Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baban Zainab na daban kamar yadda ta saba haɗa mashi, sai dai a yau ta zuba mashi maganin da boka ya bata, tana zuba maganin jikinta na kerma, hannunta na ɓari har ta ɗan zuzzubar da maganin a wajen, abinku da bata saba ba, tana yi tana leƙo wajen kitchen ɗin, dan sai taga kamar baban Zainab ɗin yana yi mata laɓe ne, sai taga kamar ya ganta, duk ta ruɗe zata tonawa kanta da kanta asiri, shi kuwa baban Zainab bawan Allah yana can cikin parlourn suna zuba hira da su Khadija, sai dai daga jin yadda yake magana zaka fahimci kawai ƙaƙalo maganar dan dole yake yi, dan kawai yaga ya kwantarwa da ƴaƴan nasa hankali kuma matsalar da yake a tsakaninsa da mamarsu bata shafesu ba, yana ƙoƙarin yaga bai ɗauko matsalar mamarsu ya shafa masu ba, yasa su rasa farincikinsu da kulawar da suke samu daga garesa a kullum ba. Bayan ta kammala haɗa mashi lemun ta shirya a saman try ɗin jug ɗin tare da cup's ta ɗauka sai cikin parlourn, sam bata ji tsoron kada su Khadijah su sha ya zamar masu matsala ba, ita dai bukatar ta ya biya taga abubuwa sun dai'dai ta mata kamar da....... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce ki kauce hanyar Allah kuma ki yi tunanin abubuwa zasu dai'dai tun maki? Lallai kin tabba babban kuskure kuwa, domin wane mutun, babu wanda ya isa ya ga dai'dai idan ya sauƙa daga kan haryar Allah, ai yama kullah da rashin daidai kenan har sai ya tuba, idan kuma bai tuba ba haka zai mutu cikin ƙunci da baƙinciki, ya je lahira kuma ya girbi abin da ya shuka, Allah ka kiyashemu sauƙa daga kan hanyarka, Allah ka tsaremu kaucewa faɗar ma'aiki, ka kare mu daga sauka daga turbar da ma'aikinka ya ɗauramu, duk wuya duk daɗi ya Allah ka tausaya mana ka barmu da imaninmu, ya Allah cikin jarabarwa da zaka yi mana kada ka haɗa mana da raunin imani tare da tawakkali. Kamar yadda ya saba shan lemun ya kuma ci abincin haka yau ma ya ci ya sha, sai dai fa yau ɗin ya ci ne kawai saboda su Khadija, ba dan haka ba bai da niyar cin girkinta yau, bama yau ba bai da niyar sake cin girkinta har sai ta gaya mashi in da take zuwa, idan ta gaya mashi kuma sai ya bincika yaga da gaske ne ko karya, dan haka kawai ya ji hankalinsa sam yaki ya kwanta. Bayan sun kammala cin abincin, har da su Khadijah duk sun sha lemun baban nasu, miƙewa ya yi tare da nufar room ɗinsa, ita kuma maman Zainab jiki ba kwari ta zo ta tattare wajen, ta shiga damuwa sosai na ganin yaki ya kulata, har ta yi tunanin ta bisa ɗaki ta bashi hakuri, sai kuma ta sake cewa bari ta barshi tun da ya sha maganin nan, wata kila zai sauko ya zo ya fara yi mata biyayya................ Babbar magana, akwai case kuwa ba karama ba, ga su Khadija ma dai sun sha magani, ko me zai faru? Mu dai je zuwa zamu ga komai dallah dallah, kun san ni dama da iya yi maku komai dallah dallah ta yadda zaku fahimta da kyau da kyau, to mu dai je zuwa, na yi gaba sai kunzo!. Shirin komawa kasuwa ya je ya yi tare da fitowa, bai yi mata sallama ba ya sa kai ya fice izuwa harabar gidan. Da sauri Zee and Khadijah suka bi bayansa.1k ha ciro daga cikin aljihunsa ya basu a kan su sai wani abin idan sun je islamiya, ya san ba'a rabasu da kayan kwalama. Sai zuba mashi godiya tare da adduar a dawo lafiya suka rinƙa yi, ita kuwa maman Zainab ta maƙale a windown parlourn tana leƙansu, ji take yi kamar ta je ta bashi hakuri, amma kuma idan ta tuna ya sha magani sai ta ce ina babu wani hakurin da zata bashi, da kansa zai kawo kansa gabanta yana mai ƙasƙantar da kansa a ƙasa, a nan ne zata zuba mulkinta ita kuma. Babbar magana. Tana ji tana gani ya fice ya tafi kasuwa, su Khadijah kuma suka dawo cikin parlourn, room ɗinsu suka nufa domin su yi wanka tare da ɗauro alwala su yi shirin zuwa Islamiya, dan lokacin sallar la'asar ta kusa, saura kaɗan, suna yin sallah kuma zasu wuce Islamiya. Ita ma mamar tasu nata room ɗin ta shiga ta kwanta, dan ta huta, duk a gajiye take, dutsen nan da suka hau ya ja mata ciwon kafafu................ Ni kuwa nace har da uban ciwon kafafu ma zai ja maki ai, ai kafafu ma kaɗan ne ba dai saɓon Allah ba?. Sai da suka kammala shiri cikin uniform ɗin islamiyarsu, sannan suka yi sallar la'asar, dan a lokacin an kira, bayan sun idar da sallar lafiya lou suka zo suka yi mata sallama a kan sun tafi islamiya, kuɗin kayan miya kamar yadda suka saba ta basu su sayo mata a hanya idan suna dawowa, daga haka bata sake yi masu magana ba, suma karɓa kawai suka yi suka wuce abinsu, dan sun san kwana biyun nan fa gidan nasu sai addu'a kawai. Yara masu hankalin manya kenan, kullum cikin yiwa iyayen nasu addu'a suke yi bayin Allan!. Tamkar Khadija zata dawo ta ce mata an kira sallar la'asar, sai kuma ta fasa saboda kada ta yi mata faɗa ta ce ai ita ba kurma bace tana ji. Haka suka wuce Islamiyarsu, gwanin birgewa idan suna tafiya islamiya, cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kai daga ganinsu kasan tarbiya ta ratsasu sosai. Maman Zainab kuwa barcinta ta hau yi ba tare da ta yi sallah ba, dan ta ci mugun wuyar hawa dutsen, duk gaɓɓan jikinta ciwo yake yi mata, hakan yasa da ta kwanta ta ƙasa iya tashi, sai kawai ta hau barci ƴar kaniya. Ɗan tsokaci, saɓon Allah komai ƙankantarsa yana mugu mugun nesanta bawa da Ubangiji tare da raba shi da imani, barema saɓon Allah mafi girma wato shirka, haɗa Allah da wani kenan, kun dai san maman Zainab tana da ƙoƙari wajen yin ibada, amma da yake ta saɓawa Allah kunga har abin ya fara shafar ibadarta, ko a jikinta ta kwanta tana barci lokacin sallah, to haka saɓawa Allah yake, kishiyoyi ne da rabaka da Ubangiji, daga nan kuma zaka ga komai yana taɓarɓare maka, please ƴan uwana mata, zan yi amfani da wannan dama na ja hankulanku sosai, duniya dai ba matabbata bane, kwana nawa ya rage? Lahira ita ce madauwamiya, kada ki je garin neman duniya ki ɓata lahirarki wadda kuma ita ce madauwamiya, duniya tamkar kasuwa muka zo ci mu koma gidan gaskiya, duk daɗi duk wuya kada ki taɓa yarda ki rasa lahira, gara maki ki rayu cikin ƙunci na tsawon rayuwarki da ki lalata lahirarki, Allah ka karemu da kariyarka, ka shiga cikin lamuranmu, ka dafawa musulmi da musulunci, ka kara ɗaukaka musulunci da musulmai bakiɗaya, ya Allah ka jikanmu, ka tausaya mana, kai mana rahmarka, dama kai arrahman ne kuma arrahim, ka gafarta mana, dama kai algaffar ne, mai gafartawa bayinsa a duk lokacin da suka ƙasƙantar da kai suka nemi afuwa, ya Allah ka kawo mana zaman lafiya a duk in da muke. Ku ce amin a cikin zuciya!. Bari mu leƙa wani wajen, wata kila kafin mu dawo baban Zainab ya dawo mu ga result ɗin maganin bokan ya ake ciki?!. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🏞️FOREST🏞️🌼 After some days. A cikin ƴan kwanakin nan da suka suɗe, Kamran sun yi muguwar sabo da su Pretty, kullum yana zuwa kamar yadda ya saba, har yau kuma ya kasa iya tambayar mammarsa menene aure, tun da ya tambayeta menene Alhdulillah ta ɓata rai sosai kamar zata maresa, ta kuma tsare shi a kan dole sai ya gaya mata a ina ya jiyo wannan kalmar ta Alhdulillah? Da kyar ya iya shawo kanta ya gaya mata cewa wasu maharba ne suna wucewa ya ji suna faɗin Alhdulillah, shi ne yake son sanin ma'anarta, warning ta yi mashi sosai a kan babu ruwansa da jin abubuwan da mutane masu wucewa zasu faɗa, a wannan rana dai sam bai je wajen su Pretty ba, saboda mamma ta yi mugun ɗaukar zafi na jin kalmar Alhdulillah ta fito daga bakinsa, hakan yasa ni PRINCESS TEEMA na kara sakawa mamma ayar tambaya a kai, duk yadda aka yi tana da sani a kan addinai ba iya musulunci kawai ba, tana da sani sosai a kan har sauran addinan, dole akwai wani abin da yasa ta ce ita bata yarda da addini bama kwata kwata, ita bata da addini, yadda ta ɗauki zafi daga jin kalmar Alhdulillah ya nuna tasan ma'anar kalmar. Shi kuwa Kamran a bakin su Pretty yake yawan jin wannan kalma ta Alhdulillah, sai ya yi gangancin tambayar mamarsa bai tambayi su Pretty ɗin ba, tun da yaga ta ɗauki zafi sosai haka sai ya ji tsoron yi mata tambaya a kan menene aure, dan gudun kada ya zamana shi ma auren wata magana ce babba da zai ja mashi a rabashi da su Pretty, duk abin da zai sanya a rabasu baya kaunar ko jin makamancinsa, dan sun zama wani ɓari na rayuwarsa, wani abu guda ɗaya da ya lura da shi shi ne, duk wani abin da zai fito daga wajensu Pretty yana cin karo da ra'ayin mammarsa, ma'ana zaka tarar da Mammarsa ta tsani jin makamancin wannan abin, abin har ya fara bashi mamaki yana kuma ɗaure mashi kai sosai, hakan yasa ya fara zargin lallai Mammarsa tana da sani a kan irin wannan addini nasu su Pretty, sai dai ya barwa zuciyarsa wannan tunani, saboda baya son ya ɓallo ruwan da zai rabashi da sanyin idaniyarsa wato su Pretty, ga shi mum ɗinsu ta bashi amanarsu, ai kunga nauyi ya karun masa a ka, dole ya zage dantse wajen kula da su. A ƴan kwanakin nan da suka shuɗe sun yi muguwar sabo da shi na ƙin karawa, har ta kai ta kawo yanzu sai ya zo suke cin abinci a tare, suna fita waje filin ƙoramar nan su yi ta wasa, a yanzu yana koyawa Pretty harbi da kifiya, sakamakon ya rage jin feeling da yake yi, hakan kuma ya samo asaline saboda maganin da mammarsa take basa ba tare da saninsa ba, so yanzu idan ya taɓa Pretty baya jin abin sosai. Yanzu ya koya mata busar wannan sarewar tasa da yake kyarawa da abin ayaba, ya koyawa Sweetie ma, idan suka zauna a wajen ƙoramar nan yana koyawa Pretty harbi da kifiya ita kuma Sweetie tana yi masu busa mai daɗi, abin gwanin birgewa, wani lokaci ya goyi Pretty su hau saman bishiya su ciro mangoro, Sweetie tana ƙasa tana yi masu busa, sai dai su ciro su zo su wanke mata su bata ta sha. Sai dai fa har yau har gobe Pretty dai taki yarda da Rocky, taki yarda su zama abokai, ta ce babu wannan magana, kowa ya tsaya a matsayinsa, Kamran dai bashi da zaɓin da ya wuce ya yi masu iyaka idan yana son zaman lafiya, baya yarda ya bar Rocky ya taɓata, dan yana taɓata zata haukace masu ne a wajen. Taƙa tsantsan sosai Kamran yake yi wajen zuwa wajen nasu, dan kada Mamma ta gane shi. A yanzu warriors ɗin nan sun ɗan rage shigowa cikin wannan dajin, yau tsawon kwanaki biyar kenan Kamran bai haɗu da ko mai kama da su ba. Gawarwakin warriors ɗin da wannan jarumin sadaukin mutumin ya kashe su ma duk Kamran ɗin ya jefasu cikin ruwan dake gudu har izuwa wajen babban teku ruwan ya tafi da su. 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ Gari ya yi sanyi, rana ta yi yamma ta kusa faɗuwa, inuwa ta sauko a dajin, ƴelwar ni'imar iska tana kaɗawa a ko'ina, iska ce mai matuƙar daɗi da ratsa jiki, dogayen bishiyoyin sai kaɗawa suke yi, ba iska bace ta ruwan sama, ba kuma iska bace ta hunturu, iskace ta bishiyoyi suke kaɗawa, yanayin gari ya yi matuƙar daɗi musamman ace ga masoya, dajin ta yi shiru sai sautin kukan tsuntsaye ne yake tashi da kuma sautin zubar ruwan koramu, gari babu hadari. Rocky yana kwance a kasar wata jibgegiyar bishiyar ɗorawa da take a kusa da ƙoramar wajen su Pretty, da alama ma barci yake yi. Sweetie tana zaune a kusa da shi, kasancewar bata gani baiwar Allah bata san a kusa da ita Rocky yake kwance ba, kayan marmari ne a gabanta take sha cikin nutsuwa. Su kuma sarakan suna saman dutse, Kamran yana zaune ya miƙe kafafu ruwan koramar tana sauƙa a saman kafafun nasa, ita kuma Pretty tana zaune a ta gabansa, sai dai ta bashi baya ta ɗan kwanto a jikinsa, ita ma ta miƙe waƴan nan ƴan guntayen kafafun nata, ko wajen ƙoramar kafafun basu iya kaiwa ba saɓanin nasa da yake cikin ruwa tsulumdum, sai takura mashi take yi a kan su matso baki bakin dutsen dan ita ma kafarta ya shiga cikin ruwan. Shi kuwa ya ce ai ita gajera ce ko sun matso kafafun nata ba zasu iya taɓa ruwan ba, ta bari sai ta zama babba kamar shi. Mai hali dai baya fasawa shi ne ta sa mashi kuka tare da miƙewa tsaye wai zata faɗa cikin ruwan mai gabaɗaya. Jawota ya yi ta zauna, dukkansu biyu hannunsu na rike da abin busar suna busawa ne dama, sun yi harbi da kifiya har sun gaji ne suka koma yin busa. "Kai our Pretty kin iya rigima fa". Ya faɗa yana jan hancinta. "Ba wani rigima, ni ka matso nima kafata ta rinƙa taɓa ruwa". "Sai ki yi mun busar da ta fi ta jiya daɗi zan matso". Ya yi maganar yana tattare mata gashin kanta da iska ke kaɗata tana rufe mashi fuska. "Idan na yi maka zaka goyani mu hau kan Giwa?". Ƙulle mata gashin nata ya yi yana faɗin. "E amma ai ba yau bako? Dan yau ba zamu je wajen giwayen can ba, kinga lokacin komawata gida ta kusa". Turo baki ta yi kafin ta ce. "To ba kai ne ka je ka jima wajen cirowa Sweetie fruit ba? Ni Allah ba zan yarda ba sai mun sake zuwa wajen, akwai daɗi hawa bayan giwa......" Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Akwai daɗi kuma kike yi mana ihu? Jiya duk kin yagushe mun wuya da waɗan nan faratunan hannun naki, duk saboda tsoron giwa, kin wani ƙanƙameni kamar idan zasu cinyeki ba zasu haɗa da ni ɗin dukka su cinye ba, kin sa na koma mamma tana tambayata me ya jimun ciwo, sai da na ce mata mage ne ta yakusheni". Ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar kamar mai raɗa. Sweetie dake shan fruits ɗinta ne ta amsa zancen da cewa. "Ai ba zaka kara kaita ba Kamran, jiya da daddare muna barci sai ta yi ta kurma ihu cikin tsakiyar dare wai ga giwa ya buɗe baki zai cinyeta na ceceta, sai da na rinƙa tofa mata addu'oi sosai kafin na samu ta yi barci". A hanzarce Prettyn ta ce. "To waye ya ce ki gaya mashi? Ya tambayeki ne? Ni ba wani ihun da na yi, sharri ne kawai dan baki son a kaini, kuma sai ya kaini ɗin". Shi dai dariya suke bashi idan suka fara wannan diramar tasu, ita Pretty bata son ace ta gaza a kan wani abin, ta fi son ace ta iya komai, ita kuma Sweetie sai iya faɗar gaskiya bata rufawa Prettyn asiri......... 😅 "Nikam Kamran ka kammala karanta littafin da mum ta baka ɗin ne?". Sweetie ta tambaya, dan a cewarta ba zata biyewa Pretty ba, haka dama take yi kullum, bata biyewa Prettyn. "No na dai fara karantawa, amma ban samun ishasshen lokaci sosai ba, ni kai'na ina son na kammala karantawa, a ƙage nake da na karanta, dan naga duk wani abin da ta bar mun a cikin saƙo kama daga waɗan nan ring ɗin da komai da komai akwai labarinsu a cikin littafin, shiyasa nake son karantawa na ji me zan yi mata da su, amma da na fara marantawa ne sai Mammata ta zo, bana son kuma taga littafin da kuma kayan, shiyasa sai na ɓoye, bana samun lokaci a gida na karanta, a waje kuma ina tare da ku, da daddare kuma ban isa in kunna wuta a ɗaki na ce zan yi karatu ba, mamma zata ce me nake yi ban yi barci ba, amma soon zan karanta". Yana magana yana ta murɗawa Pretty kyakkyawar dark black curly hairnta. Ita kuma ta wani kwanta mashi a jiki sarkin son jiki. Sweetie tana ƙoƙarin yin magana Prettyn ta rigata da cewa. "Ni Kamran ka matso bakin dutsen nan please, ina son kafata ta taɓa ruwa, kuma gobe zaka kaini wajen Giwa, Allah Sweetie babu ruwanki, tun da ke kin ce ba zaki je ba ai sai ki barni ya yi ta kaini yawo nikam". Dogon hancinta ya ɗan ja tare da faɗin. "Ki yi ta wahalar da ni ina goyaki ko? Saboda tsoro sai ki ce ba zaki tafi da kafafunki ba, kisa na goyaki duk na gaji". Sweetie ce ta ce. "Katuwa da ita zata yi ta karya maka baya ko ta saka ka ciwon kwankwaso ba?". "Allah Sweetie bana so, babu ruwanki da ni, ni ƴar karama da ni ɗin ne zaki ce zan karya mashi baya? To ni yaushe ma nake da ƙiba? Baki fini girma bane? Kin fini ai, kuma a haka shekaran jiya ya goyaki muka tsallake duwatsun can, ke baki ɓalla mashi baya ba sai ni? Kamran kada ka kulata sharri take yi mun ko? Ina bani da nauyi?". Yadda ta yi maganar gwanin ban dariya, irin ita ma wai zata yi mashi wayon nan ta saka mashi magana a baki. Shiru ya yi bai amsa masu ba, dan yanzu idan ya amsa da cewa tana da nauyi Sweetie zata ji daɗi, ita kuma Pretty ba sai na faɗa ba kunsan kuka zata yi mashi ance tana da nauyi, idan kuma ya amsa bata da nauyi, to Prettyn zata yi dariya har ma ta yi wa Sweetie gwalo, ita kuma Sweetie bara ta ji daɗi ba ga watsa mata ƙasa a ido, dan haka sai ya yi shiru ya kyalesu, haka suke yi mashi wani lokaci, sai su saka shi a tsakiya ya rasa bayan waye zai bi bawan Allah. Idan ya bi bayan wannan, sai wannan ta yi fushi, idan ya bi na wannan, wannan ta yi kuka, shirun dai shi ne mafita a gare shi!. Rayuwarsu gwanin birgewa sosai da sosai, sai sun baka sha'awa idan ka gansu, sun ɗauki Kamran tamkar ɗan uwansu na jini, shi ma duk da yana jin son Pretty a ransa sosai da sosai baya taɓa yarda ya nuna masu banbanci, ya fi nunawa Sweetie ma kulawa, saboda akwai ranar da ta ce mashi Kamran saboda bani da ido bana gani ne yasa baka hira da ni sai Pretty kawai ko? Wannan maganar tata ta taɓa mashi zuciya sosai da sosai, hakan yasa ya ɗaura ɗamarar koyan zama dasu su dukka ba tare da nuna masu wani babanci ba, sai ma ya fi bawa Sweetie kulawa dan kada ta ji babu daɗi ta ji kamar cewa ita ba mutun bace dan bata da ido, yana janta a jiki sosai yanzu. Ita kuwa Pretty ta daban ce a cikin zuciyarsa, yana bala'in kaunarta, kome ta yi kyau take yi mashi, amma kuma abin da bai sani ba shi ne Sweetie ce take son shi ba Pretty ba, ita Pretty da kauɗi ya yi mata yawa a kai ina ma take wani bi ta kansa sosai, ta dai shaƙu da shi fiye da Sweetien, tana kuma kaunarsa a matsayin ɗan uwa da suka ɗaukesa, bayan haka babu wani abin, amma watakila a gaba zata iya fahimtar tana son shi. Akwai cakwakiya sosai kam, domin ita Sweetie da iya gaskiyarta take son shi, bata san ya kamaninsa yake ba, amma zuciyarta ta kamu da kaunarsa, wannan ita ce ma kauna ta gaskiya duk da ita ma bata san me kaunar ba a yanzu, saboda ƙananun shekarunsu. Hmmm akwai case ba kaɗan ba, mum ɗinsu ma auren Pretty ta bashi bana Sweetie ba, Allah sarki baiwar Allah ga cutar makanta gana soyayya, to Allah ya baki ikon cin jarabawarki. Bari mu leƙa DUBAI mu dawo. 🌼DUBAI🌼 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/8/2024.....✍️📚🌹 For information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________32🔥 🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️ 🌼DUBAI🌼 After some days.🕊️ LEESHARH🌼 Kwance take a saman bed ɗin nata, idan ka kalleta zaka yi zaton ba ita bace, ta goge ta yi wani kyau da ita, dattin gidan AAJ duk ya fita, ta ɗan yi dumurmur da ita, alamar ta samu huta da kula, ba karya suna kula da ita sosai, dan a halin yanzu ita ce kawai hope ɗinsu, ita ce zata biya masu buƙatarsu da suke ƴinwace wajen nema, kula da ita sosai suke yi tamkar kwai a saman bajajjen plate. Mayuka da sabulan gyaran jiki kala kala masu kyau da tsada suka saya mata take amfani da su, wannan mata dai ta zage sai koya mata aikin take yi kamar yadda suka gaya mata. Sai dai kuma har yau bata iya samun damar ganin ko face ɗin mutun ɗaya daga cikin gidan ba, ta yi iya ka baƙin ƙoƙarinta wajen ta samu ta ga face ɗinsu, amma abin ya ci tura. Daga harshe dai sai ta hakura ta fawwalawa Allah komai... Hmmm ga shi ita da kanta bata san a wani location wannan gida yake ba, an dai keto da ita cikin unguwa, ga gidajen da yake a unguwar duk ginin iri guda ne, in fact bama ta san wace unguwar bace ba, bata san komai dan gane da su ba. Duk nacinta da yadda ta so ta iya sanin wani abin a dangane da su to fa hakura ta yi, domin ance duk wanda ya rigaka kwana to zai rigaka tashi, wannan haka yake, sun ko fita wayo, idan juranta sammako to su a tafe suka kwana, sun ki yarda su bata wani dama, a shirye suka tsab kafin su fara duk abin da za su yi. Ta kwanta shiru tana tunanin duniya, mahaifinta ne kawai a cikin ranta, ta ƙurawa sama idanu kamar wata mai kallon wani abin, dama kun san akwai ta da ido kam, tafi kowa manyan idanu a gidan AAJ. Wani irin jiniya ne ya karaɗe gabaɗaya unguwar ta su, jiga jigan motoci ne suka saki jiniya tun daga nesa da wannan gida, ya karaɗe ko'ina, tun da Leesharh ta zo wannan gida bata taɓa jin jiniya makamancin hakan ba, wani lokaci jefi jefi tana jin karar jiniyar motar ƴan'sanda ya wuce, da yake unguwa ce ta manya, akwai irinsu ƴan majalisu, ciyamomi da sauransu, hakan yasa wani lokaci motocin ƴan'sanda da sojoji suke giftawa tare da motar wani ɗan majalisa, to amma na yau jiniyar ta daban ce, domin ta karaɗe ko'ina a faɗin unguwar, daga ji kasan wasu manyan shegu ne suka dimfari arear. Kamar wadda aka tsira ta miƙe zaune a tsakiyar bed ɗin, tunani ta fara yi akan wannan jiniya kuma na menene? Waye ne kuma ya zo?. Bata ankara ba sai jin jiniyar ta yi har tsakar kanta kamar zasu tashi gidan nasu, alama

Chapter 44 of 75