makamai su fara sace sace suna addabar al'umma, wlh da kowanu uba tun farko yana kula da ƴaƴansa ya sakasu makarata ya basu ilimin addini dana boko, to wlh da yau babu ɗan iska ko guda ɗaya a duniya, duk ƴan iskan nan jahilai ne, ba Arabic bare boko, wani ko karatun fathiha bai iya ba, kuma ya girma ya zama matashi an fara rubuta mashi zunubi, ba gasu nan zube a layi ba, sai anyi magana kuce annabi ya ce a hayayyafa dayawa dan ya yi alfahari da al'ummarsa ranar gobe kiya ma, tambayata a nan shi ne da ƴan iskan annabi zai yi alfahari ne? Ai wlh ka haifo ƴan iska sai dai ka je cikin kabari kana kwance kana fama da azaba su kuma suna duniya suna kara labto maka wata azabar, wlh kasani in dai baka bawa ƴaƴanka tarbiya ba, to duk abin da zasu aikata kana da kaso a ciki, kana kabari kana karɓar azabar da suke aikatawa a duniya, ka je lahira Allah ya ce maka ya ka yi da amanar da ya baka? Nan idan baka bada amsar da ake buƙata ba ka sake karɓar wani sabon gashi na musamman, annabi bai ce kowa ya haifi ƴaƴan da ba zai iya kula da tarbiyarsu ba, ko shin kansa karin aure annabi ya ce in kasan ba zaka yi adalci ba ka tsaya a kan guda ɗaya, domin kuwa in dai ka yi rashin adalci aranar gobe kiyama a mai shanyayyen ɓari guda na jikinka zaka taso, amma sai kaga wasu shaiɗanun mazan da sun kara aure uwar gidansu da suka sha gwagwarmaya a tare ta zama bola kayan banza, su rabu da ita tana gantali tsakanin layi da gidajen maƙota dan neman abin da zata ci ita da yara, su watsar da yara su gasu bunsuraye iyayen son mata, wlh ku ji tsoron Allah, abu guda ɗaya Ubangiji ba zai manta ba sai ya tambayeku, idan ku kun manta shi Ubangiji ba zai manta ba, duk sai ya bi ɗaya bayan ɗaya ya tambayeku, Allah dai kasa mu dace.
(Yau dai za'a ga rubutun alƙalamin nawa ta yi zafi, abin ne yana bakanta mun rai in ga yadda maza suke walaƙanta mata a kan karin aure, wannan abin da ciwo yake wlh🥲 Allah dai ka haɗamu da abokan zama na gari masu ƙoƙarin bin tarihin manzon Allah kuma suna koyi da shi tare da litattafan musulci haɗi da Alqur'ani mai girma.)
Mu koma kan labarinmu.
Idan ran maman Zainab ya yi dubu to fa ya ɓaci a wannan lokaci, wani irin tukukin bakinciki ne ya taso mata daga ciki ya tsaya mata a wuya, zuciyarta har wani irin tafasa yake yi mata, sam bata san lokacin da ta ce mashi.
"Allah zai saka mun duk abin da suka mun, na so su, na kaunacesu tsakani da Allah, babu abin da na yi masu, babu abin da na tare masu, Allah ya gani ina yin iyakacin bakin ƙoƙarina wajen ganin na yi komai na tsakanina da Allah, amma me nayi masu da suke son sai sun cutar dani a rayuwata? Me nayi masu? Ya Ubangiji kamun sakayya cikin gaggawa!".
Tana magana tana hawaye, ta kai karshen maganar tare da miƙewa tamkar zata faɗi kasa, saboda tukukin bakin ciki, a hanzarce ta wuce izuwa cikin bedroom nata tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Already baban Zainab yasan za'ayi hakan, fin haka ma ya yi tsammani, dan yasan ta tsani kishiya, bata son maganar, yanzu shi yana cikin wani hali, duk ta in da ya je babu sauki, maman Zainab ta yi fushi, mahaifiyarsa ma ta fusata, kota ina babu daɗi, duk sai ya ji ba zai iya komawa kasuwar bama, haka zali ka ba zai iya tunkarar Maman Zainab a yanzu ba, zai barta ne sai ta huce kaɗan, yanzu ko ya tunkarata ba zata saurare shi ba, ba kuma zai sami abin da yake so ba, idan ba sa'a bama sai su yi faɗa sosai a tsakaninsu, shi mai ilimi ne, yasan idan ran mace ya ɓaci to kada ka tunkareta a lokacin, dan zaku yi ɓarattciya ne kawai, saboda a lokacin kome zaka gaya mata ba zata fahimta ba, idan ka samu ta saurareka ma kenan, zuciyar mace karama ce, kuma a kusa zuciyar take, idan ranta ya ɓaci babu abin da ba zata iya aikatawa ba, sai dai daga baya ta yi dana sani.......(Kamar aljanu haka muke idan ranmu ya ɓaci😅😅😅 mun san komai 🥱)
Dan haka sai ya koma ya kishingiɗa a saman kujerar yana tunanin rayuwa, kansa sai wani irin sara mashi take yi tamkar zata fashe gida biyu, har wani irin jiri yake gani, idanuwansa duk sun yi jajir saboda ɓacin rai, ya rasa me yake yi mashi daɗi a duniyar nan, bugu da ƙari ga auren Khadija and Haidar, sannan ga shi mamarsa ta ce nan da wata ɗaya da ita da amarya zasu koma sabon gidansa in da ya ci burin ya rayu da maman Zainab rayuwa mai daɗi, dan ta juri akwai da babunsa, ta zauna da shi tun yana talaka bai da komai, kai akwai lokacin da ita ma take ciyar da shi, harta maman Haidar ta ciyar, amma saboda rashin godiyar Allah shi ne suka saka mata ta wannan hanyar, abin sam babu daɗi, ya so ya aurar da Khadija da Zainab ga nagartattun maza da suka san ciwon kansu, sai ya zauna daga shi sai mamansu a sabon gidansu su sake more amarcinsu a karo na biyu babu kowa, babu wanda zai damesu, suyi rayuwar farinciki, ya saka mata da abin alkharin da ta yi mashi a baya, amma duk mamarsa ta rusa komai, ina shi ina soyayya mamarsa tana gidan fisabilillahi? Ai babu wannan zance!.
A haka su Khadija suka dawo daga school a tare da Sadiq da ya je ya ɗauko su suka sami baban nasu.
Hajiya Zainab sarkin raki tun daga harabar gidan take kiran sunan maman tata, sai kace wata tsohuwar makauniya, sai kwala kira take yi, sai da Khadija ta ce.
"Ni kam ke kam Zainab yaushe zaki yi hankali ne? Wai ba cikin ɗakin zamu shiga bane? Ki bari mu shiga mana sai ki gaya mata duk abin da zaki faɗa mata, amma kin wani tsaya daga tsakar gida kamar wata makauniyar da sandar dogarawarta ta ɓata kina kiran neman taimako?".
Turo bakin nan tayi kamar biro, sannan ta wuce izuwa cikin parlourn fuuuu kamar wata kumfa a saman ruwan teku, Khadija ta cika shisshigi a cewarta.
Tana shiga da ta ga babanta a kwance a saman kujera bata san time ɗin da ta saki school bag ɗin nata ya faɗi ƙasa ta ƙariso wajensa da gudu, kamar wata under 10 years tana ambatar sunansa.
"Baba, baba ya aka yi yau ka dawo da rana? Da muka tambayi kawu Sadiq ina kake ya ce mana kana kasuwa fa, ashe kana gida".
Khadijah tana ƙoƙarin cire takalmar makarantar tata a wajen ajiye takalmarsu ta tsinkayo muryar Zainab tana faɗin baba, baba, ai a ɗari ta yi maza ta ƙarisa cire takalmar ita ma ta faɗo cikin parlourn, bayin Allah suna matuƙar kaunar baban nasu sosai, dan uba ne na gari shi ɗin, yasan ciwon kansa dana iyalansa, yana koyi da fiyayyen halitta sosai da sosai.
Jin muryar Zeezeensa yasa ya buɗe idanuwansa da suke jajir da su kamar wuta.
Ɗan zaro idanu Zainab ta yi kafin ta ce. "Baba baka da lafiya ne?".
"Kai'na ne yake mun ciwo Zeezeena, shi ne yasa kika ga na dawo kasuwa da wuri, jeki ki cire uniform kuyi wanka kuzo mu ci abinci a tare, yau a gida ma zan ci abincin rana".
Da yake har yanzu yarinta sosai yana a kanta, sai ta miƙe cike da murna yau zasu zauna da babansu da rana su ci abinci, ɗakinsu ta nufa tana yi mashi addu'ar Allah ya sawwaƙa mashi ciwon kan nasa.
Khadijah dake a tsaye a bakin kofar shigowa tana kallonsu ne ta ƙariso cikin parlourn, a ƙasa saman carpet ta zauna kusa da baban nata, gaisuwa ta fara ɗaga mashi cikin nutsuwa kafin ta ɗaura da cewa.
"Baba ka dai'na sakawa ranka damuwa, zai iya taɓa lafiyarka, ni nasan kana damuwa ne a kan ni da yaya Haidar, to na yi maka alkawari zan zauna da shi kuma na yi hakuri, amma sai ka dai'na damuwa ka ji?".
Khadijah ba dai hankali ba, akwai shi kam, ga nutsuwa, bata shiga harkar kowa, kawar da kai da kawaici duk ta haɗa.
Miƙewa zaune ya yi, cikin sanyin murya ya fara saka mata albarka kafin shi ma ya ɗaura da cewa.
"Mamana ba zaki auri Haidar ba In Sha Allah, saboda ba shi ne irin mijin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce mu zaɓawa ƴaƴanmu ba, dan haka ni ba zan aura maki shi ba, ina jiran ne kawai ki rubuta Exams naki ki gama sai na san abin yi, dan haka ki kwantar da hankalinki ki rubuta Exams kuma ki ciyo mun first class kamar yadda kika saba kin ji ko?".
Haƙiƙa ya gaya mata hakan ne kawai domin ta nutsu ta rubuta Exams nata na karshe a secondary school da kyau, tabbas bashi da mafita a kan aurenta da Haidar, amma kuma baya taɓa sarewa wajen cewa ba zai aura mata shi ɗin ba, a kullum yana da kwarin gwiwar cewa Allah zai kawo mashi mafita ya kawo sanadiyar hana auren, amma for now dai bashi da wata hanya ko wata zaɓi, kawai gaya mata yake yi ba zata aure shi ɗin ba dan hankalinta ya kwanta.
"To baba ta ya za'ayi na dai'na damuwa na kwantar da hankalina bayan kai da kanka da kake cewa na dai'na damuwar kana cikin damuwa? Ni nasan yanzu haka damuwar ce ta ja maka wannan ciwon kai da har ka dawo gida da ranar nan bayan baka saba dawowa da rana ba, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar iyayena suna a cikin damuwa".
Tana magana idanuwanta a cike tab da kwallah.
"Mamana kada ki damu, muma daga ni har mamarki mun dai'na damuwa a yanzu, kema ki kwantar da hankalinki, yanzu dai jeki ki cire uniform ki yi wanka kuzo muci abinci a tare, na yi maki alkawarin ba zaki sake ganin damuwa a saman fuskata ba kin ji ko?".
Jinjina kai ta yi tana mai ƙoƙarin goge hawayen da suka cika mata idanun.
"Baba kafin na cire uniform ɗin bari na sayo maka maganin ciwon kai ɗin, idan mun ci abinci sai ka sha ka kwanta ka yi barci zuwa la'asar zaka ji sauki ko?".
Kamar zai ce mata ta bari, sai kuma ya tuna Khadija ba kamar Zainab take ba, Zainab ne zai cewa ta bar abu ba zata tambaye shi dalili ba zata bari, ita kuwa Khadija yanzu idan ya ce ta bari ma wani sabon rigima ne, dan sai ta ce mashi lallai sai ya sha magani ko kuma ta tsayar mashi da kuka, zaman lafiyar dai kawai ya barta ta je ta sayo ɗin, baya son fitarta, amma da yake lallaɓata yake son yi yanzu ta kwantar da hankali ta yi karatu, sai ya kyaleta ta je ta sayo ɗin, tun da shagon babu nisa, idan ya ce ta bari ya sayo ma zata ce a'a ya kwanta kansa na ciwo, su Zainab kam an tafi wanka, sai murna take yi yau zata ci abinci a tare da babanta da rana. Hmmmmm Allah ka bamu ƴaƴa waɗan da zasu iya fahimtar farincikinmu da kuma bakincikinmu ba sai mun gaya masu ba!.
Har ta kai bakin kofa zata fita sai kuma ta juyo tana faɗin.
"Baba ina mama kuma?".
"Mamanku tana ciki tana barci".
Ya bata amsa yana ƙoƙarin ciro kuɗi daga aljihun dakakkiyar shaddar jikinsa.
Shiru Khadija ta ɗan yi tana tunanin, hakiƙa zuciyarta ta gaya mata ba lafiya ba, ace babanta ya dawo mamanta tana cikin ɗaki tana barci? Bata taɓa ganin hakan ba, idan ma barcin ne wlh a tare suke yi, dole dai akwai abin da yake faruwa, dan mamanta da zarar babanta ya dawo to tana tare da shi, duk abin da zai buƙata ita zata yi mashi cikin ƙanƙanin lokaci cikin kuma kulawa da nutsuwa, hakan ne ma yasa shi ma baban nasu baya son yi mata abin da bata so, yana burin ganinta cikin farinciki.
"Ga kuɗin maganin karɓa ki je ki sayo ki dawo da wuri".
Muryar baban nata ya katse mata tunanin da ta afka.
Shi ma ya lura ta luluƙa duniyar tunani, kuma dama yasan halinta sarai da shegen iya saurin gano abu.
"Baba akwai kuɗin break da kawu Sadiq ya bani da safe a hannuna, zan sayo maka da shi".
Ta faɗa tare da sa kai ta fice da wuri. Da kallo kawai ya bita yana mamakin halin ƴar tasa, akwai hankali da nutsuwa, Maman Zainab ta iya tarbiya!.
Ita kuwa maman Zainab kuka ta je ta ci mai isarta, a haka har barci ya ɗauketa a saman bed ɗin, shi ne yasa kuka ji ta shiru.
Hajiya Zeezee sarkin wanka tuni ta yi wanka ta hau shiri abinta, ita dai bata san dawar garin ba, sai murna take baba ya dawo da rana, bata san wannan dawowa tasa tamkar bom ne da zai tarwatsa masu farincikinsu ba, ance ƙuruci dangin hauka, to shi ne a kan Zeezeen babanta.
Khadijah kuwa, tana fita izuwa bakin babbar titi saura kaɗan wasu danƙara danƙara motoci su bi ta kanta, domin kuwa, tana tafiya ne tana tunanin me ya haɗa mamanta da babanta faɗa? Meyasa mamanta zata shiga cikin ɗaki ta bar baba a parlourn? Wannan abin ya tsaya mata a rai. Ta yi nisa cikin tunanin ne har ta isa bakin babbar hanya, tana isa kawai ta sa kai zata wuce, dan bata ma san ta isa wajen ba, hakan kuma ya yi dai'dai da dannowar hancin wasu danƙara danƙarar motoci na familyn Sir ALAUDDIN ABDUL RAHMAN, ɗaya daga cikin manya manyan masu murya a ƙasar, babban mutun ne mai kamfanoni a manya manyan ƙasashen ƙetare, babban mutun ne sosai, so haka motocin gidansa suke, idan suka hau titi fa ba ɗaga kafa, wucewa kawai suke yi abinsu, bare ma idan motocin sun ɗauko babban ɗansa FAROOQ ALAUDDIN ABDUL RAHMAN, yaron sam bashi da kirki, baya ɗagawa kowa kafa, duk wanda ya yi kuskuren bi ta gabansu take shi suke yi, hakan yasa saura kaɗan su take mana Khadijarmu Allah ya tsareta ta farga a in da ta ja baya da sauri tana mai bin motocin da kallon banza, dama haushi take ji, zuciyarta a cike da damuwa, sun wani zo zasu kara mata damuwa a kan damuwa, sun wani wuce kamar wasu walkiya.
Sai kace mutane take gani a gabanta ta wani tsaya tana watsawa danƙara danƙarar motocin harara har suka wucewa ganinta duk yawan nan nasu, ko ciwo ma idanunta basu yi mata ba wajen jure harararsu har suka wuce.
Suna wucewa ta sanya kai ta wuce abinta tana mai kare masu zagi, dan bata ga alamar hankali a tattare da su ba a cewarta.
Pharmacyn dake a tsallaken titin ta je ta haɗowa babanta maganin ciwon kai, sannan ta kama hanyar dawowa gida, sai magana samarin layi suke yi mata, kamar dai kullum babu wanda ya isheta kallo daga cikinsu, in da ta sanya kai kawai take nufa abinta.
Lokacin da ta dawo gida Zainab har ta yi wanka ta fito parlourn. A kusa da baban nata ta zo ta ajiye mashi magungunar tana wani aikin yamutse fuska, sannan ta wuce cikin ɗakinsu dan ita ma ta yi wanka ta shirya.
Sai a lokacin kuma baban nasu ya miƙe jiki ba kwari ya nufi cikin bedroom na mamar tasu, da farko Khadija ta so ta shiga wajen mamar tasu kafin ta wuce ta je ta yi wanka, amma ganin babanta ya miƙe zai nufi ɗakin ne yasa ta wuce nasu dakin kawai.
Ya shiga cikin ɗakin dai'dai lokacin da maman Zainab ta farka daga barcin da take yi na wahala, idanunta har sun kumbura saboda kuka ga kuma barci, har ta yi barci ta tashi ɗin ma zuciyarta bai yi sanyi ba, tafasa yake yi mata sosai, musamman idan ta tuna cewa kakansu Zainab ta ce a tare da ita da kuma Amarya zasu koma sabon gida, duk sai ta ji duniya tana juya mata, yanzu ma basu zaune gida ɗaya da su ba ya ta kare da balaja'un bala'in tsohuwar bare kuma suna zaune gida guda? Ya kuke tunanin zaman zai kasance?. Akwai aiki ba kaɗan ba.
Kuma abin da baku sani ba a nan shi ne, duk abinda kakansu Zainab take yi fa zugin maman Haidar ce, ita ce nan take ƙoƙarin tura ƴar tsohuwar nan ga halaka, munafukar mata.
A gefen gadon baban Zainab ɗin ya zauna yana ƙoƙarin fara yi mata magana.
A daƙile cikin tsananin ɓacin rai ta ce. "Ba sai ka sake ce mun komai ba baban Zainab, wanda ka gaya mun ɗazun ma ya isheni har karshen rayuwata, dan girman Allah ka rabu da ni haka idan dai ba so kake kaga gawata ba".
Ta kai karshen maganar tare da zuro kafafunta ta sauka kasa daga saman gadon, ta wuce ta fice ta bar mashi ɗakin.
Bawan Allah duk sai ya rasa ina zai sanya ransa ya ji daɗi, haka dai jiki ba kwari ya sake miƙewa ya fito parlourn, nan ya isko tana shirya masu abinci, ɗaya daga cikin abin da yasa yake kara sonta kenan, komai ɓacin ran da take ciki baya hanata ta yi aikin da ta saba, baya hanata nemar aljannarta baiwar Allah.
A saman sofa ya zauna yana ta kallonta, ita kuwa ko kallon in da yake bata yi ba, abincin kawai take kwasowa daga kitchen tana shirya masu a parlourn, duk in da ta yi sai ya bita da ido bawan Allah, tana gamawa kuma ta nufi hanyar komawa cikin ɗakinta, da alama ita ba zata ci abincin ba kenan.
"Maman Zainab ina zaki je kuma? Ki zo mu ci abincin mana".
Ya faɗa yana kallon Zainab dake rike da wayar mamar tasu.
A takaice ta ce mashi. "Bana jin yunwa, so ku ci kawai".
Ta kai karshen maganar tare da shigewa cikin ɗakin abinta, har da rufo kofa ta murza key.
Tabbas yasan saboda ganin idon Zainab ne yasa ta bashi amsa, da Zainab bata parlourn ba zata kula shi ba bare ta bashi amsa. Macece mai hankali sosai, tasan duk in da yake mata ciwo, tasan da cewa abin da take yi wa babansu Zainab shi suma idan suka yi aure zasu rinƙa yi wa mazajensu, so bata son ginasu a kan turbar da bata dace ba, shiyasa kome babansu zai yi mata na ɓacin rai bata nuna hakan a gabansu, tana ƙoƙarin ta danne dan taga tarbiyar da take basu yana tafiya mata yadda ya kamata, ba wai tana basu tarbiya kuma tana sake rusawa da kanta ba, Allah yasa mata su gane illar faɗa da mazajensu a gaban ƴaƴansu, Allah yasa su gane cewa rugujewa ƴaƴan nasu tarbiya suke yi da kansu, Allah yasa su gane cewa duk abin da suke yi wa ubansu haka ƴaƴan ma zasu yi wa mazajensu idan suka yi aure, dan suna ganin mamarsu tana yi, so hakan zai sa su ce abu ne mai kyau.
Yau dai shi ma ya ci wannan abincin ranar ne kawai saboda Zainab da Khadija, ba dan su ba tabbas ba zai ci ba, amma baya son su san halin da ake ciki, dan haka sai ya zage yana ta ƙoƙarin ƙaƙalo murmushin da kuma yake wadda aka ce tafi kuka ciwo, a haka suka kammala cin abincin ya tashi ya nufi kasuwa bayan ya ɗaukawa su Sadiq nasu abincin a kula. Bai sake komawa wajen Maman Zainab ba, dan yasan har yanzu bata sauko ta huce ba, so ba zata saurare shi ba, hakan yasa ya wuce kasuwa kawai da nufin kafin ya dawo kila zuciyarta zata huce kaɗan ta saurare shi.
Haka su Khadija suka zauna a gidan har zuwa lokacin tafiya islamiya, lokaci na cika suka yi sallah tare da shirin islamiyar, ko da suka je yi wa mamar tasu sallama sam bata nuna masu kamar akwai wata damuwa ba, sai ma kuɗin sayan attarugu da Albasa tare da tumatir ta basu kamar yadda ta saba, sannan ta bisu da addu'a tare da fatan alkhari kafin ta ja masu kunne a kan biyewa ƙawaye ko kuma wani ya taresu a hanya su tsaya su kulashi, su kiyaye hakan dan su ƴan gidan mutunci ne, ba'a kan titi suke ba, wannan shi ne nasihar da take yi masu a kullum idan zasu tafi islamiyar, shiyasa kuka ga basu taɓa kula maza a hanya.
Da haka suka wuce Islamiya ita kuma ta tashi ta fito ta nufi tsakar gida, alwala ta ɗauro ta dawo.
Bayan ta gabatar da sallah ne ta nufi kitchen dan girka masu abincin dare, a haka Aunty Hauwa ta zo ta iskota.
Kamar yadda suka saba a parlourn suka zauna da Aunty Hauwar suna hira tana zuwa tana duba girkinta da ta ɗaura, cike da damuwa ta sanar da Aunty Hauwar bala'in dake shirin tunkarota a karona biyu bayan na auren Khadija and Haidar.
Aunty Hauwa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kwashewa su maman Haidar albarka tare da banka masu tsinuwa kala kala, sannan ta ce mata to wlh gara ta tashi tsaye, idan ba haka ba tana ji tana gani zasu korata gidansu bayan kuma ita ce ta sha wahalar baban Zainab ta ci talaucinsa, yanzu kuma wata zata zo ta ci arziki, wlh kada ta yarda, ta miƙe tsaye, dan rayuwar yanzu ba'a zama........ Aunty Hauwa ba dai bala'i ba.😅
"Hauwa to ya kike son nayi da su? Kina dai jin abin da suke faɗa ko? Umarni Hajiya ta bashi fa".
Nisawa Aunty Hauwar ta yi kafin ta ce. "To ai idan ba zaki iya fito na fito da su ba sai ki biyo masu ta ƙarƙashin kasa, duk kici uban shegu marasa amana butulaye kawai".
Ta bata amsa rai a ɓace
"Hauwa kamar yaya na biyo masu ta ƙarƙashin ƙasa? Yimun bayani na ji".
Tana magana cike da damuwa a ranta, kamar zata yi kuka.
"Abin da nake nufi da ta ƙarƙashin kasa shi ne, tun da ba zaki iya fito na fito da su ba kawai ki yarda muje wajen Malam sha yanzu magani yanzu, muje mu gaya mashi ya rufewa ƴan uwan mijinki baki a kanki, ya kuma sanya masu kaunarki na fitar hankali, sannan a ruguje batun auren da suke son yi wa baban Zainab ɗin, kinga fa nima haka na yi wa ƴan balaja'un ƴan uwan mijin nan nawa, baki ga yadda suke so na bane? Ai kamar su goyani suke ji saboda so, baki ganin ko da yaushe su Khalid suna wajensu bane? Suke shan reno ni kuma ina neman kuɗi, kamar su haɗiye su Khalid saboda so, dan haka kema abin da zaki yi wa ƴan iska kenan, ai in sun san wata basu san wata ba".
Ɗan zaro idanu Maman Zainab ɗin ta yi, a ruɗe ta ce. "Hauwa kina nufin wajen boka kike zuwa?!".
Wani kallon banza ta ɗan watsa mata kafin ta ce. "Sai aka ce maki boka ne shi ɗin? Ko kin ji nace maki boka ne? Malam sha yanzu magani yanzu fa nace maki, shi ba irin bokan da kika sani bane, malami ne".
Shiru Maman Zainab ɗin ta ɗan yi kafin daga bisa kuma ta ce. "To Hauwa me marabansa da boka?".
Da sauri ta amsa mata da "Wlh suna da maraba, kuma ke da kike wannan magana ma kin san me wadda zai auro maki ɗin take yi ne? Su hajiyar tasa kin san me take shiryawa ne? Ki zauna ke kam, kada ki tashi tsaye, wlh sai sun rabaki da jin daɗin rayuwa, kina ji kina gani ki zama ƴar aiki jaka a gabansu".
KAI MY PEOPLE'S, WAI YA NAGA AUNTY HAUWA NA ƘOƘARIN GURBATA MANA TUNANIN MAMAN ZAINAB ƊIN MU NE?😥😳 BAN GANE BANE😳
TO SAI DAI MUN HAƊU ON MONDAY DAN MUJI ME MAMAN ZAINAB ZATA YI, WANI ACTION ZATA ƊAUKA A KAI, ALLAH DAI KASA MU DACE KA RABAMU DA JAHILAN KAWAYE!.
🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 75