zuciyar yar'uwata ,kalli kiga yadda hankalin umma yayi mugun tashi ,mama abbanmu da mu kadai garesa ki tausaya mana dan girman Allah ta lumshe idanunta.
"kar ki kawo komai aranki yar'uwata da rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ,umma kice ta zauna dan Allah wallahi zan saki raina zan kwantar da hankalina zan baku farinciki ,bana son abba yaji ko mama zasu tada hankalinsu ,tashin hankalinku shine karin tawa damuwar .
"koma ki zauna menal ,menal tabi umarni umma tana zubar da hawayen tausayin yar'uwarta "umma .....Ummita ta kira sunanta cike da jarumta "na'am ummita me kike so ?"Babu komai umma sai abu ɗaya da nake son kiyi min tayi shiru tana lumshe idanunta "meye shi ummita ki faɗa min muddin bai fi karfina ba zan miki shi ,idan bani da shi zan sa anemo miki shi ?
" Ba wani abu bane umma illa ki saya min , ummah duk runtsi karki bari yaya ya sakeni ko mutuwa zanyi dan Allah ku barni tare dashi saboda nasan a halin yanzu yana cikin duhu da rud'ani bashi da laifin komai , muna zaune lafiya dashi , yana bani kulawar daya dace baya son ganina cikin damuwa duk abinda nake so shi yake min ko a safiyar yau din nan da abun ya faru lafiya muka rabu dashi babu wata matsala atsakaninmu ....
"Karki damu dan wannan mai sauki ne ni kaina nafi son ganinku tare ganin kamar ana cutar dake yasa na gwammaci rabuwarku ..
"Na gode umma sai abu na gaba akwai wata matsalar da nake fama dashi wanda na kasa faɗa masa na kasa fadawa kowa .....
Jikin umma na rawa tace "meye shi wannan? ba nace miki duk abinda ya faru a tsakaninku ko daga matarsa kizo ki faɗa min ba?ta runtse idanunta hawaye na sake gangaro mata lokacin data tuna irin azabar da take sha a hannun suhaima a cikin mafarkinta "kiyi hakuri ummah a tunanina mafarki ne ,a sanina mafarkin alkhairi alkhairi ne akasin haka daga sheidan ne , tun ina daukar hakan a matsayin ba gaskiya bane har nazo na fara zargin suhaima nada saka hannu gurin rasa duk cikin da zan samu ,saboda duk lokacin da zanyi mafarki da suhaima sai na rasa cikina haka duk sanda zan ganta gabana ya dinga faduwa ,zan samun ciki yayi wata biyu zuwa uku da zarar mun hadu daita shikenan zanyita ganinta cikin mafarkina tana gigitani daga karshe sai na rasa cikina zan daina ganita ...
"Haba nima zargin da nake yi kenan shi yasa data shigo tana rawar jiki nayita jin haushinta araina , wallahi na dade ina zargin haka dan dai nasan zargi a musulunci haramun ne , shi yasa ban fito nayi magana ba amman lallai na dade ina tunanin haka tun rasa cikinki na farko idan baki manta ba , cewa kika yi an turoki ta baya ,to wa zai turo ki idan baita ba? Inji cewar meenal ..
"Za'a yi magana a lokacin mama ta hana amman kuwa ta tafka babban kuskure dan wallahi bazai yiwu ba , ita bata haifa ba ,ta dinga rabaki da naki ina wallahi da sake yanzu ma zanje muyi ido hudu daita duk abinda ta kulla tayi maza ta kwanceshi shegu tsinannu masu mugun gado irin bala'i da jaraba ta mike tsaye jikinta na rawa ummita ta sake riƙo hannunta gam "ki sakar min hannu naje nayi mata rashin mutunci ta fixge hannunta da karfi "idan sun gama da zuciyarki mu ba'a gama damu ba ,ta soma tafiya cikin zafin rai , karo suka ci da mama dake ƙoƙarin shigowa dakin ta riko hannunta "muje babu inda zaki mafarki ai ba gaskiya bane, mafarki tace tayi ba ganinta tayi da idanunta ba , ta dawo daita mazauninta "zauna ki samu natsuwa amina banason ki ce mata komai , duk ma abinda mutun yayi Allah yana kallonsa kuma zai maganinsa wannan fadan na Allah ne kuma da kanshi zai kawo karshen komai mu dai mu cigaba da addu'a .
"haba mama me yasa zaki hanani bayan an zalincemu , duk wannan soyayyar da take nunawa mutane na dade da sanin duk makirci ne, suhaima baza taba son ummita ba, ta karasa maganar tana fashewa da matsanancin kuka " aikuwa ta dibo ruwan dafa kanta idan ta hanaki magana ni bata isa ta hanani magana ba , ita kadai ce mutun a duniya ko hajiya inna da bata kaunarta nan duniya bata taɓa mafarkin ta aikata mata mugun abu ba sai ita "ki natsu yaya idan rai ya ɓaci hankalin ke dawo dashi, na rokeki karkiyi abinda za'a zo daga baya aji kunya ,bama haka ba,baba zai iya jin haushi yaga kamar ana zargin matarsa ne ...
"da shi da zargin sun ci tukumar ubansu kin san Allah sai na fito mata a mutun sak ,kuma muddin ina raye ummita ce zata kasance tsohuwar gidan baba sai dai mutuwa ta rabu su ,ina dalili wannan maseefa shekara da shekaru yarinya tana cikin bala'i iri iri daga wannan sai wannan , har sai yaushe zata samu kwanciyar hankali wani sihirtaccen numfashi ummita ta sauke zuciyarta fess da jin furucin umma dan bata son rabuwa da mijinta ,a yanzu ne ta fahimci irin matsanancin son da take masa da arabata dashi gara an rabata da numfashinta ,hajiya umma ta sauke kan ummita akan pillow "ki kwantar da hankali ummita babu boka babu malamin da zan kaiwa sisi kwabona dan ubanta da kanta zata kwance daurin data yi tana gama fadar haka tayi waje ..
Mama ta biyota da sauri ta sha gabanta "ina mai had'aki da girman Allah karki ce mata komai ,dan darajan fiyayyen halitta karki mata magana ba girmanki bane suhaima fa suruka ce bai dace kiyi mata magana da irin wannan sigar ba, idan ma maganar ya zama dole ki barwa aunty komai banason kiyi mata magana da kanki ..
Hajiya umma ta dubeta tana girgiza kai sannan tace "idan kina tunani suhaima suruka tace to kin yaudari kanki maryam saboda ni ban d'auketa a matsayin suruka ba , dan babu wani d'ana da take aure ko mah'ruf dana ne ? Ta yiwa mama tambayar tana tsareta da idanunta ,
Mama tayi saurin girgiza mata kai ,"mah'ruf d'anki ne dan haka kece surukar suhaima bani ba , dan haka dole nayi magana akan zaluntar diyata da akayi ta raba ta gefenta zata wuce mama ta sake tareta ta rikota " shikenan duk naji amma ki barta dan Allah , banason hajiya inna taji abun ya dawo wani abu daban ,karshe komai yazo ya dagule ,ki taimakeni ki bar maganar nan dan girman Allah ....
"Muyi addua shine mafuta garemu, babu abinda zai samu ummita da baba sai da izinin Allah ,addu'a kuma bata faduwa kasa banza sai dai jinkiri, jinkiri kuma alkhairi ne dan Allah kiyi hakuri yaya ta k'arasa maganar kamar zata yi kuka.
"shikenan shikenan bance kimin kuka ba ,na bar maganar amman zan nemi aunty mu tautauna ...
Ta wuce zuwa part dinta ita kuma mama ta koma dakin jikinta a sanyaye , a parloun hajiya umma ta wuce suhaima zaune ko kallon inda take batayi ba ta fice ,tana shiga d'akinta ta iske mah'ruf kwance lullu'be cikin bargo , ranta a bace "tace kwanciyar uwar me kake min a daki ?"Ka gama shuka rashin mutuncin shine ka lalla'bo kamar mutumin arziki kazo ka kwanta min a daki maza maza ka tashi ka kama gabanka bana son ganin wannan fuskartaka ta karasa maganar tana tashinsa "maza ka tashi ka ɗauki wacan matartaka ku bar mana gida sha sha mara tunani ..
Ya bude idanunshi da kyar yana furzar da iska mai zafi sannan ya yaye bargon ya mike zaune yana duban Hajiya umma zai yi magana tayi saurin dakatar dashi da hannunta "ban son jin komai daga bakinka ,ni dai ka tashi kaje , ya mike da kyar kanshi na wani irin sarawa ya fice ..
*****
Daren ranar daga mah'ruf har ummita babu wanda ya runtsa illa juyi kawai da suke yi cike da matsanancin tunani kala kala ,yayinda bangaren suhaima ta rasa inda zata sanya ranta dan dadi murna ganinta ta kusan raba mah'ruf da ummita ya hana ruhinta sukuni idan ma batayi nasarar rabasu ba zata yi nasarar haddasa zazzafar kiyayya mai karfi a tsakaninsu ,a duniya babu macen data tsana take son ganin bayanta kamar ummita, bata kaunar bude ido ta ganta tayi wani juyi cike da farinciki ta mike zaune lokacin aiwatar da nufita yayi "sai nayi nasarar wargaza komai naki wannan ciki kuwa shine zai zamo ciki na karshe da mahaifarki zata dauka tare da mah'ruf dan bazai kara kusantarki ba har duniya ta nade , ni kuma na zauna naci karena babu babbaka tayi shewa haɗe juyi ta nufi gurin tsafe tsafenta a lokacin da ummita ke kwance tana ambaton sunan Allah
Washegari
da zazzaɓi mai zafi ummita ta tashi saboda idanunta da basu samu damar runtsawa ba har garin Allah ya waye da zarar ta bude idanunta suhaima zata gani sai tayi saurin budewa tana addu'ar neman tsari , tana jin ana kiran sallah a masallacin dake bakin get din small london , ta kasa tashi saboda nauyin da jikinta yayi , ga zafin zazzaɓi ga mararta da kanta dake wani irin matsanancin sara kamar ana buga mata guduma sai da mama ta farka ta taimaka mata, ta tashi ta kaita bayi da kanta tayi mata alwala ta dawo da ita daki ta zaunar daita akan dadduma domin tayi sallah a zaune ,sannan ta koma bayin ta d'auro alwala ,tazo kusa daita ta tadda sallah anan ummita ta zube ta kwanta akan dadduma dafe da mararta tana runtsa ido tunani take yi "to me ya had'ani da ciwon mara kuma kodai ciki gareni ban sani ba ?tayiwa kanta tambayar "babu shakka ciki gareni tunda har naga suhaima na min gezo shiru tayi tana zurfafa tunaninta tun farkon wata yakamata naga aladata gashi har watan ya mutu, yau goma ga sabon wata babu tantama ciki gareni "yanzu ya zanyi na tseratar da cikina daga sharrin suhaima ?
koda mama ta idar da Sallah bata koma ba ta dade zaune tana addu'a Allah ya tsare mata yaranta daga sharrin suhaima kuma Allah ya bayyana gaskiya ..
Bangaren mahruf shima bai tashi ba har sai da suhaima taje d'akinsa sannan ya tashi ya shiga toilet wanka yayi da alwala koda ya fito tana zaune tana jiran fitowarsa ganin kamar Sallah zai yi ta mike jikinta na rawa ta shimfida masa abun sallah , duk da cewar akan kunneshi akayi kiran sallah bai samu damar tashi ba , cikin kwana ɗaya yayi zuru zuru ya zabge yayi wata ƙatuwar rama ta ban mamaki ,shima da matsanancin ciwon kai ya tashi saboda kwana tunani yana saka da warwara abinda ummita tayi masa ,ya rasa a wani muhalli zai ajiye ,tunanin zama daita ko rabuwa daita yake acikin zuciyarsa yana son sakinta ya hutawa zuciyarsa yana tunani, idan ya rabu daita yaya zai yi da matsanancin kaunar da yake mata ?
"Kin cutar dani subai'a amman idan ban sakeki ba zan shayar dake mamaki ,sai kin gwamaci rabuwa dani akan rayuwa dani kai ma hafiz sai kayi daka sanin shigo min gida zan ɗauki mataki akanka , sai da suhaima ta takura masa sannan ya karya bayan ya ɗan tsakuri abinci ta d'auko masa brief case d'insa ta rako shi har waje ya shiga mota ya tayar ya wuce sannan ta dawo ciki cike da murna duk wanda ya ganta ba sai ya tambaya ba yasan tana cikin farinciki kai tsaye police station ya nufa ya nemi ganawa da dpo bayan dogon bayani ya bada cikakken address din da za'a ga hafiz sannan ya wuce Koda office,ko daya je office ma kasa aiwatar da komai yayi ya faɗa duniyar tunani mai zurfi a hankali idanunsu suka cicciko da ruwan hawaye "ina matsanancin sonki subai'a idan na rabu dake mutuwa zanyi ya rabbi ka gaugauta daukar rayuwata na huta ......
Yan sanda basu samu matsala gurin cafke hafiz almustapha ba suka fara tuhumarsa akan laifinsa ..
ummita haka ta wuni da tunaninsa da ciwon mara , ta kasa raba zuciyarta da tunanin mijinta duk yadda zuciyarta ke son ganin laifinsa taki yarda, sai dai idanunta har lokacin tsiyayar hawaye yake , bata son abinda zai rabata da mah'ruf dinta a kwana ɗaya tal da tayi babu shi tasan tayi missing dinsa "wayyo Allah idan zaka jarabeni ka jarabeni gwargwadon imanina, Allah kada ka rabani da mijina yana sona ina sonshi ,ya Allah ka tausaya min ka bayyanawa mijina gaskiya tana kwance akayi kiran sallar azahar babu kowa a dakin duk suna parloun a tunaninsu ko bacci take ta runtse idanunta da kyar ta lalla'ba ta sauko daga kan gado ta shiga bayi ta dauro alwala ta dawo dakin tayi sallah a zaune ta jingina da gado idanunta na kallon celling d'akin .
Da misalin karfe uku daidai suhaima ta shigo gidan , ummita dake zaune a d'akin mama taji qirjinta yayi wata irin bugawa da matsanacin karfi take kasan mararta ya dauki rawa ,a hankali ta mike ta shige bayin mama ta kulle tayi zamanta dan bata don hada ido da suhaima jin muryarta kadai na dagula mata lissafi bare ganinta .
Kusan min goma tana zaune qirjinta na bugawa da karfi bata fito ba ,sai dai rawar da jikinta ke yi yasa cikinta da mararta da bayanta ya dinga sarawa ,a hankali taji wani abu mai sanyi na zubowa daga kasanta cike da fad'uwar gaba ta tsuguna domin dubawa idanunta ya ci karo da jini wata irin razananniyar ƙara ta saki tana durkushewa bisa gwiwowinta a daidai lokacin da aunty ta shigo d'akin ta matso jikin kofar bayi tana kiran sunanta "shikenan shima wannan zubewa zai yi ya barni ?
" ya rabi Allah ka taimakeni ka taimakeni kar na rasa wannan ciki wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska "ummita ! ummita !!
aunty ta shiga buga kofar da karfi tana kiran sunanta "me ya sameki ki bude kofar ?
A hankali ta soma rarafawa ta bude kofar ta zube a kasa aunty ta shigo jikinta na rawa ta rungumeta "menene ?Kai kawai take juyawa da kyar tana ciza gefen bakinta ta mike da sauri zata fita ta riko hannunta "aunty ci....ckina .........
"Bari a kira doctor husain yazo ya dubaki a hankali ta shiga girgiza mata kai "ai ya fita ....ta faɗa cikin mayunwacin hali gaba-daya aunty ta rud'e ta gigice ta rasa gane inda maganarta ta dosa , suna cikin haka mama ta shigo "lafiya aunty halan jikin ne ?
"Wai cikinta kuma wai ya zube na rasa gane kan al'amarin ka mota mu kaita daki sai akira doctor husain suna kokarin d'agata idanunsu ya sauka akan jini dake bin jikinta dan tuni ya gama bata mata kaya "subuhanallahi mama ta furta aunty kuwa Gabadaya rudewa ta sake yi " daman ciki gareki duk wannan bala'in da'ake ?mama ta kasa cewa komai ta fice ranta a matukar bace hawaye na zubo mata a karo na farko ta zubar da hawaye akan zubewar cikin ummita abakin gado ta zauna ta kira mah'ruf yana ɗauka tace "kazo yanzu ina son ganinka ta kashe wayar tare da rafka tagumi ...
Ummita kuwa da kyar ta bude baki tace "nima bansan ina da ba amman tunda naga suhaima jiya tana min gezo na sha jinin jikina sai a lokacin nayi tunanin banyi period dina last month ba , yanzu kuma ina jin muryarta gaba-daya komai ya kwance min dan Allah aunty ki barni anan har ta wuce bana son ganin fuskarta ko jin muryarta "ai kuwa zata ci bantal ubanta daman yanzu hajiya umma ke koro min abinda kika faɗa, kenan dai gaskiya tana da saka hannu ciki ta soma gyarata tana tunani irin tujarar da zatayiwa suhaima.
bayan aunty ta gyara ummita tsaf ta ta nufi parloun mama inda suhaima ke zaune cikin mutane " ke munafukar Allah daga yau kar na sake ganin kafafunki acikin gidan nan suhaima tayi sororo tana kallon aunty fuskarta dauke da tmbya "ko baki ji abinda nace ba kar na sake ganin waɗan kafafun naki , abinda baki sani ba duk mun san mugun nufinki akan ummita amman da yarda Allah komai yazo karshe maza tashi munafuka mai mugun hali da mugun gado , tana gama fadawa suhaima haka ta fashe da kuka "me nayi aunty duk kokarina bakwa gani ?
Daman nasan zargina kuke "eh bama gani saboda munafurci ne idanunta ne ya sauka akan mah'ruf ta matso ta rike hannunsa "habibi kayiwa aunty bayani zata fi fahintarka meye nawa acikin rigimarku da ummita da har za'a zo ana zargina ? Ka faɗa musu babu ruwana aciki rigimarku kuma kar asakani aciki..
Ya zare hannunsa yana watsa mata wani mugun kallo "kiyiwa mutane shiru aunty sa'arki ce da zaki dinga maida mata martani kar na sake jin bakinki , ta ɗauki jakarta ta fice a fusace tana bugo kofar parloun da karfi "ai kaga irin matar daka ajiye agidanka kana zaman zamanka ka kwasowa kanka irin bala'i ?
"Matar rufin asirinka kuma kana neman yin sakainan kashi daita wallahi kayi gangancin sakin ummita sai ka dawo abun tausayi ta juya ta barshi tsaye ta koma gurin ummita .
Da sallamarsa ya shigo d'akin mama ,bai ganta ba sai ummita dake kwance da aunty dake aikin jero mata sannu ,ya tsura mata idanunshi qirjinshi na dokawa itama akaci Sa'a ta waigo idanunsu suka tsarke cikin juna a qalla sun ɗauki minti goma suna kallon juna sannan ya juya ya fita , a bakin kofa suka haɗu da mama "har ka k'araso ?
"Ya daga mata kai kawai , "kaje bangaren abbanka ka jirani gani nan zuwa "to kawai ya iya cewa dan haka nan yaji gabansa na faduwa yana zaune shiru ta shigo ta samu guri ta zauna suna fuskantar juna gabansa ne ya cigaba da faduwa ya mike tsaye ya dawo gabanta ya zauna ya tankwashe kafafunsa ya tsura mata ido, mama ta tsura masa ido sannan ta soma magana a tsanake "na kiraka ne saboda na kawo karshen dukkanin wata damuwa dake tsakaninka da ummita ya runtse idanunshi yana cigaba da sauraronta "ina son ka sawwakewa ummita auranka dake kanka bisa umarnina ya d'ago a gigice yana duban mama hawaye cike da idanunshi "me kika ce mama naji wata magana ta fito daga bakinki me kama da almara ...
"Ba alamara bane abinda kaji na faɗa gaskiya ne Ina son raba aurenka da ummita amman da sharadin bana son kowa ya sani har zuwa wani lokaci zan tura ummita kwatono kai kuma ka cigaba da rayuwa da matarka nayi rayuwa kunci a gidan nan na sha wuya na jure bakinciki iri iri amman bazan juri ganin ummita cikin irin rayuwa da nayi ba ,duk hakurin da nayi shekara da shekaru saboda ita ne rabon haihuwarta da kuma rainonta ...
A hankali ya shiga girgizawa mama kai "ka daina girgiza min kai zaka iya tunda ka furta hakan a bayyanan nasi daga ni sai kai ne bazaka iya ba "yayi shiru yana kallonta zuciyarsa na dokawa bai san ta ina zai fara ba ,ta yaya kuma ta ina zai fara furtawa mama sakin ummita ..
Ba tukuicin sakin ummita ne ya kamaceta ba ,wani irin tausayinsu kansu ne ya rufesu ya gyara durkushe a gabanta ya kamo hannuwanta duka cikin nashi yana Kallonta jikinsa na kyarma ....
TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*HAJIYAYYE UWAR GIDAN ALHAJI BASHIR*
MY YOUTUBE CHANNEL
*HAUSA BAKWAI*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 68
...ganin yadda jikinsa ke kyarma yasa mama ta mike tsaye tare da juya masa baya qirjinta na wani irin luguden bugu , yayinda zuciyarta ke cike da zullumi da tashin hankali mara misaltuwa , jikinsa na cigaba kyarma ya juyo zuwa inda take tsaye yana kallon bayanta zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfi ,
ya rarrafo zuciyarsa na wani irin kokawa da tsalle ya rike ƙafafuwanta da hannuwansa duka muryarsa na rawa ya soma magana "dan Allah mama karki min haka , karki rabani da sanyin idaniyana, wallahi ina son subai'a so mai girma son da ban taɓa yiwa wani mahaluki irinsa a duniya ba , idan babu subai'a a cikin rayuwata zan iya rasa raina , bazan iya rayuwa babu ita ba ,ina tsananin sonta mama musamman a yanzu da nake hango soyayyata a cikin kwayar idanuta ya k'arasa magana zuciyarsa na wani irin zafi ....
A tsanake mama ta juyo tare da zuba masa idanunta "kai ne fa kace zaka iya rabuwa daita a bayyanan nasi ,ka zabi rayuwa babu ita , a gaban kowa kayi wannan furucin ko karya ne ? jikinsa na rawa ya shiga girgiza mata kai yana daura yatsan hannunsa akan lip's d'insa zuciyarsa na sake shiga cikin wani sabon cakwakiyya mara misaltuwa har lokacin gangar jikinsa rawa yake .
"mah'ruf........
ta Kira sunanshi direct yayi shiru zuciyarsa da idanunshi na kan Kallonta " bazan boye maka ba naji ciwon da rad'ad'in wannan abu daka aikata ga ummita , naji zafin abinda kayi ,karo na farko da naji babu dadi a raina akan ka aikata wani abu gareta , bazan iya misalta maka irin duhun da zuciyata ta tsinci kanta ciki a lokacin da kake fadar ka ka kamata dumu dumu da laifin aikata alfasha ba , bazan iya jurar ganin ummita cikin mawuyacin hali irin wannan ba, abu mafi alkhairi shine ka sawwake mata aurenka dake kanta zuciyar kowa ta huta da damuwa , sannan ka samu hajiya inna ka faɗa mata ka tabbatar mata da cewar ka sauke aurenka dake kan ummita ita kaɗai na yarda ka faɗawa domin ruhinta ya samu salama ta daina bakinciki tarrayarku , ni kuma nayi alkwarin zan nisantaka da ummita har bada tun da baka son ganinta cikin farinciki ......
Wasu hawaye masu tsananin zafi da ciwo da rad'ad'in suka zubo masa da rawar murya yace "na san na san na 'bata miki rai mamana tun da gashi har kinyi magana da bakinki abinda baki taɓa yi ba ko nuna fushinki akan komai da zai faru ,sai dai kar ki qalubalanceni so ne wallahi .....
"son subai'a da matsanacin kishinta ne yasa na fadi haka amman wallahil azim ba abinda yake cikin zuciyata ba kenan , da banasonta a yadda na dinga jin a zuciyata lokacin da idanuwana suka gane min hoton hafiz a d'akinta akan gadonta da tuni na rubuta mata takardar saki ya kare maganar yana zubar da kwalla mai zafi yana jin zafi abinda ya faru a qirjinsa ..
"Bafa zan lamunce da haka ba gaskiya azo daga baya ana zaman doya da manja , bazan iya cigaba da ɗaukar wannan nauyin ba, ko da amincewar ummita ko babu zan rabaku domin zaman aure ba zai yiwu da zargi ba " na faɗa maka ba dan ummita tana diyar cikina ba nasan halinta ba zata taɓa aikata abinda kake zargi ba ,yanzu dai na kawo karshen zargi da komai Allah yasa haka shine mafi alkhairi a tsakaninku ,zaman auren da kukayi Allah yasanya masa albarka rabuwarku kuma Allah yasa shine alkhairi a rayuwarku .
gabansa ya cigaba da fad'uwa jikinsa na rawa ya sake rike kafafunta gam "dan Allah mama karki yanke wannan hukuncin ki bani lokaci ........
ta zubawa bayansa ido "abun al'ajabi wai mah'ruf dinta ne yau yake irin wannan marairaice wa yana zubar da hawaye akan son ummita ? bata gama mamakinsa ba taji sautin muryarsa "mama ki fahimceni hukunci da kika ɗauka akaina yayi tsauri da yawa ,ki bari mu fahimci juna da matata nasan tana sona bazata so rabuwa dani ba, bai kamata a rabani da matata ba alhalin muna son juna "menene amfani zama da matar da kake zargi ?
"Kiyi hakuri nayi nadama da danasanin amincewa zuciyata, kishinta ne ya rufe min ido yasa na kasa gane gaskiya, cikin tsananin al'ajabi da mamaki mama ta sake tsura masa ido yayinda idanunta ke zubar da hawayen tausayin kanta da diyarta ba " Banyi tsamani zaka iya rufe idanunka ka dinga farfad'a mugayen magangun da kaga dama agabana ba , a yadda muka zauna tsawon lokaci da kai ,ina iliminka da tunaninka suka tafi ?
Ya kamata kayi wa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 71 Chapter of 76