"kuma ita yarinyar ma da kake ƙoƙarin illata zuciyarka akanta bata sonka , hasalima baka cikin tunaninta ,kayi hakuri ka raba zuciyarka da soyayyarta , idan so cuta ne ai hakuri magani ne , duk kabi ka canza akan common mace ,macen ma da bata sonka .......
" ni yaushe zan iya wannan wahalalliyar soyayyar ya matso kusa dashi sosai ya dafa kafad'arsa " haba kamar ba muhd Sa'id din dana sani ba mai manyan yammata , kana fa da budurwar data fi ummita komai ka rabu daita ka hutawa rayuwarka .....
Sai lokacin muhd Sa'id ya d'ago kwayar idanunshi ya dubeshi zuciyarsa na wani irin harbawa da kyar ya buɗe bakinsa " wallahi babu kamar subai'a acikinsu , subai'a ta daban ce acikin matan duniya a zuciyata , amman zanyi hakuri tunda abun ya kai ga haka , sai dai kasani bazan taba daina son subai'a ba a rayuwata muddin rai ina tare da kaunarta .
" waɗan kayan kuma bazan ɗauki ko ɗaya acikin su ba, ya buɗe motarsa ya ciro wasu kayan, manya ledodiji ne guda huɗu har da karami guda biyar ka haɗa mata dasu duk na bar mata ,ba kaya ba ko zuciyata ce a hannunta bazan iya amsa ba bare wasu kayan banza ..... ..
Tausayinsa ya cika zuciyar ma'hruf , sosai zuciyarsa ke mamakin taurin zuciya irin na muhd Sa'id akan ummita , ina ma tana son shi ?
"Ina ma Abba bai yi mata miji ba tabbas da tayi sa'ar samu nagartacce miji a rayuwarta ya yarda ya amince da irin kyakkyawar soyayyar da yake mata , a kallon da yake masa yasan yana matukar bukata da kaunar ummita arayuwarsa , irin namijin da kowace mace take fatan samu kenan namiji da zai soka da d'aukacin rayuwarsa .......
Ya runtse idanunshi na second biyu sannan ya buɗe cike da tsananin tausayawa sai dai hakan bazai hanashi ya fahimtar dashi gaskiya ba "Muhd Sa'id ka ɗauki kayanka kaga wanda ka kawo kwanaki ma ba'ayi amfani dasu ba ,matukar ka bar kayan nan ni zaka kulle ciki tashin hankali ..
muhd Sa'id bai ce masa komai ba , ya k'arasa ya shige motarsa ya soma ƙoƙarin tayarwa "duk ma abinda zai faru da kai ya dade bai faru ba amman bazan ɗauki kayan ba , ya tashi motarsa mai gadi ya buɗe masa tangamemen get din gidan ya wuce a guje ya bar ma'hruf tsaye yana kallon get ....
Sadik da sadam ma'hruf yasa suka sake d'aukar kayan zuwa d'akinsa tun Abba bai dawo ya gansu ba sannan ya nufi bangaren inna yana huci gabad'aya ya rasa me zai yi .....
Yana shiga ya iske hajiya inna zaune tana shafawa goshinta man aboniki "lafiyarki inna ? Ya faɗa da sauri kuma hankalinsa a dan tashe saboda ganin yadda take mulkawa goshinta man zafi .
"Lafiyar nan dai da sauki babana kaina ke ciwo kamar ya cire tun jiya "
Ya zauna akan kujera yana fuskantarta "to ko asibiti zamu a duba min lafiyarki ?
"Mu bari dai zuwa gobe mugani idan banji sauki ba sai muje "
"Yauwa babana ni kuwa ina son nayi maka wata magana akan aurenka "
ya gyara zama tare da ciro wayarsa daga aljihun wandonsa "ina jinki iya rigima .
"wacan dangin agumuwar uwar taka ce iya rigima bani ba ",to ya isa Karki zagar min uwa a canza magana ina jinki "
"Yanzu kai me yasa ka zabi auren mata biyu da kuruciya ?
Ya lumshe kyakkyawan idanunshi cike da takaici , inna ta tsotsa masa inda ke masa kykyai a dan fusace yace " wa yace miki ni na za'ba ?
"Iyayenka mana nan suka zo suna babatunsu abu kamar a garin mahaukata.
Ya ja tsaki sannan yace "bani nace zan aureta ba sune dai suke son hadin amman ni me zanyi da wata sakina "
"haba abun kam da mamaki ace kai ne kace kana sonta nasan da wuya , shine kai kuma ɗan munafurci ka amince da zaka aureta ?
"To ya zanyi da iyayena inna ? ya bata amsa yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa ...
"A'a babu wani zance ya zakayi ko kana sonta zabar ɗaya zakayi a cikinsu ko sakina ko ita wacan yarinyar "
"Sai gashi kuma bana sonta ba ,bare akai da zance zaba ,wallahi inna bana sakina bana jin sonta a zuciyata zan dai aureta ne kawai saboda umarnin iyayena ....
Hajiya inna ta tabe baki "A she kuwa zakayi auren takaici baka son mace zaka yi wani zaman aure daita tayi maganar tana kwa'be baki bare babu komai acikin auren mata biyu sai ciwon hawan jini .
"Ki ajiye wannan zance dan na dade ina jin haka ajikina , ko ban auri sakina ba zan ƙara aure a nan gaba "to ai shikenan Allah ya sanya alkhairi kaine zaka tsufa da wuri ai , haka kurum da kuruciyarka amaida kai tsohon karfi da yaji "ke wa yace miki auren mata biyu yana tsufar da mutun ?
"Babu wanda ya faɗa nice naga misali akaron kaina kaga mai sunanka har ya koma ga Allah bazakace shekarunsa sun kai saba'in ba saboda yanayin jikinsa to babu hawan jini babu ciwon sugar a jikinsa nima kuma bai had'ani daita ba dagani sai ni, murmushi mah'ruf yayi saboda ya fahimci inda zanceta ya dosa "nan suka cigaba da hirarsu har bakwai saura ya mike ya shiga bayinta ya dauro alwala ya fita zuwa massalaci .
bai dawo gidan ba sai bayan isha'i, kai tsaye bangaren mama ya shiga domin cin abinci yana shiga da ummita idanunsa ya soma yin tozali tana shirya dining table sanye cikin wata atamfar cotedevo mai ruwan blue da zane fulawa mai ratsin baki , tayi kyau sosai sai sheki fuskarta keyi , kallo second biyar yayi mata ya ɗauke idanunshi akanta yana lumshe idanunshi dan baya son yawon kallonta hakan na haddasa masa shiga wani hali .
yadda bai sake kallon inda take ba haka itama bata sake kallonsa ba , ya dauki remut ya samu guri akan kujera ya zauna tare da canza chennel zuwa aljazera ya soma kallon labarai yana jin wani iri a gaba-daya jikinsa wani sanyin shauki ke ziyar gangan jikinsa yana tabo masa emotion din da yake ƙoƙarin dannewa acikin zuciyarsa .
A hankali take tafiya tana rausaya wanda ya zame mata jiki har tazo ta wuce ta gabanshi kamshin sanyayyiye turarenta mai tsuma zuciya ya kaiwa hancinsa ziyara , dole ya lumshe idanunshi ba dan yaso aikata hakan ba ya d'ago da niyyar satar kallonta itama akaci sa'ar zata saci kallonsa idanunsu ya sarke cikin juna , a lokaci daya suka ɗauke idanunsu ta cigaba da tafiya ya jan tsaki a fili " an sani ake take sani ,hukunci wanda ya sani ya take yafi wanda bai sani ba ......
Ta ɗan tsaya jimmmmm tare da juyowa domin ta ga da wa yake magana, ganin babu kowa sai ita yasa ta fahimci daita yake , bata ce masa kala ba ta tsura masa fararen idanunta masu bala'in kashe masa jiki a duk sanda ya kalli cikinsu tana kallonsa zuciyarta na wani irin tsalle tana nazarin maganar da yayi yanzu , shima kallonta yake fuskarsa babu yabo babu fallasa , a hankali ta juya abunta ta cigaba da rausaya qirjinta na dokawa ya sake jan tsaki yana takure jikinsa saboda wani sanyi daya ziyarci ilahirin jikinsa har ta 'bacewa ganinsa bai daina jin abinda yake ji akanta ba , a hankali ya dinga fidda numfashi haɗe da sauke ajiyar zuciya qirjishi na sama da kasa yana ƙoƙarin kawar da abinda yake ji .....
yana zaune yana felling abinda bai san ko meye ba da dalilin jin haka ya rayhan ya shigo, yana ganinsa ya saki fuska yana murmushi haɗe karasowa ya mika masa hannu suka gaisa ya samu guri ya zauna yana dan jan mah'ruf da hira "Mah'ruf meye shirinka ne akan bikinmu ?
Ma'hruf ya gyara zama ya kwanta akan kujera "kai shirin biki ya dama , ni dai kawai a shafa fatiha shine babban burina "haba dai ko bakayi komai ba nasan abokanka zasuyi "wannan kuma damuwarsu ce ba tawa ba "Nan kawar da batun aure suka cigaba da hirar kwallo atsakaninsu cikin haka ummita ta sauko tare da mama ,suna ganinta kowanensu ya gaisheta cike da girmamawa ta amsa cikin sakin fuska ",sannuku yarana ya weekend ?
Duk suka amsa mata da " lafiya "
my princess zubo mana abinci ni da d'an'uwana mun kwana biyu bamu ci abinci tare ba muryar ya rayhan taji ,
take tayi hanyar dining tana ciccin magani tace "ka jika da shishigi da neman suna shi yace maka zai ci ne ko kuwa shishigi zakayi masa ?
" zuba mana tare .....
On-expecting taji saukar muryar da batayi tsamanin ji ba ta doki cikin dodon kunneta da zuciyarta wani irin zirrrrrrrrrrr taji a gaba-daya ilahirin jikinta mai kama da shokin ,take jikinta yayi sanyi "ai shikenan tunda kinji daga bakinsa sai ki kyale min yarona ki daina zakewa mama ta fad'i haka tana barin parlourn zuwa part din Abba ...
Ummita ta rausayar da idanunta sannan ta soma zuba musu abinci tare kamar yadda rayhan ya faɗa ,ta saka musu spoon guda biyu, duk abinda take gabanta na faduwa haka jikinta na rawa tana jin yadda idanunshi ke yawo a sansar jikinta sai dai da zarar ta d'ago sai taga ba ita yake kallo ba .
a hankali take takowa zuwa tsakiyar parlourn inda center cafet yake ta ajiye plet din abinci still tana jin idanunshi akanta da yadda yake jan tsaki akai akai , ta koma ta d'auko musu ruwa da lemo mai sanyi ta kawo musu duk tana jin wani irin ajikinta ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba kallonta ya mah'ruf yake sai dai abun mamaki idan ta d'ago sai taga idanunshi na kan tv ko waya ko yana jan tsaki "yauwa my princess shiyasa nake ..... ..
wata uwar hararar Mah'ruf ya banka masa take ya katse abinda yayi niyyar cewa muryarsa can kasa yace " kaga malam idan kasan wannan shirmen zakayi tun wuri na kama gabana?
"kai fa matsalata da kai kenan girman kai wallahi me nayi wanda ba daidai ba yanzu da har zaka .....
"ya isa dan Allah malam banason dogon magana ya d'aga masa hannu bai sake cewa komai ba ya soma cin abinci yayinda ummi ta juya zatabi bayan mama , rayhan ya dakatar daita "my princess ki dawo ki zauna kusa dani ina ci kina ɗebe min kewa "oh my Goddess god rahyan wai meye haka ne saboda Allah?
"Shiyasa kullun yara basa ganin mutane da daraja ku tasa yara kanana a gaba kuna zuba shirme ya karasa maganar yana mikewa tsab yayi hanyar fita "to ka tsaya muci abinci mana banza yayi masa yana jan tsaki ummita dake tsaye a kusa da kofar fita tayi saurin matsawa kar ya sauke fushinsa akanta qirjinta na matsanancin bugawa da karfi ,har ya rabe ta gefenta ya bar parlourn hankalinta bai gangar jikinta .
haka nan ta tsinci kanta da rashin jin dadi fushin da yayi ,ta juyo ta fuskanci ya rayhan ,"kai ma kasan halinsa abu kaɗan ke hassalashi me yasa kayi magana gashi kasa yayi fushi da abincin ? Tayi maganar kamar zatayi kuka
Rayhan yayi shiru tare da tsura mata ido yana kallonta yana mamakin jin furucinta , abubuwa da yawa ya gani a tattare daita wanda ya kasa fahimtarsu daidai "yau ummita ce ke jin haushi dan ran mah'ruf ya baci ko me ?
Ganin irin kallon tunhumar da yake mata yasa ta kasa fita ta dawo kusa dashi ta zauna " kaci abincinka mana ka tsaya kana kallona kasan dai idan kaima baka ci abincin nan ba kuka zanyi wallahi ,dan yau nice nayi girkin ba mama ba kuma na sha wahala sosai ta k'arasa maganar hawaye na ciccikowa a idanunta tuni rayhan ya manta komai "no Karki min hasarar hawayenki kinsan banaso"to ka samo ci a hankali yake ci suna hira har ya kusan takewa da abinci ta tsiyaya lemu a glass cup ta mika masa "kai my princess kina shagwa'bani shiyasa nake ji tamkar nafi sauran mazan duniya Sa'a da zan mallakeki ,kin iya tattali ,kin iya kwantar da kai ,kin iya girki uwa uba kyau kina bayansu ma kina baiwa kala daban daban ina matukar farinciki da zan mallakeki "ni kuma ina bakinciki da zan yi rayuwar aure da kai tayi maganar a kasan zuciyarta yayinda a zahiri kuwa rausayarwa da idanunta tayi cikin nashi "ka daina zugani fa ,"babu wani batun zuga anan ke din kadarace babba d'azu na samu labarin wannan natattacen saurayin naki yazo .
"wa kenan?
Tayi magana tana yatsina fuska .
"Wannan abokin mah'ruf din mana sai dai naji dadin yadda Abba yayi masa langwa'bar da kai tayi sannan ta mike ta tattara kayan abinci ta shigar dashi kitchen ta dawo "kana nan ne ko zaka wuce ?
"Menene ? Ya tambayeta yana tsareta da idanunshi "ina son zan shiga part dinsu meenal ne" ta bashi amsa tana wasa da yatsun hannunta "okay muje daga nan naje na bawa wannan sarkin fushin hakuri dan yanzu akan wannan yar magana sai ya dauki gaba da mutun ni kuma kinsan ban iya gaba ba .
ba tace masa komai ba suka fito tare ta kulle kofar ta zare key kamar yadda mama ta koyar daita ,tare suka jera suna hira "my princess ya kira sunanta "Na'am ya rayhan "me yasa bakya son shiga gurinsu Khadeeja ne?
ki dinga shiga gurinsu mana kuna gaisawa kamar yadda kike shiga part dinsu menal "tayi jimmmmmmmm tana sauraronsa har ya dasa aya sannan tace "mutun yana zuwa inda ake maraba dashi ne ba inda zai je ana hantararsa da nuna zallar kiyayarsa ba , ta tsaya a daidai lokacin da suka kawo tsakiyar hanyar da zata kaita part dinsu meenal "to ya rayhan anan zamu rabu sai kuma gobe idan Allah ya kaimu ka kular min da kanka ,sannan karka manta da shan maganinka kafin ka kwanta tana gama fad'ar haka ta wuce "wani iri yaji a zuciyarsa saboda yasan maganarta ba akansu Khadeeja tayi ba akan mahaifiyarsa ce ..
Ya ɗan jima tsaye sannan ya juya ya bar gurin ...
Bata wani jima a bangarensu meenal ba ta soma ƙoƙarin barin part din saboda kar mama ta dawo bata sameta ba ,gashi kuma garin ya haɗe da hadari tana fitowa ana fara yayyefi da sauri ta k'araso bakin part dinsu ta buɗe tare da cire key ta shigo sannan ta maida key jikin kofar batare da ta murza ba , ta tsaya tana kakkabe jikinta sannan tayi saman .
Ta shiga d'akin mama ta kwanta akan gadonta tare da lumshe idanunta ko cikakken minti goma batayi da kwanciyar ba muhruf ya shigo da ɗan gudunsa wanda ruwan sama ya koro dicret yana shigowa yayi uwar dakan mama ganinta yayi kwance ta ta kamkame jikinta guri daya yasa ya tsaya akanta tare da tsura mata ido yana kallonta ,maganar muhd Sa'id ce tashiga dawo masa ummita ta dabance acikin matan duniya tafi sauran mata ,komai nata da daban ne aranshi yace dan mata baka ci karo da dukiyar fulaninta ba da watakila haukacewa zakayi ,jin kamshin turarensa da tsayuwarsa akanta yasa numfashinta ya soma barazanar d'aukewa daga gangar jikinta ta ɗan bude idanunta kaɗan taga ita yake kallo har lokacin yana murmushin da batasan ko na meye ba .
a hankali ta bude idanunta ta zuba masa lulu eye's d'insa take ya waske yana sosa keyarsa yayinda murmushin dake fuskarsa ya dauke ya maye gurbinta da kunci da bacin rai, hararata ya sakar mata yana ja tsaki sannan ya soma ƙoƙarin juyawa ya bar d'akin sakamakon ganin ta kamashi yana satar kallonta ya dawo parlourn ya kwanta akan doguwar kujera yana sauke numfashi "meye haka kayi kaje kawai kana kallonta to meye ma dalilin kallon ?
Yayi wa zuciyarsa tambaya yana lumshe idanunshi .
can bayan ruwan sama ya tsaya ya hangota tana saukowa daga saman bene ,yana ganin saukowarta ya runtse idanunshi kamar mai yin bacci ,har sanda ta k'araso ta tsaya akanshi tana kallonsa tana murmushi tana zagayeshi zuciyarta na dauke da lissafi iri iri can data ga alamun zai motsa sai tayi saurin shigewa bayin dake manne da parlour'n ,tayi alwala tazo ta ɗauki hijabinta dake ajiye agun sallarta na parlour'n ta tada sallah .
Zuciyarsa ta cika da mamaki saboda yasan da baya parlour'n kwance a d'akinta zatayi sallah ko d'akin mama yayita lissafi yana nazarin irin kallon data dinga masa mai kamanceceniya da wanda yayi mata ya rasa gane ma'anarsa ta idar da sallah nazarinta yake cikin haka kiran suhaima ya shigo wayarsa ya yunkura hannunsa rike da wayar ya mike tsaye batare daya d'aga wayar ba ya motsa lab'bansa a hankali tamkar wanda bai son yin magana "kije kiyi wanka sarki sannan ki dawo ki sake wata sallah a matukar firgice take kallonsa tana maimaita maganarsa gaba-daya ta rasa a wani mazauni zata ajiye maganarsa ita ba janaba tayi ba , wankan uwar me zata yi ?
har ya bar d'akin idanunta na kanshi tana kallonsa fuskarta da tsantsar mamakinsa naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tare da jan tsaki "aikin banza kawai , kai kasani kinibabbe kawai ni babu wani wanka da zanyi tunda ba jini nayi ba ko iskanci ta mike tana ninke abun Sallah..
*****
Daren ranar kasa runtsawa tayi kamar yadda rayuka da yawa suka tsinci kansu cikin kasa bacci ,ummita tunanin maganar mahruf daya faɗa mata take , Mah'ruf tunanin abinda bai san ko meye ba wanda yayiwa zuciyarsa diran makiya ya hanashi sakat , suhaima tunanin rashin lafiyar mahaifiyarta ga bikinta yana karatowa bata shirya komai ba , rayhan tunanin mahaifiyarsa da ummita yana son kowanensu arayuwarsa , abu mafi bakinciki garesa shine rashin sonsa da ummita batayi ba ,muhd Sa'id soyayyar ummita da tayi masa kamun kazar kuka ,sakina tunani da shawara barin rayuwar mah'ruf ,yayinda hajiya inna ta kwana zazzabin ciwon kai .
washegarin ranar lahadi tun da sanyi safiya mah'ruf ya ɗauki hajiya inna a motarsa sai asibiti , an dudubata tare da bata magunguna , suna kan hanyarsu ta dawowa gida ne hajiya inna ta hango ummita tare da meenal suna tafiya a gefen titi "kaga ja'irar yarinyar nan ji yadda take tafiya akan titi kamar zata balle ko tsoron titi bataji ,tayi saurin yin kasa da glass din motar ,"ke yar agumawa jikar agumawa can inna ta kurma ihu adaidai lokacin da wata mota ta kwaso aguje zatayi kansu wani irin burki mah'ruf ya taka yana dukan sitiyari tare da duban inna da hankalinta gabadaya yake gurinsu "ba zaki masa ba yar banza sai mota ta bugeki kinyi da kanki kamar na miciji, shegiyar yarinyar sai kin haifawa ubanki hawan jini koda yake idan kin mutu ubanki bai da harasa sai wannan uwartaki ..
ummita dake gefe ta watsawa hajiya inna katuwar harara ",ina ruwanki idan motar ta bugeni ?
"Sannan kin damu kanki da agumawa ai suma mutane ne kamarki killa ma agurin Allah sun fiki jin tsoronsa "Inna Lillahi wa Inna lillahi rajiun "babana kana jin abinda shegiyar nan take faɗa min ,ni agumuwa suka fi agurin Allah ? Kai buɗe min murfin mota na fita naci uwarta la'ada waje ,ni wannan yarinyar zatakawowa iskanci irin na mai shayi ya sai da uwarsa ya sai gayen shaye ?
Tana ƙoƙarin bude kofar Mah'ruf ya falla da gudu bai tsaya a koina ba sai a haraban gidan, mah'ruf na bude kofa ta fito ai kuwa tana gama fitowa ta zunduma ihu da kururuwa take mutanen gidan suka fito suna tambayarta "lafiya hajiya inna ?
injiniya dake labary a bangarensa yana karatu ya leko ta window ganin inna ya dafe goshinsa ,sannan ya fito yace kowa ya koma ciki.
Take mama ta dake ƙoƙarin fitowa ta juya ta koma cikin gida ,su hajiya ummah suka cigaba tsayuwa dan lamarin hajiya Inna babu sauki "lafiya inna wannan ihun fa ke da wa ?
"Ina fa lafiya yau a gidan idan baku ci min uban ummita ba hankalina bazai kwanta ba ,wallahi tallahi sai hawan jini ya kamani kai har dogon suma zanyi .. ....
"Kwantar da hankalinki Inna me ummita miki ?
"Wai kamar ni ummita zatace agumawa sun fini daraja agurin Allah ta k'arasa maganar tana kuka ,a gaban babana ta faɗa min haka gashin nan ka tambayeshi idan karya ne ...
Injiniya ya dubi Mah'ruf domin son jin gaskiyar lamari a daidai wannan lokacin ummita da meenal suka shigo harabar gidan .
" Ke ummita da dukkanin alamun fa Inna makirci zatayi miki "sai tayi ta Allah ba tata ba Allah yafi karfinta , ganinsu yasa injiya ɗauke idanunshi akan inna ya meida akansu .
A hankali suka k'araso "sannu da gida dady suka hada baki gurin fadar haka "sannu da gidan uwarki ni zaki kalla a bayyanar nasi kice agumawa sun fini daraja agurin Allah ?
Wallahi yarinyar nan kin cuceni kin gama da rayuwata tayi kan ummita gadan-gadan zata cafkota .
"dan Allah ni inna ki rabu dani ummita ta fad'i haka tana buge hannu inna dake ƙoƙarin sauka ajikinta nan take zuciya ta zowa mah'ruf wuya ransa yayi maseefar ɓaci bai san sanda ya k'arasa gurin ya ɗauke ummita da wani gigitaccen mari Tasssss kake ji batare da yayi magana ba , gaba-daya mutanen dake gurin sai da zuciyarsu yayi tsalle hatta mama dake bangarenta sai da taji gabanta ya fad'i ....
"yauwa babana tsohon albarka ka min daidai wallahi ,kuma sai yau na tabbatar da kana sona kana kaunata , haka nake so ,ka gama min komai tunda ka wanke min fuskar mara kunya da mari wuce muje .
injiniya ya sauke naunauyen ajiyar zuciya ya juya ya wuce shima ransa a bace ,ummita kuwa kasa kwakwaran motsi tayi hawaye ya cicciko a idanunta ta dawo tamkar mutun mutumi a tsaye , ta daina fahimtar komai saboda zafin marin , hawaye ne suka shiga turereniyar fitowa daga kwarnin idanunta "muje ciki meenal ta kamo hannuta itama hawaye na gangaro mata da kyar take d'aga kafafunta kamar yadda mahruf yake daga kafafunshi da kyar yana takawa qirjinsa na kuguden bugu saboda marin da yayiwa mata,bai taba nadamar marinta irin na yau ba , hannunshi ya dunkule guri daya sai da jijiyoyin gurin suka mike gabadaya yana jin tuttukin bakinciki mara misaltuwa .
ummita na isa bangarensu ta zube akan kujera, meenal ta zauna kusa daita tana bata hakuri kanta ta d'aura akan cinyar meenal tana kuka "me nayi masa menal ya mari ..?
"Me yasa baya tausayina ?
"Me yasa yafi son hajiya Inna a kaina ?
"Ki faɗa min abinda nayi masa yanzu ya mareni "bakiyi masa komai ba kiyi hakuri Allah zai saka miki ..
Mama ta k'araso ta tsaya akansu tana tambayar menal "halan ita da hajiya inna ne ?
Meenal ta kad'a mata kai alamun "eh ,nan ta shiga karowa mama abinda ya faru "to ita meye yasa ta fada mata haka ?
"Sauna in fada mata duk abinda inna zata faɗ akan dangina kar ta sake ta tanka bare Inna sa'arta ce maganinta kenan ai baba babba yayi min dai-dai "tana gama fad'ar haka ta hayewarta sama ...
Can bangaren inna kuwa faɗa ne ya kaure a tsakaninta da Mahruf "sai nacin take masa tana fadar "sai yau kayi min daidai babana ka sani farinciki mara iyaka yau " a fusace yace "ai dole kiyi faricikin tunda kinsa baki da gaskiya kin jawo na mareta a karon banza ,
"Dan Allah inna Sai yaushe zaki gane Allah daya ne duk abinda Allah ya kaddaro babu wanda ya ... ?
"Ya isa babana banason jin wannan cacar bakin naka duk ka tofe min jiki da yawo kana wani hakikancewa akan nice ban da gaskiya ubanka nayi mata ko uwarka da zakace bani da gaskiya ?
"Duk ma abinda zakice kice amman wallahi kece baki da gsky me yasa kika zagi mahaifiyarta , na mareta ne ba dan ta rama zagin da kika yi mata ba , na mareta dan ta kai hannuta jikinki kuma agaban dady ,da maganar baki da baki ta faɗa miki wallahi bazan mareta ba , yana gama fadar haka ya juya fuuuuuuuuu a fusace ya fito daga d'akin "ka fashe karewar kunburi mara kunya kawai fitsararre mai wuya awa marikin lema a bakin kofa suka haɗu da injiniya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 76