Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amsa tana murmushi. "Oh momma dama wannan kallon tarko kenan kuke haɗa mana ko? Kusa mu faɗar gaskiya ba shiri, to yau na gano sirrin, amma momma daddy ne ya koya maki ko? Dan nasan ke ba haka kike ba tun farko......" Tarar numfashinsa ta yi da cewa. "A'a ni dai na koya mashi, kasan ai ni ta daban ce". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Kai momma daddynmu fa na daban ne, ni nasan shi ya koya maki". "To duk dai ba wannan ba, gaya mun menene yake damunka kada ka mantar da ni?". Ta yi maganar tana ƙoƙari janye hannunta daga riƙon da ya yi mata, dan ta lura suna hirar nan zai iya kyaɓe mata flowers ɗinta, saboda yana magana yana mancewa da cewa hannunta ya rike. "Kai momma keko? Ba zaki bar mutun ba sai dai ya gaya maki ɗin, wai ma ni ya aka yi kika gane cewa ina da damuwa ne?". "Saboda ni na haifeka mana, kuma ba zan bari ba sai na ji me yake damun mun kai". Shiru ya ɗan yi yana jin kaunar mahaifiyar nan tasu, tun jiya yake fama da damuwa a kan aikinsa, ya so su zauna da Jawad su yi magana, amma ina bai samu dama ba, Jawad yana can yana soyayya, babu wanda ya iya gane cewa yana a cikin damuwa sai mommarsa, ya je wajen King almost sau uku, amma King bai iya gane yana cikin damuwa ba, ita kuma da kallo ɗaya ta yi mashi ta harbo jirginsa. "Tunanin me kake yi?". Ta katse shi. Ɗago da kallonsa ya yi izuwa saman face ɗinta, ba zai iya gaya mata abin da yake bincike a kai ba, saboda yasan halinta da zafin zuciya, yanzun nan sai ta ce da King dole a rufe wannan Company kuma dole a kama masu haɗa magunguna da kayan mayen nan, momma fa bata da sauki ko kaɗan wani lokaci, ko da yake su dama modarawa ina suka ga sauki? Ai da manya da yara duk a jininsu abin yake, akwai su da ɗaukar zafi ba wasa. "Momma wani bincike nake yi yake saka mun zafin kai, ina ganin ma zan yi tafiya na ƴan kwanaki". "Dubai zaka je?". Girgiza kai ya yi alamar a'a. Baya son gaya mata in da zai je, sannan kuma baya son ya yi mata karya, domin bai san me zai je ya dawo ba, saboda Company ne da suke da haɗaka da manyan campanoni daga ƙasashen turawan yamma, reshe suka zo suka kafa a nan, amma ainahin daga waje ake shigo da duk wasu gurɓatattun kayan aikin da sauransu, to idan ya banƙaɗo sirrin bai san a iya ina rigimar zata tsaya ba, dan abu ne na manyan kai, baya son ɗagawa mahaifiyar tasa hankali. "Brazil zaka je?". Ta sake jefo mashi tambayar. "Momma ban fa tabbatar da zan yi tafiyar ko ba zan yi ba, ina tunani ne kawai, sai na tabbatar". Ya faɗa a fili, a cikin zuciyarsa kuma ƙudurin tafiya binciken daga wani kamfani ne na waje ke turo waɗan nan kayayyakin, zai yi hakance kuma domin ƙara samun hujja, kunsan cikakken ɗan jarida komai da hujja yake yi, sai ya riƙe hujjoji masu zafi yake fasa kwai, to shi ma hakance. Sallamar Obaid and Omaid ne ya katse masu hirar ta su. Ji suka yi tamkar su juya su koma na ganin Jaish a parlourn da suka yi, sam basu son haɗuwa da yayan nasu inuwa guda, domin kuwa ya rinƙa tuhumansu kenan, kuma ya rinƙa yi masu nasiha kenan, su kuma basu so. Amma da yake sun rigada sun shigo, sai suka ƙariso ciki kawai. A kusa da mommar tasu suka zo suka zauna, sai dai a ƙasa saman carpet, sun wani nutsu tamkar wasu alaranmomi daga babban masallacin Madina, irin Jaish ya ce yanzu suna da nutsuwar nan, waɗan nan ƴaƴa sun san kan duniya. Cikin girmamawa suka ce. "Yah Jaish ina wuni?". Bai yi mamaki ba, dan shi fa yasan su waye su, fin haka ma zasu aikata in dai su ne. Da lafiya ya amsa masu sannan ya ɗaura da cewa. "Me yau kuma kuka aikata?". Ajiyar zuciya suka sauke a tare, faɗi suke yi a cikin zuciyarsu cewa ko zamu mutu sai Yah Jaish ya ɗaura mana ayar tuhuma, mu dai mun shiga uku, wai kullum mu cikin aikata abu muke yi. A fili kuwa sai cewa suka yi. "Yah Jaish babu abin da muka aikata fa, mu fa yanzu we're so silent, innocent and babu ruwanmu da kowa". Ita dai Momma sai murmushi take yi, dan tasan halin kayanta, tana da tabbacin sun yi wani abin kamar yadda Jaish ya zarga, baya zargi a banza ai. Kuma da gasken ne sun yi wani abin kamar yadda ya faɗa, mugunta suka shiryawa mama a daren yau, dan gobe zasu koma Dubai an buɗe school, shi ne ma yasa suka zo yin hira da mommsrsu, dan zasu koma, to tabbas sun aikata wani abin ne, shi ne dan iya shege har da wani kara nutsuwa kamar wasu limaman masallacin harami. "Kun gama shirin ku ko?". Jaish ya tambayesu. Har suna haɗa baki wajen ce mashi e sun kammala shiri. "To ku dai tsaya ku yi karatu, kuma a duk in da kuke ku sani Allah yana ganinku idan mu bama ganinku, ku rage rashin ji, ku nutsu ku dai'na zalintar kowa, na gaji da jin sunanku a bakunan mutane, yadda kuka san ku kaɗai ne student a makarantar nan naku, ko ziyara na kai maku sauran students har tsayawa suke yi suna satar kallona, saboda yayanku ne ni, duk kun takurawa yayan mutane a makaranta, ku akwai wanda ya takura maku ne? To wlh ku nutsu, idan ba haka ba Allah next time na sake jin wani abin kun aikata, to ba makawa sai na miƙaku ga kasar Faransa ku je ku zama sojojinta na dai gaya maku, tun da ku dama wahala bata yi maku komai, kun saba da yin up and down". Zaro idanu waje suka yi, har suna haɗa baki wajen cewa. "Allah Yah Jaish mu mun nutsu yanzu, ba zaka sake jin komai ba, mun tuba, dan Allah ka bar maganar ƙasar France ɗin nan, mu bama son ji". "In dai baku son ji to ku nutsu, idan ba haka ba kun san dai bana magana biyu". Omaid ne ya ce. "Ni dama can babu ruwana, Obaid ne baya ji" (Tab wai kun ji Omaid babu ruwansa🤔 bayan kuma ya fi Obaid iya mugunta da rashin ji😅) "Kai Omaid ni ma ai babu ruwana". Momma dai murmushi kawai take binsu da shi, dan ita bata da ta cewa, yaran nan nata sai addu'a, dan ma yayyunsu maza sun tsaya tsayin daka a kansu ne, da wlh Obaid and Omaid sai Allah, rashin jinsu ba zai tsaya a iya nan ba, amma Alhamdulillah, a cikin kingdom of power idan suka zo su Jaish basu kyalesu ba, suna kula da su tare da yi masu faɗa da nasiha, dan nasiha tafi tasiri a zukatan mutane sama da faɗa ko duka, wani ma idan ka dake shi sai ya ce ba zai yi abin da kake so ɗin ba sai dai ka kashe shi, amma koya mutun ya kai ga taurin kai wlh nasiha tana tausasa zuciyarsa koda a iya wunin ranar ce kawai, bare kuma nasihar idan aka haɗa da annabi Muhammad (S.A.W) ta fi shiga cikin zuciya ta tausasa zuciyar bawa, karya ne a kirawa mutun Allah da annabi a sake kira bai ji zuciyarsa ta risina ba, sai dai kafurar zuciya ta kafuran farko. So a gaskiya nasiha ta fi faɗa ko duka tasiri musamman ga zuƙatan yara, ku rinƙa nuna masu Allah da annabi cikin ruwan sanyi tare da dabara ta yadda zasu fahimta ya kuma nutsa cikin zuƙatansu, hakan zai sa su taso cikin kamala da nutsuwa. A Dubai kuwa ga su Ramish, suma a kullum suna yin nasu iyaka baƙin ƙoƙarin wajen ganin kannenen nasu sun nutsu sosai. Amma kuma abin mamaki yadda kuka san ba lafiya ba, kullum rashin jinsu da taurin zuciyarsu karuwa yake yi, sun iya shirya mugunta daki daki babu ko ɗar ɗar, yanzu ga shi Yusuf saurayin Sarina da mu readers muke zargin su suka shirya mashi wannan mugunta, ga shi bawan Allah nan kafin a sakesa ya koma gida baya iya tafiya da kafafunsa, commander Zafar sai da ya ragargajesu kamar ba gobe, takawa da kafafunsu dai sun ƙasa iya yinsa, a haka aka kwashesu zuwa hospital, bayan sun sami lafiya aka sallamesu zuwa gida, wai a haka ma sboda uncle Abbas an yi masu da sauki, ba dan haka ba kaciya ta biyu za'ayi masu, commander baya ɗaukar wasa ai, kuma ba abin da iyayen Yusuf ɗin suka isa su yi, domin kuwa ba wanda ya isa ya ɗaga yatsa a kan wannan masarauta kuma ya zauna lafiya, sannan kuma ai hannu dumu dumu aka kama Yusuf ɗin ba zarginsa ake ba, so dole su ja baki su yi shiru. Sosai Jaish ya yi masu nasiha mai rasa zuciyar mai sauraro, amma kuma su dai bai wani ratsa su ba, tabbas sun ɗan yi ladab, amma dai ba wai can can ba, abin nasu kamar dai ba lafiya ba. Sun ɗan jima suna hira a tare da mahaifiyar tasu kafin su miƙe su ukun dukka, sannan suka yi mata sallama suka fita. Addu'a da fatan alkhari ta yi masu har suka fice. Suna fita kuyanga Mama Haulat ta dawo cikin parlourn domin ta ƙarisar mata da lallenta, sannan ta wanke mata tare da yi mata hayakin turaren lallen da sauransu, lalle mai turare take yi mata, shi kwaɓinsa na musamman ne, ya fita daban da sauran dukkan lalle da kuka sani, shi yana yin two months kafin ya goge, kuma kullum zaka gansa kamar sabo yana kyalli, kuma zaki yi ta zuba ƙamshi mai bala'in daɗi har sai ranar da ya goge, larabawar Dubai ne suka fi yawan amfani da shi, yana da tsada sosai, ba ko'ina ake samunsa ba sai gidan mulki, shi ma sai wane da wane, to ita dai momma kowani lokaci irinsa ake yi mata, haka Gimbiya Zunaira da Chuchu ma. A bangaren Mammien Yah Jawad kuwa, haka ta yi ta jiran Jaish amma ina shiru bai zo ba, dama tasan da wuya ya zo, saboda sau da dama tana aikawa a kirasa baya zuwa, idan kunga ya je kiranta to an aiko ya zo ɗin suna a tare da Yah Jawad ne, shi ne zai je, domin kada Jawad ɗin ya ji babu daɗi, amma idan Jawad baya nan wlh baya zuwa, ko kallo ma bata ishe shi ba. Ranta ya sosu sosai da sosai, ga shi a duniya bata da burin da ya wuce Jaish ɗin ya auri Fanan, wato ƴar autarta kenan, kanwar Sarina, shi kuma abin da yasa ma kenan baya kaunar zuwa in da take, dan in dai ya je sai ta yi mashi zancen Fanan, bata ma san shi haushi Fanan ɗin take bashi ba, kai shi fa baka gane mashi, kowa ma haushi yake bashi.........😅 Tana burin Fanan ta auri Jaish ɗin ne saboda dalilai da dama, kaɗan daga ciki sun haɗa da kasancewar Jaish jika ne ga the most powerful King Badeen, and kuma ƴan uwansa daga sama har kasa part na mommarsa daga masu mulkin siyasa sai masu sarauta, sannan Jaish yana da tarin dukiya duk da bai kai mommarsa ba, momma ta fi shi kuɗi sosai, amma dai shi kuma ya fi uncle Abbas kuɗi, sai kuma kasancewar ƴaƴan Momma sun fi zama mafi soyuwa a wajen King, wannan ma yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa take son Jaish ya auri Fanan, a ganinta idan Allah yasa Jaish ya auri Fanan zasu samu dama sosai a cikin masarautar, King zai zo Fanan kamar yadda yake son Jaish ɗin, ƙudurin da take da shi na son ganin ɗanta ne a kan kujeran King zai iya cika, amma fa a nata tunanin. Sam ranta bai ji daɗi ba na rashin zuwansa, da alama akwai abin da ta shirya mashi ne wadda bata son ya tsallaka, sai kuma ga shi ya tsallaka, ranta ya sosu sosai, cikin fushi ta ƙuduri niyar sai ta yi maganinsa, zata gyara mashi zama, shi da yana can bai ma sani ba tana nan tana haukarta, har da wani ɗaukarwa kanta alkawarin ko yana so ko baya so sai ya auri Fanan, bata fa da tabbacin cewa ita Fanan ɗin tana son Jaish ɗin, ita dai tsarinta kawai take tsarawa kamar yadda take ƙoƙarin ruguje soyayyar Jawad ta gina na Rizwan, abin nata dai sai ita ta san me take nufi da bayin Allahn nan, duk so take taga kowa a cikin ƙunci ne ko yaya ne oho mata dai, lokaci ne zai nuna mana ainahin me take da buƙatar cinmawa a ranta. A bangaren su Jawad kuwa, kamar yadda ya sakata kuka ta hanyar sanyawa a ɓata mata abinci, haka ya sake sakata dariya ta hanyar kaita yawo duk in da take so, sai dai duk in da suka je sai ya tsokaneta ta ɗan yi kuka hankalinsa yake kwanciya, ita dai auta ta tara abubuwan da zata gayawa Chuchun wanda Yah Jawad ya yi mata da gangan idan suka koma gida. Ko da suka je gidan zoo ma sai da ya tsokaneta, sun je wajen wasu irin macizan mesa masu haɗiye mutane, macizan suna cikin wani irin glass mai kyau aka sanyasu, sai yawaro wasu daga cikinsu suke yi, wasu kuma sun haɗiyi saniya suna ƙawance bata gama narkewa a ciki cikinsu ba, so sun zo wajen suna kallo, sai ɗaukarsu a video suke yi, auta ta tsaya sai magana take yi wa macizan wai su nannaɗu kamar taya yadda take gani a film bari ta gani a zahiri, sai ka ce an ce mata macizan dama magana ake yi masu sai su nannaɗu ɗin, ita kuma Chuchu ta tsaresu da ido tana kallon ikon Allah, idanunsu kawai take kallo, sai dai ta takure jikinta waje guda, da alama tsoro take ji, kawai ta dake ne ta cije ta tsaya a wajen. Cikin zolaya ya ce mata. "Jannat menen a wajen kafafunki kamar kamar snaka? Kamar fa ɗan snake ɗin dake cikin glass ɗin ne ya fito......." Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata saboda wani irin ihu da ta zunduma, a guje ta bar wajen tana ƙoƙarin cire alkyabbar jikinta kamar ance mata a jikin alkyabbar macijin yake, kunsan irin wannan abin sai ka ji kamar da gaske yana taɓa maka jiki, musamman ma idan tun farko kaga macijan da idon ka, to wlh ko baa tsoratar da kai ba sai ka rinƙa jin kamar suna taɓaka, to ita ma haka ta ji, sai ta ji kamar da gaske yaron macijin ne yake taɓa mata kafa, ai kuwa ta rinƙa tsalle tana kakkaɓe kayan jikinta tana ƙoƙarin cire kayan ma gabaɗaya, sai ihu take yi. Cikin sauri ya bi bayanta, da gudu ita ma auta ta bar wajen, dan ma kada su kamata. Yana zuwa in da take ya riko wuyar alkyabbar tata dan ya hanata cirewa. Ƙanƙame shi ta yi tana faɗin. "Na shiga uku, Yah Jawad dan Allah ka cire mun shi, wlh na ji yana taɓa mun kafa". Dariya kamar zata kashe shi, yau ba karya ya yi nishaɗi over to over, bare ma idan ta zaro ido tana faɗin. Ya yi sauri ya cire mata ta ji yana haura mata saman kafafu wajen cinyarta, innalillahi Jawad kamar zai mutu da dariya, bayan rike wuyar alkyabbarta da ya yi dan kada ta cire, ya kasa iya aikata komai, saboda dariyar da yake dannewa ta hana shi ko da ɗaga hannunsa bare ya yi rarrashi. Ma'aikatan da suke wajen ne suka yi saurin ƙarisowa in da suke domin su ji ko lafiya. Hannu kawai ya ɗaga masu alamar su tafi babu komai. Cikin kuka ta ce. "Kada ku tafi, ku zo ku cire mun macijin nan kada ya kasheni, Wayyo mummyna, Yah Jawad ka mayar dani gida, ni ba zan sake fitowa ba, na shiga uku daddy yau zan mutu, idan ya cije ni shikenan na mutu". Ai a wannan gaɓar dariyar ba zata dannu ba, ta ci karfinsa a in da ya fara tikar dariya kamar wani zararre. Ita kam auta ta rigada ta gane ba wani maciji da gangan ya yi wa Aunty Chuchunta haka, dan haka sai ta sanya hakan ma a cikin lissafin abin da zata gayawa Chuchu idan suka koma gida, zata gaya mata cewa da gangan ya yi mata hakan. Ganin yana tikar dariya har da tsugunnawa a ƙasa yasa ita ma Chuchun ta ɗan tsagaita kukanta tana binsa da kallon mamaki. Da kyar ya iya tsayar da videon da yake ɗaukarsu tun farko, har murɗa mashi cikinsa ta yi saboda dariya. Jin ta ɗan tsagaita kukan ne yasa shi ma ya yi ƙoƙarin ya danne dariyar tare da miƙewa tsaye. Ɗan rungumota ya yi yana faɗin. "Ai tun ɗazun snake ɗin ya sauka daga kafafunki, ya koma wajen ƴan uwansa, kece baki gani ba". Yana magana yana guntse dariya. Duba kafafunta ta fara yi da sauri tana mai cigaba da kuka. Rarrashinta ya hauyi yana yi mata sorry. Ita dai auta ta harɗe hannaye a kirji tana ganin ikon god. "Sorry my sister, yanzu mu je muga su zaki dasu zamisa sai mu koma gida ko?". Ai a ɗari ta ce mashi. "Ni Yah Jawad ka mayar da mu gida kawai babu in da zan sake zuwa". Ɗan kara rungumeta ya yi yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. Sai a lokacin kuma ya haɗa ido da auta da ta harɗe hannaye a kirji tana ganinsu. Ido ɗaya ya kashe mata tare da ɗaga gera guda, irin alamar Malama ya ne?. Dariya ta ɗan yi mara sauti kafin kuma ta ɗan kawar da kanta tana faɗin. "Yah Jawad gida zaka mayar damu daga nan, mun yafe sauran wajen yawon". Alama ya yi mata da hannu a kan ta zo. Ba mutu ta ƙariso wajen nasa da sari, haɗata ya yi da chuchun dukka ya rungume yana kara rarrashin chuchu, sai ajiyar zuciya take saukewa, ta sha zunduma ihu kam. Sun dan ɗauki a kallah minti goma a haka kafin ya rabasu da jikinsa ya ce su wuce gidan tun da sun ce yawon ya ishesu. Chuchu ce a gaba, ta yi sauri ta wuce zuwa wajen motarsu, taki ɗagowa ta sake kallon komai a wajen, wai dan ma kada wani abin ya sake bata tsoro. Sai murmushi kaɗan kaɗan yake yi ya riƙo hannun auta suka rufa mata baya. Har suka shiga cikin mota bata dai'na sauke ajiyar zuciya ba, a haka ya tada motar suka nufi gida, sai janta da hira auta take yi, amma bata wani kulata ba, saboda hankalinta ya yi gida, so take ta koma ta cire kayan jikin nan nata, ta yi alkawarin ba zata sake saka kayan ba, zata bawa kuyangarta dake gyara mata ɗaki kyauta, dan ita tun da maciji ya taɓa kayan bata so kuma. Suna isa gida ba ɓata lokaci ta fice daga cikin motar, Jawad ya yi mamakin ganin irin saurin da take yi, ko sallama basu yi ba, bai san tana son zuwa ta cire kayan jikin nata bane. A hanzarce auta ta rufa mata baya bayan ta yi mashi sallama, har lokacin wayar momma yana hannun autar, ta haɗa kuma da wayar da Yah Jawad ya bawa Chuchun ɗazun, domin Chuchun ta bata ajiyar wayar tun da suka fita, so sai ta haɗa da wayar ta nufi cikin gida, shi kuma bai lura da ta tafin mashi da waya ba, kawai ya fito ya nufi nasa part ɗin yana ɗan murmushi. Ita kuwa auta sai sauri take yi dan ta je ta gayawa Chuchun cewa da gangan yah Jawad ya yi mata duk abin da ya yi mata ɗin nan. A ɓangaren su Kamran kuwa, wato Forest. Washegari da safe kamar yadda ya saba zuwa wajensu haka ya nufo in da suke bayan ya kammala yi wa mama dik abin da ya saba yi mata. Yana tafiya yana tunanin yadda zai yi ya fita wajen dajin nan da kuma yadda zai yi da mama ta barsa ya fita ɗin, ba zai iya tafiya bai tambayeta ba, domin yasan zata shiga tashin hankali na wuce misali, yana kaunarta over, amma kuma ya kasa iya gaya mata, domin yana tsoron kada hakan ya ja mashi rabuwa da su Pretty, ta hana shi zuwa in da suke ma kwata kwata, ƙaramin aikinta ne ta hana shi fita ma kwata kwata idan ta ji yana da burin barin wannan dajin. A kan hanyarsa na zuwa wajensu ya cikaro da Rocky, bai wani kula shi ba ya cigaba da tafiyarsa kawai, rufa mashi baya Rockyn ya yi suka jera kamar yadda suka saba, sai wani miƙa yake yi da alama ya ci nama ya ƙoshi ne ya yi barci ya tashi. Dajin gabaɗaya akwai danshi danshin ruwa, saboda ruwan saman da aka yi jiya, da wasu ganyayyakin itace suna zubar da ruwa, wasu ramukan sun cika da ruwa, idan suka zo wucewa sai Rockyn ga tsallaka Kamran yake bin bayansa, haka suka cigaba da tafiya har izuwa wajensu Pretty. A waje Rocky ya kwanta, already kunsan baya iya shiga ciki, kofar ta yi mashi ƙarami. Ciki shi kuma Kamran ya shige, ga mamakinsa sai ya tarar basu a ciki dukkansu. Zaro idanu sosai waje ya yi yana tunanin to ina kuma suka tafi? Yasan dai Sweetie ita bata fita, koda Pretty ta ce tazo suje waje, in dai ba da shi bane bata yarda ta je, kullum tana cikin abinta, to ina suka je yau kuma?. Ya jefawa kansa tambaya. Ganin babu mai bashi amsa ne yasa ya yi saurin juyawa cikin zafin nama ya nufi wajen. Rocky na kwance kamar yadda ya barshi. Bai bi ta kansa ba ya nufi wajen ƙoramar nan, dan ya duba su. Da sauri Rocky ya miƙe ya rufa mashi baya. Tun daga nesa yake baza idanu ko zai gansu, amma kuma bai ga alamar su a kusa ba, hakan yasa ya yi saurin ƙarisawa wajen, dayawan lokuta tun daga nesa yake hango Pretty a saman durse tana wasa da ruwa, to yau dai bai ganta a wajen ruwan ba. Har yana haɗawa da gudu ya ƙarisa wajen. Zaune suke a ƙarƙashin bishiya, Sweetie tana magana ita kuma Pretty ta buga uban tagumi tana kallon ruwan dake gudu a ƙasar ƙoramar. A hankali Kamran ɗin ya lallaɓo kamar wani ɓarawo, ya ce da Rocky ya tsaya yana zuwa, da yake sun saba sai Rockyn ya tsaya, sanɗo ya fara yi kamar mai son yin wani abin, da yake Pretty ta bawa hanyar da yake zuwa baya sai bata gansa ba, ita kuma Sweetie dake fuskantar hanyar bata gani, so basu san da zuwansa ba. Sanɗo ya cigaba da yi har ya iso kusa da Pretty, dama tana zaune ne a saman jijiyar bishiyar, irin bishiyoyin nan ne masu jijiya manya manya kamar jikin wani bishiyar, to a saman jijiyoyin suka zauna daga ita har Sweetien. Yana ƙarisowa wajen cikin dabara ya sanya hannunsa ya capke kan black snake dake ƙarƙashin jijiyar bishiyar ta bayan Pretty ta kuma gaban Sweetie kenan, yanayin yadda suka zauna kamar suna fuskantar juna ne, Pretty tana fuskantar ruwa, ita kuma Sweetie tana fuskantar hanyar dake bayan Prettyn, so Pretty ta bawa macijin baya shiyasa bata gansa ba, ita kuma Sweetie bata gani ma bare ta ganshi, ga shi kuma a gabanta, sai dai bai yi yunƙurin cizonsu ba, yana kwance ne shiru shi ma macijin, da alama ma kamar bai ji motsinsu ba, kuma dai hira suke yi a kan mum ɗinsu, suna tattaunawa a kan ina take? Ina ta shiga? Ina ta tafi ta barsu? Ta mutu ne ko tana raye? Suna kewarta. Yana damke kan maciji, macijin ya harɗe mashi hannunsa da bindinsa, matse kan ya yi da karfi dan ma kada ya fito da waɗan nan shegun harshen nasa mai baki biyun ya caka mashi dafi. Kusa da Prettyn ya zauna tare da ɓoye hannunsa da ya riƙe macijin ta bayansa dan kada ta gani. Jin an zauna a kusa da ita yasa ta juyo da sauri. "Lah Kamran kai ne?". Ta faɗa cikin tsantsar farinciki tana sakin murmushi. Sweetie ma cewa ta yi. "Malam Kamran ya aka yi kasan muna nan?

Chapter 59 of 75