daga cikin ɗakin, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sanya hannayenta dukka biyu ta dafe ƙuncinta, duniyar tunani ta afka, yau gabaɗaya tana cikin damuwa sosai da sosai.
🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️
IDAN MUKA WAIWAYA WAJEN SU KAMRAN KUWA WATO FOREST.🔥🤍
Zaune suke a ƙasar wata ƙatuwar dutse mai girma dake kusa da wannan ƙoramar na kusa da wajen su Pretty, da alama an fasa yin harbi da kifiyar kenan, akwai itatuwan mangori sosai a ta kusa da wajen, hakan yasa suka samu ishasshen ƴalwar inuwa sosai a wajen.
Yana zaune ya jingina da jikin dutsen ya kuma lumshe idanunsa tare da ɗan ɗaga kansa sama kamar mai yin tunanin wani abin, Sweetie na zaune a gefensa na hagu saman farin yashin da yake a wajen. Hannunta na rike da lemun zaki tana ɓarewa duk da bata gani, Kamran ɗin ne ya ciro masu lemun a wata bishiya dake ɗan nesa da ƙoramar. Ita kuwa Pretty sarkin kauɗi tana zaune kusa da shi sosai, ta ɗaura ƴan kyawawan kafafun nan nata a saman nasa ƙafafun tana ɓare nata lemun, idan baku manta ba Kamran ɗin bai fito da wukarsa bane yasa suke ɓare remun da hannu, ba halin yankawa.
Shi dai Kamran ya afka duniyar tunanin abin da yake damunsa tun daga haɗuwarsa da su Pretty, kullum yana yawan mafarkinsu sosai, ga shi a duk lokacin da ya haɗa idanu da waɗan nan sexy eyes ɗin nata sai ya ji gabansa ya faɗi, tana rikita shi, ya rasa me dalili. Haƙiƙa idanunta suna da rikita mai kallonsu, wasu irin shegun sexy eyes ke gareta, amma shi nasa rikitarwar na daban ne, har tsoron kallon cikin idanun nata yake yi, gata da shegen daddaɗar zazzakar murya wanda idan ta yi magana sai ya ratsa jikin duk wani mai sauraro, ko baka son haɗa idanu da ita idan ta yi magana sai ka ji duniya baka da burin da ya wuce ka ɗaga idanu ka kalli face nata, saboda muryar nan tata akwai ratsa zuciya, sannan ga ɗan banzan shiga rai garesu daga ita har Sweetie, bugu da ƙari ga ɗan banzan wayo kamar wasu renon tsofaffi.
"Kamran ga lemun nagama ɓarewa".
Cewar Pretty, ta yi maganar tana kai hannu zata taɓa lallausan kumatunsa.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da waro idanunsa a hankali, dai'dai lokacin ta kai ɗan kyakkyawan lallausan hannunta saman kumatunsa, a tunaninta barci ya ɗan yi shi ne zata tashe shi.
Karaf idanunsa ya sauka cikin nata. Ɗauke hannunta daga saman kumatun nasa ta yi tare da miƙo mashi lemun da yake a ɗayan hannun nata tana mai do da kallonta izuwa saman gashin kansa, duk da yana sanye da hula baka iya ganin gashin kan nasa sosai, amma ya ɗan fito ta gaban goshinsa.
"Kamran kana da gashi sosai kamar mu".
Ta faɗa tana mai cigaba da kallon kan nasa.
Nisawa ya yi tare da karɓar lemun. "Waye ya gaya maki gashina kamar naku ne?".
Gyara zamanta ta yi tare da ɗauka kafafunta daga saman nasa, ta yi zama irin na masu cin abinci ta lankwashe kafafunta dukka biyu suna fuskantar juna.
"Babu wanda ya gaya mun, kawai na gano yawan gashin naka ne duba da yadda ya cika hular kanka, hakan yana nufin gashin na dayawa sosai".
"Pretty ke dai kin cika sa ido".
Ya bata amsa yana mai raba lamun da ya karɓa daga hannun nata gida biyu. Bayan ya raba biyu sai ya miƙo mata rabi.
Maƙe mashi ɗan kafadarta ta yi alamar bata so tana faɗin.
"Ni bana saka ido, daga magana kawai sai ka ce na iya saka ido? Kuma ni ba zan sha lemun ba".
Ta kai karshen maganar tare da yunƙurawa zata miƙe, ita a dole ta yi fushi tun da ya ce mata mai sa ido.
Cikin hanzari ya kai hannunsa ya riƙo nata hannun yana faɗin.
"To sarkin fushi yi hakuri, am so sorry baki da sa ido shikenan?".
Tana ƙoƙarin sake yin magana Sweetie ta katsesu da cewa.
"Hmmmm ita kam ma ai ta ji daɗi tun da tana da idon da zata yi kallo har ace mata tana sa ido, ni kam sai dai na kalli abu da zuciyata".
Wani irin yanayi mara daɗi dukkansu suka ji da jin maganar Sweetien, haƙiƙa maganar ta taɓa zuciyar Kamran sosai, wani irin tausayinta ne ya kamashi, ya sani rashin ido babu daɗi sam, ga shi a yadda ta yi maganar kamar zata yi kuka sai ka ji kalaman nata sun ratsa maka zuciya sosai, sai ka tausaya mata duk taurin zuciyarka, ita ma Pretty da take sarkin kauɗi ta ji kalaman har cikin ranta bare shi Kamran da dama already yake sarkin tausayi mai zuciyar musulman farko, ai dole ya tausaya mata.
"Our Sweetie idanunki zasu buɗe nan bada jimawa ba kin ji ko? Kada ki damu kanki, zan nemo maki magani".
Cewar Kamran, ya yi Magana da wata iriyar murya wadda da ka ji ta zaka san lallai maganar tata ta taɓa mashi zuciya.
"Allah yasa ka samu maganin Kamran, ina son idanuna su buɗe, ina son na ga ya fuskarka take? Ina son sanin kamanninka, saboda kai kawai nake burin idanuna su buɗe".
Har lokacin yana rike da hannun Pretty bai saki ba ya bata amsa da. "Nan ba da jimawa ba our Sweetie, zaki samu lafiya sosai kamar baki taɓa yin ciwo ba".
"In Sha Allah, zan tayata da addu'a sosai nima". Cewar Pretty.
Maido da kallonsa a kanta ya yi yana kallon ɗan bakin nata da ta furta In Sha Allah ɗin.
"Take your orange".
Ya faɗa yana mai miƙo mata rabin lemun.
Sarkin rigima kara maƙe mashi ɗan kafaɗar tata ta yi tare da girgiza mashi kai. "I don't want, ba ka ce mun sarkin fushi ba? So don't talk to me again".
Tana magana tana turo baki.
"Oh sorry ba zan sake ba ai".
Ya faɗa tare da miƙo mata lemun.
"To sake mun hannu na sai na karɓa".
A hanzarce ya saketa, shi kwata kwata ma ya mance da cewa ya rike mata hannu, ya ji hannu mai laushi luwai luwai.
Karɓar lemun ta yi tare da komawa ta gyara zamanta da kyau, sarkin rigima ce sosai Pretty.
Ta ƙasan idanunsa yake satar kallonta yadda take tsala lemun nata tsala sala, a hankali take kai sala ɗaya ɗan bakinta, idan ta kai ɗin ma ba dukka take turawa a cikin bakin nata ba, sai ta gutsira ta raba biyu, ta rike rabi a hannu ta bar rabi a cikin ɗan bakin nata tana tauna a hankali hankali kamar bata son motsa ɗan bakin, da alama akwai yauki a tattare da ita, tana kara girma kuma hakan yana kara bayyana.
Sosai yake jin daɗin kallon yadda take shan lemun, hakan yasa ya mance da nasa baya sha, saukar zazzaƙar voice ɗinta a dodon kunnuwansa ne yasa ya ɗan firgita tare da dai'dai nutsuwarsa cikin hanzari kamar wani mara gaskiya.
"Kamran muje ka cigaba da koya mun harbin kwari da bakar ko?".
Shi ne abin da ta faɗa wanda ya fargar da shi daga satar kallonta da ya lula. Ta yi maganar ita kuma ba tare da ta kalli in da yake ba.
Ƙasa da idanunsa ya yi tare da sanya hannu ya fara sala lemunsa kamar yadda ya ga ta yi, bai taɓa shan lemu irin haka ba, bai ma taɓa ganin an raba lemu a haka ba sai yau da ya gani a wajenta, shi kullum Mammarsa ce take yanka masu da wuƙa sai su ɓare su sha, yau ya ga sabon salo na tsala ta tsala sala.
"Pretty koya maki harbi da kifiya sai na shirya, gara mun na fara koya maki busa tukun nan".
Ya kai karshen maganar tare da kai lemu sala ɗaya ɗan bakinsa ya tura ciki, a hankali ya fara sha.
"Amma kuma ɗazun kai ne fa ka ce harbi da kifiya zaka fara koya mun?".
Ta yi maganar a ɗan shagwaɓe kamar yadda take zubawa Sweetie shagwaɓa, sannan ta yi maganar tana kallon kyakkyawar fuskarsa tana aikin turo ɗan baki.
A hankali ya ɗago idanunsa ya saukesu a saman kyakkyawar fuskarta. "Zan koya maki, amma ba yanzu ba gaskiya, sai na yi magana da mamana na tambayeta wani abin tukun nan, yanzun na ji na kasa ne, ba zan iya ba".
Ya faɗa muryarsa a ɗan kasale, alamar kwata kwata dai baya son ya tuna da zancen koya mata ɗin, dan shi kaɗai yasan me yake ji a duk lokacin da suka haɗa jiki, komai ƙanƙantar haɗuwar fata da tsokan jikin nasu sai ya ji jikinsa ta amsa.
Matsowa kusa da Sweetie ta yi tare da kwantawa a kasa a wajen ta tada kai da laps na Sweetie, dama kun santa sarkin son jiki ce kamar mage.
"Ki tashi a jikin Sweetie kada ki ji mata ciwo sarkin rigima kawai". Cewar Kamran, yana magana yana cigaba da shan lemunsa.
"Sweetie in yi kwanciyata ko?". Ta tambaya tana mai da kallonta izuwa samar fuskar Sweetien.
"Kullum da kike kwanciya a jikin nawa izinina kike nema ne?". Sweetie ta bata amsa tana mai kai hannunta a saman fuskar Prettyn, dogon hancinta ta laluɓa ta ɗan ja.
"Wash Allah na, Sweetie kin fara ko?". Ta faɗa tana rike hancin nata da hannu ɗaya, tana kuma turo baki.
Shiru Kamran ya yi yana kallonsu gwanin birgewa, suna son junansu sosai, akwai fahimta sosai kuma a tsakaninsu, dan Sweetie tana da hakuri ga hangen nesa sosai yarinyar duk da bata gani, Pretty kuma shagwaɓa, kauɗi, saurin kuka, son jiki, rashin iya juriyar yunwa, da dai sauransu duk ta haɗa, hakan kuma baya sa su yi faɗa a tsakaninsu, duk kuma hakurin Sweetie yasa basu yin faɗar, da ace kamar Prettyn take ba hakuri ai da tuni kullum sai sun yi ta faɗa, ita fa Pretty ko yunwa ta fara ji sai ta yi kuka saboda rashin hakuri.
"Daga yanzu ki dai'na kwanciya a jikin Sweetie tun da kin ga bata da lafiya, idan kina jin kwaɗayin kwanciya ki zo ki kwanta a jikina, kada ki kara mata nauyi kan nauyi". Cewar Kamran, yana magana idanunsa yana a kansu sosai, saboda sun burgesa sun kara burgesa sun kara burgesa over to over.
"Yauwa Kamran gaya mata dai, ni yanzu ma ka duba mun ita ta yi ƙiba ne ko? Dan naji ta kara mun nauyi, da idan ta kwanta a kafata bana jin nauyi sosai, amma yanzu sosai take yi mun nauyi in ta kwanta". Cewar Sweetie.
Lumshe idanunta kamar mai jin barci ma ta yi abinta ta kyalesu, kamar bata jin me suke faɗa, tana jin Kamran yana gayawa Sweetien ai ta girma ne yanzu shi yasa take kara nauyi, amma sam taki kulasu, dan barci barci ma take ji, yanayin weather wajen ya yi mata daɗi sosai.
Sweetie da Kamran kuwa cigaba da hira a tsakaninsu suka yi cikin mutunta juna tare da nuna kula ga juna.
Kamar daga sama gurnanin Rocky ya doki doduwan kunnuwansu. Ai a dubu ɗari Pretty ta waro idanunta. Cikin sanɗo ta miƙe daga kwanciyar da ta yi, abin gwanin ban dariya ta fara rarrafawa a kasa kamar wata mage ta nufi Kamran, tana rarrafawa tana zaro idanu nan nata kamar ka ruga a kuje idan ka gansu, tana kuma rarrafawa tana ƴan waige waige tana neman ta ina zata gano ɓullowar Rockyn?.
Abin ya so ya bawa Kamran dariya, sarkin tsoro kenan, ji yadda take sanɗo tana rarrafawa kamar wadda ta je ta yi sata, kai wannan yarinya sai shirin Allah.
Yana tsoron ya yi mata dariya abin ya zamar masu rigima, dan haka sai ya yi kamar bai ganta ba, ya kawar da kansa. Kusa da shi sosai ta zo ta zauna, har da sanya hannu ta riƙo nasa hannun a cikin nata, cikin dabara tana yi tana zaro idanu ta kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa, sai muzurai take yi tana jiran taga ta ina wannan damusa mai gurnanin zai bayyana? Cikinta har ya ɗuri ruwa.
Ita ma Sweetie tsoro ne ya kamata, barema da ta ji Pretty ta tashi daga kafarta, sai ta ruɗe, a ruɗe ta fara ambatar sunan Prettyn da kuma tana tambayar Kamran Damusa ce ta sake dawowa zata cinyesu ko?.
Ɗan satar kallon sarkin tsoro Pretty ya yi, ta wani kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa tsit da ita, kamar ba ita ba fa, duk ta nutsu, wasu malaman ladab ne suka shigeta lokaci guda ƴar kaniya, sai muzurai take yi.
"Sweetie it's Rocky my friend, don't worry babu abin da zai yi maku".
Ya bata amsa yana kai hannunsa izuwa kusa da fuskar Prettyn.
Kyasta mata yatsun hannunsa guda biyu ya yi a dai'dai fuskarta, dan yaga ta kafe waje guda da kallo.
Kara ƙanƙame shi ta yi sakamakon gurnanin Rocky da ta kara ji ya matso kusa, ta kara lefewa a jikin nasa da kyau.
"Kamran wlh tsoro nake ji, ni dan Allah ka dai'na zuwa mana da wannan Rockyn, ina tsoronsa sosai".
Ta faɗa kamar zata yi kuka, har idanunta sun ciko tab da kwallah.
Hannun nasa da ya kyasta mata a saitin face nata a hankali ya ƙarisa kai shi saman fuskar tata, lallausan kumatunta ya ɗan fara shafawa kafin ya fara yin magana.
"Pretty ko da na zo nan wajen ba tare da Rocky ba, ko na gudun mashi sai ya samoni ya biyoni, in dai a cikin dajin nan ne babu in da zanje na ɓuya mashi, kamshin jikina yake bi ya nemoni, ba dan haka ba ko dan ki yi farinciki zan dai'na zuwa da shi, amma hakan ba zai yi wu ba, yanzu dai abin da nake so da ke ki dai'na jin tsoronsa kin ji ko? Babu abin da zai yi maki".
Cikin sigar rarrashi sosai ya yi maganar, ga tausasawa sosai a voice ɗinsa.
Shiru ta ɗan yi kafin a shagwaɓe kamar zata sa mashi kuka ta ce. "To ka ce ya dai'na zuwa kusa da ni idan ya zo, kuma ya dai'na taɓani, ina jin tsoronsa sosai".
Ta kai karshen maganar hawayen da suka taru a cikin idanunta suka fara bin ƙuncinta.
Hannunsa da yake a saman kumatun nata ya fara goge mata hawayen da shi yana faɗin. "Please Pretty stop crying, ba na son ganin hawayen, in dai Rocky ne baki son ya zo kusa da ke ba zai zo ba, zan gaya mashi kada ya taɓaki, amma ki dai'na kuka kin ji? Baki ga Sweetie bata kuka bane?".
Da yake ai suna da banbanci, ita Sweetie bata da tsoron da Pretty take da shi, tana da tsoro amma bai kai ko rabin na Pretty ba, kuma ta yarda da maganar Kamran ɗin, tun da ya ce Rocky babu abin da zai yi mata sai kawai ta yarda abinta, ta kuma nutsu ta kwantar da hankali saɓani hjy Pretty sarkin raki da rigima ga saurin kuka.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/7/2024.....✍️📚🌹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________24🔥
Kara matsowa kusa da shi sosai ta yi tamkar zata shige jikinsa.
"Pretty na gaya maki babu abin da Rocky zai yi maki, kuma tun da baki so ne ya zo kusa da ke ko kuma ya taɓaki na gaya maki ba zai zo ba, please ki daina wannan kukan".
Ya yi maganar muryarsa a cike da damuwa, alamar sam baya son kukan nata.
Dai'dai lokacin kuma Rocky ya iso wajen, yana wani tafiyar ƙasaita, ya ci nama ya ƙoshi, har wani lashe baki yake yi abinsa, wasa wasa kwana biyun nan har wani ƙiba yake karawa, yana wani murmurewa.
Kai tsaye Kamran ɗin ya nufo abinsa, yana wani numfashi mai haɗe da gurnani alamar ya ƙoshi sosai.
Haba kara ƙanƙame Kamran ɗin sosai ta yi, ji take yi ma kamar ta haye jikinsa kawai, zuciyarta ta kasa yardan mata cewa Rocky ba zai yi mata komai ba, ta kasa iya yarda cewa ba zai cinyeta ba, ita dai tsan Tiger suna cin mutanen.
Kasancewar a ƙoshe sosai yake, sai ya zo kusa da Kamran ɗin kawai ya kwanta, bai bi ta kan kowa ba, bai kula su Prettyn ba, dama sai yana ɗan jin sakalam a cikinsa ne yake neman tsokana, amma tun da yana ƙoshe sai ya yi kwanciyarsa, yau dai babu shinshinar jikin Pretty.
"To kinga ma shi kwanciyarsa ya yi, ki dai'na kukan haka ya isa ko?".
Yana magana yana cigaba da goge mata hawayen nata, duk wani iri yake ji a jikinsa, ji yake yi kamar mai zazzaɓi.
Hannun nasa da yake goge mata hawayen da shi ta kai nata hannu ta riƙo shi cikin nata, a hankali ta lumshe idanunta ba tare da ta saki hannun nasa ba kuma bata tashi mashi daga saman shoulder ɗinsa ba, ta yi shiru kamar mai barci.
Shiru shi ma ya yi yana tunanin lokacin da yakamata ya koma gida ya yi, dan kada Mamma ta nemesa. Jin saukar numfashinta irin na mai barci da ya yi ne yasa ya dawo da kallonsa daga kan Sweetie dake zaune shiru izuwa saman fuskarta, ta yi mashi barci a jiki, ga shi ta ƙanƙame mashi hannu kamar nata ne.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, zuba mata waɗan nan kyawawan fararen idanun nasa ya yi yana mai karewa fuskarta kallo, ba ƙaramin kyau wannan ɗan bakin nata yake yi mashi ba, sarkin raki har ta yi barci kamar ba ita ba, ya faɗa a cikin zuciyarsa. Can kuma ya sake cewa she's so very very beautiful more than anybody that I saw in my life. Ya yi maganar yana jan doguwar numfashi tare da saukewa a hankali.
Jin shirun ya yi yawa ne yasa Sweetie ta ce. "Pretty ya naji kun yi shiru?".
Ba tare da ya kalli in da take ba ya amsa mata da cewa.
"Pretty ta yi barci".
"Dama bata da wuyar barci ai rigimammiya kawai". Ta bashi amsa tana mai gyarawa ta kwanta a wajen ita ma.
Ta wutsiyar idanunsa ya kalli ta kwanta, ya kasa iya kawar da kallonsa daga saman fuskar Prettyn ne, ji yake yi kamar idan ya kawar da kallonsa wani abin zai ragun mashi, dan haka sai ya kasa iya kai kallonsa kan Sweetien ma.
Shi ma Rocky barci ya fara yi abinsa, an ci an ƙoshi sai me? Ai sai barci. Wajen ya rage saura Kamran ɗin ne kawai idanunsa biyu, dan da alama ita ma Sweetie ta yi barci............. PRINCESS TEEMA CE TAKU TA AMANA🤍🔥
🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️
KINGDOM OF POWER 💪🔥
Kamar yadda King ya umarta haka aka wuce da su Yusuf prison na cikin masarautar in da ake rufe bayi da mayaka ana horar da su idan sun yi laifi.
Bayan King uncle Abbas ya bi domin ya je ya samu su tattauna, dan ya nemawa su Yusuf afuwa da sassauci a matsayinsa na wanda ya basu izinin shigowa, kuma a matsayinsu na ƴaƴa ga abokinsa, koma dai me tun da basu aikata fyaɗen ba ba zai so ayi masu wani tsastsauran hukunci ba. Bai san cewa shi ma King zuciyarsa a cike da tunani kan cewa ba lafiya su Yusuf suke ba, saboda yasan jin sunan masarautarsu ma kawai tamkar jin isowar mutuwa ga bawa ne, bare kuma jin sunan shi King ɗin da kansa, so ya fara tunanin ba lafiya Yusuf yake ba, dan yasan abu ne wadda ba zai yi wu ba ace a sami wani mai karfin zuciyar da zai iya tunkarar KINGDOM OF POWER har ya yi ƙoƙarin yiwa wata daga cikin gimbiyoyin masarautar fyaɗe, ko mahaukaci ne ba zai yi wannan gangancin da rayuwarsa ba!.
A ɓangaren twins namu kuwa, sarakan sharp brain, suna kwance abinsu, duk bom da yake tashi a gidan suna sane da komai, suna jin hayaniyar komai, amma tamkar babu su a cikin gidan, sai shakiyancinsu kawai suke yi a saman bed, suna ta uban dariya kamar ba lafiya suke ba, Obaid sai ya yi kamar zai yi ladab ya sake kwashewa da dariya kamar zararre, shi kam Omaid dama ba gwanin yin dariya bane ba, sama sama yake ɗan taɓawa idan ɗan uwan nasa yanayi, dan ya fi Obaid iya mugunta shiyasa baya dariya sam sam.
Su Gimbiya Zunaira kuwa suna school abinsu, bama su san me yake faduwa a cikin family part ba, su momma ma sam basu sami labari ba, amma ita Mama ta sami labarin daga bakin wata munafukar kuyangarta mai yi mata leƙen asiri, duk wani motsi a cikin gidan Mama tana sani, tana da CID da suke yi mata aikin leken asiri sosai, haka zalika Mammie mahaifiyar su Yah Jawad, duk wani abin da yake faruwa in ma a part ɗin King ko kuma a cikin fada dukka tana sani, kamar wata aljana, sai ta riga uncle Abbas jin labarin abin da aka zartar a fada, sai ka rasa ta ina take samo labaran, ta fi mama iya bala'i sau dubu, ita nata mai lasisi ne. Yanzu haka duk abin da yake faruwa a wannan part na bakin har Mammie ta samu labari, ta ji komai da ya faru daga farko har ƙarshe, zuciyarta fari kal abinta, wani irin sanyi ne ya ratsata, dama ba ƙaramin kai ruwa rana da uncle Abbas suka yi ba a kan cewa ita bata yarda wani Yusuf ya zo wajen Sarina ba, saboda idan baku manta ba ita burinta Sarina da Fanan su auri ɗaya daga cikin Prince na kingdom of power, so ita bata burin kowani namiji ya kusanci ƴaƴan nata, shiyasa ta kafewa uncle Abbas a kan lallai ita fa bata son wannan Yusuf ɗin.
Shi kuma ya ce ba makawa Yusuf sai ya zo, idan kuma Sarina ta yi na'am da shi to aure babu fashi. Wannan dalilin yasa da ta ji cewa ga abin da ya faru da su Yusuf ɗin ta fara sakin wani irin shu'umin murmushi wanda babu mai iya fassara me murmushin yake nufi sai ita da ta yi shi, ita kaɗai tasan nufin kayanta, amma dai murmushi ne mai tattare da abubuwa da dama a cikinsa, dan bana alkhari bane.
Haka zalika duk wani abin da kake son sani a dangene da fada to ka tambayi Aneesa ƴar Mama zaka samu labari dallah dallah idan ta yi niyar faɗa, sai ka rasa daga ina ita ma take jiyo labarin komai.
Idan muka koma ɓangaren Yah Jawad da Gimbiya Chuchu a hospital kuwa, yana zaune rike da waya yana latsawa, amma shi da kansa bai san ina yake shiga a cikin wayar bama, bai san me yake taɓawa ba, saboda kwata kwata hankalinsa baya a kan wayar, yana kan waɗan nan nurses ɗin da suke ta faman shafawa Gimbiya Chuchu wasu mayuka a kyawawan kafafun nata.
Baiwar Allah idanunta sun yi jajir sun ciko da kwallah, ji take kamar ta saka ihu, amma tana tsoronsa kada ya yi mata wani muguntar.
Daga karshe kasa daurewa ta yi saboda wani mai mai zafi da suka sanya mata, hakan yasa ta kasa iya cigaba da rike hawayenta, nan take suka fara simtiri a saman ƙuncinta.
Ta wutsiyar idanunsa yake kallon yadda take ruwan hawayen, ga gwiwowin nata sun yi jajir da su kamar zasu fitar da jini.
Sam bai san lokacin da a takaice ya ce da nurses ɗin su kyaleta haka ya isa ba.
Ɗago idanu suka yi suna kallonsa, sai a lokacin ya fahimci ashe ya yi magana, ɗan kara ɗaure fuska ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba, ya wani tsare gida tare da miƙewa tsaye daga saman bed ɗin, ji yake yi kamar ya fita waje ya basu waje su cigaba da yin aikinsu, amma kuma ya kasa iya yin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 75