baya yarda da kowa?".
"Saboda ya ce yana da tarin makiya, kuma fa na gaya maki dukka masu aikin gidan nan daga maza har matansu amintattu ne, shi ne dai kawai bai aminta da su ɗin ba".
Shiru Leesharh ta yi tana jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwarsa, yana da gaskiya, su suke ganin kamar dukka ma'aikatan gidan amintattu ne, shi da ya san da cewa ɗan adam yanzu ba a abin yarda bane, ya san kan duniya ai ga shi bai yarda da su ɗin ba, ita kanta Leesharh ai kunga ba amintatciya bace, ƴar leken asiri ce, ƴar ɓadda kama!.
Miƙewa Sharifat ta yi. "Bari na ɗauro alwala Leesharh, kema ki tashi lokacin sallah ya yi, ki yi sallah mu je ki rakani wajen Yah Ramish mu kai masa abinci, idan mun je sai ki jirani a kofar shiga part ɗinsu, dan idan kika shiga na shiga uku na, ba kowa yasan in da part ɗinsu yake ba a cikin gidan nan, kuma Yah Ramish baya son wata ma'aikaciya ta zo arear part ɗinsu, wai kyamar ƴan aikin yake ji, idan sun zo in da yake zai yi amai, so sai ki jirani a waje".
Sharifat baki abin magana, ta aminta da Leesharh ta saki baki sai gaya mata sirrin gidan take yi, bata san cewa Leesharh dai green snake under green grass bace, ƴar ɓadda kama kuma ƴar basaja. Rashin sani bai yi ba a rayuwar nan.
Okey ta amsa mata da shi, nan take ta ji kwarin jikinta ya dawo, wani irin daɗi ta ji ya kamata, duk yadda zata yi ta zuba mashi maganin nan yau sai ta yi, dole ta san yadda zata yi ta shammaci Sharifat ta aiwatar da aikinta.
Waje Sharifat ɗin ta nufa, ita kuma Leesharh ta nufi cikin toilet, alwala ta ɗauro tare da zuwa ta shimfiɗa dadduma ta tada sallah, bayan ta idar ta sanya hannu ta taɓa aljihun wandanta dan ta tabbatar maganin yana ciki.
Jin cewa yana ciki yasa ta saki cool murmushin da bata san lokacin da ya fito ba, faɗi take yi a cikin ranta shikenan da ta zuba mashi maganin nan masu nikaf zasu haɗata da babanta ta yi magana, yau tsawon shekara kusan biyu bata ji muryarsa ba, tana kewarsa sosai, tun lokacin da aka kaita prison ta kashe mamanta, tun ma kafin lokacin take kewar muryarsa, sun ɗan kwana biyu basu a tare, shiyasa take ɗaukin jin muryarsa, take begen hakan.
Sallamar Sharifat a cikin ɗakin yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka. Ɗago idanun nan nata ta yi tare da saukesu a kanta, rike take da katon luxurious tray, shake yake da kulolin abinci masu bala'in kyau da tsada, ga cup dake shake da cappuccino, sannan ga cup na coffee mai zafi a gefe, duk suna rufe da ƴan ƙananan plate na set ɗin cup's ɗin. Sai sauran snacks dake saman wani luxurious plate.
Zubawa trayn idanu ta yi tana kallonsa sosai, ayyana yadda zata zuba mashi maganin a ciki kawai take yi. Muryar Sharifat ɗin ce ya katseta da cewa. "Let's go Leesharh".
Miƙewa ta yi suka jera a tare.
Allah sarki tausayin maraicin Leesharh da Sharifat take yi yasa zata tabka kuskure ba tare da sanin ta ba, burinta ta ja Leesharh ɗin a jiki ta yadda zasu saba sosai, duk dan ta mantar da ita damuwar da take ciki na rashin iyayenta, tana son su saba sosai su zama kamar ƴan uwa, shi ne harda gayyatota ta rakata wajen ƴan uwanta. Hmmm bata san aiki dama ta zo yi a kansu ba, rashin sani ya fi dare duhu.
A tare suka tafi, cikin dabara Leesharh ta ciwo maganin daga aljihunta, ko tsoro bata ji ba, kamar mai son gyara zip ɗin wandonta haka ta yi ta buɗe ɗan gwalbar ganin. Sai da suka shiga wajen wannan ɗan hanya in da ta yi karo da mai aikin ɗazun ɗin nan, kun san wajen akwai ɗan duhu. Saboda jajircewa da karfin hali haɗe da ƙoƙari irin nata, ga taurin zuciya da rashin tsoro, cikin dabara ta kai hannu ta bude plate ɗin cappuccino ba tare da Sharifat ta jita ba, sai hira Sharifat ɗin take zuba mata, tana bata labarin kyan Yah Ramish ɗin.
A hanzarce ta zuba maganin kaɗan a ciki, ta sake zubawa a cikin coffee ɗin ma kaɗan sabosa ƙoƙari irin nata. Tana yi kirjinta na dukan tara tara, ita kuma Sharifat sai surutu take zubawa suna tafiya a hankali cikin natsuwa, saboda girman tray ɗin yasa bata ji an taɓa komai ba.
Kaɗan kaɗan ta zuba maganin kamar yadda suka umarceta, ta yi maza ta dunƙule kwalbar a hannunta kasancewar sun fito wajen haske. Fargaba da faɗuwar gaba ne ya kusa kasheta, zuciyarta sai bugawa da karfi karfi yake yi, da kyar ta haɗiyi yawun wahala, wani irin jan numfashi da ta yi har sai da tasa Sharifat ɗin ta ɗan ci birki tare da tambayarta lafiya kuwa?.
Cikin dakiya ta ce babu komai su je kawai, duk a ruɗe take, gabanta na faɗuwa, sai karanto addu'oi take yi dan ta ji sassauci a cikin zuciyarta...... Kai Leesharh ba dai karfin hali da dakiya haɗe da taurin zuciya ba, kai irin wannan ɗanyen aiki haka? Ko tsoron asirinta ya tonu bata ji yarinyar nan, idan ta sa kanta zata yi abu, to fa sai ta yi. Ashe ba'a banza masu nikaf suka ɗaukota ba, ashe sun san wa suka ɗauko, yo dama Allah na tuba mu jinin ƴan Nigeria ai fin haka ma zamu aikata ba tare da tsoro ko shakka ba, ai mu karfin halinmu tare da jajircewa a jininmu yake, dan haka kada ku yi mamakin idan Leesharh ta aikata fin haka, yauwa jininmu a tafashe yake, babu abin da baza'a samu a Nigeriarmu ba, mu ai ba'a isa a mana gorin komai ba ato...........🥱
(Jinjina gareki Leesharh jikar baba bola Ahmad tinunbu🥱 kina da karfin hali irin na jikokin tinunbu,🔥 kin ci lambar ya bo, dole villa ta san da zamanki, irinki ake turawa aikin soja🥱)
Cigaba da tafiya suka yi. Sun ɗanyi tafiya mai nisa kafin su kai bakin haɗaɗɗen katafaren part ɗin nasu.
"Leesharh ki jirani a nan ina zuwa". Ta faɗa tare da nufar cikin part ɗin. Ita kuma Leesharh ta tsaya a bakin stair case da ya yi ƙasa.
Shiru ta yi tana tunanin me zai faru idan bawan Allah Ramish ya sha wannan maganin?. Tana son buɗe hannunta ta kalli maganin, amma tana tsoron yin hakan, dan tana zargin wajen da take ɗin da akwai camera. A hankali ta fara jiyo takun sahun mutun yana haurowa saman stair case ɗin, kuma daga jin wannan taku kasan bana ƙananan yara bane. Wani irin tsoro ne ya kamata wanda yasa ta watsa a guje ta bar wajen, kai tsaye hanyar da suka bi suka zo ta nufa.
Ita kuwa Sharifat ta kaiwa yayan nata cikin parlournsa, yana zaune saman sofa, jikinsa na sanye da hoodie mai bala'in tsada launin milk color, ya sanya hular rigar a kansa, kasancewar hular rigar ta gaba akwai gashi gashi kamar jikin mage, hakan yasa ba'a ganin face ɗinsa da kyau, ya yi matuƙar kyau sosai a cikin kayan, sai dai kayan kusan kalar fatarsa ce. Kyawawan fararen ƙafafunsa na'a saman haɗaɗɗen carpet ɗin tsakiyar parlourn mai bala'in laushi, ya mike kafafun yana latsa waya, da alama shirin fita ya yi abincinsa kawai yake jira.
A gabansa saman center table ta ɗaura tray ɗin, cikin girmamawa ta ce "Yah Ramish ga abincin nan".
Ajiye wayar ya yi a gefensa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kai hannu ya ɗauki cup ɗin cappuccino ya fara sha. Ita kuma Sharifat ta zauna a gefensa saman sofan da yake ɗin tana faɗin. "Yah Ramish fita zaka yi ne?". Da alama ta mance da cewa ta ajiye Leesharh a bakin kofa tana jiranta.
Kai kawai ya gyaɗa mata alamar e fita zai yi ba tare da ya yi magana ba. Cikin nutsuwa ya fara shan cappuccino. Ita kuma ta mayar da hankalinta kan Tv dake magana.
Tas ya shanye cappuccino kafin ya miƙe ya nufi cikin master room ɗinsa. Dawo da kallonta kansa ta yi tana son ta tambayesa ba zai ci abincin bane? Sai dai kafin ta tambayesa ya wuce cikin ɗakinsa.
Jiransa ta yi har sai da ya fito sanye da haɗaɗɗun takalma a ƙafafunsa, wayarsa ya zo ya ɗauka. "Ki barmun abincin a nan sai na dawo zan ci". Ya faɗa a sanyaye tare da nufar waje da sauri.
Kafin ta amsa mashi da okey ma ya fice. Sai lokacin ta tuna da cewa Leesharh na waje ga kuma Ramish zai fito, da sauri ta miƙe ta bi bayansa, dama dayawan lokuta idan ta kawo mashi abinci yin zamanta take yi a part ɗinsa, wani lokaci ma har barci ya ɗauketa, idan da daddare ne ta yi mashi barci a ɗaki sai lokacin da ya gama abin da yake yi sai ya mayar da ita room nata, idan su Bilal sun shigo kuma sai ya ce su mayar da ita. Magana ta gaskiya Sharifat tana son Ramish sosai, shi take burin aura, sai dai shi bai san da hakan ba, kuma babu hakan a gabansa, ita kuma ta kwallafa rai a kansa sosai, shiyasa take son zuwa in da yake, idan tana wajensa mantawa take yi da kowa da komai........,....... Lallai kuwa Sharifat tana kwale kwale, amma kuma idan ta ce shi take so anya zai iya yi wa Abu Abdussalam musu kuwa?🤔 Amma kuma ina tausayawa Sharifat gaskiya, dan son wanda baya sonta take yi, wanda ma bata isheshi kallo ba, kai suma dai da nasu cakwakiyar kunji my people's, mu fita harkarsu, kowa ma da nashi cakwakiyar a littafin nan, yanzu kuma kowa zai fara buga wasansa iya wasa, yanzu game zai fara, zamu ga winners, idan kun ji ana cewa tseren mutuwa to wannan cakwakiyar na cikin littafin nan ne, yanzu dai zamu afka cikin ainahin labarinmu da kuma cakwakiyoyinmu kala kala.
A ɓangaren Leesharh kuwa, tana watsawa a guje ta nufi hanyar koma ɗakinta. Dai'dai zata fita cikin wannan ɗan siririn hanya mai ɗan duhun suka ci karo da mutun, hakan yasa kwalbar maganin hannunta ya faɗi ƙasa ya fashe. Wani irin baya baya ta yi tana ƙoƙarin faɗuwa.
Da kyar ta iya riƙe kanta ta tsaya, goshinta ya bugu da nashi ne sosai. Kirjinta kara tsananta bugu ya yi saboda tsoro da tunanin da waye ta yi karo? Ga kwalbar maganin ya faɗi ya fashe, shikenan asirinta ya gama tonuwa, yanzu idan aka ga maganin kuma idan wani abin ya sami Ramish kashinta ya bushe!.
Shi kuwa Obaid da farko ya ɗauka da Sharifat ce suka yi karon shiyasa bai yi saurin dalla mata mari ba, sai da ta ɗan ja baya ya gane ba Sharifat bace, cikin fusata ya matso tare da sharara mata wani gigitattacen mari a karo na biyu wanda ya sanyata dai'na gane komai.
Wani irin azaba ya ji a ƙafarsa lokacin da ya matsa kusa ya mareta, ba komai ne yasa hanan ba kuma face taka kwalbar maganin da ya fashe ya yi, ƙafafunsa suna da laushi sosai, hakan yasa kwalbar ta yi saurin fasa mashi namar cikin tafin kafar tasa ta shige ciki. A hanzarce ya kai kallonsa kasa kan...............
To fa akwai cakwakiya, Ramish ya sha maganin nan! Ko maganin menene? Ga Obaid kuma ya kara dallawa Leesharh mari a karo na biyu! Da alama asirin Leesharh zai tonu! Dama kunsan Obaid yana zarginta, ya kuma kafe lallai lallai ita mai laifi ce abar zarga, ga kwalbar maganin ya faɗi ya fashe, bugu da ƙari ya fasa mashi kafa, akwai cakwakiya ba kaɗan ba, dama da Guyson suka ci karo ne, to da da sauki, amma Obaid fa, tab Leesharh kina ruwa wlh, sai dai muce Allah ya ceceki!..
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
FOREST🏞️ 🔥
Zaune Pretty take a cikin Raminsu tana daddaka ganye da wannan farar abin mai kama da lu'ulu'u nasu da suke daka, ita kuma Sweetie tana kan gado ta yi shiru tana tunanin Kamran.
Wani irin sauti Pretty ta ji ta bayanta yana fita suuuuu, sirrrrrrrr haka, da sauri ta juyo domin taga menene?. Ai kuwa tana juyawa suka yi ido huɗu da wani murtukeken kumurcin maciji bakin kirin da shi kwance a kusa da dutsen da Kamran yake zama idan ya zo. Macijin yana da girma sosai da sosai, ga shi bakin kirin.
Wani irin ihu ta kurma tare da miƙewa tsaye. Ihu da ta yi yasa macijin girgiza jikinsa ya kuma miƙe daga kwanciyar da ya yi, sannan ya yi wani irin kananannaɗa kamar ba lafiya ba, wannan maciji kamar ba maciji ba.
A guje ta miƙe tare da rugawa wajen ƴar uwarta, hannunta ta riƙo tana faɗin. "Tashi mugudu Sweetie, mun shiga uku maciji a ɗakinmu". Da karfi ta yi maganar cikin ihu.
Ai a dubu ita ma Sweetien ta miƙe, hannunta Pretty ta riƙe gam suka nufi waje da gudu. Ai kuwa macijin yana ganinsu ya rufa masu baya.
Da gudun gaske suka fito cikin ramin, sai jan hannun Sweetien take yi, baiwar Allah bata iya ganin komai sai yadda aka yi da ita. Gudu suke yi basu san ina suka nufa ba, shi kuma macijin da kyar ya fito daga cikin ramin, saboda hawace tana yi masu wahala, ko da ya fito babu alamarsu a arear, habawa Pretty sarkin tsoro tuni ya ja Sweetien suka bar arear wajen. Waige waige snake ɗin ya fara yi kamar yadda macizai suke yi idan suka bi mutun ko idan zasu yi mugunta. Ya fasa kai tare da ɗago kan yana nemansu.
Ganin babu alamarsu a wajen ne yasa ya kwantar da kansa ƙasa ya fara bin cikin ciyayi suuuuuuuu ya tafi.
Su kuwa gudu suke yi babu kakkautawa, basu fa san ina suka dosa ba bayin Allah, sai fincikar Sweetie pretty take yi suna tiƙar uban gudu.
Basu fargaba sai ganin wata bakar damisa suka yi a gabansu. Wani irin birki Pretty ta ja har sai da Sweetien ta kusa faɗuwa, a hankali ta fara ja da baya da baya. Suna ta zuba uban haki Sweetie ta tambayeta lafiya suka tsaya?.
Ƙasa iya yin magana ta yi, dara daran idanunta na'a kan hakwaran wannan damisa da yake ta faman buɗe baki. Ai bata san lokacin da ta saki fitsari a jikinta ba, zuuu fitsarin ya ganganro ƙasa, tana son ta yi kuka, amma ta rasa ina kukan nata ma ya tafi, wani irin kakkarwa jikinta ya fara yi kamar wadda sanyi ya kama, ji take yi shikenan yau kwananta ya kare.
Sai yau ta tuna da addu'ar da mun ɗinsu ta koya masu na idan sunga miyagu zasu cutar da su, sai dai ta ƙasa iya furta addu'ar ma. Sambatun Sweetie na tambayarta lafiya ne ya dawo da ita cikin hayyacinta.
Kuka ta fashe da shi mai tsananin sauti tare da cewa. "Sweetie mun mutu yau, damusa ce a gabanmu, baki ji gurnaninta ba? Mun mutu yau kam!". Tana kai karshen maganar ta kara sautin kukan nata.
Sweetie na ƙoƙarin yin magana kirjinta na dukan uku uku duk da ita bata kalli damisar ba, bata san ya take ba, amma ta tsorata, tana ƙoƙarin tambayarta damisar Kamran ne wato Rocky. Bata kai ga yin maganar ba damisar ta daka wani uban tsalle ta haykewa Sweetien wanda hakan yasa ta zube ƙasa hannunta dana Prettyn ya rabu, Prettyn ta saketa dan dole ta faɗi ƙasa a gefensu ita ma.
Ƙoƙarin capko wuyar Sweetien damisar ta yi, baiwar Allah bata gani sai ƙoƙarin kwatar kanta take yi, tana ta buge buge da hannunta.
Ganin hakan yasa Pretty ta miƙe tsaye, zuciyarta tafasa yake yi kamar an ɗaura dalma a wuta, jikinta na tsuma, da taga yadda Sweetie ke buge buge da hannu da kafa, ga shi jikin damisar ya rufe jininta ba'a iya ganinta sai hannu da kafar da take ta bubbugawa a ƙasa tana neman yadda zata kwaci kanta.
Ganin haka yasa Prettyn ta yi tunanin ko damisar cin namar Sweetien take yi, ta kara tsorita over! Jikinta na tsuma tana tsotace, nan take ta ji wani karfi ya zo mata, zuciya ba zata iya gani a kashe mata ƴar uwa ba, da wani irin mahaukacin gudu ta nufi damisar, ita kanta bata san ta nufe shi ba, jini ba wasa ba, tashin hankalin kada ƴar uwarta ta mutu ne yasa ta nufi damisar ba tare da saninta ba, bata san tana da karfin zuciya har haka da zata iya tinkarar damisa ba har sai da taga Sweetien a gaɓar mutuwa. Wani irin kukan kura ta yi ta haye saman bayan damisar ta fara kai mashi duka da ƴan hannayenta da basu wuce a kama a karya ba, duka take kai mashi har da su cizo, tana yi tana sambatu a kan ya rabun mata da ƴar uwarta, kada ya kasheta, wlh ita kaɗai kawai take da shi a duniya.
(Ni kam na ce ko yaushe damisa yasan duniya bare har yasan yar uwa kuma yasan ita kaɗai kike da shi a duniya? Jama'a ku taya jin abin da Pretty ke gayyawa damisa fisabilillahi 🤌 Allah sarki, duk wata zuciya mai imani ne ba zata ɗauki ganin a kashe mata nata a gabanta ba, barema su da suka taso a tare, basu da kowa, kullum suna manne da juna, suka kwanta ciki ɗaya kuma suka sha nono lokaci guda, ai fin haka ma Prettyn zata aikata)
Baiwar Allah ihu take tamkar maƙoshinta zai ɓalle, komai rashin imanin zuciya ta gansu a wannan hali sai ta tausaya masu. Wani irin girgiza damisar ta yi sai ga Pretty ta faɗo ƙasa tim.
Ɗago kai damisar ta yi daga kan Sweetien tana kallonta, duk ta farfasawa Sweetie wuya da faratunan hannunta, sai dai bata kai ga tsinke mata maƙogoro ba, har yanzu akwai rai a jikinta.
Ihu Prettyn ta sake kurmawa ganin jinin dake malala daga wuyar ƴar uwar tata, da karfi ta miƙewa tsaye, cikin dakiyar zuciya da ita kanta bata san tana da shi ba sai yau data ga bone, da Sweetie ta mutu gara mata ta rinkari koma wace iriyar masifa ce. Wani katon itace dake kusa da ita yashe a ƙasa ta ɗauko, idanunta ya rufe sosai, gadan gadan ta nufi damisar, a lokacin kuma damisar ta mayar da kanta kan Sweetie tana ƙoƙarin lamusheta.
Da karfi Prettyn ta daddage ta bugawa damisar itacen a kai. Hakan yasa ta ɗaga kanta sama ta saki wani uban gurnani mai tarwatsa ƙwaƙwalwale masu sauraro. Ita kanta Pretty sai da ta jefar da itacen ta sanya hannu ta toshe kunnuwanta, tare da runtse idanunta ta ɗan yi baya.
Wani irin dip da ta ji a kusa da ita ne yasa ta yi saurin buɗe idanunta. Damisar ce a gabanta, ta baro kan Sweetie ta tinkarota, shi ne ta yi tsalle daga kan Sweetien ta diro a gabanta hakan yasa ta ji wannan dip ɗin.
Sai a lokacin kuma ta dawo cikin hankalinta ta gane ashe fa damisa ce a gabanta, duk buga mata itace da ta yi bata cikin hayyacinta ne, tsoron rasa ƴar uwarta yasa ta yi duk abin da ta aikata. Yanzu kuma da ta juyo ta kanta sai ta fara tunanin mutuwa zata yi, nan take ta fara hawaye.
Cikin takun ƙatsaita damisar ta tunkarota. Habawa kafa me naci ban baka ba? Da wani irin mahaukacin gudu ta juya ta nufi barin wajen, da gudu damisar ta rufa mata baya, gudu take kamar walkiya, kamar zata tashi sama, tana gudu kuma tana ihun a kawo mata ɗauki.
(Gaskiya duk da sun ban tausayi a wannan waje, kuma na yi kwallah, amma wlh sai da Pretty ta sake bani dariya😅 dan ni kaɗai naga irin gudun da take yi kamar walkiya😅 Allah sarki gudun cetan rai😥💔 ko in da take kawa bata sani ba, yi take kamar zata fire sama kawai)
Ita kuma Sweetie jin damisar ta bar kanta ne yasa ta miƙe jini ba ɓulɓula daga wuyar tata, ta kai hannu ta rike wajen tana kuka gwanin ban tausayi, ga shi bata iya gani, haka ta bazama cikin dajin nan tana layi tana kiran sunan Pretty, kuka take yi sosai gwanin ban tausayi, sai kutsawa cikin dajin take yi ba tare da ta san ina ta nufa ko in take takawa ba.
Hanyar yamma ta nufa dan neman Prettyn tana kuka, ita kuma Pretty ta yi gabas ne, so kwata kwata ma basu haɗa hanya ba. Bata yi nisa a lalluɓen hanyar da take yi tana tafiya ba sai ga wasu jiga jigan zaratan matasan maza da mace ɗaya masu ji da lafiya sun sha gabanta, dukkansu sanye suke da fararen kaya tas except macen, kumma dukkansu suit ne a jikinsu, macen kuma wani irin kaya ne mai kama dana mayaƙa ta sanya, macece da a shekaru ba ba zata wuci 22 years ba, mazan kuma zasu iya haura 30 haka. Face ɗinsu da wani irin bakin fenti na zanen bakar damisa, ba zaka taɓa iya gane su wanene bane, maza ne majiya karfi madaka katti. Su goma ne cif sai macen. Daga sama har ƙasa su da gani kasan daga wani ɗaular suka fito, dan babu harkar karanta a tattare da su, sun jiku da naira, sai dai kuma babu alamar imani ko ɗigo a tattare da su, sannan babu annufi a kan fuskokinsu, duk yadda aka yi waɗan nan basu ƙunso alkhari ba!! Dan daga ganin yanayinsu kasan babu lafiya!.
Macen cikinsun lafiyayyar mace ce wadda da kallo ɗaya zaka yi mata kasan e lallai ta karɓi horo iya horo bana wasa ba, macece amma damtsen hannunta kamar na Assistant commander wato HOORAIN, daga ganin wannan mayakiya ce ko dai wani abin makamancin hakan. Macen ce ta matso ta ɗauki Sweetie cak ta saɓa a saman shoulder ɗinta, da alama nemanta ne ya kawosu cikin wannan daji, duk yadda aka yi sun san face ɗin Sweetien kuma ita suke nema, dan suna ganinta babu wata wata suka nufeta, duk yadda aka yi ita ce dalilin zuwansu wannan dajin. (Da alama Sweetie ce zata kai mu ga RAWANIN ZALINCI)
Gaba da ita macen ta yi, waɗan nan zaratan mazan suka rufa mata baya, da alama itace shugabansu, kuma itace karama a cikinsu, duk sun fita shekaru, amma yadda suke yi mata biyaya sun yi mubaya'a zaka gane e lallai duk yadda aka yi ta fisu matsayi. Gata jajircecciya, daga gani jininta a tafashe yake.
Tafiya suka yi da Sweetien ta hanyar da suka fito, sai sambatu take yi tana kiran sunan Kamran da kuma Pretty, Allah sarki bata ma san wanene ya ɗauketa ba. Su kuma sam babu wanda ya ce mata ko sannu a cikinsu, kuma ba kayan mayaƙa ne a jikinsu ba bare muce mayakan da suke nemansu su da mum ɗinsu ne suka kamata, ko dai su ne suka sake yin ɓadda kama da fararen suit? To lokaci ne zai nuna mana koma su wanene.
A ɓangaren Pretty kuwa, tana tsaka da tikar gudu wannan damisa ta daka wani uban tsalle da nufin ta sauka a kanta, sai dai bata kai ga yin hakan ba Kamran ya shiga tsakaninsu, dan kuwa hanyar da Pretty ta biyo hanyar kogonsu ne, yana zaune a saman dutsen a waje suna hira da Mammarsa ya jiyo ihu tun daga nesa, ko ba'a gaya mashi ba yasan ita ce, dan muryarta hadda ya yi mata. A ɗari ya miƙe Mamma na kiransa amma ina, ko kallonta bai yi ba, da gudun gaske ya nufi in da ake ihu, to kun ji yadda aka yi.
Ai kuwa yana shiga tsakaninsu damisar ta sauka a kansa, rigizib ya zube ƙasa. Habawa hayke mashi damisar ta yi, kokawa da ita ya fara yi yana ƙoƙarin kwatar kansa, ita kuma damisar da waɗan nan shegun faratu nan nata duk ta farfashe mashi fuska, so take ta damki maƙogwaransa ta tsinketa ta kashe shi.
Ita kuwa Pretty da bata san ma da cewa Kamran ya zo ba, cigaba da tikar gudunta kawai ta yi tana ihu, a tunaninta damisar na binta, gudu take yi sosai har ta bar yankin mai gabaɗaya, ta yi nisan kiwo.
Kamran kuma gabaɗaya damisar ta gama da shi, ko motsin kirki baya yi, duk ta farfashe mashi fiska jini na malala, tana ƙoƙarin capko wuyarsa da bakinta dan ta ƙarisa kashe shi kwatsam ba zato ba tsammani sai ta ɗaga kai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 74 Chapter of 75