kallo sannan ya rungumeta tsam ajikinsa yana kissing din goshinta "kinyi kyau sosai You are so beautiful qauna "kaima kana da kyau sosai dan har kafini ta kamo habbarsa ta manna masa kiss a goshi , ta juya ta kara gyara gadon tare da goge inda suka bata ta feshe dakin da turare sannan ta dawo gurinsa zanje na daura abinci ya kai hannunsa kugunta zuciyarsa na tariyo masa rayuwarsu sam baya gajiya daita gashi itama tana hakuri dashi bata masa rowar kanta sai dai idan bai zo ba ko bata da lafiya.
"muje na tayaki ya soma tafiya daita "ka zauna ka huta ko kayi bacci ka samu natsuwa banason ka wahala "nima banason ki wahala muje sun dauki minti goma tana fama dashi amman yaki tare suka shiga kitchen "da me zan fara ? tayi murmushin ta dauko masa wuka da doya ka bere ka sai dafa kai kuma ka soya tayi mgnr tana shafa fuskarsa .
"an gama qauna ya matso kusa daita ya manne mata ta dauki karamar tukunya "aiki kace zakayi ba soyayya ba, ta karasa ta tari ruwa a tap ta kunna gas ta daura tana kallonsa "duka zanyi a lokaci daya idan kuma aiki kawai zanyi na fasa "ta mika masa hannu tana haɗe rai "kawo nayi aikina" kiyi dariya tukun sai nayi tayi masa dariyar yake ,yayi shiru yana cizan lip's d'insa Yana girgiza mata kai alamun bai yarda ba ,tayi murmushin data san yafi so ya dage mata girasa ɗaya "haka kake so ya kashe mata ido sai daya, sanyata yayi a jikinsa sannan ya iya bare doyar , yana barewa yana kising din wuyanta tare suka haɗa breakfast cike da tsantsar kulawa da juna ,suna zaune a dinning table byn sun gama break fast "kinsan duk duniya babu abinda ke faranta min rai kamar kallonki, idan ina kallon sai naji kamar kar na daina, kallonki kadai na kosar dani "kamar gaske kai da idan ka kama mutun kamar ka samu inji ......
Ya kai hannu zai kai mata cafka ta kwasa a guje ya biyota suka fara zagaye parlou'n daga karshe ta gaji ta zube akan kujera ya kwanto jikinta ya soma yawo da hannunsa ajikina yana mata kwakulkuli "wa na kama ?"kayi hakuri bazan sake faɗa ba ,yana mata kwakulkuli tana bankaro masa kirji nan fa ya zarce da shafa brest d'inta wayarta ce tayi ƙara ya share ya cigaba da saffarata nan take tayi lakwas tana amsar sakonsa haɗe da shafa qirjinshi jin karar yaki karewa yasa tace nurul qalab ana kira a waya ya mike haɗe da rungumeta ya janyo wayar dake center table , yana sawa a hands free saboda ganin sunan menal sallama akayi Assalamu alaikum sai data saisaita muryarta sannan ta amsa "wa'alaiki salam yaruwa ya kike ko kin haihu ne? "menal tayi dariya abinda na kira na faɗa miki kenan "dan Allah ?ummita ta faɗa cike da murna "wallahi tun da asuba nayita kiranki a waya ban samu ba na faɗa miki kinyi d'a ,wani irin tsalle tayi ta makale ajikin mah'ruf tana murna "yeeeeeeeee nayi da ......
TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*AUNTY RAHMA ABBA KYARI*
MY YOUTUBE CHANNEL
*HAUSA BAKWAI*
WATTPAD @HAUESH
Bismillahirrahmanirrahim
PAGE 65
.....Katse kiran yayi yasa hannuwansa duka ya zagaye bayanta dashi yana kai bakinsa cikin kunnenta "ko ke kika haifi babyn iyakar murna da zakiyi kenan " ta sake fad'ad'a fuskarta da murmushi "wannan ma nawa ne halak malak dan ɗan menal d'ana ne, haka nima d'ana ɗan menal ne babu wani bambanci , bari nazo na soma shirin zuwa ganin babynah shima baby yaga mamansa ta faɗa tana sake zubewa a jikinshi ....
"karki zake dayawa fa ita da shan wahalar haifo d'a ke da zakewa , ki bari ki haifo naki da kanki tukuna ya haɗe fuskarsu guri daya yana shaƙar numfashinta " kinsan ranar da kika haifa min baby ya zan dawo ? ta girgiza masa kai tana shakar numfashinsa " ni ne zan dawo mai jegon bake ba ,dan zan tare a gindinki bazan bari a dinga jagwalgwala min baby ba duk wanda zai ga baby daga nesa "aiki fa ? " daga ranar na ajiye har sai na sake sabon ajiya ... ...
Wani matsanancin kunya ce ta ka mata ta sake shigewa jikinsa sosai tana cusa fuskarta a qirjinsa "bari na shirya ka kaini yanzu banason a rigani zuwa ganin baby azo ana min gori , murmushin nan nashi mai narkar da zuciya yayi wanda ya sake bayyana kyawunsa sannan ya ja numfashi kaɗan yace "ba dai yau ba ya fad'i yana zareta a jikinsa ya mike ya nufi fridge yana murmushi , ta bi bayansa da kallo zuciyarta na bugawa da matsanancin karfi, hankalinta yayi maseefar tashi ta runtse idanunta " ba dai yau ba ta sake maimatawa , kar fa ya hanani zuwa ya janyo min fushin menal ,ai kuwa wallahi da ya cuceni muddin ya hanani zuwa ganin baby yau tayi maganar a kasan ranta .
dawowa yayi inda take zaune qirjinta na dokawa hannunsa rike da glass cup da kwalin hollandia mai sanyi, ya zauna kusa daita yana fuskantartata sannan ya tsiyaya hollandia a cikin cup ya mika mata " maman baby sha kiji sanyi ko , tayi murmushin karfin hali tana girgiza masa kai alamun bata sha ,ya zuba mata kwayar idanunshi yana kallonta still hannunsa na mika mata cup , kasa hakuri tayi cikin sanyayyiyar muryarta tace "nurul qalab .......
"Yes qauna ya'akayi ? ya amsa yana kai cup bakinsa ya kurbi kaɗan sannan ya maida idanunshi kanta yana mai tsura mata idanunshi ,cikin natsuwa ta motsa labbanta jikinta a sanyaye "da gaske bazaka kai ni naga menal da baby ba yau ? ya d'age mata girasa ɗaya alamun "eh yana riko laulausan tafin hannunta cikin nashi ya soma murzawa "dan Allah karka min haka kasan yadda muke da menal bai dace wasu su rigani zuwa ba, ta karasa maganar tana zumburo masa baki ya sake tsareta da ido "bafa zakije ko'ina yau ba alhalin ina gida kunyi waya yanzu , anjima sai ki kirata kiji yadda take .
ta marairaice fuskar idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye "
me kake son nayi maka ka kai ni yau ?
" ka faɗa min duk abinda kake so wallahi zanyi maka "koda kuwa kwana zanyi ina having sex dake ?yayi mata tambayar cike da zolaya yana kallonta yaji abinda zata ce ,ta damke hannunsa dake cikin nata tana kad'a masa kai"ka kaini idan mun dawo kayi duk yadda kake so dani na yarda ...
Har kwanciya yayi saboda dariyar mugunta , ta 'bata rai "wallahi ka fiye mugunta ,dan mugunta yasa zaka hanani zuwa dan baka dalilin da zaka hanani zuwa , sai da yayi dariya mai isar sa sannan yace "babu inda zaki sai monday idan zan wuce office na ajiyeki tasan halinsa tunda ya nace bazata ba to bazai kaita ba sai lokacin dayaga dama fuuuuuu ta mike a fusace ta barshi zaune yana dariya ..........
juyowa yayi yaga wayam babu ita babu alamunta agurin ,yayi shiru yana dauke wuta mikewa yayi a hankali ya fita ,bayan kamar awa daya ya dawo hannunsa rike da fararen ledodi guda biyu ya fara shiga part din suhaima ya bata nata sannan ya dawo bangaren ummita lokacin tana zaune a parlou'n ta cika bam tana fidda numfashi da kyar ,jira kawai take ya tabata ta sauke masa , ko kallon inda yake bata yi ba ta maida hankalinta kan tv ya ajiye ledar batare da yace mata komai ba, ya shiga kitchen ya d'auko plet da cup ya dawo ya zauna kusa daita yana satar kallonta ya buɗe ledar daya shigo daita ya fito da farfesun kaza wanda akayi raping d'insa , ya da'ura akan plet "bisimilla madam ki sa hannu muci idan kuma abaki kike so na baki ki bude , a fusace tace "na koshi bana ci ..
"Uhmmmmmmm qauna kar muyi haka dake fa ki matso tun kafin raina ya ɓaci "idan ya ɓaci sai ka wanke da omo da hypo , zaro idanunshi yayi yana Kallonta cike da tsantsar mamaki "kenan ta rama abinda ya taba mata ," ya rabbi ya furta a zuciyarsa , ta mike a fusace ta shige kitchen ta soma ƙoƙarin daura girkin dare ya shigo ya kalleta tana tsaye gaban belender tana nika ,ya sha mur "ke.......... juyo ki fuskanceni da kyau , qirjinta ya buga da karfi , sai dai ta dake taki juyowa tayi masa banza ta cigaba da aikin da take, ganin tana bata masa lokaci yasa hannunsa ya fincikota daga inda take tsaye zuwa faffad'an qirjinshi idanunsu suka tsarke cikin juna take zuciyayoinsu yayi mummunar bugawa a tare ,saurin fizge jikinta tayi daga nashi cike da jin haushinsa "wai meye ne ? "nace bana ci ko dole sai naci " kina hauka ne ni kike d'agawa murya ?
Ta kalleshi a wulakance "daga gidan mahaukata aka kwantoni , yasa hannun zai fizgota ta ingijeshi "karka ta'bani banaso matsala dan Allah , ta bi gefensa ta shige d'akinta, ransa yayi mugun ɓaci ya biyota da sauri yana kiran sunanta "subai'a ! subai'a!! tayi masa banza ya kara sauri ya rikota yana daka mata tsawa cikin awanin da basu wuce biyu ba ya dawo kamar wani zautacce "subai'a zan bata miki rai banason rainin hankali meye bambamcin yau da jibi ? "Wallahi akwai bambamci "koma menene karki tunzura zuciyata idan kika sa wasa zan hanaki zuwa ko'ina har ayi suna naga karyar wulakanci .
Muryarta na rawa tace " karabu dani kishinka baya karewa akan kowa sai akaina ga matarka nan kullum tana hanyar fita baka taɓa hanata ba sai ni da zani duba yar'uwata da duk duniya bani da kamar ta " ya zauna a bakin gado ya riko hannunta ta fixge ta shige bayi ta kulle tana kuka , jikin kofar ya karasa "na lura sai na nuna miki 'bacin raina sannan zaki fahimceni ...
tsayuwa yayi yana jiran fitowarta har kusan minti talatin taki fitowa ya fito yayi abinda zai yi ya sake fita, bai dawo gidan ba sai gurin tara na dare kai tsaye part din suhaima ya shiga tana kwance a parloun akan doguwar kujera tana chart da y'an'uwanta a wayarta gefe guda kuma zuciyarta cike take da tunani saboda sanar daita da hajiya rahma tayi ciwon kafar mahaifiyarsu ya tashi gobe zasu asibiti, a zuciyarta take tunanin dalilin wannan ciwon kafa abu kamar wasa ya fara da yatsa an yanke still ya cigaba da ciwo tana tausayawa mahaifiyarta bata son rasata a wannan lokacin.
sallamarsa ce ta dawo daita daga duniyar tunani da charting din da take da y'an'uwanta ,ta amsa masa sallama haɗe da mikewa zaune ta amshi ledar hannunsa tana dubawa kayan fruit ne ,haka halinsa yake da wuya ya fita ya shigo gida hannu haka duk runtsi duk wuya zai shigo da abu komai kankatarsa, ta saisaita muryarta sosai sannan tace "sannu da zuwa habibi "sannuki tunanin me kike yi haka ? tayi shiru tana dubansa sai daya sake kallonta tace "rashin lafiyar hajiyarmu ne wallahi yanzu yayyarmu take faɗa min gobe da sassafe zasu asibiti saboda ciwon kafar ya tashi ko bacci bata yi ga fitsarin jini ga ciwon baya ba "duk ita kaɗai ? ya tambaya yana canza channel .
"Wallahi ina matukar jin tsoro habibi banason rasata tayi maganar muryarta na rawa "Allah ya bata lafiya ya kawo sauki , haka ciwo yake lokaci daya zai kama mutun ,sauki kuma sai a hankali ga hajiya inna nan itama abu kamar wasa har yanzu kafarta ciwo take bata ko iya takawa kullum magani ake amman shiru abun nata kamar sammu ,tayi shiru tana tunanin itace fa silar ciwon hajiya inna , parlou'n yayi shiru bata sake cewa uffan ba haka shima da hankalinsa ya tafi ga ummita ,ko da wasa bata masa tayin abinci ba, dan tasa halinsa bai fiyye cin abinci dare ba sai dai yaci da yamma da daddare kuma ya sha fruit ko tea ya kwanta bare kuma ba itace dashi ba, suna kallo suna dan taɓa hira wanda hirar kusan duk na mahaifiyarta ne da halin zulaihat take ciki ,hirar abu daya ya soma gudurarsa dan ya tsani ayita hira akan magana daya, ya mike tsaye yana mata sallama ya wuce bangaren ummita da ledar fruit dinta .
kai tsaye d'akinta ya shiga bai ganta ba ya ajiye ledar hannunsa yana kallon d'anki ko'ina fes a gyare yana kamshi air freshener da turaren da take amfani dashi , jin saukar ruwa a toilet dinta ya fahimci wanka take ,murmushi yayi ya tura kofar yaci sa'ar a buɗe take ,tsaye ya ganta tana cuda jikinta da sabulu nano soap ruwa na sauka ajikinta, tsayawa yayi yana Kallonta batare da yayi kwakwaran motsi ba har sanda ta gama wanka tana kokarin ɗaukar towel ta ganshi tsaye kamar mashi idanunsa na yawo a sansar jikinta ganin zata dauki towel ya Kai hannunsa da sauri zai kamota wani kallo ta watsa masa haɗe da buge masa hannu tana daura towel ta fito ya biyo bayanta yana cafkota jikinsa tare da matseta gam a jikinsa ya daura kansa akan kafad'arta yana lasar wuyanta hannunsa na gyara sumar kanta tare da lumshe ido ,muryarta a raunane tace "banaso !banason abinda kake min "dole ki so tunda kina matsayin matata, dole nayi abinda naga dama dake yayi magana yana hadeta da qirjinsa .
ta sake zare jikinta zata wuce ya sake janyota jikinshi da karfi yana ƙoƙarin zare towel din dake daure a jikinta ta kamkame towel "wallahi banaso ka barni ,banza yayi mata yayi kasa da hannunta ya sake matseta gam , towel din jikinta ya zame kirjinta ya bayyana sosai a hankali ya kai hannunsa qirjinta ya soma zagaye kan nipples dinta da yatsan hannunsa yana lumshe ido ,ya kusan minti goma yana zagaye yatsansa akan nipples dinta haɗe da shafawa brest d'inta yana lumshe ido,takaicinsa yayi mata diran makiya ta tattara karfinta gabadaya ta fixge ta faɗa saman katifa tana kukan bakinciki hanata zuwa gurin menal da yayi ,ya biyota ya tsura mata ido sai data yi kuka mai isar batare daya bata hakuri ba .
ta mike ta dauki doguwar rigar data ciro kafin ta shiga wanka tana kokarin zirawa ajikinta ya k'araso ya rike rigar yana kallonta "kinsan bana son irin wannan shigar da daddare kou? ta fixge tana jan tsarki a ranta tace "ina ruwana , kai ma bazan maka yadda zaka ji dadi ba , yayi shiru zuciyarsa nayi masa zafi da kuna, dan yaji zafin tsakin data ja masa ,fixgota yayi da ita da rigar gabadaya ya rungumeta ta karfi tsiya yana kissing dinta "kinsan banason mutsu, banason tsaki ,banason taurin kai ,bare wannan kukan naki mai cin rai ya kwantar da murya " kiyi hakuri mana qauna bazan iya wasu a wani bana tare dake ba alhalin ina gida , "karka bani hakuri ,hakurin da zanyi bai wuce gobe ka d'aukeni ka kaini naga menal da baby ba ta faɗa hawaye na zubo mata ..
ya lumshe mata idanunshi yana daura hannunsa kan lip's d'inta ya shiga yawo dashi kafin daga baya ya haɗe bakinsu guri daya ya shiga kissing dinta , kin yarda tayi ya sha bakinta har sai da tayi kokarin kwace bakinta cikin nashi tana fidda numfashi ta duro daga gadon , ganin iskanci da wulakanci ne abun nata ya sauko bai tsaya wata wata ba ya d'auketa ya makata akan gado ya haɗe kirjinsa da nata yana sakar mata nauyinsa "dan kinga Ina binki an faɗa miki tsoroki nake ji ? bakinsa ya kai kan nipples dinta cike da mugunta ya soma tsotsa kan yana cizawa da karfi ,kokarin turesa ta dinga yi amman ina ta kasa dan jin kirjinsa tayi kamar dutse ,kuka ta fashe masa dashi tana fesar da numfashi da kyar tana turesa da hannunta duk inda ya taba sai ta buge tun tana matse jikinta har jikinta yazo ya mutu murus ta soma amsar sakoninsa masu birkita kwakwaluwa ,ranar dai sai da mah'ruf yayi yadda ya gadama daita ya dinga juyata son ranshi ,sai daya gaji dan kansa sannan ya barta ya juya mata baya .....
Kwana tay kuka zuciyarta ta dauki fushi mai tsanani dashi ,washegari tunda ta tashi tayi wanka ta canza kaya ta shiga kitchen ta Haɗa masa simple break fast ta dawo daki ta hayewarta gado ta kame , koda ya tashi ko kallon inda take bai yi ba, tana kallonsa yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya wando masu kyau , yana fita dining ya nufa yaga abinda ta dafa masa soyayyayen dankali da soyayyen kwai ,sai ruwan tea a flask ya ja tsaki ya shiga kitchen Kai tsaya yaki cin breakfast dinta , a ransa yace " bani za'a wulakanci ba, ya daura ruwan zafi ya dafa indomi daidai cikinsa ya ci ya dawo parlou'n ya zauna ya kunna tv , ta fito parlou tana rausaya tana ganinsa ta ɗauke kanta tana hura hanci ta nufi kitchen nan idanunta suka hango mata plet din abinci data hada masa a rufe alamun ba'a taɓa ba ta bude yadda ta ajiye haka yake ta waiga ta kalleshi ta k'arasa tsakiyar parlou'n ta tsaya nesa kaɗan dashi "ga break dinka fa "bana ci ya faɗa atakaice idanunshi na kallon tv juyawa tayi ta koma d'akinta zuciyarta na tafarfasa ta tsani tayi masa abu yaki ci tunda tashiga bata sake fitowa ba haka shima bai shiga dakin ba ...
sai gurin la'asar ya bar part dinta zuwa na suhaima kasancewar girkinta ne , bata sake ganinsa ba sai a safiyar monday ya kirata a waya kira uku yayi mata bata ɗauka ba sai a karo na hudu ta ɗauka tana magana da kyar kamar wata jinin sarauta "idan kin shirya ki fito mu wuce "ka tafi kawai zanje da kaina tunda dai ka barni , kit ya katse wayarsa yana jan tsaki ..
Tana jin ya katse kiran ta ɗauka ya fita ,dan haka ta fito da yar karamar akwatinta dan daman a shirye take ,sam hankalinta bai kai ga inda motarsa take ba ,ta fito tana tafiya a hankali har ta karasa bakin titi tana neman mai mashin , cikin kankanin lokaci ta samu tana kokarin hawa sai ga motar mahruf tun daga nesa ya hangota ya kara gudu yana hon amman mai mashin yaki tsayawa,ya kara gudu ya sha gaban mai mashin tana ganin motarsa gabanta ya buga da karfi ,tace "kai mai mashin muje ko kasanshi ne da zaka tsaya? tayi maganar a firgice dan tasan halinsa yana fitowa zata sha mari , mai mashin yace" a'a bansan shi ba ya bin gefen motar mahruf tun kafin ya fito ya kwasa a guje yabi wata karamar hanyar da mota bazata iya bi ba ...
ran mah'ruf yayi bala'in ɓaci ya shiga mota mai mashin na sauketa a kofar gidan ya kara gaba a daidai lokacin daya k'araso kofar gidan tana tafiya a Compand din gidan ya fito da sauri ya biyo bayanta sam ya manta da wata suhaima ,kai tsaye part din Hajiya umma ta nufa yana biye daita, yana shiga ya tarar da hajiya umma aunty har ma da mama suna zaune ummita na ganinsa tayi bayan hajiya ummah ta boye jikinta na rawa "menene kika shigo a firgice ? ganin mahruf a haukace tasan shi ne " ya nunata da yatsa "uban wa yace ki hau mashin ? Ta haɗe rai tana turo masa karamin bakinta "wai yarinyar saboda ta rainani akan idona ta hau mashin ,aunty tace "mashin gaskiya bata kyau ba amman kayi hakuri bazata sake ba "ba wannan ne karo na farko ba wallahi zan ballata idan ta sake min irin wannan gangancin yayi maganar yana huci kamar zaki , ummita najin haka ta nufi inda take jiyo sautin mutane , tana shiga dakin ta kulle kofar da key dan tasan halinsa bakaramin aikinsa ya biyota yaci ubanta a gabansu ba.
can parlou'n kuwa hakuri aunty da mama suke bashi , ita kuwa Hajiya umma ko kallonsa batayi ba har ya juya ya fita a zuciye "Yara kamar kaji basa rabo da tashin hankali ,duk bayan minti biyar suke faɗa can kaga sun shirya wallahi idan ka zauna dasu baka kamu da ciwon zuciyata ba ka auna arziki inji cewar aunty ,bayan fitarsa ,suhaima ta shigo da sallama ta durkusa har kasa ta gaishe su tayi musu barka sannan ta nufi dakin da menal take tana bugawa "daga cikin dakin aka tambaya da waye tace "nice suhaima ummita najin haka tayi wuf ta shige bayi ta kulle kanta dan bata qaunar ko haɗa ido daita , bata fito ba sai data tabbatar da ta bar dakin sannan ta fito nan suka shiga chapter da sauran mutane ban menal da tun shigowar ummita ta ɗauke wuta taki ce mata komai "ummita ta matso kusa daita "kiyiwa Allah kiyi hakuri wallahi ba laifina bane tunda akayi haihuwar nan nake son zuwa ,menal tace "wallahi nayi fushi wai ace sai yau kwana biyu da haihuwa "ke ki godewa Allah ma da kika gani a raye "me ya faru ? "Ke dai zamuyi maganar later ta sake d'aukar baby ta rungume ajikinta tana jin farinciki mara musaltuwa ,taji kamar itace ta haifosa kyawawa ,kyawun iyayensa ya ɗauko menal da abdulshakur ..
Suhaima tsaye tana yi musu sallama mama ta dubeta tace "da wuri haka suhaima na ɗauka sai yamma idan baba ya taso daga aiki ya daukeku ku wuce gida "ba gidan zan koma ba daga nan asibiti zani hajiyarmu tun jiya bata da lafiya tun safe tana asibiti ga zulaihat itama ba lafiya ta karye akafa "ayya Allah kara sauki yasa zakkan jiki ne duk suka mata Allah ya sawwake ta wuce "aunty tace ta ina zasuyi lafiya tunda basa zama guri daya, shiyasa kullum nake addu'a da sadaka akan umminta da baba Allah ya tsaresu daga sharrin su "ameen Allah ya kyauta ni fa idan kuna fadar wasu abubuwan sai inga kamar karya ake mata sam basu yi kama da mutane masu irin halin ba "ke raba kanki dasu kinga yadda uwarsu ta dawo abar tausayi amman har yanzu batasan abinda ta shuka take girba ba ,nan suka yita tautaunawa akan lamarin inda aunty ta sha alwashin muddin umminta ta sake rasa cikinta sai dai araba musu gida ko ya sawwake suhaimar kowa ya huta dan ta soma zargin akwai sanya hannunta cikin rasa cikin da ummita take ..
Kai tsaye suhaima asibitin ta nufa inda ta iske sabon tashin hankali dan kuwa an yanke kafar mahaifiyarta ,ta dawo mai dunguli tana kwance kamar matacciya ,sunyi kuka kamar ransu zai fita gabadaya abun duniya ya ishesu sai mahaifinsu ne ya dawo yana basu hakuri , jiki a sanyaye ta kira mah'ruf ta sanar masa abinda ya faru ya tayata jimami da fatan samun lafiya ga mahaifiyarta .
Misalin ƙarfe biyar na yammaci rana ya iso asibiti hankalinsa yayi matukar tashi da ganin halin da mahaifiyar suhaima take ciki ,duk ta fige ta rame tayi baki duk sauran kibar nan nata daya santa dashi babu shi, fuskar ta zurma sosai tayi kashin ido da wuya yadda taga ya nuna tausayinsa akan mahaifiyarta ta ɗauka idan ya tashi tafiya zai ce ta zauna tayi jinyarta sai kawai taji yace " tashi mu wuce gida babu mutsu ta ɗauki jakarta ta rataya tana bakin rai tayiwa hajiya rahma sallama , suka wuce zuwa gidansu , haushi yasa taki fitowa daga cikin motar dan tasan gurin ummita zashi ..
Ya shigo parlou'n a lokacin ummita na tare da hajiya umma tana ninke kayan baby da'aka wanke jin sautin muryarsa hankalinta ya daga matuka tace "wayyo na shiga uku gaba-daya tsoro ya kamata ta soma hawaye Hajiya umma ta kalleta tace "lafiya ummita menene na kirawa kanki kalmar kin shiga uku? "dan Allah umma ki taimakeni kice yaya mah'ruf ya barni har ayi suna wallahi idan na koma nasan bazai kara bari na fito ba, yau ma da kyar ya barni tun shekaranjiya nake bi sa "kuntata miki da dukanki yake ko ? Tayi saurin girgiza mata kai "ni dai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 68 Chapter of 76