bin bokaye da matsafa kuma idan kika yi wasa shi mijin da kike takama dashi na kwace shi babu boka babu malam naga uwar uban da zakiyi .
",wannan kuma karyaki karamar karuwa mijina yafi karfinki ko da asiri "aiko ummita taji zafin kalmar karuwa data kirata dashi ranta a matukar 'bace tace "ai wacan mahauciyar uwartaki ce ta koya min harka karuwanci ki koma gida ki tambaye , mijikin kuma babu boka babu malam zan kwashe ki zuba ido daga yau zaki ga aikin daya fi na boka tasiri ,tana gama fadar haka ta nufi kofa fita ba tayi parlourn kasa ba ta ta shiga dakin mama ta kwanta akan gadonta ta rushe da kuka "kowa sai ya fadawa baya sona, me nayi maka ya mah'ruf ?
",Me yasa ka fadawa matarka baka sona ?
"nafi matarka komai me yasa bazaka soni ba ?
"Ummita ki natsu ki janyo mijinki gareki koda kuwa baki sonshi zuciyarta ke bata wannan shawara "ki janyo shi ko dan ki nuna wacan matar ita din ba kowa bace
"Ta mike tsaye tana zariya hawaye na zubo mata "zan yi kokari na dauki shawarki kyakkyawar zuciyata ..
A hankali ta k'arasa jikin window mama ta tsaya wasu sabbin hawaye na zubo mata ko cikakken minti goma batayi da tsayuwa ba ta hangi tsayuwar motarsa tana tsaye taga ya kira saifullahi da sauri ta fito daga d'akin zuwa kasa a daidai lokacin da saifullahi ke faɗa suhaima sakon shi "aunty suhaima wai ki fito inji ya mah'ruf mikewa tayi tsaye saboda daman a shirye take ta rataya jikarta tayi wa mama sallama tayi gaba mama ta biyota har harabar gidan ta kawota da tsarabarta cike da leda yayinda tuni ummita tayi nata shirin cikin doguwar riga da mayafin abaya ta la'be a bayan bangaren mahruf tana kallon mama ta juya zuwa cikin gida .
tayi saurin fitowa ta fito wajen gidan lokacin tuni suhaima ta shiga gaban motar yaja suka fice , da hannunta ta tsaida mai mashin "kaga wancan motar zaka bi duk inda tabi kabita "babu matsala hajiya hau muje da kyar ta hau machine din saboda rashin sabo ..
TWO FRIENDS BSBD
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*AUNTY MODA ABUGA*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 45
.... Duk inda motar Mah'ruf yabi sai mai mashin yabi hanyar , yayinda suhaima da Mah'ruf dake zaune cikin motar zuciyoyinsu ke cike fal da tunanin ummita , maganganun data faɗa musu a yau ya bala'in tsayawa kowannensu a rai, idanunsu gabad'aya sun kad'a sun yi jajir tsabar 'bacin rai .
ya ɗan waigo inda suhaima take zaune yaga gabadaya yanayinta ya sauya fuskarta tattare da damuwar da bai san ko ta meye ba ,kamar ya tambayeta dalilin sauyawarta sai kuma ya share ya cigaba da murza sitiyarin mota yana cigaba da tunanin maganganu ummita dana jafar .
Ummita dake zaune zuciyarta na tafarfasa a bayan mai machin tace "malam dan Allah ka dan qara sauri, idan ka isa daidai mazaunin direban motar ka daidaita ta yadda tafiyarku yazo daidai koda na second biyu ne sai ka wuce gaban motar sannan ka dawo baya ka cigaba da binsa a baya "an gama ya fadi haka yana fixgar machin din aguje yayi kamar yadda ta faɗa masa ..
kamar ance mah'ruf ya duba gefen madubin motarsa a daidai jection din depomu express ya ganta zaune a bayan mai machin kamar a mafarki tana hura hanci take gabansa ya fadi ya shiga dukan tara tara ware idanuwanshi yayi sosai domin tabbatarwa kanshi itace ko me kama daita ya gani a bayan wani kato .
Cikin d'acin rai haɗe da bakinciki ya soma rage gudun da yake, ya gangara gefen titi yayi parking sakamakon tabbatar da ita din ce
ya soma dai-dai tsayuwar motarsa domin yaga wucewarsu sannan yabi bayan mai mashin dan sanin inda zata a daidai wannan lokaci
yana gama daidaita tsayuwar motarsa yaga mai machin ya tsaya daf dashi "yauwa gaskiya kana da hankali kuma ka iya aiki ya karkata mata mashin din ta sauka da kyar tana yi masa magana tana tafiya yayinda mai mashin ya soma biyota abaya .
Runtse idanunshi yayi zuciyarsa na wani irin tafarfasa , matarsa ta sunnah ce abayan wani kato , katon ma ɗan okada har da magana atsakaninsu ? Ya ilahil alameena
mamakinsa bai kare ba sai daya ga ta nufo inda motarsa yake , suhaima ta ɗan dubeshi tace "lafiya habibi naga ka tsaya anan ?
Ai ko gama rufe bakinta batayi ba taji ana 'kwan'kwasa glass din motar, da kamar ba zai buɗe mata ba saboda bakinciki abinda tayi , sai kuma yayi tunanin halin da take ciki , ko babu komai akwai cikinsa ajikinta idan wani abu ya samu cikinsa ba zai ji dadi ba, hasalima shine zai yi hasara dan haka yayi kasa da glass din motar idanunshi na kanta cikin doguwar riga sai lokacin suhaima ta fahimci abinda ya tsaida shi , kallon ummita kaɗai sai daya saukar mata da mummunar fadawar gaban da batasan dalili ba ....
Kallota ya cigaba da yi yana jin zallar 'bacin rai mara misaltuwa saboda shigar dake jikinta sun maseefar yi mata kyau bayan bayyanar da surarta da sukayi filli kusan minti biyar ya ɗauka yana kallonta batare da yayi magana ba fuskarsa a haɗe kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa , yayinda zuciyarsa ke kunshe da bakinciki da azaɓaɓɓen kishinta .
Ta lumshe masa idanunta kana ta bud'esu fess akanshi sannan ta juya ta dubi inda mai mashin yake tsaye "ga wanda zai biyaka kudin aikinka ta sake maida idanunta kan mah'ruf cike da yauki tana kad'a masa kwayar idanunta "ka biyasa kudin aikinsa .....
"Akan wani dalili kenan da zan biyasa na aikeki ne ? yayi maganar yana ƙoƙarin buɗe murfin motar zuciyarsa na tuttukin bakincikin mara misaltuwa, yana gama fitowa ya sauke mata yatsunsa biyar a kuncinta "ubanwa yace ki hau mashin din wani kato ?
"ina ma zaki a daidai wannan lokacin ? yayi mata tambayar a matukar fusace jikinsa na rawa tsabar 'bacin ran da yake ciki .
Zubewa tayi kasa tana mai kife kanta bisa kafafunsa ta soma rera masa kuka mai tsayawa a rai wanda da jin kukan kasan na zallar shagwa'ba ne , aiko take hankalinsa ya tashi ya dimauce haɗe da gigicewa ya tsuguna gabanta ya kamo hannuwanta duka cikin nashi ,ta fixge hannuwanta da karfi tana kuka ,cikin bala'i da matsanancin tashin hankali yace "kina hauka ne fatlion me yasa kika fito haka ?
"Kalli yadda idanun mutane ke kanki kowa fa anan ke yake kallo oh my goodness ? ya dafe goshinsa .
"Ina ruwanka da fitowata haka ?
kowa ma ya kalleni ,baka da case dani tunda baka sona baka kaunar kasancewa dani, to ka bar masu sona su kalleni ,ni wallahi na ma fi son suyita kallona dan bana jin haushi bare naga laifinsu sai ma dadi da nake ji idan suna kallona .
Ya sake kai hannunsa jikinta hankalinsa a matukar tashe ta buge masa hannu , ta mike tsaye har dankwalinta na ƙoƙarin zamewa yayi saurin janyo mayafin abayarta yana gyara mata "dan Allah ka rabu dani meye matsalarka dani ne live me alone ta buge masa hannu ya sake matsota da sauri "ke bana son hauka fa ya kike wasa da matsayinki ......
"ga ƙatuwar mahaukaciya can acikin motarka ka baro amman ni bana tare da hauka , batun matsayi kuma kai kasashin dan ni ban san shi ba ,ni dai ka biya mai mashin kudin aikinsa sannan muyi abinda ya kawo ni .
"idan naki biya ba fa ?
"Zaka sha mamaki kuwa dan zanyi abinda sai ka tsaneni gabadaya ,mai machin yaga maganarsu
taki ci taki karewa gashi ba wai yana jin abinda suke faɗa bane bayan ka biyashi kudin aikinsa kawai yake iya jiyowa , hakan yasa ya karaso sosai inda suke "hajiya kina 'bata min lokaci fa gashi yamma nayi ,kuma wannan shine lokacin neman na abinci.
"kaji ko ka biyashi kudinsa ya wuce ko kuma ka sauwake min aurenka anan na bishi a matukar fusace yace "bazan biya ba , kifa kiyayeni fatlion , ba fa ke kadai kika iya zafin kai da zuciya ba , ya kai hannu zai shako wuyanta saboda bakinciki ganin mutane sun fara taruwa akansu har suhaima ta fito daga cikin motar ta tsaya tana kallonsu tayi saurin gocewa tana hura masa hanci .
mai mashin ya rasa yadda zaiyi ya amshi kudinsa ya kara gaba, cikin haka wani mai tireda ya tsallako daga d'ayan bangaren ganin hausawa ne " ki bishi tunda iskanci kike ji dan kosisi bazan biyasa ba, dan ban aikeki daukosa ba kuma wallahi sai kin gane kurenki stupid Kawai ya juya "suhaima shiga mota mu wuce .
"kasan Allah idan kaga ka bar gurin nan abu daya kayi min cikin uku , sakina ko kuma biyan mai mashin ko sanin yadda zakayi dani ban cin haka wallahi babu inda zani kai ma babu inda zaka ta k'arasa maganar cikin kuka tana zubewa ajikinshi "Allah ni sai ka sakeni wallahi na gaji da auranka .......
"Hajiya wai me ke faruwa ne ? Mai tireda ya tambayeta
Ta d'ago daga jikin Mah'ruf hawaye Shabe Shabe a fuskarta kamar wacce akayiwa dukan mutuwa , ta nuna kanta da ɗan yatsanta tana kallon mutumin "ni matarsa ce ta sunah wannan kuma karuwarsa ce ya d'aukota acikin motarsa ban san inda zasu ba ta karasa maganar tana sake rushewa da wani kukan wallahi bazan yarda ka dinga wulakantani saboda wannan karuwar ba ....
"inna lillahi wa ina ilaihi rajiun ya shiga furtawa a fili ,a matukar tsorace mah'ruf da suhaima suke kallonta fuskokinsu ɗauke da matsanancin mamakinta " take gumi ya shiga tsatsafo masa ya dinga kallonta kamar wata sabuwar halitta a gabansa , ta sake maida idanunta da hankalinta ga mutanen dake tsaye agurin "wallahi mijina ne ita kuma wannan ka.....
Yayi saurin toshe mata baki "zan fa miki rashin mutunci kika sake furtawa suhaima wannan kalmar , ta buge hannunsa tana kallon cikin kwayar idanunshi hawaye na tsiyaya daga cikinsu " wallahi kasan yadda zakayi dani , kana kallona Kamar nayi maka karya ita din wannan matar wacece agurinka ?
"wacece fa kika ce ?
ta rausayar idanunta cikin nashi batare da tace komai ba yayinda
suhaima tayi shiru zuciyarta da jikinta na wani irin rawa yau taga bala'in daya fi karfinta ita ake kira da karuwa alhalin da aurenta ?
mai tireda yace "Alhaji ka d'auketa ku tafi gida tunda matarka ce in yaso idan kunje gida kwa sasanta ,naunayen ajiyar zuciya mah'ruf ya sauke ya janyo hannuta "kin san Allah sai na shuka miki rashin mutunci idan ban jefaki cikin guater din can ba zaki sani ne .
"ni dai kome zakayi kayi amman kasan yadda zakayi dani tana k'ok'arin fizge hannunta ya sureta gabad'aya yayi sama daita ta saki ƙara mai sauti tana kiran " ka saukeni tare ta runtse idanunta, tana jiran ta jita cikin quater kamar yadda ya ambata kawai taji ya buɗe gidan baya ya ajiyeta a hankali zuciyarsa na wani irin dokawa da karfin gaske ,ya matso kusa daita ya kamo hannuwanta gabadaya ya rike cikin nashi tare da tsura mata idanunshi "ki zauna karki kuskura ki fito , idan kika fito sai na shakeki kin mutu na huta zaki gane baki da wayo , ki fito idan kin isa ya dawo gurin mutane yana huci kamar zaki ya biya mai mashin kudinsa sannan ya kamo hannun suhaima data dawo tamkar wata mutun mutumi a tsaye zuciyarta da kwalkwarta na wani guri ,ya kalli mutane dake gurin yace "wallahi itama wannan matata ce ta sunah, dukkanisu matana ne ,take mai tireda da sauran mutane sukayi murmushi domin sun fahimci kishi ke damun ummita ...
a hankali ya soma tafiya da suhaima data dawo kamar wata matacciya , yana buɗe gaban mota yaga ummita zaune ta hakince tana cika tana batsewa " ki fito ki koma baya bana ce karki fito ba saboda kin rainani shine kika dawo nan ?
"to ni me nayi ita ta koma baya mana dan nan ne mazauninta yayi shiru yana kallonta .
"Ya mah'ruf.........
ta kira sunanshi tana tsareshi da idanunta na tambayeka mana " auren wa aka soma d'aurawa tsakanin ni da wannan matartaka?
"Ban sani ba idan kika sake min irin wannan banzar tambayar zan tattakaki agurin nan .
"a zuciyarta tace kada Allah yasa ka sani , azahiri kuwa cigaba da maganarta tayi ba tare da ta damu da gargadinsa ba "aurena aka soma d'aurawa sannan na riga wannan matartaka tarewa gidanka amman tsabar makirci yasa aka dawo dani gida a daren farkona , ni bama dawowata gida ne yafi damuna da min ciwo ba kamar aurenka dake kaina ,ya kai hannu zai ciccibota "sai kuwa kin mutu dashi ba dan bazan taɓa sakin ba ..
"kasan Allah wallahi kana ta'bani ka taɓa aurenka ,dan fitowa zanyi na faɗawa duniya ka sakeni saki uku ,na fito nayi zawarcina son raina na kula duk uban da yayi magana idan ma takama nayi aure akan aure .......
"Zan fito dake kuma bazan sakeki ba Allah ya tsinewa wanda ya fasa yin zawarci ki fito da kafafunki tun raina bai gama ɓaci ba ya k'arasa maganar yana huci, suhaima ta karaso garesa ta dafa shi "rabu daita habibi ni na zauna a baya shiga muje kawai idanun mutane na kanmu .
Ummita taja tsaki "aikin banza kawai ni za'a kawowa makirci da bariki da ......
"karki sake ki zagar min mata dan basa'arki bace ,idan ke ba kya ganin mutuncinta ni ina gani .
"ta juya masa keya tana zabgawa suhaima harara "to kayi mata magana ko kaja mata kunne idan ina magana da mijina ta daina saka min wannan banzar rubabben bakinta shine zaman lafiyar dani dan banason shishigi da neman suna ta karasa maganar tana juyowa ...
Ya d'aga hannu zai buge mata baki suhaima tayi saurin rikeshi "haba habibi ka daina biye mata yarinya ce fa ,ummita ta kalleta cike da takaicin kalmar tana jin kamar tace uwarta yarinya ba ita ba amman ta share ....
Mah'ruf ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa "wallahi kin ci darajarta suhaima da abinda zan miki yau yayi shiru yana jan tsaki ....
ta yatsina fuska aranta tace" babu abinda zakayi da ya wuce mari ,shi kuwa idan da sabo na saba har ya zame min man shafawa , yau dai sai kun gane kuranku daga kai har ita .
Tana kallo suhaima ta bude gidan baya jikinta a sanyaye ta shiga ta zauna zuciyarta tamkar ta buga yaja motar da karfi ya wuce ya bar mutane suna fadar albarkacin bakinsu .
"Ni matarsa ce ita kuma wannan karuwarsa ce kalmar ta dinga yawo acikin 'kwa'kwalwar suhaima , sosai ta shiga matsanancin tunanin yadda zatayi da rayuwar ummi .
Tafiya kaɗan yayi taga mai siyar da agwaluma a bakin titi tayi saurin kai hannunta jikinshi "a tsaya zan sha agwaluma , har zai buga mata tsawa ya fasa yaja ya tsaya yayi kasa da glass din motar ya kira mai siyar da agwaluma, ta k'araso "nawa ne wancan karamin kwando ?
"5k ne "okay juyo shi a leda "nifa duka yayi min yawa guda biyar ma ya isa tayi magana a shagwa'be cikin zazzakar muryarta "tafi ki kawo yadda nace miki?
ya fad'awa matar yana ciro wallet dinsa ,ta mika masa bakar leda ya amsa haɗe da mika mata kudi ya ajiye mata a saman cinyarta ya ja mota ,ta buɗe ledar ta ɗauki agwaluma ɗaya zata kai bakinta , ya rike hannunta da sauri "no ki bari sai an wanke "ni dai kabarni na sha kayana haka dan wallahi miyona ya tsinke idan ban sha komai zai iya faruwa dani , dole ya sake tsayawa ya siya ruwan roba ya dibo agwaluma guda biyar ya wanke mata ya mika mata jikinta na rawa ta soma sha tana lumshe idanunta.
motar tayi shiru har suka kawo gidan babu wanda ya sake cewa komai ita kuwa sai shan agwalumarta take tana yatsina fuska ,yayi parking a harabar gidan ,suhaima ce ta soma ƙoƙarin fitowa shima ya yunkura zai fito ummita tayi saurin riko hannunsa cikin nata tana murzawa a hankali haɗe da kafeshi da idanunta da ruwan hawaye ya kodar dasu , ita kuwa suhaima ganin haka yasa ta dawo cikin motar ta zauna tana kallonsu zuciyarta kamar zata buga .
a hankali ummita ta soma hura masa iskan bakinta a fuskarshi da hucin numfashnta , da sauri ya kawar da fuskarshi yana jin wani iri a gabad'aya ilahirin jikinshi ya yunkura cikin sauri zai fita ta sake rikoshi da hannuwanta duka "dawo ka zauna magana zamuyi mai mahaimaci ya dawo ya zauna yana kallonta wani irin kwarjini tayi masa "uhmmmm ina jinki?
cikin wani salo da yin kasa da muryata tace " ya mahruf ........
A yarda ta kira sunanshi bakaramin rud'ashi tayi ba ,cikin Sa'a ta janye hannunta cikin nashi ta d'aura a sama fad'ad'd'en qirjinshi take bugun zuciyarsa ta karu dan har tana jin yadda take bugawa tayi wani murmushi "ka tsaida zuciyarka sosai sannan ka tambayeta menene matsayin subai'a acikinta ,kana ikirarin baka sona amman a zahiri ake gane zallar kishinka akaina ,tsaki yaja yana sauke wani wahalallen numfashi tare da cire hannuwanta "daman wannan banzar tambayar zaki min ?
" Kai kake masa kallon banza , amman ni agurina ba banza bane, yakamata dai ka sauke nauyin dake kanka ka bawa wasu dama ko kuma ka inganta aurenka ,yana sauraronta yana jin kamar ana janyoshi gareta da wasu mahimman farinciki amman bazai iya bayyana su ba ,gara su kare rayuwarsu haka . "tun da bazaka iya inganta damar da Allah ya baka ba ka lamuncewa masu so domin su amfana dashi ....
zuciyarsa tacigaba da dokawa kamar zata tarwatse saboda fahimtar inda maganarta ta dosa , cikin rad'a ta cigaba da maganar da zaka ɗauka kalaman soyayya take faɗa masa nan kuwa bukatar saki take daga garesa.
"why fatlion iyayenmu bazasuyi farinciki ba most especially mama ya kai bakinsa cikin kunneta "zan rayu dake koda bana sonki , janye kunnenta tayi ta zuba masa idanunta tana jin zallar 'bacin rai na ratsata take hawaye ya soma bin kuncinta ji take duk duniya babu mutumin da yake mata tozarci kamarsa , furta kalmar bai sonta akoina baya masa wahala kuma ko agaban waye ,take kanta ya soma sarawa ta kalleshi ta sake rushewa da wani kuka tace "nima ai bana sonka dan baka dace dani ba hasalima baka kai matsayin wanda zan so ba ,idan bazaka rabu dani ba zanyi komai na rabu da kai wallahi ya bud'e baki zai yi magana tayi saurin rufe masa baki da hannunta tana girgiza masa kai alamun kar yace komai dan tasan duk abinda zai fito bakinsa a lokacin ba alkhairi zai faɗa ba.
a hankali tayi kasa da hannunta tana shafa qirjinshi tana magana muryata can kasa .,.
Jikin suhaima na rawa ta bude motar da karfi ta fita tana bugo kofar da karfi sai lokacin ya tuna tana cikin motar "oh my god ya furta " sai kinga yadda zanyi dake yau ya fixge jikinsa ya fito tayi murmushi "kaɗan kuka gani sai na addabe rayuwarku sai na hanaku zaman lafiya ,ta fito da sauri itama "ai baku ga komai ba , yadda suhaima ke d'aga kafafunta da sauri haka shi da ummita ke d'agawa .
Ko taku biyu bata yi da shigowa parlourn ba ,ya risketa da sauri ya nufota haɗe da cewa "dan girman Allah baby kiyi hakuri nasan fatlion bata kyauta ba furucinta sunyi tsauri dayawa ya faɗa yana ƙoƙarin rungumeta ajikinshi sai ganin ummita yayi ta shiga tsakaninsu tana duban suhaima "haba malama yau fa ranata ce a gigice ta kalleta zuciyarta cike da tsoro da firgici "yes na faɗa yau rana ta ce kuma banga uban daya isa ya hanani morar wannan ranar ba , wata nawa da d'aura auranmu amman kullun kuna tare dashi , kin like masa kamar chungum kin hanashi sukuni amman hakan bai hana mu had'uwa boye ba , yau kuwa na rantse da girman Allah ko sama da kasa zata haɗe sai ya kasance tare dani a bayyane sai dai idan mutuwa zakiyi ki mutu ......
Tsawar daya buga mata ne yasa gabadaya ta rude ta juyo a gigice ta rungumeshi ajikinta tana fashewa da kuka cikin damuwa yake sauke numfashi kamar zai yi kuka hannu suhaima ta kai ta fizgota da karfi ta wanketa da mari .
"duk iskancin da kikayi a titi bai isheki ba sai kin yi a gida bari kiji na faɗa miki.......
tasssss tasssss kake ji itama ta sauke mata biyu ajere "how dare you slap me?
"wannan ne kawai zai iya marina na kyaleshi shima darajar aure ne , amman irinki dari suka d'aga hannunsu akaina sai na rama double dinsa, mah'ruf ya riko hannu suhaima yana rarrashita ..
Ummita ta matso kamar zata shige jikinsa "ya Mahruf ta kira sunanshi cikin wani salon murya da ita kanta bata san tana dashi ba ....
Yayi mata banza tamkar ba da shi take magana ba fuskarshi da alamun damuwa ,hannu ta kai jikinsa tana mai tsura masa ido "am talking to you my husband ..
"what the fuck do you want me to do ya fada a zafafe Yana juyowa ? matsoshi tayi sosai ta had'e qirjinshi da nata tana busa masa numfashi " just kill me ta fada atakaice.
" well I have already hate you before so it's normal if I wishi to kill stupid lion like you ya k'arasa maganar yana sake kamo hannu suhaima ya nufi d'akinta ya zaunar daita yana fuskantartata "am sorry suhaima zan san abun yi zan ɗauki mataki sosai akanta ...
"no ka barta plz nima nayi nadamar kulata danayi amman ka barta kawai babu komai na yafe mata ,ya rungumeta ajikinshi "baki taɓa faranta min ba kamar yau, na gode Allah yayi miki albarka baby nah ina alfahari da kasamcewarki matata tace "ameen zuciyarta cunkushe da bakinciki ," ki kwantar da hankalinki bari naje nayi maganinta "nace ka barta dan Allah komai ya wuce "amman da gaske kuna had'uwa a boye daita ?
ya kamo goshinta ya manna mata miss " rabu daita wannan ba gaskiya ta faɗa ba , ko alqurani zaki bata bazata rantse miki akan haka ba , ni dai kiyi hakuri ina zuwa bani minti biyar yanzu zan dawo gareki ya fita, yana fita taja tsaki a ranta tace " zaki san kinyi dani wallahi sai na daydayta rayuwarki sai kinga kashi kince kudi ne ...
Yana dawowa parlourn ta matso kusa dashi kamar zata shige jikinshi saurin dakatar daita yayi a fusace yace "look fatlion kina son tarwatsa min faricikin gidana ko ?
Ta yatsina fuska ," ba magana nake miki ba kika min banza ? ta cigaba da kallonsa batare da tayi magana ba "kinsan Allah ko me zakiyi sai dai kiyi amman bazaki taɓa samu matsuguni acikin zuciyata ba, muje na kaiki part dinki tunda kin kawo kanki ya ja hannuta ta soma turtujewa tana kuka "ni wallahi bazan shiga ba gida zan koma kuma ai nima ba sonka nake ba ,kai ne kake sona tunda gashi kaki rabuwa dani ta fixge hannuta da karfi zata kwasa aguje da sauri ya cafkota jikinsa "inna lillahi wa ina ilaihi rajiun "wani irin wulakanci ne haka ?
"kinga natsu plz ki daina wannan gudun ba'a son masu irin ciwonki na gudu haka fa ,"to kace wasa kake min , tayi maganar a shagwa'be "bazan ce ba kin dawo kenan ta sake ƙoƙarin fixgewa ya matseta gam ajikinshi cikin kuka tace "bayan baka sona kake rungumeni "eh ba'a sonki kuma baza'a soki ba baza'a daina rungumarki ba .
Tasa masa kuka" Allah ka daina fad'awa wacan matartaka cewar baka sona idan ma ya zama dole sai ka faɗa ni ka dinga faɗa min tayi maganar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 76