bata shigo cikin gidan ba ta juya tare da waɗan nan motocin, dole ita ma nata team ɗin daban, sannan suma waɗan nan motoci da alama bana wannan gida bane, suma na wani team ne na daban, abin dai akwai ɗaure kai sosai.
Ƙananun shekarun Leesharh yasa ta kasa iya gane cewa ba komai ake yi dan kuɗi ba, ba kuma komai ne kuɗi yake iya saya ba.
"Leesharh this is your room, ki je ki yi wanka, zan kawo maki kayan sakawa da abinci ki ci ki ƙoshi kin ji? Sai ki kwanta ki ɗan huta zuwa anjuma mai koya maki aiki zata zo, don't mind about what my mum said kin ji? Babu abin da zai sami daddynki, zaki koma wajensa lafiya lou, babu wani abin da zamu yi mashi, yadda kika ga kina cikin wannan room ɗin cikin daula haka shi ma yake, mun ajiye shi ne kawai a ɗaya daga cikin gidanjenmu yana cin arziki shi ma, so dan haka ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki koyi duk abin da za'a koya maki, sannan ki yi aikin ki cikin natsuwa da iya taku ta yadda ba za'a ganeki ba, idan ma kika mayar da hankalinki two months ya yi ti yawa ki kammala mana aikinmu ki koma gida kin ji ko?".
Allah sarki yarinyata, kai kawai Leesharh ta gyaɗa mata alamar ta gansu da maganganunta. Juyawa matar ta yi ta fita domin ta bata waje ta yi wanka.
A hankali kamar mai tsoron taka ƙasa ta ƙarisa bakin shinfiɗaɗiyar bed ɗin ta zauna, sai buɗe hanci take yi tana shakar daddaɗar kamshin perfume ɗin dake room ɗin, tunani kala kala ne a cikin ranta, sai dai zantukan babanta ya fi yi mata yawo a cikin kanta sosai, tana kaunar baban nata sosai, musamman ma da ta zauna da Jasrah yarinya mai ilimin addini, ta koyar da ita abubuwa da dama, a nan ne ta gane cewa babanta yakamata ta so sosai ba mamanta ba, domin baban nata ya fi mamarta gaskiya.
Ta kai a kallah 30 mins a zaune a wajen tana aikin tunanin zantukan babanta dana mamar tata, lokacin da tunanin Jasrah ya ratso mata ta cikin ƙwaƙwalwa tata, nan take wasu siraran hawayen ya fara bin ƙuncinta, har ga Allah bata kawowa ranta rabuwa da Jasrah ba, sam bata taɓa yin wannan tunani ba, amma rana tsaka an rabasu, rabawa mara daɗin ji, ta tabbata yanzu haka Jasrah tana can tana ruwan hawaye, ga shi bata da wata kawa a gidan AAJ, ba kowa, yanzu haka zata yi zaman kaɗaici cikin kunci?.
Kara tsananta gudu hawayen face ɗin nata ya yi, a gaskiya tana kewar Jasrah over. Dafa shoulder ɗinta da aka yi ne ya fargar da ita tare da dawowa cikin hayyacinta. A hanzarce ta ɗago da dara daran idanun nata da suka yi jajir saboda kuka da damuwa.
"Leesharh baki yi wankar ba kin zauna a nan kina kuka? Kukan me kuma kike yi?". Cewar wannan matashiyar matar, hannunta na rike da wasu kaya masu shegen kyau da tsada, abaya ne da mayafinta launin brown color, ya ji stones jikinsa sosai, sai kyalli yake yi.
"Aunty ina kewar Jasrah ce, and ina son ganin babana da kuma kabarin mamata".
Zama a kusa da ita matar ta yi, cikin mutawa tare da nuna fifikon ilimi da shekaru ta fara tsara mata magana kamar haka. "Leesharhi i promise you that idan kika tsaya kika fara aikin nan da kyau, kika yi one to two weeks kina aikin na ga yadda kike tafi da komai, komai ya tafi dai'dai, idan kika mayar da hankali naga kina ƙoƙari, to na yi maki alkawari zan zo na ɗauke ki daga gidan Abu Abdussalam muje na kai ki ki kalli babanki, sannan mu wuce AAJ ki kaiwa Jasrah ɗin ziyara, idan muka dawo naga kina ƙoƙari a kan aikin sosai to duk end of the week zan rinƙa kai ki wajensu kuna ganawa".
Yadda ta yi maganar kana ji kasan kalaman karya da yaudara tare da makirci ne, amma da yake ita Leesharh ba ilimi ishasshe ne ke gareta ba, ga kuma ƙarancin shekaru, sai ta yarda da zancen, kuma da alama ta yarda da wannan mata sosai.
Cigaba da lallaɓata matar ta yi tana kwantar mata da hankali har sai da taga ta samu nutsuwa, sannan ne ta riƙo hannunta suka miƙe ta raka cikin toilet, da kanta ta haɗa mata ruwan wanka saboda makirci, duk cikin taku ne.
Bayan ta haɗa mata ta nuna mata yadda zata yi komai ne ta nufo waje ta barta a cikin toilet ɗin. Sai da Leesharh ta ɗauki almost 30 mins a tsaye a cikin toilet ɗin tana tunane tunane kafin ta fara wanka.
Sosai ta wanke jikinta tsab da tsadaddun shower gels ɗin da suke a cikin toilet ɗin, har wani ɗan haske ta kara yi, dattin gidan AAJ ya fita. Daga yanayin yadda take amfani da abubuwan cikin toilet ɗin zaka fahimci ba yau ta fara ganin ire-irensu ba, da alama ta saba gani, so bata wani nuna kauyanci ba, towel ma ta ɗauro ta nufo waje bayan ta kammala, sai tashin kamshin take yi.
Lokacin da ta fito sai ta tarar da an kawo mata abinci kala kala na larabawa masu shegen tashin kamshi, an geresu a saman rug da yake a cikin room ɗin. Da ido ta fara bin abincin da kallo, wajen kala huɗu ne abinci, duk kuma ita kaɗai aka kawowa, kara jinjinawa wannan al'amari ta yi kafin ta wuce ta ɗauki kayan da yake a saman bed ɗin wanda wannan mata ta ajiye mata. Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanya kayan a jikinta. Sun yi mata kyau sosai, sun kuma zauna a jikinra kamar sun san size ɗinta, har jikinta ya fara sanin cewa ta fara samun canji.
Zama ta yi a gaban abinci, ta zaɓi wanda zata iya ci, ta zuba a plate, hannu baka hannu kwarya ta fara kai abincin nan bakinta, dan a yunwace take baiwar Allah, hakan yasa ta ci sosai da sosai. Wani irin ƙoshi da ta yi ma har sai da ta ji numfashinta yana yin sama sama, da kyar ta iya tattare wajen ta haɗa kayan abin waje guda. Kaɗan ta sha ruwa dan gudun kada ta yi amai, sannan ta ɗan sha lemu kaɗan.
Bayan ta kammala ne ta tashi ta fara gabatar da sallolin da suke a kanta a wajen saman rug ɗin, dan ta ɗauro alwala tun daga cikin toilet da ta gama wanka.
Tana idar da sallar a wajen ta ɓige da barci, anci an ƙoshi me ya rage? Ai sai barci, dama ga wahala da gajiyar gidan AAJ a jikinta.
Ba ita ta farka ba sai da yamma, nan ma wannan matar ce ta zo ta tasheta a kan ta tashi ga mai koya mata aiki ta zo. Da kyar ta iya buɗe idanunta, yau ta kwanta a waje mai laushi ga sanyin Ac haɗe da daddaɗar kamshin perfume, sannan ta ci abinci mai rai da lafiya ta ƙoshi, barci ya yi daɗi har da munshari, duk jikinta sai ta ji ya yi mata nauyi, sam barcin bai isheta ba. Idanuta sun ɗan kumbura sun kuma yi jajir, alama ce ta barci bai isheta ba.
Ba ƙaramin madarar mamaki ta shaba lokacin da ta kalli mai koya mata aikin, ita ma matar tana sanye da nikaf, wannan batu na nikaf ɗin ya fara ɗaurewa Leesharh kai sosai, kowa ka gani a gidan da nikaf? Ita a yanzu bata san face ɗin ko mutun ɗaya daga cikin ƴan gidan ba, su kansu securitys ɗin gidan sanye suke da face mask a fuskokinsu, abin da alamar tambaya sosai, duk da yarinta irin na Leesharh yanzu ta fara tunanin anya akwai gaskiya a wannan gida kuwa?.
Fita wannan matashiyar matar ta yi ta basu waje, ya rage daga Leesharh sai mai koya mata aiki, ita ma matashiyar macece wadda ba zata wuce 30 years a duniya ba, tana tare da wani haɗaɗɗen echolac ɗinta ɗan ma dai'dai ci, hakan ya nuna cewa tare zasu rinƙa kwana da Leesharh a wannan ɗakin kenan.
Sannu da zuwa Leesharh ta yi mata tana ƙoƙarin miƙewa tsaye, ga mamakinta sai taga duk an kwashe kayan abincin da ta ci ta bari, babu komai a room ɗin.
Sam matar bata amsa mata ba, yadda kuka san wasu abokan gaba, sai wucewa da ta yi ta sanya echolac ɗinta a cikin katafaren wardrobe da yake a cikin ɗakin, sannan ta nufi toilet.
Cike da mamaki sosai Leesharh ta bita da kallo, ta sha madarar mamakin ganin yadda matar bata amsa sannunta ba, tunani ta fara yi to ko dai matar bata jin larabci ne? Ga dukkan alamu kuma balarabiya ce, duk da cewa baka iya ganin komai na jikinta sai ido, saboda kayan da ta sanya ta rufe ko'ina nata, amma da alama ba bakar fata bace ba, ko meyasa ta ki amsa mata? Allah masani.
Cike da tunani Leesharh ta wuce wajen katafaren windown da yake fiskantar harabar gidan dan ta leƙa taga ko zata iya samun damar ganin fuskar ɗaya daga cikin ƴan gidan.
Ta kai 10 mins a tsaye a wajen, amma shiru bata ga giftawar wani ɗan adam a harabar gidan ba, jin motsin alamar wancan mata tana ƙoƙarin fitowa daga cikin toilet ɗin ne yasa ta yi saurin barin jikin window ta koma bakin bed ta zauna.
Fitowa matar ta yi a in da ta zo ta ciro dadduma daga cikin echolac ɗinta ta shunfuɗa a kasa saman tiles ɗin ɗakin tare da tada sallah. Sai ƙure mata kallo Leesharh take yi, dama ita fa ba baya ba wajen iya yi wa abu kallon ƙurilla, ba kallon wasa take yi wa abu ba, ƙure mashi kallo take yi ta haddace komai.
Tana ta ƙurewa wannan mata kallo har ta idar da sallarta cikin nutsuwa tare da dai'daito kamar yadda addini ya faɗa, daga ganin yadda wannan mata take sallah tabbas addini ya ratsata sosai, to amma meyasa duk da tana da sani take yi wa waɗan nan unknown mutane aiki? Wannan amsa sai alƙalamina ne kawai zai warware maku, ku dai kasance a tare da ni dan mu warware komai a tare, nasan kuna da tarin tambayoyi sosai a kan rayuwan kowani part na cikin wannan littafi, to kada ku ji komai, sannu a hankali zan nemo bakin zaren kowace part in warware maku dukkan wasu amsoshinku my people.
Bayan wannan mata ta idar da sallah ne ta miƙe ta nufi wajen bed in da Leesharh take a zaune kenan, cikin harshen larabci ta umarceta da ta tashi su nufi cikin gidan, domin ta je ta fara nunnuna mata abubuwa, shi ne abu na farkon da zata fara koya mata, zasu koya mata hakan ne kuma saboda kada Leesharh ɗin ta je ta yi masu kauyanci, dan duk ba ƴan kauye bane suke yi wa familyn Abu Abdussalam bin Badeen aiki, sai mai kwalin maratu suke ɗauka aiki, dan basu son shirme da shiririta, dan haka duk sai an wayarwa da Leesharh kai sosai da sosai, ta zama kamar cikakkiyar ƴan boko, an kara buɗe mata idanu, kada a samu matsala.
Gaba matar ta yi ba tare da ta jira ta ji me Leesharh zata ce ba. Jiki ba kwari ta tashi ta bi bayanta tana mamakin hali irin na wannan mata, ita kuma haka rayuwarta yake kenan? A haka kuma zasu zauna har tsawon sati ɗaya zuwa biyu? Tab akwai matsala kuwa.
To nima dai bari na motsa na leƙa wani bangare kafin mu dawo watakila Leesharh ta iya aikin da suke son ta iya.
🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
GIDANSU KHADIJAH💔😥
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 8/8/2024.....✍️📚🌹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________31🔥
🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
GIDANSU KHADIJAH💔😥
Sai can rana wuraren karfe 2 su Maman Zainab suka dawo daga wajen malamin nasu, gidanta Aunty Hauwa ta wuce, ita kuma Maman Zainab ta nufo nata gidan. Tun da ta kamo hanyar gida take jin gabanta yana faɗuwa, amma bata kawo komai a ranta ba, a duk lokacin da ta tuna alkawarin da wannan malami ko ace bokan ya yi mata na cewa tana komawa gida zata ga result ɗin aikinta, sai ta ji wani sanyi ya ratsa zuciyarta.
Kuɗi raina na dukan naira har naira 200k ta kwasa ta bawa wannan bokan, Aunty Hauwa ce nan ta yi ta zugata a kan ta bada kada ta wani damu tun da buƙatarsu zai biya, da yake tana da kuɗi issassu, da ni da ku duk mun san da cewa baban Zainab dai bai rageta da komai ba, tana samun kuɗi a hannunsa sosai, wani lokaci haka kawai zai dunƙule dubu ɗari ya bata ya ce ko zata yi wani buƙata, to tara kuɗin take yi, dan kunga bata sayan komai a gidan, ko ashana shi yake sayowa dayawa ya ajiye, hakan yasa take da isassun kuɗaɗe a cikin account ɗinta, shiyasa bata nemi ko sisi daga hannunsa ba da zasu je wajen malamin, sai dai single ɗinsa da ta ɗauka da kuma hularsa, dan Aunty Hauwa ta ce mata ta ɗauki wasu daga cikin abubuwan da yake amfani da su, domin bokan nasu zai buƙaci hakan, ita ma haka wai aka yi mata na mijinta, to shi ne yasa ta ɗauki wannan ma.
Ko da ta iso gida cike da murna, ga mamakinta sai ta ga kofar gidan a buɗe sabanin fitarta, ta dai san ta rufe gidan kafin ta fita, kuma lokacin dawowar su Khadija daga school bai yi ba bare ace kawunsu Sadiq ne da ya dawo da su ya buɗe masu gidan, kowa na gidan daga kan Baban Zainab, Haidar, Sadiq duk suna da key ɗin kofar gidan.
Ciro wayarta ta yi ta fara duba time, nan take kirjinta ya fara dukan uku uku na ganin cewa lokacin dawowar su Khadija bai yi ba, to kenan waye ya buɗe gidan? Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsarta.
Fargabarta ɗaya kada ace Baban Zainab ne ya yi masu dawowar rana irin na kwanaki biyu da suka wuce, idan kuwa shi ne to fa akwai cakwakiya, dan kuwa zata sha faɗa ba kaɗan ba na fita bada izininsa ba, ya fita kishi sosai, kawai dai kawar da kai wani lokaci yake yi dan a samu zaman lafiya, amma ita nata kishin nafila ne a kan nasa.
Cike da fargabar abin da zata tarar a cikin gidan ta turo kofar ta shigo. Tsoro da mamaki ne suka kara kamata lokacin da ta turo kofar ta ji ko jam lock ba'a sanyawa kofar ta ciki ba. Ta san da cewa tabbas suna sanya jam lock ta ciki, saboda matasan marasa tarbiyar da suka yi yawa a unguwar, ga shaye shaye, kana zaune baka san hawa ba baka san sauƙa ba zasu faɗo maka cikin gida, sun sha sun bugu ba hankali a tattare da su, basu san ma sun faɗo gidan ba, hakan yasa suke rufe kofar duk wanda ya zo sai ya yi knocking azo a buɗe mashi. Amma yau sai ta ji kofar a buɗe, hakan yasa ta kara fargaba da shiga tsoro, sai yanzu ta fara danasanin fita bata tambaye shi ba da ta yi.
Sai kuma yanzu ne abubuwan da suka faru ɗazun ɗin suka fara dawo mata cikin kanta, gabaɗaya sai ta ji jikinta ya saki, duk sai ta ji ta yi nadama kuma ta ji babu daɗi. Kutsawa cikin gidan ta yi tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ita kaɗai tasan me take tunani.
Ƙasa ƙasa ta yi sallama a bakin kofar shiga parlourn. Shiru babu wanda ya amsa mata, cike da fargaba ta sanya hannu ya yaye curtain ɗin kofar.
Kwance yake a saman doguwar sofa mai zaman mutun uku, ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman fuskarsa, ɗayan hannun nasa kuma yana riƙe da remote na Tv, ga Tvn yana magana ƙasa ƙasa, sanye yake da brown ɗin jallabiya wadda ta sha guga sosai, har wani kyalli take yi saboda an saba gogeta sosai, ga karin gugan nan a jikinta ya fito ɓaro ɓari, sam ba barci yake yi ba, yana jin sallamar tata, a cikin zuciya ya amsa, magana ne baya son yi mata.
Wani irin dum dum ta ji gabanta ya faɗi, tunani ta fara yi a kan tun yaushe ya dawo? Idan bai jima da dawowa ba in ya tambayeta ina ta je sai ta yi mashi karyar maƙota nan ta shiga, tasan cewa ko gidan Aunty Hauwa bai yarda ta je ba, idan tana son zuwa shi yake kaita da mashin ɗinsa, idan ya kaita kuma zai gaya mata ga time ɗin da zai dawo ya ɗauketa, lokaci na cika kuma ɗan halak zaku ga ya zo ya ɗauketa sun dawo, bata zuwa ko'ina ita kaɗai ko da kanta, saboda yadda ya ɗaukota daga garinsu ya kawota nan garin da bata da kowa sai ƴan uwansa da basu sonta sai kuma Aunty Hauwa, hakan yasa yake kula da ita sosai, saboda ya sauke hakkinta da yake a kansa, akwai shi da ilimin addini sosai, kuma yana aiki da ita, duk wani hakkin mace ya sani, kuma yana ƙoƙari wajen saukewa iya iyawarsa.
Cikin parlourn ta shigo jiki ba kwari, sai faɗuwa gabanta yake yi, tun da ta shigo take binsa da kallo, ko gezau bai yi ba, bai yi kamar ma yasan da mutun ya shigo ba, hakan yasa ta fara jin fargaba da faɗuwar gaba. Room ɗinta ta wuce da sauri dan ta je ta ɓoye abubuwan da bokan ya bata da ta sanya a cikin jakarta.
Tana ajiyewa ta yi maza ta dawo parlourn, da yake bata da gaskiya ko da ta je ajiye jakar sai taga kamar baban Zainab ɗin ya biyo bayanta yana leƙarta, hakan yasa ta yi saurin ajiyewa ta fito, abin ku da bata saba ba, duk sai ta bi ta tsargu tana neman tonawa kanta asiri, ta rasa a ina zata sanya ranta.
Saman sofa mai zaman mutun ɗaya ta zo ta zauna tare da ce mashi sannu da dawowa, tsoro da fargaba yasa ta manta da cewa faɗa suke yi, ta manta da cewa tana fushi da shi bata yi mashi magana.
Yana jinta amma bai amsa ba, ya yi kamar bashi a parlourn, dan iya ɓacin rai ta ɓata mashi rai, tun karfe 11 ya dawo gidan domin ya ɗebe mata kewa, ya dawo ya cigaba da rarrashinta tare da bata hakuri kamar yadda ya saba, amma sai ya zo ya ga bata nan, kuma bata sanar da shi ga in da zata je ba, ya kira numberta a lokacin suna kan dutse babu network, ya gwada numberta ya fi sau hamshin, amma bata shiga, ya kira number Aunty Hauwa ma bata shiga, ya je gidan Aunty Hauwar Khadija kanwar mijin Aunty Hauwar ta ce mashi Aunty Hauwa bata nan tana wajen business ɗinta na yawon bin gidan dillalai, ita kuma maman Zainab bata zo gidan ba, bawan Allah ya shiga damuwa sosai a kan to ina ta je tun da bata je gidan Aunty Hauwa ba? Ya dai san bata san kowa ba, bata kuma zuwa gidansu Haidar, gara ma gidan hajiyarsa wani lokacin yana kaita su kuma dawo a tare, baya yarda ya barta a can, dan yasan hajiyarsa zata takura mata, a tare suke zuwa su gaisheta su kuma dawo a tare.
Bawan Allah nan ya yi tunani sun fi kala ɗari a kan ina taje? Wani zuciya ya rinƙa raya mashi cewa kila ta yi fushi ne ta shiga mota ta koma gidansu, ya kira mamanta cikin hikima ta yadda ba zata yi zargin komai ba ya tambayeta ko ta yi magana da maman Zainab da safe ne? Da maman ta tambayesa lafiya? Sai ya ce lafiya lou kawai dama maman Zainab ɗin ce ta tambayesa a kan zata je gida shi kuma ya hana, shi ne ta ce sai ta gayawa mama, to shi ne ya kira ya ji idan ta kawo kararsa ya bada hakuri. Bawan Allah.
Murmushi kawai mahaifiyar tata ta yi tare da gaya mashi bata kira ta kawo kararsa ba ya kwantar da hankalinsa, rabon ma da su yi waya tun shekaran jiya, hakan yasa ya fahimci lallai ba garinsu ta tafi ba, dan da garinsu ta nufa dole zata sanar da mamarta, ya kira Sadiq da ya baro a kasuwa ya tambayesa ko ta gaya mashi zata je wani waje?.
Mamaki ne sosai ya kama Sadiq ɗin, domin kuwa bai taɓa jin maman Zainab ta fita har baban Zainab ɗin ya nemeta ba, abin ya ɗaure mashi kai, haka dai ya bawa baban Zainab ɗin amsa da a'a ai shi ta kwana biyu ma bata yi mashi magana tun lokacin da suka yi wannan faɗar.
Da okey kawai baban Zainab ɗin ya amsa mashi tare da katse kiran. Yana katse kiran Sadiq ɗin ya hau kiran numberta dan ya ji a ina take? Amma ina number bata shiga, babu network.
Tunani baban Zainab ya fara yi a kan to kodai dama haka take yi kullum ne? Abin ku da shaiɗai ko ya ya samu kofa sai ya cusa maka wani mummunar tunanin, sai ya fara raya mashi cewa ai dama kullum idan ya fita ita ma fita take yi ta tafi yawonta, sai yau ne Allah ya nufa dubunta ya cika ya kamata, wannan tunani shi ne yafi tsaya mashi a ransa sosai, kawai burinsa yanzu ya ji ina take zuwa to?
Kamar zai yi hauka haka ya rinƙa nemanta har wajen karfe 1 na rana, sannan ne ya hakura ya dawo gida ya kwanta, sallar azahar ma yau a gida ya yi, damuwa tasa ya kasa iya zuwa masallaci ya bi jam'i, ya rasa ina zai sanya ransa bawan Allah nan, ta ko'ina ba sauki, ga hajiyarsa a gefe ga kuma maman Haidar, yanzu kuma maman Zainab ta kawo mashi sabuwar bala'i, kunga kuwa ai bai yi laifi ba da ya shareta da ta dawo! Yana ma da ƙoƙarin da kuma hakuri tare da juriya, idan wani namijin ne wlh kina yin sallama zai fara sauke maki buhu buhun masifa a kan gidan uban waye kika je ba tare da izininsa ba? Amma shi sai ya yi shiru yana mai cigaba da haɗiyar bakin cikinsa a ransa, ya yi kamar bai ganta ba, da alama kuma ya yi hakan ne dan baya son ya yi magana da ita cikin fushi da ɓacin rai, yana da ilimi, yasan cewa idan mutun yana cikin fushi ya buɗe bakinsa to tabbas sai ya yi danasani, hakan yasa bai kulata ba, sai ya huce tukun nan.
Ta kai almost 20 mins a zaune a wajen bai ko ɗago idanun ya kalleta ba, idanunsa na a kan Tv kamar mai yin kallo da gaske, alhalin ba wani kallon da yake yi, duniyar tunani ma ya afka, yo bakinciki ma ina zata barshi ya iya yin wani kallo? Ai babu wannan zance kuma.
Da dai taga bashi da niyar kallon in da take ma bare ya yi mata magana sai ta miƙe ta nufi kitchen domin ta girkawa ƴaƴanta abinci sun kusa dawowa daga school. Farar shinkafa ta dafa masu, already tana da miyar steew ɗin da ta yi da safe, so sai ta ɗauko shi ta sake ɗumamawa, ta zubesu a kulolinta kamar yadda ta saba ta kwasa izuwa cikin parlourn.
Tana kokarin shirya abincin su Khadija suka shigo, sun dawo daga school, lemun kankana da abarba ta haɗawa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 43 Chapter of 75