min ba ban damu da rashin lafiyarta ba , kin je kinyi zamanki a wata ƙasa da sunan jinya yanzu kuma kin dawo kina shirin yin bidia alhalin bata gama samun isasshen lafiya ba, well duk ma abinda zakiyi kina iya yi wannan damuwarki ce amman ni babu ni ciki kamar zatayi kuka tace "dan Allah kayi hakuri nasan shine ma yasa kake son hadani da wata ...
A zuciyarsa yace" duk ke kika jawo ...
"Ni dai kayi hakuri hajiya ta samu sauki sosai kamar yadda na faɗa maka yan'uwana zasuyi biki idan baka zo ba abun zai zama su...
Saurin d'aga mata hannu yayi "kinsan Allah babu inda zani kuje ke da ya uwanki marasa tunani kuyi duk abinda zakuyi yayi wa account dinta transfer din kudi masu yawa ya mike ya fice.
da Kuka ta shiga parloun'nsu ana suka kusan cin karo da hajiya rahma yayarta ta faɗa jikinta tana kuka,hajiya rahma ta tambayeta "menene kuma ?
"Yayarmu ki taimakeni Mahruf baya tatawa hankalinsa na wani guri ..
"ki kwantar da hankalinki zai zo hannu ne wannan shegiyar yarinyar da zai aura bama zata gane kanshi ba,duk cikinmu wa kika ga ya zauna da kishiya ?
Ta girgiza mata kai "to Kinga kuwa babu yadda za'ayi ki zauna daita ,ke dai kisa ido akwai dabaru masu yawa da zan koyar dake , kin shafa masa maganin kuwa ?
Ta girgiza kai "ko fuska yaki saki bare na shafa masa ,"okay duk ki rabu dan burouba zai gane kurenshi ne , ni addauta a soma d'aura naki aure "shine yayarmu , nima nafi son haka, daki suka karasa tana rarrashinta ..
****
Tana kwance a parlour'n hannuta rike da carbi tana ja taga ana shigowa da wasu hadaddun akwatina sai da aka gama shigowa da akwatina aka jeresu a aguri daya site shida shida ne kala iri daya guda biyu sannan aunty ta shigo ta zauna kusa da mama, ummita ta mike a hankali ta gaishe da aunty "ya karfin jikin ummita ? Ta tambayeta cike da tausayinta
"Alhamdullahi aunty naji sauki sosai ya su maryam ban gansu ba ko sai zuwa gobe zasu zo?
"Eh sai zuwa gobe zasu zo "ok tayi hanyar sama tana cigaba da jan carbi
"Waɗan kayan fa aunty ? Inji cewar mama ,
Cike da fad'ad'a murmushi aunty tace "lefen ummita ne da suhaima har an kai can bangaren hajiya ummah tace aka su duka nan domin gurinki yafi cancanta aka kawo "yanzu ita ummita har wani lefe za'a yi mata bayan ga na rayhan can ko ta'basu baayi ba dan kawai a wahalar min da yaro ?
" Kai kinji jiki da wata magana rabon diyata ne dole kuma ayi mata na rayhan daban nashi daban ai bashi yayi yaya ne yayi hajiya umma kuma ta dage lallai sai anyiwa diyarta mama tayi murmushin jin dadi tace " Allah ya sanyawa auren albarka yanzu yaushe za'a kai na suhaima ?
"Da dai gobe da yamma nace amman me kika gani ?
"Babu wani abu ai duk yadda kuka ce daidai ne ...
Washegari gidan ya cika da wasu daga cikin dangi domin kai lefen suhaima , mota uku suka tafi dashi an tarbeshi cikin mutumtaka bayan an dan yi barkwanci dangin suhaima suka soma duba kaya sosai suka dinga yaba kaya, da zasu wuce aka basu tukuici dubu ashirin , dubu hamsin suka kawo musu da buhun shikafa biyu da akwaiti shida da kayan lalle ...
akan hanyarsu ta dawo gida ne daya daga cikin makotan aunty data gayyata tace "maman aisha gaskiya d'anku bai yi dacen gidan aure ba ,gashi zaku had'a diyarku kishi da yar gidan ,kowa ya san yan gidan basa zama da kishiya ,haka suka taso har uwarsu duk auren da ubansu zai nema sai an gama komai ake fasa shi "da gaske hajara ?
"Kwarai kuwa ai ingaya miki ciwon uwar ma mutane cewa suke tsabar bin bokaye ne ya mai daita haka kullum ciwo ba'a wannan kasa daita ba'a wancan kasa daita duk dan neman magani , ku dai ku tashi tsaye da addu'a dan ko peper chicking din da sukayi bazan ba ta k'arasa maganar tana dariya har.
"kudin fa ko shima kin yafe ? " Kudin kam zan amsa tunda cikin wanda muka kai musu ne har suka kawo gida hirar suke dan haka bayan an bawa Kowa takuici ya kama gabansa aunty take sheidawa mama sannan ta karasa maganar da "ki tashi da addu'a muryarta a sanyaye tace "addu'a kullun cikin yinta muke salama sai dai zan sake dagewa na gode sosai da kulawa Allah ya yara zuri'a har harabar gidan mama ta rako aunty inda tayi bangaren mahaifiyarta hajiya inna ita kuma mama ta dawo part dinta cike da zullumi..
Da daddare hajiya ummah da kanta ta shigo duba jikin ummita har dakin ummita ta shiga ta isketa zaune cikin halin nata data saba na tunani ,tayi gyaran murya da sauri ta dawo hankalinta tana ganinta ta zube kasa ta gaisheta kamar koda yaushe ,ta karaso ta kamo hannunta ta damke cikin nata ta mikar daita ta zaunar daita , itama ta zauna a gefenta murya a sanyaye tace "kiyi hakuri da duk hukuncin da Allah yayi miki ,ina kaunarki ummita kamar yadda nake kaunar mahaifiyarki kauna irin wanda bazan iya misaltawa ba , ina farinciki da wannan auren ummita na dade ina mafarkinsa a she zai faru ina raye ,na rokeki ki kiyi farinciki dashi ,nasan nan gaba dukkaninmu zamuyi alfahari dashi , wannan auren wani qaddararen al'amari ne daga Allah dan haka ki saki jikinki ayi duk wani shirye shirye da za'a dake Allah yayi muku albarka ku ruke juna da amana dukkaniku abu daya ne agurin mamanku duk abinda yayi miki kada ki boye min ki sanar dani kinji ni din tamkar mahaifiyarki ce zan ɗauki mataki ,bazan yarda ataka min ke ba .....
Har ta gama dogon bayaninta ummita bata ce komai ba kanta na sunkuye a kasa tana wasa da yatsun hannunta hawaye na zubowa daga cikin idanunta tashi muje bangarena ki daina zama ke kadai ,tare suka fito ta ta sata gaba ...
*******
Kira ɗaya hajiya rahma babbar yayar suhaima tayiwa kanwarta zulaihat dake binta , bayan sun gaisa tace "har yanzu baki k'araso bane me kika tsaya yi ?
"ina kan shiryawa ne yayarmu gani nan zuwa bazan bata lokaci ba saboda nasan mahimmanci abinda ke gabanmu ..
Ko cikakken minti goma batayi da ajiye wayar ba, ta karaso suka fito Cikin had'add'iyar motar hajiya rahma ,babu abinda suke tautaunawa sai yadda zasu mallake Mah'ruf ya zamo sai abinda yar'uwarsu tace ..
Hanyar mafoluku suka ɗauka dake unguwar oshodi ..
TWO FRIENDS ( BSBS)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
MY QAUNA KINA RAINA , INA YINKI OVER DA BADAN BA DA NACE KAF MEDIA ..................
WASU ZASU YI TUNANIN TO ME YASA BANYI MAGANARKI A TUN FARKO BA , NO NO QAUNA NAKI SAUDAKAWAR TANA CIKIN ZUCIYA , ZUCIYA DA ZUCIYA NE KAƊAI ZASU FAHIMCI HAKA MUCH LOVE
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 37
..bai fi tafiyar minti talatin daga cikin agege ba suka k'araso mafoluku ,
Can nesa da gidan babalawo dinsu suka yi parking ,Suka fito suna cigaba da hirar abu ɗaya , sun iske babalawo zaune cikin wani kangon d'akin da yake tafiyar da aikin tsaface tsafacensa jikinsa sanye da kaya masu matukar datti kamar koda yaushe farar siglet ce data koma ruwan brown tsabar kazanta da dogon wando yana cin namiji goro yana kur'ban ruwan giya.
yana ganinsu ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yana musu marhabun da zuwa " Ramota (e,ma wole) yau kune a garin ?
" kwana biyu najiku dif (bawoni alaja ) ya hajiya take ?
zama sukayi tare da cewa "wallahi rashin lafiyarta ne ya hanamu zuwa ,gabadaya bama cikin natsuwa da kwanciyar hankali .."shongo awo afun ni alafiya .
tun kafin su fad'i bukatarsu ya soma buga kasa yana wasu zane zane a cikin kasa da yatsunsa biyu "kanwarku ce zata auri wani mai shegen taurin kai kuma zasu kasance su biyu a gurinsa sannan mahaifiyarku na bukatar a fasa aurensa da wacan yarinyar sannan kanwarku ta mallakeshi mallakewa ta har abada sai yadda tayi dashi .
hajiya rahma ta girgiza masa kanta alamun haka ne "boka mai gani har hanji dubanka haka ne sai dai bana bukatar a fasa auren a yanzu saboda mutane zasu iya fahimtar daga garemu ne , ayi auren amman muna son suhaima ta zamo tauraruwa a gidansa har acikin zuciyar miji da danginsa gabadaya, yarinyar tazo amatsayin yar aikinta , mijin ya tsaneta , bayan ta zamo ba kowa ba agurin miji ,ta zamo baiwa ga yar'uwarmu suhaima ta dinga jin tsoronta sannan a cire masa tunanin kowa ce mace a duniya idan ba na suhaima ba, duk kuma abinda ta umarce shi, yayi mata cikin rawar jiki..
(Babalawo
ifa to ri ifun owo eyon)
( Boka mai gani har hanji) ya sake bushewa da wata mahaukaciyar dariya har yana buso musu warin giyan bakinsa .
" duk abinda kika lisafa babu wanda zai gagara hajiya rahma ta sauke naunauyen ajiyar zuciya mai hade da farinciki ," zanyi aiki amman dole wani aikin zai soma aiki ne bayan ita yarinyar ta kasance a gidansa, za'a bene aikin a tsakankanin d'akinta na bacci ta haka ne zaman gidan zai gagareta sai ta zama abar tausayi, sannan zan baku wani abu da kanwartaku zata saka agabanta tayi tsawon kwana biyu tana sakashi a gabanta sannan ta cire ,wannan ruwan kuma ya d'auko wani kwalba dake ɗauke da ruwa da duk tsutsotsi ne aciki ya ajiye a gabansu ,," zata dinga fitsari acikinsa ,amman sai ta kalli gabasa ta ambaci sunanshi da abinda take buƙata akanshi shima na tsawon kwana biyu da wannan itacen zaiyi a gabanta ,sai tayi mishi girki yaci kafin a d'aura aure amman banda bismillah matukar yayi bismillah aiki ya karye sai dai wani aikin bashi ba .
nan take ya dinga musu bayani yana haɗa masu tsafinsa ya bawa hajiya rahma layar da za'a benne da sauran magani asiri kala kala ya haɗa , hajiya rahma tace "babalawo ina son ayi mata gbere a gabanta kamar yadda aka mana ta yadda zata kara mallakeshi "wannan ba matsala bane bayan bikin sai ku zo daita ayi mata suka zube masa kudi masu yawa sukayi gaba cikin farinciki ...
Kai tsaye gida suka nufa suka tasa mahaifiyarsu gaba suna mata bayani , ta dinga saka musu albarka "rahma Allah yayi muku albarka gabad'ayanku nasan ko bayan raina zaki rike kannenki , ina alfahari dake saboda kina wanke min zuciyata da farinciki "kina ma raye hajja , idan bakya raye duniyar ai bazata mana dadi ba, Allah dai ya ƙara miki lafiya nan suka shiga tautaunawa agaban suhaima.
" yanzu ya za'a yi a benne layar nan ? "wannan ba damuwa bane idan mun je kai kayan suhaima ko balla part dinta nayi a abenne, wuyarta dai mu shiga gidan , "haka ne rahma sai dai na so a fasa d'aura auren yarinyar ,na saka rai suhaima ita kaɗai zata zauna a gidanta tayi mulki kamar yadda kowanne ku yake a gidansa .
"Hajja Ki kwanata da hankalinki duk yadda kike son tayi mulki zatayi ,kun gani nan bana da ra'ayin korar kishiya nafi son ta zauna taga rayuwa ,ta rayu ina bautar daita har zuwa sanda zaki mutu ..
"Yayarmu ya zanyi dana abinci ?"yanzu ba fa son zuwa gurina yake ba wallahi ,tayi maganar kamar zatayi kuka "ke dan Allah kiyiwa mutane shiru da anyi magana ki narke fuskar kamar wata mai takaba , dan durin uwarsa da kafarsa zai zo ance miki mu na wasa ne ,gwada cewa yazo kiga aiki da cikawa , rungume y'an'uwanta tayi tana farinciki "na gode na gode yan'uwana Allah ya bar min ku rungumeta sukayi suna suna shafa bayanta hajja ta sake fadada fuskarta da murmushi tana sake jin tsananin qaunar ƴaƴanta akan yaranta babu abinda baza iya ba ..
Cigaba da shirye shiryen biki sukayi bayan sun aiwatar da abinda ke ransu ,sun balla bangaren ummita sun binne layar da babalawo ya basu a bakin uwar d'akin ummita sannan suka bawa kafintar da suka zo dashi umarnin ya rufe kofar ....
sauran kwana uku a daura auren ummita ta ɗan saki ranta ta shiga cikin y'an'uwanta hakan kuwa yayiwa Hajiya umma da mama dady ,tana zaune a dakin mama ya shigo d'akin ya ganta zaune hannuta rike da plet tana shan farfesun kifi, ya tsura mata ido tausayin kanshi ne ya kamashi saboda ganin gabadaya ta sauya tamkar babu abinda ke damunta lamaran gabanta kawai take , ya ja tsaki yana kiran aikin banza kawai tare da sunan "mama .....
sai lokacin tasan ya shigo cikin natsuwa ta d'ago ta kalleshi da fararen idanunta , kallo ɗaya tayi masa haɗe da mikewa tsaye ta soma wata irin tafiya mai daga hankali da ita kanta bata san ta iya ba ta ajiye plet din hannunta da spoon , tayi wata irin mika da sallati ta nufo inda yake , take yaji wani iri ajikinshi a sanadiyyar mikar data yi , jijiyarsa ta soma harbawa ,idanunshi ya tsura mata yana mamakinta ta karaso daf dashi tana cigaba da mika da tsura masa idanunta tana kallon cikin idanunshi ,kallonshi take eye's to eye's babu wata fargaba ko tsoro , saurin ɗauke numfashinsa yayi yaki ce mata komai yana ƙoƙarin juyawa zai fita daman mama yake son gani tunda bata nan bai ga amfanin cigaba da tsayuwa
yana kallonta tana daga masa hankali a banza ba , har zai fita tayi wani tunani dan haka ta kira sunansa cikin sanyayyiyar muryata "ya Mah'ruf ya tsaya cak ba tare daya juyo ba, ta zubawa bayansa ido tana kallonsa zuciyarta na harbawa da sauri "ma..mama kake nema ?
Tayi maganar cike da in ina ya juyo a fusace yana tsare gida "Ban sani ba , da iskanci sai yanzu zaki min magana ai kinsan ita na shigo nema da tsaya kina kina wani shirme .
"Allah ya baka hakuri mai da wukar ta matso gabanshi ta tsaya zuciyarta cike da tsoro a hankali ta kai hannunta fuskarshi ta shiga goge masa gumin dake tsatsafo masa "wannan gumi menene ...?
Sannan ta cigaba da magana "amman sai nake ganin kamar na wani abu da .....
"Dakata dan Allah malama bana son zakewa plz ina ruwanki ko a cikin teku kika gani ba gumi ba ?
"Wai da zan fahimtar da kai ..
Ya sake katse mata hanzarin zuciyoyinsu na dokawa a lokaci daya, "fahimtar dani me ?
"ki shiga hankalinki sannan ki kama kanki dan ban son shishigi da rainin hankali Yana gama fadar haka ya juya ya fice , shiru tayi tana kallon kofar daya bi ,"me ruwanki da shi?
" me ma yasa kikai masa magana shiru ta cigaba yi tsaye tana wa kanta Allah ƙara, sai dai a kashi dari na tsoronsa kashi hamsin da wani abu ya kau kuma tana jin duk runtsi zata tsaya tsayin daka akan rashin jin tsoronsa .
A kwanakin asirin yan'uwan suhaima ya soma tasiri acikin kwakwalwar sa
wani kallon gani gani yake kowa , yana cikin tunanin kai kanshi gareta ,kiranta ya shigo masa kasa ignoring din Kiran yayi ya ɗauka cikin rawar jiki ta lura duk kwanaki idan ta kirashi yana ɗauka, dan haka yanzu daya ɗauka ta sakar masa kuka ita lallai tana son ganinsa cikin rawar jiki yace "an gama gani nan zuwa ki bani wasu yan mintiuna .
cikin shigar kananan kaya ya isketa kwance a sitroom tayi lamo tana jiran karasowarsa ta zuba masa ido tana cikin kololuwar farinciki da ganinsa da sauri ta mike ta shige jikinsa bai wani damu ba ya rungumeta tsam ajikinshi yana shafa bayanta , wani kukan munafurcin ta sakar masa ",habibi ina sonka bakina yayi kadan ya misaltan irin soyayyar da nake maka , sai dai idan na tuna mu biyu zaka aura duk farinciki da nake ciki sai ya gushe amman kai sai naga kamar farinciki kake zaka hadani da wata ...
Ya sake kamkameta ajikinshi "am sorry my suhaima nasan irin zafin da kike ji wallahi nima ina ji zafin abun a zuciyata ina daurewa ne kawai, dan bin umarnin iyaye , ko kadan aurena daita bazai sa na canza miki ba, babu macen da nake so kamarki babu macen da zata sha gabanki ,kece zabina ita kuma zabin rayhan ce biyayya zanyi kece zabin zuciyar Mah'ruf batun kamar ina murna wannan zargi kike dazaki shiga zuciyata da zaki tabbatar da gaskiyar lamari , sosai ranta yayi sanyi da jin dadaddan kalaman dake fitowa daga bakinsa.
ta saki murmushi tana sake shigewa jikinsa tare da shimfida masa manya dukiyar fulaninta da suke a narke acikin bra "am so happy Habibi ka sanyaya min zuciya muje kaci abinci ta janyo hannunshi a koshe yake amman bazai iya cewa ya koshi ba, duk da abinda yake son fadi Kenan.
gaban kular abinci ta zaunar dashi akan wani ratsantsen kafet mai shegen kyau ta bude kular abinci sai kamshi jollof din shinkafa data sha kayan hadi da kori ya tashi , ta zuba masa tana masa fari da idanunta ,ta rufe kular , ta rike spoon a hankali tana fuskantar shi "bude bakinka da kaina zan baka yayi murmushi ta kai spoon bakinsa ya bude tare da furta Bismillah rahmanir rahim .........
Take gabanta ya fadi ,lumshe idanunta tayi saboda jin haushi abinda yace , hankalinta yayi kololuwar tashi tasan aikinsu na daf da karyewa , taki bashi tana buɗe idanunta tare da janye spoon din ta rausayar da idanunta cikin nashi tana jan hankalinsa ta sake kai hannunta bakinsa ya rike hannun yana kai abincin bakinsa tare ambaton sunan Allah batare da sanin ta ba loma uku yayi yace ya koshe bata damu ba tunda ko loma daya yaci bukata zata biya .
kan kujera ta dawo dashi tana haɗe fuskarsu guri ɗaya, shiru sukayi bayan sun zubawa juna ido bakinsa da hancinsa da idanunshi take kallo cikin tsananin sonshi ,a hankali ta sake matso da fuskarta daf da nashi har tayi nasarar haɗe bakinsu ta soma tsotsa , a hankali ya dinga yawo da harshensa cikin bakinta, ta rike fuskarshi sosai da hannuwanta duka tana tsotsan miyon bakinsa yayi mamakin yadda ta kware gurin shan baki gaba-daya ta manne masa ajiki ,ita kuwa a zuciyarta addu'a tayi dan daman ta san zai iya fiyye da yadda take hasashoshi gurin iya sarrafa mace, iya shan baki ma kenan ina ga mai gabadaya suka yi ,
sosai suke tsotsar bakin juna tamkar zasu hadiye bakin junansu da kyar ta kwance bakinta saboda ba karamin cafka yayi musu ba numfashi suke fitarwa idanunshi sun yi jawur tamkar wanda aka xubawa garin barkono aciki ,ta shafa fuskarshi lokacin da yake kokarin sake kamo bakinta "no Habibi akwai zafi fa "
Ta fadi hk tana kashe masa idonta daya murmushin yayi ",zaki san akwai zafi iya wannan kike wa raki gabad'aya ta zube jikinsa tana rudashi bashi ya bar gidan ba sai gurin 12 ya koma gida tamkar bugage ..
Ranar daurin aure da safe mah'ruf ya shirya cikin sabuwar farar shadda da hula abokinsa jafar da sauran abokansa duk shiga fararen kaya sukayi na Mah'ruf kawai ya bambamta da nasu sai kamshi yake zubawa ya dinga Allah Allah su wuce gidansu suhaima amman baba sarki ya nuna auren gida za'a fara daurawa sannan suje ga iyayen suhaima ,
An daura auren ummita lafiya sannan iyayenta suka zarce da biki.. yayinda maza suka wuce gidansu suhaima domin daura aurenta da Mah'ruf , Diner da yayita cika baki baza shi ba sai gashi shine kan gaba wannan ne ya bawa su aunty damar mika ummita gidan mijinta kafin aka wo suhaima bayan sunyi mata huduba ta gari ,da haka ne ummita ta kasance uwar gida a gidan mahruf yayinda suhaima zata kasance amarya.
Daga gurin diner gida aka yo da amarya suhaima inda aka nufi dakin mahaifiyarta daita ,ta canza wasu kayan sannan hajiyarsu ta soma yi mata magana "duk da muna da madafar dafawa amman ki sake saka wa zuciyarki natsuwa ,ki zamo mai fuska biyu a tsakani
ta yadda zaki san sirrin danginsa da nashi , ki dinga shiga ko'ina acikin danginsa har ma daita kanta yarinyar ,hajiya rahma tayi saurin karbe maganar da cewa " ni Kuma zan dinga zuwa miki da salon sihiri iri iri da koyar dake makirci wanda zaki dinga kulla mata, ina tabbatar miki wannan yarinyar bata isa ta tsallake tarkonmu ba kina zaune zai korawa iyayenta ita, gida ya zama namu mu kadai, idan kuma bata fita ba zata zamo tamkar baiwa ce agaremu , acikin y'an'uwanta babu wanda yayi mata hudubar arziki daga nan aka mikar daita tsaye bayan sun yi mata hudubar tsiya suka taho gidan mahruf tare da yan kawo amarya ..
gabadaya dangin ummita suna gidan aka kawo suhaima amman babu wanda yayi kokarin fitowa .
wannan abu bai yi musu ciwo ba , dan kuwa a banza suka d'auke shi ,su dake da ragamar gidan gabadaya , batare da wata damuwa ba hajiya rahma ta riko hannun suhaima zuwa ga family Mah'ruf , a parlour'n suka iskesu gabadaya da alamun tunda suka zo amarya bata shiga dakinta ba ,ummita na zaune a tsakiyar wasu mata biyu meenal da maryam suna gefe guda tsaye suna kallon suhaima dake lullu'be cikin mayafi , an yi musu faɗan su zauna lafiya sosai , inda daga karshe aunty ta nunawa suhaima ummita ce uwar gida duk da karancin shekarunta, y'an'uwan suhaima suka mikar daita tsaye suna cika suna batsewa suka koma zuwa bangarenta .
suna shiga hajiya rahma tace "kai da alamun mutanen nan fa yan zafi kai ne, kalli yadda wancan kanwar uban nasa ke wani tada jibiyon wuya tana maimaita ummita ce uwar gidan ," mu ina ruwanmu da wata uwar gida ko amarya bayan mu baiwa aka kawo mana , suka kwashe da dariya "kai yayarmu Allah ya barmana ke " ai ko amarya aka kawo mana gida sai mun bankadota waje bare wata uwar gida .....
"Ta dauki mayafinta ta rataya a kafada da jakarta "kunga tafiya wanda ya tashi yazo mu wuce ,zulaihat ta mike tsaye "muje yayarmu ki saukie ni wannan mayataccen ma ya soma dumuna da kira Hajiya rahma tayi kusa da suhaima "karki
yarda ya kwana agurinta , ki san duk makirci da zakiyi ya kwana agurinki shi asiri sai da makirci da jan hankali yake kara tasiri tana gama fadar haka ta juya suhaima ta riko hannuta "yayarmu sai naga kamar bata shiga d'akin ba "eh nima haka na lura amman ai zata shiga ne dan ubanta tunda baa parlour'n zata kwana ba ,karki damu tsalakar kawai ake bukata kuma ina da tabbacin zata yi .......
"Ke dai ki janyo hankalinsa ya kwana agurinki Allah ya tashemu lafiya mun wuce tana gama fadar haka suka fice ..
TWO FRIENDS ( BSBS)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*AYSHA MUSA TILLI*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 38
.... a cikin mota ma babu abinda hajiya rahma da zulaihat suke facce maganar akan makirci da tasirin sihiri har sanda hajiya rahma ta sauke zulaihat a kofar gidanta ta murza kan sitiyarin motarta ......
Kowa ya watse a bangaren ummita daga aunty sai meenal Maryam da aslamiyya da aunty jidda wacce ita daman a d'ayan ɓangaren baya take " sosai aunty ta sake yiwa ummita faɗa akan rayuwar aure "ki yawaita addua azkar din safe da yamma kada ki kuskura ya wuceki duk da nasan kina yi amman ki sake dagewa kiyi hakuri irin na mahaifiyarki matukar kika yi hakuri irin hakurin maryam ina tabbatar miki babu wata mace da zata sha gabanki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 76