rufe masa ido dan koda ya shigo idonshi sun gama rufewa akan matarsa burinshi bai wuce ya kawar dashi ba, mama ta riko hannun amad batare da ta sake cewa komai suka shiga cikin gida...
Cike da taikaici da masifa dake cinsa ya maida idanunshi kan ummita yana sake tambayar cikin zafi kamar zai mareta "Ki faɗa min abinda ya faru kinsa a rashin sani nayiwa d'an uwana rashin mutunci ,me yasa kina kallon abinda ke faruwa kika boye min ,baki san haka cutawar bane?
sai lokacin ummita ta dawo hayyacinta sosai ganin wulgawar amad babu abinda ya sameshi, ta yunkura ta mika daga jikinsa tana kakkabe jikinta, ya mike tsaye zai kamota ta bige masa hannu, cikin tsiwa ta dakatar dashi da hannunta "Karka sake ka taɓani, ji irin haukan da kayi yanzu, idan anyi mgn kace baka so na kishin auranka kake haka ake kishi?
Yanzu wannan kishi ne saboda Allah "?
ta kai hannunta daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da matsanancin karfi "shima wannan kishi ne ba so ba? kana yaudarar kanka ya mah'ruf na tabbatar da kana so na idan ma baka sona a wannan abun daka aikata yanzu na sake tabbartawa kaina da kana mahaukacin so.......
katseta yayi ta hanyar d'aga mata hannu
"Don't deceiving your self fatlion , ko kina hauka ne? ko kuma kwakwalwarki ta dusashe ne ? " kwakwalwarki da tunaninki basu faɗa miki gsky ba saboda wannan ba so ne?
"Uban wa ya faɗa miki haka ake so ?
" to bari kiji wannan ba so bane , da aurena akanki dole nayi kishin aurena, dole kiga hankalina ya tashi nayi hauka fiyye da haka na sha faɗa miki ni ba addayus bane mutumin da baya kishin iyalinsa dole nayi kishinki idan ba haka ba wutar Allah ta cini dan haka ki dawo cikin hankalinki " ya karasa maganar cikin masifa yana huci, ya dunkule hannunsa da iyakacin karfinsa ya sake kaiwa bango naushi yana huci , runtse idanunshi yayi gam saboda yasan karya zuciyarsa ta faɗa sam ba abinda yake zuciyarsa ba kenan yana jin fiyye da yadda yake kishinta ......
Idanunta ta zaro Sbd jini data gani a hannunsa ta matso jikinsa tana rike hannunsa ya waigo a hankali fuskarshi a haɗe sai da gabanta ya fad'i , ya tsura mata ido "jini a hannunka ya mahruf!" dakatar da ita yayi ta hanyar cewa "Stop touching me ki barni kije kawai amman kinsan Allah sai naci uban menal yau " ummita tace "Dan Allah kayi hakuri ka yafe wa menal bata da laifi Ina son ƴar uwata , bana son wani abu ya sameta ni ka hukuntani idan bazaka hakura ba amman ka barta tana gama maganar sai hawaye shar-shar suka gangaro saman kyakyawar fuskarta.
Sauke naunayen ajiyar zuciya yayi batare daya furta komai ba , tasa hannu ta share hawaye tace "Muje ciki ta riko hannunsa suka nufi bangaren mama still bai mata mutsu ba Suna shiga ta nufi sama dashi ya turje yaki motsi ta juyo tana kallonsa da lulu eye's dinta "plz now muje nayi maka treament din hannunka yayi mata banza yana cika yana batsewa " mama dake tsaye a bakin kitchen tana kallonsu tace " kabita ku shiga ciki mana ko ba treament zata maka ba .?
Yayi shiru zuciyarsa na dokawa da zafi idan yayi bai ji ciwon abinda suka yi masa yayi karya har shi zasu haɗawa plan ?
"Dan Allah muje yaya na yi maka treatment din hannunka ummita cike da rauni da tsantsar jin zafin jinin da ke fita daga hannunsa ta furta haka ,"mama dan allah kiyi masa magana ...
Tun kafin mama ta sake cewa wani abu , ya fixge hannunsa dake cikin nata ya soma motsawa yana daga kafarshi da kyar , jiki babu kwari ummita ta biyo bayansa bugun zuciyarta na tsananta, duk ta firgici a dalilin haɗe fuskarshi da yayi dan har yasa miyon bakinta ya kafe daga tsittarwa da take ..
Juyawa mama tayi tana murmushi ", kuna wahalar da zuciyoyinku" ta faɗa a zuci ta karaso gurin amad tana tambayarsa da jiki "Sannu amad ya kake jin wuyanka?" amsawa yayi "Da sauƙi mama amman na shaku gaskiya ni wucewa ma zanyi yanzu daman sautsayi ne ya biyo dani ,mama tayi murmushi "ai duk laifinsu ne ,sun san halinsa me yasa zasu yi masa irin wannan wasan" koma dai menene wallahi tafiya zanyi dan ko awa daya bazan qara ba, bansa dakiyar zuciyar mah'ruf ya kai haka ba.
"ya wuce duk yadda kake tunani idan ransa ya ɓaci gara yayi shiru akan yayi zuciya amman dai
ka bari zuwa gobe da safe ka wuce ,ya girgiza kanshi "tafiya zanyi ya ɗauki jakar school bag ya rataye a bayansa yayi mata sallama yana ƙoƙarin cewa ta tsaida shi "jirani nazo ta wuce d'akinta .
Suna shiga ɗakin ummita ta kama hannun mah'ruf sai wani fizgewa yake yana cin magani a dole an bata masa rai , haka ta zaunar dashi saman gadonta ta ɗauko kayan dressing ɗin tazo ta zauna dab dashi har suna iya jiyo hucin junansu, ahankali ta ɗora idanunta kan kyakyawar fuskarshi, tana kallonsa cike da mayen soyayyarsa ji take daman ciwon ya dawo kanta, ƙin kallonta yayi ya sake haɗe rai , idanunta ta runtse na second biyar sannan ta buɗe ta tattaro jarumta ta sanyawa jikinta ta buɗe ƙwalbar hydrogen ta k'ara shigewa jikinsa, ta kamo hannunsa mai ciwo cike da wani irin mugun shauƙin ƙaunarsa, ta shiga goga masa hydrogen ɗin cikin wani irin yanayi tana manne masa ta yanda ba zaiji zafi sosai ba .
da farko yaji zafin hydrogen ɗin, amman yanayin yanda ummita take masa dressing ɗin cikin wani irin shauki ta haɗe jikinsu waje ɗaya, tana masa sannun cikin wata irin muryata mai rikitarwa sai yaji zafin babu sai wani irin zirrrrr yrrrrrr yammmm ya dinga ji a sansar jikinsa sai dai ya dake ya basar yaki nunawa ko motsin kirki bai ba dan karta fahimta .
Yayinda hankalin ummita ya sake tashi sosai da ganin yadda yanayin fuskarshi tayi alamun yana jin zafi ,ta runtse idanunta dan kusan tafi shi jin zafin ciwon daya ji , taci gaba da masa dressing ɗin hannunsa, Cikin tsantsar kulawa da tausayinsa.
wani irin fitinanniyar soyayya da take ji yana ratsa sansar jikinta a lokacin da take masa dressing , duk ta shige masa cikin jikinsa, koda ta gama masa luf tayi a saman ƙirjinsa, tana riƙe da hannunsa tana ƙara hura masa iskar bakinta , mah'ruf ya lumshe idanunsa yana jin wani irin mugun yanayi mara musaltuwa, gaba-daya komai ya soma kwance masa "
Bayan ta gama yi masa treament ta koma kan kujera ta tsura masa idanunta tana zance zuci tana son ta saisaita natsuwarta ta kawar da abinda take ji akansa amman sai take jin abun na ninkuwa acikin zuciyarta ,sama da minti 30 suna zaune a haka tana kallonsa ,shi kuma yana kwance rigingine yana furzar da iska .
a hankali mama tayi sallama ummita ta sake daidaita kanta tare da amsa sallamar, mama ta turo kofar ta shigo , ummita ta mike domin bata gurin zama ta zauna idanunta na kan mah'ruf ,"har yaushe zaku daina wannan fad'an ?"ya kamata zuwa yanzu ku fahimci junanku ,ku tsaida wannan tashin hankalin haka banaso ta k'arasa maganar tana sauke numfashi "ai mama shine yake ɗaukar komai da zafi , ki faɗa masa duk abinda zai faru ya dinga saisaita zuciyarsa , kalli yadda yajiwa kanshi ciwo ta fadi tana gyara zaman gashinta da yake kokarin rufe mata fuska "ni fa wasa nake masa shi.......
"ni abokin wasanki da zaki dinga wasa da rayuwata ?
"Ko ina irin wannan wasan dake ?
Tayi shiru tana kallonsa zuciyarta na harba tsabar haushin jin abinda ya faɗa bata san sanda tace " nayi kayi abinda zakayi ,wallahi ka ma bala'in rai min hankali, kai baka sakeni ba ,kai baka maidani matarka ba, sannan baka barni na huta ba gaskiya na gaji enough mahruf zan baka lokaci kasan abu yi if not "if not sai .....
"Ya rabbi baba a gabana saboda Allah mai yasa bazaka dinga hakuri ba ? ta karasa maganar kamar zata zubar da hawaye, yayi saurin riko hannun mama cikin nashi " shikenan mama kiyi hakuri na daina inshaallahu,duk laifi na ne "no kaima ba laifinka bane ,duk baku da laifi Allah yayi muku albarka ke kuma kar na sake jin yana magana kina maida mishi martani zan ci mutuncinki idan na sake ji "to ni yanzu mama haka zanyita zama da .. "shiru nace banason jin komai ta mike ta fice ta barsu "wallahi zan d'aga hankalin kowa a gidan yau amad ne daga gobe ....
"Daga gobe me zakiyi wallahi fatlion ki kiyayeni zan canza miki kamani ,kina cin daraja daya ne agurina if not da tuni na gyara miki zama ta turo masa karamin bakinta tana juya masa keya ya ja tsaki ya fita ..
Bata juyo ba har sai da taji fitarsa daga d'akin gabadaya sannan ta mike ta tattara kayan da tayi masa treament din hannunsa ta maida,
tayi kwanciyarta zuciyarta na bugawa .
kai tsaye part din hajiya umma mah'ruf ya nufa yayi sallama ya shigo ya isketa zaune ita da menal tana ganinsa ta mike a firgice wani irin kallo ya watsa mata ya samu guri ya zauna kusa da hajiya umma "hajiya barka da yamma ?
"Barkanmu baba ya gida da aikin ?"alhamdullahi jikinta menal na rawa tayi saurin durkushewa
a gabansa tana yarfa da hannu "kayi hakuri yaya wallahi bazan sake ba hajiya umma ta dubeta "ke kuma lafiyarki daga shigowarsa kika wani durkushe agabansa kina rokonsa "barta kawai hajiya tasan abinda tayi shiyasa , cike da tashin hankali menal tace "umma dan girman Allah ki bashi hakuri kar ys dakeni duk da san laifina ne, bana laifin umminta "shiiiiiiiiiii You very stupid ita tace laifinta ne ke kince laifinki ne "to ayi musu hakuri ba zasu sake ba .
yayi shiru batare da yayi magana
ba, ba shi ya bar gidan ba sai da yaji an soma kiran sallar magariba sannan ya fita yayi sallar, mai makon ya kama hanyar wucewa gida sai ya dawo bangaren mama da niyyar sake ganin ummita kafin ya wuce gida , ya zauna parloun shiru bai ga fitowarta ba har mama ta zubo masa abinci yaci bata sauko ba ,yana ganin mama ta fita zuwa part din Abba ya mike tsam ya haye sama a kwance ya ganta da alamun bacci take ya tsura mata idanunshi yana kallonta kafin daga bisani a hankali ya kwanta ajikinta yana sakin wani irin naunayen ajiyar zuciya, juyowa tayi a rashin sani ta shige jikinsa yasa hannunsa mara ciwo ya matseta ajikinsa , wani irin zazzafar soyayyarta ke fixgarshi sai dai duk yadda yake jinta a ranshi bazai iya furtawa ba, kissing din goshinta yayi a zuciyarsa yace "Allah ka ga halin da bawanka mahruf yake ciki ,allah ka sausata min nasan ita din ta daban ce tun daga kan ni'imar daka mata .
Ya runtse idanunshi tsigar jikinsa na tashi "tun daga lokacin dana kusanceki zuciyata ta dana tunanin kowa sai ke ,komai nake is perfect ....
"I don't know how to explain amman Ina jinki sosai ajikina ya sake motsowa jikinta yana kissing din wuyanta " a yanzu Yake sake jin zazzafar soyayyarta kusan minti goma ya ɗauka yana kallonta yana sambatu da zuciyarsa sannan ya yunkura ya mike ya zuro kafafunsa kasa yaji ta rike masa hannu tare da fixgoshi jikinta, ya ware idanunshi yana mai tokare hannunwansa da katifa dan kar ya fado saman cikinta tasa hannuwanta duka ta zagayeshi dashi tana sanya kwayar idanunta cikin nashi "meye haka kina son na illataki ne ?
Ta kashe masa idonta daya alamun
eh "
"Bazan iya ba saboda darajan abu daya "meye shi darajan ?
Ya runtse idanunshi " bazaki fahimta ba amman idan lokacin da zaki fahimta yayi zaki sani ne "idan ma sona ne ai tuni na fahimta ..
ya bala'in haɗe rai "har yaushe zaki daina wannan tunani ?ta sauke ajiyar zuciya da karfi "sakar min jiki zan wuce gida "babu inda zaka yau ma ka shirya kwana anan "what ?
"Uhmm anan zaka kwana ko bazaka kwana bane ?"ba zan iya ba ya ja dogon hancinta yana waskewa .
"dole ka fadi haka saboda matartaka tafi karfinka sai abinda ta faɗa kake yi wallahi har kunya nake ji idan naga kana rawar jiki akanta "uban yace miki tafi karfina ?
"Ubana ta bashi amsa da haka tana zare hannuwanta daga jikinsa ta sauko daga kan gadon zata shige bathorrom ya sauko da sauri ya fixgota ta fado jikinsa ya manne da qirjinsa,yasa hannuwansa duka ya zagaye cikinta ya soma shafawa a hankali yana kunshe ido "me yasa zaki zagi Abba ?
"Ba zagi bane amsarka na baka ,shikenan bazan sake cewa haka ba ,amman karki sake cewa ina jin tsoron suhaima ko nayi miki kama da matsoraci ne ?
Ta juyo tana fuskantar shi tana watsa masa harara tare da turo masa karamin bakinta bakinsa ya kai kan lip's dinta "zan tabbatar miki da bana shakka ko jin tsoron suhaima tana ajikinsa ya karasa ya sanyawa kofar key ......
TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
WATTPAD @HAUESH
Page 49
.... A hankali ya juyo daita tana manne ajikinsa , ha'barsa na kan kafad'arta yana shinshina kwantaccen sumar kanta mai fitar da kamshn dake tsuma zuciya zuwa wuyanta ,
tsaye yayi a tsakiyar d'akin yana kare mata kallonta ta cikin mirrow yayinda kowani part na jikinsa ke sake bud'ewa da kar'barta a cikin zuciyarsa ..
jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago Idanunta ta kalli cikin madubi domin ganin abinda yake , take idanuwansu suka sarke cikin juna , cigaba da kallon kwayar idanun juna suka yi qirjinsu na dokawa da matsanancin karfi ,ta kasa ɗauke Idanunta acikin nashi haka shima ya saka daina kallonta "a duk lokacin da zan kasance dake ina tsintar kaina cikin natsuwa mara misaltuwa ,ko fushi nake da zarar na kalli kyakkyawar fuskarki sai naji fushina ya kau , gabad'aya ji nake bana tattare da wata damuwar da zata dakushe farincikina muddin ina tare dake , sosai ya shagala yana zance zuci yana shafa cikinta zuwa kasan mararta , ta lumshe kyawawan idanunta tare da motsa ɗan ƙaramin bakinta "kana magana ne ? yayi saurin saisaita natsuwarsa ya kashe mata idonsa ɗaya yana cigaba da shafa cikinta da bashi da alamun tasawa "abinda faru d'azu sam banji dadinsa ba ya dakata yana nazarinta tayi shiru taki cewa komai tana cigaba da sauraransa "kinyi kuskure gurin wasa da abinda yake da mutunci da daraja arayuwarki karki sake irin wannan kuskuren da gangancin dan bazan dauki kalmar sorry ko rarrashi ba ...
"Zuciyata bazata jurar ana tangaliliya da aurena kiyi respecting d'insa zan ji dadi tsaki taja acikin zuciyarta ..
a hankali ya k'araso bakin gado ya kwantar daita ya soma ƙoƙarin cire agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa da wayoyinsa ya ajiye saman mirrow dinta kamar ya cire kayan jikinsa sai kuma fasa ya kwanta ajikinta yana sakin numfashi da ajiyar zuciya wanda kusan a tare suka yi , matsowa yayi kusa daita sosai batare da yayi magana ba ya manneta a jikinsa , ya d'aura hannunta saman fad'ad'd'en qirjinshi ,
yayinda hannunsa mai ciwo ke kan sumar kanta yana shafawa yana lumshe ido , sun kusan minti talatin suna kwance haka kowanensu da abinda zuciyarsa ke sakawa .
wayarsa ce tayi ƙara sharewa yayi ya cigaba da shafa sumar kanta zuwa wuyanta da gadon bayanta yana jin wani irin qaunarta na fizgarsa wanda yake jin zai iya komai akanta .
tayi shiru tana sauke numfashi yanayinta na sake ɗaukar sauyi na daban kiran ya katse, wani ya sake shigowa amman still yaki ɗauka ganin yaki ɗauka ta buɗe idanunta ,ta tashi daga jikinsa ta kai hannunta kan mirrow ta ɗauki wayar tana dubawa sunan suhaima ta gani yana yawo akan screen din wayar ,ta janyo numfashi da kyar ta sauke haɗe da cewa "matarka ce ka ɗauka mana "i cant ...
"I can't ta maimaita fadar haka a zuciyarta a zahiri kuwa cewa tayi " ya dai tabbata kana jin tsoronta kenan ?
ya ja dogon tsaki tare da ɗan mirgina gefe ya zuba mata manya idanunshi masu narkar mata da zuciya "me yasa kike min haka yau kika sanni da zaki dinga dangantani da kalmar tsoro? "suhaima fa matata ce......"
" naji amman kai me yasa bazaka ɗauka ka tabbatar mata da inda kake ba ?
"Babu dalili kuma karki sake min .......
"Ko kaki ko kaso ya dai tabbata kana jin tsoronta ta karashe faɗa tana matsowa gareshi ta dora lip's dinta akan nashi haɗe da busa masa numfashi yayi saurin lumshe idanunsa "idan har ka tabbatar da baka jin tsoronta ka ɗauka .......
ya sake lumshe idanunshi jikinsa a
mace ya kamota jikinsa, ta shige masa sosai tana lumshe lulu eye's dinta da son dagula masa lissafi "pick up the call ....
wani irin hot kiss ya soma bata a fuskarta yana jin soyayyarta da sha'awarta na kawowa zuciyarsa farmaki "ya mahruf ...ta kira sunansa cikin wata irin kasalalliyar murya "kasan me ake kira da soyayya ?
Ya furzar da iska yana kallon kwayar idanunta "da alamun baka sani ba ,yayi shiru yana jin wani irin sauyi a gabobin jikinsa "a soyayya akwai sadaukarwa,kyautatawa ,
tattali kaffa kaffa , yiwa zuciya abinda take so, ita zuciya ba'a takura a soyayya sannan ba'a hanata ta hanu saboda shi kanshi so idan ya bukasa da kanshi yake bayyana kanshi ...
Tun da ta soma magana yake sauraren yadda zuciyarsa ke tsalle da jin wani dadi na ratsa sansar jikinshi da zuciyarsa , ya sake matsowa jikinta yana jin kamar ya soma lasheta daga tsakiyar kanta zuwa yatsun kafafunta. "duk abinda na lissafa babu wanda baka wa subai'a ba ,ban taɓa maka irin taimakon da ka min ba ,ka yantoni daga makiya kashi da kashi sai dai .........
Ta tsinci kanta da kasa fadar abinda take son fada ta tsuke bakinta tana kallon cikin idanunshi " you still have time ya mah'ruf life is beautiful tana gama fad'ar haka ta mirgina ta sauko , yayi saurin riko yatsunta biyu ta tsaya batare data juyo ba .
yana rike da hannunta ya sauko ya mikar daita tsaye ya tsaya a gabanta yana kallonta "ban fahimci maganarki ba ki fito kiyi min bayani abinda kike nufi dani "nothing kana iya tafiyarka sai da safe daman nice na tsaida kai yanzu kuma na sallameka sai dai daga rana mai kamar ta yau karka sake zuwa inda nake ko magana ban yarda ba matsawar bakasan yadda zaka yi da aurenka dake kaina ba ,ba na matsu da kasancewa da kai bane"no no kamar yadda kace shi aure ba abun wasa bane abun mutuntawa ne , kana da ilimi daidai gargado an very proud of you yaya ta wannan bangaren amman ilimin naka ya zama na ......
Yayi saurin toshe mata baki ta hanyar d'aura nashi yana zaro mata ido kafin daga baya yace "okay dan Kinga na biye miki shine zaki nemi raina min hankali har da zagin aurena ? ya karasa fadar haka yana sake kai bakinsa kan lip's dinta bata ce masa komai ba ta cire bakin daga cikin bakinta sannan ta zare hannunta ta zagayeshi ta shige bayi haɗe da murda key ta jingina bayanta da kofa tana shafa fuskarta " na hakura bazan sake yarda na kusanci inda kake ba har sai na tabbatar da soyayyata ta gama bunkasa acikin zuciyarka , nayi wa kaina alkwarin nan kusa zaka furta da bakinka ...
Jikinsa na rawa ya matso jikin kofar bayi "fatlion ki buɗe min kofa "kayi min idan na bude ka tafi gurin firgitacciyar matarka da kake jin tsoronta "nace ki bude min yayi maganar a tsawace "bazan buɗe ba ya ja tsaki yana juya ya kai hannunsa ya dafe goshinsa tare da rike kugunsa ya soma zagaye d'akin can ya sake komawa jikin kofar "ki bude dan babu inda zani ana zan kwana tayi masa banza har minti talatin ta wuce bata fito ba , wata minti talatin ta sake wuce amman tana ciki bayi taki fitowa ganin idan har bai fita daga dakin ba zata iya kwana acikin bayi yasa ya kwashi wayoyinsa ya buɗe kofar d'akin da karfi ya fita.
Tana jin motsin buga kofarsa ta fito tana sauke numfashi ,ta kwanta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 49 Chapter of 76