har zuwa haraban gidan sai data ga fitarsu sannan ta dawo tana saisaita natsuwarta ,cike da natsuwa ta shiga dakinsa kai kace ba itace tantiriyar dake daukar darasin makirci ba , tana shiga ta hangosa zaune yana tunani alamar yana cikin damuwa, ta samu guri ta zauna kusa dashi tana dafa kafad'arsa yaki dagowa ya kalleta "dan Allah kayi hakuri komai zai wuce ,amman kana ganin idan aka tsananta bincike baza'a sake binciko abinda zai d'aga maka hankali ba ? ya d'ago ya kalleta da idanunshi da suka kada suka yi ja zuwa lokacin ,kwata kwata ya rasa abinda zai ce mata , ya mike tsaye yana kallon kanshi a madubin mirrow "komai zai faru sai dai ya faru amman sai an nemo wanda ke da saka hannu acikin lamarin nan, bai juyo ya kalleta ba duk da tana tsaye a bayansa gabad'aya tsoronta ya sake fito filli tasan halinsa maye ne akan abinda yasa gaba tunda ya nace akan sai an binciko wanda ke da saka hannu tabbas tasan za'a nemo ya ja tsaki yana barin gurin ya karasa wordrobe dinsa yana sauke wani wahalallen numfashi, jallabiya ya dauko baki ya saka ya dawo ya raba ta gefenta ya hau kan gado ya kwanta ya runtse idanunsa gam haɗe da yin pillow da hannunwansa .
jikinta a matukar sanyaye ta matso kusa dashi tana kai hannunta kanshi ",bacci bayan la'asar ...? bana son damuwa ,Kwakwaluwata na bukatar hutu ya kawar da kansa gefe yana furzar da iska mai zafi ta mike tsam idanunta na kanshi kallon second biyu tayi masa sannan ta nufi kofar fita daga dakin, ya bude idanunshi yana binta da kallo tun daya shiga daki bai fito ba sai goshin magariba yayi alwala ya fita zuwa matsalaci bashi ya dawo gidan ba sai gurin tara ..
Da daddare suna zaune a daning table suhaima ta sha jini jikinta sosai saboda tsura mata idon da mah'ruf yayi yana Kallonta ta d'ago kai ta kalleshi gabanta na fad'uwa , daga ita har mah'ruf kallon juna suke bai yi kokarin sanyawa cikinsa komai ba ita kawai yake kallo ,itama babu wani abincin kirki da taci sai tsakura da take yi ,tana kallonsa ya dauki cup ya haɗa coffe take ta narke fuska " haba habibi gani zaune zaka hada coffe da kanka ni meye amfanina ? " karki damu ki cin abincinki kawai ,yana gama sha ya mike ya shige d'akinsa, ta biyosa duk jikinta a sanyaye hankalinta a matukar tashe kwanciya tayi a bayansa zuciyar cike da matsanamcin tsoro ,shima baya ya juya mata yayi shiru yana tunani gabad'aya bacci ya kauracewa idanunsu, tunaninta duk ya kare akan son sanin abinda ya sauya shi , tasan dai yana cikin damuwar abinda ya faru amman ko da safe ai lafiya suka rabu kuma tasan daya ji tautaunawarsu da y'an'uwanta ba zai boye ba, dole zai yi magana washegari ya tashi da wuri ya shirya ya bar gidan ya bar zuciyarta da wasiwasi .
Qarfe goma da minti goma sha biyar ummita ta farka bakinta ɗauke da salati ta tashi zaune tana kallon dakin motsinta ya tadda shi ya tashi yana gyara mata sumar kanta daya baje kallonsa tayi da mamaki a saman fuskarta shima kallonta yayi haɗe da sakar mata kasalalliyar murmushi ya shafa gefen fuskarta zuwa wuyanta sannan ya matsota sosai yana busa mata iskan bakinsa "ya karfin jikin ?
Lumshe idanunta tayi cikin sanyayyiyar muryarta tace "Better tana ƙoƙarin ja da baya, lumshe idanuwansa yayi tare da jinjina kai ya sake matsowa zuwa inda take ya daura kanshi a saman cinyoyinta mamakinsa yasa ta kasa magana
"lokaci zuwa lokaci yake rikidewa yana canzawa ,ta rasa dalilin canzawarsa ko dai ya gano gaskiya bata aikata laifin da yake zarginta bane ?
"Allah kasa gaskiya ta bayyana bata gama dogon tunaninta ba taji ya riko hannunta cikin nashi yana kallon zara zaran yatsun hannunta kafin daga baya ya fara shafawa a hankali take tsigar jikinta suka mike yrrrrrrrrr , ta tsura masa idanunta tana kallonsa ya buɗe bakinsa ya zira fingers dinta cikin bakinsa ya hau tsotsa yana shafo gashinta, kusan minti goma ya ɗauka yana tsotsar fingers dinta sannan ya maida hannunsa yana shafo cikinta dake lafe yana kallonta cikin wani irin yanayi na galabaita ya bude bakinsa da kyar "nayi kuskure *QAUNA* daga yanzu ba zaki sake fuskantar wata matsala a tare dani ba ,kimin uzuri ,ba kowani mutun zai ga abinda na gani ya iya kawar da zuciyarsa ba, dole ne a matsayina na mijinki naji babu dadi araina wallahi ina da tsananin kishi akanki ke kanki da zan yi shiru akan matsalar batare da na nuna fushina ba zaki ji babu dadi ,zaki ɗauka baki da matsayi a zuciyata ne zama ki iya tunanin ko bana sonki ....
"Ina sonki Ina son abinda zaki haifa min i love you with all my heart
Zare hannunsa tayi cikin nata tana fesar da iska ta d'ago kanta a hankali suka hada ido ya kashe mata idonsa daya ya tashi ya kai hannusa kan kafafunta yana mammatsa mata
yana faɗa mata kalamai masu sanyi ...
"Ya sallama baba ba dai har yanzu kana gidan nan ba , maza ka tashi ka wuce aiki ,"babu inda zani mama ki barni haka zuciyata na cike da matsanamcin tsoro da firgici ya fadi haka yana ɗauke hannunsa daga kan kafafunta sai lokacin ta sauke wadataccen numfashi "ni dai ka tashi ka wuce gida, ka wani zauna kamar wani bawanta "barni kawai mama ai sai mace ta cika mace sannan namiji zai zama bawanta ko karya ne qauna ?tayi shiru tana dan ciza lip's dinta ya kamo hannuta cikin nashi ya tsarke yana shafawa "ni dai kaji abinda nace maka ka tashi ka tafi aiki ta faɗa a daidai lokacin da ummita ta zare hannunta ta sauko daga kan gado ta shiga bayi mama ta biyo bayanta, ya zauna shiru yana tunanin .
Ruwan zafi mama ta haɗa mata ta zaunar daita runtse idanunta tayi saboda zafin daya ratsata sai data tabbatar ruwan zafin ya shigeta sosai sannan ta bata umarnin tashi ta sake hada mata wani ruwan zafi tayi wanka "mama ......
Ummita ta kira sunanta "ya'akayi mamana ?" jini ya tsaya fa tun jiya ,mama tayi shiru taki cewa komai dan kusan tafi su jin zafin fitar cikin ,ummita ta fito daure da towel a tunaninta mah'ruf ya tafi sai ganinshi tayi zaune ya mike ya tarota ya rungumota jikinsa yana mata sannu ta matsa baya da sauri saboda jin motsin fitowar mama ,mama ta wucesu tana cewa "sai ka haɗa mata tea tunda bazaka wuce ba , tana fita ya d'auketa ya maidata kan gado bayan ya dauko mata kaya ta canza ya fita ya hado mata tea mai kauri da zafi ya dawo dakin yana shigowa ya k'araso inda take kwance ya dagota da kyar ta yarda ya bata ta sha tana hararasa "karki damu duk zan wanke laifina ta hanyar dawowa bawanki , rabin cup ta sha ta kawar da bakinta , ya janyo laidar magungunanta ya bude ya ciro ya balla ya bata ta sha kwanciya tayi shima ya kwanta ya janyota jikinshi ta tashi da sauri ta zauna tana dubansa tana yatsina fuska "ka tashi ka tafi aiki mana tayi maganar cike da shagwa'ba .
ya kai hannusa ya janyota ya mannata a qirjinshi yana kyakwayon maganarta "karki damu kasancewata dake yafi zuwana aikin mahimmanci ,ya soma ƙoƙarin lullu'besu "muyi bacci qauna "nifa ba bacci zanyi ba na gaji da bacci "to mu kwanta muji dumin juna "gaskiya a'a ban yarda ba ka tashi ka wuce kawai "ba zani ba ko dole sai na tafi aiki ?jikin ummita a sanyaye ta sauko zuciyarta na bugawa da karfi ya fizgota ya matseta gam ajikinsa ya kai bakinsa cikin kunneta "banason abinda kike min ,ya buɗe bakinsa da niyyar sake magana aka bude kofar dakin atare suka kallo kofar d'akin aunty ce tsaye "inna lillahi baba meye haka ?ya lumshe mata idanunshi ke kuma shine kika wani manne masa yar dadi son miji shi yasa nan da nan kin ɗauki ciki maza tashi ka fita "haba aunty kinsan fa bama haka dake "mu fara daga yau amman wallahi sai ka tashi ka fita , dole ya sauko ba dan ya so ba sai dan aunty ta rantae , tasa keyarsa tayi gaba har sai daya ya fita ya bar gidan
Daren ranar daga mama har Hajiya umma babu wacce ta runtsa suna zaune suna kaiwa Allah kukansu , hatta Abba shima ba'a barshi a baya ba yana tsaye akan daddumar sallah bayan ya idar ya d'aga hannunwansa sama "ya Allah ka karemin yarana ka tsare minsu ,ya Allah kada kasa wani mugun ya cutar min dasu Allah kaga halin da diyata subai'a take ciki Allah kafimu sanin komai , Allah ka gaugauta bayyana gaskiya Allah ka bawa mahaifiyata lafiya da sauran marasa lafiya waɗan da suka rigamu gidan gaskiya Allah ka jikansu ya shafa ya cigaba da lazimi .....
******
Bincike ake sosai sai dai har lokacin babu wani cigaba da'aka samu ta bangaren wanda yake da sa hannu , mah'ruf da mahaifin hafiz da kanin mahaifinsa zaune a office din dpo ,shiru suna kallon hafiz wanda zuwa lokacin kumburin idanunshi ya sabe yana iya gane kowa ,hakuri kanin mahaifin hafiz yake bawa mah'ruf "yaro kayi hakuri mun san d'anmu yayi ganganci da kuskure shiga gidanka , ina tabbatar maka a halin yanzu daya yasan inda matar data sashi wannan danyen aiki daya dade da bayyanata shi kansa ya huta ,ta bangaremu muma muna kokarin muga an kama ko wacece dan tayi amfani da girman son da yakewa yarinyar ne tayi amfani dashi ,dan Allah kayi hakuri bama son maganar ta je kotu ka taimaka shi kadai Allah ya bamu ....
mahruf ya sauke numfashi yana furzar da iska mai zafi sannan ya ciro wayarsa daga gaban aljihunsa ya shiga gallary dinsa ya dubo wani hoto ya mikawa hafiz wayar hannun hafiz na rawa ya amsa yana dubawa "wannan matar ce tasaka aiki ?shiru hafiz yayi yana kallon hoton kwakwaluwarsa na caji gurin tunani "ba ita bace amman tabbas suna matukar kama da matar data sakashi aiki yayi magana a zuciyarsa "kayi shiru mahruf yayi magana a tsanake "itace wacce ta sakaki aikin ya sake tambayarsa a karo na biyu ? girgiza kansa yayi ,cike da matsanancin faduwar gaba ya shiga motsa bakinsa yana son yin magana akan cewar suna kama da matar amman ya kasa lankwasa harshensa, kawai sai hawaye sharrrrrrr suka shiga gangaro masa ,wanda take mahaifinsa ya shiga goge nashi hawaye idanunshi na kan tilon dansa , tausayin mahaifin hafiz ya kama mahruf sai dai duk da haka bazai daga kafa ba .
ya dubi hafiz sosai sannan ya kalli dpo "a cigaba da rike shi har sanda zai dawo hankalinsa ya gane waɗan da suka sakashi aikin yana gama fadar haka ya mike ya kama gabansa yana mamakin abinda yasa hafiz ya kasa fadar gaskiya , mahaifin hafiz ya shiga tashin hankali matuka ya dinga turowa mah'ruf manya mutane dabam dabam domin bashi hakuri a kashe case din ,shi kuwa mah'ruf ya rantse sai hafiz yayi magana da bakinsa ,yayinda harshen hafiz ya rikice duk sanda za'a zo akan maganar sai kuka da karyar da kai gabadaya an rasa gane kansa har police suka fara tunanin ko ya samu tabin hankali ne batare da bata lokaci ba aka nufi asibiti dashi iya bincike anyi sai dai likitoci sun tabbatar da lafiyar kwakwaluwarsa lau , cikin kwanaki sam mah'ruf bai samu zama ba gida da office ,kullum yana gurin ma'aikata gabadaya suhaima ta rasa gane kanshi yana tsaye a dakinsa yana duba wasu mahiman bayanai ta shigo sad'af sad'af bai ji motsin shigowarta ba sai tsayuwarta a bayansa yaji da hucin numfashinta , ya ɗan juyo ya kalleta ya ɗauke kanshi ya cigaba da duba file din hannunsa "habibi ta kira sunansa a raunane , ya juyo gabad'aya yana fuskantartata batare daya amsa ba ,sai dai ta fahimci ita yake sauraro ",gaba-daya ka canza habibi tunda ummita ta bar gidan na rasa fahimtarka ka kaurace min a shimfida ka daina cin abincina ka daina duk wata muamula dani ka taimakawa zuciyar dake tsananin sonka , ina tsananin sonka da bukatar kulawarka ..
"nasan kina sona kuma zaki iya yin komai akaina ko ba haka ba ? yayi maganar yana ajiye file din hannunsa ya dauki wani "haka ne zan iya yin komai akanka kamar yadda nasan kai ma zaka iya komai akaina jin abinda ta faɗa yasa ya zauna yana ci-gaba da aikinsa , ta zauna kusa dashi "ina ji ajikina kamar nayi maka laifi ya juyo inda take zaune tare da tsura mata idanunshi sai da yayi second biyu sannan yace "idan kin min laifi zan fada miki idan kuma har jikinki na baki kin min laifi a tafi haka ya karasa maganar yana furzar da iska mai zafi a fuskarta haɗe da mikewa tsaye ,itama ta mike da sauri ta tsaya gabansa "ya tabbata dai nayi maka laifi dan Allah ka faɗa min abinda nayi maka dan gaba na kiyaye ? "matsa na wuce ina da abubuwan yi .......
idanunta ta lumshe batare da ta sake furta masa komai ba ta matsa gefe guda tana kallonsa zuciyarta cike da mamaki a natse ya wuce ta gefenta yana rabe jikinsa dan baya son abinda zai sake haɗa gangar jikinsu, shiru tayi kafin daga baya ta fito cikin sauri ta nufi d'akinta ta kira number hajiya rahma tana ɗauka ta fashe mata da kuka tana koro mata yadda sukayi da mah'ruf "kina da matsala wallahi mutun bai fito ya nuna miki komai ba ke meye naki na damuwa? "ina da tabbacin da yasan shirinmu da tuni ya fahimtar damu ki kwantar da hankalinki yanzu haka ana aikin ne akan hafiz dan na samu labarin an kama shi yana hannu ma'aikata sai dai ina tabbatar miki babu abinda zai faru karshe akai maganar kotu, rashin kwararan hujoji da sheidu zai sa case din ya mutu murus kinga munyi win gobe ya sake biyewa soyayya, ke kuma yadda bai faɗa miki komai ba ki rabu da dan iska ki share shege ki cigaba da rayuwarki ko zaki kashe kanki akansa ne kiyi mana hasara ? bari na faɗa da hauka ake maganin hauka sharesa tunda shi asiri bai aiki ajikinsa kissa ma ko anyi masa bai san ayi ba move up ur life joooo nan Hajiya rahma tashiga kwantar mata da hankali har ta dawo daidai suka cigaba da tautaubawa ..
tun daga nesa mah'ruf ya hango daya daga cikin police din dake case din hafiz gurin mai gadin gidansa a hankali yake takowa inda suke zaune daga yake yana iya jiyo sautin police yana magana da mai gadi "malam kamilu oga Umar ya kira sunansa "naam ranka ya dade barka da yamma ? "ya kake malam kamilu ya aiki? " lafiya ranka ya dade "sunana s p Umar kamar yadda kagani a rubuce nazo domin tautauna wani abu mai mahimmanci ne da kai "inshallahu baka da matsala dani muddin nasani zan fadi gaskiya ," ko zan iya sani dalilin da yasa kake barin mutane dabam dabam suke shigo gidan nan ? tambayar ta daure masa kai cike da mamaki yace "mutane dabam dabam ranka ya dade gaskiya babu mutanen dake shigo wala mace wala namiji idan har kuma suna shigowa sai dai idan shigo dasu ake "wa kake tunani yake shigo dasu ?"eh to akwai wata mota dake zuwa gidan nan yayyar matar mai gidan ce
amman asanina babu masu shigowa barin ma wancan bangaren babu masu zuwa gurinta ya nuna part din ummita "kuma babu mai aikenka siyan wani abu acikin matan gidan ? "gaskiya babu wacce ta taɓa aikena tunda tazo gidan nan aikina iya get ne kuma bana wuce haka "shinkena na gode ya mike a daidai lokacin da mah'ruf ya karaso ya mikawa oga umar hannu suka fita zuwa wajen gidan suna magana kasa kasa har suka isa gaban motarsa oga umar suka shiga tare suka bar unguwar daga station Kai tsaye massalaci ya nufa bayan sallar isha'i ya shiga part din mama domin ganin abar kaunarsa ya murd'a kofar d'akinta yajita a kulle gam ya kwankwasa , daga cikin daki tace waye ..?"ki bude Ni ne "me zan maka dan Allah bana son damuwa ta faɗa tana gyara kwancinyarta shiru yayi yana kallon kofar ya lura duk zuwan da yake bata wani sakewa dashi , shima ya saki ranshi me yasa bazata sauko ba su cigaba da rayuwarsu ?
Mama na zaune a gefen abba yana cin abinci a parlou'nsa yayinda bangare guda yana sauraronta cikin gamsuwa da irin binciken da'ake yi "bazan yarda ummita ta koma gidan baba ba sai an gama bincike an gano gaskiya shine nake bukatar ka bani goyon baya duk da shi kansa baba bai nuna damuwarsa akan ta koma ba "wannan shawara ce mai kyau dan nima abinda yake raina kenan sallamar da yayi ta dakatar dasu a tare suka maida idanunsu akanshi cike da girmamawa ya karaso ya zauna agabansu ya lankwashe kafafunsa Abba yace ",ya akayi babana da magana ne ? "Abba ina tunani jibi zanyi tafiya zuwa Cross river Ina da meeting zuwa wenesday zan dawo nasan lokacin yansanda sun gama bincike zan so ayi komai ina nan "Masha Allah Allah yayi rayuwa albarka kular gabansa ya tura masa "kaci abinci duk ka rame da alamun baka cin abinci " kar ya soma ci idan yaci yayi yaya dana matarsa? mah'ruf bai d'ago ya kalli mama ba ya soma cin abinci "ban fa yarda kaci ba sai lokacin ya d'ago ya kalleta yana karyar da kai "rabu daita kaji yarona kaci daga abincin da abbanka yaci ya rage "ni dai babu ruwana idan yaci kasan yadda zai dana matarsa "dan Allah mama ki daina fadar haka sai naga kamar kina fushi dani ne .. ....
sai gurin goma ya koma gida a kwance ya tarar daita tana kallo sallamarsa tasanyata mikewa da sauri ta mike ya wuceta ya shige daki yana shiga ya soma haɗa kayansa a karamar jakar matafiya ta shigo tana kallonsa ",me kake yi haka habibi?" ina zaka kake shirya kaya ?"tafiya zanyi ko akwai damuwa ne ?"tafiya zakayi shine bazaka faɗa min ba sai kawai naga kana hada kaya ?" haka abun yazo , ta kai hannu zata tayashi ya dakarta daita yana cigaba da shirinsa ya gama ya zuge zip yayi kwancinyarsa "na kawo maka abinci ?"no ya faɗa atakaice ta juya jikin a sanyaye ta shiga jan kafa tana tunanin abinda tayi masa washegari jirgin karfe shida yabi zuwa Cross rive yayinda suhaima ta tashi tun bakwai ta haɗa masa break duk da tasan ba zai ci ba sai dai tana murda handle din kofarsa taji gam a kulle ta juyo zuwa d'akinta can tayi tunanin zuwa gurin Hajiya rahma ta faɗa wanka ta Sharya cikin riga da siket ta nufi gidan Hajiya rahma hankalinta ya tashe da gani suhaima a daidai lokacin ta karaso gurinta "lafiya nagaki adaidai wannan lokacin ..?
"Lafiyar nan dai da sauki gabadaya komai ya kwa'be min mah'ruf ya canza min gashi na rasa dalili yanzu ma tafiya yayi kika gani ", wannan miji naki akwai dan tusa gashi aiki baya cin irinsu bare ace asan abun yi "mu ajiye maganarsa mai sauki ne , ya ake ciki da wacan matar tasa ya sake ko kuwa suna tare har yanzu ? "Suna tare wallahi ni abun ma ya fara damuna ya isheni "matsalarki Kenan ke komai sai an koya miki kamar ba mace ba , zaman me kike yi kije gidansu ki daga mata hankali ta yadda da kanta zata bukaci saki daga hannunsa, kina nan zaune sake da baki yana zuwa yana rage zafi daita "uhm maganarki gsky yayarmu matsalata kenan ummita muddin tana duniya bani ba farinciki ," bari naje gidan yanzu ta mike ta nufi gidansu taci Sa'ar mama bana part din tana bangaren Hajiya inna bata abinci da magani ,kai tsaye ta nufi dakin ummita tana zaune ganin suhaima akanta yasa tayi wata irin zabura ta mike,"meye haka zaki shigowa mutane daki babu sallama kamar wata arniya ?
wata mahaukaciya dariya ta tayi tana nuna ta " ki ajiyeni a ko'ina kike so zan zauna muddin zan ga rayuwarki cikin kunci ,zaman gidan dole ina tabbatar miki sai dai ki tabbata a wannan daki ba dai a gidan mahruf ba "sannu mayya diyar mayu mai mugun hali ta Allah ba taki ba kina tunanin duk abinda kike ban sani ba ? "nasani na san komai da kike yi akan cikina sai da sannu Allah zai min magani ..
"Abinda kika sani ne zan sake tuna miki yanzu ni suhaima nice nan na turoki daga sama bene kika gangaro kika kifa saman cikin na farko kikayi nagudar dole saboda tsananin kiyayyar da nake miki "nasani sai dai meye ribaki a yanzu ? baki ma ji kunya ba har kina iya faɗa da bakinki saboda jahilci wallahi kina cikin bala'i da fushin Ubangiji ina tausayawa rayuwarki saboda karshenki bazai kyau ba ,ina guje miki tsincetsince a bola kafin mutuwarki ........
"Enough kice zaki yi tsince tsince a bola bani ba kuma nice nan da kaina zan tabbatar da haka tabbas zan baki mamaki ina tsaye akanki da kuma taimakon yan'uwana, ummita tayi shiru tana dubanta cike da mamaki "oh kina mamaki ne ? "Ki daina mamaki saboda yanzu aka soma wasan dan banyi komai ba tukun tunda har yanzu ban haukataki ba ban rabaki da gidan mah'ruf ba , ina faɗa miki ne saboda babu abinda zaki iya yi, kuma muddin baki fita rayuwar mijina ba rayuwarki zata dawo abar tausayi na dade ina faɗa miki ki bar rayuwar mahruf na baki dama kin kasa fahimta, ki saurareni da kyau idan zaki yi dauki cikinsa sau dari ni nan suhaima zan zubar dashi sau dari kuma na zauna lafiya idan kin gwamaci karasa rayuwarki cikin kunci da bala'in rayuwa ki cigaba da rayuwa da abinda nafi so a duniya , Ina boye miki ko wacece ni sai naga boyewar bashi da wani amfani gara kisan ko ni din wacece ki san cewa gaba da gabanta ba'a kishi da irinmu kishi da zuriyarmu tashin hankali ne maseefa ce duk abinda zan miki babu wani mahaluki a duniya da zai sani ko zai yarda ,gani damana ne na bari mutane su sani sannan ganin damana ne na rufe musu baki ruf su gagara sanin ta karasa maganar tana rufe hannuta guri daya...
" wani irin kallo ummita ke mata mai tattare da tsananin tsoro da firgici mutun kamar aljana "kina son cigaba da sanin abubuwa akaina ? Tayi mata tambayar tana zagayeta hatta ciwon hajiya inna nice nan silar komai duk da mahaifiyarki na so ta dawo abar tausayi ba wannan rikitacciyar tsohuwar mai bala'in tsiya ba ,kina son sani wani abu bayan shi ?tayi mata tambayar tana dariyar mugunta "ina da abubuwa da zanyi na ruguza rayuwarki da rayuwar mahaifiyarki take jikin ummita ya kama rawa jin ta ambaci mahaifiyarta, zan iya komai kuma a lokacin dana so dan haka kiyi hanzarin fita rayuwata da mijina duniyata , kema sautsayi ne aurenki, dan dani mah'ruf ya fara aure da duk runtsi da maseefa da jaraba ta iyayenku basu isa su aura masa ke ba , akan mah'ruf zan iya dauka ran kowa ina da kwakwaluwar shirya komai koda babu wata a kasa ki gaugauta fita rayuwarsa idan ba haka ba zan kashe mahaifiyarki a banza kuma akan idanunki .......
Tass kake ji ummita ta dauketa da wani gigitaccen mari,"kika mareni ta faɗa a gigice ? "an mareki ta d'aga hannu zata rama ummita tayi saurin rike mata tana kallon tsakiyar idanunta kafin daga ba ta saki hannun da karfi ta soma magana a fusace "suhaima ki tsaya iya kaina dan mahaifiyata tafi karfinki , dan da adduarta kika kasa cin galaba akanmu idan kika sake wani furuci akan mahaifiyata zan kasheki kafin ki kasheni ke ko ciwon kai tayi wallahi zaki sha mamakin yadda zanyi da rayuwarki zan so ki sausautawa zuciyarki ki daina wannan haukan banza dan zuciyar mah'ruf tawace mah'ruf baya sonki kin dai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 73 Chapter of 76