Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne dan ma kada wani abin ya samun min ke". Yana magana yana kara kare mata kallo daga sama har ƙasa, dan iya shege sai kalle mata kirji yake yi a cikin sleeping dress ɗin, da yake kayan sun zauna a jikinta dai'dai ita, sai alamar komai ya bayyana. Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Amma fa Yah Jawad akwai wahala idan aka toshewa mutun hanci!". Ɗan zaro idanu ya yi tare da cewa. "Kunji wahala ne?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Kaɗan fa na ɗan rike maki hancin, amma kin ji wahala?". Kai ta gyaɗa mashi still tana turo baki. Hannu ya kai ya ɗan shafi kumatun nata. "Sorry my Jannat, ba zan ƙara ba, to yi murmushi". Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi wadda ya sanya shi sakin murmushi shi ma. "To shikenan ni zan wuce bedroom ɗina, sai da safe ko?". Ƙasa ƙasa ta ambaci sunan. Lafiya ya amsa mata da shi. "Allah Yah Jawad bana son ka tafi, ina jin daɗin yin hira da kai". Ajiyar zuciya ya sauke tare da duba time a wayarsa. 11:44, "Jannat dare ya yi fa, ki kwanta ki yi barci akwai school gobe". Ɗan turo mashi baki ta yi kafin ta amsa mashi da to. Miƙewa ya yi zuciyarsa cike tab da tunanin zai yi kewarta, ɗan matsowa ya yi ya bata sumbata a goshinta kafin ya ce ta kwanta bari ya mayar mata da bargonta ya lulluɓeta. Ba musu ta kwanta, ya lulluɓeta, zuciyoyinsu bai so rabuwa ba, amma haka ya yi mata sallama sai turo baki take yi ya fice zuwa nasa room ɗin. Yana tafiya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita ba tare da ta kunna wayarta ba, daɗin hira da Yah Jawad yau yasa ta manta da hira da Yah Rizwan. Shi kuwa a nasa ɓangaren ko da ya kwanta bai iya yin barci ba, tunani ne kala kala cike tab a ransa, har wuraren karfe 2 ya gagara barci, daga karshe ya miƙe ya ɗauro alwala ya zo ya fara gabatar da nafilfilu. Washegari da safe misalin 6:30. Shirye yake cikin wandon Jeans baka, daga ta sama t-shirt fara ce tas, sai ya ɗaura long coat zuwa gwiwarsa a saman kayan, ita ma coat ɗin baka ce kalar wandonsa, takalmar kafafunsa ma bakake ne, matsayinsa na farar fata sai bakaken kayan suka yi mashi kyau, ga arab hairnsa bakin kirin da shi ya sha gyara. Kai tsaye part ɗin Akka ya nufa sai zuba kanshi yake yi, office zai je yau da wuri, amma yana da buƙatar sanya ta a idanunsa kafin ya tafi, yasan kuma a part ɗin Akka kawai zai sameta by this time around. Dai'dai zai shiga part na Akkar shi kuma uncle Taheer kanin Mama yana fitowa, kusan karo suka yi, da sauri ya ɗan ja da baya yana faɗin good morning uncle. Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mashi tare da tambayarsa ya ya kwana ya kuma ya wayi gari. Da Alhdulillah ya amsa kafin ya wuce ciki, shi kuma uncle Taheer ɗin ya fice ya nufi part na mama dan ya duba jikinta............. Allah sarki mama, su Omaid sun ja mata bala'i, sun barta da jinya, suna can gidan Abu Abdussalam, ko me suke aikatawa yanzu?...🤔 Baki a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin. Babu kowa sai Chuchu dake ta ƙoƙarin sanya uniform ɗinta, yanzu Akka ta shiga toilet bayan sun gama gaisawa da uncle Taheer, ita kuma Chuchu uncle Taheer ɗin yana fita ta hau shirin zuwa school, dama ta yi wanka shigowarsa ɗakin yasa ta zauna suka gaisa. Ta zura rigar a kanta tana kokawar sauke shi ƙasa, da yake rigar dai'dai ita yake hakan yasa sanya shi yake ɗan yi mata wahala. Cike da tsokana Jawad ɗin ya ƙariso ciki, samar rigar ya rike ya hanata janyo shi ƙasa. Ja da karfi ta yi sai ta ji kamar an rike, ga shi bata iya gani bare taga wanene? Dan ta zura rigar a kanta. A ƙule ta ce. "Auta bana son walaƙanci fa, zaki sakar mun riga na samu na sauke shi kasa na shaki numfashi ne ko sai kin kashe ni?". Shiru bai amsa mata ba, sai ma da shaiɗan ya ɗan ruɗesa ya zura hannunsa daga ta bayan nata izuwa saman plat tummynta. Janyota ya yi ta zo jikinsa. Sai surutu take yi a tunaninta Auta ce, sai da ya ɗan wahalar da ita kafin ya sakar mata rigar tare da jan mata shi ƙasa har lokacin hannunsa yana saman cikinta. Yana sakar mata rigar bayan ya sauke mata a hanzarce ta fara ƙoƙarin juyowa domin taga wanene? Hanata juyowa ya yi ta hanyar ƙara ƙanƙame mata ciki. A garin ƙanƙame ta ɗin kuwa hannunsa ya ɗan haura sama izuwa kusa da kirjinta, hakan yasa ta kurma ihu mai sauti wadda tasa dan dole ya saketa a ɗari ya shiga dressing na Akka. Yana shiga Akka kuma ta fito daga cikin toilet cikin zafi tana faɗin. "Nashi uku! Jannat lafiya? Ihun me kike yi?". Ƴar waige waige ta fara kamar mai neman wani abin, kuma fa ta gansa lokacin da ya shiga room ɗin, amma ta rasa ita kanta waige waigen me take yi, ta kuma rasa me zata gayawa Akkar. Shi kuwa sai addu'a yake yi Allah yasa kada Jannat ta gayawa Akka shi ne ya taɓata ta yi wannan ihun, yasan halinta sarai, idan ba shi ya ce kada ta faɗa ba Akka na tambayarta zata shi ne ya zo ya taɓa mata kusa da kirji, yasan yanzu da wuya idan ba gaskiya zata gayawa Akkar ba, ya shiga talatin yau ba uku ba. Da alama addu'ar King na daren jiya ne ta kama shi, dama King ya gaya mashi one day one time Akka zata kama shi yana yi mata soyayya a ɗaki, kuma idan ta kama shi ya shiga uku, to da alama yau ranar tonon asiri ne....... 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥 Ko da Leesharh ta shiga cikin kitchen ɗin sai ta rasa ina zata nufa, ma'aikata ne birjik suke maƙare a ciki suna ta aikin dake gabansu, babu wadda ta ɗaga idanu ta kalleta ma bare ta sa ran zata iya tambayarta. Da farko a tunaninta abin da sauki ne, sai yanzu ta fahimci isn't easy ooooo, damuwa ta shiga sosai, ta rasa wa zata tinkara da zancen?. Ta juya gabas da yamma gudu da arewa a cikin kitchen ɗin nan bata ga ƴar aikin da fuskarta yake a sake bama bare ta tinkareta, ga shi babu wadda ta kulata, sai ka ce basu ji shigowar mutun ba. Ita fa Leesharh bata ma san da cewa masu girki daban, masu shirya abinci a parlourn daban, sannan masu serving ƴan gida abinci suma daban, bugu da kari masu kaiwa zaratan samarin gidan abinci suma daban suke. To a gabaɗaya cikin kitchen ɗin nan a yanzu dai iya masu yin girke girke ne a ciki, a lokaci guda sai a girka abinci almost kala sha biyu, kunga kuwa dole masu yin girkin su kasance suna da yawa, kowacce da aikin da take kamawa, haka zalika kowacce da kalar girkin da take yi, kun san laraba da iya shirya abinci kala kala a saman table. Idan suka kammala yin girkin ne sai masu kwasa su kai dining room su shirya a saman table kuma su zo su fara aikin jidansu su kai, masu kaiwa su Ramish suma su zo su kwasa nasu, haka tsarin gidan yake, Ta kai almost 30 mins a tsaye a tsakiyar kitchen ɗin babu wadda ta ce mata ko ci kanki. Da dai taga tsayuwa ba zai amfana mata da komai ba sai ta duba a cikinsu ta ga mai ɗan dama dama dan ta nufeta. Can ta hango wata ƴar matashiyar yarinya da ba zata wuci 17 year ba a duniya, sai aikin yanka kayan lambu irin su Chinese cabbage, cucumber da dai sauransu take yi. Ita kuma sune aikinta, sai ta wuni tana aiki ɗaya, dan duk girkin da za'ayi ana amfani da haɗin salad dan cin abincin, da rana haka da daddare haka, ga gidan da girma da kuma yawa, cikin wani katon kwando mai girma take yankawa, da yake ta saba sai sam bata ganin wahalar aikin. Sannu Leesharh ta yi mata, yauwa ta amsa da shi, ta amsa kuma ba tare da ta ɗago ta kalli Leesharh ɗin ba, saboda aikin da yake gabanta, daddatsa su cabbage ɗin take yi babu wasa, cikin sauri sauri saboda ta kware, kwararriya ce. Shiru ta yi tana tunanin ta yadda za'ayi ta tambayi wannan yarinyar abin da take buƙata. Ta ɗan yi nisa cikin tunanin da take yi kawai ta tsinkayo muryar yarinyar a kunnenta tana faɗin. "Kina buƙatar wani abin ne? Da me zan iya taimaka maki?". Tana ƙoƙarin yin magana wani tunani ya faɗo mata a cikin ranta, ba komai bane kuma face tunawa da ta yi da akwai cameras sosai a cikin kitchen ɗin, tambayar mai kaiwa Ramish abinci a wajen babbar barazace a gareta, dan ana ganinsu. Tuna haka yasa ta yi maza ta juya ta fita ba tare da ta sake cewa yarinyar ko sannu ba......... Kai Leesharh fa tana da basira sosai yarinyar. Kai tsaye room nata ta nufa domin ta je ta sake yin tunani a kan mafitarta. A dai'dai lungun da ta yi wa Ramish laɓe ɗazun suka ci karo da mutun, kasancewar wajen babu wadatatcen haske dan a tsakanin ɗakuna yake, kuma wajen babu Camera. Rashin haske yasa bata san da waye ta yi karo ba, sai dai koma wacece tabbas macece, dan karon da suka yi kirjin wancan ta buji kafaɗunta, to ta ji tana da breast. Wucewa ta yi da sauri ba tare da buƙaci sanin da waye ta yi karo ba. Ita ma wadda suka yi karon a hanzarce ta wuce kamar maras gaskiya. Dakatawa da yin tafiya Leesharh ta yi tare da juyowa ta bi yarinyar ne ko matar za'a ce ne da kallo, haka kawai sai ta ji gabanta ya faɗi, ji tayi bata yarda da matar ba, duba da yadda ta wuce da sauri kuma bata yi magana ba, ita ce ta bugi Leesharh ɗin, amma bata ce mata ko uppan ba ta wuce da uban sauri har haka, hakan yasa Leesharh zarginta sosai. Da sauri ta juyo domin ta bi bayanta ko idan suka fita haske zata iya ganin wacece?. Sai dai kash! Kafin ta fito wajen haske sam bata ga ko mai kama da alamar matar ba, ta ɓacewa ganinta, da alama wani lungu ta shiga ko kuma wani wajen. Jiki ba kwari ta juya ta nufi hanyar koma ɗakin nata. Tana barin wajen matar ta fito daga in da ta laɓe ta kusa da hanyar shiga part ɗin su Ramish, ashe tasan Leesharh ɗin ta biyo bayanta, da gaskiyar Leesharh matar bata da gaskiya, kuma ɗaya ce daga cikin masu aikin gidan wadda take a hawa na biyu, ko me ya kawota nan? Ko me ta aikata take wannan uban sauri har da ɓuya haka?. A bakin gadonta ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin yadda zata ɓullowa wannan al'amari. Wayarta ta janyo domin ta duba ko matan nan sun turo mata wani saƙo. Tana kunna hasken screen ɗin wayar sai ga saƙon kuwa ta ci karo da shi sun turo. Buɗewa ta yi ta fara karantawa duk da ba wani kwarewa ta yi a karatun ba. Ba wani saƙo suka tura mata ba face cewa da suka yi ta duba cikin akwatinta sun ajiye mata maganin da suke son ta zubawa Ramish a cappuccino, dan haka ta ɗauko maganin kuma ta kula. Zaro idanu ta yi tana mamakin ta ya akayi suka iya kawo mata maganin kuma? To ko dai suna tare da ita a cikin gidan ne bata sani ba?. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi wajen akwatin nata. Tana zuwa ta buɗe akwatin da wuri, ga mamakinta sai ga maganin a saman kayanta kamar yadda suka faɗa. Ita dai tasan ɗazun da ta ɗauki kayan sakawarta babu magani a ciki. Maganin a cikin wani ɗan ƙaramin kwalba yake, kamar kwalbar maganin ciwon idanu, zubawa maganin ido ta yi tana kallonsa, tana son sanin maganain menene? Sai dai ba dama, dan basu gaya mata ba, ita kuma bata isa ta ce zata nunawa Sharifat ta ce zata tanbayeta ko ta san na menene bane, kada ta zo ta ɓata aikinta, amma tabbas tana son sanin maganin menene kafin ta zubawa bawan Allah. Zuciyarta na ta ayyana mata maganin nan cutar da shi zai yi, zantukan babanta take yawan tunawa a kullum in da yake yawan gaya mata kada ta kuskura ta cutar da wani a duniyar nan, da ta cuci wani gara a cuceta, wannan dalilin yasa duk wani aiki da zasu sakata take yawan shiga zulumin a kan kada ta je ta cutar da wani. Ta jima sosai a wajen tana tsugunne tana kallon kwalbar maganin kafin daga bisani ta miƙe da maganin riƙe a hannunta, sannan ta rufe akwatin nata, shi kuma maganin ta tura a cikin aljihun wandon jikinta. Waje ta sake nufa domin kudurinta na neman mai kaiwa Ramish abinci, tana da jajircewa da kuma kafiya a kan abin da ta sanya a gaba, kuma bata taɓa sanyawa ranta sarewa ko karaya. Sai dai a wannan karon tana yi tana fargaba tare da tsoron kada ta cutar da bayin Allahn da basu ji ba basu gani ba, mutanen da suka karɓeta hannu bibbiyu, suka yi mata gatan da bata taɓa samun makamancinsa ba a rayuwarta, bata taɓa yin tunanin zata taɓa samun irin wannan gata ba, sun bata bedroom haɗaɗɗe, ga cima mai kyau, ga sabulai masu zafi na gyaran jiki, ga haɗaɗɗun kayan sakawa duk bayan wata guda ana sayo masu dayawa, gasu da halacci da kirki sosai. Amma idan ta tuna mata mai nikaf ɗin can ta ce mata ba cutar da shi zasu yi ba, taimakonsa zasu yi, sai ta ji sanyi a ranta, sai ta ji zata iya aikata komai dan ita ma ta taimaka da nata gudunmawar. Amma wani ɓangare na zuciyarta ya ki yarda a kan taimakonsa suke son yi. Tana da ƙwaƙwalwar da basira sosai, amma akwai yarinta sosai a tattare da ita. Masu nikaf kuma da wannan yarinta tata suke amfani dan cika burinsu!!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 13/9/2024.....✍️📚🌹 For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________51🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼 KINGDOM OF POWER 💪🔥💘 "Jannat lafiyarki kuwa?". Akka ta sake faɗa cike da damuwar son sanin me ya sami jikar tata ta zunduma ihu haka. Dawo da kallonta a kan Akkar ta yi, a hankali ta sake satar kallon dressing room ɗin, da farko kamar zata gaya mata gaskiya, amma sai wani tunani ya faɗo mata a rai, tunawa ta yi cewa to idan har Yah Jawad zai gudu ya ɓuyan wa Akka bai kamata ta gaya mata cewa yana nan ba, yin hakan zai sanya ya ji babu daɗi. Wannan tunani yasa ta dawo da kallonta kachokam kan Akkar. "Akka babu fa abin da ya sameni, ji nayi ne kamar wani abin ya shiga mun cikin rigata yana tafiya, shiyasa na yi ihu" Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke daga in da yake tsaye, sanyi sosai ya ji tana ratsa zuciyarsa, ba ƙaramin daɗi ya ji da bata faɗi gaskiya ba, sai albarka yake saka mata a cikin zuciyarsa. Matsowa kusa da ita a hanzarce Akkar ta yi, riƙota ta yi tana faɗin bari ta duba cikin rigar tata ta gani kada ya zamana akwai wani abin a ciki ya ji mata ciwo, ko ya cutar da ita. Ƙanƙame rigarta ta yi bata son Akka ta kalle mata tula tulanta, mamaki ne ya kama ƴar tsohuwan. "Jannat lafiya? Ki bari na duba mu gani". Girgiza kai ta fara yi. "Akka ni ba sai kin duba ba, koma menene ya tafi, kuma ma babu komai a ciki ni ce na ji kamar da akwai wani abin". Ta faɗa tana turo baki. Haba da yake Akka sarauniya ce wajen iya magana, tuni ta fara sababi. "Ah ah ah lallai Jannat, ƴan nonuwar naki ne baki son in gani ko menene?" Nan fa ta fara jero mata kan cewa ai ba ita ba su Aunty MieMie duk taga nasu bare ita, dan haka sai ta duba..........😅 Dariya ne ya so kubcewa Jawad dake laɓe cikin room, yana jiyo duk abin da suke faɗa, yau yaga ikon Allah, yarinya da kayanta Akka ta ce sai ta duba, duk sai ya ji haushi za'a kalle mashi abin da shi ma bai taɓa kalla ba, wai shi ya zai yi da Akkar nan ne? Mata idan ka nuna baka son abu sai ta ce sai ta yi shi, ita fa idan taga kana kin abu ka ce baka so, sai ta ce rashin gaskiya ka kullah a wajen, dan haka sai ta ce sai ta gani!!. Jawad dai bai ji daɗin hakan ba, dan yasan ran Chuchunsa zai ɓaci sosai, babu wata budurwa da take tasowa wadda zata so a kalle mata abinta, bare ma idan tana da kunya, wannan dabi'a ce ta mata, a jininmu yake. Ita kam Akka ta kafe sai ta duba cikin rigar, ita kuma Chuchu taki yarda har da kukanta, ran Jawad ya ɓaci sosai, kamar ya kifawa Akkar nan mari yake ji, sai dai ba hali, ya suka iya da ita? Ai dole sai hakuri. Da Akkar ta ga da gaske kuka Chuchun take yi da hawayenta, sai ta kyaleta ta koma cikin toilet dan dama wanka zata yi, tana shirin farawa kenan ta jiyo ihunta, so sai ta koma kawai tana yi mata sannu haɗe da surutun Chuchu na ɓoye mata ƴan nonuwa. Tana shiga cikin toilet ɗin ya fito da sauri, ransa a ɓace saboda sanya mashi beb ɗinsa kuka da tsuhuwar nan tasu ta yi. Ya ɗaure fuska kamar hadari. Yana zuwa in da take ya riƙo hannunta tare da ɗauka mata school back ɗinta dake saman gadon Akkar wadda ta ajiye da kanta. Ya riƙo hannunta tare da nufar kofar fita. Har lokacin ƴan siraran hawaye suna bin saman ƙuncinta. Kai tsaye part ɗinsa ya wuce da ita ba tare da ya ce mata ko uppan ba, ya kuma yi sa'a bai ci karo da kowa a hanya ba har ya isa part ɗin nasa, kasancewar da safe ne kowa yana can yana ta faman aikin shiryawa, masu zuwa school suna nasu shirin, masu zuwa office suna nasu, masu yin breakfast suna fama, kowa dai yana room nasa yana abin da yake yi. A bakin bed ɗinsa ya zaunar da ita tare da ciro handkerchief mai kyau daga aljihunsa, ya zauna saman bedside drawer, a gefenta ya ajiye mata jakarta kafin ya kai hannu a hankali ya fara goge mata hawayen nata. "Am so so sorry my sister, duk ni na ja maki yin kuka da sassafen nan, kyale Akka hai ki dai'na kuka ba zata gani ɗin ba". Ya faɗa ƙasa ƙasa. Ƙasa ta yi da kanta, kunyarsa take ji sosai saboda ya ji yadda suka yi da Akka, ga Akka bakinta babu full stop ta rinƙa kiran sunan tula tulan a tsiraransu, abin ku da tsoffi sam bata wani sakaya sunan ba, ta rinƙa ambatarsa ba kakkautawa, wannan dalilin yasa Chuchun ta ji tana bala'in kunyar yayan nata, dan ya ji komai. Shi ma ya fahimci kunyarsa take ji, sai ya kawar da zancen da cewa. "Yau na kai ki school da kai na ko?". Ya yi maganar yana ƙurawa jikinta ido, gani yake kamar gizo idanunsa suke yi mashi, kamar kuma da gaske ne bata sanya vest a ciki ba, kuma bata sanya bra ita. Yana son ya tambayeta kuma yana jin fargabar yadda zata ɗauki abin, tsoro yake ji kada ta kalli hakan da wata manufa ko kuma ta fara gudunsa ko dai ta fara jin kunyarsa sosai. Idan ɗaya daga ciki ya faru ba zai ji daɗi ba!. Wani tunani ne ya faɗo mashi cikin ransa, idan ya tashi daga office ya je ya yi masu shopping na vest dayawa ita da Auta, sai ya bawa Autar ya gaya mata kada su sake saka kaya ba tare da sun saka vest a ciki ba, wannan ce tunanin da ya yi, yanzu haka sam ransa bai so ta tafi school a haka ba, amma ba yadda zai yi, idan ya ce zai yi mata magana a yanzu to tabbas zata haɗa maganar da abin da Akka ta yi mata ta kwaɓesu, daga haka zata fara ja baya da shi. Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e ya kaita school da kansa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Kin yi breakfast ne?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a. Waya ya ɗauko ya kira kuyanga Zubaida a kan ta kawo mashi kayan breakfast yanzu. Yana ajiye wayar ya hau janta da hira dan ta saki jiki ta mance da abin da Akka ta yi mata ta koma walwalarta. Ba'afi minti biyu da kiran da ya yi wa kuyanga Zubaida sai gata ta iso baki ɗauke da sallama. Izinin shigowa ya bata ba tare da ya kawar da kallonsa daga kan Chuchu dake ta faman murmushi ba, har ya mantar da ita kuncin da take ciki, ya sanyata farinciki. Saman carpet ya yi mata umarnin ta ajiye mashi abincin, a hanzarce ta karɓi umarninsa tare da aiwatarwa. Bayan ta fita ne ya ce da Chuchun ta zo su je su yi breakfast a tare. To ta amsa mashi da shi, hannunta ya riƙo suka nufi wajen kayan abincin. Zama ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi. Cup mai shake da coffee mai zafi ya ɗauko ya kai mata bakinta. Ba musu ta buɗe baki ta fara karɓa. Wayarsa ce ta fara kara daga cikin aljihun coat ɗin jikinsa. Hannu yasa ya ciro wayar tasa. Yah Rizwan, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Cigaba da bata coffee ɗin ya yi yana haɗa mata da pepper soup na kaza mai bala'in daɗi. Cike da kaunar yayan nasa ya ɗauki wayar yana kuma mamakin kiran da yayan nasa ya yi mashi da sassafe haka. "Assalamu alaikum Yah Rizwan barka da safiya". Ya faɗa cikin nutsuwa, yana magana yana yanko tsokar kazar yana cusa mata a baki. Ta saki jiki sai ci take yi abinta. "Jawad ka tashi lafiya?". Rizwan ya tambaya, daga jin muryarsa kasa yana kaunar ɗan uwan nan nasa sosai, sannan muryarsa da alama damuwa matuƙa a tattare da ita. Da lafiya lou Alhdulillah ya amsa mashi da shi, sannan ya ɗaura da cewa. "Yaya ya naga ka kirani da sassafe haka? Ko dai akwai wata matsala ne?". Sai a lokacin Chuchu ta ɗago idanu tana kallonsa jin ya ambaci matsala. Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mashi da. "E akwai matsalar babba ma kuwa, amma ba ita ce tasa na kiraka ba, na kiraka ne dan naji ya ka kwana? Ya kuma ka tashi? Jiya ban samu ishasshen barcin kirki ba, saboda tunaninka". Miƙawa Chuchun cup ɗin coffee ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Matsala kuma Yah Rizwan? To matsalar me? Meyake faruwa?" Bin shi da kallo ta yi har ya ficewa ganinta. Cigaba da cin abin nata ta yi tana tunanin to matsalar me aka samu kenan?. After some minutes ya dawo cikin ɗakin fuskarsa babu annuri ko kaɗan, da alama Rizwan ɗin ya gaya mashi wani abin da ya ɗaga mashi hankali sosai, jikinsa duk ya yi

Chapter 71 of 75