fito da sauri ya buɗe masa get ya cilla hancin motarsa waje ya fice .. .
"Yana tuki yana mamakin karfin halin Inna ,me yakama nayi wa wannan tsohuwar ?
"Tsohuwar nan ta damu kowa acikin family's da rikinci, tafi ƙarfin zuciyar kowa ,kowa na tsoronta tunkaranta akan zancena da fatlion.
"Nagaji da wannan rayuwar na gaji dan dole nasan abun yi akan aurena , tsoron Allah shine farko akan komai bazan cigaba da biyewa son ran hajiya inna ba .
"Bazan cigaba da sake jin komai daga bakin kowa ba, kawai a bani matata ,idan basu bani nan kusan zan dauke matata tunda abinda take tsoron faruwarsa ba haramun bane ,ya ma rigada ya faru meye amfani cigaba da boyewa ?
Yayi shiru kawai yana tuki yana sake zurfafa tunaninsa zuciyarsa , ke bashi shawara kawai ya bari har sanda cikin ummita zai fito ya bayyana kanshi kowa ya gani ,kada ya ka sake biyewa hajiya inna , da wannan shawarar ya wuce gida .
kamar dai wancan ranar a parloun'n kasa ya iske suhaima kwance hannuta rike da waya bai tasheta ba saboda gudun maseefarta ya shige d'akinsa ....
Duk yadda yayi tunanin zata d'aga hankalinta , sai yaga batayi ba sai ma tarairayarsa tayi wanda bai sani ba tun bayan data yi ta kiranshi bai ɗauka ba ta kira yayarta hajiya rahma , itace ta kwantar mata da hankali "karki ce masa komai idan ya dawo, akwai shirin da nake masa "gaskiya yayarmu bana son aiki irin na wannan babalawo din na mafuluku dan kwata kwata aikinsa baya ci nafi son ki kaini inda akayi miki aikin da kika mallake abbansu Yusuf ...
"Okay ijoko Kenan ? Tace "eh " gaskiya da matsala zaki jira har ya dawo kenan ?
'dan shi baya zama sai bayan shekara shekara yake zuwa amman idan yayi miki aiki sai wani ikon Allah.
"irinsa nake so dan wannan karon har uwar goyonsa da mahaifiyarsa nake son rabawa nan sukayi sallama ta cigaba da neman layin mah'ruf ..
******
Da yammaci ranar ummita da meenal suka kulle kansu a d'aki, ummita na bata labarin abinda ya faru ,meenal tayi dariya har da rike ciki "ai daman nasan kyalesu kawai kikayi da tuntuni kin tada bom ɗinkin da yanzu an wuce gurin "ke dauriya fa nayi kinsan halinsa da hauka da wayo na dinga zuba iskanci ..
"Kin burgeni ta wajena wallahi gara da kika rikeshi ya kwana a agurinki ,nan da zuwa wani lokaci ma da kanshi zai maganta abinda ke ransa ,ke ko bai sonki kiyi kokari ki dasa soyayyarki acikin zuciyarsa dan gaskiya ni banason ku rabu da juna kun dace fiyye da kowani ma'aurata "har ke da abdulshakur ɗinkin ?
Meenal tayi dariya "ina gaskiya anan ban zance komai ba , suka bushe da dariya "kinsan Allah bayan iskancin da n kikayi jiya ki soma kula samari inji cewar meenal zai gane bashi da wayo "me ....? Ummita ta faɗa tana zaro ido waje "samari meenal ta sake maimatawa "gaskiya ban bazan iya ba gudunmawa wannan ba ai kasheni zai yi , ni da nake son na janyo hankalinsa idan ya ganni da wani wallahi zai iya sakina .......
Menal tayi ihu haɗe da rungume ummita ajikinta "wallahi da gaske ta kamu ,ta kamu da son yayana "mtssssss ummita taja tsaki kina da matsala wallahi janyo hankalin da ban soyayya daban tunda yace bazai sakeni ba ai gara nayi abinda zan dan samu matsayi agurinsa amman gaskiya bazan iya daukar wannan shawarar ba ,"ai kuwa dole kiyi , kuma dole ki sanya hannu idan babu saka hannunki komai bazai tafi yadda nake so ba ,kuma ai hakan ma zai sake haukatashi har ki fahimci irin son da yake miki "kai menal bazan iya ba "zaki iya kawo kunnenki kiji shiru ummita tayi tana binta da ido "karki damu ni zan shirya komai nan suka cigaba hirarsu ..
Yana kwance a parlour'nsa kan doguwar kujera mai zaman mutun uku yayi pillow da hannunsa ɗaya yayinda d'ayan hannun ke saman fad'ad'd'en qirjinshi tun daya dawo daga aiki yake kwance agurin yana tunani , abinda ya faru daren
jiya yaki barin kwalkwaluwarsa ,yaki barin zuciyarsa ta huta , duk inda yayi da zuciyarsa tunanin fatlion ne daskare har ta soma masa gizo .
Ya kira suhaima da sunanta yafi sau biyar a dawowarsa gida , shiru dai tayi masa tana kallonsa up and down a lokacin da abun ya faru , shima kallonta yayi kawai dan bashi da mafuta, komai zai faɗa ba yarda zatayi dashi ba ..
A hankali ta sake fitowa sanye da riga iya gwiwarta mai wuyan otanet har lokacin yana kwance a inda ta barshi ta matso gabanshi sosai ta durkusa gabansa tana shafa qirjinshi zuwa kasan mararsa tana murmushin dole wanda yafi kuka ciwo, dan ita kadai tasan bakinciki da zuciyarta take ciki daga jiya zuwa yau
ya buɗe idanunshi da kyar qirjinsa na dokawa yana kare mata kallo tare da kai hannusa ya shafi fuskarta "fat.......... yayi saurin runtse idanunshi tare da furta "oh sorry baby , I don't know what's wrong with me ,but I den mean to hurt you , " ta sauke numfashin bakinciki tana cewa "koma menene bazan damu ba, I don't care about all that saboda nasan soyayyata daban take acikin zuciyarka ,ka soni fiyye da komai , fiyye da kowace mace a duniya ,nice macen ta farko da zuciyarka ta yarda ta kuma amince da ita a matsayin abokiyar rayuwarka , ba wacce aka baka aurenta a bisa sautsayi ba sannan ba dan kana son kasancewa tare daita ba .
"am so different to you habibi ko ba haka ba ? ya lumshe mata idanunshi kawai ,duk da nice na fara dating dinka but zuciyarka ta amince dani , ka sadaukar min da farincikinka...
" duk da haka am sorry nasan babu dadi .
ya k'arasa fadar haka tare da yunkurawa ya mike zaune sanye da kayan shan iska a jikinsa riga hamless da gajeren wando iya gwiwa sai kamshi mayataccen turarensa yake , ta mike ta zauna kusa dashi ya jawo kugunta ya haɗe da nashi yana kissing din gefen wuyanta ,sai lokacin ta ɗan jin sauƙin zugin da zuciyarta ke yi, ya juyo yana fuskantartata hade da sanya kwayar idanunshi cikin nata take idanunsu ya tsarke suna shaƙar numfashin juna , idanunta suka kad'a ta fara lumlumshe su dan bata iya jurar irin wannan kallon daga garesa, da zaran hakan ya kasance komai kwance mata yake taji bata bukatar komai sai shi , shi kanshi ya lakanceta bata iya d'aurewa kallon cikin kwayar idanunshi , "i love you habibinah ta faɗa tana zubewa ajikinshi tana shaƙar Kashim turarensa ,sam bai ji komai ajikinsa ba kamar yadda yake ji idan jikinshi ya haɗu dana fatlion ,ta ƙara shigewa jikinsa sosai ta rungumeshi sun kai kusan minti goma a haka tana shishige masa da yamutsashi , yayinda hakan ke haddasa masa jin haushinta a cikin zuciyarsa, dan shi jikin fatlion dinsa kawai yake muradi a lokacin da zai sameta bakaramin dadi zai ji idan ya tuna yadda ta dinga masa jiya komai kwance masa yake .
Suhaima na kan sarrafa shi qarar wayarsa ta katse abinda take masa, ta kai hannu ta ɗauka tana dubawa , sunan jafar ta gani rubuce akan screen din wayar dan haka ta sauke naunauyen ajiyar zuciya a fili tana mika masa wayar "jafar ne ya amsa yana dubawa ita kuma ta mike ta shiga kitchen .
Tana shiga ta la'be domin jin abinda zai faɗa sai dai bata ji komai ba sai "gani nan zuwa yanzu ta ga ya mike tsaye ya ɗauki keyn motarsa , da sauri ta fito "ina kuma zaka a daidai lokacin nan ta tambayeshi "zan dan fita ne zuwa gurin jafar ,
d'aga kai tayi kawai sai dai da tana da hali gsky bazata barshi ya fita ko'ina ba , dan duk inda zai je yanzu da wuya bai dangana da gidansu ba, amman bata da halin hanashi ya hanu da ta hana "sai ka dawo ka kular min da kanka dan Allah "an gama babynah ya manna mata kiss a goshi ya fice .
kai tsaye unguwarsu jafar ya nufa ,a haraban gidansu suka haɗu yana zaune akan daya daga cikin fararen kujeru hannunsa rike da waya , jafar na ganinsa ya saki murmushin mugunta "kaga na fatlion bada kanka a sare kaje gida kacewa su.......
"dakata dan Allah malam banason haka ya fad'i haka a daidai lokacin daya k'araso inda jafar yake , jafar ya nuna masa kujerar dake kusa dashi "zauna Sarkin miskilanci , kana son yariya kana kaiwa kasuwa , wallahi mah'ruf ka fito ka fitar da abinda ke ranka .
"matsalata da kai kenan jafar rashin fahimta ,"kai ne dai baka da fahimta amman ni tuni nagama fahimtar inda zuciyarka ta dosa, baka taimakon kanka idan ka tsinci kanka cikin damuwa , koda yake wannan kamar a jininku yake kuna cikin matsala amman sai ku bar abun acikin zuciyarku har sai abun yayi muku illa .
"dan Allah jafar me kake son nayi ? Kai da ni musan halin da zuciyarka take ciki akan yarinyar nan ,kana son matarka itama kuma da alamun tana sonka,kai fa gabad'aya na gama fahimtarka so kake sai itace zata fito ta furta tana sonka .......
"Exactly abinda nake so kenan amman batun so babu ina dai son kasancewa tare daita a koda yaushe ...
"ai kuwa wannan matartaka ta fika dakiyar zuciya da d'aurin kai bana tunanin zaka samu wannan damar , sannan ka daina yaudarar zuciyarka akan baka sonta ,kai bani ba har matarka idan tana da hankali da tunani zata fahimci halin da kake ciki ,soyayyar subai'a ta gama kama zuciyarka da komai naka tunda har kana bukatar kasancewa tare daita me kuma ya saura ?
"Ban sani ba ajiye wannan maganar me yasa kace nazo kana son ganina ?
Ajiyar zuciya jafar ya sauke sannan ya maida kallonsa ga mah'ruf yana murmushi yace "abinda yasa na kiraka ina son nayi aure ....kallonsa mah'ruf yayi yana murmushin jin dadi sannan ya rungumeshi "amma naji dadi "a ina yarinyar take ?
" A family dinku take tun lokacin bikinka naganta naji ta kwanta min a rai ya karasa maganar tare da yin shiru .
"uhmm ina jinka "wacece acikinsu Sa'ada , maryam aslamiyya ko Khadeeja?
"Duk babu ko ɗaya acikinsu sakina yarinyar da kaki aurenta a gaskiya ni tamin kuma ina son na aureta ......
"Sakinar gidan baba sarki ......?
"Yes wallahi ina sonta ,soyayyar da bazata misaltu ba nan dai ya kwashe duk yadda yake ji akanta ya faɗa masa ,kallon mamaki mah'ruf yake masa shima jafar tuni ya lura da irin kallon da yake masa " jafar hauka ka soma ko me ?" sakina yarinyar da age mate dinmu ce " so what ina ruwan soyayya da wani age , shekaru ai ba wani abu bane ni dai na gani kuma ina so ,na sanar maka ne dan ka shege min gaba idan kuma bakinciki zaka min sai na sane .
"sorry my friend walkahi haukan naka ne ya bani mamaki "kai aboki ka bar wannan maganar na makance akanta nayi istahara yafi sau babu adadi akanta still the same thing nake ji akainata ,ni bana neman wani kuruciya ko shahararren kyau blessing nake nema arayuwata , idan na aureta zanji dadi .
"lallai kam zakaji dadi ajikin tsohuwa "ka cika maida abu baya wallahi yanzu haka ma so nake ka rakani gurinta ka faɗa mata da bakinka ..
"Baka da hankali wallahi kuma idan ni kake jira na shige maka gaba agurinta zaka dade baka aureta ba sun dade suna tautaunawa daga bisani sukayi sallama jafar nayi masa dariya dan shi da wasa yake masa ɗaya ce ya rakashi gurinta ...
Daga gidansu jafar hanyar gidansa ya dauka yana cikin driving kira ya shigo wayarsa ya dauki wayar ya duba yaga babu suna da kamar bazai ɗauka sai dai ya maida wayar ma'ajinsa sannan ya ja koren maddani ya manna bluetooth a kunneshi "hello ..
Daga can bangaren aka asma da hello mah'ruf ne ?
Yace "eh "
" to wallahi kayi maza kazo gida ga matarka ummita can tare da wani tana zance a bayan conpaund"what ya furta hankalinsa a matukar tashe "wacece ke ?
"Sanin ko wacece yake da mahimmanci agurinka ko matarka ?
Bai sake cewa uffan ba,
hankalinsa a matukar tashe ya dauki hanyar unguwarsu wani irin kishi ya dinga jin yana taso masa "waye wannan ?
"Uban waye ya isa ya wulakanta aurenna ?
yau shi kaɗai yasan yadda zai yi dasu a haukace ya dinga tuki...
Taimakon Allah ne ya kawo shi gidan ..
Yana shigo gidan ko gama daidai tsayuwar motarsa bai yi ba ya fito zuciyarsa na wani irin dokawa da karfi ,jikinsa har tsuma ya nufi inda aka fada masa tun daga nesa idanunshi yake kansu har ya k'araso inda suke ,lokacin da ta ganshi sai da hantar cikinta ta kad'a taji wani irin kuluuuuuuuuuu wani abu ya tsarga mata a ciki take jikinta ya soma rawa, a hankali ya ɗauke idanunshi akan matashin saurayin dake zaune kusa daita ya maida kan ummita dake zaune qirjinta na dokawa da matsanancin karfi .
zuciyar mah'ruf cunkushe da bakinciki jin haushin ganin ko alamun tsoro bata nuna da ganinsa ba ,wani irin zafi zuciyarsa ke yi shi kasan matashin ya firgita da ganin irin kallon zakin da mah'ruf ke masa "wanene kai da har kake da karfin zuciyar zuwa gurin matata ....?
Tambayar da yayiwa matashin kenan wanda yasa ya zabura ya mike tsaye jikinsa na rawa yana duban ummita, ganin bai bashi amsa ba ya nufeshi gadan gadan "uban wa ya naka izinin zuwa gurin matata ?
"malam me kake faɗa ne wacece matarka anan ni sam bam fahimceka ba ka wani gigice ka fita haiyacinsa haka ......
Ai bai dasa aya ba yaji yayi masa wata muguwar shaka " uwarka ce wannan da kake tare daita ko matarka ce ?
TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*MUHAMMAD SALIS BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Page 48
"how dare you tost my wife ? "dont you know she's married ?
"I will teach you a lesson today , not my wife even the dog in my house u can't tost , "don't don't ever try ......
da ganin yadda mah'ruf yake maganar kasan gaba-daya ya gama fita haiyacinsa, zuciyarsa ban da tuttukin zafi da zugin kishin matarsa babu abinda yake .
Shi kuwa matashin idanunsa gabad'aya sun yo waje , yayi bala'in galabaita a hannun mah'ruf ,sai da mah'ruf ya tabbatar da yaji jiki sosai ta yadda gobe idan yaga mai kama da ummita a guje zai falla sannan ya sausauta rikon da yayi masa ...
A matukar firgice ummita ta rike damtsen hannunsa, tana fad'in "ya mah'ruf ka sakar masa wuya wallahi bashi da laifi , bai san hawa bai san komai ba karka kasheshi pls ta fad'a hawaye na zubowa kan fuskarta .
Mah'ruf ya maida idanunshi kanta yana watsa mata wani kallo mai haɗe da harara idanunsa yayi ja sosai, fizge hannunsa yayi yana ƙoƙarin buga kan matashin da bango, ta saki wani razananniyar ƙara tana faɗin "Shikenan zai kashe amad".... ......
zaman dirshan tayi a kasa tana ihu tana yarfa hannu cikin rawar murya take furta "ya mah'ruf karka kasheshi amad ne fa wallahi babu ruwansa , duk shirin menal ne , menal ki kira mama tazo , na shiga uku duk ke kika jawo sai da nace miki no ! no !!" ta k'arasa magana numfashinta na sama da kasa, gani numfashinta na ƙoƙarin d'aukewa ya saki wuyan amad tare da kai wa fuskarsa naushi amad yayi saurin zubewa kasa hannun mah'ruf ya naushi bango runtse idanunshi yayi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ,tsayawa yayi yana kallon ummita da idanunshi da suka kad'a sukayi jajur kamar garwashin wuta, saboda tsansar ɓacin ran da yake ciki......
take jikinsa ya kama rawa yana jin wani matsananci kishinta from know where yana sake bin jinin jikinsa.
da ɗan saurinsa ya matso gabanta kamar zaki ya gurfana a gabanta, ya sanya tattausan hannunsa ya tattarota zuwa jikinsa ya rungumeta tsam tsam yana kiran sunanta cikin wata irin murya mai cike da tsantsar tashin hankali .......
"Fatlion! Fatlion !! kin kuwa san yadda nake jin aurena dake kanki ? "you are so much to me fatlion ,"mai yasa zaki tsaya da wannan da bai kai ni komai ba ? " ki buɗe idanunki nasan kina jina ki bani amsa ...? ya ƙarshan tambayar cikin ƙaraji da masifa tamkar zai shaƙeta saboda haushinta, ba dan darajar cikinsa dake jikinta ba da shi kaɗai yasan irin mugun hukuncin da zai mata,
ko wani namiji ta gani sai ta firgita ....
naunauyen ajiyar zuciya ummita ta sauke jikinta na wani irin kyarrrrma saboda tsawar da mah'ruf ya daka mata ta gigitata, cikin fizgo numfashi ta buɗe kyawawan idanunta fes akanshi
"Ki min bayani akan furucin da naji ya fito daga bakinki mai kama da alamara ya k'arasa maganar yana zuba mata kyawawan idanunshi da suke ƙara narkar mata da zuciya a hankali ta shiga girgiza masa kai tana lumshe idanunta ........
Duk abinda ya faru akan idon meenal ne ,take cikinta ya duri ruwa ,a hankali ta furta "Wayyo Allah" aguje ta falla tayi hanyar bangaransu jikinta na rawa ta shige uwar d'akan hajiya ummah tana sake furta "na shiga uku shikenan ummita zata tona min asiri ,nasan muddin ya mah'ruf ya ji shirinsu akan shi sai yaci ubansu ta ƙarshen maganar tana kai kawo a d'akin kamar wacce tayiwa sarki karya , zariya ta dinga yi daga farkon d'akin zuwa karshen d'aki domin neman mafuta, kafin ya gama da ummita ya dawo kanta .
A matukar firgice mama ta fito sakomakon ihun ummita data jiyo , tana gama isowa inda suke ta tsaya cak tana duban amad dake rike da wuyanshi yana cire wata fuska daban yana fitar da numfashi da kyar kayan dake jikinsa yasa ta fahimci shine , sannan ta waiga inda mahruf da ummita suke suna kallon fuskar juna kai tsaye wajen amad ta nufa ta riko shi tana tambayarsa, shi kuma yana ƙoƙarin cire fuskar da yayi amfani daita.
" amad lafiya me yasa meka haka kake numfashi da kyar ? "Wannnan face din fa na menene tayi masa tambayar gabadaya hankalinta bai Kan ummita da mah'ruf dake durkushe a kasa ..
Shiru amad yayi yana dubanta hankalinsa a tashe "shikenan bashi da mafuta dole sai mama tasan komai kamoshi tayi ta zaunar dashi akan kujera tana sake tambayarsa "Ka fada min me ya same ka? Sannan karar me naji yanzu ? naji Ƙara Sautin ummita tana ihun kiran sunanka?
Da hannunshi ya nuna mata inda suke , tsura musu ido tai tana kallonsu tare da neman Karin bayani "na gansu ai ka faɗa min me ya faru ...?
A hankali ya soma yiwa mama bayani cikin yaren agumanci "Wallahi mama Ina zaune d'azu ummita da meenal suka sameni da wata mgn wai suna son na zauna tare da ummita a matsayin saurayinta ita kuma a matsayin budurwata sannan ko ya mah'ruf yazo ya tambayeni na nuna masa bansan ko ita din wacece ba....... nan ya korowa mama duk abinda suka tattauna a tsakaninsu har zuwa sanda mah'ruf yazo ya damki wuyansa .
"Shi wannan face din fa a ina kasamoshi ?
"Menal ce ta bani ya k'arasa maganar yana shafa wuyansa dan ba ƙaramin jin jiki yayi a hannun mah'ruf ba ,
mama tai shiru cike da mamaki jin abinda ya faru dama da meenal da ummita zasu iya aikata wannan dayen aikin ? muryarta a matuƙar sanyaye ta kira sunan mah'ruf " baba"
ya d'ago idanunsa da kyar ya maida gefen da mama take wanda sai lokacin yasan da zuwanta " ka kwantar da hankalinka amad ne fa"
ya bude idanunshi sosai yana kallon mama da amad ya nuna sa da yatsana yana son yin magana amman ya kasa "ka natsu kaga abinda yasa baka ganeshi ba ,ya sake runtse idanunshi gaba daya shi bai ma tsaya tantacewa ba sbd tsabar kishi daya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 48 Chapter of 76