Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yake ciki mu koma da shi masarauta, idan dai muna son rayukanmu da lafiyarmu!!". Kenan hakan yana nufin abin da yake cikin cikin nata suke da buƙata?.........🤔...... Kenan ba niyar kashe abin da yake cikin nata suka yi ba? To in dai haka ne meyasa zata gudun masu? Meyasa ba zata tsaya ta haifa ta basu ba tun da ba kashewa zasu yi ba? Su meyasa suke son karɓar babyn dake a cikin natan? Me zasu yi da shi? Waye ne ma mamallakin cikin nata? Ma'ana uban cikin?. Tab akwai cakwakiya ba kaɗan na. PRINCESS TEEMA ce taku ta amana🤍 Da alama wanda ya yi magana yanzu shi ne babbansu, dan tun da ya fara magana suka wani sunkiyar da kai, suka kara nutsuwa tamkar masu karɓar umarni. Jinjina kai suka yi suna mai nuna alamar sun ji maganarsa sun kuma gamsu. A tare dukkansu suka diro ƙasa daga saman dawakan nasu, ji kake yi dip, dip, dirowar manya. Fara kewaye wajen suka yi, dan su ga ko zasu yi nasarar samun wata makama, dukkansu basu da wani burin da ya wuce ace sun ga wannan matar, kowannansu burinsa ace shi ne ya yi nasarar ganinta ya kuma ciro babyn dake cikin cikin nata ya mayar da shi masarauta, da alama ba karamar kyauta aka sakawa duk wanda ya kawo babyn dake a cikin wannan matar ba, saboda yadda suka zage da iya karfinsu tare da kwarin gwiwa suna aikin nemanta. Amma duk da hakan kuma sun kasa yin gigin yunkurin shiga cikin ruwan, dan sun san zurfin ruwan nan ya wuci tunanin mai tunani. Sun jima suna kewaye a wajen, amma babu komai a cikin ruwan sai manya da kananun jiragen ruwa dake shawagi a can nesa da in da suke, ta tsakiyar ruwan. Daga karshe dai suka hakura ba dan sun so ba, suka haye saman dawakansu, suka kutsa ta cikin wasu dogayen bishiyoyi dake a wajen, suka tafi. *TO FAH, FARKO KENAN DAGA CIKIN LITTAFIN RAWANIN ZALINCIN, KU DAI KASANCE DA ALKALAMIN PRINCESS TEEMA DAN JIN YANDA ZATA KASANCE, KUN DAI JI TA YADDA LABARIN NAMU YA SOMA, NA SAN ZAKU SO JIN AINAHIN KAN LABARI, WACECE WANNAN MATA? MEYASA SUKA KASHETA? SU WAYE SU? MEYASA SUKE SON ABIN DA YAKE A CIKIN CIKINTA? ME ZASU YI DA SHI? ITA MEYASA TA ZAƁI MUTUWA A KAN TA BADA ABIN DA YAKE A CIKIN CIKIN NATA? SHIKENAN YANZU RUWA YA TAFI DA ITA? TA MUTU DA GASKE? GA KIFIYA A CIKINTA SUN HARBETA DA SHI? GA SHI TANA NAKUDA BAIWAR ALLAH. TO DAI MU KASANCE A TARE DAN WARWARE WANNAN SARKAKIYA A TARE, KADA FA KU YI WANI TUNANI TUKUN NAN,🥱 MASU YI MUN PREDICTION ME ZAI FARU A GABA NA LITATTAFINA SAY HII😂 KAMAR YANDA TRIPLETS YA RIKITA MAKU TUNANI, KUKA KASA HASASHEN GABA, TO WANNAN KO FARA HASASHENSA BA ZAKU YI BA, DAN KUWA SALONSA DABAN NE!🔥 AKWAI RIKITA KWAKWALE, MU JE DAI ZUWA, NAYI GABA SAI KUN ZO!!.* *PRINCESS FATEEMAH, PRINCESS TEEMA DUKKA SUNANA NE, DAN NAJI WASU SUNA TAMBAYA💫❤️* To!! To!! To!! Ina masoyana? kai harma da makiyana, ina kuke? Ina masoyan littafin TRIPLETS? Ina masoyan Noorish and Meesha? Ina masoyan babyn baby and his baby? Ina masoyan Heartbeat and Heartbeat? Ina masoyan Sudais and Anaya? Ina masoyan Uncle T and Aafia? Ina masoyan sir Arvin and Maryam?, Ina masoyan Alex and Adiva?, ina masoyan Imran and jelly, Akila and Umaisha, Irfan and Pinky, masoyan Hjy gwaggo mai zamani, duk dai Ku matso da sauri, dan a yau PRINCESS TEEMA ta sake dawo maku da wata zazzafar littafin mai tashin kai, shi wannan ba zazzafa bane ba, tafasa yake yi yana bada tiriri, salonsa daban ne, ina mai tabbatar maku salonsa daban ne, ku my peoples kun sani already ba sai na sake faɗa ba, PRINCESS TEEMA taku mai abin ban mamaki ce, kun san zaku sha mamaki a wannan karon ma, kun san idan nace salonsa daban ne, to fa daban ɗin ne, trust me ya sha banban da sauran labaran da kuka sani, dan fa a shiryena na taho In Sha Allah,🤍 zan tashi kanku in sanya maku hayakin kwakwalwa my peoples, yanzu dai ba QUADRUPLE bane fa😂 kada ku yi mani irin ruɗewar da kuka yi a TRIPLET'S🥺 wannan ina kara gaya maku yasha banban da kowani irin littafi, dan haka kada ki yarda ki bari a baki labari, da a baki ai gara ki bayar, gani ya kori ji, dan haka ki hanzarta maza ki kasance a cikin tafiyata, dan ki gani ba ki ji labari ba👌 ina kara jaddada maku wlh ba zaku taɓa yin danasanin bibiyar wannan littafi mai suna RAWANIN ZALINCI ba In Sha Allah, tabbas zaku yi alfahari da ni fiye da tunaninku, kun sani Alkalamin PRINCESS TEEMA alkalamina mai ilmantarwa, fadakarwa, wa'azantarwa, tare da nishaɗantarwa ne, na san kun san da hakan, dan kune ma kuka shaideni da hakan, bani na faɗa da bakina ba, shaidarku ce wannan, kun shaidani bana rubuta shirme da abubuwan banza a labarina, bana rubuta abin da hankali ba zai ɗauka ba! Bana rubutu kamar tatsuniya! Ina rubutu ne kamar gaske, abin da yake kewaye damu!! Kada dai na cikaku da surutu, mu haɗe daku a cikin littafin RAWANIN ZALINCI page 2 kawai.🔥🌹 Ku daga jin sunan RAWANIN ZALINCI kun san da akwai abubuwa ba kaɗan ba wadda baki ya yi kaɗan ya kwatantasu. *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻 ❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 29/6/2024.....✍️📚🌹 🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E____________2🔥 Baƴan lokaci mai tsawo da tafiyar waƴan nan jiga jigan worries ɗin, har lokacin ruwan sama na cigaba da zuba tamkar da bakin kwarya, ga garin sai kara wani uban duhu na hadari yake yi, tamkar yanzu za'a fara ruwan ma, wani irin walkiya mai matuƙar haske ne yake ta famar walwali a sararin samaniyar, ga wani irin uban rugugin tsawa mai sanya hanjin cikin duk wata halitta razana, sai ka rantse da Allah tsawar nan zata faɗo kasa ne. Da kaɗan da kaɗan haki da nishi yake tasowa daga ɗan nesa da bakin wannan teku, da sauri da sauri nishin yake fita tamkar idan mutun ya rike numfashinsa na ɗan lokacin daga baya ya saki, to a wannan lokaci numfashin zata fita da sauri sauri kuma da karfi karfi, dan hanya da ta samu, haka wannan numfashi da hakin yake tashi!. Kara yawaita wannan numfashin yake yi, daga can nesa da wannan tekun. Wasu ramuka ne masu ɗan zurfi kamar rijiya a ɗan nesa da bakin ruwan, mafiya yawan manyan dajuka irin hakan ana samun irin waɗan nan ramuka sosai, wasu ramukan zaka tarar irin bishiyoyi masu fitowa a kwancen nan suna rufe kofar shigarsu, wasu kuma ganyayyaki da dogayen ciyayine ke cika rakukan, bare yanzu da ya kasance gari na damuna, akwai yelwar ganyayyaki koraye shar a ko'ina a dajin, hakan yasa baka iya ganin wasu ramuka ma sosai. Kwance take a cikin wani katafaren rami mai kama da rijiya, ramin yana da ɗan zurfi kuma yana da faɗi, haka zalika akwai yelwar dogayen ciyayi a cike a ciki wanda suka rufe har baki, muddin mutun yana ciki ba zaka iya ganin shi ba har sai idan shi ya yaye waɗan nan ganyayyaki ya leko kansa waje, sannan ne zaka gan shi. Abin da ya faru shi ne, a lokacin da ta faɗa kasan dutsen ne iska ya kwasheta zuwa cikin ramin, dama kunsan idan kazo faɗawa waje irin wannan akwai igiyar iska mai karfi tamkar ta ruwa da take fisgar mutun, bugu da kari ga iskar ruwan sama mai karfin gaske, Allah ya taimaketa ya kuma ceceta ta yi sa'a a in da ta faɗa cikin ciyayin ba tare da ta ji ciwo ba, ta kuma faɗa ta baya baya ne ba ta gaba ba, Allah ya kare mata cikin nata, ikon Allah kuma bata ji wani jiri ko wani abu makamancin shi ba, sai dai suma da ta yi saboda razana na irin tsayin wajen da ta faɗo ɗin, dama kunsan irin wannan akwai razana zuciya. (Sai dai ni Princess Teema ban yarda da cewa ita ta shiga cikin ramin nan ko iska ya kai ta ba, dan dole akwai ayar tambaya, amma dai bari mu cigaba da bibiyarta mu gani!) Bayan faɗawarta da ɗan tsawon lokaci ne ta farfaɗo daga sumar da ta yi saboda ruwan sama dake zuba yana taɓata, har a lokacin babu alamar hawaye a idanunta ko kaɗan, idanunta suna bushe, da alama ta saba da wahala sosai, zuciyarta ta bushe sosai, dan duk wannan abin da ya faru bata sare ba, bata karaya ba, muradin cigaba da rayuwa ne ziryan a cikin kwayar idanunta, da alama jaruma ce ta gasken gaske! Dan kuwa ko da ta faɗa cikin ramin babu alama na wahala ko nuna gajiya a tattare da ita, tana da taurin zuciya da taurin rai, da alama an gwabza abubuwa da ita ba kaɗan ba, an kara da ita ba kaɗan ba a baya, ga dukkan alamu ba karamar yaki aka buga da ita ba kafin a iya kaita ƙasa ko in ce a iya samun nasarar jefata cikin wannan hali da take a ciki!. Jini ne yake zuba sosai daga cikin nata, sai dai da ikon Allah ta iya cire kifiyar da suka harbeta da shi, kuma ta yi sa'a kifiyar bata soketa sosai ba, da alama wanda ya harbeta da kifiyar duk yadda aka yi akwai wani abin a ƙasa tsakaninta da shi, domin kuwa bai harbeta a in da zata raunata sosai ba, bai harbeta a in da zata mutu ko kifiyar ta yi mata illah ba, kuma da alama kwararren maharbine, yasan kwari da baka sosai, yana da saiti, domin kuwa yadda ya harbeta a gefe guda babu saɓa saiti ko kwana kwana, alamu sun nuna yana sane ya kaucewa harbinta a in da zata iya mutuwa ko ta cutu, wata kila da wata manufa ya aikata hakan, amma lokaci ne zai nuna mana komai. Tattare iya karfinta ta yi tare da miƙewa zaune ta cire alkhabbar jikinta, sai haki take yi sosai, dan a lokaci da ta farfaɗo ta fahimci waɗan nan azzaluman mayakan sun nufo in da take suna nemanta, hakan ne yasa ta rike numfashinta ta hanyar toshe hanci da bakinta da gefen alkyabbar tata, shi ne yasa yanzu take numfashi sama sama, dan sai da ta ji motsin barinsu wajen, sannan ta saki numfashinta, kunga kuwa dole ta yi haki sosai, dan rike numfashi ba wasa ba. Da kyar ta iya zare alkyabbar daga jikinta, a in da ta ɗaure gefen cikin nata da yake zubar da jini da shi, sai buɗe baki take yi alamar kishin ruwa kamar zata mutu. Idan ya jima ya jima sai ta ɗaga kanta sama tare da buɗe baki tana tarar ruwan sama dan ta samu ruwan ya shiga bakinta ta ɗan sha, so abin ku da ruwa idan ba'a indararo yake ba, sam baya zuba sosai duk karfin gudun ruwan sama, amma Alhadulillah ta ɗan sha sosai har ta ji duniya ya ɗan saki mata ta dawo cikin hayyacinta. Ƙoƙarin miƙewa ta yi dan ta fita daga cikin ramin, lokacin ta ji ta ɗan sami sauki bayan wasu mintuna kenan, amma ina ta kasa miƙewa, koda kuwa ta miƙe ba zata iya fita daga cikin ramin ba, saboda yafi tsawonta sosai zurfi, da wannan katon cikin nata kuma ba zata iya buɗe kafafunta ta taka gefe da gefensa dan ta fita ba. Komawa ta yi ta zauna sai a lokacin ta lura da ta kukkuje a hannunta, jajir kuma lallausan fatarta na singalalin hannu zuwa yatsunta duk sai jini yake yi, dama ga fatar luwai luwai da shi, zai yi saurin jin ciwo, ba iya hannu ne kawai ta kukkuje ba, har da kafafunta da sauran sassa na jikinta. Har lokacin bata iya wani numfashin kirki, runtse idanuwanta ta yi a inda ta fara karanto addua'o'i kala kala dan neman taimakon mahaliccinmu, domin kuwa idan ba Allah ba, babu wanda ya isa ya ceceta daga cikin wannan hali da take a ciki. A hankali ruwan sama ya fara cika wannan rami, da yake a gangaren tekun ramin yake, sai ruwan gudu ya fara shigowa. Jin hakan na ruwa na shigowa ne yasa ta yi yunkurin ta sake gwada miƙewa a karo na biyu, amma ina, ko motsin kirki ta kasa yi. Hasbunallahu wani'imal wakil shi ne abin da take ta maimaitawa a cikin zuciyarta. Wani irin azababben murɗa da cikinta ya yi ne yasa bata san lokacin da ta kwallah kara wanda har sai da muryarta ta fita duk dashewa da ta yi ba, da yake ta sha ruwa ne sai muryar tata ta ɗan saki har sauti yana fita. Dafe cikin nata ta yi tana mai cigaba da furta sunan Allah a ranta. Da kaɗan da kaɗan ciwon cikin nata yake karuwa yayinda mararta ya kulle gam yana yi mata wani irin azababben ciwo. Nan take idanuwanta suka kara raina fata a in da a wannan karon suka yi jajir kamar wuta, saboda azaba. Cigaba da murkusoso tayi a wajen tana damke ganyayyakin dake kusa da ita, ta ciza laɓɓa gam da kyawawan fararen hakwaranta tas kamar audiga, tamkar zata fasa laɓɓan nata da hakwaran, idan cikin nata ya murɗa sai ta kara ciza laɓɓanta da karfi, Baiwar Allah, kamar laɓɓan ne suke yi mata laifi. Haka ta yi ta fama na tsawon mintocin da a kallah zai kai arba'in zuwa hamsin, duk ta galabaita ta fita a hayyacinta, duk wasu sauran albarkatun karfi da suka rage mata sun kare, harta ciyayin da take rikewa ma yanzu ta kasa rikewa, saboda babu wani karfi da ya rage a tattare da ita, sunan Allah ma yanzu a iya zuciya kawai take iya furtawa, bakinta banda kerma tamkar wanda ciwon sanyi ya kama babu abin da yake yi, ruwan sama na cigaba da gangarowa izuwa cikin ramin, a yanzu haka yanda take zaune ruwan ya kai mata har zuwa kugunta daga zaunen. Nakuda gadan gadan take yi, da kyar ta samu ta iya cire kayan jikinta, bata rage komai a jikin nata ba, duk ta kwaɓe komai saboda azabar wahala, Baiwar Allah sai take ganin kamar kayan ne suke kara mata zafin da wahala, duk wasu gwala-gwalai tayi wurgi da su gefe guda, ta yi ƙoƙarin ta yaga rigarta ko alkyabbar ta dan ta ɗaure cikin nata in da suka harbeta da kifiyar da kyau, amma ina ta kasa, bata da karfin iya yaga komai, haka ta daure ta hakura tare da dafe wajen kawai. Ganin cewa kamar lokacin mutuwar tane ya yi saboda azaba yasa ta daure cikin wani irin mawuyacin hali ta fara faɗin. "Ya Ubangiji na, kai kaɗai zaka taimaka mun a cikin wannan bakin azabar da nake a ciki, ya Allah dan karfin ikonka ka kawo mun ɗauki cikin gaggawa, ka saukakamun wannan nakuda cikin gaggawa, ya Allah kada ka bari na mutu ba tare da na kalli abin da zan haifa ba, ya Allah ko bayan raina kasa abin da na haifa ya zamana shi ne sanadiyar rugujewar RAWANIN ZALINCI ya tayar da RAWANIN ADALCI da aka kwantar, ya Ubangiji ko na mutu ko ban mutu ba na baka amanar abin da zan haifa, Allah ka kula mun da shi, ka raya mun shi, ya Allah ka bashi basira da kaifin kwakwalwa da tunanin da zai iya tunkarar waɗan nan azzaluman da suka zaɓi ɗaura RAWANIN ZALINCI a kansu, ya Allah ka bashi iko cika mun burina, ya Allah ka sanya mashi tsoronka da kuma aiki da abin da kace, kasa ya zamana Zaki a cikin zakuna mai ruguje ZALINCI ya kafa ADALCI tamkar jinin ABDUL MUTALLAF na hakika, ya Allah kada ka bar mahaifinsa........." Bata kai karshen addu'ar tata ba wani irin azababben nishi ya kwace mata wanda ya sanyata dakatawa daga addu'ar nan take. Babu wani sauran karfi da ya rage mata, dan haka nishin ma bata iya yin shi sosai ba, amma a haka take ta ƙoƙari tana fama, abin gwanin ban tausayi. Sai dai kuma abin mamaki a nan shi ne yadda take faman tana son ganin ta haihu tamkar wadda ta taɓa haihuwa, kamar ta san komai dangane da haihuwa, ga dukkan alamu wannan ba shi ne haihuwarta ta farko ba, idan ma shi ne to tabbas tana da sani sosai a wannan ɓangare, ko kuma likita ce ma. Jim kaɗan ta saki wani nishi wanda ya zo mata da karfinsa, nan take baby ya faɗo cikin wannan ruwa, ya kuma faɗo duniya da kukansa na nuna alamar lafiyayyene. Cikin sauri ta sanya hannu ta ɗauke shi, dan saboda kada ruwan ya kashe mata shi. A saman kirjinta ta manna shi sai kuka yake yi, ita ma sai a lokacin ta sami damar yin kuka sosai. Jim kaɗan bayan faɗowar baby kamar da minti ɗaya wani sabon nakuda ya taso mata gadan gadan, kankame babyn nata ta yi a saman kirjinta tana salati a cikin zuciyarta tare da ciza laɓɓa, murkusoso ta fara yi, tana wani irin numfashi mai matuƙar ban tausayi. (Kai ko ni Princess Teema ina son sanin labarin wannan mata, kuma ina yi mata fatar Allah ya amsa mata addu'arta ta samu mai kwata mata ƴanci kamar yadda ta buƙata😭 irin wannan azabar zalunci haka?😭) Duk kuma wannan wahala da take ciki taki sakin babyn da yake hannunta, haka ta kankame abinta gam. UWA KENAN BA WANDA ZAI IYA YIN HAKAN SAI ITA!. A nakuda na biyu bata wani wahala sosai ba, ba ta ɗauki lokaci ba shi ma sai ga nishi ya zo mata da karfi, nan take baby na biyu ma ya sake faɗowa, ga na farkon sai kuka yake yi mata, da faɗuwar baby kamar da minti ɗaya sai ga mahaifa ya biyo baya. Mahaifa na faɗowa kuma ta nemi duk wani ciwon kaf ta rasa, Allah ya sawwaka mata. A hanzarce ta ɗauko ɗayan babynma ta haɗe su a saman kirjinta, sai dai baby na biyun sam bai yi kuka ba, bai kuma yi motsi ba, tamkar babu rai a jikinsa, bata damu ba, kuma bata ma lura da babayn bai yi kuka ba, saboda kukan na farkon ya toshe mata kunne kuma ya ɗaga mata hankali, dan tana tsoron kada ace waƴan nan dakarun yaki da suka biyota ɗin suna kusa su jiyo kukan jariri su zo su hallakata su karɓe mata baby's su rabasu, saukin abin ma ɗaya da akwai karan zubar ruwan sama na tashi kuma suna cikin rami, so kukan baya tashi zuwa waje sosai. Kasancewar har lokacin ruwan gudu nan na gangarowa cikin ramin ne yasa ruwan ya kai mata har izuwa saman cikinta a yanzu. Ganin hakan ne yasa ta yi yunkurin miƙewa tare da baby's ɗin suna manne a kirjinta. Amma ina sam ta kasa tashi, wani irin kuka ne ta ji ya zo mata, yanzu idan wannan ruwa ya cika ramin ya zasu yi? Ƴaƴanta mutuwa fa zasu yi, abin ku da jarirai mutuwarsu ba zai yi wahala ba. Tuna cewa idan ruwan nan ya cika ramin nan baby's ɗinta mutuwa zasu yi ne yasa ta sake yin yunkurin tashi, amma ina ta kasa, kara ƙanƙame ƴaƴan nata tayi tana ambaton sunan Allah da ya kawo mata ɗauki, ruwa kuma yana ta kara cika rami, ga ruwan sama sai kara karfin zuba yake yi, walkiya da kuma tsawa ya yawaita a sararin samaniya, duniyar ta yi duhu sosai tamkar dare ne. TO KO TA YA YA WANNAN MATA ZATA FITA DA ƳAƳAN NAN NATA⁉️ A hankali ta dawo da kallonta a kan wannan baby daketa zuba kuka tamkar makoshinsa zai ɓalle. Wasu zafafan hawayene ta ji sun fara zubo mata a saman kuncinta gwanin ban tausayi, yanzu shikenan tana ji tana gani baby's nata zasu mutu a hannunta? Ita sam bata damu da kanta ba, burinta kawai ƴaƴanta su rayu, koda kuwa ita zata mutu, dan tana da yakini da kuma sa ran Allah zai amsa mata addu'arta. Ga baby's ɗin kuwa, jajir da su, haskensu ma irin hasken Koreans ne, dukkanninsu idanunsu a rufe gam, kyawawan gaske ne na wuce misali, dogon hancin nan sak irin na mahaifiyar tasu, wannan mai ihun ɗan bakinsa ɗan karamin, bata duba me ta haifa ba, mata ne ko maza or mace da namiji, sai hankali a kwance ake wannan, ita dai ta rungume kayanta, amma fa ba karya kyawawa gaske ne baby's ɗin, bare ma wannan mai tsallah ihun, ɗan bakinsa jajir sosai, da yake yanayin fatarsu kalar madara kalar Koreans, sai jan lips ɗin ta kara bayyana over. Ɗayan baby dai shiru har yanzu bai motsa ba, da alama dai kamar babu rai a jikinsa, shi kuma lips nasa dark purple ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Wannan baby da bai motsa ba gashin kansa launi ne mafi tsada a duniya, wato launin white color, ba irin normal white da kuka sani ba ne, a'a na babyn ya yi wani irin gold white ne a kwance yana ɗaukar idanu, mai azababben kyau da shi, ba kasafai aka cika samun masu irin gashin a duniya ba, sai ɗaiɗaiku, ɗaiɗaikun ma sai ta can ƙasashen AREWACIN DUNIYA, ta yanki Asia ta Arewa kenan, kuma a bincike ya nuna mafiya yawan masu gold white hair nan, ba karamar baiwa da basira ke garesu ba, amma sai dai kash baby baya motsi, yaki ya motsa, babu rai a jikinsa. Ɗayan baby dake ta tsallah kukan kuwa, gashin kansa bakinkirin ne mai bala'in tsantsin gaske, ya yi tamkar an kifa mishi hula ne a kan nasa, tsabar bakin gashin nasa har ya yi tamkar dark blue, yana wani irin kyalli na daban, ga gashin nasu yar'yar sai tsawo ba cika, kana iya ganin farin fatar kansu, saboda rashin cikar gashin, tsawo kuma ya sauko musu har gaban goshinsu, ya kusa rufe masu idanu. A takaice dai dukkansu biyu suna da tsananin kyau na wuce misali. A hankali hankali fa ruwan nan sai haurowa sama yake yi, yanzu ya fara taɓa mata baby's ɗin nata. Kara haurar da su saman wajen shoulders ɗinta ta yi, tana mai cigaba da kuka tare da ambato sunan Allah da ya kawo mata ɗauki. Bata gaji ba, haka take ta kokarin miƙewa dan ta ceci ƴaƴanta, amma duk wasu gaɓoɓi na jikinta sunki yarda su bata haɗin kai wajen ta iya miƙewa, kada ku manta tana da ciwo a cikinta na kifiya da aka harbeta, ga kuma haihuwa, ai ta auna babban arziki ma da har yanzu take cikin hayyacinta, har yanzu tana karkashin kariyar Ubangiji dan shi kawai take ambata a baki da zucinta, idan kuma ka riki Allah to wlh wani abin idan Ubangiji ya hukunta a kanka, sai mutane su rinƙa kallon kamar tsafi ko asiri, saboda irin baiwar da kuma iko na mahaliccinmu, babu abin da ya fi karfin Allah a duniyar nan. WANNAN ABIN DA SANYA MUTUN CIKIN TASHIN HANKALI YAKE... *Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.* 🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥 Share fisabilillahi 👏 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍 🔥CROWN OF INJUSTICE🔥 🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡 ❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥 (❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥) 🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

Chapter 2 of 75