da kansa, ai shikenan kuma ta samu gado da katifa har ma da pillow.
Ganin yadda take kallon cikin kwayar idanunsa sosai ne yasa ya hura mata iskar bakinsa a ido, a tunaninsa hakan zai sanya ta rufe idanun nata. Ga mamakin sa kuma sai yaga ko kyafta idanun ma bata yi ba bare asa ran zata rufe su, yadda kuka san ta sume ido a buɗe, kawai kallonsa take yi...... Dole ya ce idanuta suna rikita shi, wanna yarinyar akwai abubuwan mamaki sosai a tattare da ita, koya aka hurawa mutun iska a cikin idanu sai ya ɗan ji wani iri, wani ma harda kwallah yake yi saboda iskar, wani kuma a take zai datse idanun, amma ita kunga ko kyaftawa ma bata yi ba bare asa ran zata rufesu.
Ba ƙaramin mamaki ta bawa Kamran ɗin ba, sake hura mata iskar ya yi a karo na biyu yana mai cigaba da kallon idanun nata. Ko gezau bata kyafta ba. Tsoro ne ya ɗan kamashi kada ace sume mashi a jiki ta yi, da sauri ya ɗan girgizara tare da ambatar sunanta.
Nisawa ta yi tare da amsawa tana sakin wani irin cool murmushi. Nannauyar ajiyar zuciya shi kuma ya sauke tare da cewa. "Kekam ba mai iya maki, yanzu me kika tsareni da ido haka?".
Hannunta ɗaya ta kai ta dafa shoulder ɗinsa ta gaba tare da gyara kwanciyarta a jikin nasa ta ce. "Yanzu me na yi?".
Yadda ta gyara kwanciyar tata sai gurun wuyarta ya fito sosai. Yatsunsa biyu na hannun da yake rike da Alqur'ani mai girma ya kai saman wuyar tata yana faɗin. "Pretty wannan tsokar da take a wuyar nan taki tana yi mun kyau over, tana kara maku kyau sosai har Sweetie, amma kuma kamar mum ɗinku bata da shi ita".
Girgiza kai Pretty ta yi, cikin sauri ta ce. "Kasan mum ɗin mu ne?".
Sai a lokacin ya san ya yi suɓutar baki, ƴan kame kame ya fara yi yana son waske mata kada ta gane shi ne wanda mum ɗin nasu ta ce su nemo.
Tsare shi da ido ta yi, sai gabaɗaya ya tsargu ya rasa me zai ce. Ƴan hannunta ta kai saman karan dogon hancinsa ta ja da ɗan karfi har sai da ya ce wash. "Amsa me, kasan mum ce?".
Girgiza mata kai ya yi alamar a'a bai san ta ba, kawai tunani yake yi kamar ita bata da gurun wuyar. Da yake dukkansu yara ne sai ya yi wasa da ƙwaƙwalwarsu ya waskar da zancen, sai dai fa ita Sweetie ta fahimci akwai abin da baya son su sani, tabbas ko dai shi ne wanda mum ta ce su nemo, ko kuma dole da biyu yake zuwa wajen nasu, ko dai yama san in da mum ɗinsu take kawai baya son gaya masu ne, shi ne tunanin da Sweetie take yi.
"Kamran bari na ɗauko maka wani rubutu da Mum ɗinmu ta yi, ta ce mu bawa wannan mutumi idan muka gansa, sai kuma wani littafi karami da ta ce shi ma mu bashi, yanzu bari na ɗauko maka takardan tun da ka iya karatu sai ka karanta mana mu ji me mum ta rubuta". Cewar Pretty sarkin kauɗi, ta yi maganar tare da yunƙurawa ta bar jikinsa.
Da kallo kawai ya bita, har cikin ransa yake jin duk wani magana da zata yi, zazzaƙar voice ɗinta yana ratsa shi sosai da sosai.
Wannan envelope ɗin da ya ɗauka ranar shi ta ɗauko mashi, a saman gado ta zauna tana faɗin. "Sweetie in nunawa Kamran ya karanta mana mu ji me mum ta ce?".
Sam Sweetie bata so hakan ba, bata so ace Pretty ta ɗauko wannan ajiya ba, saboda mum dai ta ce sai wannan mutumi kawai zasu bamawa, amma ta je ta ɗauko shi, ga shi ba halin ta ce mata ta mayar da shi kada ta nuna mashi, zai ji babu daɗi tun da yana wajen, da baya nan ne, amma a gabansa ba zata iya cewa kada a nuna mashi ba, dan haka bata da wani zaɓin da ya wuce ta ce. "Ki nuna mashi iya takardan kawai, sauran abubuwan kuma duk ki barsu a cikin envelope ɗin".
To ta amsa mata da shi, cikin hanzarce ta fara fito da abubuwan da suke a ciki, ba iya takardan da aka yi rubutu bane kawai a ciki, har da wasu ring guda biyu iri ɗaya sak, da wasu chain suma gida biyu irin ɗaga, irin siraran chain ɗin nan ne, kansu akwai tambarin ɓauna kamar tambarin gidan sarauta, haka shi ma ring ɗin da yake a cikin, shi ma yana ɗauke da wannan tambari, akwai dai karikitai a ciki, sai wani littafi mai kama da diary, da alama tarihin rayuwarta ta rubuta a ciki ko makamancin haka.
Wata farar takarda dake nannaɗe ta fito da shi, sannan ta kwashi duk sauran abubuwan ta mayar ciki tare da rufe envelope ɗin ta ajiye a gefe guda.
Warware takardan ta yi tare da cewa Kamran zo ka gani. Ba musu ya taso hannunsa rike da Alqur'ani ya dawo kusa da su ya zauna. Ita dai Sweetie shiru abinta baiwar Allah.
Shinfiɗe takardan a gabansu ta yi tare da cewa ya karanta masu su ji.
Fara karanta rubutun da aka rubuta cikin harshen turanci ya yi, amma kafin ya fara karantawa sai da ya tsaya ya tsare rubutun da idanu sosai, yadda kuka san ba hanu bane ya rubuta shi, kamar computer ce ta rubuta, rubutun ya tsaru sosai da sosai, komai daki daki.
"Gaisuwa da fatan alkhari a gare ka Kamran, nasan da izinin Allah saƙona zai iso gareka, ban yarda da kowa ba a rayuwata sai kai, ga amanar ƴaƴana na baka, na san zaka kula mun da su sosai, a yanzu basu da kowa a duniyar nan sai Allah sai kuma kai, zan so kasan tarihin rayuwarsu ko in ce rayuwata, akwai wata littafi da na ajiye maka a tare da wannan saƙo da kuma wasu abubuwa, a nan zaka sami dukkan wata amsa a kan rayuwata, daga karshe ina mai yi maku fatan alheri tare da yi maka albishir da idan Pretty ta girma na baka aurenta duniya da lahira, ita kuma Sweetie ka rike mun ita tamkar kanwarka na jini, na gode sosai godiya mara iyaka". Shi ne abin da yake rubuce a jikin wannan takarda.
Slowly ya ɗago da idanunsa bayan ya kammala karanta saƙon, saman face ɗin Pretty ya sauke fararen idanun nasa, while ita ma shi take kallo har cikin idanu. Cikin nutsuwa da sanyin muryar ya ce mata. "Pretty menene kuma aure? Na ji mum ɗinku ta ce ta bani aurenki".
Ya kai karshen maganar yana cigaba da kallonta.
"Kamran ɗan sake karanta mun layin farko na sakon bari na kara ji". Cewar Pretty, ta yi maganar kamar wata mai cike da ɓacin rai.
Bai kawo komai a ransa ba, sam bai fahimci ya yi suɓul da baka ba, kawai ya sake fara karanta mata. "Gaisuwa da fatan alkhari a gareka Kamran........"
Dakatar da shi ta yi a wajen tare da sake tambayarsa wani suna ya karanta a wajen?. Sai a lokacin ya fahimci ya saki layi wajen karanta sunansa da yake rubuce a wajen, abin gwanin ban dariya, shi gabaɗaya ma ya mance da cewa ya ɓoye masu shi ne wanda suke nema, to yau dai fa Pretty ta kamo shi tsamo tsamo, ba sauran waskiya kuma.
Ƙasa ya sunkuyar da kansa tare da ɗan fara shafa hular da yake a kansa, ƙasa ƙasa ya ce. "Kila wani Kamran ɗin ne mai irin sunana, amma bani bane".
A ƙule Pretty ta yi kansa tare da kai hannunta dukka biyu ta riƙo kunnuwarsa, da karfi ta fara ja tana faɗin. "Ashe ma wani Kamran ɗin ne ko? Har yanzu baka tuba ba kenan? Ba zaka dai'na yi mana wasa da hankali ba?".
Da yake da karfin take jan mashi kunnuwan nasa hakan yasa ya ji zafi ya ziyarcesa, da sauri ya janyota ta faɗa jikinsa tare da cire ƴan hannayen nata daga kunnuwar nasa yana faɗin. "Haba mana, ki bari kada ki cire mun kunnuwa, da zafi fa".
Kuka ta saka mashi har da hawaye, ita a dole ta ji haushi ya yi masu karya. Ita kuwa Sweetie cikin nutsuwa ta ce. "Kamran da gaske kai ne ko ba kai bane? Please kada ka yi wasa da zuciyoyinmu ka ji? Kai mutumin kirki ne sosai, na tabbata ba zaka so ka ganmu cikin ƙunci ba, so please ka gaya mana gaskiya".
Yana ƙoƙarin ƙanƙame Pretty dake son tashi daga jikinsa ta nufi waje, sai kuka take yi hawaye wani na bin wani ya amsa mata da cewa. "Da gaske ne Sweetie, ni ne, na ɓoye maku hakan ne ba dan komai ba sai dan naga zaku iya ganeni da kanku ne ko ba zaku gane ba, amma kuyi hakuri kin ji?". Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da Pretty ta kwace kanta tare da barin jikin nasa, ta diro kasa daga saman bed ɗin ta nufi waje tana kuka sosai.
"Pretty sarkin rigima, to me abin kuka kuma? Ai daɗi ma yakamata ta ji tun da mun ganoka yau, shiyasa mana kake kula damu sosai, dama mum ta gaya mana zaka kula damu sosai" Cewar Sweetie.
"Haka ne Sweetie, amma ku yi hakuri da ce maku bani bane da na yi". Yana magana hankalinsa na a kan Pretty da ta bar cikin ramin, burinsa kawai ya bi bayanta ya je ya rarrasheta.
"Ba komai Kamran, ai kai yakamata ma mu bawa hakuri". Cewar Sweetie baiwar Allah.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe tsaye tare da ɗaukar kayan da ya kawo masu wadda Pretty ta zubar da su a kasa ta nufi waje, ya ɗaura kayan a saman gadon tare da ajiye Alqur'ani hannunsa a kan gadon yana faɗin. "Bari na bi bayan Pretty ina zuwa yanzu". Yana kai karshen maganar bai tsaya jiran me zata ce ba ya nufi wajen shi ma.
Yana fitowa ya fara waige waige ta ina zai hangota, a hankali ya fara takawa yana naman ta ina take wannan yarinyar.
Can saman dutse wajen ƙorama ha hangota, ta takure jikinta waje guda, da alama a tsorace take da zamanta a wajen, kawai dai karfin hali ne yasa ta zauna, irin ita ta yi zuciyar nan, ta yi fushi. Dariya ma ta bashi, gata da tsoro kuma ga ban tsoro.
A hankali ya lallaɓa ya nufi wajen nata, har lokacin kuma gawarwakin warriors ɗin yana wajen, sai dai ba ta gefen da Prettyn ta zauna ba, ta can gefe ita Pretty ta je ta zauna, da yake wajen yana da matuƙar girma sosai.
Ta yi shiru ta zubawa ruwa idanu tana kallon yadda yake zuba gwanin ban sha'awa, ga hawaye a saman fuskarta. Ruwan wannan ƙoramar yana da matuƙar haske sosai, tankar yake.
Sam bata ji motsin mutun ba sai ji ta yi an rufe mata idanu ta baya. A tunaninta warriors ɗin ne suka dawo, dama a tsorace take da zama a wajen, kawai dan tasan Kamran yana nan, kuma zai biyo bayanta ne ma yasa ta daure ta cije ta zauna a wajen, ba dan haka ba ina ba ita ba fitowa yau.
Wani irin ihu ta kurma har sai da arear wajen ya amsa, a dubu ɗari ta fara ƙoƙarin tashi ta gudu, dan kwata kwata bata kawowa ranta cewa Kamran ne ya rufe mata idanu ba.
Ganin a garin gudunta tana ƙoƙarin faɗawa cikin ruwan yasa Kamran ɗin ya yi saurin zame hannun nasa daga idanun nata ya yi maza ya riƙo kugunta ta baya. Jikinsa ya janyota dan kada ta faɗa ruwan. Sai ƙoƙarin kwace kanta take yi, dan bata san waye bane, ga shi yana ta bayanta babu halin taga fuskarsa.
"Sarkin tsoro ai sai ki nutsu ni ne to". Ya faɗa yana ɗagata sama zai sauko da ita kasa daga saman dutsen, dan ma kada ta yi ta afka cikin ruwan nan ta sanya shi faɗawa ba shiri, bai shirya shiga ruwa da safiyar nan ba.
Yana sauƙo da ita kasa ta juyo tare da fara kai mashi duka a kirji na tsoratata da ya yi, ya wani zo ba excuse ya tsoratata a banza, ya sa ta kusa sumewa. Ƴan hannayen nata da take dukan nasa ya riƙo tare da cewa. "Sorry our rigimammiya, wai ma da kika fito wajen nan idan warriors ɗin nan wasu sun zo fa? Idan suka kamana mana ke ya kike son mu yi ni da Sweetie? Kin san fa za mu iya mutuwa idan suka kamaki suka cutar dake".
"Ni kada ka yi mun magana mun ɓata". Ta faɗa a shagwaɓe tana ƙoƙarin raɓawa gefensa ta wuce.
A hanzarce ya riƙo hannunta yana faɗin. "To ai ni bance mun ɓata ba, ki bari sai nima na faɗa sai ki tafi". "Ni bawani jiranka da zan yi kawai mun ɓata".
"To shikenan am so sorry, zo ki gaya mun menene aure? Dan na ji mum ta ce ta bani ke na aure! Sannan ki gaya mun menene mum take nufi da ta ce da izinin Allah, menene Allah?" Ya yi maganar cike da ƙaguwar son jin amsa, dan duk abin da zai fito daga bakin mum twins yana ɗaukar hakan da mahimmanci kamar maganar Mammarsa yake ji.
"Nima ban san menene aure ba, amma dai nasan Allah, Allah shi ne wanda ya haliccemu dukkanmu, shi ne wanda ya halicci wannan daji da komai da komai, shi ne abin bauta da gaskiya shi kaɗai, bashi da abokin tarayya, ba'a haɗa shi da wani, shi ne mai riƙe da rayukanmu da komai dai da kasani".
Hannunta ya riƙo suka zauna a saman dutse domin ta cigaba da yi mashi bayanin wanenen Allah, shi kuma batun aure ya barwa ransa cewa zai tambayi Mammarsa idan ya koma gida, ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce lallai akwai case idan ya tambayi Mamma, jiya ya gaya mata yana jin feeling a jikinsa, yau kuma ya tambayeta menene aure? Me kuke tunanin zai faru? Me kuke tunanin zata ɗauke shi ko zata yi tunani a kansa? Ai dole ta zargesa sosai ma. To bari dai mu leƙa KINGDOM OF POWER, daga baya zamu dawo mu saurari hirarsa da Pretty mu ji ya zasu kaya.
KINGDOM OF POWER 💪🔥💘
Kwance twin's Obaid and Omaid suke a saman katafaren bed ɗin Obaid, dama kullun a gado ɗaya suke kwana, basu rabuwa duk da kowa da gadonsa.
Omaid dai yana aikin latsa waya, chatting suke yi da sistersa Jannat ƴar uncle Rahab dake a Dubai, dama itace kawarsa, suna mugun shiri sosai, idan suka koma Dubai kullum tana tare da su a gidan King Badeen, wato kakansu, sun fi yawan zama a gidan, basu cika zuwa gidansu Abu Abdussalam bin Badeen ba, a cewarsu su Yah Ramish suna takura masu, ko gidan uncle Rahab ɗin ma basu zuwa, sun fi son zama da mai ran karfe, wato kakarsu mace kenan, ita kuwa ba kamar Akka take ba, sam bata da tsauri, goya masu baya take yi suna tsula tsiyarsu, ita ce nan ta koya masu kada su yafe laifi idan aka yi masu, ita ma tsohuwar ƴar yi ce.
Obaid ya buga uban tagumi kamar mai tunanin wani abin, ya yi kwanciyar ruf da ciki, ga wani haɗaɗɗen pillow da ya sanya a dai'dai chest ɗinsa ya kwanta a kai. Kullun dai cikin tashin daddaɗar kamshi suke, haka zalika bedroom ɗin nasu ma, kullum cikin ƙamshi yake zubawa, kuyangunsu sun iya gyara sosai.
Ganin alamar Obaid fa ya luluƙa duniyar tunani ne yasa Omaid ya yi wa Jannat voice na karshe a in da yake ce mata cikin harshen larabci yana zuwa two mins. Yana tura mata ya ajiye wayar tare da fara bin Obaid da kallo, dukkansu daga short sai single ne a jikinsu.
"What are you thinking blood?". Omaid ya faɗa yana zare pillow da yake a tsakanin chest na Obaid ɗin da kuma bed.
Mirginawa Obaid ya yi ya sake mirginowa kafin ya ce. "Am thinking about Mama, kasan me zan yi mata kuwa?".
Tsare shi da waɗan nan shegun eyes ɗinsa masu shegen rikita mutun idan suna kallonkan nan Omaid ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba. Jira kawai yake yi ya ji me Obaid ɗin ya shirya.
Wan nan munafukin dariyar tasa ya saki, har da kara kwanciya a saman pillow, da alama mugun abu sosai yake shriyawa.
"Please Obaid stop this laughing mana, ka fara ko? Please i ƙage nake da na ji me kake tunani a kanta".
Ya yi maganar yana ɗaure fuska kuma cikin ƙaguwa da son jin me blood ɗin nasa yake shiryawa, nan take kamanninsa da Jaish ta kara bayyana sosai, twin's ɗin nan idan suka ɗaure fuska sai ka kalli kamar Yah Jaish ne a wajen.
"Wait mana pleasure, i will tell you dolena ka sani ai, but please ka barni kaɗan, let me laugh more so that na samu damar iya ɗaure fuska idan abin ya faru, kasan we can't laugh a wajen da abin zai faru, kada a gane mu, dan haka ka barni na yi dariyar tun daga nan".
"You're a bad boy Obaid like Akka". Omaid ya faɗa
(Hasbunallahu lallai yaran nan sun tsani Akka 😅 wato ita mutuniyar banza ce a gabansu 😅 kash wayyo ciki, idan kunji ance dariya ya kasheni to su twin's ne sila.)
Tsabar dariyar mugunta har da hawaye ne yake fita mashi a cikin idanunsa izuwa saman lallausan kumatunsa, ya dafe ciki, kamar wani zararre, da kyar ya iya cewa Omaid ɗin. "I think I'm even better than Akka ma ai".
Dukan wasa Omaid ɗin ya kai mashi a shoulder ɗinsa yana faɗin. "To is okey, now gaya mun me ka shirya?".
Da kyar ya iya dakatar da dariyar tasa tare da haɗe nutsuwarsa waje guda, sannan ya fara magana. "Snake mana zamu sakar mata ko kuma scorpion, kuma sai cikin dare zamu yi hakan, ya cijeta ko sau ɗaya ne".
"Obaid you're not serious fa, so kake ka kasheta ko? Idan snake ko scorpion suka cijeta ai kafin a kaita hospital ma ta mutu, kuma tsabar kai you're a very very bad boy sai cikin dare za mu yi mata hakan ko? Wlh Yah Jaish yana nan, idan ya rikemu ina ga ko daddy ba zai iya kwatarmu a hannunsa ba, kuma kowa ya sani a cikin gidan nan mune kawai muke da su scorpion, muna sakar mata su za'a san aikin mu ne, ina ga kafin wayewan gari ni kam ina hanyar Dubai da kafafuna, ba zan jira jirgi ba, dan da punishment ɗin Yah Jaish gwara na je Dubai da kafa".
Dariya sosai Obaid ya sake kwashewa da shi kafin ya ɗan tsagaita kuma, ko me ya tuna sai kuma ya sake cewa. "Yakamata sai mun shirya zamu bar ƙasar nan mu sakarwa Yah Jaish ma scorpion guda ɗaya".
A wannan karon Omaid bai san time ɗin da ya fashe da dariya ba. Waɗan nan yara wlh anyi ƴan albarka, ba'a faɗin ɗayan, sai dai shirin Allah kawai zamu yi masu fata.
"Amma ni ban taɓa sanin cewa blood kai mugu bane sai yau, wato sai mun shirya barin ƙasar zamu sakarwa Yah Jaish ɗin ma nasa scorpion ko? Ai wlh ina ga ko cikin momma muka koma sai Yah Jaish ya bi mu". Cewar Omaid. Yana magana yana ɗan dariya, da yake shi na gaya maku bai cika yawan dariya sosai ba, Obaid ya fishi yawan dariya.
"Ai Yah Jaish ɗin ne ya cika takurawa mutane, yakamata mu ɗan ɗan ɗana mashi azaba kaɗan, shiyasa fa ni bana son zuwa gidan uncle Abu Abdussalam, saboda muguntar su Yah Ramish". Obaid ya faɗa yana janyo wata pillow ya rungume.
"Kai mu yi magana serious me yakamata mu yi wa mama kafin mu koma? I really hate this woman, da idonta kamar na Akka".
(Wai kowani kayan tsiya yaran nan suka ɗebo sai su ce irin na Akka?🤔😅 Ita dai Akka tana shan zagi a hannunsu ba tare da saninta ba.)
"I think this night mu je mu san ta yadda zamu yi mu saka mata diaza a cikin drink nata or water ta sha". Cewar Obaid.
Wani irin zaro idanu waje Omaid ya yi, dama ga idanun dara dara a waje, yadda ya zarosu a yanzu idan ka gansu sai ka ruga a guje dan tsorata. A hanzarce ya ce. "Real bad boy without a mix, kai Obaid wani irin bakin mugu ne wai? Yanzu Mamar zamu bawa diaza ko? So kake yi ka zubarwa da daddy mutunci kawai. Tab wayaga mama ta sha diaza? Wai da kuwa KINGDOM OF POWER ya ɗauki jan launi". Ya kai karshen maganar tare da kwashewa da wani ɗan iskan dariya.
Cikin dariya yake faɗin. "Har na hango Mama tana bin jikin bangon kingdom ɗinnan dukka tana wankewa, kai amma kuma da ta taimaka fa". Cike da shakiyanci da iyashege ya yi maganar.
A hanzarce Obaid ya karɓi zancen da cewa. "Ba iya jikin bango ba, ai wlh idan ta sha diaza ina ga harta motoci da dawakan gidan nan ba zata bari ba sai ta wanke, har mu ba barinmu zata yi ba sai ta wanke mu, komai na gidan nan babu abin da zata bari, caf zata wanke komai, 24 hours tana aiki". Shi ma cike da shakiyanci ya yi maganar. Sun zauna sai tsiya suke zubawa Mama ƴan albarka.
Kara fashewa da dariya Omaid ya yi tare da ɗaukar pillow yana kaiwa Obaid duka, da kyar yake iya faɗin. "Please blood ka barni haka kada kasa dariya ta kasheni, dan ka tuna mun da uncle Muslim da muka bawa diaza a school, bawan Allah har bangon jikin class namu sai da ya wanke, gobe ya kara yi mana faɗa har ma ya raba mana wajen zama uban diaza a aiki zamu bashi ".
Wani irin bushewa da dariyar iskanci Obaid ya yi, kamar wasu zararru suna ɓaɓɓaka dariya mai sauti ba tare ma da sun san sautin yana fita ba, sun kulla mugunta kala kala yaran nan, uncle Muslim uncle nasu ne a school wanda kullum yake yi masu faɗa a kan su dai'na ana yi masu magana suna yin banza da mutane. A gaskiya su idan kaga suna magana to a gida ne da su Sarina, amma wlh a waje ko uncles ɗinsu a school basa yi masu magana su amsa, kamar wasu masu aljanu haka suke, sai ayi ta magana su yi banza da mutane, idan kaga twin's ɗin nan suna dariya to sai sun haɗu su biyu irin haka, su biyu suke hira, su yi dariya, to shi ne fa uncle ɗin ya yi masu faɗa sosai dan ya ji haushin yana yi masu magana sun ki amsa mashi kuma suna ta hira a tsakaninsu a cikin class ɗin, izzar bala'i ke garesu suma, jinin sarauta na gudu a jikinsu.
Har uncle ɗin ya so ya zanesu ma kuma sai ya hakura ya kyalesu, daga nan sai ya raba masu wajen zama a class ɗin, dan idan suna a tare wlh ko malami yana class suka so yin magana sai sun yi, basu jin magana ne na wuce misali, ga shariya da mannin hauka game da izza. To su wannan raba masu wajen zama da ya yi ne ya baƙanta masu rai, ba zasu iya rabuwa da juna ba ko dede da minti ɗaya, hakan yasa suka shammaci bawan Allah suka sanya mashi diaza a cikin ruwan shansa, yana sha ya haukace a school ɗin, 24 hours yana aiki kamar computer, ko barci bai iya yi ba, bawan Allah ya wahala a lokacin, abin gwanin ban tausayi kuma gwanin ban dariya idan kuka kalli yadda yake tiƙar aikin. Diaza wata shegiyar kwaya ce mai haukatar da mutun, yasa ka yi ta aiki kamar jaki babu gajiya. Ko a ina suke samo abubuwan kulla muguntar tasu? Ƴan yara da su, abin da mamaki, dole akwai mai basu wasu abubuwa, dan dai su idan ba shopping ba basu zuwa ko'ina bayan school, ko gidan uncles nasu kaisu ake yi a kuma dawo dasu, basu driving da kansu ma bare ace sun ɗauki mota sun fita sun je sun sayi wani abin, idan zasu fita sai da driver and bodyguards masu rai da lafiya da zasu yi tsaron lafiyarsu, su kaisu su kuma dawo da su gida lafiya, to a ina suke samo kwayoyi masu haɗari haka? Akwai matsala
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 75