An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
🔥💔𝑨 𝒕𝒐𝒖𝒄𝒉𝒊𝒏𝒈 𝒉𝒆𝒂𝒓𝒕𝒔 𝒍𝒐𝒗𝒆 𝒔𝒕𝒐𝒓𝒚, 𝒅𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚 𝒐𝒃𝒔𝒕𝒂𝒄𝒍𝒆, 𝒂𝒏𝒅 𝒓𝒐𝒎𝒂𝒏𝒄𝒆💔🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
*Gargaɗi! Gargaɗi!! Gargaɗi!!! Ban yardaba! ban Amince ba! ban lamunceba! A juya mun labarin LITTAFINA tako wacce sigar, bana so, ban bada damaba, idan kana buƙata akwai numberta a jiki ki\ka nemi izinina, ban yarda a karanta mun shi a youTube ba, ko a haɗa mun Document, a kiyaye domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki! In kunne yaji gaggan jiki ya tsira. Wannan littafin RAWANIN ZALINCI haƙin mallakarsa nawane FATEEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA)!.*
*Ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara wannan littafi lafiya, Allah ya bani ikon kamala shi lafiya.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. mun fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, da shi muka dogara kuma a gare shi kawai muke neman taimako.🥰 Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Rahma ɗan gata a wajen Allah, kuma fiyayyen halitta wato Annabi MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA🤍*
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 28/6/2024.....✍️📚🌹
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
❤️𝑬𝑷𝑰𝑺𝑶𝑫𝑬__________1🔥
Iska mai matukar ƙarfin gaske ne yake kaɗa dogayen bishiyoyin dake a kewaye da wannan ƙungurmin dajin! Tamkar za'ayi ruwan sama, garin ya haɗe ya yi duhu bakin kirin da hadari, sararin samaniya ya bada wasu launuka, ja, sky blue, navy blue, da kuma dark ash masu matuƙar ɗaukar hankalin, saboda hadirin!.
Daga gabas ta tsakiya wani tapkeken bakar gizo ne wato Rainbow ya fito a sararin samaniyar.
Sannu a hankali walkiya ya fara wanzuwa a sararin samaniyar, haka zalika tsawa ta fara bayyana, alama ce ta ruwan saman ya gabato.
Iskar kara tsananta take yi sosai, while shima hadarin kara baki yake yi sosai, yana mamaye ko'ina a faɗin garin, gabaɗaya korayen ganyayyaki da dogayen ciyayin dake cike a wajen, sai wani irin kaɗawa suke yi har suna kwanciya, tamkar za su tsigo daga jikin tushensu, da alama dai wannan ruwa ne mai karfin gaske yake zuwa, da iska da tsawa!.
Daji ne mai cike da yalwar itatuwa, dogaye, manya manya masu kauri, akwai yalwar ƴaƴan itatuwa kala kala sosai a cike a cikinta, akwai ƴelwar abubuwa masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, irinsu koramai dake zubar da ruwa mai ban sha'awa, duwatsu manya manya masu ɗaukar hankali, koguna wato kogon dutse manya da kanana, tsaunika masu tsawo, rafuna masu cike tab da ruwa mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, a saman mafiya yawan tsaunikan dake a cikin wannan dajin da akwai jiga jigan kogunan duwatsu a wajen, ga kuma bishiyoyi masu ɗaukar hankali, da dai sauransu.
Sai dai da alama akwai haɗari matuƙa a cikin wannan daji, domin kuwa ba za'a rasa muggayen namun dawa masu haɗari irinsu Zaki, Damusa, Kura, Giwa, Sloot, dabba mai nawa da saiɓi, Puma Tiger, Guanaco, dabba mai kama da raƙumi, Vampire Spader, masu kashe sauro, Honey vaja, Dage, Damusar chiter, Dila, Dilar Jakal, Birrai, Gorillas, Tsuntsaye, Macizan kubras, Hayanas da dai sauran mugayen namomin daji.
Wani irin sauti ne yake tasowa tamkar na sahun gudun ɗan adam, sautin yana fitowa ne daga bayan wasu dogayen bishiyoyi na zaitin dake fuskantar gabas ta tsakiya, bishiyoyin suna a cunkushe ne waje guda, sai wajen ya bada duhu tamkar maraice ne a lokacin.
Da kaɗan da kaɗan sautin nan ke tahowa, har ya fara karaɗe kewayen wajen.
Bayan wani ɗan lokaci wannan sauti ya kara matsowa kusa sosai, kasan cewar gari ne na damuna, ta ko'ina akwai ruwa wanda ya kasance ya yi ramuka kanana, sannan wasu gurare daga cikin wannan katafaren dajin sun kasance da akwai taɓo, wasu kuma farin kasa yashi ne tas, kamar dai sauran manya manyan dajuka da kuka sani.
Wannan ramuka kanana masu ruwan, duk in aka takasu sai ruwan ya yi kara palcam, hakan yasa sautin gudun ya kara fitowa ɓaro ɓaro sosai da ya karaɗe yankin wajen!.
Jim kaɗan ta bayyana a tsakiyar dogayen bishiyoyin nan.
Mace ce fara tas tamkar balarabiya, a kallon farko idan ka yi mata sai ka yi wani irin razana, saboda tsannin kyau da kuma yanayin da ta bayyana a wajen, tamkar wata rafaniya ko ace irin kyawawan aljanun nan masu kamar su suka yi kansu dan kyau.
Launin hasken fatartata gwanin ban sha'awa, luwai luwai, jajir da ita a cikin korayen ganyayyaki, ya kuke tunanin bayyanarta zai kasance a idanun ɗan adam?, dole duk wanda ya ganta a wajen sai hantar cikinsa ta kaɗa ya tsorata aihun, dan kyau na ɗiga.
Da kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci cewa daga gidan hutu ta fito! Dan jiki duk madara da ice cream ce! Kyakkyawar gaske ce, gata da tsawo, doguwa da ita, a shekaru ba zata wuci 22 to 23 years a duniya ba.
Sanye take da kaya masu bala'in kyau da tsada, kaya ne irin na hamshaƙan gimbiyoyi, ire iren waɗan nan dogayen riguna ne da ƴaƴan manya manyan jiga jigan sarakuna suke sanyawa, rigar kawai abar kallo ce, dan ta tsaru iya tsaruwa, ta sha kwalliya da wasu shegun duwatsu masu bala'in haske har suna wani ɗaukar idanu.
Daga kanta har ƙasa wani dankarere kuma haɗaɗe tsadadden alkyabba ce mai hula, launin Golden color, while shi kuma doguwar rigar jikin nata launun ligh ash ne, sai launin alkyabban ya hau da rigar sosai.
Kunnenta hannunta zuwa wuyarta, shake suke da dankara dankaran kayan ado na gold masu bala'in tsada, shi sarkar wuyarta ma yana da tsawo har saman breast nata, ga shi da faɗi, na zallar madarar gold ne babu sirki.
Takalmar dake kafafunta ma kawai abin kallo ne, irin takalmar nan ne da manyan gimbiyoyi da ake ji dasu a duniya suke amfani da su, takalma ne masu matukar tsada wanda kwalliyar jikinsu ma da gold aka yi su, sai wani ɗaukar idanu suke yi. A takaice dai jikin wannan mata daga sama har kasa narkakkun makudan dukiya ne ba na wasa ba aka kashe, bakina ni dai PRINCESS TEEMA ya yi kaɗan ya zayyana maku irin kuɗin da aka narka a kwalliyar dake jikinta.
Daga cikin hular alkyabbar jikin nata, kana iya hango wani kwantatcen bakin gashi siɗif da ya zubo mata ta saman shoulders ɗinta har izuwa kirjinta ta gefen dama. Tana da dara daran idanu sosai, launin kwayar idanunta ash color ne, irin light ash ɗin nan da zaku kalli kamar basu iya ganin mutane, saboda kyallin idanuwan nasu, dan ya yi light, sai ya yi kamar yana. Tana da dogon fuska, amma ba sosai ba, sannan ba laifi tana da ɗan cikar fuskar, haka zalika tana da innocent face sosai, da kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci she is so silent, bata da hayaniya, bata da ƙiba sosai, ƴar caras cas da ita. Karshen haɗuwa ce ita ɗin!! Kamar ba mutun ba dan kyau!.
Daga saman kanta har izuwa fararen lausasan kafafunta, gabaɗaya gumi ne ya jiketa sharkaf, daga gefe da gefen face nata, wasu zufa ne suke kara tsastsafo mata kamar ruwa, fuskarta gabaɗaya ya jike sharkaf da gumi, tamkar wadda aka watsawa ruwa a face ɗin tata, wani irin uban haki take fitarwa sama sama, idanuwanta har wani irin juyewa sama suke yi, saboda wahalar gudun nan da ta sha, gabaɗaya a tsananin razane take, wannan innocent face ɗin tata ta koma a wani irin razane gwanin ban tausayi.
Daga gani kasan gudun cetan rai take yi, ga tsohon cikin a jikinta, wanda a kalla ya kai watanni haihuwa, kuma da alama ma ta fara naƙuda, ko kuma wahalar gudun ne ya bayyana a jikinta tamkar mai naƙuda. Amma a haka take wannan uban gudun, daga ganin kasan bala'in da ya korota ta shigo cikin wannan bakin daji ba ƙaramin abu ba ne.
Duk da wannan tsohon cikin nata, haka ta jure take tika uban guda, ta gaji iya gajiya, amma bata tsaya ba, ta yi wani wiki wiki da ita gwanin ban tausayi, duk ta fita daga cikin hayyacinta.
Gudu take yi bata san ina ta dosa ba! Duk wanda ya kalleta a cikin wannan hali da take a ciki, sai ya matsa mata kwallah, babban abin tausayin ma shi ne wannan tsohon cikin nan da yake jikinta.
Kutsawa ta sake yi ta cikin wasu bishiyoyin mangoro dake ɗan nesa daga in da ta fito, sai wani irin haki take yi mai matukar razanarwa, sama sama take fidda numfashi mai sauti, da sauri sauri tamkar wadda aka shake na tsawon lokaci bata sami iska ba, daga baya aka saketa, haka take fitar da numfashi, da alama ma faɗa take yi da numfashin nata, domin ta dai'dai ta shi ya dawo dai'dai, wani irin razanannen tashin hankali ne bayyane a saman fuskarta. Tabbas wannan mata tana cikin bakin bala'in tsaka mai wuya!!.
Wani uban sautin gudun lafiyayyun dawakai ne yake tasowa daga ta hanyar da ta fito ɗan nesa kaɗan, da karfi-karfi dawakan nan suke gudu, kai daga ji kasan suma suna gudune domin cinma wani abin da idan ba su cin mishi ba, suna iya rasa rayukansu, ma'ana suma dai gudun cetan nasu rayukan suke yi kenan.
A lokacin already matar ta kutsa ta cikin bishiyoyin dake fuskantar yamma kenan. Da karfi karfi gudun waɗan nan dawakai ke kara dimfarowa kusa, sai wani irin uban haniniya dawakan suke yi, da alama waƴan da suke a kan dawakan, a ƙage suke da su je in da suke da buƙatar zuwa, suna ba wa dawakan wuta sosai ne, ma'ana suna sanya dawakan gudun wuce ka'idar dabbobi.
Jim kaɗan!.
Duk wani mutun mai rai matuƙar yana wannan waje, to sai ya yi mahaukacin razana a lokacin da waƴan nan dawakan suka bayyana a tsakiyar filin bishiyoyin nan. Wasu irin mahaukatan manya manyan dawakai ne, masu tsantsar lafiya tare da ƙoshi! Da alama sun kiwatu fiye da tunanin mai tunani, dama can kun san doki da shegen karfin tsiya, bare ace ya samu kiwo mai kyau, ai abin sai wanda ya gani kawai.
Wasu irin shirga shirgan jiga jigan manya manyan sadaukan yaki ne a saman waƴan nan ƙosassun dawakan, wanda ganinsu kawai sai ya razana duk wata halittar ɗan adam mai rai. Gabaɗayansu sanye suke cikin kayan yaki a jikkunansu, kayan yaki kuma irin wanda ake yin su da dafaffen karfe, wadda bullet ko kifiya or takobi bata huda su, daga ganinsu kasan daga wani katafaren Kingdom (Masarauta) suka fito, fuskokinsu gabaɗayansu a rufe da irin waɗannan hular kayan yakin nasu da suke sawa, kayin hular nasu yana da kaho guda biyu kamar na ɓauna, baka iya ganin fuskokinsu, sai ido, hanci da kuma tsagen baki, dan hular nasu tamkar mask haka yake, dan ya tare musu kansu idan ana yaki, kun dai gane hular mayaka dai ko? To su dai.
Daga bayansu kuma manya manyan lafiyayyun kwari da kifiyoyi ne tsakale a bayan nasu, wanda ba sa saɓa saiti, shi suka ratayo a bayan nasu, dai'dai kugunsu kuma, wasu irin mahaukatan zaratan takuban nan ne, masu kaifin bala'i, wanda kaifin su zai iya fille wuyar mutun nan take, kafafunsu na sanye cikin irin waƴan nan takalmar nasu na mayaka, masu kama da waterproof shoe, sai dai nasu yana da igiya wanda aka ɗaure har saman kaurin damatsan kafafunsu.
Ko baka ga fuskokinsu ba, kasan waƴan nan basu da imani ko miskala zarratin a ransu, saboda mawuyacin abu ne mai imani ya biyo mace mai tsohon ciki tana naƙuda a irin wannan dokar bakar daji haka, babu tausayi ba imani su biyota da dawakai suna neman hallaka ta, innalillahi wa inna ilaihir rajiun........😭
Dawakai shidda ne, haka zalika Warriors (mayaka) shidda ne a kansu, sun horu a fagen yaki sun ƙoshi, kamar wasu bujuman mayunwatan zakuna haka suke.
Tamkar sun san hanyar da ta bi, suma nan suka nufa da wani mahaukacin gudu.
A ɓangaren wannan mata kuwa, tun da ta kutsa ta cikin waɗan nan bishiyoyin, wani azababben kuma balaƴaƴƴen ciwon ciki ne ya turnuketa lokaci guda, wani irin kullewa mararta ta yi, ta riƙe gam tana yi mata bala'in ciwo na gasken gaske kuwa.
(ALLAH SARKI KO DAN JIJJIGA CIKI NATA DA TA YI NA WANNAN UBAN GUDU DA TA SHA, DOLE NEMA CIKIN NATA YA YI CIWO......😭)
Da kyar take jawo wani wahalallen yawu tana haɗiyewa, saboda bala'in kishin ruwa da take ji, maƙoshinta ya bushe sosai.
Ƙasa cigaba da guduwa ta yi, wanda hakan yasa ta zube kasa a saman gwiwowinta gaban wasu bishiyoyin kashu, tana mai fafutukar jawo numfashinta, ta daidai ta shi dan ta ceci rayuwarta da na abin da yake a cikinta.
Baiwar Allah da hannu bibbiyu ta tallaɓo katon cikin nan nata ta kasa, ji take yi tamkar cikin nata zai faɗi kasa ne, dan tsabar bakar wahala har ji ta yi cikin nata ya rabu da mahaɗar haƙarƙarinta ya yi kasa,.............. Wayyo Allah, ya ilahi ya lillahi.
Zufar azaba da wahale ne yake cigaba da tsantsafo mata daga gefe da gefen kunnenta, fuskarta kuwa tuni ya kara jikewa sharkaf da gumi, tamkar wanda aka watsawa ruwa, wani irin wahalallen marayar kuka ta saki, wanda kuma muryarta kwata kwata bata fita, babu sauti a tattare da ita, wahala ta yi wahala, ta ma nemi hawayen a jikinta ta rasa, yau hawayen kukan ma babu shi, dama kuma duk wahalar da ake yi wa hawaye, to bata kai wahala ba, muddin ta kai wahala, da kanka zaka nemi hawayen ka rasa shi.
Tana a tsaka da wannan hali, kunnuwanta suka fara tsinkayo mata sautin gudun tare da haniniyar waƴan nan dawakan daga can nesa da ita a karo na biyu!.
Jin sautin na kara dinfarota gadan gadan ne yasa ta ji wani irin mahaukacin karfi ya zo mata, a wahale ta daure tare da ciza laɓɓanta da karfi tamkar zata fasasu, da iya karfin da ya rage mata baiwar Allah ta miƙe dan ta cigaba da gudu ko zata tsira da ranta.
Bata san ina ta nufa ba, bata san ina take takawa ba, haka ta cigaba da gudu, ta cigaba da tsaga tsakanin manya manyan dogayen bishiyoyi tana wucewa!.
Wannan Baiwar Allah dai ta ci bakar wahalar da ko makiyinka ba zaka yi mashi fatar faɗa wa makamancin wannan wahala da bala'i ba, sai nishi take yi sama sama, da alama tana da yakinin da kuma burin cigaba da rayuwa, alamu sun nuna akwai tsantsar burin son ta cigaba da rayuwa a tattare da ita, kuma daga kwayar idanunta zaka fahimci akwai wani babbar Al'amari da take buri da kuma fatan cinma shi a rayuwarta, daga yanayin yanda take gudun take ƙoƙarin ganin ta rayu duk da mawuyacin abu ne ta zullewa waƴan nan mayun azzaluman dakarun yakin, sai dai wani ikon Allah, amma dai bata sare ba, kuma bata yanke kauna ba, haka zalika bata cire rai daga samun Rahmar Ubangiji ba. BABBAR MAGANA KO YA YA WANNAN AL'AMARI ZATA KASANCE? FARKO KENAN DAGA CIKIN LITTAFIN RAWANIN ZALINCI, (🤍 PRINCESS TEEMA CE 🔥💘 HAR WA YAU.)
Bata yi nisa a gudun nata ba ta isko karshen hanyar, wanda kuma ya kasance wani katon dutse ne da baka ganin iyakarsa a faɗi, ƙasan dutsen kuwa, katafaren teku ne mai girman gaske, tekun cike yake maƙil da farin ruwa tas, har wani ɗaukar kalar sararin samaniya ruwan nan yake yi, saboda haskensa! Sai dai kuma tsakanin tekun da wannan dutse da take a kai, akwai nisa sosai, sannan kuma, akwai dogayen bishiyoyi ta gefe gefe ruwan, bayan haka akwai abubuwa da dama dai irin na ko wace babbar daji da ta amsa sunanta daji.
Dakatawa ta yi daga gudun da take yi tana mai kallon wannan tapkeken tekun, tana sakin wahalallen nishi. Wannan shi ne gaba babu hanya baya ma babu hanya, gaba teku baya warriors! Ya kenan?.
A hankali tamkar mai tsoron juyowa ta juyo dan ta kalli waɗan nan masu bin nata, wanda suma a daidai lokacin suka cin mata, har lokacin tana cije da laɓɓanta bata saki ba, hakan zai fahimtar da kai tana cikin azaba.
Juyowarta ya yi daidai da ɗaya daga cikin warriors ɗin ya ciro kwari da baka daga bayansa, ya ɗana kifiyarta tare da ja da karfi, ya saitata, kai tsaye ya harbeta sai saman katon cikin nan nata ta gefen hagu.
Wani irin jini jajazir ne ya fallatsa ya fito daga jikinta, da alama jinin nata ma, ya jijjiga sosai, dan kuwa yanda ya fallatsar nan tamkar jira yake yi a huda mishi hanya ya fito.
(*PRINCESS TEEMA CE....✍️🔥💘* )
Saboda gajiya da kuma bakar azabar wahalar da ta sha, muryarta baya fita sosai, wani irin wahalallen ihu ta saki wanda sautinsa bai fita ba, cikin bakin azaba da wahala ta sanya hannunta bibbiyu ta dafe cikin nata tare da riƙo kifiyar da suka harbeta da shi ɗin gam tana nishi, lokaci guda fuskarta ta sauya, har wani kumburi ta yi cikin ƙanƙanin lokaci, dama kuma ga na ciki a gefe, sai abin ya haɗu ya yi mata yawa, duk wanda ya kalleta a halin da take a ciki, komai rashin imaninsa matuƙar musulmi ne yasan kalmar shahada, kai ko ba musulmi ba sai ya matsa mata kwallah ba kaɗan ba, domin tana cikin wani irin bakin mawuyacin hali wanda baki ma ba zai iya misilta shi ba.
Su kuwa waƴan nan shaiɗanun azzaluman, ko a jikinsu, tamkar ba mutane bane, tamkar babu zuciya a kirazansu, tamkar wasu dafaffun karafuna ne ko ace duwatsu ne a matsayin zukatansu ba zuciya ba, saboda tsantsar zallar madarar rashin Imani dake tattare da su, sai ma ƙoƙarin ciro wani kifiya ɗaya daga cikinsu ya yi domin ya kara sake mata a cikin nata, duk da halin da take ciki basu da niyar raga mata ko su tausaya mata.
Cikin fitar hayyaci ta saki wani marayar wahalallen kuka tare da yin baya baya ta faɗa kasan wannan katafaren kogi ko ace teku, dan ko rani ya yi damina ya ɗauke, wannan tekun bata ƙafewa, shi kuma kogi yana iya kafewa a lokacin da ba damuna bane.
Faɗawarta kasar wannan dutsen ya yi dai'dai da kecewar ruwan sama kamar da bakin kwarya, ga tsawa da walkiya mai karfin gaske.
Tsakanin wannan dutse da kuma ruwan dake a ƙasansa, zai iya kai a kallah 3.6 meter, amma haka ta faɗa kasan, hakan kuma zai kara tabbatar muku da cewa tabbas bata son mutuwa a hannun waƴan nan azzaluman, tabbas tana da bukatar cigaba da rayuwa.
Ganin ta faɗa kasan ne yasa suka ƙariso waje ba tare da sun sauƙa daga kan dawakansu ba, babu alamar tsoro, tausayi, imani a tattare dasu, sai ma alamar jarumta tare da taurin zuciya.
Ruwan saman na dukansu, haka suka tsaya a cikinsa dan cimma burinsu, sai wani irin numfashi mara daɗin ji dawakan nasu suke fitarwa, su kansu warriors dake a saman dawakan, sai wani numfashin suke yi alamar sun wahala a gudun da suka sha.
Suna ƙarisowa ɗaya daga cikinsu ya sauƙa daga saman dokin nasa yana wani irin taku wanda yake nuna cikakken warriors ne, wato (Mayaki) lafiyayye mai jini a jika, duk in ya taka kasa, sai wajen ya amsa, yana da tsawo ga faɗin kirji sosai, sannan ga cikar halittar namiji, wanda yake nuna maka cewa cikakken gwarzon mayaki ne, ya horu ainun.
Kasan dutse ya zo ya leƙa a yayin da su kuma sauran suke a saman dawakansu suna jiran su ji me ake ciki.
Ko alamarta bai ga ni ba, da ya leƙa, alamu sun nuna ruwa ya tafi da ita, a nasa tunanin, katafaren teku ne wanda ya kai har mararrabar Masarautar su da kuma ƙasar dake makwabtaka da su, ma'ana wannan tekun ya zama kamar itace bordersu kenan.
Juyowa ya yi ya nufi bujumin dokinsa yana girgiza masu kai, alamar su je kawai babu wata matsala.
Juya kan dawakan nasu suka yi, a guje suka bar wajen suka nufi hanyar da suka fito.
Sun ɗan yi gudu mai nisan kafin su zagayo ta kasan dutsen, wajen ruwan kenan, dan su duba ko za su iya ganin wannan matar.
Duk da idanunsu ya gane masu faɗawarta kasar tekun, ba gaya masu aka yi ba, gani suka yi, amma basu yarda da cewa ruwa ya tafi da ita ko makamancin haka ba, shi ne yasa suka zagayo dubawa.
Warriors (Mayaƙa) guda biyu ne suka sauƙa daga saman dawakansu, suka nufi bakin ruwan dan su duba da kyau da kyau.
Kash ko alamar wannan mata babu a wajen, da alama ruwa ya tafi da ita da gaske ne, ga kuma baiwar Allah tana nakuda, ga kifiya a cikinta, ya ilahi ya lalliahi.......😭
Juyawa ɗaya daga cikinsu ya yi ya dubi waƴan da suke akan dawakan.
"Da alama fa ruwa ya tafi da ita, ku muje kawai, domin ina da tabbacin ba zata taɓa rayuwa ba, ba'a taɓa wanda ya shiga cikin wannan ruwan ya fita da rai ba! Ko da kifiyar da muka harbeta da shi bai kasheta ba, mugayen dabbobin cikin ruwan nan za su hallakata!".
Ya yi maganar cike da nuna jarumta da izza, kalaman nasa akwai kaushi, kuma suna nuni da cewa ya jima a sadaukan yaki, domin kuwa babu tsoro ko ɗar ɗar a tattare da shi, ko ace da su bakiɗaya, babu wani shayi a maganarsa.
Ɗaya daga cikin waƴan da suke a kan dawakan ne ya girgiza kai yana faɗin
"No, ya zama dole mu nemota, mu fasa cikinta mu ciro abin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 75