tsirara kowane rufe da kunba masu tudu da sheki sam babu wani alamun datti a tattare dasu suna nan kamar yadda nashi suke ,lumshe sexy eye's dinsa yayi " bari na shafa miki man zafi ba dan halinki ba ....
ta zumburo masa karamin bakinta tana watsa masa harara cike da shagwa'ba , a hankali ya soma shafa mata man dake sake haddasawa zuciyarta shiga wani yanayi da mawuyacin halin da ita kanta bata san ko meye dalilin da yasa take jin haka ba .
sosai idanunta ya cika da ruwan hawaye saboda zafin dake ratsata , a hankali ya d'ago idanunshi yana dubanta hakan ya tsinci kanshi da girgiza mata kai saboda tarin hawayen daya ga yana kokuwar tsiyoyowa daga kwarnin idanunta , wani irin abu yaji yana fizgarshi da bai taɓa jin irinsa akan kowa ba , tsawon minti biyar ya dauka yana Kallonta hannusa na aikin massaging din kafarta a hankali zuciyarsa ta shiga kwa'be shi tare fahimtar dashi abinda yake aikatawa , wacece ummita agurinsa da matsayin da take dashi wanda ke tattare da kiyayyarta , dan haka yayi saurin dawowa hankalinsa da nutsuwarsa .
Ita kuwa ci-gaba da zubar da hawaye take da shesheka tana bukatar ko dan hakuri ya bata taji sanyi amman ya shareta .
bata ankara ba taji sautin muryarsa "ba zan baki hakuri ba saboda bani nace kar kiyi tafiya a natse ba yanzu ma bansan dalilin da yasa nake taimaka miki ba alhalin babu wannan a tsakaninmu ,idan kika dameni da wannan banzar kukan naki zan bar miki kafarki na kama gabana so that kiyi kukanki da tushe .....
Yayi maganar yana lakatan man zafin a daidai gurin ciwon ya cigaba da murzawa gurin ...
A ranta tace" aikin banza harara a duhu taimako kuma na nawa ?
"ka bar min mana sai me idan ka bari "
Sake d'agowa kanshi yayi yana dubanta saboda jikinsa ya bashi zaginsa take a cikin zuciyarta suna haɗa ido ya watsa mata harara yana murza mai da karfi ,kusan minti goma ya ɗauka yana murza mata gun , yana ƙocƙarin mikewa kenan nan ya rayhan ya shigo parlour'n bakinsa ɗauke da sallama "Assalamu alai.....
Saurin katse sallamar yayi sakamakon ganinsu tare da yayi hannun mah'ruf duka na bisa kafarta ɗaya a matukar kid'ime yake binsu da wani irin kallo mai tattare da alamomi tambaya ,
jin motsin shigowarsa yasa suka d'ago a lokaci ɗaya qirjinsu na kuguden bugu ,a tsanake mah'ruf ya mike ya nufi step batare da yace uffan bare ya kalli inda rayhan yake tsaye yana kallonsu .
Cike da sanyi jiki ya rayhan k'araso ya tsuguna a gabanta "my princess me ya sameki yau ma mahruf ne kou ?
Tuni wasu sabbin hawaye suka sake samun nasarar biyo kuncinta ,jikinsa na matukar rawa ya matso da fuskarshi daf da nata har suna iya shaƙar numfashin juna , tayi saurin kawar da fuskarta tana kallon wani gefen " kiyi hakuri sarauniyyata ki daina kuka nan kinsan bana son ganin kina zubar da hawayeki ,idan ina ganin kukanki zuciyata na kuna ina jin tuttukin bakincikin mara misaltuwa ,ki taimakeni ki daina kuka, kiyi min magana mah'ruf ne sakaki kuka kou ?
Ya sake tambayarta yana juyo da fuskarta tare da ƙoƙarin sanya kwayar idanunsa cikin nata , ta girgiza masa kai "shine kou ? ta d'aga masa kai alamun "eh .
" ki rabu dashi kwana nawa ne da zai daina ganinki gabadaya , idan na killaceki a gidana babu wanda zan bawa damar gane min kyakkyawar fuskar sarauniyata ..
"Zaki zamo tamkar lu'ulu'u ne a gidana , ganinki sai wanda ya shirya saboda ke kadara ce mai girma da mahimmanci ,kadara ce ta kimanin billion's of dollars , koma nace kin zarta haka saboda kinfi sauran matan duniya agu......
Dogon tsakin da aka ja ne ya katsewa rayhan maganarsa a sukwane ya ɗan juyo , ma'hruf ya gani tsaye a kusa da tv yana ƙoƙarin daukar wallet dinsa,
ya cigaba da kallonsa har sanda ya tura wallet dinsa a cikin aljihun wandonsa ,ya dauki agogonsa na fata ya daura a tsintsiyar hannunsa ya nufi kofa domin barin parlour'n .
ya rayhan ya girgiza kai kawai "aikinka kenan bakin rai da mugunta , ki daina shiga shirginsa plz .....
Dan a halin yanzu bana son duk wani abinda zai dinga had'aki da kowane namiji ,nafi son ya zamanto ni kadai ne ,lokacin dana shigo naganku tare zuciyata kamar ta buga ,ina da tsananin kishi akanki subai'a ki tayani kishin kanki kinji .......
Wani haushi da takaici ne ya bakunci ilahirin jikinta gaba-daya maganarsa haushi suka bata , tana zantuttukansa ne tamkar dalma a qirjinta ,ta yunkura ta mike da niyyar barinsa ...
yayi saurin riko yatsun tafin hannunta cikin nashi "ina kuma zaki ki barni bayan kinsa saboda ke na shigo?
Ta yatsina fuska haɗe da jin zafi dan kullun kiyayyar mahaifiyarsa gareta ke sake haddasa nashi tsanara zuciyarta .
ranta a matukar bace tace "daki zani na kwana bana jin dadin zuciyata ,Ina jin kamar zata kama da wuta ,ya rayhan ina jin kamar ma mutuwa zan yi .......
Yayi saurin runtse idanushi yana jin wani iri yasan duk saboda shi take son barin duniya ..
" ki daina furta kalmar mutuwa banason ji ,banason ki mutu ki barni , duk da nima haka nake jin kamar mutuwa zanyi subai'a , yadda nake jin zuciyata din nan bazan yi wani yawancin rai ba , amman nasan ba lallai bane hakan ya zamo sanadiyyar mutuwar tawa ba sai abinda Allah ya kaddaro min jin furucinta yasa ta tsinci zuciyarta da matsanancin tausayinsa "ina laifin wanda yace yana sonka ai yafi makiyinka ,jikinta a matukar sanyaye tace "inshaallahu ma bazaka mutu yanzu ba ya rayhan muna tare muddin rai .......
"Yauwa my happiness haka nake son ji daga bakinki , Allah yasa sai muyi aure naga kyawawan baby's din da zaki haifa min .. murmushin bakinciki tayi wanda ya bayyanar ainihin damuwar da take ciki ,shi kanshi yasan bataji dadin maganarsa ba babu dai yadda zatayi ne "ameen ta tsinci zuciyarta da fadar haka batare da ta sani ba, sannan ta zare yatsun hannunta dake cikin nashi ta nufi step yayi shiru tare da bita da wani mayataccen kallo ..
"Ya san babu digon soyayyarsa acikin zuciyarta tana dai karfin hali ne kawai , shi da zai iya daya ɗauki maganar mahaifiyarsa ya hakura daita , ya barta ta auri cikar burinta wanda take so shi , kuma ya ɗauki qaddarar rayuwa ko mutuwa ......
Ya ɗan jima yana tuni maganar mahaifiyarsa dake cike da aibuntawa akanta , kwata kwata bata son haɗa iri da tsatson mama mairo , babu abinda bata faɗa masa ba ,har cewa tayi sun iske ummita a dakin mah'ruf ta shimfida masa dukiyar fulaninta ranar da yan daban suka kawo musu ziyara amman fur yaki yarda domin yasan wacece ummita sannan yasan waye mah'ruf basu taɓa aikata wani abun asha ba dan cikinsu babu ɗan iska ,Kirjinshi daidai tsaitin zuciyarsa ya rike inda ke masa wani azaɓaɓɓen zafi ya mike tsaye ya fita .....
********
Bamgaren sakina kuwa da kuka ta shiga parlourn gidansu tamkar wacce aka zane , a parlour ta samu aunty Jamila zaune tana kallon tasha arewa 24 , da gudu ta isa gareta kamar wata karamar yarinya yar kimanin shekara sha takwas ko ashirin, alhalin ita din yar shekara ashirin da takwas ce a duniya, ta fada jikin aunty Jamila tana Kuka "subuhanallahi sakina lafiyarki kuwa kike irin wannan kuka? "waye ya mutu a gidan inna ?
Aunty Jamila ta faɗa tana sake rungumota jikinta , sai data ɗauki lokaci tana kuka sannan tace "aunty ma'hruf .....
"Me ya samu ma'aruf din ?
"Aunty ma'hruf baya sona na rasa yadda zanyi dashi "aunty me ye illa ajikina da ba zai soni ba ?
Tayiwa aunty tambayar tana fashewa da kuka girgiza mata kai aunty Jamila tayi alamun babu, "ban da abinki sakina shi so ai babu ruwan shi da jiki , so halitta ne musamman daga Allah, Allah ne yake halittawa mutun a zuciyarsa ki daina kuka nan haka inshaallahu da zarar anyi aurenku dashi komai zai daidaita daga nan kiyayyar ta kare sai dai kibawa wani labari..
"aunty ma'hruf ba zai taɓa sona ba ya faɗa min da bakinsa "
aunty Jamila tayi saurin katse maganar kar mahaifiyarta taji, abinda bata sani ba kamar a kunne Hajiya sukayi , takaici ya kamata taji kamar ta mutu tsabar takaicin sakina ,ta k'araso inda suke zaune " wallahil azim aunty ina son shi idan.....
"Allah ya wadaran naka ya lalace sakina kinyi hasarar rayuwa , suka tsinkayi maganar Hajiya a tsakiyar kansu ,"baki gama kuka ba wallahi sai kin aurensa ya gallaza miki azaba a gidansa tukunna , ba dai kin iya naci kamar bakar kaska ba, yaro yace bai sonki , ya nuna miki da ido, ya nuna miki da gangar jikinsa har ya ya furta miki da bakinsa amman dan naci kika ce kinji kingani ..
"ni mahaifiyarki ce matukar kika rabu dashi wallahi bazan yi kaffaran ba zaki samu wanda yafi shi kuma ya soki fiyye da tunaninki amman idan kin ce zaki nace akanshi bismillah ga fili ga mai doki kece zaki kwana aciki maseefa dan kuwa bazaki ga daidai ba tunda baya sonki , a wannan zamanin namiji da kanshi yace yana sonka yaya ka kare a gidansa bare an nace masa ?
"Haba yaya Karki mata baki mana kefa uwa ce " aunty Jamila ta katse hajiya kema kinsan wannan auren idan kinga an fasa shi wani ikon Allah ne ,amman babu wanda ya isa ya hana auran nan , duk mun san halin baba Sarki sarai baya magana biyu gara ma kiyi mata addu'ar samun kwanciyar hankali a gidansa tunda magana tayi karfi .
naunauyen ajiyar zuciya hajiya ta sauke tana duban sakina " banki ta taki ba aunty yara amma tayi tunanin auren namijin da bai sonta ,ba kuma zan gaji da bata shawara ba ,"ki saki ranki ki rabu dashi Allah zai miki zabi wani mai sonki idan kika ɗauki maganata Allah zai duba lamarinki, amman idan kin nace masa wallahi babu ruwana tayi maganar cike da gargadi ..
"Haba yaya dan girman Allah ki daina fadar haka yaya kike son tayi yanzu ?
"Tasan yadda tayi akayi maganar auren tun farko yanzu ma ta koma can ta warwaresa shine samun saukinta , tana gama fadar haka ta juya tayi d'akinta...
da wani sabon kuka sakina ta fashe dashi
Aunty Jamila na rarrashinta"Kiyi hakuri kukan ya isa haka sannan shawarata gareki ki nemi zabin Allah idan auran ma'hruf alkhairi ne arayuwarki da addininki Allah ya tabbatar miki ..
maza kije ki bawa mahaifiyarki hakuri ranta ya ɓaci sosai dake ..
A hankali sakina ta mike jikinta a matukar sanyaye ta soma jan kafa hawaye na gangaro mata dan dole ta yakice soyayyar ma'hruf a zuciyarta idan so cuta ne ai hakuri magani ne .
zaune ta iske mahaifiyarta bayan ta tura kofar dakin ta shigo ta karasa , ta durkushe bisa gwiwowinta cikin zubda hawaye "hajiya ki yiwa Allah kiyi hakuri ki yafemin inshaallahu zanyi ƙoƙarin cire ma'hruf acikin zuciyata dama rayuwata gabadaya , nasan nayi kuskure tun farkon dana tsinci kaina a duniyar soyayyarsa ban nemi zabin Allah ba amman har yanzu ban makara ba zan mikawa Ubangijin daya halitta min kaunarsa gareni zabi mafi alkhairi, ki taya ni addu'a kada kiyi fushi dani Ki ya femin hajiya ta k'arasa faɗin hk tana sake rushewa da matsanancin kuka .....
" Shike nan sakina kukan ya isa haka,daman baki min laifin komai ba ,Allah yayiwa rayuwarki albarka yayi miki zabi mafi alkhairi idan shine alkhairi Allah ya tabbatar idan kuma bashi bane Allah ya musayan miki da mafi alkhairi , kuskure rashin yin istahara domin neman zabin Allah kenan , istahara na da matukar muhimmanci barin ma akan aure, "inshaallahu zan tsananta addu'a tashi kije d'akinki hajiya tayi Maganar tana tausayawa diyarta ..
Daren ranar sakina bata runtsa ba , kwana tayi tana kaiwa Allah kukanta , sannan zuciyarta cike take da ɗaukar shawarar mahaifiyarta "me ye amfanin auren mijin da bai sonka ?
"Babu zuciyarta ta bata amsa da hakan ,lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo mata "kada ki kashe kanki da tunanin mutumin da bai san da zaman rayuwarki ba ..
Ta jima sosai tana addu'a tare da kudurcewa zuciyarta zata barshi har abada ..
*****
Bayan kwana uku da yammacin Abba yana zaune a dakin shakwarsa , jaridar daily trust ce rike a hannunsa , yaga shigowar mota haraban gidan , yayi zaton ko bako yayi ,ya mike ya leka ta window sosai ya sheida fuskar matashin yaron ,ya jima yana kallonsa kallo irin na tausayawa da jimami , ganin matashi kyakkyawa karfafafa lafiyayye ma'abocin siffa da kamala kamar ma'hruf dinsa ya tsinci kanshi cikin zazzafan so , babu yadda zai iya koda rayhan bai furta son ummita ba akwai wanda zuciyarsa yake da muradin mallaka mata ....
Ya matsa daga jikin window jikinsa a sanyaye ya fito fuskarsa babu yabo babu fallasa muhd Sa'id ya fito daga cikin motarsa cikin rawar jiki ya dukar da kanshi a kasa ya gaisheshi tausayin muhd sa'id ya kama Abba sai dai tuno dan d'an'uwansa da kuma halin da ita kanta ummita take ciki akansa dan har tafi yarda da rayhan akan shi .
Abba ya amsa gaisuwarsa tare da cewa "Muhd Sa'id ko? Ya nuna shi da yatsa
"Eh Ni ne Abba " "abinda nake so in sanar da kai duk dai nasan ma'hruf ya sanarmaka yanzu tuni dai zama ,kar na sake ganin koda mai kamarka a kofar ........
take jikin muhd Sa'id ya dauki rawa ya sake dukar da kai "dan girman Allah kayi hakuri ni da aure nake son subai'a ....
Abba ya katse shi da cewa " 'ya dai tawa ce kuma abar ikonna ce da kace tana subai'a tana sonka ne bazan hanaka ba amman subai'a ta nuna bata ra'ayinka bugu da kari nayi mata miji bazan iya hana dan dan'uwana na baka ba ....
"Dan Allah kayi hakuri karka matsawa rayuwarta zuwanka na firgita min yarinya kaje gaba Allah zai baka wata ina maka fatan alheri ".
Ya juya cikin gida yana kwalawa ma'hruf kira ........
TWO FRIEND'S (BSBS)h
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
https://youtu.be/-Xy64PJiHiQ
domin sauraron abinda muka daura a YouTube danna blue din rubutun dake sama. 👆🏻
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*MAMMAMU MAMA MAI VOICE ,ALLAH YA QARA MIKI LAFIYA, MUNA JIN DAƊIN KASANCEWA TARE DAKE, UWA UBA D'INBIN ADDU'OINKI GAREMU, GODIYARMU BAZATA MISALTU BA , IDAN ANA NEMAN UWA AKA GANKI AN GAMA ,DOMIN KUWA KE DIN UWA CE DA KIKA SAN HAKKIN YA'YA , ALLAH YA BAR MANA KE MAMA MAI VOICE 😄😄😄,KI CIGABA DA SAMBADO MANA ADDU'A, DA FARANTA ZUKATANMU BEST MOMY A DUNIYARMU*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 27
....... Mah'ruf dake kwance a d'akinsa a saman tintimemiyar katifarsa yana kallon wani amercan film the hobbit kasancewar weekend ce, ya tashi da sauri sanye da gajeren wando baki iya gwiwarsa ya soma ƙoƙarin ɗauka rigarsa dake rataye ajikin hanger ya d'aura a saman farar singlet din dake sanye a jikinshi ya fito da sauri zuwa harabar gidan in da yafi zaton daga nan sautin muryar abba ya fito .
ya k'araso garesa cike da ladabi da biyayya "Abba gani " tare da aunawa muhd Sa'id ƙatuwar harara ta kasan idanunshi sobada yasan kiran ba zai wuce akansa bane.
Abba ya dubi mah'ruf "baka shiedawa abokinka sakona bane ? Muryar mah'ruf a kasalance yace "na faɗa masa Abba ya k'arasa maganar yana tamke fuska tamkar bai taɓa murmushi ba .
muhd Sa'id daya dawo kalar tausayi a tsaye a gurin ya kalli fuskar mah'ruf kamar zai yi kuka sannan ya sake dukar da kanshi kasa yana jin kamar zuciyarsa zata buga , shi kanshi da yana da hali da tuni ya cisge soyayyar ummita dake addabarsa ya hutawa rayuwarsa ...
abba ya sake juyowa inda muhd Sa'id yake "wannan shine karo na karshe da zaka tako cikin gidana da sunan kazo gurin ummita ,duk abinda zai kawo ya tsaida kai a wajen gidana ban lamuncewa shigowarka ba fatan ka fahimceni ?
"kai kuma baba babba maza kaje gurin mammanka kace ta bada kayan yaron nan daya taɓa kawowa ummita yana magana yana nuna muhd Sa'id da ɗan yatsansa wanda ya gama haɗa gumi sharkaf tamkar wanda ke cikin tsakiyar rana ..
"bana bukatar komai naka ina fatan zaka mutunta umarnina ?
Yana gama fadar haka ya juya a hankali yayi cikin gida a hanya sukayi kicibis da sadam da sadik da mah'ruf tare da kaya niki niki saboda yawonsu ba zai iya d'auka shi kadai ba .
Abba ya wuce tare da fad'in " maza ku kai masa kayansa bai tsaya ba ya cigaba da tafiya ya nufi cikin gida, mah'ruf na biye dashi a baya yana bashi hakuri saboda ya lura ransa yayi matukar ɓaci ,tunda yake bai taɓa ganinsa cikin ɓaci rai irin na yau ba, Abba bai saurari ma'hruf ba ya shige bangarensa .
Cike da sanyin jiki ma'hruf ya dawo inda muhd Sa'id yake tsaye har lokacin ,ganin halin da yake ciki yasa gwiwarsa yin sanyi, shi daya dawo da niyyar yi masa bala'i sai ya dawo rarrashinsa " haba muhd Sa'id yarinyar nan na faɗa maka Abba yayi mata miji ,a sanin dana yiwa Abba baya magana biyu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 76