa, haƙiƙa yana son Sarina sosai, ya sha suit ɗinsa launin navy blue mai bala'in tsada, kafafunsa suna a cikin cover shoe masu kyau, bashi da yelwar gashin kai sosai, amma ya sha gyara yana kwance luf gwanin birgewa. Sai raba idanu yake yi yana jira yaga isowarta, abokin nasa ma burinsa ya ga isowarta kawai, dan Yusuf ya gama zuzuta masu kyanta, kuma ba karya ya yi ba, jinin Akka ba dai kyau ba, sun haɗu ne, bare ƴan'mata masu tsantsara kwalliya irin Chuchu, Zunairar da kuma Sarinar, ai idan ka yi ido biyu da su sai ka kalla ka sake waigowa, idan ma baka yi hankali ba a garin kallonsu ka je ka faɗi ƙasa. Sautin takalmarta mai uban tsini ne ya fara dakar dodan kunnuwarsu, fuska ba yabo ba fallasa, irin waɗan nan high heel masu tsawo sosai ɗin ta sanya, gata da tsawo dama, sai dressing ɗin nata ya kara kawata idanun mai kallo, ta fito sosai fa ba karya. Tafiya take yi tamkar wata hawayniya, kamar bata son taka ƙasa, tana sanya kafafun nan nata ɗaya bayan ɗaya a ƙasa, kai daga ganin tafiyar kasan ba yau bane farau, ta saba yin wannan shu'umin tafiyar mai ɗaukar hankali. Ga wasu kuyangunta biyu da suke binta a baya, ɗaya hannunta rike da kwando mai shake da kayan fruits, ɗayar kuma hannunta rike da wani katon try mai ɗauke da wasu shegun haɗaɗun cup's masu bala'in kyau, ga robar ruwa a shirye a saman, ruwa ne masu sanyi sosai, duk kayan cima da aka shiryawa su Yusuf ɗin a parlourn basu isheta ba, saboda munafurci dan ta nuna cewa tana son shi kamar yadda suka shriya da su Obaid yasa ta zo mashi da wasu, irin ta nuna shi na musamman ne a wajenta, waɗan nan Team ɗin sai dai shirin Allah na gaya maku, sun san kan duniyanci........😅 Duk in da ta wuce sai kuyangu sun zube ƙasa domin kwasar gaisuwa, amma kamar kashi haka take wucesu, sai ma yamutse fuska da take yi idan ta gansu kamar wadda ta kalli kashi, akawai ta da izzar bala'i tare da jiji da kai yarinyar. Tana sako kafafunta a cikin parlourn Yusuf ya miƙe tsaye, kawai ido ya kafeta da shi yana kallonta daga sama har ƙasa. Ita kuwa da yake ƴar duniya ce sai ta basar kamar bata san yanayi ba, ta cigaba da wannan ɗan iskan takun nata mai tafiya da tunanin mutum. Shi kansa abokin Yusuf ɗin sai da ya miƙe tsaye yana kallon tsantsar kyan da Allah ya yi mata, bayin Allah sun faɗa tarkon jinin Akka, sai dai Allah ya fitar da su. Takowa ta yi har izuwa wajen tsala tsalar sofas na parlourn, kamar ba ta kalli Yusuf da ya saki baki yana kallonta ba, zama ta yi a saman ɗaya daga cikin sofas ɗin, ko da ta zo zaman ma sai da ta yi wani rangwaɗa mai kara birkita tunanin duk wani lafiyayyen namiji, sam bata sanya idanuta ta kalli Yusuf ɗin ba har sai da ta zauna a saman sofa ɗin. "Kana iya zama yanzu ai malam Yusuf". Ta faɗa cike da izza sosai a muryarta, ka kwainane da kisisina, tana magana tana wani dakewa. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke kafin ya iya komawa saman sofarsa ya zauna. "Barka da isowa gimbiya kuma tauraruwar mata". Ya faɗa muryarsa cike tab da tsantsar so da kuma kaunarta. Wani irin ɗan iskan shu'umin murmushi kaɗan ta saki wanda ya kara fito da tsantsar kyanta, hakan kuma ya kara tafiya da imanin bawan Allah Yusuf. Shi ma abokinsa ya ƙasa iya kawar da kallonsa daga kanta, gata ƴar caras da ita. Juya waɗan nan fararen dara daran idanuwan nata ta yi kafin ta ɗan ja gajeran numfashi. "Yauwa barka dai malam Yusuf, fatan ka zo lafiya?". Ina ai ta gama tafiya da imaninsa, kara rikicewa ya yi a in da ya amsa mata da lafiya lou da hanzari. "Bari na zuba maku ruwan sha ko?". Ta faɗa ba tare da ta kawar da waɗan nan shegun idanun nata daga kan Yusuf ɗin ba. Da mamaki kuyangun da suka rakota suka bita da kallo, wannan yarinaya akwai shegen makirci, ita da ko kanta bata zuwaba ruwan sha idan zata sha, komai yi mata kuyangun nata suke yi, bata son yin aiki ko kaɗan, amma wai take cewa bari ta zuba mashi ruwan sha? Duk dan ace tana son shi kenan? Kai Sarina duniya. Ni ko na ce ko ina su twin's? Ko me suke shiryawa Yusuf bawan Allah? Ga shi dai ya gama afkawa gogin sonta, sai Allah sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA ne kawai yasan me waɗan nan Team ɗin suke shiryawa, sai mun haɗu da ku gobe idan mai dukka ya kai mu, amma fa akwai kallo ba kaɗan ba, dan nasan za'ayi dirama a cikin wannan KINGDOM ɗin yau, dan haka ku gyara zama!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 25/7/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________22🔥 Malam Yusuf dai ya ƙasa iya cigaba da magana, kallonta kawai yake yi, ikon Allah ikon gaske, abokinsa da ya zo rakiya ma sai kallonta yake yi, wannan da a tare suka ganta to ba shakka zata raba abotansu, dan sai sun yi faɗa a kanta, yanzu ma waye san gaibu? Ai sai Allah, bamu san me gaba zata haifar ba, amma dai koma me wannan abokin ya faɗa dayawa, Allah kaɗai yasan me yake tunani a cikin zuciyarsa kuma. Saboda shegen makirci irin na Sarina har da ɗan saukowa ƙasa kaɗan ta hau zuba masu ruwa yadda kuka san irin tana son shi kamar ta cinye shi ɗanyen nan, shi ma ya zaci haka ne, har da wani cewa. "Gaskiya na jima ban shiga farinciki irin na yau ba, bana jin kishin ruwa, amma saboda ke ce zaki zuba mun ruwan ko dukka kika ce na sha zan shanye". Ya yi maganar a nutse, da alama yana da nutsuwa sosai. Wani ɗan iskan shu'umin murmushi ta yi mai kara rikita mutun, a zahirin gaskiya saboda ma bata saba da yin murmushi ba, sai yazama sam murmushi bashi da gurbin zama a saman face ɗinta, ko ta yi baya yi mata wani kyau, amma da yake malam Yusuf sabon shiga ne, sai yazamana shi murmushin nata ya zama mashi wani abin na musamman, kuma sai yake ganin kamar idan ta yi murmushin nan har wani haske parlourn yake karawa.......... E ba shakka kai kam ka shiga tarkon Team ɗin nan na marasa jin magana, duk kuma wanda ya shiga hannun waɗan nan team ɗin to wlh sai dai Allah ya fitar da shi, yara ne yadda kuka san babba mai shekaru 50 wanda ya sha gwagwarmayar rayuwa ne yake shirya masu plan, ba zaka taɓa yarda cewa su ne suke shirya wasu abubuwa ba, saboda abin ya wuce tunanin mutun, idan zasu yi mugunta sai su juye su zama na Allah, su zama mutanen kirki, tsabar kuma sun iya basajan idan suka zama mutanen kirkin ma ba wanda yake iya ganewa, kai waɗan nan yara idan suka girma kada ka yarda ka shiga hannunsu, dan mutuwa ba makawa zaka yi. Cikin tsantsar rangwaɗa mai jan hankalin ta miƙewa Yusuf cup mai ɗauke da ruwan da ta zuba mashi. Bawan Allah jiki na rawa ya karɓa, tuni ya kai bakinsa ya fara sha yana zuba mata godiya. Haka ta sake zubawa ta miƙawa abokin nasa ma. A hanzarce shi ma ya kai hannu ya karɓa, daga yanayin yadda take zuba wannan ruwa ma kawai ya isa yasa ka fahimci bata iya aikin siɗiɗi bare saɗaɗa ba, kawai iyayi ne. Saman sofar ta koma ta zauna tare da ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, cikin wata iriyar voice mai sanyaya zuciyar mai sauraro ta fara magana daki daki. "Malam Yusuf ka sauko ku ci abinci, ga abubuwa nan mun tanada maku". Irin wannan voice da ta yi magana da shi ɗin nan sam ba zai iya tsalleke tayinta ya ce ba zai ci wannan kayan cima ba, dole ya amsa mata da. "Okey gimbiyata". Wani irin fari da ido ta sake yi mashi kafin ta ce da kuyangunta dake tsaye ta bayansu su zuba mashi abin da yake ra'ayi, dan a gaskiya bata iya serving na abinci ba, ruwan ma da yaya ta yi? Already kun san ita ko tsinke bata ɗagawa, komai sai dai ayi mata, so bata iya ba, shiyasa tasa kuyangun su yi masu. A hanzarce suka karɓi umarninta, ba ɓata lokaci suka zo suka fara serving ɗinsu, a wannan lokacin ne kuma Yusuf ya sami damar iya gabatar mata da kansa tare da abokin nasa da suka zo a tare. Bawan Allah abokin nasa bai yi kasa a gwiwa ba kuma bai bari kansa ya yi marfi ba ya yi maza ya ce. "Gimbiyarmu Please kina da sister? Allah dai yasa ba ke kaɗai bace". Ba tare da ta kalli in da yakeba ta bashi amsa, idan baku manta ba ita bata cika ɗaga idanu ta kalli mutane ba, bare ma kuma mutanen da ta raina class ɗinsu, ai gani take yi ma kallonsu kamar ɓata idanuta zata yi, hakan yasa sam bata kalli in da yake ba, shi ma Yusuf ya ci sa'ar akwai abin da aka shirya mashi ne yasa ake kallonsa, ba dan haka ba ina mai tabbatar maku Sarina ba zata ɗaga idanun ta kalli in da yake. "Yes ina da sisters ma dai ba sister ba, sai dai sun tafi school, amma idan kana son ganinsu sai na nuna maka pic's ɗinsu ai". Cikin rawan jiki kamar wani mazari ya buƙaci da yana son kallon hotunan sisters ɗin nata, dan har ga Allah ya afka kogin madarar kaunar jinin Akka....... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce aikuwa kana ruwa, dan ba Sarina ba, duk wanda ya ce zai yi soyayya da jikokin wannan tsohuwa in ma mace or namiji wlh yana ruwa, dan wasu murɗaɗɗun mutane ne, ko Zunaira da kuke gani kamar shiru shirun nan idan aka zo batun maza bata da daɗin sha'ani, bare su hjy Chuchu, duk kusan haka suke, babu wanda ya taɓa kula wani namiji a cikinsu, gani suke yi ma kula maza zubar da class ne, bare ma Aneesa ƴar Mama, ita ma kusan halinta ɗaya da Sarina a ɓangaren rai'na mutane, Fanan kuwa cewa ta yi sai ta samu namiji kamar yayansu zata yi aure, yayansu wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya nake magana, yayan Jawad mai suna Rizwan kenan, yana ƙasar Dubai, to shi ne wai sai namiji irinsa idan ta samu zata yi aure, ko shi ɗin wani irin hali gare shi da yasa ta ce sai irinsa zata aura? Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA, koma wani irin hali gare shi lokaci ne zai nuna mana, ga shi kuma yayanta ne uwa ɗaya uba ɗaya bare ace a haɗasu aure kawai, hakan ba zai yi wu ba. Wayar Mammie ɗinta da yake a hannunta ta ciro ta fara duba mashi hotunan su gimbiya Zunaira, ko a jikinta bata damu ba zata nuna mashi hoton, dan tasan idan ma a cikin ƴaƴan King ne wato su Chuchu, Zunaira or Aneesa zai zaɓa ya yi a banza, dan wlh bai isa ya tinkari King da wannan zance ba ato. Fito mashi da hotunansu a lokacin da Gimbiya Chuchu ta kammala primary school zata shiga secondary ta yi, a lokacin sun shirya gagarumin party sosai, an gayyaci manya daga ƙasashe da dama, sun sha kyau iya kyau, an yi hotuna anyi kyaututtuka da abubuwa daban daban, so iya waɗan nan hotuna na partyn kawai ne a wayar Mammie ɗin nata, dan na gaya maku ita Mammie ba kaunar jinin King take yi ba, har ga Allah bata son su Zunaira, kawai dai dan ba yadda zata yi ne, amma ta tsanesu kamar ta kashesu, wanɗan nan hotuna da kuka ga ta ajiye su a wayarta ma ta ajiyesu ne saboda akwai ƴaƴanta Sarina and Fanan a cikin hoton, da na su Zunaira ce kawai wlh ba zata ajiye ba, tsab zata gogesu munafukar mata. Miƙa mashi wayar ta yi a kan ya karɓa ya kallesu, a dai'dai lokacin kuma su kuyangunsu suka gama zuba masu abincin. Ƙasa saman haɗaɗɗen carpet ɗin suka sauko domin fara cin abincin. Hannu ya kai ya karɓi wayar domin ya kalli hotunan. Yusuf kuwa abincin ya fara ci domin ta gaya mashi idan ya ci zata yi farinciki, ya ce ta sauko su ci tare, ta ce tom su fara zata sauko. Shi kuwa Abokin nasa yana kyallah idanu yaga hotunan taurarin King Zuhair haba sai ya ruɗe, idanuwansa suna a tsaye kyam a kan Gimbiya Zunaira ƴar auta, shi ai yaga mata, ina sai ya ga ashe Sarina ma ba wata kyakkyawa bace idan aka dangantata da Zunaira da kuma Chuchu, sun fita kyau nesa ba kusa ba, sai dai Zunaira karamar yarinya ce, kuma shi baya jin kamar zai iya jiranta ta girma, yanzu yana da 28 years a duniya, ita kuma 11, ace ya jirata nan da shekaru 7 zuwa 8 haka, gaskiya da kamar wuya, ita ma dai Chuchu koda ya ce yana so zai yi jiran shekaru 4 zuwa 5 kam, dan 14 years ke gareta, Aneesa mai 15 years ma nawa take? Duk cikinsu dai Fanan ɗin ce sai kuma Sarinar suka isa aure, shi kuma Fanan bata yi mashi ba, dan kyawun Gimbiya Zunaira da Chuchu sun dishashe kyan kowa da yake a cikin hoton, su biyu ne taurarin da suka haska kowa, so shi a ɗaya daga cikinsu yake so a bashi mata. Taɓa shi Yusuf ɗin ya yi yana faɗin. "Ya dai? Bata yi maka bane?". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Yi kai, ai ni naga mata". "To mu gani". Yusuf ɗin ya faɗa. Miƙawa Sarina wayarta ya yi yana faɗin. "A'a ba zaka gani ba, kai baga naka Gimbiyar a gabanka ba? Me kuma zaka ce zaka ga wata? Gaskiya ban yarda ba". Yaki nuna mashi su ne kawai dan yasan yana ganinsu zai kallin kyan Sarina ya dishashe a idanunsa kamar yadda ya gani a yanzu shi ma, hakan yasa ya ki bashi ya gani. Ko a jikinsa Yusuf bai damu ba, shi dai Sarina kawai yake kallo abinsa. Ƙasa saman carpet ɗin ita ma ta sauko, duk dan ta nuna mashi kulawa ta kuma nuna yes tana kaunarsa, shi kuwa ya saki baki ya

Chapter 29 of 75