mahimmancinki abinda ya faru ba laifi bane , sannan babu yadda zanyi da rayuwata da hakan bai kasance ba a wancan ranar ta ya samuwar wannan cikin jikinki zai kasance ?
"Ki fahimceni wallahi ban cutar dake ba , ta dubeshi cike da sarewa zuciyarta na tsalle abu biyu sun haɗe mata a lokaci daya farincikin jin kalmar da tafi bukata agareshi da bala'in hajiya inna , idanunta na zubar da hawayen farinciki da bakinciki ta juya tana kuka , yayi saurin fizgota ta faɗa fad'ad'd'en qirjinshi suna kallon kwayar idanun juna "me yasa zaki wuce ki barni ? "Ina zaki ki barni yayi maganar a fusace take jikinta ya kama rawa tana son barin wajen ne saboda idanun inna dan tasan abinda mah'ruf yake bakaramin kona mata zuciya yake ba , hakan kuma zai sa taji haushin mama fiyye dashi mah'ruf din .
"tambayarki nake ina zaki ki barni ? nasan nayi kuskure , duk yadda nake ƙaryata gaskiyar dake zuciyata yau gashi ta bayyana kanta a idanun shakikaina wand'a duk duniya su nafi jin kunya fiye da komai ,na soki tun ban san sonki nake ba, na shiga tashin hankali iri iri a kanki , zuciyata ta shiga rud'ani da tashin hankali akanki , idanuna sun sha kwana a buɗe saboda tunaninki ,
ban taɓa sanin mahimmancinki ya yiwa zuciyata tasirin da ni kaina bazan iya magance matsalar ba sai lokacin da zaki auri rayhan wanda nasan aurensa daidai yake da rasaki da zanyi gabadayan ,na shiga damuwa da tashin hankali mara misaltuwa akanki , duk abubuwan da suka faru ban yi dan tuntata miki ba , a yanzu da nake jin kalmar rasaki na sake tabbatar da irin qaunar da nake miki ,ina sonki fiyye da komai da kowa dake cikin duniyar nan .....
" kin amince da irin soyayar da nake miki ?
Tayi saurin girgiza kanta alamun a'a "me yasa ?"why fatlion ? ya faɗa a tare ..
Ta cire hannunsa dake kafad'arta "dan Allah fatlion ki fahimceni karki min haka don't do this to me, ki fahimci yadda nake sonki dan Allah karki barni , karki bar magangun hajiya inna su yi tasiri arayuwamu alhalin muna tsananin son juna.....
gaba-daya maganarsa sake Kunno mata emotion din soyayyarsa suke da take ƙoƙarin dannewa a cikin zuciyarta, a hankali take cigaba da rera kukan farinciki da bakinciki "Allah na gode maka da kawo wannan ranar ina cikin koshin lafiya a gaban kowa mahruf ke nacin yana sona ya kamo yatsun hannunta cikin nashi yana muzwa yana kallon cikin idanunta yana girgiza mata kai alamun ta daina kuma ya fixgo numfashi da kyar "ina fatan ki fahimceni ki ajiye maganar hajiya inna agefe is normal thing ...
"A yanzu ne kake son na fahimceka ? "tayi masa tambayar tana tsareshi da raunannun idanunta , shiru yayi qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi idanunshi da suke cike da tashin hankali ya sake zuba cikin nata yana kallon kwayar idanunta "ka manta lokacin da ka dinga ikirari kana fad'awa duniya cewar baka sona me zakayi da subai'a ?"Idan kai ka manta ni ban manta ba yana cikin kwakwaluwata sannan yanzu kace you're in love with me ta ya kake son na fahimceka ?
kai kullun tunanin kanka kake da muradin bawa zuciyarka abinda take so , as you wish it happen today ,fellings dinka kawai ka sani you don't care about my feelings batun hajiya inna kuma wannan ya rage gareka dan nima babu ruwana kuma ba matsalar subai'a bane , da ka sakeni , ko ka cigaba da rayuwa dani am not care , am nat scared dan ita kalmar ma da kake magana akanta ban santa ba bare zuciyata ta amince min da ita , tana gama fadar haka ta juya.
"fatlion Ki tsaya kiji ya dawo daita gareshi jikinsa na rawa ya talla'bo fuskarta da hannuwansa duka "dan Allah ki fahimceni "I know I hurt you tare da yi miki abubuwan da basu dace ba amman ba wai dan bana sonki bane hasalima soyayya ce amman daga yanzu komai zai kasance miki yadda kike so ,mah'ruf zai zame miki yadda kike bukata ,ki kalli cikin kwayar idanuna zaki fahimci gaskiyar dake cikinsu "oh my goodness ta furta tana runtse idanunta wasu tsiraran hawaye masu zafi suka zubo mata "ni yanzu me kake son nayi maka bayan ga abinda hajiya inna tace ?" Is to late now plz ko ina sonka son bashi da wani amfani "is not too late fatlion I said that I love you with all my heart ya faɗa yana bin iyayensa da kallo wand'a suka dawo tamkar poster tsaye suna kallon ikon Allah ,hajiya umma kuwa tafi kowa murnar faruwa wannan abu ,taji dadi yadda ya furta yana son matarsa a gaban hajiya inna , kuma duk runtse duk wuya bazata yarda ya saki ummita ba ,sai dai duk abinda za'a faru ya faru amman baza ta yarda ba ..
Kallonshi kawai ummita take bata ko iya kiftawa idanunta a hankali ya hura mata iskan bakinsa da sauri ta lumshe idanunta , wata kalar kunya ce ta rufe a lokaci daya , gabadaya jikinta rawa yake ta juya zata wuce ya riko hannunwanta duka cikin nashi dole tayi kasa da kanta ta kasa kallonsa "kasa d'agowa tayi , cikin wani salon magana yace " ki fahimceni babu wanda ya isa ya raba aurenmu zamu rayu tare ...
" no ya mahruf this no possible "me yasa ba zai yiwu ba ?
ta sake juya ya rikota cikin zafin nama " Ki tsaya ki fahimceni mana plz fatlion don't do this , don't do this to me , ki fahimci iri zafi da rad'ad'in da zuciyata take ciki a yanzu , plz don't do this , hajiya umma ta k'araso garesa cike da tausawa halin da yake ciki ta dafa kafad'arsa "ka barta tukunna a gama da wannan matsalar "no hajiya Ki bari na sake fahimtar daita dole ta fahimceni ,ni wannan itace babbar matsalata ba wancan damuwar ba, dole hajiya umma tayi shiru tana runtse idanunta "uhm ina jinki ? ta tsura masa idanunta " dan girman Allah ka rabu dani , da kace ba zaka taɓa sona ba yanzu kuma kazo kana min nacin magana ɗaya ,a gaskiya ka daina min naci dan bana sonka , kuma bazan taba son mah'ruf ba , idan ma kana tunanin subai'a zata soka ka cire hakan a cikin zuciyarka dan subai'a bazata so mah'ruf ba ,"dan girman Allah ki fahimceni "wai me zai na fahimta idan dai son da ka furta ne gaskiya bazan fahimta ba , "ya mahruf zan so ka tuna wani abu saboda Allah da saboda kai da ni ,ya tsuke bakinsa cikin zafin rai yana kallonta ," ina son rayuwar farinciki wa kaina banason abinda zai dangwamar dani cikin tashin hankali da damuwa , zai fi kyau ka nisanta kanka dani tunda ba'a sonka dani nima kuma bana sonka , bazan iya irin rayuwar auren da mahaifiyata tayi ba " amman ni ina sonki ,kuma mahaifiyata tana son aurena dake meye damuwarki da wata hajiya inna ?
"ni hajiya inna ba damuwata bace tunda ba itace ta kawoni duniya ba ,ina dai kyautata mata ne darajan su abba , ba zata zama matsala a rayuwata dake ba, abinda zai daga min hankali shine rashin sona da kika furta bakya yi a yanzu shine damuwata kuma shine matsala ..
Bangaren suhaima kuwa tunda ta bar gidan hankalinta yaki kwanciya, ta kira gidansu mah'ruf yafi sau goma ,amman magana ɗaya dai ake faɗa mata wacce kwakwaluwarta ta kasa ɗauka a karo na karshe ne aka faɗa mata abinda yafi komai daga mata hankali "suhaima subai'a ta rigada ta kwace miki miji ,ta ɗauke miki hankali miji ,bayan cikin da yayi mata har da nasaran sace zuciyarsa tayi , wannan gobarar tafi karfinki ba zaki iya kasheta ba sai wani ikon Allah ta runtse idanunta tana furta " wayyohlly zan iya kashe kowace irin gobara ce muddin akan mah'ruf "to sai kinji duk abinda ake ciki zan sanar miki sai ki san matakin da zaki ɗauki amman wannan yarinyar tayi nisa acikin zuciyarsa tana gama fadar haka kira ta kashe wayarta suhaima ta mike daga zaunen da take ta soma Zariya tana furzar da iska "cikin mah'ruf ai tunda ban dauki cikinsa babu shegiyar da zata haifa masa ta shige dakinta da sauri kamar zata kifa ...
A parlou'n mama kuwa tunda mah'ruf ya soma dramar soyayyarsa idanun hajiya inna ke kanshi ta kasa ɗaukewa ta tsura musu ido tana kallonsa ta a jin zallar 'bacin rai na ratsa kowa ni sashi na jikinta ,ji tayi duk duniya babu mahalukin daya taɓa 'bata mata rai kamar mah'ruf ya gama wulakanta kanshi daita kanta , data san haka zai dawo akan mace da tun farkon tafiyar bata bari an saka mata sunan mahaifinta da mijinta ba bare ta dauki soyayyar duniya ta 6daura masa, ranta a matukar 'bace tace "yanzu na sake tabbatar da cewar ba'a barka haka ba akwai wani kulli a karkashin kasa da aka kulla ,Kiri kiri yarinya tace ka saketa ba tayin aurenka bata sonka amman dan naci irin na asiri sai wani rawar jiki kake kana furta ta fahimceka, fahimtar uwarka da ubanka zata maka illa ka dankarawa shegiya saki uku rasssss ka huta ,ka zauna da matarka mai kaunarka ,kasan Allah ko mutuwa zaka yi sai ka rabu da kwallon mangoro ka huta ,kai yanzu nan burgewa kayi ka tsaya kana wannan shirmen a gaban mace kai dole da ayar tambaya cikin wannan lamari tabbas biri yayi kama da mutun asirin agumawa yayi tasiri amman kasan Allah wannan asirin bazai tasiri akan ba sai na karya shi yau dan muddin ina raye sai na rabaka da wannan abar sai na karya asirin da aka maka ta karasa maganar tana nuna sa da yatsanta ,a natse ya d'ago da idanunshi ya zuba mata su "wato dai ita hajiya inna tayi nisa bata jin kira mugun halinta dashi zata mutu ,duk yadda ya'yanta dasu kansu ke kokarin daurata akan hanya taki canzawa, bazata taba canzawa ba ,bazata taɓa fahimta ba duk abinda suke faɗa mata banza ne 'bata bakinsu kawai suke ,kai jama'a ko mutuwar rayhan babba aya ce gareta amman saboda daurin kai taki saduda ya k'arasa zance zuci yana jan katuwar tsaki ,itama hajiya inna tsaki taja tana Allah wadai da shi ....
Aunty jikinta na rawa ta matso gurin hajiya inna tana bata hakuri da kokarin shawo kanta" baba babba kazo ka bawa inna hakuri "sau nawa zan bata hakuri yayi maganar a zuciye jikinsa na rawa ?
na rigada na bata iya hakurin da zan iya bata, ku dai ku cigaba da bata hakuri zata hakura amman wallahi duk abinda zatace tace amman bazan iya sakin matata ba tunda ina sonta itama kuma nasan tana sona kawai dai bata son faɗa ne a gabanku ni babu ruwana da fada da karta faɗa ba damuwata bace as far as ina sonta ,soyayyata da nake mata ya isa ba sai ta soni ba ..
Ya dawo gurin ummita ya rike hannunwanta duka cikin nashi "Kina jina ki kwantar min da hankalinki zan killace ke da mama bazan taɓa barin ku dangwama cikin wahala da kuncin rayuwa ba ,ina son mama fiyye da tunaninki " taho muje ya riko tafin hannunta Kema mama taso muje , abba idan zaka biyomu kai ma bimillah kai duk ma wanda yaga zai iya biyo yazo muje mu bar mata gidan tayi rayuwarta ita kaɗai , babu mutsu mama ta biyo bayansa itama hajiya umma ta biyo bayansu abba kam kasa tashi yayi duk abinda yake son yi kenan amman rawan da jikinsa yake yasa ya kasa aiwatar da haka .
suna fita ko minti goma basu yi ba sai ga baba sarki ya shigo a daidai lokacin da numfashin abba ya soma ƙoƙarin d'aukewa....
TWO FRIEND'S BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*AMEENA AUTAR HAJIYA*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 55
gaba-daya hankalin sauran mutane dake gurin ƙara tashi har hajiya Inna , suka yi kan abba hajiya inna na kiran sunanshi "Ibrahim! Ibrahim !! aunty ta fashe da kuka haɗe cewa "hajiya kinga abinda kika haifar ko , ya Ibrahim na iyakacin kokarinsa gurin miki biyayya ,yana gudun ɓacin ranki idan ya rasa ranshi ke zakiyi hasara saboda bazaki sake samun kamar shi ba, dan Allah ki hakura ki barshi ya k'arasa rayuwarsa da 'yarsa da matarsa ta k'arasa maganar tana sake rushewa da wani kuka .
"Ibrahim ka buɗe idanunka ni ne babu abinda zai faru ba zaka rasa matarka da yarka ba, a gaugauce injiniya ya dibo ruwa ya kawo ya soma shafa masa a fuskarshi zuwa qirjinsa amman shiru bai motsa ba , kallonsa kawai hajiya Inna take bata ko kifta idanunta ga wani kalar tashin hankali daya bayyana akan fuskarta gabad'aya jikinta rawa yake daga karshe ta soma furta kalmar data ji ta karad'e parloun'n wato " Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun tana cigaba da kallonsa tana jin sabon tashin hankali ganin tsayuwa na neman gagararta yasa ta zube kasan tayis ta rushe da matsanancin kuka "shikenan na rasa d'ana , Ibrahim dina ya mutu ya barni jikinta ba ƙaramin mutuwa yayi ba, ta sake fashewa da wani gigitaccen kuka "shikenan na cuci kaina na kashe d'ana da kaina da gaske mutuwa zaka yi ka barni ? Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun Ibrahim karka mutu ka barni haka ta dinga furta kalmar tana maimatawa a zahiri da badini tana jin jikinta kamar ba nata ba , kuka take sosai tana jan gindi domin son Isa inda yake .
Cike da tsananin tashin hankali injiniya ya kira layin doctor husai yana ɗauka ya sheida masa abinda ya faru ko cikakken minti goma doctor husain bai ɗauka ba ya k'araso . gabadayan suna tsaye akan abba sun kasa motsawa jikinsu na rawa hatta hajiya saudat ta shiga tashin hankali ganin halin da abba yake ciki ,likita ya ɗauki minti goma yana duba abba sannan ya d'ago ya tabbatar musu da "damuwa ce tayi masa yawa, zuciyarsa na daf da tsayawa a ko wani hali matukar bata samu hutun da take buƙata ba , amman a yanzu inshaallahu da zarar anyi masa allura ya samu hutu na wani lokaci zai dawo daidai jakar aikinsa ya d'auko ya soma yi masa allura , gabad'aya suka tsura masa ido fuskarsa sharr sai dai da gani yana cikin damuwa da tashin hankali , hannunsa injiniya ya riko yana mai tsananin tausayawa d'an'uwansa , gabad'aya kana kallonsa zaka san damuwa tai masa mummunar kamu shi kanshi wani irin zazzaɓi ne ya rufeshi kusan minti biyar yana rike da hannun abba yana zubar da hawaye ,hawayensa dake diga saman hannun abba ne ya farkar dashi ya bude idanunshi kaɗan yana sauke numfashi take ya furta kalmar alhamdullahi "sannu yaya bai iya furta komai ba yayi shiru yana kallon injiniya idanunshi cike da kwalla numfashinsa na sama da kasa ..
Alhamdullahi hajiya inna taji suna furtawa a hankali, ba tasan sanda tayi wata irin zabura ta k'araso inda suke "yana raye bai mutu ba inji cewar baba sarki ,"alhamdullahi Allah na gode maka ta furta tana share hawaye jikinta na rawa .
Da kyar aka samun numfashin Abba ya daidaitu , a hankali yake bin mutanen dake gurin da kallo, shiru parloun'n yayi baka jin motsin komai sai na saukar numfashin mutanen dake zaune a cikinsa .
"a soma kira min ma'hruf tukunna tunda an samu Ibrahim din ya farfaɗo sautin muryar baba sarki ta ratsa kunnuwansu sannan ya maida hankalinsa gurin hajiya inna wacce tayi tsuru tsuru cikinta na kad'awa a kan yanayin Abba bata son rasa d'anta duk duniya babu abinda take so da kauna kamar shi tafi son shi fiyye da sauran d'anta bujerewa umarninta yasa take nuna ko'in kula akansa ..
"Kinyi shiru hajiya kamar bakece silar faruwan komai ba ? injiniya ya buɗe baki ya soma magana "baba ka taimaka ka saka baki mairo ta dawo gidan nan banason ta bar rayuwar yaya ,barinta rayuwarsa ba karamin hasara bane ..
"Ai sagiru al'amarin mahaifiyar taku ne abun tsoro , shekara da shekaru har yanzu ana kan abu daya , abu yaki ci yaki cinyewa me take son ayi mata ?
"Wani irin hakuri ne ban bata ba Allah take son take son ya sauko daga sama ya bata hakuri ko me ?" kin shiga rayuwar d'akin kuma kina son shiga rayuwar jikokinki dan rashin imani irin naki ,ya k'arasa maganar yana takaicin halinta .. adaidai lokacin da injiniya ya samu layin ma'hruf .
"Ma'hruf na tsaka da tuki yaji kira a karo na uku gefe ɗaya ga kukan da Ummita ke damun kwakwaluwarsa dashi ,a hankali ya soma rage gudun da yake tare da gangarawa gefen titi yayi parking ya bala'in had'e ranshi yana dubanta.
kwakwaluwarsa ce ta shiga tunani abinda ya kamata yayi mata sai dai yanayin daya tsinci kanshi ciki adalilin kallonta da yayi ya shafe komai da yake ji , baya jin zai iya yi mata wani abu saɓanin rarrashi saboda tsantsar soyayyarta da yake jin yana bin dukkan sansar jikinshi , gaba-daya ya manta mama da umma dake cikin motar ,ya matso kusa daita ya riko laulausan tafin hannunta cikin nashi ya matse gam yana ci-gaba da kallonta "dan Allah ki daina kukan nan yana ci min rai yaya kike son nayi ?"nima Ina cikin tashin hankali fiyye da wanda kike ciki ,tabe bakinta tayi haɗe da fixge hannuta "ina ruwana da tashin hankali da kake ciki kowa tashi ta fisheshi ni abbana ka maidani ina son sanin halin da yake ciki nayi nadamar biyoka da nayi alhalin abbana na cikin wani hali , yayi shiru yana kallonta ta kawar da kanta gefen titi alamun bata son ganin fuskarshi ,yana shirin magana wani kiran ya sake shigowa wayarsa ya lumshe idanunsa ya buɗe yana saukesu akan wayarsa ya ɗauka domin ganin mai damunsa da kira da sauri ya ɗauki wayar ya manna a kunnenshi sakamakon ganin sunan wanda ya kira "dady ..... ya kira sunan zuciyarsa cike da mummunar damuwa .
"kana ina ?
Yayi saurin katse shi da sauri na kusan karasawa gida ,"maza ka dawo yanzu yanzu baba sarki yazo yana son ganin mama da umma ya fad'i haka ne saboda yasan muddin yace shi yake son gani ba zai dawo ba, naunayen ajiyar zuciya ya sauke sai lokacin ya tuna suna tare da mama ya juya baya a hankali inda suke zaune suna karanto duk addu'ar data zo bakinsu domin samun natsuwar zuciya ya sauke wayar a kunneshi "lafiya baba ? mama ta Kira sunanshi hankalinta a tashe tana addu'ar Allah yasa ba wani abu ne ya samu abba bayan fitowarsu ba .
"Wai baba sarki ne yazo yake son ganinku bari na juya, ya soma ƙoƙarin juyawa haɗe da cewa "ke kuma karki sake damuna, dan kukanki yana damun kwakwaluwata ya cilla motarsa kan titi ya figa aguje .
Minti goma sha biyar ne ya kawo ma'hruf gida ,mama da umma da ummita suka shigo ma'hruf na bayansu , Abba na ganinsu ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya gyara daga kwanciyar da yayi ya zauna yana kallonsu zuciyarsa na dokawa hawaye na sake zubowa daga idanunsa ..
Guri suka samu suka zauna bisa ga umarnin baba sarki ,kallonsu
abba yake yana jin sanyi a ranshi su kaɗai suke sakashi farinciki a duniya .
A hankali baba sarki ya cigaba da magana "Rayuwa dai duk yadda Allah ya rubuto babu wanda ya isa ya canza ta, ita kaddara kuma tana kan kowa hajiya ki maida hankali ki,karki bari ki mutu da hakin rayuka da yawa akanki kina abu tun da sauran kuruciya har zuwa yanzu da rai ya kai gargara kina kan abu daya kamar addini .....
" a yanzu dai bazan sake miki nasiha akan abubuwan da kike saboda na gaji da halinki, na gaji da yi miki nasiha , sai dai Allah na ganin komai kuma shi zai hukuntaki bisa abinda kike saboda baki dalili ko hujja na tsanar baiwar Allah nan maryam , babu abinda tayi miki illa tsabar kabilanci dake damunki akanta , tana binki tana miki biyyar da ko hausa fulani da kike son Ibrahim ya aura albarka ,a irin biyayyar da take miki kina ganin da bahaushiya ce zata jura ?
" Sannan yadda kike tunanin da iko da gadarar kina da karfi da iko akan yaran nan haka nima nake dashi a matsayina na kanin mahaifinsu .
Baba sarki ya juya ya dube Abba cikin sarewa yace "ban lamunce maka rabuwa da matarka maryam ba har abada sai da mutuwa ta rabaku haka kaima ma'hruf ka ɗauki matarka ka wuce daita , Kema mairo ki koma d'akinki matsawar zaki fahimceni barinki rayuwarmu ba ƙaramar hasara bace ..
A qalla baba Sarki ya ɗauki kusan awa uku yana magana yayi da mama sannan ya juyo ya dubi hajiya Inna, sannan ya dubi sauran jamar dake gurin a karshe ya mike tsaye duk mazan suka mike Abba zai tashi ya dakatar dashi "kayi zamanka Ibrahim na yafe Allah ya baka lafiya Allah yayi maka albarka , ka daina biyewa shirmen mahaifiyarka saboda babu biyayya ga bawa a gurin sa'bon Allah , ita mahaifiyarka ce kayi mata biyyaya daidai yadda Allah yace amman gurin sakin aure babu wannan biyayyar ko ta tsine maka babu abinda tsinuwarta zata maka gabadaya suka rufa masa baya har hajiya Inna suka bar ummita da Abba da mama .
Mama ta mike ta nufi d'akinta tana kuka tana tausayawa kanta da diyarta a hankali shima Abba ya yunkura da kyar yabi bayanta a bakin gado ya sameta tana zubar da hawaye ya zauna kusa daita ya riko hannunta "ki ƙara hakuri Maryam , nasan kina hakuri dani sai dai ina neman alfarma ki ƙara hakurin , kuma hakurin nan naki ba zai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 57 Chapter of 76